Turken gida book 3 cmplete - Chapter 21
Turken gida book 3 cmplete Chapter 21: Turken gida book 3 cmplete Chapter 21. Yadda ta yi saurin kallona da razana a yanayin ta shi bai yi haka ba sai ma…
3,278 words
Yadda ta yi saurin kallona da razana a yanayin ta shi bai yi haka ba sai ma dariya da ya yi kafin ya ce" Wannan kuma lamari ne na Ubangiji. In ya kaddaro mini zan gode masa." "Yallaɓai dai zai yi ginin mata huɗu ne. Wata ƙila shashen naka ma in ka ji ra'ayin aure zai tashi a naka ya koma nata." Ni na faɗa amma yana ta dariyan nishaɗi.
"Ke ko?
Ya faɗa ya na nuna ni da hannu. Nima dariyan nake yi ina faɗin" To ai gaskiya ne." Gimbiya na tsaye amma ta kasa magana sai dai ina kallonta ta gefen ido ta ƙara kumbura. Har tana wani kifta idanuwana kamar na yi dariya sai na kanne. Yaran suna can gefe Khalipa da Baby suna ta wasan ƙasa Jidda na tsawarta musu har da Anwar da shima yana tafiyan shi ko'ina.
Ban ɗauka za ta yi magana ba tun da har muka baro wajen muka shiga mota. Muna hanya zai fara sauke mu gida Gimbiya ta kira sunana daga bayan mota.
"Madam"
Da man haka take kira na ko ta ce Maman jidda.
"Na'am"
Na amsa mata ina ɗan waiwayawa bayan in da take zaune ita da yara.
"Kina ta wani dariya yana faɗa miki in aure na cikin kaddaransa zai ƙara."
Sai na saki dariyan nishaɗi kafin na ce" To kuka kike so na yi? "Amma bai kamata ki yi masa dariya ba." "Ikon Allah." Ni da shi muka haɗa baki wajen faɗa.
"Ka gama aure Daddy. Ni da Madam mun ishe ka in sha Allahu."
"Gaskiya ne."
Na biye mata ina ƴar dariya.
"Ba ku isa ba. Ku ji minI ƙarfin hali ni na ce kun ishe ni ne?
"Ko ba ka ce ba mu mun ce ko Madam?
Ta faɗa tana sako ni a ciki.
"Tabbas. Yallaɓai mun rufe ƙofa. Gimbiya ce a madadin biyu nima a madadin biyu shike nan mun cike maka ƙofa."
Na ƙarishe faɗa ina dariya.
"Shi kenan ko."
Ta faɗa cikin jadadadawa.
"To ba ku isa ba."
Ya faɗa yana wani haɗe rai irin da gaske nake yi ɗin.
"Mun isa har ma mun yi yawa."
"Haka kuka ce?
"E haka muka ce."
Ta mayar masa da martanin cikin nuna da gaske take yi.
"Ok we shall see."
"See me?ba abin da za mu gani sai alheri wallahi ko ɗauko auro ka yi ni da Madam sai mun ruguza shi. Mu ai ka gama auro wata mace kuma a duniya tun da ka aure mu."
A yadda take magana kaɗai ya isa a fahimci da gaske take yi. Har suka sauke mu a gida ina jinjina zafin kishin Gimbiya. Wato wata rana in har Yallaɓai ya ɗauko auro akwai yaƙin duniya na uku ita da Yallaɓai kanbu! Da abin na kwana a zuciyata gari na wayewa na kira Munnira na tsegunta mata yadda muka kwashe da Gimbiya jiya. Matar nan da ta laulayo ashar sai da na ce.
" Ke Munnira ki ji tsoron Allah wannan ashar ɗin fa?"
Na faɗa ina dariya saboda na ga ta ma fini kambama lamarin.
"To ba dole na danno ashar ba. Ba a aure ita aka auro ta! Ba a yin kishiya ke kika bari aka yo miki da ita? Ba na son iskancin banza."
Ina ƙyatata dariya na ce" Ita ai za ta zo a matsayin kishiyar wata amma ita ba za ta bari a kawo mata wata a matsayin kishiya ba."
Munnira ta ce" Taɗijam! Tana da aiki ni tun da har aka yi miki da ita fata na yanzu itama ayo mata ta ji in da daɗi."
Ina dariya na ce" To waya sanin ko zai ƙara." "To ke ba ki ga alamu ba? "Ban gani ba amma in dai ana maganar za ki gan shi cikin nishaɗi ba ya ƙoran maganar gaskiya." "An gama magana. Tafida in ya ga wata yar shila zai yi tunanin ƙara aure." "Zai iya yuyuwa tun da ya iya yi mini kishiya itama ba abin mamaki ba ne don ya yo mata."
"Namijin kenen. Uhm Maza mutanen mu." Muna ta dariya ni da ita, har ina tsokanarta in Nasir ya gano wata yar jan fata haka. "Ta zo ai ba a kaina za ta zauna ba." Na yi mamaki jin haka Munnira ta yi sanyi. "Ke kuma yau? Kin saduda ne yanzu ta shigo." "To na ga ko ka yi haukan ma in suka yi niyya sai sun yi." Na kwashe da dariya ina faɗin" In dai ji maza kawai matar nan bana son sadudan ƙarya"
Itama dariyan take yi mun daɗe muna mgana kafin mu yi sallama. Da Yallaɓai ya dawo gidana sai da na yi masa taɗin da cewa" Kai Gimbiyar taka ba ta son kishiya. Sai ka shirya in dai za ka ƙara aure za ta yi maka daru."
"Za ma ta yi ta gama ne. Tun da har na iya yi miki kishiya ita nata mai sauƙi ne." Amsar da ya ba ni kenan, sai na kalle shi kawai ina dariya. Ban sani ba amma haka kurun na ke ji a jikina watan wata rana Yallaɓai zai iya ƙara aure ko bai cike gurbin ba. Wata ƙila kuma ya yi gadon marigayi mahaifin su. Tun da jajirtattace ne, sannan yanzu ya samu buɗin da riƙe mata sama da biyu ba zai zama wahala a gare shi ba.
Maganar lunching ɗin kamfanin Yallaɓai ya ta so. Ya ce ya na so a yi komai a gama kafin azumi. Shi ya sa ya ke ta shirin sa muma muna taya shi. Sanin rana ce babba a gare shi, ya yi katin gayyata kuma ya gayyaci mutane sosai abokan karatun shi, abokan harkokin shi, ƴan uwan shi na nesa da na kusa. Ya gayyaci yan siyasa amma ba sosai ba, Kawu Abba da Tariq sun yi gayya suma daga bangaren su. Tun da shi Tariq a matsayin shi na lauyan kamfani shima ya gayyato ƴan uwan shi lauyoyi. Kaf ƴan uwan shi maza za su hallarta hatta Ya Usman da ke nesa. A hankali yake ta shirin sa mun yi shawara da shi, akan za a yi abincin na sadaka sannan zai ba da a yi masa saukan Qur'ani acan ma'aikatan kafin a fara amfani da shi ya ce mini To. Abincin da lunching kuma Mimisco ta ce za ta ɗauki nauyin komai da komai har da ruwan da za a sha da lemu a wajen. Kayan da ya yi oder suka iso kamar su kujerun ofishoshi da I.C, cafet da sauran su a ƙarshen watan Febuary kayan suka sauka daman kuma ranar lunching goma ga watan March ne. Ranar lahadi za a fara taron goma na safe zuwa ƙarfe ɗaya na rana.
Ya ɗauki Nene da su Maman Farko ya kai su wajen sun gani sun yi murna da addu'o'i. Alhajinmu da Gwaggo da na je na faɗa musu sun kira shi sun yi masa fatan alheri yana ta jin daɗi. Shi dai ya ce walimarsa ta maza ne amma in za mu yi gayya a gida ƴan uwa a zo a yi murna bai hana ba, shi ya sa duk na faɗa ma yan gidanmu. Sai su Munnira sauran tawagan gidan su Yallaɓai yan bangaren Gimbiya ne. Ni Jamila da Suwaiba ne daman na sa ka ran in ma za su fito ranar kenan. Da bakin shi ya ke faɗa mini Gimbiya kayan snaks ta yi mishi har da ƙananun kofunan mug da sunan kamfani, ni kuma lokacin ba ni da kuɗi. Duk na ci ubansu da sunan Yumna hijaban ma tun da na haihu sau ɗaya aka kawo mini. Ba domin Gimbiya ta yi ba a'a sai domin nima matarsa ce kuma ya kamata nima na nuna nawa bajintar. Da na yi tunanin memo amma sai Adnan ya faɗa mini su Anty Bahijja sun yi masa Memo, sai na ce tun da har an yi memo da mug ni bari na yi jaka wacce za a saka gift ɗin a ciki ba ni da kuɗi amma haka na yi ƙarma ƙarma sai da Ya Auwal ya cika mini wajen 30k sannan na ba da a ka yi masa guda hamsin ta hannun Adnan.
Jakar ta kwali ce an saka sunan kamfanin ne. Congratulaton Md Yusuf Muhammad Inuwa on your opening ceremoney of your company. Hm Tafida and son's Limited. Cut ceey. "Miss Sadiya Yusuf Muhammad, Hauwa'u Yusuf Muhammad, Maimunatu Yusuf Muhammad and Rukyyatu Yusuf Muhammad. Bai sani ba, kuma na ce kar Adnan ya faɗa masa sai ranar kawai sai dai ya gani. Bangaren abincin sadaka ni ya bar ma ragama buhun shinkafa za a dafa da wake, sai na raba biyu rabi na ba ma Maman Saude aikin rabin kuma sai na ba ma Maman Naana mai yi mana kitso. Na ce in sun yi su raba shi ga almajirai sadaka ce. Bangaren kayan da zai saka kuma ranar ya zo ya na cw mini da ya saka suit ko manyan kaya wanne ya fi? Ni kuma na ce ya saka manyan kaya zai fi ƙwarjini. Sai ya ce shima haka ya ce amma Gimbiya ta ce suit zai saka har ta siya masa ma ni kuma jin haka ya sa na ce duk wanda ya yi masa ya saka zai yi kyau tun da da man shi ɗin mai kyau ne. Sai ya ce kawai shi dai zai saka manyan kaya. Ya nuna min wata dakakkiyar gezner fara da ya siya ya ba da ɗinki har da babban riga. Sannan ya siya cover shoe baki mai kyau da hula dara sai agogon fata mai tsada. Ranar dai Yallaɓai sai wanda ya gan shi kawai amma kyau ne zai yi har sai ya gaji da kyau.
Tuni status ya ɗauka yan gidan su kaf sun ɗora katin gayyatan suna ta ya shi murna. Nima na dora har Samira ta yi min magana ko mata na zuwa na ce mata e amma mata gida ne, nan take ta ce mini za ta yi ma Hauwa magana wata ƙila su shigo fatan alheri. Su Ya Hamza duk na tura musu sai aka ci sa'a a satin zai shigo Kano ya ba ni tabbacin zai je Ya Auwal dai a waya ya kira Yallaɓai ya yi masa murna. Amma Ya Muntari da Ya Abubakar da Datti duk sun ce za su je. Sai jin daɗi nake yi domin ni kaɗai na san dararen da Yallaɓai ya ɓata bai samu barci ba saboda zuwan wannan ranar mai ɗimɓin tarihi.
****. . RANAR TARO. 10 March. 2021. Lahadi.
Ko da ba a gidana Yallaɓai ya kwana ba amma ya biyo ta gidana ya yi mini sallama ni da yara muka rumgume shi domin ta ya shi murna a wannan rana mai matukar muhimmamci a gare shi. Kun ga Yallaɓai? Cancaɗi ni kaina sai da na saki baki da hanci ina kallon shi. Domin ya dawo min wani ɗan saurayi ɗan shekara talatin. Da man ya na son fararen kaya ko don ya san suna yi masa kyau ne oho? Har da wani farin gilashi su Yallaɓai manya an fito sharr. Tare da Kawu Abba shima ya sha Babban riga. Ya kuma kyauta domin da Marwa ya taho mini duk da tana ta fama da laulayin ciki. Tariq na hanya bai riga ya iso ba. Hadda su Khalipa su kan yan kanti suka saka da su za a je ni kam ni da ƴa'ƴana ko ba mu je ba mun cakare a gida har ko da Yumna na mata gayu kuma itama sai da Yallaɓai ya ɗauke ta na ce murna ta ke taya shi tun da tana jin muryansa ta fara harba ƙafafu.
Sun fita gidana tara da wani abu ba a fara taron ba sai sha ɗaya na safe. Har sarkin Rano ya zo da Tafidan Rano kanin mahaifin Gimbiya. Ta waya muke ganin komai live Adnan ke yi da wayarsa ya na turawa a group ɗin gidan su. Irin su Musbahu suna ta hotuna suna ɗorawa. Sun gayyaci yan jaridu da masu Video da hotuna. Muna gida amma kamar mu yi tsuntsuwa mu gan mu a wajen Baby sai tsallen murna take yi, su Ma'u da Rahila ne suka zo mini sai su Munnir. Hauwa ta ma dafa shinkafar jalop mai nama muka ci muka sha da lemu. Suma duka mazajensu na can wajen taron
Kafin a fara Yallaɓai ya turo min saƙo. Saƙon da na maimaita shi sama da sau goma saboda daɗin kalaman na shi. saƙon da ya samu wajem zama na musamman a ƙasan zuciyata.
"Sadiya ta ki sani kome yau na zama Nene ce sila tun da ita ce ta haife ni. Amma ina so ki sani bayan ita ke ce mace ta farko da kika bani ƙwarin gwiwa. Na gode Sadiya ta. Adnan ya nuna min abin da kika yi mini. Ina rubuta miki wannan saƙon cike da godiya a bakina. Zuciyata cike da ƙaunarki. Hawayen farincikin kasancewarki matata sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana."
Nima sai na ji taruwan ƙwalla kafin na fita daga shauƙin da na shiga wani saƙon na shi ya sake shigo mini.
"A yau a wannan rana mai muhimmaci nake so na faɗa miki ni ke ce abu mafi muhimmanci da na mallaka a rayuwata. Na gode Abar ƙaunata. Yusuf na ƙaunarki. Ki tuna haka Halimatussadiya."
Sai kawai na samu kaina da ƙwalla, har sai da na saka hannu na share Allah ya sa ni kaɗai ne a ciki daga ni sai Yumna. Ita na ja na rungume ni ina jin wani irin shauƙi na motsawa daga ƙasan zuciyata.
An fara taro cikin nasara bayan an nuno hoton Yallaɓai ya yanka igiyar nan da almaka shi, tare da addu'oi. Sannan a ka shiga ciki da a ka ƙawata shi da kujeru da kanofi. Manyan baki sun yi jawabai sosai na godiya da jinjina da burgewa. Kawu ya ba da labarin Yallaɓai. Tariq ya ƙara da irin gwagwarmayan da ya sha kafin ya kawo yau. Sannan ya yi amfani da haka wajen zaburar da matasa domin su nemi na kansu. Ya faɗi har tarin alherin da Yallaɓai ya cimma a shekaru ashirin da wani abu . Mafi rinjayen ciki samar da matasa aiki daga karƙashinsa sannan da gina wannan ma'aikatan bayan ya fara da kama hayan ƙaramin shago sai gashi yau ya mallaki ƙaton waje da sunan mallakin shi. Ya Usman ya yi jawabi a matsayin babba Yaya.
"Yusuf ƙanina ne amma zan iya cewa ya fini jajircewa. Ni gidan soja kawai na sani amma shi ya san gwagwamarya. Ya san zane ya san gine gine, ya san ya ɗau kankare akan sa. Sanadin shi matasa da dama sun samu aikin yi. Ciki har da ƙanin mu dake aiki a ƙarkashin sa. Abin da zan ce shi ne Yusuf is a good Exmples ga matansa mu. Ku tashi ku nema. Ku jajirce in kuka gwada kuka faɗi ku sake miƙewa ku cigaba da tafiya. Watan wata rana za mu iya samun kamar Yusuf ko ma waɗanda suka zarta shi da samun ɗaukaka sanadin jajircewarsa. Congratulations My Bro. Allah Ubangiji ya sa nan da shekaru goma duka arewa kowacce state kana da reshe Amin."
Sai tafi raf! Mu kan mu mun zagaye waya muna kallo kamar mu yi hawaye. Mimisco ce ta ɗora jawabin a status har mijinta ma ya je shima ya yi jawabi, daga ƙarshe ne Yallaɓai ya yi jawabinsa. Da farko ya yi sallama sannan ya yi salati ga Annabi(SAW) sannan ya gangaro wajen gode ma iyayen shi. Tare da addu'an Allah ya jiƙan Marigayi Muhammad Inuwa.
Mace ta farko bayan Nene ni ce wacce Yallaɓai ya gode mawa. Wallahi ina kallo ina hawaye ban sani ba su Munnira na ta minI sowa amma ni ina hawayen farinciki.
"Zan miƙa sakon godiyata zuwa ga Matata Uwargidana. Sadiya Sulaiman Yashe(Mrs Yusuf Muhamma Inuwa) bayan iyayena da ƴan uwana. Ita ce macen da ta yi gwagwamaryan rayuwa da ni cikin samu da rashi. Sadiya ta kasance wata mace mai hikima da baiwa. Wannan sunan kamfanin idea ɗin ta ne, duk da burina ne amma da shawaranta yau na kai ga gaci. Sunan da ke jikin wannan kamfanin ma nata ne. Ita ta samar da shi. HM TAFIDA ba mallakina ba ne ni kaɗai. Namu ne ni da ita da ƴaƴanmu. Ni zan kasance Md a idanuwanku amma asalin mai juya kujeran tana gida. Miss Sadiya Yusuf Muhammad ina miki jinjina ina kuma ta ya ki murna. Da girmamawa ina mai sanar dake MUN YI NASARA"
Ya faɗa sannan ya ɗaga hannu sai ihu da tafi. Daga nan Vedio ya yanke tuni na ɗauka na saka a status ɗina na ma kasa magana sai emojin kuka na saka. Munnira faɗi take yi" Wallahi gaskiya ya fada. Da bai ambace ki ba da ya yi butulci." Ni dai ina ta sharan ƙwallar farinciki. Sauran jawabin na shi godiya ne ga amininsa guda biyu Tariq da kawu sai ƴan uwan shi gabaɗaya sannan ya jinjina ma Musabahu domin da jajircewan shi suka samu nasara. Daga ƙarshe ya yi godiya ga matasan da ke aiki a ƙarkashinsa domin ya ce ba domin su ba, da bai yi nasara a yau ba a ƙarshen ƙarshen dai ya kira sunanayen su Jidda da su Khalipa da Gimbiya ya gode musu a cewarsa suma suna cikin labarin nasarar shi a wannan ranar. Kafin taron ya tashi sai da matasan da yake aiki da su bangaren gine gine suka bashi award na takarda da gilashi sannan aka tashi taron za a ci abinci a raba gift shike nan taro ya tashi.
Ni Yallaɓai ya gama mini komai. Na maimaita kallon jawabin sa ban san iyaka ba. Ya Hamza sai da ya kira ni ina ɗauka ya ce" To Miss Sadiya yau ta sha godiya wajen Mr. Yusuf. Ya dai ce ke ce Md shi acting Md ne." Sai kawai na hau dariya shima ya na taya ni. Nan ya fara mini nasiha ya na fadin" Kin yi abu mai kyau ko Alhajinmu in ya ji zai ya ba miki kin tsaya ma mijinki. Da daɗi ba daɗi yau kun yi nasara. Congratulatons"
Saƙonni sai da suka yi mini yawa nima murna ake taya ni. Tabbas ni ma na samu nasara. Datti daga wajen taro gidana ya taho ya na ta sake ba ni labari. Shima ya taho da jakarsa na gift faɗi yake yi" Ya Sadiya Yallaɓai ya gama tashin kaina da jawabin sa. Danƙari." Kowa sai ya ce abin ya burgeshi ba kamar wasu mazan butulu masu manta alheri ba. Ni kam Yallaɓai bai manta da ni ba ranar ba a gidana yake ba amma da daddare bayan sun sallami baki sai da ya zo gidana lokacin duk an watse daga ni sai yara. Marwa ma tun dazu Kawu ya zo ya ɗauketa.
Baby ta yi barci Jidda ce ta ce sai ta jira Abban ta. Ai ko muna jin buɗe get ni da ita muka fita. Ni saboda zumuɗi da sauri a falo na baro Yunma. Sai ga ni, ni da Jidda muna rige rigen faɗa ma Yallaɓai. Ture Jidda ya yi yana faɗin" Jidda ya za ki ture mini mata kuma" Tana dariyan farinciki ta ce" Congratulations Abba. You make us proud Today." Sai ya sake ni ya rugumeta sannan ya ɗago ya dafa kafaɗunta yana faɗin.
"Thank you Fav Daughter."
Ni ko sai da na sumbaci gefe kumatunsa sannan na ce" Da ikon Allah ka fara hawa matakin nasara kenan." "Amin My Sady." Ya faɗa ya na mini mirmishi, ya shiga gidan amma ruwa kawai ya sha ya tafi bayan na ce gobe ni zan ba shi na wa gift ɗin.
"Mai daɗi ko Sadiya ta?
"Sosai ma. Ya fi mazan ƙwaila."
"Ina godiya Hajiya ta."
Muka raka shi har haraba muna ɗaga masa hannu.