Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 18

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 18

Turken gida book 3 cmplete Chapter 18: Turken gida book 3 cmplete Chapter 18. A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai…

3,339 words

A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai kayan jaririya guda bakwai bayan su pampers da mayuka da rigunan sanyi. Har su Aina sun ƙariso suna ta ɗaga kaya suna gani da farinciki. Amina ta ranguɗa guɗa tana faɗin" wannan yarinya ta ga gata. Ta shaida ita ɗin yar dangi ce gaba da baya."

"Tabbas yar dangi ce. Ya Hamza ya nuna bajintarsa ga Ya Auwal ma ya nuna na shi Ubangiji Allah ya bar zumumci."

Aka amsa da Amin gabaɗaya da gayya ba na ce" Kuma duk sun tura mini kuɗi duk da su na yi wasu hidiman." Mu mun man ta da su Gimbiya a falon ma ballanta su ce da gayya mu ke yi sai da daga baya ne da muka haɗa ido da Gimbiyar sannan na ce bari nima na ɗan ɗana.

"Na daɗe da sanin ni yar dangi ce amma na ƙara ganin kara a haihuwan Rukayyatu. Na ga karamci a wajen ku yan uwana na gode. Alhajin mu ma buhun shinkafa cir shanshera ya ba ni saboda Rukayya" Su Rahila har da kabbara Ni kuma na cigaba da faɗin "Mijina ya yi mini dukkan gata na gode masa. Sannan ƙawayena da ku dangina gabaɗaya kun rufa mini asiri kuma ina mai gode maku uUbangiji ya ruɓanya muku."

Munnira da Amina sun fi kowa zaƙin murya wajen amsawa da Amin Munnira har ta na faɗin wani abun ma sai gobe. Ta ba ni hannu muka tafa ni da ita. Gabaɗaya su Gimbiya sun gama muzanta Anty Bahijja ma ba san tafiyarta ba na ji daɗin haka saboda ta fahimci ba Yallaɓai kaɗai ya yi mini hidima ba, Gimbiyar ma sai wajen tara na dare suka fita tare da Naja da Halima sai bayan tafiyar su ne da muka zauna da Sameena nake jin wasu manganganu. Ni da ita ba mu taɓa zama mun yi maganar zama na da Gimbiya ba sai ranar. Kusan raba dare muka yi muna hira na faɗa mata wasu rigingimun da suka faru tsakanina da Gimbiya. Itama tana ba ni wasu labaran da ban san da su ba.

Ashe Gimbiya kishi take yi da ni da tana da iko da tuni ta koreni. A bakin Sameena nake jin ko maganar haihuwan ta ce Tafida sai rawam jiki yake yi a kaina kuɗin shi duk a kaina da yayana ya ke ƙarewa to daɗin abin ma dai ban yi irin haihuwanta ba mace na haifa. Haka ƙannenta suke ta faɗa da masu goya mata baya. Kuma wai a haihuwan nan da na yi sai da ta nemi ya ranta mata kuɗi ta biya kuɗin shipping, amma ya ce mata ba shi da kuɗi aamma ni ga shi nan ya ba ni kuɗi ina ta wadaƙa har suna na shirya mai kama da biki. Har cewa ta yi yadda Yallaɓai ke jin maganata ko Nene albarka.

Na yi dariya kafin na ce ma Sameena." Duk maganganun su Anty Bahijja a kaina ne itama ta ɗauka. Ni gaskiya na riƙe kuma shi ke riƙe da ni har gobe. Maganar hidimar suna kuma wallahi kayan abinci da kayan sawa kawai Yallaɓai ya yi mini. Sai sauran abin da ba a raasa ba. Maganar gaskiya nima na yi hidima da kuɗina sannan ku ma da muke tare kun yi mini amma ba kuɗin Yallaɓai ba ne balle hankalinsu ya tashi kar na karar da kuɗin ɗan'uwan su."

Sameena ta ce wallahi ita ta sani ita ko magana ta ji a kaina ba ta yarda. Lamarin Gimbiya ya daina ba ni mamaki tun da kishin take so a yi to za a yi. Sannan suna kuma za a yi sai dai ta mutu.

Ni Allah ya ji ƙaina da ban yi haƙuri a lokaci haihuwar Gimbiya ba, da tuni an buga mini tambari amma yau da na yi haƙuri ga shi komai ya wuce abin da Yallaɓai ya yi mata ko rabin shi bai yi mini a haihuwan Rukayya ba amma Na tsaya mata a ƙahon zuciya saboda kishi da baƙin ciki.

*Janafty**TKGB3I09*

RANAR SUNA. Talata. 17,November. 2020.

A safiyar talata muka tashi da hidiman sunan Rukayyatu(Yumna). Da yake duka nan suka kwana tun asuba suka tashi da aikace aikace kafin ka ce kwabo an gama komai. Alele ne ma ƙarshen gamawa amma waina tun asuba suka fara suya tun da tun a daran jiya suka haɗa ƙullun wainar miya kuma da safen nan wuta kawai suka ta da mata tun jiya sun gama haɗa komai. Kafin azahar komai ya kammallah gida ya fes sannan duk mun yi wanka amma ba mu saka anko ba sai bayan ƙarfe biyu amma ni da yara da ba su je makaranta mun saka sabbin kaya muna walwali. Yunma ma tun safe a ka yi mata wanka a ka saka mata kyakyawan kayan jarirai masu kyau da safa da takalminta na yara mai kyau da hula cikin kayan da Yallaɓai ya ba ni kuɗi na siya mata ne.

Da safen nan ya zo ya gan mu har Amina ta matsa masa sai da ya tsaya muka yi hoto. Shima ya sha farar shadda har da babban riga har sai da na ce masa " Yallabai hala kai ma walima za ka haɗa mana?

"A'a kawai na yi shigar fararen kaya ne domin nuna murnata a wannan ranar"

Abin da ya faɗa mini kenan na yi shuru kawai ina kallon shi ya yi kyau sosai. Sajen sa na shafo in da tsillin furfura suka fara fito masa, Yallaɓai fa yanzu shekarunsa wajen arba'in da takwas ne yana ƙoƙarin shiga gidan hamsin Allahu akbar jiya ba yau ba, ni ina ta kallon shi a matsayin ɗan saurayin da na aura ɗan shekaru ashirin da bakwai da takwas a duniya.

"Kallon fa Madam?

Shi kan shi ya gaji da kallon sa da nake yi sai da ya yi mini magana sai na yi mirmishi. Na isa gare shi na rumgume shi, shima sai ya kama ƙuguna ta baya yana faɗin" Wata Sadiya ta yi kewar Yusuf ɗin ta ko? Ya faɗa yana sumbatar wuyana. Sai na noƙe ina ɗan mirmishi mun daɗe a haka muna shaƙan turaran juna sannan muka saki juna lokaci ɗaya muna masu kallon juna. Mun raja'a a kallon juna sai da shigowar Amina da kukan Yunma ya fargar da mu sannan muka saki juna na karɓeta na zauna gefen gado shima biyo ni ya yi shi ya zage min zip ɗin gaban riga ta na fito da nono ina ba ma Yunma. Yana zaune gefena muna hira yana faɗa mini Tariq da Kawu sun tura mai kuɗi wai ya ƙara na hidimar suna.

"Allah ya saka musu da alheri. To sai ka ƙara mini wani abu don Allah Yallaɓai."

Na faɗa har langwaɓe kaina sai ya wani kalle ni kafin ya ce" Da ga jin na ce an ba ni kuɗi sai ki ce na ba ki? Ke yanzu me ya rage ba ki yi ba ko ba ki siya ba? "Yallaɓai ban ɗauko mai DJ da mai hoto ba fa" Na ƙarishe faɗa cikin shagwaɓa har ina tura masa baki.

Yallaɓai sakin baki ya yi hakan bai ishe shi ba sai da ya riƙe haɓa yana faɗin" Kika ce me? "Na ce DJ da mai hoto. Domin kasan Haihuwan Yumna na dabam ne za a sha shagali." "To ni ba da ni ba." "Acikin gida ne fa Yallaɓai ba matsala tun da duka taron na mata ne." "Ba amince ba." "Yallaɓai." "Sadiya na ce ban amince ba ko?

Ya faɗa yana mai kallona a fuskarsa da maganarsa na fahimci ba wasa yake yi ba.

"To shike nan."

Na so na yi fushi ne amma sai na ga bai damu ba kawai ya miƙe yana saɓa babbar rigan shi. Duƙawa ya yi ya sumbaci goshin Yunma kafin ya dago nima ya sumbaci kumatuna lokaci ɗaya yana faɗin" Na tafi. Take care a yi suna lafiya." Da dai na ga zai tafin sai na ce to ya taimaka mini da kuɗin zan kira ko mai hoton ne.

"Wani irin mai hoto kuma Sadiya? In hoto kike so ba ga wayoyi nan ba? Sai kin gaji da hotuna yau."

"Ni fa ba irin shi ba. Na camera nake so"

"Lalle."

Yallaɓai ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni ba ni da kuɗi kin cika tsarabe tsarabe Sadiya. Suna ba dai a ci a sha ba ne? Kuma na tanadi abinci miye wani hoto? Hoton ma da a ka ce haramun ne?

Ni dai ai sai na kasa mgana ina ji ina gani Yallaɓai ya fice ya bar ni zaune bai ba ni ko sisi ba, to ya za a yi ya ba ni shi da ya ce hoto ma haramun ne. Dj dai tun da ya hana amma mai hoto kam zai zo daman mun yi magana da Samira class mate ɗina ita ce na taɓa zuwa sunan yaronta na ga an kira shi sai ta ce mini ƙanin mijinta ne. Na ɗauka zan samu wani abu a wajen Yallaɓai ne sai na ƙara tun da ban samu ba sai na ɗauka cikin kuɗina na tura mata rabi, anjuma da yamma zai zo, na samu kuɗi sosai ko Anty Zabba 20k ta tura mini ta ce ba yawa ni ko na ce mai yawan kenan, ina ta mata godiya. Har mai makeup na samu ita kuma ƙawar Anty Khaleesat ce tare suka yi makaranta ta yi mata mgana itama anjuma za ta zo ta yi mini kafin baƙi su fara suwa.

Kaf yan uwan Mama na gandun albasa sun taho mini suna. Kuma na ji daɗi sai na sauke su a ɗakin su Jidda. Falon Yallaɓai kuma na ce a bar ma dangin Yallaɓai saboda ba na son ƙananun mganganun falon su Jidda kuma yan gidanmu da sauran mutane ciki kuma ga bedroom ɗina na zauna ni da ƙawayena da mutanen arziƙi. An kawo sinasir da tsiren sannan tun jiya a ka haɗa da kunin aya suka ɗuɗɗura a gorinan suka saka sticker a fridge ma suka kwana ina ganin haka sai na kira su Ya Aina na ce su raba komai kashi uku, ɗaya namu ne da ƴan'uwan mu ɗaya kuma na yan uwan Yallaɓai ɗaya kuma ni da ƙawayena da yara tun da Baby ta ce mini yan ajin su za su zo Jidda dai na san hali ba gayya za ta yi ba.

Bayan na saka an diɓar ma su Gwaggo na ba da a ka kai musu sannan na saka Hauwa ta ɗibar ma Gwammaja suma suka aika da shi can wajen su Nene. Na saka suka ɗibar ma Yallaɓai na ce zam kira shi in yana office ne zan kira Musbahu da Adnan matan kuma na ce su ɗibar ma yaran su da mazajen su a yi komai cikin tsari. Na bangaren mu ragamar na hannun Amina na bangaren su Yallaɓai kuma Munnira ce ni dai na gama jan kunnenta kar ta yi faɗa da kowa a yi suna a tashi lafiya. Ta ce mini ba za ta yi ba amma ni na san sai ta yi mgana ni da na san halin Munnira.

Karfe biyu na rana mai kwalliya ta iso kusan ma lokaci ɗaya suka iso tare da Khaleesat wai mota ta lalace musu a hanya. Itama ta kawo mini turamin atamfa da riga tare da kayan sanyi na karɓa ina ta godiya. Swiss lece na saka cikin wanda na siya na ɗinka sannan a ka tsantsara min kyakyawan kwalliya wanda tun kafin a gama kowa ya shigo sai ya yi santin kyan da na yi kyau ma sai da a ka gama ta yi mini wani irin ɗauri mai kyau da na duba madubi na ɗauka jidda ce tsabar yadda na dawo kamar budurwa. Na yi amfani da takalmi baki mai tudu kaɗan da mayafi baƙi da jaka, Na saka ɗan kunnaye na masu kyau da tsada, ba ni da zinare ko na zobe sai da na yi hawayen takaici na tuna wanda a ka siya mini da Sadaki na, Yallaɓai ya saka na siyar da shi muka cinye kuɗin, da cewa in ya samu zai siya mini wani har yau lokacin bai yi ba ina jin ma ya manta da abin da ya faru. Ni kaina na san na yi wani irin kyau duk kuma in da na gifta Ƙamshi ke tashi, oil ne mai bala'in, wajen wata mai siyar da turaruka a faceebook na san ta Maryam kitty. Tun da na fara siyan turarenta ban taɓa saka shi ba a yi santin kamshin ba Yallaɓai ya daɗe da sanar da ni yana son ƙamshina. Har na ce in na samu kuɗi zan ce ta haɗa masa na maza daga baya da ya ɓata mini rai na fasa.

Yumna ma an sauya mata kaya ta yi kyau daman ta sha kunshi a hannu da kafa da Ya Murja ta sake kun sa mata yau da safe yau ma mun so komawa asibiti amma sai Yallaɓai ya ce mu bari gobe da safe kar mu je a yi mata allura ta dawo da rigima amma dai tun kwana uku da haihuwanta wanzami ya zo ya cire mata belu sannan ya yi mata askin gashin kanta kamar yadda ya zo a cikin sunna. Zuwa biyu da rabi shagalin suna ya kamkama, baki suna ta zuwa ban yi tunanin zan tara mutane haka ba ni da ban damu da zuwa suna ba, duk sun saka ankon su sai suka yi kyau sosai. Maijidda Bala daman ta zo garin lokacin da na haihu da ya ke mijinta ya samu aiki a Dutse sun koma can da zama ita ce ta yo mini gayyar su Samira da Hauwa jamilu sai da na yi ƙwalla da suka kawo min pampers da mayukan jiki da hoda na jarirai sai safa da huluna suka ce kuɗin da a ka haɗa mini ne suka siya mini da shi, duk da ina ba da wa in na gani amma ba kowanne na ke yi ba, amma dai tabbas na ji daɗi na kuma martaba wannan karan da suka yi mini, sun kuma saka ankon su gwanin ban sha'awa. Muna cikin bedroom ɗina tare da su muna hiran yaushe gamo. A nan Rahila ta kawo musu abinci sinasir da waina sai alale da ruwa da drinks can cikin gida kuma su Munnira na ta ji da baƙi.

Suwaiba da Jamila sun zo mini suna da wuri amma ko Gimbiya sai wajen uku na rana ta zo tare da Halima da Naja. Mimisco daman ta ce mini tana Abuja amma yaranta ƙananun suna nan, Anty Maimuna ba ta zo ba sai can wajen la'asar suka zo ita da Anty Bahijja. Su Nasara da suke kusa duk sun zo mini suna kuma an ba su abinci kamar na kowa ba nuna bambamci ko da suka zo na sauya kaya na saka anko da suka shigo suka ganni sai da mamakinsu ya nuna tun ballantana da suka ga gefen gado na cike da kayan arziƙin da a ke kawo mini. Gimbiya ta ta ba ni saƙo a leda Anty Bahijja ma ta ba ni leda Babba cike ta ce na su ne gabaɗaya daman haka suke yi bai ɗaya suke mini hidima in har na haihu. Naja ce kawai ta ɗauki Yunma amma bayan ita haka suka fita ba su ɗauke ta ba sun fita fuska ba daɗi domin ba haka suka so su ganni ba. Ga shi sun tarar da ɗaki cike da mutane su da ba su yi anko ba sai suka ga su ne ma dabam a wajen domin kowa ya yi ban da su.

Ba abin da zan ce ma mutane sai godiya domin sun yi mini karam kaya sai da na koma jefa su a ƙasa saboda gadon nawa ya cika kowa ba ya zuwa hannu rabbana in ba a bani saƙo a leda ba za a ba ni kuɗi hatta Ya Abubakar da Ya Muntari sun tura mini kuɗi sannan matan su ma sun zo sun kawo mini turame, sai da a ka yi sallar la'asar sannan mai hoto ya zo a haraban gidan shi da yaran shi suka yi decration na ɗaukan hoton. Mamaki kawai na ke ba ma su Anty Bahijja sun kasa magana na fito da tawagata mun sha hotuna zafafa na shiga na fita da kaya sama da kala biyar ni da Yumna, na kuma gayyaci su Anty Bahijja zuwa hoton sun shiga amma a cunkushe Gimbiya ma mun yi ni da ita sannan mun yi da yara. Muna cikin hoton ne sai ga ƴa'ƴan su Anty Bahijja da na Anty Maimuna waɗanda ke gida wasu sun yi aure wasu kuma suna makaranta. Ana gamawa da hoto suka saka kiɗa a speaker suka yi connecting da waya daman Munnira na da home thearter ita ta zo da su daga gida saboda ta ce chasu za su yi ni dai na sulale na koma cikin gida na kira Musbahu na tambaye shi Yallabai ya ce yana office tare da Kawu sai na ce ya zo gida ya karban musu abinci ba daɗewa sai ga shi ya zo na saka Mubeena ta je ta kai mishi har da na shi gabaɗaya.

Sun ta saka kiɗa su suna ruwa ni dai ban shiga ba, ina da ɗinki a ƙasana duk da ya kusa warkewa amma gwara na kiyaye amma da Munnira da Hauwa da Amina suna rawa na shiga na yi musu manni, Yumna ta na hannun Sameena itama ta shiga tana juyawa, har su Suwaiba duk sun shige daman su ai ba ruwan su ana cikin shagali ana ta farinciki suma Gimbiya da tawagarta suna wajen Anty Maimuna dai da Anty Bahijja sun yi mini sallama za su tafi na saka Munnira ta salleme su da ledan su ta ce mini sai da Anty Bahijja ta taɓe baki kafin ta ce"Lalle Tafida ya riƙe ma Sadiya kan macijin har da wani leda ne in mutum zai tafi? Duk abincin da aka ci bai isa ba? Ni dai a yadda ta faɗa mini ta ce ba ta tanka ba amma ni na san ƙarya take yi sai ta ba ta amsa. Sun tafi sun bar su Gimbiya da yaran su ina ga sai daga baya suma za su tafi.

Ana cikin shan wakar ado gwanja na kujeran tsarkar gida, Munnira ta sauya zuwa kirarin uwargida. Kirari ne da wani mawaƙi ya yi ga uwargida je, kuma tabbas kirarin ya yi sosai ni dai ina ta dariya da farinciki su ka ja ni cikin fili suna kuma bin kirarim suna nuna ni.

"Uwar gida ran gida in babu ke gida ya ɓaci. Haka zalika kowa ya zo ke ya tarar. Ke ce Amarya kuma ke ce uwargida, ke kika fara kafa gida saboda haka kowa ya zo ke ya tarar. Ke ɗin dai ce Uwargida haka za su gan ki kuma haka za su bar ki, hassadansu sai dai ta koma kansu. Allah Ya barki da Alhaji Tafida ya kuma kashe ki a ɗakin Tafida. Takalmin kaza mutu ka raba."

Ina ta dariya saboda duk in da a ka ce Megida sai su sauya suna su kira sunan Yallaɓai. Jin daɗin kirarin ya saka na fiddo kuɗi a jaka ta sabbin yan ɗari bibbiyu da Khaleesat ta ba ni na riƙa manna musu. Daga baya ma Jamila kashe speaker ɗin ta yi ta ɗaga muryanta ta na rausayawa a gabana ta fara faɗin.

"Yau taken naki ne Uwargida a gidan Tafida. Uwar gida ran gida shalele a wajen Tafida. Kowa ya zo ke za ya tarar. A buga a bar ki sai ta Allah ta yi Uwargida sai gaban ki in da kike so. Wallahi ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya. Mun sani mun kuma tabbata da tsohuwar zuma ake mgani. In ka ji ana a wasa a wasa ba kaifi, ke ce wakiliyar Tafida kowa ya zo arziƙin ki ya ke ci, kin zama Tafida Tafida ya zama ke, maganarki a ke yi wa ke batun yan karere. A matsa a matsa ga Uwargida Sadiya a gidan Tafida ta hallara na ce a matsa a matsa."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull