Turken gida book 3 cmplete - Chapter 16
Turken gida book 3 cmplete Chapter 16: Turken gida book 3 cmplete Chapter 16. Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina…
3,304 words
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732
Ganin da na yi Yallaɓai a ruɗe yake, ni kuma jikina duk ya saki ina kwance itama jaririyan na kwance cikin ƙazanta tana ta callara kuka, tun lokacin da ta faɗo ta callara kuka na san cewa da gaske ƴa mace na sake haifa. Sai na kira sunan Yallaɓai ya taho wajena sai na ce ya kamani cikin rawan jiki ya kamani na tashi zaune. Sai a lokacin na fahimci jaririyar tare da uwa mahaifa ta faɗo shi ya sa na ji fitowar abu sau biyu daga ƙasana.
Zanin da ke jikina da ya yi gefe na ce ya ɗauko jiki na rawa ya tashi ya ɗauko sannan na ce ya buɗe dirowan gadon mu ya ɗauko kit ɗin mu na magunguna akwai reza a ciki, bayan ya kawo mini na karɓa na rike jaririyan shi kuma na ce ya riƙe zanin na saka ta a cikin zanin tana hannun shi sannan na daidai ta na yanke cibiyar na ce ya matsa daga wajen tun da gabaɗaya mun yi dama dama daga ni har shi cikin kazantar haihuwa.
"Ya zan yi mata Sadiya?
Ya faɗa yana kallona ya na kuma riƙe da jaririyar.
"Ka naɗe ta a cikin zanin ka kwantar da ita a kan gado ka zo ka kama ni na tashi."
Haka ko a ka yi bayan ya kwantar da ita sai callara kukan jarirai take yi ya zo ya kamani na tashi tsaye. Na saka shi ya buɗe karamar akwatina in da na tara kayan haihuwa na ce ya ba ni na ɗaura. Bayan na ɗaura na ce ya je ya saka min ruwa a hiter tiolet da gudu ya fita ni kuma na tattaka ina ware ƙafa domin sai ina jin kamar na ƙaru ta ƙasana na isa in da yarinyar ke kwance na ƙura mata ido ina kallonta lalle dole ta ci sunan uwata. Domin a kammanni ma ni ta ɗauko.
Yallabai ya dawo ɗakin ya ganni tsaye ina kallon ta yana zuwa na kalle shi da mirmishi kafin na ce.
"Alhamdulillah mace na haifa Yallaɓai. Mace Allah ya sake ba mu"
Sai kawai ya rumgumeni bai damu da yanayin da nake ciki ba. Cikin tsananin farinciki ya ke faɗin.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka da ya sake nuna mini wannan ranar"
Wai a haka don ƙarfin hali Yallaɓai sai da ya sumbaci bakina na ture shi ina faɗin" Ko minti goma ban yi da haihuwa ba Yallaɓai? Sai ya yi mini dariya kawai bai ce komai ba.
Shi na saka ya kwashe kayan su Jidda dake zube akan gado ya saka musu cikin wardrope kar su ɓaci. Ba ni da tsummokarai sai kawai na ce ya kwaso doguwayen rigunan da na ɗinka na yi amfani da su lokacin ina da ciki waɗanda shi da kan shi ya saka musu suna da buhu in naɗe kazantar da su kawai a kai su bola bayan an wanke tun da sun gama amfani.
Jaririyar kuma na goge mata jiki da dotel, tare muka goge kazantar ni da Yallaɓai ina cewa ya bar shi yana mini faɗa wai na mayar da shi mara tausayi ta ya ina cikin wannan halin zan ce ya koma ya zauna yana kallona ai sai na yi shuru. Tas muka gyara wajen duk da ba sosai ba amma mun goge kazantar haihuwar. Ita kuma uwa mahaifa na ce ya je ya haƙa rami a haraba ya rufe. Ya ɗauka cikin wani zani ya fita dashi ya je ya rufe bayan ya dawo ya sake fita da cafet tun da a kan shi na haihu na ce ma Yallaɓai kawai a wurgar da shi ya ce a'a sai an wanke in zan yi kyauta da shi ne sai na yi amma ba zai bari a wurgar da shi ba.
A baho babba da ya ɗauko muka tara kayan da muka yi gogen-gogen na ce ya fita dashi can ta ƙotar kitchen.
"Kar ka ce kuma za ka wanke ka bari su Ya Aina su zo don Allah.'
Sai ya ce minI to, sai da ya dawo ne na ce ya miko mini wayata, tana falon su Jidda ya je ya ɗauko ya kawo mini jikin sa na rawa. Jaririyar na jikinsa ya nace sai da na ba shi ita.
"Kar ta ɓata ma ka jiki. Kasan gogewa kawai na yi ba a yi mata wanka ba.'
"To ai jikin nawa ya riga da ya ɓaci ba matsala in ta ƙara ɓatawa" Sai da ya yi magana na lura shima dogon wandon da ke jikinsa duk ya ɓaci da jini har farar vest ɗin jikinshi wa ya ga maza yau sun yi aiki.
Ya Aina na kira na ce mata ta zo gida na haihu. "Ke Sadiya" "Wallahi da gaske Ya Aina. Na samu ƙaruwan mace." Sai ta yi kabbara kafin ta ce min gata nan zuwa domin na ce ta yi sauri ko yarinyar ma ba a wanke ba Sai da na gama wayar na duba lokaci sha biyu ne da wani abu zai iya zama gab da sha biyun na haihu ko kafin ma.
Saboda na kira Ya Aina ya sa na matsa Yallaɓai ya je ya yi wanka jikin sa ya ɓaci.
"To ke da ita fa?
"Za mu yi in Ya Aina ta zo.'
"Amma za mu je asibiti a duba mini ku ko?
Sai na yi dariya kawai ganin yadda ya kama jaririyar ya rumgume.
"Za mu je asibiti mana. Ka je ka yi wanka kafin ta zo"
Da kyar ya ba ni jaririyar nan ya tafi ya yi wanka nima ya bar ni rumgume da ita har lokacin ina yi ma Allah kirari. Ina jin jini na zuba ta ƙasa na Allah ya sa na samu wani zani na tara a ƙasa na kafin na yi wanka. Na yi ta ma Allah kirari ina riƙe da kyautar da Ubangiji ya sake yi mini bayan na fidda rai. Ina ta hailala da kabarbari a cikin zuciyata domin Allah shi kaɗai ne wanda kum fa ya kum ne a lokacin da ya so a lokacin komai yake faruwa.
Ina nan zaune Yallaɓai ya fito wanka, yana ma saka kaya ne Ya Aina ta kira wayata da cewa ga ta nan a bakin get shi ya sa a gurguje Yallaɓai ya shirya ya fita ya je ya buɗe mata suka taho ciki a tare yana gaba tana bin shi a baya har cikin bedroom ɗina sai ga shi ta ganni a zaune gefen gado riƙe da jaririya ai sai ta riƙe haɓa kafin ta ce.
"Ikon Allah da gaske dai kin haihu?
Sai kawai na yi mata dariya ba tare da na yi magana ba.
"Wallahi Ya Aina ni kaina na yi mamakin haihuwar nan, abin da bai gaza mintina goma ba har ta haihu."
"Sannu Dubu. Sannu Dubu na ce barkan mu da arziƙi."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana karɓan jaririyar da ke hannuna ni kuma sai na sakar mata ina faɗin" Yauwa Ya Aina." Na faɗa ina mata mirmishi, gefena ta zauna a kan gadon ta na kallon jaririyar kafin ta ce" Ma sha Allah. Ga ta nan ko kamaanninki ta ɗauko Sadiya"
"Shi ya sa na ce ta gama cin sunan Mama."
"In sha Allahu."
Yallaɓai ya ba ni amsa lokaci ɗaya yana kallona nima shi na kallah ina mai jadadda masa godiyata ta idanuwana. Ya Aina ko sai washe baki take yi cikin hamdala. Yallaɓai ne ya yi maganar tafiyar mu asibiti ya sa ta tashi ta ce bari ta saka ruwan zafi ta fara yi ma jinjirar wanka sai na ce akwai ma ruwan zafi a hiter ta tiolet Sai ta ce to bari ta yi amfani dashi bam damu ba sanin duk abin da ya kamata za ta yi kamar yadda ta yi mini a haihuwan Baby ita ta yi jinyata a asibiti har muka dawo gida shi ya sa nake ganin ƙimar Yaya Aina ta na yi ma zumunci kara da jikinta da aljihunta.
Nan ta bar ni da Yallaɓai zaune mun ta sa jinjira muna kallo bakin mu ya ƙi rufuwa sai da ta ɗebo ruwan a baho sannan ta karɓe ta. Tas ta yi mata wanka bayan ta yi ta sauya ruwan Yallaɓai na faman kai da kawo, ta saba saboda in dai na haihu kaf dangina da dangin Yallaɓai sun san shi ba mai zama ba ne, da shi za a yi ta shiga da fita in na kamawa ne ya kama sai ya ga jama'a sun taru ne yake haƙura ya fice daga gidan. Na taɓa jin Anty Maimuna na yi masa tsiya a haihuwan Anwar wai yadda suka san shi da hidima a kaina in na haihu amma Gimbiya an mata aiki a asibiti ya bar gida kaca kaca bai iya gyara komai ba. A gabana ne ranar na je giden bayan an sallamota kai tsaye ya ce Sadiya kika ce, ba lalle abin da na ke yi a can na yi shi a nan ba. Sannan bai zama dole shima abin da na ke yi anan na je can na yi ba. Tana jin haka sai ta yi shuru ni ko a fili ma sai da na murmusa ban ji wani mamaki ba saboda sai da a ka yi mini kishiya na fahimci abu kaɗan ma da bai kai ya kawo ba in ba ka kai zuciyarka nesa ba sai kishi ya turniƙe ka.
Shi ya jawo mata akwatin da na haɗa kayan haihuwan ta shirya jaririyan cikin kayan sanyi masu kyau bayan ta shafe mata da man zaitun ta kuma gasa cibiyar sosai ta saka mata mgani saboda ta yi saurin faɗi, ta nannaɗeta cikin towel ta miƙa ma Yallaɓai da yake jira daman. Faɗa mini yake yi yanayin jikinta irin na Baby ne ƙatuwa ce mai kiɓa haka na haifi Baby kuma har gobe ta na nan da ɗan jikinta kuma wannan jikin na su Anty Bahijja ne ko na ce na Nene domin har yanzu da shekaru suka tura akwai jiki a tare da ita. Nan muka bar Yallaɓai Ya Aina ta iza ƙeyata tiolet ta kama mini na gasa jikina kuma sosai na ji daɗi a ciki ta bar ni ta fita zuwa kitchen ashe tea ta haɗo mini mai kauri da ƙwai sannan ta kawo min saban buredi ta bincika ta ga ma ina da garin kunu amma ba shi da yawa sai ta yi ma Yallaɓai maaganar gero sai ya ce in ya fita zai yi magana za a kawo.
Ko da na fito shi yake faɗa mino ya yi ma ta huɗuba da suna Rukayya bayan ya lasa mata dabino a bakinta. "Allah ya raya mana Ruƙyyaatu Yallaɓai na." "Na gode. Na gode. Na gode da wannan martabawan na ka. Ubangiji ya yi maka sakamako da wannan karan da ka yi mini."
Kafin ya yi magana Ya Aina ta dawo ɗakin tana tambaya ta omo sai na ce ta duba a dirowan kitchen duk da bai da yawa sai Yallaɓai ya ce in rubuta duk wani abu da ake bukata za a kawo anjuma. Ta juya da nufin fita sai na kira ta ina faɗa mata Yallaɓai ya yi mata huɗuba da sunan Mama.
"Ma sha Allah. Allah ya raya mai sunan Mama. Allah ya sa ki biyo halin mai sunan."
Dukkanmh muka amsa mata da Amin Amin nan ta fice ta bar mu. Yallaɓai na riƙe da ita na shirya na saka wata doguwar rigana sai gashi ta shige ni, na ɗan ragu amma ciki na nan kamar ban haihu ba sai da Yallaɓai ya ce ko akwai twin ɗin Rukayya ne a ciki ba mu sani ba ina dariya na ce wani twin jini ne a ciki a hankali a hankali zai ta sauka amma zan ɗan riƙa ɗaure shi saboda koyarwa iyayen mu na da kenan ka riƙa ɗaure ciki a cewarsu in ka sake shi haka shi kenan zai bi jikin ka. Pamper na saka na tare ƙasana da shi sannan na zauna ina zaman ƙaryawa na biyu domin sai na ke jin kamar na shekara ne ban saka komai a cikina ba saboda yunwar da na ke ji ina tusa buredi a bakina ina kallon Yallaɓai na yi mata hoto.
"Yallaɓai ba ka sanar da kowa haihuwan nan ba fa."
"Zan sanar yanzu."
Ya faɗa yana ƙara yi mata wani hoton har yana wani karkacewa sai da na yi dariya. Ni dai ai na sha mamakin yadda na iya ta da jug guda da tea na kuma haɗa da ƙaton saban buredi na cinye ga ƙwai manya faifai biyu lalle a gaida Haihuwa domin wani abu sai haihuwa in ba haihuwa ba da cikin jego ba ina ni ina ta da wannan uban ruwan shayin? Haka na faɗa ma Yallaɓai da na ga yana kallona sai ya yi dariya kafin ya ce.
" Ni wallahi hankalina baya kan ki. Ban ma lura da aikin da kika yi ba. Na ce to sannu da aiki Umma Sadiya."
Sai na fashe da dariya yana ta ya ni, a gurguje na shirya muka yi ma Ya Aina sallama muka fita muka barta tana ta wankin kayan haihuwa. Wayata ma a gida na bar ta, muna hanya ne, na ce ma Yallaɓai alkunyar Ruƙayya za mu riƙa kiran ta YUMNA. Ya ce abin da na ke so ai shi za a yi tun da Yallaɓai ya zama ni, nima na zama shi muna ta hiran mu har muka isa asibitin Aminu kano shashen masu awo suma sun yi mamakin haihuwanta da nake faɗa musu yadda lamarin ya faru, suka karɓi Yumna suna ta santi barin ma da suka ganni ras da ni kamar ban haihu ba. Ita dai Yumna an yi mata alluran su na jarirai ne domin rigafi aka ce ranar da ta yi kwana bakwai za mu dawo a yi wasu, ni kuma suka duba ni a tunanina ma na samu ƙari sosai sai suka ce na samu ƙari amma ba sosai ba. Amma dole ne suka rike ni sai sun yi mini ɗinki shi ya sa na kira Yallaɓai na faɗa masa sai ya ce ba damuwa sai ya jira ni daman muna zuwa sai da ya je ya yi sallar azahar da ta suɓuce masa.
Ni ban sani ba ashe Yallaɓai ya ɗora hoton Yumna a status ya yi magana sannan ya tura a family group ɗin su na gida da cewa na sauka lafiya. Ana ta kiran waya ta, mu kuma muna asibiti sai wajen gab da la'asar muka koma gida bayan an yi min ɗinki da dokokin na yi ta shiga ruwan ɗumi,tare da wasu magungunar da likita ya rubuta mini. Tun muna asibitin ruwan Nono ya fara zuwa har na ma bata ta sha, saboda tana ta rigiman alluran da a ka yi mata. Mu na mota a hanyar komawa gida sai da na ƙara ba ta, tana ta rigima ni kaina azaban nake ji daga ƙasana, saboda ɗinki kana ganina duk na jigata shi kuma Yallaɓai sai kiran shi a ke yi a waya a na masa barka yana amsawa a muryan shi cikin farinciki da Annushuwa.
Ko da muka koma gida, jama'a cike. Rahila ta zo ita da Ma'u da Ya Murja. Ya Balki ce ba ta nan ta je suna a dangin mijinta Jigawa amma ta ce gobe za ta dawo. Nan na iske Hauwa mun dawo ba daɗewa sai ga Munnira da Mubeenan Musbahu sun iso suma, suna ta mamaki wai kamar ban haihu ba, ita kuma Munnira ta kama min masifa wai ace na haihu tun sha biyun rana amma na kasa kiran su sai dai kawai ta ga Mimisco ta poster jaririya a status ina dariya na ce ta yi haƙuri wayar a gida ma na bar ta mun tafi asibiti amma ba ta haƙura ba tana ta mita yadda suka shirya ma haihuwan nan ai kamata ya yi a ji haihuwan daga bakin su da ƙyar na samu ta haƙura amma in dai Munnira ce akwai ta da na cin magana.
Nan na bar musu jaririyan Ya Murja ta saka mini ruwan ɗumi na shiga na gasa ƙasa na sannan na sake yin wanka ina fitowa suka kawo abinci mai rai da lafiya shinkafa da miya da nama suka ce cefane a ka kawo bayan fitan mu na san Yallaɓai ne ya tura kuɗi a ka kawo mana cefane, sai da na natsa sannan na ɗau wayata na ga tarin kira ba adadi. Har Gwaggo ta kira ni sai da na sake dubawa ne sannan na ga har Alhajin mu ya kira ni. Ya Auwal da Ya Hamza dukkansu tare da matayen su sun kira wayata. Sameena ma ta kirani ita da Nafeesa, ina ga lokacin da suka ji labarin haihuwan ne suka yi ta kirana sai dai na riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya ina kiran su muna gaisawa da ƙarfin gwiwata na ke faɗin sunan Mamana ta ci Rukayya amma za mu yi mata alkunya da Yumna. Sameena ta ce ai sun sa ni Yallaɓai ya saka a status ɗin shi lamarin ya ba ni mamaki na san ya kan saka hoto wani lokacin amma bai cika yin rubutu a ƙasa ba. Ban da Haihuwan Jidda lokacin a na cikin samartaka wannan ya ɗora ta ya yi ta ma Allah godiya amma Haihuwan Baby bai saka hoto ba ya dai yi rubutun ya samu ƙaruwa. Haka ma na su Anwar da Khalipa amma ita Yumna ta zo a sa a tun da har ya ɗora ta ya yi rubutu nan da nan na buɗe data na shiga na gani. Ta yi kyau ƙwarai a hoton wato wanda ya ɗauke ta ina zaune ne a ɗazu ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton shi ne.
"Alhamdulillah. Allah na gode maka. Ubangiji ya sake azurtani da samun ƙaruwa daga Sadiyata. Na yi ta jira ban fidda rai ba, na yi ta ji a jikina Ubangiji bai yanke mini samun zuru'a daga tsatson Sadiya ba. Na yi haƙurin jira. Na shekara ɗaya,biyu, uku har zuwa shekaru goma ban cire tsammani ba. Kwatsam sai ga Ruƙayyatu(Yumna) kyautar da Ubangiji ya yi mana ita da misalin ƙarfe 12pm na rana. Ku yi mata addu'ar Allah ya raya mana ita tare da sauran ƴan'uwanta."
Ni kaɗai ina ta faman mirmishi, hoton na ɗauka nima na ɗora a status ɗina. "It's Baby girl. Name Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna)" Nan na ga ruwan comments ana ta Allah ya raya. Har Hauwa Jamilu sai da ta buga ihu ta yo mini VN tana ce mini ikon Allah ba ta taɓa tunanin zan ƙara haihuwa ba. Maijidda Bala yar anguwan mu kuwa ta ce mini ita ko in sha Allahu sai ta zo suna sai na ji daɗi na ce mata ina gayyatar duka yan set ɗin mu in sha Allahu gagarumin suna zan haɗa saboda murnan samun Rukayyatu da na yi a lokacin da na fidda tsammani. Nan ta ke Maijidda ta tura mganar haihuwan tawa a cikin group ɗin mu na makaranta sai tagging ɗina a ke yi ana mini barka wanda bai gane ni ba ma su Hauwa na ta yi masu kwatance, a zuciyata sai na ji wani iri lokaci ya yi da zan gyara mu'amalata da ƙawayena ana yi da kai ai ya fi a ce ba a yi da kai.