Turken gida book 3 cmplete - Chapter 20
Turken gida book 3 cmplete Chapter 20: Turken gida book 3 cmplete Chapter 20. Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen…
3,325 words
Washegari ma bai bar ni na huta ba, ko falo bai bar ni na fita ba sai wajen sha ɗaya na safe su Jidda ma shi dai ya fita suka gan shi suka gaishe shi. Daman ba sa jira na yanzu sun girma komai na buƙatunsu, su suke yi ma kan su. Sai alokacin na samu damar yi ma Yumna wanka sannan nima na shiga wankan kuma na bar mishi Yunma kwance a gefen shi shi kuma yana duba abu a cikin laptop ɗin shi.
Ina fitowa ɗaure da Towel a ƙuguna na iske sa har ya gama abin da yake yi ya ture laptop ɗin gefe. Tambayarsa nake yi Yumna ta yi barci ne? Sai ya leƙata yana faɗin ta soma barci.
"Ai gwara ta yi barcin nan kowa ya huta."
Na faɗa ina mai zama saman stool ɗin madubin dake bedroom ɗin namu. Ban san tahowar shi ba sai kawai jin sa na yi yana shafa min wuya a lokacin ne na ci karo da fuskarsa ta jikin madubin dake gabana.
"Me ya faru Yallaɓai?
Na faɗa ina mai kallon shi ta madubin, bai amsa ba sai ma sunkuyowa da ya yi ya na mai sumbatar wuyana. Tun da na ga haka na sha jikin jikina da sauri na ture shi ina faɗin" Na yi wanka fa Yallaɓai." "Me ya sa kika yi wankan? Mamaki ya sa sai da na ɗago ina kallon shi. "E. Ai ban sallameki ba hajiya." Ya faɗa har yana wani ƙara tsumewa irin shi fa da gaske yake yi.
"Yallaɓai tun daran jiya kake abu ɗaya. Yau da safe ma don Allah kai baka gajiya ne?
Na faɗa ina cigaba da shafa ma jikina man shafawar da na lakuto a hannuna.
"To ni ban gaji ba."
"Ba ka gaji ba?
"E"
Ya amsa mini har yana wani haɗe rai sai na kalle shi kafin na ce" To ai sai dai ka yi haƙuri zuwa anjuma ka ga na riga na yi wanka." Amma Yallaɓai ya ce bai san wannan ba sai ma jikina da ya matso da ƙarfi ya ta da ni tsaye ya rumgumeni yana faɗin. "Ke ce kin ƙara sugar. Wato ta bakin ki haihuwan Yumna na dabam ne." Ya faɗa ya na shafa cikina, hannunsa na bige sai ya kai shi saman ƙirjina yana matsawa da ɗan ƙarfi har sai da na yi yar ƙara yadda na haɗe rai ne ya sa ya fara mini dariya yana faɗin" Ki gama shan kunun ki sai na ƙara horan ki kenan. Me ya sa kika yi wanka ni ban ba ki izini ba?
Kasa magana na yi, kuma abin da ya faɗa sai da ya cika shi. Lalata mini wanka ya yi kuma bayan mun gama ina shirin sauka daga gadon ya riƙo ni wai bai ba ni izini tashi ba haka nan na koma na kwanta ya cigaba da jagwalgwala ni son ran shi sai da ya nishaɗi don kansa ya ce mu je mu yi wanka sai tura mishi baki na ke yi amma ko a jikinsa. Ban samu lafiya ba sai da ya fita sallar azahar ma ta suɓuce masa sai dai ya yi ta a gidaa bayan mun karya a lokacin sannan ya yi mini sallama ya fita.
Yana fita nima bayan na yi sallar na koma barci. Daman Yumna tun da ta ji ruwan zafi take barci. Ba mu muka tashi ba sai gab da la'asar shima ɗin kukan Yumna ne ya tashe ni. Sai da na ba ta Nono sannan na tashi na ɗauro alwala na yi salla sanin Yumna ba za ta kwanta ita kaɗai a ɗaki ba ya sa na goyata sannan na shiga kitchen domin neman abin da zan dafa ma su Jidda kafin su dawo daga makaranta. Da yake Yallaɓai ya yo mana cefane cikin satin nan sai kawai na yi mana cous-cous mai kayan lambu. Da yake ba shi da wahala nan da nan na kamalla shi. Ko da suka dawo ina falon su ina cin nawa Yunma na hannuna tana ƙiriniyar su na yara. Suna dawowa Baby ta fara damuƙarta daman in dai tana gida ba ni da haufin yar reno tun tana kuka in ta ɗauke ta har ta saba in ma ta ganta ta dinga kallonta alamun tana nuna mata sani. Sai da na karɓe ta sannan Baby ta samu daman cin abinci. Bayan sun gama na goya mata ita, Jidda kuma ta je ɗaureye musu kayan makaranta.
Ranar da wuri Yallaɓai ya dawo gidan ko kafin tara mun shige ciki ni da shi da Yumna Baby ta yi barci Jidda ce ke karatu tun da mun shiga sabuwar shekaran 2021 akawai jarabawowi a gabanta. Ni dai kwana biyun da Yallaɓai ya yi a gidana da wayyo Allah na ƙarishe shi duk cinyoyina ciwo suke yi da gaɓɓaina saboda bai sarara mini ba, in na yi ƙorafi sai ya ce wai ai ya yi ƙoƙari wajen kwana hamsin sai na ce ba yana da wata matar ba sai ya harare ni ya ce ita sunanta Saudatu ke kuma Sadiya kin ga kowacce na da nata tarim bambamcin da ya bambamta ta da ƴa'ruwata tun da na ji haka ban ƙara yi masa magana ba.
Da ba ya gidana barci na yi ta sha ina hutawa ina zan iya. Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya. Shekaran 2021 ta zo ma da Yallaɓai da babban buɗi na alheri domin ya dace da samun wani babban kwangilan gina jami'ar kuɗi a nan garin Abuja. Yadda Yallaɓai ke murna ne ya sa na san cewa ba ƙaramin alheri zai samu ba abin farincikin ma sun bashi 70% na kuɗin aikin shi satin kaf yini ya yi cikin farinciki shi ya sa ba tare da sanya ba ya saka Khalipa a makarantar su Jidda. Amma shi Gimbiya ke kai shi da kanta su Jidda kuma Salisu ne. Samuwar kuɗin hannun shi ya sa ya tsayar da lokacin buɗe kamfanin shi ƙarshen watan Feb. Tun da ya ce yana tunanin kayan da ya yi oder su sauka a tsakiyar wata mai kamawa.
A cikin haka ne aka fara shagalin bikin mijin Ma'u. Mu ne gaba gaba masu dannen ƙirji, na ba ma Ma'u gudummuwa sosai a wajen auren nan, a ka yi taro lafiya aka tashi lafiya ba tare da na bari an ga gazawarta ba. Ta ji daɗi ta kirani tana ta yi mini godiya har shi Alhajin ya yi ma Yallaɓai maaganar daidaitarwar mu ba ƙaramin canji yake gani a tattare da Ma'u. Ni daman haƙuri na ce ta yi gashi da ta yi haƙurin har an yi auren komai ya wuce. Har Baaba da ke adawa da ni yanzu ta ɗan sakar mini,nima sama sama tunda daman can ni da ita jininmu bai haɗu ba.
Jidda ta sake sabunta rigister ɗin ta na Jamb. Da ƙyar da saka bakin Kawu Abba Yallaɓai ya bari ta cike ABU zaria a first chioce ɗin ta. Shi dai wai baya so ta yi nesa da gida ni kuma na ce ai duk in da take addu'armu na tare da ita kuma ai zaria gida ce. Hmm kawai ya ce shi fa daman ya amince ne domin an fi ƙarfin shi ba domin yana ra'ayin haka ba. Ita dai Jidda tun da ya amince sai murna ta ke yi sai bayan salla za su yi jamb ɗin da sun zana ta, za su fara rubuta jarabawar fita babban sakandiri. Shi ya sa ba ta zama yanzu ita ce jamb class da lesson har asabar da lahadi yanzu ba ta zama Jidda na ci gare ta kamar mahaifinta in suka saka kansu a abu agaba sai sun ga sun cin ma nasara.
Ranar kawai Yallaɓai ya ce mu shirya da ni da yara gabaɗaya har da Gimbiya mu je mu ga ma'aikata sannan mu ƙarisa mu ga filin da ya siya tuntuni wanda zai gina ma gida da zai haɗe mu gabaɗaya. Ranar lahadi ne kuma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne. Jidda ma ya hana ta zuwa lesson ɗin ta da ake yi musu a makaranta saboda fitan da za mu yi, mun cakaree gabaɗayan mu har Yumna na yi mata gayu, shi muka rika jira tun da yana can gidan ne sai ya kwaso su sai ya zo mu wuce ta gidana.
Sai da suka ɓata mana lokaci sannan suka zo. Gimbiya an ci gayu abaya ta saka ta yane mayafin a saman kanta ta saka wani takalmi mai rufi har da uban gilashi su Khalipa ma sun ci gayu cikin riga da wando yan kanti. Ni daman doguwar rigar atamfa na saka ɗinkin kaftan na saka mayafi kalan kayan sai na saka takalmina baki mai saukakken tudu. Jidda ma haka ita dai Baby pakistan ne riga da wando a jikinta da breziya Hijab. Tana kuma riƙe da Yumna ni ce ke ɗauke da jaka da na sako mata ruwa da ƙyallen goge tumbulunta tun da tumbuli take yi shi ya sa take yi kiba kamar ana hurata.
Mun gaisa sama sama da ta so ta shige gidan gaba ne sai kuma ta fasa ta shiga baya da yara. Ni ko ba ta san mota ba ta dame ni ba, mijin ma gabaɗaya na raba shi ballantana wata motar banza. Muna tafe ni da shi muna hira shi ne ma yake sako ta a cikin maganarmu shima ɗin a daƙune take amsa mishi ban san me aka yi mata ba, ko Yumna ba ta ɗauka ba nima ban tura mata ba. Na fahimci bata kaunar fita ta haɗamu ni da mijina ta aure mini shi, ni ban yi kishi ba sai ita? Mamaki take ba ni in dai fita ta haɗamu gabaɗaya ta riƙa cin mgani kenan. Ni ba na ta ita in muka gaisa ban ƙara jan ta da magana sai dai in har ita ce ta sake yi minI magana. Ina da aji ba zan zauna ina bin kishiya ba. Har muka isa hira muke yi da Yallaɓai yana faɗa mini yanzu ƙasa za su fara amfani da shi sama sai zuwa gaba. Wancan kuma wajen tun da ya siye shi tuntuni yanzu yana matsayin mallakin shi ne. Zai ba da hayan saman ƙasan kuma yana tunanin abin da zai saka a wajen.
"Yallaɓai to ka buɗe shagon sai da kayan gine gine mana "
Yana tuki ne amma sai da ya juyo yana kallona.
"E mana. Na ga kai ma in ka buɗe amfaninka ne tun da in kwangila ta samu suma kayan ginin siyansu kake yi."
Sai ya jinjina kai alamun gamsuwa kafin ya ɗan waiwaya baya yana faɗin" Ke fa Daughter ba ki ce komai ba? "Me zan ce? "Ke ma ki ba ni shawara. Kin ga Sadiya ta. Kusan komai da zan yi in na nemi shawaranta tana kawo mini shawarwari masu kyau kuma in na yi amfani da su ina ganin alfanu sosai."
"To ba gashi ta baka ba"
Ta faɗa har a muryanta haushin ta bai boyu ba.
"Duk da haka kema ina son jin na ki shawaran"
Shuru ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai da ya sake yi mata magana sannan ta ce" Ni a ganina me zai hana ka buɗe shagon provision tun da wajen a bakin titi ne." Jinjina kai ya yi kafin ya ce" Good. Ke ma kin kawo point amma na Sadiya ya fi muhummanci. Bari mu fara da na ta, daga baya in komai ya tafi daidai sai a buɗe shagon provision ɗin"
"Ka san shawaran ta za ka ɗauka me ya sa ka na ce sai na yi magana?
Ta faɗa a zafafe.
"Saboda kema kina da haƙƙi a kan haka."
"Uhm"
Kawai ta ce ba ta ƙara magana ba, ni ko ina zaune kamar zan yi magana sai na kwaɓi kaina. Yara ma ba sa jin abin da muke tattaunawa suna ta wasannin su. Gwara ma Jidda amma ita hankalinta na kan Tab ɗin da ke hannunta. Na yi na yi da Yallaɓai ya siya mata waya ya ce sai ta shiga Jami'a. Tab ɗin daman shi saboda karatu ya siya mata. Ko rigister ɗin jam da sim ɗin Yallaɓai ta yi amfani wani lokacin yana da tsauri wani lokacin kuma yana da sauƙin kai. Har muka isa ma'aikata ba ta ƙara magana ba sai ma amsa wayarta da ta riƙa yi lokaci bayan lokaci.
Ƙwarai waje ya yi kyau fiye da labari da gani a hoto. Kafin shiga ma'aikatan akwai babban get in da masu gadi ke tsaro har mutum biyu saboda sace sacen kayan aiki. Sannan daga gefe an makala wani allo da aka yi ma rubutu kamar na zaiba mai ɗauke da sunan ma'aikatan HM TAFIDA AND SON'S LIMITED"
Ma'aikatan na nan a kan titiN zaria road gaba kaɗan da in da office ɗin su yake na yanzu. Kuma wajen babba ne akwai fili a haraba da zai ci kimanin motoci sama da goma. Sannan an yi shuke-shuke daman Yallaɓai na son shuke-shuke. Ko'ina sai da Yallaɓai ya zagaya damu an gama komai fenti ne ma ake ƙarisawa a wani wajen. Office ɗin Yallaɓai babban yana benen sama ne amma tun da ba yanzu za su fara amfani da can ɗin ba sai ya samu wani a ƙasa da aka saka masa suna da zane kamar na zaiba wato Managin Director Md. Har office ɗin Musbahu na gani shima makeke na ce tabbas ya cancanta har sama mun haura shi dai ba a ƙarisa ba amma ma'aikata suna kan aiki. Akwai ɗakin hutawa da sauran su ba abin da dai ma'aikatan ba ta mallaka ba sai godiya.
Ina kallon Yallaɓai ina tuna a farkon auren mu in ya ce mini shi ba ya son aiki a ƙarƙashin wani ya fi son aiki na ƙashin kanshi. In ya ce mini ya na son gina kamfanin shi na zane zane da abin da ya shafi kwangilan gine-gine a shaci faɗi nake ɗaukan duka mganganunsa. Ban taɓa tunanin bayan shekaru ashirin Yallaɓai zai cimma burin sa ba. Sai ga shi ya cimma burin sa da nasara tabbas ya yi aiki taƙuri sannan ya jajirce wahala da rashin kuɗi bai sa ya nuna gazawarsa ba. A gaban yara a gaban Gimbiya na rumgume shi sannan na bashi sumbata a gefen kumatun shi, ina mai faɗin.
"Congratulation Yallaɓaina. Im so proud of you."
Na faɗa ina yi masa wani irin ƙayattacen mirmishi. Sai ya sake riƙo ni gefen kafaɗansa na dama yana mai kallona ya ce.
" Amin. Nima ina alfari dake Sadiya ta. Duk matakin da wannan kamfanin zai kai ke ce a gaba. Kin ba ni dukkan gudummuwar da macen ƙwarai ke ba ma mijinta. Thank you so much haƙika da ban haɗu da ke a shekaru ashirin a baya ba da na tafka babban asara rasa mace kamar ki."
Sai na ji wani farin ciki ya lulluɓe ni har ina ƙara narkewa a jikin shi, Jidda na gefe sai ji muka yi ƙyars ta yi mana hoto. Baby da su Khalipa ba su san ma me ake yi ba suna can suna wasa.
"Jidda Allah ya sa hoton ya yi kyau."
Na faɗa ina dariya. Yallaɓai ko sai faɗin yake yi ta ƙara yi mana wani.
"Kun yi kyau sosai Umma da Abba."
"Mun gode yar albarka ta wajen Abban ta"
Yallaɓai ya faɗa har yana ɗaga mata babban yatsan shi alamun jinjina. Jidda na ta ɗaukan mu hoto kwata kwata na sha'afa da Gimbiya sai da ta yi tsaki na ji sannan na juya muka haɗa ido, wallahi na gan ta harara ta, ta yi sannan ta yi motsi da bakinta ta ɓata rai, duk da na ga abin da ta yi mini ban riƙe shi a wani abu ba sai na juya ina kallon Yallaɓai kafin na ce
"Mun manta da Amarya. Kira ta a yi mana hoton tare mana."
Saboda ba lallai in ni na yi mata magana ta saurare ni ba. Wataƙila za ta iya ganin hakan a matsayin cin fuska.
"Haka ne. Daughter taho mu yo hoto in an gama sai mu yi da yaran gabaɗaya."
Amma sai ta yi kamar ba ta ji ba, sai ma ta juya yana kiran ta ta yi banza dashi ta fita daga office ɗin na shi, da muke ciki Jidda na ɗaukan mu hoto.
"Ka je ka yo lallashi Yallaɓai."
Na faɗa ina kallon sa. Ni kaina yaƙe nake yi amma a ƙasan zuciyata ina jin wani abu kamar kishi na motsa mini.
"Me a ka yi mata? Ƙyaleta."
Ya faɗa ne kawai amma sai na ga hankalinshi ya tafi a kallon ƙofa ko za ta dawo sai na ƙara roƙon sa da ya je ya ba ta hakuri ta zo a yi musu hoton.
"Ƙyale ta kawai."
Jin abin da ya sake faɗa ya sa sai na kama kaina ban ƙara yi masa magana ba. Ina lura dashi saboda fushin da ta yi ya sa sama sama muka yi hotuna da sauran yaran sai ya ce a bar shi haka ya na so mu je filin can mu gani ya mai da mu gida yana da wajen zuwa. Ko da muka fito tana cikin mota kila da ace da motarta ta zo sai dai su haɗu a gida. Ya yi sallama da masu gadin sannan muka tafi a cikin motan ma Khalipa sai da ya sha mari wai ya ta ka mata kafa.
"Kawai saboda ya taka ki sai ki yi masa irin wannan marin haka?
Yallabai ya faɗa cikin mamaki, ni kaina ban yi maagana ba ne amma marin da ta yi masa ya yi tsauri a bi sa dai laifin da ya yi.
Yaron sai ya fashe da kuka Baby ce ke lallashin sa.
"Sorry. Khalipa sorry."
Amma sai ƙara ɓare ma mutane baki yake yi, ni dai na sake tallafan Yumna dake hannuna da ta yi barci faɗan da ba ruwanka daɗin kallo ne dashi.
"Kar ki sake yi masa irin wannan marin."
"Ya yi laifi kar a hukunta shi?
Ta faɗa a zafafe ni a tunanina ko dai daman suna faɗa ne kafin su fito? Domin na ga a zafafe take kamar za ta kai duka.
"Ni dai na faɗa miki kar ki sake. Ba a hana ki yi masa hukunci ba amma ba mari irin haka ba."
"Na ji."
Ta ce a ƙasa ƙasa, shima sai na ga ya yi wani ƙyaci na ɓacin rai a raina na ce can ta matse muku. Tafe tafe sai ga mu a anguwar Alu veneu in da Yallaɓai ya siya wawaken fili. Mun sauka daga mota dukkan mu muka shiga filin babba ne Yallaɓai ke nuna mana yadda fasalin ginin zai kama. Ya tabbatar mana da kan shi zai yi zanen gidan shi, ya yi masa irin fasalin da ya ke so a cewarsa yanzu ginin ne a gaban shi bayan taron lunching na buɗe kamfanin shi za a fara yin katanga a saka get sai kuma a fara gini.
"Flat huɗu zan yi a cikin filin nan in sha Allahu."
"Kuma duk a gida ɗaya nufina a haɗe?
Na faɗa ina kallon filin, babba ne amma flat huɗu na su waye?
"E mana. Naki ɗaya na Daughter ɗaya. Ɗaya nawa ɗayan kuma ko saboda baƙi."
Ina shirin sake magana Gimbiya ta yi zaraf ta ce. " Me ye amfanin yin shashen baƙi tun da ga shashen ka? Infact ma mu kan mu na san akwai spare room a bangarorin mu."
Sai na zama ƴar kallo, domin kai tsaye Yallaɓai ya ce" Duk da haka flat huɗu zan yi." "Babu amfanin yin haka." Ta bashi amsa sai ya share ta bai yi magana ba. Ni kuma da ƙarin bayani sai na ce" Yana da amfani ko saboda su Khalipa in sun tasa zai musu amfani.
"To kin ji ma."
Ya faɗa cike da ƙarfin gwiwa. Amma ita duk ba ta gamsu ba na san fargabanta kar Yallaɓai ya ce zai ƙara aure amma saboda na ƙara samun tabbacin sai na tsaƙalo maganar.
"Yallaɓai ko dai shashen ɗin Amarya ne."