Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 5

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 5

Turken gida book 3 cmplete Chapter 5: Turken gida book 3 cmplete Chapter 5. Na faɗa ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daɗe, ni kaina ban…

3,374 words

Na faɗa ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daɗe, ni kaina ban samu kiran shi ba sai a lokacin har ya ba ni Baba Aminu muka gaisa da shi yana ta saka mana albarka.

Ina shirin tafiya sai ga saƙon naman suna da yawa daga gidan su Saude har da omo da sabulu na Gwaggo. Da zan tafi tare da Gwaggo muka shiga gidan ta yi ma Saude barka a nan na bar ta na wuce gida na shiga gida ba daɗewa domin ruwan zafi kawai na ɗora ban ma san me zan dafa ba su Jidda suka dawo daga makaranta kawai sai na sulala mana indomie na haɗa da ƙwai na dafa mana muka ci, tun da yamma ta yi sannan yau Yallaɓai na gidan Gimbiya ba ni da wata matsala.

Saboda yana neman shiri bayan mangariba sai ga kiran shi, tambayarsa ita ce na dawo? Na ce masa na dawo tun ɗazu sai ya ce mini zai shigo gidan in ya dawo. Ban ma san ashe tafiya ya yi ba sai da ya zo gidan wajajen taran dare, ina ɗakina saboda yana son shirin da gaske har ciki ya biyo ni, muka gaisa shi ne fa ya ke faɗa mini Dutse ya je akwai wani gidan radio da za a gina kuma shi a ka ba ma kwangilar wajen shi ya sa ba ya samun zama ni dai nawa fatan alheri kawai.

Tare da shi muka fito falo ina ba ma su Jidda naman sunan da a ka bani na gidan su Saude. Tsoka bibbiyu na ba su ni kuma sai na saka sauran tsoka ɗayan a bakina akwai kuma saura biyu a hannuna da ƙashi.

" Umma Sadiya. Ni ina nawa naman sunan?

Ba zato kawai na ji maganarsa ban tsaya nuna masa mamakina ba na miƙa masa sauran na hannuna. Sai dai na shanye mamakin nawa da na ga ya saka hannu ya karɓa har kuma ya ɗauki tsokan da ta rage ya saka a baki ya na taunawa.

"Lah Abba kai ma kana cin naman suna?

Baby ta faɗa tana yi masa dariya duƙawa ya yi daga in da muke tsaye a bayan kujerun falon ya lakace mata hanci yana faɗin" E mana. Ai har na ki naman sunan na ci." "Na Ya Jidda fa? Ta faɗa ta na dariya. "Har na ta ma na ci." "To na Umma fa? Sai na kalle shi, nima ni ya kallah kafin ya yi dariya ni kuma sai na kauda kaina na zagaya na zauna saman kujeran da Jidda ke zaune ta na ta duba wani littafin Chemistry ba ta shiga maganar Baby da Abban na ta ba.

Na ga dai ya yi mata raɗa a kunne tana kallona tana dariya amma ban san me ya faɗa mata ba. Bai zauna ba ya yi mana sallama ya tafi. Saboda gulma har yana zuwa yana sumbatar goshina. Yaushe rabon duniya da ayyarahe? Amma dai ban kushe sa ba, na yi masa yaƙe Baby ce ta raka shi har haraban gida amma daga ni har Jidda muna daga in da muke ko motsawa ba mu yi ba.

Washegari da safe bai zo ba amma ya kira ni a waya yana tambayan yadda na tashi ni da yara. Na ce masa muna lafiya sai ya ce zai ta fi Dutse sai zuwa anjuma in ya dawo na ce a dawo lafiya. Ranar a gida na yini ina warware gajiya mun yi waya da Anty Laila maƙotan ta na son hijabai sun gani a wajenta da yake ta siya kuma shima Ya Auwal ya siya mata wasu. Nan da nan na ji ciniki na ce ta tura mini colours da simple ɗin irin wanda suke so sai na tura a ɗin ka musu daga can za a tura musu Abujan ba sai an ma an kawo mini shi nan ba. Datti ma mun yi waya amma ni na kira shi ina masa tsiyan tun da ya fara zaman kansa ya daina neman mutane.

"Kai Ya Sadiya ko kwanaki ba na kira ki ban same ki ba "

"Uhm kai Datti fita idanuwana na rufe. "

Sai ya fara dariya yana faɗin" To na ji na amsa laifina a yi min afuwa" Sannan na yarda muka gaisa yana tambayan ya yara na ce suna lafiya. "Ko jiya sai da Jidda ta yi zencen ka da cewa Uncle Datti shuru kwana biyu" "Allah sarki Jiddodi ta na lafiya ko? Ya mganar jarabawarta? "Yallaɓai ya ce a wannan shekaran za ta yi har Jamb ma." "Za ta iya ai ta na da ƙwanya mu ta yi gado"

Dariya na yi shima yana ta ya ni, mun sha hira da shi ya ce ma ƙarshen wata zai shigo garin ba sa samun hutu ne mai tsawo ni ko na ce daman aikin kamfani ai sai mai haƙuri. Ina jin zumunci har Ya Aina na kira da Ya Balki muka gaisa Ya Murja ce da na kira ba ta gida yara suka ɗau wayar Rahila kuma Ya Muntari ya ɗauka ya ce min wayar na hannunsa tun jiya wutar layin su ta lalace wayar ta kwana ba chaji sai ya fita da ita yau ɗin domin ya sa mata chaji bai ma daɗe da kunna wayar ba sai ga kirana. Na dai ce ya gaisheta in ya koma gida ya ce in sha Allahu zai faɗa mata. Amina ce kaɗai da ban kira ba saboda ita ko kafin tafiya ta Jigawa ai mun yi waya. Ma'u kuma daman na yanke alaqa da ita, ba ta kirana ba na kiranta sai dai in mun haɗu a gidajen ƴan'uwa amma dai ban goge lambarta ba kamar yadda nima na ke da yaƙinin ba ta share tawa ba.

Daga nan na yi ta shige shige na a I. G. Ni kaɗai ban taɓa jin ina jin haushin halina ba sai kwanakin nan ba ni da wata ƙawa Aminiya shaƙiƙiyan da yau in na shiga matsala zan je mata da mgana ta saurareni kuma ta ba ni shawara kamar yadda na ga wasu suna dashi, ni ko ni ɗaya tal ban taɓa ƙawa ba bare ba sai su Munnira su kuma aure ne ya haɗa ni da su duk da mun shaƙu amma akwai wani matsalan nawa da ba na iya faɗa musu saboda shi aure ai sirri ne, kuma cikin kowani aure da zamantakewa akwai matsaloli kowa kuma da irin na shi matsalan. Ba komai ba ne za ka zo kana faɗa akwai wani abun da ya ke buƙatar sakaya. Yau da a ce bani da shigen halin rashin sakin jiki da mutane da yanzu ina da ƙawaye na tuna tun muna makaranta ƙawayen da suka yi ta shige mini ina ba sar da su. Har na zo matakin jami'a yan set ɗin mu sun yi ta shige mini amma na ƙi ba ma kowa fuska har Maijidda ma ta layin mu ta so ni har muka haɗu a jami'a da ta ga dai ba na yi da ita sai ta kama kanta.

Ta yi aure a cikin garin Kano nan amma ban taɓa zuwa gidan ta ba na dai je bikin da Rahila ta matsa mii kuma har gida Maijiddan ta kawo min IV da mintin gayyata. Kaf waɗanda muka yi karatun jami'a da su ba na zumunci da kowa. Wasu ina ɗan kiran su a waya jaje ko murna shima na zo na daina daga baya nima tun suna bina har kowa ya rabu da ni ina dai cikin group ɗin kuma ina ganin ana ta abubuwa in sha'ani ya tashi na ɗayan mu a haɗa kudi kuma a je, ni dai na kan ba da wani lokaci amma zuwa ban taɓa yi ba. Sai dai in ga ana turo hotuna suna zumunci su amma ni na ware kaina kamar saniyar ware. Ban taɓa jin abin ya dame ni ba sai yanzu amma a ƙasan zuciya na ƙudiri a raina nima yanzu zan nemi jama'a domin na fahimci jama'a rahama ne.

Ranar ma sai dare Yallaɓai ya zo gidan kuma again a ɗakin barcin mu ya sameni ina ta rubutu.

"Madam wai labarai kika fara rubutawa ne?

"Me ka gani?

Na ɗago ina kallon shi bayan na dakata da rubutun da nake yi. Gyara zama na yi a gefen gadon lokaci ɗaya ina gyara zaman doguwar rigar material ɗin dake jikina.

"To gani na yi kwanan nan kina ta faman rubuce rubuce."

Kallonsa na yi ina tuna yaushe ne ya ganni ina rubutu? Ni dai ina tunanin wannan ne na biyu amma zai ce wai kwanan nan ya na ganina ina rubuce rubuce.

"Kawai abin kasuwanci ne. Ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ne."

"Da kyau Hajiyar Business"

"Ya Hanya?

Sai na kau da maganar ganin duk ya gaji daga yanayin ma yadda ya ke mgana.

"Lafiya lau. Amma na gaji sosai"

"To ka zauna mana."

Na faɗa ina nuna masa gefen gado saboda na ga yana tsaye kuma ga shi ya ce ya gaji."

"Bari kawai na ƙarisa gida na yi wanka na huta gabaɗaya."

"Kuma fa haka ne."

Na faɗa ina kau da tunanin ya ƙi amsar ta yi na ne. Ni fa taimakon sa na yi ganin ya ce ya gaji kuma yana tsaye kamar wani dakaren soja.

"Maganar mu fa Sadiya?

"Wacce magana?

Na tambaya ina kallon shi. Sai ya gyara tsayuwa yana mai harɗe hannayensa a ƙirji kafin ya ce.

"Mganar da na ce in kika dawo za mu yi. Domin mu warware rashin jituwan dake tsakanin mu."

Sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Muna gabar ne har yanzu? Ai ina jin kamar mun warware komai."

"A'a.

"To me ya yi saura?

"Komai ma."

Ya katseni ya na mai tsareni da idanuwansa.

"Kin daina gaba da ni amma kuma kin ƙi komawa kamar yadda kike a baya Sadiya."

"Mun daina gaba da juna za ka ce ko?

Ya na kallona na cigaba da faɗin" Tun da kaima ba ka yi mini magana Yallaɓai."

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Duk na ji na amsa laifina shi ya sa na ce mu zauna mu yi magana domin mu fahimci juna."

"Na ji za mu yi in sha Alkahu."

Na faɗa ina ƙokarin komawa in cigaba da rubutuna.

"To yaushe?

Sai da na ɗago na kalle shi ido na cikin ido sannan na ce.

"Sai ranar da na karɓi girki."

Murmishi ya yi kafin ya ƙariso gaba na ban yi aune ba kawai ya ɗan rankwafa ya sumbaci laɓɓana kafin ya miƙe ya fice yana faɗin.

"Sai da safe Sadiya ta."

"Sai da safe."

Na amsa masa a saman laɓɓana bayan fitan shi har ina shafa wajen. Yaushe rabon da a yi haka! Tun kafin faɗan mu da shi a kan Khalipa. Yaron na raina ina son tambayan shi amma na fasa tun da ya nuna min iyakata ya je amma ƙaunar da nake yi ma jininsa ba zan fasa saboda shi ba, ko faɗan mu ne ya sa kwana biyu tun da na dawo bai tarkatomun Khalipan ba, amma na ƙudiri niyyar in na ga ba a kawo shi ba zan kira Gumbiyar na ce ta kawo shi ya yi mini kwana biyu na saba da shi duk da ɓarnar shi, shi kuma na san ya yi sabo da gidana sosai kawai dai kwana ɗaki ɗayan da Yallaɓai ya tsiro da shi na ga ana cutata shi ya sa na yi magana amma ba da niyyar Khalipa ya daina zuwa ba tun a baya ban hana shi zuwa ba sai yanzu?.

******

Tun da yau Yallaɓai zai dawo gida na na kira Maman Nana na ce in ta samu lokaci ta zo ta yi mini kitso. Da safen ko ta zo ta yi min 2step ƙananu. Kuma kitson ya yi kyau tun da na duba a cameran waya ta na gani. Sai azahar ta tafi bayan na yi mana girki duk dai macaroni na dafa mana muka ci da ranar. Bayan tafiyan ta na gyara gidan na yi shara na saka turare ɗan kwanciya na yi na ɗan huta zuwa la'asar na tashi bayan na yi sallar la'asar Sannan na ɗora ma su Jidda girki da man macaronin guda ɗaya na dafa.

Cous-cous na dafa mai kayan lambu daman kuma Yallaɓai na so shi ya sa na yi. Sai zoɓon da na haɗa daman tun safe na riga na dafa genyen zoɓon haɗawan kawai na yi. Sai sauran kayan marmarin da suka rage mana na yanka na yi mana fruit salad ni da Yallaɓai. Shidda saura su Jidda suka dawo makaranta ajaran majaran saboda yunwa ko uniform ba su cire ba suka fara cin abinci. Baby na faɗa min Umma cikina kamar an kwashe min kayan cikina ina gefe ina ta yi mata dariya ganin tana cin abinci hannu baka hannu ƙwarya.

"Baby ki ci a sannu kar ki shaƙe.'

"Umma ba ki san yunwan da na ke ji ba ne"

Ina ta mata dariya ni na je na kawo musu da zoɓon ya yi sanyi na saka a firiza.

"Ya Jidda ke ma duk yunwar ba baka sai kunne?

Sunne kai ta yi ta na faɗin.

"Umma ni kin ji na yi magana ne?

"Ba ki ce komai ba. Ke dai ci abinci kawai."

Na faɗa ina yar dariya. Yarinya na jin yunwa tana noƙewa.

Bayan sun gama cin abincin sun ƙoshi, suka sauya kaya zuwa na gida lokacin an kira salla sai muka yi alwala muka yi salla yau ba mu yi karatu ba saboda wankin uniform muka fita ta baya muka wanke su tare da yan riganunan barcin Baby da ƙananun wandunan ta daman Jidda ke wanke musu tare da na ta. Muna gamawa ana kiran sallar isha'i muka sake ɗauro alwala muka yi sallar isha'i. Muna idarwa ni kuma na faɗa wanka bayan na fito na yi gayu na cikin riga da zani na wata atamfata hollond ta na cikin kayan da na siya lokacin auran Yallaɓai da Gimbiya.

Na kashe ɗauri na ture ka ga tsiya na ba za gashina ya sauko har kafaɗuna. Har da su jan baki na saka na kuma zirara gazal a girana, na fita falo wajen yara da dai na ga shuru Yallaɓai bai shigo ba sai na diɓi abincina na ci na kora da zoɓo da fruit salat. Bai kuma shigo ba sai goma har ta ma gota. Tuni har na kaɗa su Jidda ɗakin su na ce su yi shirin kwanciya so ni kaɗai ya iske zaune a falon ina kallo duk da hankalina ba akan kallon yake ba.

Miƙewa na yi ina kallon shi, nufar sa na yi ganinsa da ledoji a hannunsa.

"Sannu da zuwa."

Na faɗa ina karɓan ledojin hannunasa.

"Yauwa Madam ya gidan?

Ya faɗa lokaci ɗaya yana sakar min ledojin a hannuna. Na amsa da lafiya lau lokacin da na nufi kitchen na duba ledojin tsire ne sai fura mai sanyi an dama ta a leda. Na san ni ya siyo mawa da yake ya san ina son fura duk da cikina ya cika amma ta ba ni sha'awa zan sha zuwa anjuma in cikina ya sassaɓe. Naman dai a firiza na saka shi da safe sai mu ci na san na mu ne Yallaɓai ba ya son tsire ya fi son gashi na naman rago. Sai ya ce wai tsire duk ƙuli ne ba nama ba.

Ko da na fito ba shi a falon ya na ciki sai na koma kitchen ɗin na hada masa abinci na kai dining sai da na gama shirya masa duk abin da zai buƙata sannan na koma bedroom ɗin na iske Yallaɓai ya fito daga wanka ya na saka sauƙaƙƙun kayan zama cikin gida riga da wata ƙaramar riga mara hannu. Sai ma yau na ƙare ma Yallaɓai kallo da gaske kam Yallaɓai ya fara ijiye tumbi da na ƙura ma gashin kansa ido har na hango ƙyali ƙyalin furfura a saman kan shi har ma da sajen shi. A raina na ce su Yallaɓai tafiya ta fara miƙawa.

"Tunanin me Sadiya ta take yi ne ahalin ga ni a kusa?

Ya faɗa ya na mai sagalo hannun shi a kafaɗana sai na tattaro murmushi na kalle shi na yi masa.

"Abinci.?

Na faɗa ina kallon shi sai ya shafa cikin sa yana faɗin daman yunwar yake ji. Ya ƙi sakina ya na dafe da ni muka fita can falo sai da zai zauna saman kujeran dinning ne ya sake ni. Nima gefen sa na zauna na zuba masa cous-cous ɗin da zoɓo sai fruit salaf ɗin sai ya ce na zuba masa leda ɗaya na fura yana so zai sha sai na koma kitchen na juyo masa a wani ƙaramin mug. Ina gefen shi har ya gama cin abinci kuma daga yanayin sa na fahimci ya ji daɗin haka. Barin ma yadda na ga ya ci abincin sosai da alamu dai yau Yallaɓai ya yi ta su Baby ta babuwa ta addabi cikin sa.

"Girki ya yi daɗi. Haka ma mai girkin ta yi kyau."

Ya faɗa ya na kallona sai na yi murmushi k amma ban ce komai ba.

Bayan na tattara abubuwan da ya ɓata na mai da kitchen ina dawowa ya ce wai kallo za mu yi, kujera mai zaman mutum biyu na samu na zauna amma Yallaɓai sai da ya biyo ni ya nane minI, ina basarwa ina komai karshenta dai sai gani a saman jikinsa kamar yadda muke yi a baya in muna kallo. Ɗankwalin kaina ya zame min yama ta wasa da gashin kaina shi ke kallon ni kuma na kwantar da kaina kawai a saman ƙirjinsa ina tunanin rayuwa juyi juyi. Yanzu fa yadda nake yi da Yallabai haka itama Gimbiya take yi da shi gabaɗaya sai na ji ƙuncin zuciyata ya dawo. Har wani gishiri gishiri na ji miyan bakina na yi saboda takaici ina jin sa yana ta ɓabatun magana amma ban biye masa ba.

"Ƙitson nan ya yi kyau. Yaushe a ka yi shi?

"Yau."

Na bashi amsa kai tsaye.

"Lalle ko za ki karɓi tuƙwaici domin kitson ya yi kyau sosai."

Ya gama faɗa sannan ya sumbaci kaina. Ni ko mgana ban yi ba ganin haka ya sa ya leƙo fuskata yana faɗin" Kin yi shuru? "Me zan ce? "Komai ma ki ce Sadiya ta." Sai kawai na yi masa shuru saboda ni ai ya gama shanye ruwan kaina ba wani sauran abin da zai yi mini da zai kankare mganganunsa a wajena suna nan damfare a ƙasan zuciyata sun yi min tsataa.

Ganin kamar ba ya jin barci ya sa na fara yi masa hamman ƙarya na ce ina jin barci dole ya kashe kallon muka koma bedroon ɗin mu amma ni na fara yin gaba shi kuma ya tsaya duba yara sannan ya kashe wutar duka ɗakunan kafin ya shigo har na yi shirin kwanciya amma ban kwanta ba. Na saka wata doguwar rigar barcina mai taushi. Ina shafa humra a wuyana da hannayena ya shigo. Shima dai tiolet ya shiga ya kama ruwa ya wanke baki sannan ya dawo ya tuɓe riga ya kuma tuɓe wando da ga shi sai gajerun wando ya hau gadon a gefena maimakon ya yi nashi ɓarayin sai ya mirgino har kan filona ya tsoma na shi kan

Muka yi shuru ni da shi, muna kallon rufin dakin da hasken wutar tun da bai riga ya kashe ba. Juyowa ya yi ya na kallona ni kuma da sauri na ce" Ka rage mana hasken wutar mana." "Ba yanzu ba." Sai na ƙura masa ido kafin na samu sararin magana ya cigaba da faɗin. "Sai mun yi maganar mu." Na kalle shi amma ban yi magana ba sai na ga ya miƙe zaune nima ya umarce ni da na tashi ba ni da mafita dole na mike zaune a saman gadon muna kallon juna.

"Sadiya"

"Na'am."

Na amsa mishi kamar yadda ya kira sunana.

Sai kawai na ga ya kama duka hannuwana ya jimƙe cikin tafukan hannayen shi.

"Ki faɗa mini duka abin da na yi miki da ya ɓata miki rai ni kuma na yi miki alƙwarin zan ba ki haƙuri."

Ya faɗa yana murza hannayena sannan kuma yana mai tsareni da ido.

"Ni fa ba komai. Komai ya wuce."

"Bai wuce ba."

"Allah na ce maka ba komai ba sai ka ba ni haƙuri ba.'"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull