Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 19

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 19

Turken gida book 3 cmplete Chapter 19: Turken gida book 3 cmplete Chapter 19. Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu…

3,303 words

Kaina na ji ya fashe,na ji na yi girim girim nan da nan na zazzage musu kuɗaɗen dake jakata sai shewa da ihu ya ta shi Amina da Munnira suka ɗora da guɗa. Har da Sameena a wajen ni ban ma lura da Gimbiya ba, ballantana na ji cewa ina yi da gayya ne sai bayan mun baro haraba zuwa cikin gida Hauwa ke tsegunta min ga Sameena can naja na yi mata faɗa wai ba ta kishin ƴar'uwanta ta biye mana a na yi ma yaruwanta habaici. Na riƙe haba cikin mamaki ina faɗin habaici kuma? Hauwa ta ce wallahi su haka suka ɗauka sai kawai na ce to Allah ya kyauta ni dai fata na mu rabu da kowa lafiya.

Ai ko na gan su da Sameena a can haraba bayan mangariba lokacin da na fito zan raka su Samira. Su ko salla ma ba su yi ba suna nan suna mganganu har da Halima a wajen, suna ganina suka yi shuru Sameena ko daga gani ranta ya gama ɓaci domin juyawa ta yi ta shige ciki a fusace kamar za ta tashi sama ni dai ban ce komai ba iyaka dai na ce musu ya kuka tsaya a nan? Sai Halima ta ce minI wai tafiya za su yi sai na ce su je su karbi saƙo a wajen Munnira sai ta amsa mini da to.

Ni na dawo cikin gida ban san me ya faru ba Sameena ɗayan ɗakin ta shige nima ban neme ta ba kawai muna cikin ɗaki ni da su Ya Aina suna ta ƙwashe min kayan da na samu nawa da na Yumna sai ga Khaleesat ta shigo tana faɗin wai ga Amina can suna hayaniya da ƙanwar mijina mamaki ya kamani ina tambayan kaina me ya haɗa su? Gabaɗayan mu muka fita can falon Yallaɓai muka iske Amina da Halima suna cacan baki ga su Gimbiya zaune Munnira ce me ke jan Amina da cewa ta yi shuru amma Halima da rashin kunya ina falon ta ce ma Amina.

"An zo an samu banza an tattare, za a kai gida. Saboda babu a house ɗin tsoho sannan a house ɗin miji ma babu."

"Ke Amina me ke faruwa! Me ya haɗa ki da ita?

Na faɗa ina shiga tsakiyar su saboda Amina ta ta so tana faɗin" Wallahi ƙarya kike yi. Kin san ko daga yanayin mu za ki san mun fi ƙarfin wannan abun da kike haƙilo a kan shi. Ni mijina ba mai kuɗi ba ne amma yana da rufin asiri kuma a gidan ubana mun fi ƙarfin abincin shekara. Kaf yayyena suna gidan mazajensu cikin rufin asirin mazan kuma akwai ma'aikacin banki da ma'aikacin bankin kuɗin duniya wato CVN kin ga ko tsakanin ni da ke sai a nemi wanda ke rigima kan tsire. Tsiren da dubu biyat ɗin ki ta gama biya miki bukata amma kin tsaya kina ta da jijiyan wuya. An daɗe ba a gamu ba miyau ya tsinke ƙwadayi ya tashi ba."

"Amina."

Haka na ke kiran sunanta amma ce min take yi" Ya Sadiya don Allah bar ni na ga karshen rashin kunyar yarinyar nan."

"Ni ba mara kunya ba ce. Sannan yarinya na bayan uwarta."

"Ke Halima."

Na daka matsa tsawa domin raina ya gama baci na ga tana shirin zagar mini uwa ne a gaba na kuma a gidana.

"Ni da gidan yayana ke ɗin banza?

"Ƙwarai kin fita iko da shi. Abin da a ka hana ki ma ai yayan na ki ya siya ko?

Naja ta shigar mata, Amina na ja ina mata faɗa.

"Me ya haɗa ki sa'in sa da ita? "Ya Sadiya ni fa ban shiga harkan ta ba, ba kin ce na riƙe na bakin mu a hannuna ba, kawai ta na ganina da shi ta ce sai na ba ta leda ɗaya ni kuma sai na ga ai ga shi nan a hannunta Munnira ta ba ta, amma matar nan ta na ce sai na sake bata sai na ce ita ta samu wasu ba su samu ba ta bari a sallami waɗanda ba su samu shike nan ta fara zagina ta na gaya mini mangaganu duk yadda na kai ga haƙurina sai da ta ƙure ni."

"Nima na zo ina yi ma Haliman magana tana neman yi mini rashin kunya."

Munnira ta faɗa tana kallona sai na kaɗa kai ina faɗin" Amina dauka ki ba ta. Ko ba yayanta ya siya ba matar yayanta ce ta siya. Ko guda goma take so ki ba ta ai arziƙi ne a zo wajen ka har kana da abin da za ka ba da."

Ina faɗin haka sai Amina ta miƙa mata leda ukun da ke hannunta, su Ya Aina ma suka ce shikenan ko rigima ta ƙare. Amma sai Halima ta ƙi karɓa sai ma falati da ta yi da ledan daga hannun Amina. Suka watse mini a tsakiyar falon na yi jagale ina kallon Halima na ɗauka iya nan za ta tsaya amma ba ta tsaya ba kamar ta na jirana.

"Ai ni nafi ƙarfin wannan abun. Ke dai ki kara akai gida."

"Kin fi ƙarfin shi kike rigima don an hana ki?

Munnira ta katse Halima. Ya Balki ta saka baki da cewa kowa ya yi hakuri ta duka ta na kwashe wanda Halima ta zubar Hauwa ta amshe ta. Amina za ta sake mgana Ya Aina ta tare ta ni ko daman ina ta danne zuciyata ne amma ba domin haka ba wallahi Halima ba ta isa ba. Gimbiyar ta su na zaune ta haɗa kafafu tana kaɗawa

"Na gode Halima. Tun da masalahan da na nema da ke baki yarda ba, ba na son tashin hankali zo ki fice ki bar mini gidana."

Na faɗa ina nuna mata hanya. Yadda ta kalle ni cikin mamaki ne ya sa na ƙara haɗa rai na.

"E ki fita ki bar mini gidana na gode da sunan da kika zo amma ni ba na son rigima"

"In fita fa ba kika ce?

"E ki fita na ce"

Na ina ƙara jadadda mata sai ta juya tana kallon su Naja suma da mamakina a fuskokinsu.

"Sadiya ƙyaleta kawai. Ai Aminar an shiga da ita ciki maganar ta ƙare."

In ji Ma'u sai na juya ina kallonta kafin na ce" Wallahi sai ta bar mini gida. Ta zo ta fita kawai." Na faɗa cikin ɓacin rai, ina sake nuna mata hanyar fita.

"To ba zan fita ba."

Ta faɗa tana ƙara cijewa har da riƙe kugu.

"Ba zan fita ba, tun da nan ɗin ai ba gidan ki ba ne."

"Ok to ke gidan ki ne?

Na katsete cikin ina saita kaina domin wallahi in na harzuƙa zan iya jawo ta na yi mata bugun tsiya ba ruwana da aurenta ballanta ya'yan ta.

"Ba gidana ba ne amma gidan yayana ne na fi ki iko da shi. Kuma ai nan ɗin ba gidan ubanki ba ne"

A bazata na ji maganar duk lalacewata a idanuwan Halima ban ɗauka za ta iya zagin ubana ba.

"Ke Halima Sadiya kika zaga?

In ji Suwaiba da ta shigo falon yanzu daman na bar ta a ɗakina tana salla.

"Ita wace ce da ba za a zage ta ba. Na ga za ta nuna mini iko ne da gidan Yayana. Alhalin ba ta isa ba ita ɗin banza abanza k"

"Tas!

Sai ƙaran saukan mari suka ji na sharara ma Halima mari sai ga ta dafe da ƙuunci.

"Ko giwa ta mutu ba ta yi lalacewar da kiyashi zai ja ta ba. Ba ki isa ki zo har gidana ki ci kasuwa a kaina ba ƙaryan ki yarinya gwara tun wuri ki shiga hankalin ki, ki kuma kwashi jikinki ki fice mini a gida kafin raina ya ɓaci wallahi na yi miki dukan tsiya"

"Ni kika mara?

"In ba ki fice mini a gida ba duka zan yi miki wallahi."

Na faɗa ina nuna mata zan iya ya ɗin. Munnira ta kwashe da dariya Suwaiba da Jamila suka ce da kyau.

"Me ya sa kika mare ta a kan gaskiyan ta?

Naja ta miƙe tana challanging ɗina.

"Na mare ta ko za ki rama mata ne?

Na faɗa ina kallonta domin kaɗan na ke jira yanzu sai na saka a yi musu dukan tsiya su bar mini gida amma sai na ga Gimbiyar ba ta yi magana ba. Kuma ba ta tsawarta ba.

"In nan gidan Yayanta ne ni kuma matar yayanta ne da gidan da shi kan shi yayan nata a ƙarƙashin ikona suke. Kuma ko shi bai isa ya zo yana mini wulaƙanci ba, ballanta ita ɗin banza. Duk wacce ba lafiya ya kawo ta ba, ta zo ta fice mini a gida kafin na haukace muku."

Kawai sai na fara masifa ina faɗin ni da gidana ba shege ko shegiyar da ta isa wallahi. Amma suka ƙi fita na ce zan yi ma Halima duka Ya Murja da su Rahila suka rike ni ashe tun fara faɗan Gimbiya ta kira Yallabai ana cikin haka sai ga su shi da Kawu ashe ma suna hanyar zuwa ne ta kira shi wai gani nan na kori Halima har ina marinta. Lokacin da suka shigo na gama harzuƙa yana tambayan ba'asi ni ban bi ta kan shi ba Suwaiba ce da su Munnira ke ma yar musu da zence.

"Wallahi sai Halima ta bar minI gida in kuma ba ta fita ba ni zan fita na bar mata gidan."

Na faɗa ina numfarfashi Kawu ne ke ba ni haƙuri har yana cewa" Gwara da kika mare ta. Kuma kina dai-dai da ki kore ta tun da, ba ta da kunya." Yallabai da suka yi tunanin zai goyi bayan su sai ya kware musu faɗa ya yi mata kaca kaca ya kuma ce ta fita ta bar gidan tun da ba alheri ya kawo ta ba.

"Amma Uncle."

Naja ta tare shi za ta kare ma Halima.

"Rufe min baki kawun me? Me ya sa ba ki tsawarta mata ba?

Ta yi shuru ta kasa mgana Gimbiya ma tas ya yi mata ya ce ta iya kiran shi ta faɗa masa na mari Halima amma a gabanta Haliman na yi mini rashin kunya ba ta iya mata mgana ba.

"Ni miye nawa a ciki? Na saka baki sai a ce kishi ne. Ba ruwana kar ka sakani a ciki "

Ta faɗa tana wani tura baki ni saboda haushi ciki na koma ban san yadda suka ƙare ba amma na so wallahi na yi mata dukan tsiya. Kuma ta ƙara dawo mini gida ta gani sai ta raina kanta. Sameena ke faɗa mini daman suna jirana ne sunq ta zagina wai na yi albuzurranci da kuɗin Tafida na ce bakomai na isa ne. A nan ta ke faɗa mini yadda suka yi mata wai ta shige mini saboda munafunci ita kuma ta ce tana tare da ni tuntuni saboda Gimbiya ba za ta ja baya da ni ba.

Ranar raina ɓace na kwana da safe a hanyar mu ta zuwa asibiti ya ke sake ba ni haƙuri na ce bakomai. Mun je an duba ɗinkina suka ce ya kusa warkewa sannan an sake yi ma Yumna allura. Mun dawo gida na iske suna ta suyan ragunan da aka kawo su a yanke yau da safe. Daman na san magana za ta je ta dawo sai da Anty Bahijja ta kirani wai me Halima ta yi mini na mare ta? Na ce rashin kunya ta yi mini buɗe bakin ta sai ce mini ta yi ashe ba daɗi ni ba na yin rashin kunyar ne? Ni kuma na ce ni ban bi kowa gidan shi na yi masa rashin kunya ba itama gidana ta zo kuma ko yau ta dawo wallahi ta ƙara mini rashin kunya duka zan mata ba ma mari ba. Ai sai ta ce to kar na fasa mu ka kashe waya zukata na ƙuna.

Ranar yini na yi zuciyata ba daɗi da wuri suka gama suya suka ɗibar mini nawa. Sai na su na can Gwammaja. Na saka su Ya Aina suka ɗiba na su har da y'an can gandun albasa. Nima na ɗibar ma su Hauwa a ka raba da yaji kafin yamma gida ya watse har su Laila suna koma Ɗorayi za su kwana washegari su ɗau hanya. Ina ta musu godiya na su Samira Rahila na ba mawa na ce ta aika ma Maijidda za ta kai ma su Samira. An yi taron suna an ta shi lafiya gyaran gidan washegari Saude da Marwa da Mubeena suka gyara mini tun da sai ranar da Yamma Kawu ya zo ya ɗauke ta suka koma rano.

Tun da a ka yi suna a ka gama na mai da hankalina wajen renon Yumna. Ta tsiri rigiman dare ba ta barina na yi barci ɗan kumarin da na yi duk na fara sakewa. Ga shi Yallaɓai can gidan Gimbiya yake kwana nan ya gama cika mini baki shi bai amince ya koma can ba amma sai ga shi an gama taron suna gida ya watse amma bai dawo ba ni kuma ban yi masa magana ba daman na san can munafumcin ne irin na su na maza. Sai dai ya zo duba mu safe da yamma. Daga ni sai yara suma suna zuwa makaranta sai yamma asabar da lahadi kuma Tahfez Jidda har ta kusa sauka izifinta hamsin da biyar Baby kuma ta na cikin izifinta na ashirin. Ni kaɗai a gida ga fama da aiki ga fama da Yumna wacce ta cika rigima ga tsotso mintina kaɗan ta fara rigiman nono shi ya sa ta zama wata burkuta da ita.

Muna da kwana goma sha biyar da haihuwa na ga Yallaɓai ya dawo kwana a gida na kamar zan yi masa magana sai dai ban yi ba. Kwana biyu tsakani kuma sai ya ɗauke kafa ya koma can ni sai na koma kawai na zura masa ido saboda na ga jeka ka dawon da ya ke yi, na kasa gane nufin sa.

Sai a tsakanin Munnira ta sake leko ni a bakinta nake jin rigima ce suka yi shi da Gimbiyar ta sa har sai da Nene ta shiga ciki. A kan dai maganar kuɗin da ta ce ya ara mata na shipping ɗin kayanta ya ce ba shi da kuɗi amma ni ya ba ni kuɗi na yi suna har ina kiran mai hoto. Ita ko abin ya tsaya mata a rai ta ce mini ranar ta na gidan a ka yi har da su Maman farko a shigar maganar shi kuma ya rantse ba shi ya ba ni kuɗin wasu abubuwan ba da kuɗina na yi, amma ba ta yarda ba ita a dole ya yi rashin adalci. Wato dalilin dawowan shi gidana kenan sannan kuma ya koma bayan sun shirya. Ni dai na ce ma Munnira Allah ya kyauta can su ƙarata.

Sai da ma muka yi maganar hotuna da Munnira sannan na tuna na tura ma mai hoto ragowan kuɗin sa ya turo mini hotuna. Washegari ko carbi na yi a status ɗina hotuna ne ba adadi na saka. Na farko nawa da Yallaɓai na saka da yara wanda Amina ta ɗauke mu ranar suna da safe. Na yi caption da cewa" Shekaru ashirin da albarka ƴaƴa uku. Alhamdulillah." Sai na saka wanda muke mu uku ni da shi da Yumna. Shi ke riƙe da ita ni kuma sai na shafa sajen sa. A ƙasan hoton na saka sticker ɗaga hannu na za a saman kai sannan na ce" Jama'a na ba ni Yallaɓai na ne na ga ya fara furfura" Ai ko na sha comments har Ya Hamza sai da ya yi mini mgana da cewa. Ke kina nufin ya dauwama a saurayin da kika aura ne? Sorry yarinya."

Maijidda Bala ta yi dariya ta ce" Sadiya rayuwar auranki da Yallaɓai a bar sha'awa ce Allah ya bar ku tare." Na amsa mata da Amin ba ta san tarin ƙalubalen da na fuskanta ba ne. Ba su san ma an yi mini kishiya ba sai a sunan Yumna na faɗa musu suna ta mamaki ai ni yanzu na yi hankali na kama jama'a. Ni dai ban ɗora hoton Gimbiya ba amma ma tura mata wanda ta ke ciki haka ma su Anty Bahijjs. Yan gidanmu duk na tura musu sun ɗora mu. A gidan su Yallaɓai da ga Mimisco sai su Suwaiba su Munnira daman nawa ne, mazan kuma daman Musbahu da Adnan suka yi ta ɗora mu suna addu'a. Yallaɓai ma turamai na yi wajen guda hamsin sai turo mini emojin mamaki ya yi ni kuma na ce masa miye? Da alaman tambaya sai ce mini ya yi wai wa ya ba ni kuɗin waɗanan hotunan? Na ce tun da bai bai ba ina ruwan shi sai ya turamin na emojin baki da zip kuma ina tunanin bai buɗe hotunan ba, shi ya sa ko a status bai saka ba. Ban damu ba sanin halin Yallaɓai wani lokacin ba ya yin abin da a ke zaton shi da shi sai saɓanin haka

Har Shemau Ma'un ta kirani ta mini barka saboda ma yafe ma Ma'u shi ya sa itama na ji na yafe mata. Ta ce mini in ta shigo garin za ta shigo ta ga Baby na ce sai ta zo so. Kara an yi mini shi sosai kuma na gode ni ce na tara turamen atamfa kaɗan ne babu a hamsin bayan kayan jarirai da sabulai da sauran su da masu tura mini kuɗi. Da na nuna ma Yallaɓai sai da ya jinjina kai kafin ya ce wai ni da kaya sai nan da shekaru biyar na ce bai isa ba. Ya saka albarka yana dariya a ciki na nemi shawaran shi na ce zan ba ma Gwaggo ɗaya Nene ɗaya sabulai kuma na ba su Maman farko da su Inna Mariya ya ce duk yadda na yi dai-dai ne tun da kayana ne. Ban damu ba sanin halin shi, shi ya sa na yi gaban kaina na ware musu da niyyar in na yi arba'in in na je gaishe su na kai musu.

Mun shigo watan december ƙarshen shekara. Ina ta jego na ina kula da kaina gefe ɗaya bikin Alhaji Mustapha na ta ƙaratowa. Ma'u duk ta damu ni ce ma ƙarfin gwiwanta. Sai ma Allah ya sa a ka ɗaga bikin sai Jan ƙarshe. 27 ga watan december na yi arba'In a ranar da na yi arba'in Gwammaja na yini na kai ma su Nene saƙon su suna ta godiya tun da na je Yumna na tsakanin ɗakunan su Maman farko da Hajiya iya sai da zamu fita. Washegari kuma na yini a ɗorayi na kai ma Alhajinmu matarsa nan da nan ya ce shi kan ya saki jidda ya samu sabuwa Gwaggo na dariya ta ce da tsohuwar zuma dai a ke mgani. Ranar ma a wajen Alhajinmu ta yini kuma ikon Allah ba ta yi rigima ba, a jere na haɗa fitan na je gidajen su Ya Aina na je har can gandun albasa wajen su Inna Mariya. Na je gidan Munnira da Hauwa na yi musu yini da ban gajiya wajen kwana goma har Yallaɓai ya ce ba zan sake fita ba duk gari an gama gani na kullum sai na fita sannan na samu natsuwa a gida na fara gyara kaina.

Surayya dee ce mai kayan ɗa'a ta gyara ni da haɗin kazar sababi na masu jego. Daman kuma bayan haihuwata na dage da cin kayan marmari da ganye da kuma kifi domin ƙarin ni'ima. Sannan Amina ma ta aiko mini da Gumba na sha da madara Yallaɓai na ta rara gefe na hana shi sai da na ji na yi tsab sannan na gayyace shi. Ranar na sha sambatu amma na gane ba ni da wayau, domin Yallaɓai kaca kaca ya yi wajen ɓarnan ruwa sai da ya famshe kwanakinsa har yana haɗa wanka ma.

*Janafty**TKGB3J010*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull