Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 2

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 2

Turken gida book 3 cmplete Chapter 2: Turken gida book 3 cmplete Chapter 2. "Topha. Me ya faru? Aminar ba ta da lafiya ne?

3,367 words

"Topha. Me ya faru? Aminar ba ta da lafiya ne?

"Lafiyanta ƙalau na zo ganinta ne kawai."

"Ki ce zumumcin ganin Amina ya motsa. To yara fa? Ko suna Gwamnaja?

"Ban sani ba. Gida na bar su tare da babansu."

"Wata ƙila suna gidan Gimbiya."

Da haka muka bar mganar hira muka ɗan yi sama sama kafin mu yi sallama sai da ta ce yaushe zan dawo?

"Ban saka rana ba."

"Eyye. Kin ji ki tsaya ki ɗan huta"

Ina mata dariya daga nan muka yi sallama. Ita ta faɗa ma Hauwa ina kaduna sai gashi ta kirani, su har sun damu da ni amma wanda ya ijiye ni na koma ni da banza duk ɗaya a wajensa. Ban taɓa tunanin zan kai tsawon kwanakin ba tare da Yallaɓai ya neme ba amma ganin har na kwarari sati biyu bai kirani ba sai na daina mamakinsa na kuma ɗauka da gasken na gama yi ma Yusuf amfani a rayuwarsa. Duk na yi waya da su Ya Aina amma ban nuna musu ba na gida ba har Ya Balki mun yi magana wasu maƙotan ta na son Hijabai na ce na hannuna sun ƙare sai an sake kawowa.

Ban faɗa ma Amina komai ba, itama ba ta dame ni da mgana ba. Amma tabbas a raina na san cewa ta yi shuru ita kanta ta san lafiya lafiya ba zan zo gidan ta na shantake ba. Ashe ma duk ta na lura da motsi na ban sani ba sai ranar da na ke da sati biyu muna zaune a falo ni da su Yunma in na kallon su tuna wa na ke yi da nawa yaran da suka yi min nisa ina cikin kewarsu sai na yi kamar in kira Yallaɓai ba sabo da shi ba sai saboda yarana amma sai na ji na kasa domin wani irin haushin shi na ke ji haushin da ban taɓa ji ba shi ya sa na ke danne komai amma Allah kaɗai ya san damuwar da na ke ciki. Duk dare sai na yi kukan ɓarin cikina kuma sai na ji na ƙara jin haushin Yallabai daga ƙasan zuciyata.

"Ya Sadiya"

Amina ta kirani sai na bar kallon yaran da ke wasa a tsakar falon na koma ina kallonta. Tsaye ta ke a gefen kujeran da na ke zaune daman muna tare ne muna hira sai ta tashi ta shiga ciki.

"Mu je ɗaki na mu yi mgana."

Ban kawo cewa mganar Yusuf ba ne da ba zan yi saurin tashi na bi ta ciki ba

Gefen gadonta muka zauna gabaɗaya.

"Me ya faru?

Na faɗa ina kallonta ganin ta yi shuru ta ƙi mgana.

"Ya Sadiya kun samu matsala da Baban su Jidda ne ko?

Sai na kalleta kafin na ce" Me kika gani?

"Abubuwa da yawa. Ba ya kiran ki ke ma haka. Infact ma ni ban taɓa ganin ya kiran ki ba tun dawowar mu daga asibiti."

Sai na yi shuru na kasa mgana saboda ba ni da amsarta a lokacin

"Ko bai san kin taho nan ba ne?

"Ya sani"

Na amsa mata da sauri ina ƙokarin mai da kwallar da suka cika min ƙwarmin idanuwana.

"Ya sani fa kika ce?

"Ya sani Amina."

Wannan karon na faɗa cikin kwarin gwiwa. Sai kuma hawaye suka ke ce min wasu na korar wasu sai ta ruɗe ta riƙo hannayena ta na faɗin.

"Na shiga uku ba dai sakin ki ya yi ba ko?

"Bai sake ni ba."

Na amsa mata ina kallonta ina ganinta ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce" Alhamdulillah da sauƙi." Sai kuma ta koma ta na kallona kafin ta ce" Me ya faru? Na kasa mgana kawai sai kuka ya kece min, na riƙe hannayena Amina a saman fuskata ina kuka har da shessheƙa.

"Amina wai ni Yallaɓai ya kalli idanuwana ya ce ina yi ma baƙin ciki da Matarsa da ƴaƴansa saboda ban ƙara haihuwa ba."

Amina ta ƙwalalo idanuwana ta na kallona. Hannayenta na jinƙe cikin nawa ina jin kamar za ta iya cire min ƙuncin da ke zuciyata in na faɗa mata halin da na ke ciki.

"Amina bai tsaya anan ba sai da ya yi min gorin haihuwa. Ya ce ina baƙin ciki da yayansa kuma sai dai na mutu. Sannan ya ce gida gidan shi ba gidan ubana ba ne."

"Shi Yallaɓan ya ce miki haka?

Amina ta katse ni cikin mamaki da alja'abi na gyaɗa mata ina kuka ina ba ta labarin duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe na ƙarishe da faɗin" Amina na taho gidan ki cikin damuwa da kuka. Tsawon kwanaki nan Yallaɓai bai nemi ba? Me ya ke nufi? Hakan da ya yi ba ya nuni da abin da ya faɗa har zuciyarsa ba ne? Amina yau Yallaɓai ya nuna min ba ni da sauran amfani a wajensa Gimbiya ce matar arziƙi uwar yaya maza ita ce mai amfani yanzu a wajen shi da ƴan'uwan shi."

Na faɗa ina kuka. Kukan baƙin ciki kukan kishi da kukan nadaman yadda na yarda da Yallaɓai daga ƙarshe ya tozartani na baro gidanshi na zo gidan ƙanwata ina zaune. Me ya fi wannan tozarci da cin zarafi? Amina ma kamar ta yi kuka mamaki ma ya hana ta mgana.

"Shi Yallaɓai nan duk ya aika miki haka Ya Sadiya?

"Ya wuce wai Amina. Ni yanzu na rasa ya zan yi? In na kashe aurena ina za ni Amina? Shekara sha takwas da aurena jidda ta isa minzali amma ban wuce tozarcin Namiji ba."

Sai a yanzu na ke jin sauƙi sauƙi da na ke fada ma Amina damuwata. Amma a kasan raina danƙare ya ke da nadama. Nadamar yadda na yarda da duka kalaman Yusuf Inuwa tun a ranar farko na da fara ganin shi da ace ban bari ya ruɗe ni da kalamansa ba da wata ƙila wannan ranar ba ta zo ba.

"Gaskiya ya ba ni mamaki. Ƙiri ƙiri ya yi miki rashin adalci ki yi mgana kuma ya nemi tozarki? Tsskani ga Allah ya dace ya ce da yaro zaku riƙa kwana? Ba ya tunanin in kina buƙatar sa fa?

"Shi ba ya buƙatata domin ina tunanin rabo na da Yallaɓai na ƙarshe ranar da na samu cikin da ya zube ne Amina. Sai ya zo gida na har ya koma can wani abu ba ya shiga tsakanina da shi."

Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso min.

"Bai kyauta ba. Kuma wallahi zai gane kuren shi."

Kai kawai na girgiza na kasa mgana saboda in na zauna ina faɗin wani abun ma sai a ce na yi masa sharri ne.

"Amina ki yi fatan ki mutu tare da mijinki da ƴaƴan ku. In kuma ƙarin aure na cikin kaddaran shi ki yi ta fatan Allah ya ba ki haƙuri da juriya sannan ya ba ki wuyan ɗauka. Domin kishi na da zafi sannan masifa ne kuma bala'i ne"

Amina sai ta yi shuru ta kasa mgana. Ni kuma ina share hawayena na cigaba da faɗin" Domin duk zaman lafiyan da ke tsakanin ki da mijin ki in ya auro ta sai ta shiga tsakanin wannan zaman lafiya. Sannan duk amincin da ke tsakanin ki da shi sai ta zo ta raba shi haka ma duk yardan da ke tsakanin ku wata rana sai ya ce ke ba abin amincewa ba ce. Duk faɗan da za ku yi da mijin ki ke kaɗai ba zai kai girman faɗan da za ku yi in ya karo aure ba ki sani duk haƙurin ki da kawaicin ki wara rana sai an ƙure ki. Ki sani kishiya ƙalubale mai zaman kanta a gidan aure wanda ba a yi mawa ba ko za a bashi labari ba zai taɓa ganewa ba sai wanda ya tsinci kan shi a yanayin kaɗai zai iya sanin raɗaɗi tare da ƙalubalen."

"To in haka ne Allah ya raba mu da kishiya."

"In ta alherin ce fa ?

"Ko ta alherin ce Allah ya yi mana tsari da ita."

Sai Amina ta ba ni dariya sai da na murmusa. Ita manaki ta ke yi a tunanin Yallaɓai ba zai taɓa juya min baya ba na manta namiji mai manta alheri wasu mazan da yawa batulai ne, an yi musu alheri su manta su nemi saka ma mutumin da ya yi musu alheri da sharri. Amina ta ce ita ma ta na goyon baya kar na sake na neme shi har mahadi ko ya bayyana tun da bai san mutumci ba.

Maganar da muka yi da Amina sai ya fama min da mikin da ke cikin zuciyata. Ranar sukuku na yini sannan na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitar da zan nema ma kaina ba zan zauna takaicin wani namiji ya kashe ni ba, in ma bai kashe ni ba ya saka min zuciyan da zan rayuwa sunan mattaciya. Ya zama dole na koyi jajircewa na kuma koyi tsayuwa da ƙafafuwana. Na yi tunanin ba zan cigaba da fakewa a gidan Amina ba in mijin ta ya dawo lamarin zai zama wani iri. Ba kuma zan koma Kano ba saboda duk da in da na je ba za a fars duba masalahata ba. Ni kuma a yanzu na shirya ma Yallaɓai da duk abin da ya ke takama da shi. In koma gida Alhajinmu ba zai zauna ina zauna a gida kuma ya yi shuru ba. Gwara kawai daga nan na wuce Yashe wajen Baaba Aminu na fashe masa da kuka ya na tausayi na tabbata zai fara duba masalahata kafin wani abu ya biyo baya.

Haka na tsai da shawara da ni da zuciyata ko Amina ba ta sani ba. Washegarin da muka yi maganar da ita Gwaggo ta kira waya ta har gabana ya faɗi na ɗauka ma ko maganar ba na gida ta je musu ne amma sai na ji ta ce kwana biyu ta ji ni shuru ne ya sa ta kira ni. Ga ma Alhajinmu nan ya na ta cigiya har ta ba ni Alhajin mu ka gaisa ya na min zolayan shi da ya saba na Hajiya Dubu kwana biyu. Sai na yi ƙaryan ba na ɗan jin daɗi ne shi ya sa har muka gama waya ina ɗari dari saboda ba na so su ji wani abu yanzu na fi so komai mai zai faru ya zama na tsakanina da Yallaɓai ne kamar yadda aka saba. A ranar har Marwa ma mun yi waya da ita amma itama ban faɗa mata ba saboda da ta ji Kawu Abba ya ji shi kuma in ya ji zai yi shuru ba faruwan haka sai Yallaɓai ya dauka shi ɗin ya isa ne shi ya sa na kai ƙaran shi wajen abokinsa kuma ɗan'uwan shim shi ya sa ban bari ma ta fahimci wani abu ba.

Ranar da na ke da kwana ashirin a gidan Amina da daddare Gimbiya ta kira wayata. Har sau biyu ban ɗauka ba saboda ban san me ya haɗa ni da ita da za ta kirani ba sai da na ga kiran ya ƙi ƙarewa sannan na ɗaga kiran amma maimakon na ji muryanta sai na ji muryan Jidda.

"Jidda."

Na faɗa ina mai tashi zaune saboda mamakin jin muryan ta ban za ta ba.

"Na'am Umma mun yi kewar ki yaushe za ki dawo?

Ta faɗa cikin sanyin ta a koda yaushe.

" Ina nan dawowa Jidda. Kuna lafiya? Ina Baby?

"Ta na can falo ita da Abba da Anty Gimbiya."

Wani abu ya tsaya min a ƙasan maƙoshi da ƙyar na ce" Wa ya ba ki waya? "Ɗauka na yi Umma ba ta sani ba. Ina ta tambayan Abba yaushe za ki dawo ya ce kin je Kaduna gidan Umma Amina."

Ashe dai bai manta da in da na je ba. Lallashin Jidda na yi da cewa zan dawo kwanan nan, na ce ta gaishe min da Baby ina nan dawowa muna magana wayar sai na fara hawaye a ƙasan zuciyata ina ta tsine ma Yallaɓai domin shi ne ya yi sanadiyar da na yi nesa da ƴaƴana. A ƙasan raina ina jin daɗi in na tuna yau ni na samu ciki duk da ya zube amma dai na samu sassaucin cewa wataƙila mahaifata za ta iya ɗaukan ciki ba shike nan ba kamar yadda na ke tunani a baya. Ke nan gidan Gimbiya ya tarkata yaran ya kai mata? Oh itama ta ji in da daɗi godiyar ta ma ɗaya daga Jidda har Baby ba yara ba ne ban da girki ba ɗawainiyar da za ta yi musu girkin ma Jidda ta iya makaranta ne kaɗai cikas ɗin ta.

Da safe na tashi fuska a kumbure. Sai kuma Amina ta ke faɗa min Dr gobe zai dawo sai hankalina ya tashi.

"Amina zan zo na tafi ba zan bari Dr ya dawo ya same ni ba."

"Me ya sa?

"Da kunya Amina. To zaman me na ke yi a gidan sama da sati biyu?

Itama sai ta yi shuru domin ta hasaso abin da ni na na hasaso.

"Abin kunya ne fa Amina. Ke ƙanwata ba yayata ba."

"To Ya Sadiya ba sai na faɗa masa matsala kuka samu da Baban Jidda ba?

Hararanta na yi kafin na ce" Ban saka ki ba. Ba ki da hankali yarinyar nan." Ina tunanin wucewa Yashe ya kamani gwara na fara shiri yau na wuce.

"To ina za ki je? Ko gida za ki koma?

"Ba zan koma ba Amina. Zan dai nemi wani wajen na je kawai"

"Ina to za ki je?

Sai na kalleta amma ban yi mgana ba na wuce cikin ɗaki sai ta biyo bayana ta na na cin sai na fada mata in da zan je.

" Ke ki ƙyale ni "

Na faɗa ina jawo akwatina sai ta riƙe ta na faɗin" Don Allah ya Sadiya ki zauna Allah ba na son ki tafi." Ta faɗa cikin shagwaɓa sai ta warce shi daga hannunta ina faɗin. " Na ki wasa ne yarinya"

"Abuja za ki je?

Sai na kalleta shuru ina wani nazari ni ban kawo gidan Ya Auwal a raina ba saboda in dai na je sai ya ji ba a si ba kuma zai kira Yallaɓai. Dama dai Ya Hamza ne shi ne ɗan goya min baya amma shima ba zan je gidan shi ba saboda shima zai iya kiran Yallaɓai ni kuma ba na so ya ji a ran shi na damu da shi ne shi ya sa na je na kai karan shi yadda ya zaɓa nima haka na zaɓar ma kaina.

"A'a ba zan je can ba."

Amina sai ta kasa mgana, ni kuma na fara haɗa kayana kenan wayata da ke gefen gado ta fara kuka alamun ana kira Amina ta fi kusa da wayar ba tare da na kalleta ba na ce.

"Wa ye ke kira hala?

"Yallaɓai na."

Amina ta faɗa a hankali da sauri na kalleta cikin mamaki a kallo nawa ganin haka yasa sai ta miƙa min wayar na karɓa cikin san yin jiki. A hannuna wayar ta yanke kuma ba daɗewa ya sake kira. Sai da ya yi min kira biyae bi da bi ban ɗauka ba sannab shuɗewar mintina huɗu tsakani saƙon shi ya shigo.

"Yaushe za ki dawo ne? Yara sun damu da tambarki."

Yara ne suka damu ba shi ba, to tun da shi da ya ijiye ni bai dami ba shike nan yara kuma shi ne uban su tsaki na yi na dankwar da wayar gefe na cigaba da haɗa kayana Amina ta ɗau wayar ta na dubawa kafin ta ce.

"Ka ji wani kutumar uba wai yara sun damu? Shi ne fa ya damu ya rasa abin da zai ce shi ne ya fake da yara."

"Mtsewww.!"

Muka ja wani dogon tsaki a tare ni da ita sannan muka kalli juna muka yi dariya.

*Janafty**TKGB30B2*

*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*

Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732

Itama Amina sai ta samu gefen gadon da nake zaune ta zauna lokaci ɗaya tana saka hannu ta na taya ni nin ke kayan da na zube kan gado muna kuma sakawa a cikin ƙaramar akwatina. Allah ya sa ma sauran kayan Amina ta haɗa cikin wankin su mai wankin su ya zo ya karɓa an wanke su tas an kuma goge. Waɗanan da muke ninkewa zannuwa na sakawa a gida ne sai rigunan barci da wanduna sai unders su ne jiya da na samu sauƙin jiki na wanke su da kaina Amina ma ta yi ta yi na bari ta wanke mini na ce ta bar su zan iya yi da kaina.

"Ina za ki je daga nan Ya Sadiya?

Amina ta ƙara tambaya na ni kuma sai na yi mata shuru har muka gama ninke kayan gabaɗaya na ja akwatin na rufe daman sauran kayan na ciki na ja ta can gefen wardrope in da take a jingine sannan na koma in da na tashi na sake zama.

"Na ƙi ba zan faɗa miki ba."

"Don Allah fa na ce."

Ta sake marairaicewa kamar wata ƙaramar yarinya.

"To Yashe zan wuce."

Sai ta ƙwalalo ido ta na kallona kafin ta ce"Yashe fa Ya Sadiya?

Sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" To ina zan je in ba can ba?

Sai Amina ta gyara zama har da matsowa kusa da ni ta na faɗin" in ba ki shawara Ya Sadiya? Ina kallonta sai na gyaɗa mata kai kafin na ce" Me zai hana? Ina sauraran ki."

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Gaskiya in dai za ki ji shawarata kar ki je ko'ina. In dai ba za ki zauna anan ba sannan ba za ki je Abuja gidan Ya Auwal ba, ko gidan Ya Hamza ba to shawarata ita ce da dai ki je wani wajen gwara ki koma gida kawai Ya Sadiya."

Ta gama faɗa har tana ɗaga mini hannu ni kuma daman kallonta nake yi kafin na daƙuna fuska ina faɗin. "Wani gidan kenan? "Gidan auran ki mana Ya Sadiya."

Wata uwar harara na jefa mata kafin na yi ƙaramin tsaki ina faɗin" Ai ni da ke na faɗa miki megidan har gorin gidan ya yi mini ko?

"To ai bai kore ki ba Ya Sadiya ɓacin rai ne."

"Oh kina nufin na koma duk cin kashin da ya yi mini ya tafi a banza kenan ko?

Da sauri ta ce" Ni ban ce ki ƙyale shi ya tafi a banza ba."

"To me kike nufi Amina?

Na faɗa a ƙufule.

"Ba ki ba ni dama na gama maganata ba ne shi ya sa."

"In jin ki."

Na faɗa a tsume har ina kauda kaina domin ita kanta Aminar sai na ji ta fara ba ni haushi so ta ke yi ni ta kwaye min baya ta goyo bayan Yallaɓai?

"Nufina yanzu duk in da za ki je Ya Sadiya wani ƙarin tonon asiri ne. Abin da ba ki taɓa yi ba kar ma ki fara. Har gwara ma ki koma gida wajen Gwaggo da ki je Yashe can fa ƙauye ne in wani ya yi shuru wallahi wani ba zai yi shuru ba. Gwara ki koma gidan ki amma shi ma Yallaɓai ki gasa mai aya a hannu yadda zai fahimci shayi ruwa ne madara ake saka masa ya yi kauri."

Ta gama faɗa ta na kallona ganin na ƙi mgana kuma na ƙi sakin fuska sai ta marairaice ta na sake faɗin" Ko ba haka ba? Ki duba magana ta da idon basira Ya Sadiya."

Yadda ta ce idon basira ne ya sa sai da na yi dariya, itama sai ta hau dariyan Kafin na jinjina kai ina fadin" Haka ne kin yi gaskiya."

"Yauwa Ya Sadiya ki koma ko saboda su Jidda."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull