Turken gida book 3 cmplete - Chapter 29
Turken gida book 3 cmplete Chapter 29: Turken gida book 3 cmplete Chapter 29. Gaisawa muka yi ta ba ni Muhammad na ɗauka shima an yi masa gayun su na yara…
3,368 words
Gaisawa muka yi ta ba ni Muhammad na ɗauka shima an yi masa gayun su na yara da kaya masu kyau da tsada. "Allah Ya raya mana Muhammad" Na faɗa sai ta amsa da Amin Amin. "Ina Baby? Ko ta je makaranta ne? "E ta tafi. Amma na kira Salisu zai kawo ta nan, tun da na zo mata da kayam da za ta saka."
"Ayya. Su Jidda ana can makaranta. Ta kirani da safe muka gaisa ta ce Anty wani suna za mu riƙa kiran Muhamnad na ce ta saka masa suna cikin sanyin ta ta ce Anty Ammar ya yi? Ina dariya na ce" Ta ko iya zaɓan suna. Allah ya raya Muhammad(Anwar)" Aka amsa da Amin gabaɗaya da waɗanda ke gefen mu suna jin mu. Ina nan zaune sai ga Hauwa ta shigo sai na matsa mata gefena tazauna ta mika mata Muhammad, sannan na karɓi ledan sakonta na mika mata ta karɓa tana faɗin.
"Ba kya gajiya Madam! To na gode Ammar na godiya Allah ya saka da alheri "
"Haba ba yawa fa. Amin"
Yumna ta tambaya na ce tana wajen Marwa, yarinya Marwa ɗin ma ta yi barci nan saman gadom Gimbiya na kwantar da ita. Har ita Gimbiyar sai da ta tambayi Munnira wai ya ta gan mu mu biyu daga ni sai Hauwa na yi dariya na ce ta yi baƙuwa ne amma za ta taho daga baya. Mun saba in dai wani abu ne a dangin mazajen mu to mu uku suke ganin mu. Kowa ya san ni da su Hauwa mun zama aminai ne ba facaloli ba.
Abinci ta ce a kawo mana sai na ce a kai mana falo can za mu koma, ba mu ma kai ga barin dakin ba sai ga Suwaiba ta iso tare da ita muka fita falo ana ta hira. An kawo mana abinci tuwon shinkafa mai naman rago. Sai dambun zogale sai alale, sai muka haɗu da ni da Suwaiba da Hauwa muna cin abincin ina tambayan Jamila ta ce itama yau ƙanwar mijinta ake suna ta haihu sai anjauma za ta leƙo. Muna cin abinci muna hira su Marwa suka dawo in da muke suka zauna a cikin hiran ne Hauwa ke maganar me ya sa ba ta ga Suwaiba da ankon sunan ba?
"Wa? Mu a suwa. Naja ta tura mini na ce ba ni da halin yi."
"Au da man ankon ma sai wanda ya isa ake nuna ma wa?
Hauwa ta faɗa tana riƙe baki. Suwaiba na dariya ta ce" Ku ba a nuna muku ba? Wataƙila saboda Sadiya ne domin na ga ana kishi da ita ko sunan ma in kun lura yanayin na Yumna aka kwaikwaya. Duk haihuwar su Khalipa ba ta yi anko ba sai wannan?
"Uhm'
Kawai na iya cewa kafin na yi magana Ashe ta karɓe da cewa" Wai ba a nuna muku ankon ba da gaske? "Wallahi ba mu sani ba." Na rantse mata sai ta yi kasake kafin ta ce" To har Rano wannan akon bari mu ku ji." "Zai kai can mana. Kun manta gidan su na can ne." In ji Suwaiba, Marwa ta ce itama Anty Bahijja ta tura ma Kawu Abba ya ce ba zai siya ba sunan ne sai an yi anko. Shi ne ta ce ai nima da na haihu na yi anko kuma ya siya mata a lokacin shi ko ya ce ba shi ya siya ba da kuɗinta ta siya a wancan lokacin. Yanzu ma shine ya nuna mata in tana da kuɗi ta siya Marwa ta ce ita kam ba ta da kuɗi ba ta siya ba.
"Ikon Allah.!
Suwaiba ta sake faɗa tana mai mamaki, Hauwa ta ce da man ko na Yumna ba su yi ba gwara ma da ba su nuna mana ba muma ba za mu yi ba.
"Da sun sanar damu za mu yi ko don mu tura musu Aniyar su."
Na faɗa ina mirmishi.
"Wallahi kuwa."
In ji Marwa.
Muna ta hiran mu, Naja ta zo ta ga ba a kawo mana ruwa ba da kunin Aya ba.
"Wa ya kawo muku abincin?
Ta tambaya tana kallon mu.
"Maryama ce ta kawo musu abinci ba ruwa ba lemu."
Ashe ta faɗa cikin gatse sai Naja ta yi dariya ta ce Ashe ta biyo ta karɓo mana. Ita ta bita sai ga shi ta dawo da ruwan gora da fanta sai kunin Aya da zobo cikin wani roba. Tana ta masifa wai an ce Maryama ta ba da zobo da kunin aya tana wani daga kai.
"Har tana ce mini ba kin sha ba ke Ashe? Na ce na sha in zan ƙara za ki hana ni ne?
Na kwashe da dariya ganin yadda Ashe ta yi da baki tana kwantata mana yadda suka kwashe da Autar su Gimbiya.
"Sai ta ce me?
In ji Suwaiba itama tana dariya.
"Me kuwa? Ta yi shuru ai ta san ni yadda ba ta taɓuwa nima haka. Naja ta ce na ku ne sai ta wuce ta buɗe dakin ta ba ni."
Hauwa na dariya ta ce"Da man Maryama ba ta da dama. Ga rashin kunya da ta yi auran nan ne ma ta yi sauƙi." "Rashin kunya ai duk tare muka yi muna yan mata. Ni yanzu ai sai dai ta nuna mini zaman agolege ni kuma na gwada mata na Sulaja." Ni dai dariya har ina kwarewa, Yunma na zaman jikina ina ba ta alale har tana sulmiyowa.
"Ke da man ba cikin garin Lagos ɗin take aure ba?
"In ji wa! Ko dai ake raina ma wayau. Tana cikin garin Agege can mijinta yake kasuwanci. Shine da ta zo garin ta yi ta buɗa hanci wai ita a dole tana auran miji mai kuɗi suna zaune a garin lagos. Allah na tuba wallahi ko ni da mijina ke aikin gwammati a kallon farko mai hankali in ya yi mana ya san na fita jin daɗi "
Ni da Suwaiba muna tsintsira dariya ina faɗin Munnura ta yi missing na so tana wajen nan da an ji muryanta a sama. Abin da ya ɗan tsagaita hiran ma Faridan Tariq ne ta kira ni a waya ta ce ita ba ta samu zuwa ba suna sai sallar azumi take tunanin za su shigo garin. Sai na ke faɗa mata ina gidan sunan gamu nan ana ta hira ana dariya ta ce na gaida kowa da kowa. Muna zaune a falon sai ga Mubeena ashe tana makaranta suna da test duk ta sha wuya Naja na yi ma magana na ce a kawo ma Mubeena abinci daga makaranta take. An kawo mata itama irin na mu, muna nan muna ta hira sallar la'asar ne ya tada mu bayan mun yi salla mun idar muka fito an kira mai hoto kamar dai lokacin sunan Yumna.
Mun fiffito, sai ga Munnira yar halas ita da Hadiza ƙanwarta tana ko ganin mai hoto sai da ta riƙe baki kafin ta ce" To pha sabon salo tusa a lasifika." "To za ki fara ko? Hauwa ta tare ta, tana dariya. "To ai na ga ana ta so a kwaikwayo mu ne." "Ai komai ma irin naku ne. Ba ki ga har da su anko ba.? Suwaiba ta fada mata tana dariya Munnira ta waiga ta sake waigawa kafin ta saki shewa da ƙarfi tana faɗin" Ahayye nanaye. Yau ina ganin abin da yafi karfina ni haihuwar mutun biyu"
"Kishin ne har da na suna?
Hadiza ta faɗa tana dariya Ashe ta ce" To miye ma ba a yi ma kishi yanzu? Kishi ya zama ɗan gata yanzu." Ni dai ganin hankula sun fara dawowa kanmu na ce Munnira ta yi wa Allah ta yi shuru "Zan yi shuru amma in na ga abun da zan magantu wallahi sai na mangantu." "Nima ina bayan ki." In ji Ashe har suna tafawa sai na lura hatta Hadiza irin su Munnira ne, har tana cewa tun da dai a dake ba za mu dakun ma kowa ba ai da sauƙi.
"Ni dai ku rufa mana asiri mu bar gidan sunan nan lafiya kafin a yi mana rubuti."
"Ai wallahi ba wacce ta isa tab.!"
Munnira ta faɗa har tana ɗaga murya na balla mata harara. Munnira ba ta shiga ciki ba sai da aka gama hotuna yadda ba a gayyace mu, mu ma ba mu tura kan mu ba, ni ko a sunan Yumna na kirata mun yi amma ni ko kallona ba wanda ya yi. Su Naja ne da su Anty Bahijja sai ƙawayenta da dangin ta ba ma kamar Maryama ɗin nan na yadda ta cika kauɗin tsiya.
Bayan an gama hotunan muka dawo cikin gida muka zazzauna a falo muna hira. Munnira ina kwabarta sai da ta yi ma Naja magana wai an fidda anko an nuna ma waɗanda aka so. "Haba. Ban tura muku ba? To wallahi na manta ne" Ta faɗa daga ji ma karya ne, Suwaiba ko ta ce" Sadiya ai ba a waya ya kamata a nuna mata har gida ya kamata a kai mata ta gani."
"Anty Suwaiba abubuwan sun yi mini yawa. Jibi za mu bar kasar ni da Honey. Ankon ma Gimbiya ba ta so a fitar ba ni ce na matsa. Mantuwa ne duk wanda ban turamawa ba ya yi hakuri."
"Ai ba komai. Kun hutattashe mu da kuɗin mu "
In ji Munnira.
"Afuwan Anty Sadiya."
Naja ta faɗa, tana kallona ni ko sai na yi mirmishi na ce ba komai. Nan dai ta wuce tana juya mazaunai.
"Ƙarya take yi wallahi kunya ce, da man domin ta ji kunyar na yi magana "
"Allah ya shirye ki Munnira "
Hauwa ta faɗa tana dariya ni kuma sai na ce" Kuma da ba haka take ba. Da ni ce mai bakin amma yanzu Munnira ta taka ni." Na faɗa ina dariya kai tsaye ta ce" Wallahi da bakina kawai dai na ɗan yi lamɓo ne. Sai da na gama ganin takun kowa sannan na bayyana kalata."
Muka kwashe da dariya gabaɗaya muna nan zaune aka mai do nepa falon ya yi haske Suwaiba ke tsokanan Anty Bahijja da ba chasu ne ta ce ita ina ruwanta da chasu yanzu ma gida za ta tafi, ba ta kuma daɗe da maganar ba muka ga tafiyarta ta fita ba daɗewa Maryama ta zo ta kunna waya da wakar Amarya ki haɗa kayan ki na Nura. Inuwa tana wani takawa yan gidansu na yi mata ihu
Ba zato kawai Munnira ta ce" wannan ai tsohuwar waka ce. Kuma ƙauyanci ne mu taka rawa da ita." Kallon Munnira kawai na ke yi kallon ina ruwan ki. "Gaskiya ba. Kuma sautin waya ai ba sauti ba ne. A nemo speaker." Hadiza kanwarta ta amsa mata, daman duk zamu ce ta iske mu je mu.
Suka yi kamar ba su ji ba, Maryam ɗin ta cigaba da rawan ta suna yi mata tafi. Ita ke fadin a je ta fito mata da Gimbiya ta zo ta yi rawa. Sai kawai ta saka wakar uwar gida ran gida har Gimbiyan ta fito lokacin ta sauya kaya ma Maryam ɗin ta kamo hannunta tana bin wakar. "Uwar gida ran gida Tafida yana yi miki rawa." In da aka ce shaba sai ta kira sunan Yallabai
Ni da su Munnira muka kalli juna kafin mu yi dariya cikin mu ba wacce ta yi tunanin Munnira za ta mike sai ganin ta kawai mu ka yi a cikin su tana juyi tana faɗin" A fagen na mu ne mu Uwagidaye ne bai kamata amayar ta shigo ba." Sadiya, Hauwa wannan fagen namu ne."
Ni dai ban tashi ba Ashe da Hadiza suka mike suka mara mata baya Suwaiba na zuga su da tabbas filin naku ne. Sai kawai a ka bar musu filin Maryama ta saki baki ita da su Gimbiya. Ita Gimbiyar ba ta yi magana ba sai ita Maryam ɗin ta ce"Miye haka? Ai ko fili na Anty Gimbiya ne. Domin ita ce Uwargida ita ce Amarya."
"Ina kika baro Uwargida Sadiya? Kirarinta ta Yallaɓai. Ta zama Tafida Tafida ya zama ita." Munnira tafaɗa cikin sigan wasa.
Sai kawai Maryama ta yi ja tsaki kafin ta ce" In ana babbakan giwa wake ta kiyashi? Uwargidan banza da wofi. Ai ko Amarya ita ke da Gida. Ita ta yi farar haihuwa zaranta maza har guda uku ta haifa. Kin ga ita ce gidan ma gabaɗaya."
"Ai kuma ba a nan take ba ai an take bodari ta kai."
Ashe ta mayar mata da martani Hadiza ta karɓa da cewa" Ko goma Amarya za ta zo ta haifa sai sun jira domin za su kira wasu yaya da Anty suma za a kira su yanzu kafin baya."
Tun muna ganin abin cikin wasa har aka koma jefa ma juna mganganu cikin zafi. Sai na mike ina yi ma Munnira magana akan ta yi shuru.
"In yi shuru! Daga magana na ga yarinyar nan za ta yi mini rashin kunya. Ba ta sanni ba ne ko?
"Da aurena da yayana ki kirani yarinya dan sake tunani dai baiwar Allah." Maryama ta faɗa har tana tafawa hannuwa Gimbiyar na yi mata magana ta fara masifa tana faɗin" Ina ruwan su damu daga saka waka sai su shigo suna neman gaya mana mgana! Wa ke tsoron su?
"Na ce dai ki yi shuru ko?
Ta tsawarta mata.
"To abun na su ne kamar da gayya Anty Gimbiya."
In ji Halima ni wallahi ban ma ganta ba sai yanzu ina tunanin ko yanzu ta zo, ko kuma ta zo da safe ta je gida ta dawo.
"E mana da gayya ne. Tawagan uwargida ne ta bakin su, to wallahi mata ba ta isa ta watsa mana taro ba sai dai mu watse ta"
"Ke ai kin yi kaɗan ki watse mu Maryama sai dai ke mu watse ki wallahi. "
Ashe ta shige tsakanin Munnira da Maryama tana faɗin haka.
"Anty Munnira bar mini wannan faɗan koma gefe ki yi kallo"
Ta matsar da Munnira gefe tana nuna Maryama da yatsa kafin ta ce" Maryama karyan iskanci kike yi. Ni ce nan daidai da kugun ki wallahi "
Kawai sai ta saka hannu ta kabar da hannun Ashe tana faɗin" Ke Ashe kin sanni na san ki. Faɗan nan ba naki ba ne amma tun da kin shiga saboda yayarki Hauwa na ƙawar matar can mu zuba da ni da ke shege ka fasa." Ta faɗa tana shan gaban Ashe har tana ture ta baya. Abu kamar wasa wasa ashe na gaske ne ni ina gefe rike da Yumna ina ta ma Munnira mganar su bari domin har da ita maryama na magana tana ma yar mata ita da Ashe har da Halima. Hauwa ma da wasu yan Rano suka je suna jan Ashe amma ta ce tun da rigima Maryama take so to ta tare shi ta same shi a wajen ta.
Gimbiya ma da ƴan'uwanta suna ta yi ma Maryam ɗin magana amma ba su ji ba. Irin su Halima yan kan zagi suna faɗin daman da gayya ne. Ga shi ba wasu manya Anty Bahijja ta tafi Anty Maimuna daman ba ta zo ba. Naja ce ta shiga tsakiyar su ta raba domin kaɗan ya rage afara kai ma juna duka.
"Miye haka? Daga suna na farinciki sai kuma ku ma yar mana da taro na tsiya.? Ta faɗa cikin bacin rai kafin ta kalli Munnira tana faɗin" Anty Munni wannan ba girman ki ba ne don Allah ki ja tawagarki ku koma gefe domin a samu zaman lafiya." Munnira kuma ta ce sun yi kaɗan daga abin arziki sai a nemi a ce sune suka zo da fitina. Karaf wata ƙawar Gimbiya ta ce" Kune mana. Ina ruwan ki da waƙar da aka saka na uwargida ko na Amarya. Maganar gaskiya ku ne ba kwa son zaman lafiya. Ko kuma daman domin ku lalata mana suna kuka zo."
Munnira ta yi shewa ta dire da cewa an lalata su yi wani abun mana. Suwaiba na yi ma magana ita na samu ta jawo hannun Munnira amma sai Maryama ta ja tsiyar da cewa" Abin da ya kawo su kenan mana. Ga munafukar can ita ce ta turo su ita kuma ta koma gefe ta bakam kamar ba ta san me ke faruwa ba. Anty Gimbiya ki faɗa ma Kishiyarki ta ja tawagarta ta bar gidan nan kafin raina ya ɓaci a yi ɓaattaciya"
Maganar ta ba ni mamaki, sai kallo ya koma kaina duk sai na ji na muzanta. Naja ta zo gabana tana faɗin" Don Allah Anty Sadiya ki yi musu mgana su daina." "Na yi musu magana mana Naja ko ba ki gani ba ne? Ni zan ce su zo suna ne su yi rigima da wata? Ku yi mini adalci mana"
"Ba wani adalci, ke ce munafukar da man tun da kika zo kika ga abubuwa sun tafi daidai kishin ki ya motsa ba haka aka so wai ƙanin miji yafi miji kyau."
Maryama ta faɗa tana wani girgiza jiki, sannan ta nuna Munnira da su Hauwa tana faɗin" Saboda baƙinciki sai ki ka yi amfani da waɗanan yan koren naki domin su wargazamana taro. To daga ke har su ba ku isa ba. Sai dai mu mu wargazaku mu kore ku tun da ba zaman lafiya ya kawo ku ba."
Baki na saki ina kallonta kafin in nuna kaina ina faɗin" Da ni kike?
"Akwai wata munnafukar ce bayan ke. Kin ga Anty Gimbiya na ta farar haihuwa. Bakin cikin ki ya kasa boyuwa sai da kika bayyana. To sai dai ki mutu aamma gida ya zama namu haka ma Yaya Tafidan shima namu ne sai mun ga dama mu ba da aron shi."
Maryama ta ba ni amsa ba tsoro ko tunanin wani. Kafafuwata suka fara rawa saboda ɓacin rai har ni na yi lalacewan da ƙanwar Gimbiya za ta ci zarafina. Yarinyar da ko Amina ta girme meta. Marwa ke rike ni tana cewa na yi haƙuri kar na tanka Suwaiba kuma tana yi ma Gimbiya mgana ta ja ma ƙanwarta kunne manganganunta suna tsauri da yawa.
"Me zan ce Anty Suwaiba? Ni ba zan hana ta ba domin duk abin da ta faɗa gsskiya. Taro na suka zo su watsa kuma sun ji daɗi.'
Kawai sai ta fashe da kuka munafunci, Munnira kuma ta fashe kawai sai ta dira kan ƙanwar Gimbiya ta shaƙo tana faɗin karya take yi, ai sune ma za su ce kishi ne ke damun yayarta domin duk wani abun da ta yi a wannan taron Sadiya ta kwaikwaya mu ba mu ce tana baƙin ciki ba sai mu ne za ki ce muna bakin ciki? To mun watse taron in ta isa sai ta yi wani abu ko ta ɗau mataki. Ni ban san me ta buɗe baki ta faɗa ba, sai ji kawai na yi kaya kaya an fara kai duka Munnira ta fara kai ma Maryama Mari, ita kuma ta rama kawai sai suka fara dambe na ruɗe ina kiran sunan Munnira.
"Haba Munnira ba girman ki ba ne faɗa da wannan yarinyar."
Hauwa ta fada har da ni a masu rabo Yumna wajen Marwa na bar ta,ƴan'uwansu na Rano suna ta faɗa suka ce ga mota can ta dawo ɗaukan su za su wuce ba za su iya da masifa ba, da man yau za su koma, ita kuma Hadiza ganin ana faɗa da yayarta sai ta shiga suka yi ma Maryanma taron dangi suka kaita kasa. Gimbiya da Naja ganin haka suka shiga tsakani, wajen ƙokarin raba su Munnira idanuwanta ya rufe ta ture Gimbiya sai da ta faɗi gefe kusa da kujera hannunta ya bugu sai da ta yi ƙara. Kukanta ne ma ya raba faɗan sai kowa ya koma kanta Naja ta ɗaga ta irin kukan da Gimbiya ke yi ko dukanta aka yi sai kuka.
"Innalillahi shike nan sun karya ta burin su ya cika."
In ji wata cikin kawayen Gimbiyar.
"A kira Yaya Tafida mana shi sai ya zo ya ganin ma idanuwansa matarsa da Tawaganta za su nakasa masa mata."
In ji Halima, ni gabaɗaya kaina ya kulle ma, amma sai da na yi na Munnira masifa.
"Da wannan yarinyar ne zaki zo kina faɗa Munnira! Gaskiya wannan rashin sanin kimar kai ne "