Turken gida book 3 cmplete - Chapter 3
Turken gida book 3 cmplete Chapter 3: Turken gida book 3 cmplete Chapter 3. Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce" To shi ke nan zan koma Amina."…
3,375 words
Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce" To shi ke nan zan koma Amina." Sai ta murmusa kafin ta rumgumoni tana faɗin" Ko ke fa My Ya Sadiya." Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi mgana ba. Duk in da ɗan uwa ya ke daɗi gare shi ni kaina sai na ji kamar kar na tafi, sai dai kuma gaskiya ta faɗa minj duk in da zan je yanzu kamar na soka wuƙa a cinyata ne na yi kururuwa na yi kirari gwara na koma amma ni da Yallabai zaman yan marina za mu yi tsakanin ni da shi.
Falo na kuma wajen yara Amina na kitchen ta na girkin Yamma. Yasir ne da Sumayya a gidan Afra ta tafi islamiya daga baya barin su na yi a falon na shiga kitchen wajen Amina ina ta ya ta aiki jefi jefi muna hira har muka gangaro kan mganar Ma'u.
"Wai Ma'u shuru kamar ba ta nan"
"Ta na nan, ai tun da aka yi wannan turken ni da ita sai ta shafa mini lafiya."
Amina ta ƙyalƙyace da dariya ta na faɗin" Ni kaina sai mu daɗe ba mu yi waya ba, ko a group na gida ta daina mgana kamar baya."
"Ni kaina na ga ta yi sanyi kamar ba ita ba."
Na faɗa ina yanka albasa.
"Rabon da mu yi waya tun lokacin da ta kirani ta na faɗa mini auren shema'u na ce mata ba zan samu zuwa ba."
"Ni dai bayan nan mun ɗan hadu a ɗorayi "
Na ba ma Amina amsa, an yi bikin Shema'u ko wata biyar ba a yi ba ta yi aure a gombe. Wani tsohon chairman ta aura matansa huɗu ɗaya ce ta rasu ya cike da ita dukkan mu mun je bikin amma ba mu je can Gombe ba Ma'un ce ta je su Shema an gama yawon duniya an gaji dai an yi aure can kwanaki da na je gida Gwaggo ke faɗa mini ta zo ganin gida har ta shigo gaishe su har ta ba ma Alhaji dubu biyar a raina na ce su shema an samu duniya kenan.
Mun cigaba da hiran Ma'u ni da Amina har muka gangaro kan Anty Bahijja nan na ke ba ta labarin irin sunayen da suke kiran Gimbiya da cewa ita ce mai ƙashin arziƙi.
"Allah na tuba Amina ai ni da arziƙina Yusuf ya aure ni. In ma tsiyar ne sai dai in shi ne ya goga mini"
Me Amina za ta yi in ba dariya ba har ta na rike ciki na kusa buga mata ƙasan wuƙan hannuna ina faɗin" Ban son iskanci fa Amina"
"To ke ce Ya Sadiya da wata magana."
"Allah kuwa. To har ni za a yi ma gorin ƙashin arziƙi."
Ni da ita muna ta dariya cikin annushuwa da hira muka gama girkin nan ana ta kiran sallar mangariba ni da ita muka je muka yi salla, Afra ta dawo ta isko ni daki tana mini hira akwai surutu kamar Baby ce daman kuma tsaran juna ne.
Bayan sallar isha'i muna falo muna cin abinci Yallaɓai na ta kiran wayata bai haƙura ba.
"Ya Sadiya ki ɗauka ki faɗa masa gobe za ki dawo"
"Wallahi ba zan ɗauka ba."
Na faɗa ina hararanta sai ta sunne kai tana yar dariya. Kira uku ya yi mini bayan na ɗazu da na shiga sallar asuba na ga huɗu, ni kuma na ce wallahi ba zan taɓa daga kiran shi ba sai yau? Sai yau ne ya tuna da ni matarsa ce? Sai yau? Ai ya makara wataƙila da ya kira kafin yau ɗin da wata ƙila na saurare shi.
Mun gama cin abinci mun dawo falo Amina ta kunna mana kallo ni ba na ma kallon hankalina na wajen Afra ina koya mata aikin makarantan da a ka ba su a english Yasir da sumyyah na ta wasannin su a tsakiyar falon
Na ji ana kiran wayar Amina amma ban dai bi ta kai ba sai da na ji tana faɗin" Ya Hamza ke kirana."
Ban kawo komai a raina ba na ce" To ki ɗaga mana."
Na ji ta ɗauka da sallama suna gaisawa daga nan sai na ji tana faɗin" Ya Sadiya wai? E ga ta nan ina ga wayar tana ɗaki ne shi ya sa ba ta ga kiran ba."
Sai na dawo da hankalina kanta har ina miƙewa. A ina Ya Hamza ya san ina gidan Amina.?
"Ga Ya Sadiyar"
Na ji Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na ta isowa in da nake ta miƙa mini wayar na karɓa ina mata inkiya da ido a ina ya san inan nan? Sai ta rika min nuni na yi mgana Ya Hamza na jin mu.
"Salamu Alaikum Ya Hamza."
"Sadiya kina lafiya?
Ya faɗa daga bangarensa.
"Lafiya lau. Ya su Anty Khaleesat da yara?
"Duk suna nan lafiya."
Shuru na wani lokaci na kasa mgana amma gaba na ya faɗi ina tunanin a ina ya san ba na gida ina kaduna ko dai Yallaɓai ne ya kai masa ƙarana? Dam! Na ji ƙirjina ya amsa ban samu sararin mgana ba na ji Ya Hamza na faɗin
"Ashe kina kaduna?
Ina shirin na amsa masa sai kawai ya cigaba da faɗin.
"Ke haka ake yi ehe da ga zuwa ziyara sai ki shantake a gidan ƙanwarki sama da kwana goma ba ki da ranar ƙomawa gidan mijin ki?
Mamaki ma ya hana ni mgana. Mamakin Yallaɓai da zai tashi wasa da ni.
"Dama daman gobe nake shirin komawa."
"To ya dai kamata. Shi ya kirani yanzu yana faɗa mini ba ki a gida sama da sati ya na ta kuma kiran wayarki ba ki ɗauka ba."
"Wayar ta na silent ne ban ji kiran na shi ba."
Na samu kaina da furtawa.
"To sai ki kira shi yanzu ku yi magana. Sannan gobe ki koma gidan ki Sadiya. Shi kan shi Dr sai ya ga rashin hankalin mu gandan gandan dake, ke ba suna kika zo ba sannan ba biki ba daga kun ɗan samu matsala da miji sai ki kama hanya ki tafi gidan ƙanwarki? In ma yajin za ki yi kuma tun da ba ki je ɗorayi ba me ya hana ba ki taho gidana ko gidan Auwal ba?
"Ka yi haƙuri Ya Hamza."
"Ba maganar haƙuri ba ne. Ba a haka kin ji ko? Amina ƙanwarki ce bai kamata ki je gidan ta in wani abu ya faru ba. Mu ya kamata ki fara nema."
"To Ya Hamza."
Na furta ina ƙokarin mai da ƙwalla da suka cika mini ƙwarmin idanuwana.
"Ki yi haƙuri ki koma giden ki ki rumgumi mijin ki da ƴaƴanki. Ya faɗa mini da kan shi ranshi ne ya ɓaci ya ɗan faɗa miki wasu mganganu ma su zafi sai kika ji haushi kika ce za ki taho kaduna. Ya ce ya bar ki taho ne saboda ke da shi ku samu zukatan ku su huta sai kuma ya ga kin shantake kin ƙi dawowa yana ta kiran wayarki kuma ba ki ɗauka ba."
Shuru na yi domin kalaman bakina sun gama ƙarewa. Yallaɓai ya shirya wasan ƙwaikwayon shi ya nemi yan wasa kuma har an yi wasa an tashi karshe dai shi ke da nasara akaina bayan tarin tozarcin da ya yi mini
"Ki yi haƙuri kin ji ko? Haba Sadiya da girman ki ai yaji bai kamace ki ba, ki yi hakuri ki koma gidan ki, ke yanzu uwa ce sai dai ma ki yi ma wasu faɗa."
"To Ya Hamza in sha Allahu gobe da safe zan koma."
"Yauwa. To mu kwana lafiya amma ki kira shi yanzu."
Da haka muka yi sallama da shi muna gama wayar Amina ta zauna gefena tana faɗin" Wai me Babansu Jidda ya kira Ya Hamza ya faɗa ma sa? Na ji ya na miki faɗa ne?
Sai na kalleta, lokaci ɗaya hawayen da na ke ta riƙewa suka kece mini amma sai na yi saurin saka hannu na goge hawayen ina faɗin.
"Ya kira shi ya faɗa mai mun ɗan samu sabani ranshi ya ɓaci ya ɗan faɗa mini mganganu ni kuma sai na ji haushi na ce zan taho Kaduna a cewarsa ya bar ni na taho saboda ni da shi mu samu zuciyarmu ta yi sanyi amma sai ya ga na daɗe ban dawo ba kuma yana ta kirana a waya ban ɗauka ba"
"Lalle ne ma. "
Amina ta faɗa ta na riƙe haba kafin ta cigaba da faɗin" Yallaɓan nan na ki ya Saduiya sai ke" Ta faɗa tana dariya na kalleta amma ban yi mgana ba.
Na fahimci manufarsa ya yi saurin kiran Ya Hamza ne ya faɗa masa saboda ni ya rigani wanda ko daga baya na faɗi wata mgana ba za a goya mink baya. Yallabai ya san ni sarai kamar yadda na san shi ciki da bai. Ya san ba zan taɓa zuwa na kai ƙaran shi ba ya kuma san ba zan taɓa fasa mganar faɗan mu ba amma ya san ina da kafiya zan iya ƙin dawowa a lokacin da ya so ya kuma san in ba Ya Hamza ko Ya Auwal ba, ba wanda zai matsa mini na koma shi ya sa sai ya yi saurin kiran Ya Hamza. Ya san da gangam na ƙi ɗaga wayarsa ya kuma sha jinin jikinsa ko kunya ne zencen ban sanin masa ba. Sai yanzu ne ya tuna da ina da amfani a rayuwarsa? Wallahi tallahi sai ya raina kansa kuma bashin gorin da ya yi mini na gida da na haihuwa watan tara na zai biya su. Sannan ya yi sanadiyar na rasa gudan jinina bana jin ko da na yafe masa laifinsa to ba na jin zan iya yafe masa wannan kasadar da ya ja mini na rasa wani abu mai muhimmaci a rayuwata.
Zan koma ba domin Ya Hamza ya yi min mgana ba sai domin ina da niyyar komawar. Amma kuma kiɗa ya sauya dole rawa shima ya sauya. Na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitan da zan nema ma kaina in na koma gida. Na yi tunanin zan koma makaranta na yi masters ɗina sannan zan inganta sana'ata ta hijabai har ma da ƙarin wani sana'o'in na daina dogara da Yallaɓai na kuma daina dogara da duk abin da ya ke takaman ya mallaka. Daga ni sai ƴaƴana domin nan duniya su ne kaɗai na aminta da ɗari bisa ɗari ba za su taɓa juya min baya ba.
Da safiyar talata na yi shirin komawa Kano. Tare muka fita da Amina za ta je saloon ita da Yasir ne Afra da Sumaiyya na makaranta Amina sai sha'awata take ba ni ta iya driving ba in da ba ta zuwa a garin Kaduna da yar motar ta da Dr ya siya mata. Ni ma a raina na kudiri niyyar zan dukufa da sana'a har nima na mallaki mota ta kaina da gumina. Ita ta kai ni tasha na samu mota sannan muka yi sallama sai da motar ta tashi na bar ta a tasha. Kuma har kuɗin motar ita ta biya mini da cewa Dr ne ya ce ta ba ni na ƙara riƙewa a hannuna. Mun rabu ina ɗaga mata hanmu tana ɗaga mini nima.
Motar mu ta tashi goma saura ba mu isa Kano ba sai biyu na rana. Daga tasha na hau adaidaita zuwa gidana. Ba kowa a gidan sai da na saka makulli na buɗe gidan na shiga ko'ina ya yi ƙura. Na shiga cikin bedroom ɗina na ijiye akwatin hannuna da jaka sannan na zare mayafi na shiga tiolet na kama ruwa na yo alwala na taho na yi salla ina idarwa na tashi na shiga kitchen, shima dai duk ya yi ƙura amma dai ba a yi amfani da komai ba.
Gas na kunna na dafa ruwan zafi na sha tea, sai ƙwai da na soya guda uku bayan na gama na koma ɗaki na ɗauko wayata kamar in kira shi sai na fasa. Domin ban bi umarnin Ya Hamza, jiya ban neme shi ba shima bai sake nema ba ina da tabbacin wata ƙila ya sake kiran Ya Hamzan ne shi kuma ya faɗa masa na ce yau zan koma gida.
Ganin ba zan iya kiran shi ba sai kawai na tura masa saƙo.
"Na dawo gida."
Ina gama tura masa sai na kira wayar Salisu direba bayan mun gaisa na ce masa yau in ya dauko su Jidda ya kawo mini su gida na dawo. Yana ta min sannu da zuwa na gama waya dashi kenan Balaraba ta kira ni ta na faɗa mini Saude ta sauka duk sai na ji ɓacin raina ya tafi ina mata barka ta samu megida tun da namiji ta haifa. A Lokacin na kira wayar sai mijinta ya ɗauka ya ce ta na wankan da yake ba a asibiti ta haihu ba a gida ne amma sun kira anguwan zoma. Mun rabu a kan cewa in ta fito zai faɗa mata za ta kirani. Sai ko gashi ta na fitowa ta kira ni muka yi magana abin hamdalar shi ne ta haihu lafiya ba wata matsala na yi mata mganar za ta dawo gida ne ko anan za ta zauna sai ta ce min ita ba ta sani ba, ni ko kai tsaye na ce mata gwara dai ta dawo gida a kula da ita ko bayan suna ne sai ta ce mini za ta yi magana da megidanta na ce ya kamata.
Na ɗan kwanta sai la'asar sannan na tashi na yi salla sannan na fara gyaran gidan na share ko'ina na goge na saka turaren wuta gidan ya fara ƙamshi duk da na gaji ban zauna ba na fara tunanin abin da zan dafa na duba friza na sai na ci karo da miyar da na yi ana gobe tafiyata tana nan ba ta yi komai ba kuma ina da sauran kayan miya da kayan lambu sai dai duk sun bushe sai na kwashe su kawai na zubar har da ma su kankana suma duk ƙanƙara ya sa sun yi wani nakwa nakwa saboda daɗewa sai kawai duk na kwashe na zubar a bola na goge firizan. Miyan na sake gyarawa na dafa mana farar shinkafa na gama shidda saura na yamma na goge kitchen ɗin sannan na je na yi wanka na fito kenan ina saka kaya na ji ana buga get a raina na ce to yan makaranta sun dawo.
Wani riga da wando na saka pakistan ne rigar ja ne da baƙi ba ta da hannu sai daga kasa an ɗan zoɓa ta, sai wando sakakke ne bai kama min jiki ba sai na saka hula baƙa mai kwalliya ta sama, kaina akwai kitso a can Kaduna Amina ta yi min shi duk da ba ta wani iya kitson ba amma na gaji da kan ya tsufa sai na tsife na ce ta yi min ko kalaba ne shi ne ta zarga min shi haka, kuma gashi ba ta kama shi da kyau ba duk ya fara sukurkucewa har kunya na ke ji na buɗe kan a gaban mutane.
Silafas ɗin cikin gida na saka sannan na saka mayafi na fita zuwa haraban gidan na buɗe ma yara ƙofa suna ganina har Jidda sai da suka faɗa jikina suna min oyoyo na tarbe su cikin farinciki. Da gaske na yi kewar su sosai musamman ma surutun Baby. Salisu bai tafi ba daman in ya kawo su sai ya tabbatar da an buɗe gida sun shiga ya ke tafiya mun gaisa da shi ya yi min barka da dawowa ni kuma na ce ya gaida iyalan na shi, na rufe gida muka dawo cikin gida ni da ƴaƴana.
"Baby ciwo kika yi? Na ga kin rame ne?
Na faɗa ina tattaɓa wuyan ta lokacin da muka dawo cikin gida.
"Ta yi zazzaɓi na kwana biyu a gidan Anty Gimbiya."
Jidda ta ba ni amsa sai na zauna saman kujera na jawo Baby ta zauna saman cinyata ina shafa fuskarta na ke faɗin.
"Ayya sorry My princess Umma ta tafi ta bar ki ko?
Sai Baby ta fara tura baki tana faɗin" Umma ni dai kar ki ƙara tafiya ba ki tafi da ni ba ina ta kuka Abba sai ya yi ta cewa za ki dawo ba ki dawo ba sai da aka daɗe." Dariya na yi ina mai rumgumeta kafin na ce" Ba zan ƙara tafiya na bar My princess ba in sha Allahu " Jin haka ya sa ta fara tsallen murna ita dai Jidda na zaune ta na mirmishi. Ranar ni na ta ya Baby cire kayan makaranta ta saka na gida Jidda ma ta sauya ta fito na zubo mana abinci a filet muka ci tare. Na sha labarai wajen Baby duk abin da ya faru da ba na nan sai da ta faɗa mini Jidda na gefe ta na cin abincinta tak ba ta ce ba, ashe ranar da na tafi ranar daga makaranta ya ce salisu ya kai su sharaɗa ba su ma kwana a gidan ba kenan.
Bayan mun gama Jidda ta tattara komai ta kai kitchen ta kuma share in da muka ɓata. An kira mangariba muka yi alwala muka yi salla a falo, muka yi azkar sannan na ce mun dade ba mu yi karatun Qur'ani su ɗauko mu yi karatu. Ba mu muka tsagaita da karatun ba sai da a ka kira sallar isha'i sannan muka dakata muka yi salla, muna idarwa na ce su yi aikin makaranta ni kuma sai na shiga ciki na ɗauki wayata ina dubawa sai na ga Yallaɓai ya yi min saƙo.
"Ya yi kyau."
Abin da ya ce kenan a saƙon na shi ƙaramin tsaki na ja na danna delete saƙon ya goge daga wayata. Data na kunna ina ganin saƙonni nata shigo mini ma su tambaya hijabai ne daga yan makarantar mu ta BUK daman suna siya tun da duk na yi musu tallah. Na amsa na yi ta ba su da cewa cikin satin nan za a kawo tun da ina Kaduna ma mun yi mgana da mai ɗinkin Hijaban lissafi kawai za mu yi na tura masa kuɗin shi, sannan na fara tunanin yadda zan in ganta kasuwancina shi ya sa a I.G na yi ta following ɗin masu ƙananun kasuwanci domin na ga yadda suke marketing ɗin kayan su sai na fahimci ina bukatar suna da ledan da zan rika saka ma kowa hijabin shi in ya siya shima duk inganta kasuwanci ne, sannan ina bukatar ɗinka hijaban in diffirent styles ma'ana kowani yanayin ɗinki ya kasance ana samu bambamci sosai da ganin abu unique a hijaban da na ke siyarwa sannan akwai bukatar na ƙara da wani abu. Ni kaɗai na zauna ina ta tunanin da me zan kara? Na fi son abin da ni kaɗai na ke siyarwa ba ko ba ma ni kaɗai ba to ya kasance bai yi yawa ba. Lamarin ya kai har littafi da biro na ɗauko na fara rubutu har takalma na saka da atamfofi amma sai na ji hankalina bai kwanta da su ba sai kawai na saka under wears irin su pant, bra, sikat gajerun wanduna da dogaye tare da sleeping drees sai na ji na fi karkata anan sai na fara tunanin sunan da zan saka a jikin logon kasuwancina daga jarshe da na ga na matsa ma kaina da yawa sai na ijiye zuwa da safe amma waya na hannuna ina ta shige-shige ina ganin sunayen da mata ke sanya ma kasuwancin su very interesting.
Ina cikin shige- shige na sai ga kiran Surayya Dee Bojuwa herbel, da na ga kiran ta sai da na ji kunya na daɗe ban nema ta ba daman ina shirin neman ta ne muka samu matsala da Yallaɓai. Ta ce kwana biyu ba ta ji motsina ba shi ya sa ta kira ta ji ko lafiya Ina dariya na ce" Lafiya ƙalau wallahi kwanaki can ne na kwanta asibiti da yake na samu ɓari." "Subhanallahi Sannu. Allah ya kawo wani mai albarka." Na amsa mata da Amin sai ta fara min mganar tun da na yi ɓari ai ya kamata na yi gyara sai na ce mata zan yi in sha Allahu amma ba ni da kuɗi a hannu in na samu zan yi mata mgana.