Turken gida book 3 cmplete - Chapter 6
Turken gida book 3 cmplete Chapter 6: Turken gida book 3 cmplete Chapter 6. "Me ya sa kike haka ne?
3,283 words
"Me ya sa kike haka ne?
Ya faɗa ya na tsareni da idanuwansa a kaushashe ya cigaba da faɗin.
"Fahimtar juna nake so mu yi Sadiya. Ni dake ba shekaranjiya muka faro rayuwar nan ba, ba kuma jiya ba ne, ba kuma yau ba ne. Sabo da haka maganar komai ya wuce ni dake mun san ba haka ba ne ko?
Ya gama faɗa ya na mai tsare ni da idanuwansa kuma ya kama hannayena ya riƙe ba halin na ƙwaci kaina.
"Haka ne"
"To ki yi magana domin mu fahimci juna."
"Na ce ba komai fa"
Na faɗa ina kauda kaina sai ga shi ya saka hannu ya dawo da fuskata zuwa in da yake.
"Ni na san akwai komai fa"
"To mene ne? Komai ya wuce tun da na haƙura ga shi ni da kai muna zaune a waje ɗaya."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Komai bai wuce ba. Saboda na yi miki mganganu ranar marasa daɗi kuma na san har ga Allah ke ma ranki ba zai yi miki daɗi ba.'
Ashe ya san abin da ya yi? Shima ya san bai kyauta ba! A lokacin ya sani ko sai yanzu daga baya."
"Raina ne ya ɓaci a ranar har na kasa fahimtar ki sai daga baya da na zauna na yi tunani sai na fahimci ni ne ban kyauta ba sannan na yi miki rashin adalci."
Ƙura masa ido na yi, hawaye suna taruwa a ƙwarmin idanuwana. Maganganunsa na baya suna mini amsa kuwwa kamar a lokacin yake faɗa mini.
"Na yi kuskure. Kuma na gane kuskure na don Allah ki yi haƙuri ki manta komai."
"In manta komai fa ka ce?
Na katse shi cikin rawan murya.
"E ki manta na ce. Ki ɗauka na faɗa ne a fatar baki amma ba har cikin zuciya ta ba."
"Har gorin haihuwan da ka yi mini Yusuf? Har cewan da ka yi ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴanta? Har goran ta mini da ka yi na cewa ba kai ka ce na je na yi planning ba ni na saka kai na? Har shi na manta har shi kake so na manta kamar komai bai faru ba?
Sai ya kasa mgana na ƙura masa ido, amma ya dukar da kaina ya na faɗin
"Ki yi haƙuri ɓacin rai ne."
"Sai ɓacin rai ya sa ka yi mini gorin gida Yallaɓai?
Na faɗa ina mai kecewa da kuka. Kukan da ke taso mini daga ƙasan zuciyata. Kukan sanadin rasa gudan jinina kukan ɓacin rai da baƙin ciki da mganganun Yallaɓai suka dasa min a cikin zuciyata.
"Ka rufe idanuwan ka. Ka manta da ko planning ɗin da na yi da amincewar ka na yi. Kuma in da na tara sanin haka zai faru da ni zan yi har jawo mini matsala ne? Kuma ka sani ko ban yi ba in Allah ya ce Jidda da Baby kaɗai ne rabona na ƴaƴana a nan duniya ba ni da yadda zan yi kokawa da kaddara ta. Kuma ka ce ina baƙin ciki da Gimbiya da ƴaƴan ka, wannan kam sai na ce ba ka yi mini adalci ba ban taɓa zama da matarka da wata zuciyar ba sai zuciyar musulunci su Khalipa kuwa ɗaya suke da su Jidda a wajena. Amma rana ɗaya kuskure kaɗan da kai ne ka yi amma ka rufe idanuwanka ka ce ba na son jininka. Sannan daga ƙarshe ka yi mini gori. Gorin nan gidan uban su khalipa ne ni kuma ba gidan ubana ba ne.'"
Na dakata ina shessheƙan kuka ina ji ya na damƙe hannayena da ke cikin na shi alamun rarrashi amma bai hana ni kuka ba.
Na nuna saitin zuciyata ina cigaba da faɗin.
"A nan mganganun ka suka yi min illa. Ban taɓa tunanin irin ta ka martabawan ba kenan Yusuf. Na ɗauka ni ina da ƙima da karamcin da za ka guji faɗa mini kalaman da za su sosa mini rai in har kana yi min karan shekarun da muka shafe ni da kai muna zaman aure. Ni da kai mun wuce karnin soyyayya mun koma abu ɗaya. Abu ɗaya Yallaɓai."
Na ƙarishe ina mai cigaba da kukana sai na ji kamar lokacin ne ma lamarin yake faruwa.
"Ki yi haƙuri. Sharrin sheɗan ne."
Ina jin sa amma ban yi magana ba ina cigaba da kukana, sai ga shi ya matso kusa da ni ya rumgumeni ya na faman lallashina.
"Am sorry."
"Ki yi haƙuri don Allah ki yafe mini Sadiya ta."
Sai kawai na ƙara karfin kukana ina ƙokarin ƙwace kaina daga riƙon sa amma shi bai sake ni ba.
"Wallahi ni kaina na azabtu da kalaman da na faɗa miki. Sharrin zuciya ne."
Hannayena na saka duka biyu ina dukan shi a ƙirji lokaci ɗaya ina kuka har da sheshesheƙa.
"Sharrin zuciya ne ya sa ka yi min goron haihuwa? Ƴaƴana biyu fa, ko a haka Allah ya bar ni na gode masa kuma ko garke Gimbiya za ta haifa maka wallahi ni mai farinciki da haka, ban taɓa jin zan yi baƙin ciki saboda ka samu ƙaruwa da wata matar ba ni ba. Illa ni mai farinciki be ina cewa jinin ka jinina ne, duk ɗaya na ɗauke su da su Jidda. Amma kai zuciyarka ta saka maka bambamci Yusuf."
Na faɗa ina ta dukansa ta ko'ina kuma bai hana ni ba sai da na gaji don kaina sannan na lafe a jikinsa na yi laushi.
"Ki yi haƙuri ina mai neman afuwarki."
Ya yi ta nanata na yi haƙuri har sai da muryansa ta dishashe nima nawa ya daɗe da disashewa saboda kuka.
Ɗago kaina ya yi ya na share mini hawaye.
"Ba zan ƙara ba. Kin ji ko?
Ya faɗa ya na matse mini fuska sannan ya sumbaci goshina. Sai kuma ya gangaro wajen laɓbana ya na sumbatata. Ban buɗe masa bakin ba sai na datse shi kuma sai ya kalleni ya na faɗin" Ba ki maraba da ni ne? Ko ba ki haƙura ba ne?
Ina kallon shi saboda akwai hasken a ɗakin shima ni yake kallo na tsawon wani lokaci.
"Na tsufa Yallaɓai me za ka ji in ka maraban ce ni?
Ya buɗe baki da sauri zai yi magana na yi saurin rufe masa baki da hannuna guda ɗaya.
"Yaushe rabon da ka neme ni mu yi ɓarnan ruwa? Na tsufa ko? Ko na ƙafe ne yanzu babu danshin ruwa?
Na faɗa ina zubar ƙwalla da sauri ya fizge bakin shi, yana kallona na buɗe baki na yi magana ya damƙe bakina ya shiga sumbata na da karfi da karfi lokaci ɗaya yana sabule min rigar barcin da ke jikina. Sumbatata yake yi da zafi zafi tun ina tamke bakina har dai na saki na ba da kai bori ya hau. Bai saki bakina ba sai da ya kai ni kwance bayan ya raba ni da rigar jikina. Ina haki ya na haki, ya dakata ya na kallona. Ya yi wurgi da gajeren wandon da ya cire daga jikinsa. Ni da shi naked muna kallon duka jikin mu abin da ba mu taɓa yi ba in za mu ribaci juna sai a cikin duhu ba mu taɓa kaɗaicewa da juna cikin haske irin na yau ba.
"Ni za ki faɗa ma kin tsufa Sadiya? Ni na ɓare ki a leda kina ƴ'ar yarinyar ki. Ni ma ke kika ɓare ni a leda ina saurayina. Sadiya ko wajen babu danshin ruwa ni Yusuf zan da dasasa shi har sai na ɓulɓulo da wannan danshin"
Ina shirin mgana ya saka nauyin ƙirjinsa ya danne ni. Lokaci ɗaya ya na haɗe nipples ɗin sa da nonuwana. Har tsakiyar kaina na ji abin ban dawo hayyacina ba na ji ya ƙara kama bakina, komai da zafi zafi yake yi mini alamun yau in na shiga hannu sai na gane ba ni da wayau. Ai ko na gane domin da gaske ya ke ko ba danshi sai da ya ɓulɓulo da wannan danshi na yi ta zubar ruwa. Ranar ba in da Yallabai ba lashe a jikina ba hauka ne kawai ban yi ba amma har ihu sai da ya sakani, kusan fa famshe duk kwanakin sa ya yi, da ya sauka muna gama sauke numfashi sai ya sake damƙo ni da na fara masa magiya sai ya ce ai na ce wajen babu danshi to danshi ya ke so ya ɓulɓulo mini da shi.
Da hasken wutar lantarki muka yi komai yana kallona ina kallon shi ni da na ji nauyi sai na runtse idanuwana muka daina haɗa ido da shi bai ƙyale ni ba sai da ya ce na yarda ban tsufa ba? Na yarda ko mun tsufa za mu iya samo wannan danshin ruwan na ce masa na amince sannan ya sarara mini sai da na yi gashi. Dukkan mu sai da muka tsarkake jikinmu muka saka wasu kayan barcin muka koma muka kwanta maƙale da juna. Zuciya ta yi sanyi duk haushin da nake ji a kan Yallabai ya tafi ban ma san in da fushin na wa ya je ba, amma na danganta haka da yadda ya fahimci ya yi laifi kuma ya ba ni dama na yi magana ya ba ni haƙuri. Barci muka yi cikin salama makale da juna wanda mun daɗe rabon mu da wannan yanayin.
Ko bayan sallar asuba sai da Yallaɓai ya sake biyo danshin nan ta bakin shi, bayan mun gama ne muna sauke numfashi ba mu ma tsarkake jikin mu ba a lokacin kaina na saman hannunsa na hagu da ya rumgumo ni da shi.
"Yallaɓai."
"Uhm"
"Ranar da na je kaduna."
"Uhm"
Ya sake faɗa kamar mai jin barci.
"Na samu miscarriage"
"Uhm"
Sai kuma na ga da sauri ya mike zaune har ya na wancalar da kaina sai kuma ya saka hannu ya ta da ni zaune ina mai danne kafaɗuna da duka hannayen shi guda biyu.
"Me kika ce"?
Ina murmushi na ce" Na ce na samu ɓari a kaduna. Cikin wata ɗaya ne ni kaina ban san dashi ba sai da ya fita."
Ƙura minI ido ya yi kafin ya ce" Da gaske kike yi Sadiya? Ya faɗa da wani irin murna a muryansa. Sai na gyaɗa masa kai alamun haka ne sai kawai ya rumgumeni ƙamƙam yana faɗin. "Alhamdulillah." "Ka ji abin da na ce da kyau Yallabai? Na faɗa ina tantama in ya fahimci na ce ɓari na yi.
Sai da ya saki rumgumar da ya yi mini ya na kallona sannan ya riƙe hannayena yana dariya ya ce" Na ji da kyau. Kin yi barin ciki ko Sadiya? Sai na gyaɗa masa kai sai kawai ya ce" Ina farincikine ne a ƙalla dai ina da yaƙinin za ki sake haihuwa zan sake ganin ki ɗauke da cikina Sadiya" Murnan da ya yi ta ba ni mamaki ban taɓa tunanin zai yi murnan in na ƙara samun ciki ba.
"Na yi kewar laulayin ki. Fushin ki in kina da ciki na yi kewar ganin kumbararun kafafuwanki. Na yi kewar ganin cikin ki ya turo Sadiya. Ina kewar ganin kina shayar da Baby everything da kika sani ina kewar shi a tare da ke"
Hawaye suka cika min ƙwarmin idanuwana.
"A ƙalla yanzu zan ta saka hop. Sannan zan ƙara dakewa ko?
Ya ƙarishe faɗa yana mai shafa jikina. Shi murna kawai yake yi.
"Kai ba ka jimamin rashin cikin da muka yi?
Sai sannan ya ɗan sauya fuska kafin ya ce" Na yi jimami sosai amma me ya fitar da shi? Wannan tafiyar da kika yi ranki a ɓace ko? Ban ba shi amsa ya saka hannuna ya ɗan mari kan shi yana faɗin" Ni ne ko ? Ni ne ko? Sai kuma ya koma ya kwanta a kan cinyata ta wajen cibiyata ya na faɗin" Ni ne na ɓata ma Umma rai, laifina ne da ya sa muka rasa gudan jinnin mu. Sadiya ki yafe mini"
Ya faɗa lokaci ɗaya ya na rungumo cikina zuwa kuguna. Sai na shafa kan shi cikin tattausan lafazi na ce" Ba laifinka ba ne daman can Allah ya yi ba mai zama ba ne."
"Kuma Allah zai ba mu wani ka ji ko?
Sai ya ɗago ya na kallona kafin na gyaɗa masa ina faɗin" In sha Allahu. Kar ka damu.' Sai ya sake komawa ya kwantar da kansa a cinyata yana faɗin" In sha Allahu ma ya bi cikin danshin ya shige.
"Me?
Na tambaya ina kallon shi.
Cikina ya shafa kafin ma ya yi magana na samu amsana sai na samu kaina da amsa wa da Allah ya sa. Duƙawa na yi da kaina na sumbaci goshin sa.
"Ina ƙaunarki Sadiya ta."
"Nima haka."
"Kema me?
"Ina sonka Yallaɓai na."
Na faɗa ina yi masa murmishi, shima kallona ya ke yi cike da so da ƙauna. Muna wannan kwanciyar ta soyayya na zayyane masa abin da ya faru a Kaduna da kwanakin da na yi a gadon asibiti.
"Ban ji daɗi da ba ni na wahala da ke ba."
"Haka Allah ya so."
"Allah ya saka ma Amina da mijinta da alheri."
"Amin Amin."
*****
Shike nan faɗa ya ƙare tsakanina da Yallaɓai ni da na ce ko na yafe masa ba zan manta ba sai gashi tuni na manta na kama mijina gam mun fi ma baya ɗinkewa da nuna ma juna soyayya. Jidda kam ta na lura da mun shirya ranar har tsiya ta yi mini da ta ga na kira mai ƙunshi har gida ta na yi mini buɗe bakin yarinyar sai ce mini ta yi.
"Su Umma manya an gama fushi da Abba kuma yanzu an dawo ana yi masa kwalliya."
Da na balla mata harara sannan na rakata da daƙuwa sai ta shige ɗaki tana mini dariya. Da Yallaɓai ya dawo sai da na faɗa masa shima dariyan ya yi ta yi kafin ya ce" Ahto da gaskiyan uwata an gama min yanga da jan Aji an ga dai ba wani sai ni an dawo mini." Da ya faɗi haka sai da na maka masa filon da ke hannuna ina kunƙuni ina cewa zan dai yi maneji da shi, shi ko ya ce ko yanzu ya tashi ƙara aure zai samu budurwa ni kuma in na samu tsoho ma na gode Allah domin duk ya gama suɗe danshin haka na yi ta maka masa filo amma bai yi shuru ba sai da ya ƙarisa ai ko ya daku da filon kujera.
Amina ma sai da ta yi mini shaƙiyanci daga ta kira muna waya ina faɗin Yallaɓai ma ya ce a yi musu godiya ita da Dr. Sai cewa ta yi" Ya Sadiya wai kin yafe ma Yallaɓan ne da har kika bashi labarin kin samu ɓari?
"To ya na iya Amina. Ya yi ta bani haƙuri sannan ya ce sharrin sheɗan ne shi ya sa na haƙura."
Sai kawai Amina ta fara mini dariya.
"Nan fa kika ce har abada ba za ki manta da abin da ya yi miki ba."
Cikin masifa na ce" Ai ban ce na manta ba na dai ce na yafe masa. Kuma kowa ai yana kuskure ko? Ganin ta mai da ni mahaukaciya ya sa na kashe wayata ina masifa. Ni kaina ina mamakin yadda duk yadda na kai ga ƙullatan Yallaɓai da ya zo ya lallasheni ya ba ni haƙuri shike nan sai na ji na haƙura sannan na manta da komai mun cigaba da rayuwarmu kamar komai bai faru ba.
Ganin mun shirya ya sa na ce ya dawo mini da ɗana Khalipa. Ya na jin haka washe gari sai ga Gimbiyar ya kwaso mini ita da yaran gabaɗaya. Nan suka yi mini yini, har dare muna tare ranar kuma Yallabai ya na gidana ne daddare muna falon Yallaɓai yaran kuma suna falon su sai ga Baby ta zo kawo min ƙaran Khalipa wai yana mini tsalle saman kujera.
"Ƙyale shi Baby shima gidan su ne ki bar shi ya shaƙata"
Yallabai ya gano mgana na tusa masa ita kums sai ta miƙe tana faɗin don ya na gidan su ai ba za a bar shi ya yi ɓarna ba. Da motar ta ta zo bayan isha'i ta tuka kanta da yara suka koma gida Khalipa da na ce a bar mini shi ta ce jibi za su tafi Rano ganin kamar ba ta son barin na shi ya sa sai na ƙyaleta Yallaɓai kuma na ji amma bai yi mgana ba.
Sai da muka yi shirin kwanciya sannan Yallabai ya yi maganar akan maganar da na yi ɗazu a kan Khalipa.
"Laa Allah ni ba da wata munafa na yi mganar ba."
"Uhm to shike nan tun da kin ce haka."
Da haka a ka bar maganar amma na ji sanyi a raina tun da ya fahimci in da magana ya dosa. Ni dai ban san ya abin ya ke ba amma ranar da Khalipa ya zo gidana zai kwana da ya yi barcin uban ya kai shi ɗakin su Jidda ya kuma ce ko zai yi kukan jini su bar shi in ya gaji zai kwanta. Sai ga shi ranar barcin mu ka sha, sai da safe Jidda ke faɗin ya tashi yana rigima ya na kiran sunan Abba da ya ga an yi banza da shi ne ya koma ya kwanta. Tun daga lokacin na samu lafiyan Khalipa a raina na ce daman iskanci ne da na yi shuru da yanzu an daɗe ana cuta ta.
Ganin mun samu jituwa da Yallaɓai a wani dare da yana gida na bayan mun gama samun natsuwa sai na ce masa ina so zan koma makaranta.
"Makaranta? Wata makarantar? Islamiya?
Yallaɓai ya tambaya cikin mamaki.
"A'a boko dai. Masters nake so na koma na yi."
Kawai ba sai Yallaɓai ya fara mini dariya ba sai ka ce ya ga mahaukaciya sabon kamu nan da nan na harzuƙa.
"Mene abin dariya a mgana ta?
Sai ya dakata yana faɗin" Ki yi haƙuri amma mganar ce ta ba ni dariya ke yanzu gotai gotai da ke da budurwan ƴ'a ki ce za ki koma makaranta?
"To ana girma da karatu ne?
"A'a kawai dai."
Sai kawai ya cigaba da dariyan shi. Na cika na yi fam ina shirin fashewa.
"Kin ga yi haƙuri."
"Izinin ka na ke nema shekaran da za mu shiga nake so na koma."
"To ai ni ba zan hana ki ba amma da zan ba ki wata shawara."
Sai na kalle shi ta wutsiyar ido duk da akwai duhu a ɗakin amma muna kallon juna ta hasken dake shigowa ta jikin labulan window ɗin bedroom ɗin.
"Kina so?
"Ina jin ka"
Na faɗa a daƙune.
"Ki haƙura da karatun nan Sadiya. Digree gare ki fa yanzu mata ne nawa ne ke neman kwalin karatun ki ba su samu ba? Komawa makaranta abu ne mai kyau amma wahala kawai za ki ƙara ma kan ki a yanzu. Saboda ƙwaƙwalwar ba za ki haɗa ta da lokacin baya da na yanzu ba?
"Wannan ne shawaran?
Na faɗa ina kallon shi domin so na yi ma na juya masa baya.
"Shawaran ita ce ki bari kawai na ƙara miki jari ki cigaba da kasuwancin sai da hijaban ki kawai "
Ya gama faɗa har yana wata dariya. Raina ya ɓaci na ƙufula.
"Ka ba ni izinin na cigaba da karatun?
"Why not in kina sha'awa? Sai na ce Allah ya ba da sa'a."
"Amin"
Na fada azafafe sannan na juya masa baya sai ya biyo ni ya na faɗin" To jarin fa? "Ba na buƙata" "To shike ko kuɗina sun huta" Ya faɗa yana mini dariya kara shige min ya yi yana tsokanata da Sadiya ta masu mastars ke dole sai kin kamo kwalin karatuna ina jin sa na yi masa banza domin haushi ya ba ni ya ina mganar cigaba na kuma yana mini dariya.