Turken gida book 3 cmplete - Chapter 17
Turken gida book 3 cmplete Chapter 17: Turken gida book 3 cmplete Chapter 17. Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka…
3,321 words
Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka dawo daga makaranta ai sai buga ihun murna da suka ganni da jaririya na haihu, Baby ta haye gadon ta ɗauke ta ta ƙamƙame tana faɗin na bar mata ina ta mata dariya Hauwa ta ce ta ɗauka ai daman na ta ne. Jidda kuma ni take kallo kafin ta ce" Wai da gaske kin haihu ne Umma? Ina hararanta na ce" A a ban haihu ba jaririyar roba ce." Munnira da Hauwa na ta mata dariya sai ta ji kunya ta kauda kanta. Baiwar Allah sai ta matso kusa da ni a hankali ta na ce min" Umma amma ba abin da ya same ki ko? Sai na dafa kafaɗanta ina faɗin.
"Ba abin da ya same ni Hauwa'u. Na gode da kulawa Allah ya yi miki albarka."
Sai ta yi mirmishi ta amsa da Amin a hankali. Da ƙyar Baby ta bari ta ɗauki jaririyar nan sai da Munnira ta zare mata ido tana faɗin" Ke ba fa taki ce ke kaɗai ba." Sai Baby ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka Hauwa ta rumgumeta tana lallashinta ni dai ina gefe ina mirmishi su da iyayen su. .Su Rahila da Ma'u da su Ya Aina suna can tare da su Mubeena suna aiki Tuwo suke yi Ya Murja kuma ta koma gida sai da safe za ta dawo da yamma nan sai ga Zabba'un Ya Abubakar fakam fakam da cewa daga gidan Gwaggo take ita ke faɗa mata na haihu sai a lokacin na tuna ban kira su ita da Alhajin mu ba sai na bari sai da a ka idar da sallar mangariba sannan na fara kiran Gwaggo. Ita ce bayan ta min barka na faɗa mata sunan Mama jaririyar ta ci.
"Haka Aina'u ta ce. Allah ya raya mana ita cikin addinin musulunci"
Na amsa mata da Amin Amin sai ta miƙa ma Alhajin wayar ni na fara gaishe shi cikin girmamawa.
"Lafiya lau Dubu an buɗe ido lafiya! Na amsa masa da lafiya lau.
"Kin tabbatar da ba abin da ke damun ki?
Ina mirmishin jin daɗi na amsa masa da cewa ba na jin komai alhamdulillah.
"To Allah ya ba ki lafiya. Gwaggon ku ta faɗa mini sunan jmRukayya kika ma yar ko? Na ce E Alhajin mu nan take ya fara kwarara mata addu'o'i.
"Allah ya albarkaci rayuwarta Allah ya raya ta. Allah ya tsare ta daga sharrin zamani. Allah ya ba ku ikon yi mata tarbiya. Allah ya yi musu albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya. Shi kuma mahaifin su Allah ya yalwata masa arziƙinsa yadda ba zai gajiya ba wajen hidimar ku gabaɗaya."
Na yi ta amsa da Amin Amin ni dai sai da na kashe wayata ina jin tahowar ƙwalla a cikin ƙwarmin idanuwana. Allah sarki iyaye ma su daɗi a fili sai da na ce" Allah ya jiƙan ki Mama " Na faɗa ina mai kallon jaririyar da ta ci sunan ta, ta na kwance tana sharan barcin ta, duk ba su tafi ba sai bayan isha'i bayan har wanka Ya Aina ta sake yi ma Yumna ni ma na sake yi na shiga ruwan ɗumi sannan na take cikina da tuwo miyar agushi da kuni dukkansu sun tafi da cewa sai gobe za su dawo suka bar sai ni kaɗai sai yara can zuwa ƙarfe tara sai ga Yallaɓai ya dawo gidan ya taho mini da fura da kayan marmari da yawa na ce Jidda ta karɓa ta ɗaurayo ma na sauran kuma bayan sun ɗiba ta saka shi cikin frizer.
Yallaɓai na gidan Mimisco ta kira ni ta yi minI barka bayan ita sai Anty Bahijja ita Anty Maimuna daman tun ɗazu ta kira ni, abin mamaki Gimbiya ba ta kira ni ba sannan ta ga status ɗina amma ba ta mini magana ba. Na so na yi ma Yallaɓai magana sai ban yi ba yana gidan har wajen sha ɗaya saura na dare nan ya ci tuwo ya zauna riƙe da Yumna muna ta hira da ni da shi da yara. Amma Gimbiya da ta kafa kira sai da ya yi mana sallama ya tafi, yau girkinta ne a fargabanta kar ya kwana a wajena tun da na haihu. Dama muna mganar abubuwan da babu ne na ce masa akwai komai sai dai kayan abinci in zai ƙaro sai omo da sabulun wanka da na wanki sai geron da Ya Aina ta yi masa mgana sai ya ce mini na rubuta na aika masa da shi gobe da safe Musbahu zai kawo min. Haka ko a kayi kafin na kwanta na rubuta na tura masa, tare da yara muka kwana Yumna ta tashi da kukan dare bayan na ba ta nono na sakar ma Jidda ita tana lallashinta ban ma san yauahe suka kwanta ba ni dai kamar ƴar maye haka na kwanta ina barci.
Washegari tun safe Ya Murja ta fara dira ko da ta zo ma har Jidda sun yi wanka ta gama ɗumama sauran tuwon jiya. Baby ce har da rigiman ita ba za ta je makaranta ba na ce lalle ta na da aiki ni masifa na fara mata za ta fara mini kuka na ce zan mata bugun tsiya ƙarshen ta dai Ya Murja ta lallaɓata sannan ta amince suka tafi. Yau Ya Murja ta yi ma Yumna wanka nima ta taimaka mini na gasa jikina bayan na shiga ruwan ɗumi saboda ɗinkin dake jikina. Sannan ta fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Gwaggo ita da Balaraba Maman Saude sun zo mini barka kamar haɗin baki sai ga Nene da Hajiya Iya sai Maman farko Adnan ya kawo su sai da na faɗa musu Yunma ta zama mai sa'a kishiyoyinta na ta kara kaina a kanta suna ta dariya. Sun ji daɗin ganin mu tas lafiya lau kamar ban haihu ba. Ba su wani jima ba suka tafi amma Balaraba sai ta tsaya tana kama ma Ya Murja aiki. Bayan fitan su ba daɗewa sai ga jama'ar Gandun albasa ni da kaina na kira Inna Mariya na sanar da ita na haihu, tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u dukkansu dai suka yi mini barka ba daɗewa suka tafi. Da safen Musbahu ya kawo buhun gero sai rabin buhun siga sai kwalin omo guda biyu, tissue sai kayan tea da yawa saboda daman na ce masa sun kusa ƙarewa. Kayan abinci kuma ya ce sai anjuma za a kawo daga kasuwa.
Ranar ma kamar jiya ne, yini gidan ya yi a cike da yan barka Amina ta kira ni a waya tana faɗin tun ana jibi suna za ta taho na ce daman ban ɗauke ma kowa ba har su Ya Hamza na faɗa musu in su na yafe musu to ban yafe ma matan su ba. Tun da na haihu kullun gidana Munnira da Hauwa suke yini da Mubeena , Su Ya Aina ma kullum sai sun leƙo Ma'u da Rahila suma kullun sai sun taho kamar haihuwar farko. Yadda na daɗe ban haihu ba , ba shakka na faɗa ma Yallaɓai taro zan yi ba ni da taro ba domin na yo gayya. Har Tariq da ya kira ni ya yi mini barka sai da na ce ban ɗauke ma Farida ba. Haka ma Kawu da ya kawo Marwa shi da ita na ce to ya sani tun ana gobe suna domin suna zan shirya sunan da ban taɓa yi ba yana dariya ya ce ya amince mini domin ya cancanci na yi taro na gani da za a ba da labari.
Amma Yallaɓai na neman ya kawo minI yawa wai shi ba shi da kuɗi ya faɗa mini an gama ginin kamfamin shi yanzu oder kayan amfani ke gaban shi zuwa farkon shekaran 2021 yake son su fara aiki. A takaice dai yana faɗa mini ba shi da kuɗi na ce na ji ya ba ni iya abin da ya yi niyya. 100k ya tura mini na shgalin suna, 100k kuma ya ce na siya kayan fitar suna ni da yara. Daman ni bai san ina da kala uku a ɗinke ba cikin kuɗin da ya ba ni na hidimar haihuwa na siya ma kaina. Da kuɗin da ya ba ni sai na siya mana wani swiss lece mai kyau blue ni da yara daman suma na yi musu kala ɗaya na Atamfa super kowaccen su na yi mata riga da zani. Nima na ɗinka super wax ɗin amma kalata na dabam ne. Sannan su Munnira sun fitar da ankon suna wata vatik mai kyau da yarari, suka kuma ce ba su ɗauke ma kowa ba. Kaf yayyena sun siya tun da Munnira ce ta saro ankon haka Farida ta ce a ɗaukan mata in kai mata ɗinki ita da Amina Marwa ma an nan kano a ka kai mata ɗinki har Saude da ke dutse ta siya itama za ta zo matan su Ya Hamza a mota a ka sanya musu na su a cewar su ba su yarda a ɗinka musu a nan ba. A dangin Yallaɓai daga Sameena sai Jamila da Suwaiba suka yi, Mimiaco ba ta yi ba amma ta yi ma yaranta ƙananun Mubeena daman yar gidana ce, Munnira duk ta nuna ma su Anty Bahijja amma take faɗa mini Anty Maimuna sai da ta ce wai na cika tsirfa haihuwa ta ukun ne sai na fidda anko ita kuma ta ce su suka fidda. Ba dai wacce ta yi mu ma ba mu damu da su yi ɗin ba domin ba saboda da su muka fidda ba. Na tura su Hauwa Jamilu da su samira duk sun siya an akai musu har gida sun yi mini alƙwarin zuwa mini suna.
Gimbiya ma ba ta siya ba ni da sai da na kwana biyu da haihuwa sannan ta zo mini barka da borin kunya wai ba ta samun zama ne ga aiki ga shago ni dai tak ban ce mata ba. Da Munnira ta nuna mata ankon sai ta ce ba a nuna mata da wuri ba ba lalle ta samu ɗinki ba har tana cewa ai irin wannan in an san za a yi sai a fiddo shi tun kafin in haihun. Munnira na ba ni labarin amsar da ta ba ta sai da na yi dariya wai su yanzu suka ga damar fiddawa kuma ba dole a ka ce sai ta yi ba daman fita haƙƙi ne. Na yi dariya sanin halin Munnira da ba ta barin ta kwana. Har Naja tana ta ya ƙawarta kishi ba ta yi ankon nan ba, ba domin ya gagare ta ba Anty Zabba ba za ta samu zuwa ba amma ta ce mini zan ga saƙo in sha Allahu. Su a tunanin su sunan da zan yi duk na salon na saka ɗan'uwan su kashe kuɗi ne domin Anty Bahijja ma ta furta a can gidan Nene a na jibi suna Suwaiba da ta zo ta ke faɗa mini, ni ko na ce ya ba ni kuɗi da kayan abinci amma sauran hidima tawa ce ba hannun Yallaɓai a cikin shi. Ni Halima ce ma ta ke ƙara ba ni mamaki sau ɗaya ta zo mini barka shima ba ta wani daɗe bs ta yi tafiyarta. Na tuna lokacin da nake zuwa gidanta na ci uwar aiki amma yau ni ce banza a idanuwanta Gimbiya ce gwana. Na yi kyafci a cikin zuciyata domin na saka ma raina akwai ranar da in ta mu ta haɗo mu sai na yi mata wankan tsarki da za ta gane ba ta da wayau.
Tun ranar litini da ya kama ana goben sunan Yumna gidana ya ɗinke da baƙi. Daman tun da na haihu na ce Yallaɓai ya koma wajen Gimbiya ya ce bai ga dama ba sai jiya ne ya tafi can amma ban sanin masa ko zai dawo bayan suna ba amma ni dai na ce masa ya koma gidanta har sai na yi arba'in ya ce ban isa ba. Amina tun safe suka sauka ita da Farida tare suka haɗa tafiyar Marwa ma da azahar ta iso. Rahila da Ma'u da kayan su suka taho tare da yaransu daman na faɗa musu in suka zo sai an gama suna can kuma sai ga Sameena sai da muka rumgume ga shi dai ƙanwar Gimbiya ce amma tana ƙaunata saboda da Allah. Daga Rano ta ke sannan ta sauka a gidana. Su Munnira daman ai suna nan sai suna ya tashi. A ranar mai ƙunshi ta zo ta yi mini saloon kuma tun safe na je shagon Amesty ta yi mini. Har su Munnira sun ce za su yi ƙunshin. Can sai ga Saude ta iso itama sai na ji daɗi su Khaleesat ne sai gobe amma Laila Ya Auwal ya ce mini ta na hanya.
Gida ya kacame da ayuuka. Da yake za su yi waina sai sinasir da aikatau muka kai sannam za su yi alale da shinkafa jalop mai kaza. tun da akwai naman miya da Yallaɓai ya aiko da shi. Raguna kuma uku Yallaɓai zai yan ka ma Rukayy suma ragunan su Suwaiba na faɗa mini su Anty Bahijja suna ta surutu ni a bakin ta ma nake jin raguna biyu Ya Usman ya siya masa ɗayan kuma Mimisco ce kuma ya ce tun da da sunan Rukayya a ka ba da su to duka za a yanka mata su. Sannan nima na ba da a yi mini tsire sannan na saka mai yin ledojin kayana na hijabai ya buga mini na suna da jakar nan mai ɗauke da sunan Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna) name on 17 November 2020. Cut-ceey: Hauwa'u Yusuf Muhammad(Jidda) and Maimunatu Yusuf Muhammad(Baby) Lemuka da ruwan roba katan katan Yallaɓai ya saka a ka sauke mini sanman ni kuma za mu yi zoɓo da kunin aya duk za mu saka a robobin ma su ɗauke da sunan Rukayyatu. Wanda a ledan za a saka mutum da jalof ɗin shinkafa mai kaza sai tsire da zoɓo wannan na in zai tafi gida ne. Da yamma kwandon tumatir da solon tattasai da attarugu mai yawa Musbahu ya zo da shi tare da gyararrun kaji guda ashirin a buhu, lokacin su Anty Bahijja da su Gimbiya duk suna gidan ba aikin da suke yi sun kame a gefe suna tsegumi tare da taɓe baki ni ko kallo ba su ishe ni ba, da suka ga an kawo wannan kayan nan kamar su mutu sun ɗauka Yallaɓai ne ke ta kashe mini kuɗi tun da nima yar matsiyata ne ba ni da kuɗi. Ya Hamza da Ya Auwal sai suka suka haɗa mini 150k na kuɗi saboda na ce musu zan yi suna kuma Yallaɓai ba shi da kuɗi, abin da ya ba ni ba za su ishe ni ba, Shi ya sa suka tura mini kuɗi har Datti sai da ya tura mini 30k ya ce na ƙara. Kawu Abba 50k ya tura mini bayan Marwa ta zo mini da atamfofi masu tsada guda uuku da kayan jarirai. Amina ma turamen ta kawo mini da kayan jarirai Farida ita ma turminta huɗu da kayan jarirai sama da guda biyar, tun kafin goben ta yi gefen gadona ya fara cika da kaya sannan wasu ma hidiman su Munnira ke yi ba sa faɗa mini. Suma ita da Hauwa turame uku suka yi min da su pampers da kayan sanyi sannan sun ba da an yi mini yajin jego mai yawa mai daddawa.
Ina can cikin ɗaki ban sani ba Hauwa ta zo tana faɗa mini wai ashe sai da Anty Bahijja ta kira Musbahu tana tambayan shi ko Tafida ne ya ba da saƙo ya kawo? Shi kuma ya ce ni na tura masa kuɗi ba Yallaɓai ba ni tana faɗa minibsai da na bushe da dariya. Matar nan ba za ta bar ni na huta ba na yi alƙwarin in ta sake magana a gabana sai na mayar mata da martani ana cikin gida a na aiki su kuma suna zaunes sai ji da jiyarwa.
Bayan mangariba mai ɗinkin mu ya kawo mini sauran nawa da na yara sai na Farida da Amina. Ni na fita har haraban gida na karɓa muka yi maganar ƙarishen kuɗin ɗinki na dawo kenan falon Baby ta tare ni tana faɗin wai Anty Gimbiya ba ta zo da su Khalipa ba. Kayan ɗinkin da ke hannuna na miƙa ma Amina da ta zo ta tare ni da mgana na ce ta bari in zo. Ina sanye da doguwar riga tsaraban makka ne cikin tsaraban Yallaɓai., rigar ba takai mini har ƙasa sosai ba tana da mayafinta shi ne ma jiki na, na yi kyau ɓulɓul da ni domin ga ruwan zafi daman sannan kuma na saka Aisha lame ta kawo mini mai da shower gel, kuma ina kula da jikina ina cin mai kyau ina shan mai kyau ni kaina na san na yi kyau da haihuwan Yumna sannan cikina ya fara komawa jikina ya yi cif sai na zama wata yar dumduma gwanin sha'awa kowa ya zo ya ganni sai ya ce mini na ƙara kyau da na haihu mene ne sirrin? Na ce Yallaɓai ne sirrina muna ta dariya.
A tsakiyar falon Yallaɓai na tsaya tun da nan suke zaune har da su Halima. Anty Maimuna ba ta zo ba itama Anty Bahijja gulma ne ya kawo ta. Yau ga shi Anty Bahijja na zaune amma bayan gaisuwa ba abin da ya ƙara haɗa su da Ma'u duniya juyi juyi. Gimbiya ta ƙura mini ido tana kallona ita kuma Naja da gayya take ce mini" Ka ga uwar gida a gidan Uncle Tafida" Na yi mata fari ina faɗin" Faɗi ki ƙara Uwargida mai babban muƙami a wajen megida "
Sai ta yi shuru ai ba zan bari ta saƙa mini magana ba Gimbiya na kalla ina faɗin" Baby ta kawo min ƙaran ki." Sai ta yi wani luu da ido kafin ta ce" Ni fa? Me ta ce miki na yi? "Ta ce ba ki zo da Khalipa ba" Anwar ma da za ta zo da shi ya na wajen Halima. "Ayya ai Khalipa na Rano Anty Marliya da ta zo ya saka rigima sai ya bita sai kawai na ce su ta fi dashi." Sai na jinjina kai kafin na ce" Amma ai da kin ce su zo da shi saboda suna ko? Kawai karaf Halima ta saka bakinta.
"Don dai suna me ya sa zai dawo? Suna dai ba biki ba fisabilillahi."
"To nima shi na gani."
In ji Naja.
Anty Bahijja dai ba ta yi mgana ba, ni ko sai na juya ina kallon Halima kafin na ce" Aa. fa ba suna kawai ba wannan sunan ya sha bambam da sunan da kika saba zuwa ko gani Halima. Suna ne garurumin da baki taɓa ganin irin shi ba."
"Allah ko?
Ta faɗa cikin mamaki ni kuma sai na gyaɗa mata kai, muna cikin haka ne sai ga su baby da murna da akwati Laaila ta iso mutanen Abuja. Muka rumgume juna ina yi mata maraba ta gaggaisa da su Anty Bahijja. Yara wajen ɗaukan wata leda suka yagata kayan ciki ya zube kayan fulawa ne ta yo mini cincin da donot sai cake, ina ta faɗa sai ta ce ai namu ne ta zo mini da shi saboda gobe. Ta ce mini ma ta saka ƙanwarta ta yi mini meatpie gobe za ta kawo. Su Amina duk sun taho falon da suka ji tahowar Laila.
Munnira ta daddage ta rangaɗa guɗa Amina na ta ya ta. Ina ta dariyan farinciki na ce"Na gode Anty Laila." "Ba komai an zama ɗaya. Kin ga yadda yayanki ya ruɗe. Ki yi ki gama aikin nan ki tafi kayan fulawan nan ma duk tare da shi muka shiga kasuwa muka siyo komai ina cewa ya bari na siya da kuɗina ya hana shi dai faɗi yake Sadiya ce ta haihu ta yi ma Mama takwara saboda haka muma za mu yi ma wannan haihuwan na ta kara."