Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 30

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 30

Turken gida book 3 cmplete Chapter 30: Turken gida book 3 cmplete Chapter 30. Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara…

3,238 words

Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara mu tafi na je da niyyar na ba ma Gimbiya haƙuri ta juyar mini da kai tana faɗin" burin ki ya cika kin samu abin da kike so. Amma ki sani wallahi ba zan bar maganar nan haka ba." Sai na ga ma tsayawa magana kamar ɓata bakina zan yi kawai sai na wuce. Har Ashe da Halima sai da na yi ma faɗa. Muka rankayo gabaɗaya zuwa waje muna fitowa Salisu na sauke Baby sai na ce kawai su juya. Motar na ce Munnira da Hadiza su shiga ya kai su gida ni kuma na ɗauko Hauwa da Ashe, tun da tace can za ta kwana sai Marwa da nima a gidana ta ce za ta kwana. Suwaiba na cikin gidan mun bar,ta tana ban haƙuri.

"Munnira ta goga mini baƙin fanti a dangin Yallabai. Yanzu ko rantsuwa na yi ba za a yarda ba ni na saka Munnira dambe da ƙanwar Gimbiya ba "

Na faɗa cikin damuwa. Ni na san abin da na ke hange da man yaya lafiyan kura ballantana ta yi zawo. An ce ina baƙin ciki saboda ban haifi namiji ba kalaman sun yi mini dafi a zuciyata.

"Gaskiya ba ta kyauta ba. Haba ke kuma Ashe wallahi sai na faɗa ma Mama. Yanzu Sadiya kuka bar ma abin mgana."

Hauwa ta faɗa tana dungurar kan Ƙanwarta Ashe. Tura baki ta yi kafin ta ce" Ni fa ban yi nadama ba. Ni Anty Munnira ma shigan sauri ta yi mini. Ni ce na so na yi ma Maryama bugun tsiya wallahi"

"Kuma bakin ki bai mutu ba ko?

Hauwa ta sake faɗa sai ta yi shuru ni kuma na ma kasa mgana hankalina ya tashi. Ba wai domin za a kira Yallaɓai ba sai domin ni ban je sunan nan da wata zuciya ba. Amma gashi abubuwa marasa daɗi sun faru Allah kaɗai ya san a yanayin da labarin nan zai fita. Fuskata ba walwala na sauke su Hauwa a gida tana faɗa mini wai na kwantar da hankalina ko Yallaɓai ya zo zai fahimceni in na yi masa bayani kallonta kawai na yi. In har an so ya fahimcenin ba.

Mun koma gida muka iske Baby a ƙofar gida tana jiran mu ita da Salisun. Shi ya bude mini get na shiga da motata ciki.

"Umma me ya sa muka dawo! Ni ba zan je sunan Anty Gimbiyar ba ne?

Baby ta fara tare ni da mgana bayan na fito daga mota.

"Ni matsa ki ban waje kafin na gwabje ki."

Na faɗa a fusace saboda ta ba ni haushi. Marwa ce ta ja ta gefe tana yi mata mgana ni kuma na wuce cikin gida. A falon Yallaɓai na samu matsugunni ina mai da numfashi, gabaɗaya sai na tsargu kaina, wallahi ban ji daɗi ba ba kuma a son raina abin da ya faru ya faru ba. Ina zaune su Marwa suka shigo ko kallon su ban yi ba na tashi jaka da mayafi a hannu na shige ciki ina ji Yunma na kuka tana Uma na yi banza da ita.

Kwanciya na yi a kan gado kawai na rasa mafita. Tunanin maganar da zan harhaɗa na kare kaima a wajen Yallaɓai na ke yi amma da kamar wuya. Tun da a san tare nake da Munnira Allah ne kaɗai zai iya fitar da ni, na kasa haƙuri sai na ɗauki waya na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba har sau uku a raina na ce shike nan wayar na hannuna sai ga kiran Suwaiba da sauri na ɗaga kiran

"Suwaiba sun kira Yallaɓan ne?

"E ya ce gashi nan a hanya zai zo. Ni dai na gaji da ba ma Gimbiya hakuri na baro gidan gani ni da Mubeena za mu samu adaidaita."

Ta amsa mini, sai na furzar da iskar bakina kafin na ce" Wallahi Suwaiba na kasa sukuni Allah ne kaɗai zai fidda ni a wannan sabgar."

"Gaskiya. Domin Gimbiya sai kuka take yi shima jaririn na kuka. Ina jin hannun nan da ta bugu ta yi gocewa ko targaɗe. Allah kaɗai ya san mganganun da za su faɗa masa in ya zo. Halima can na barta tana ta faɗin duk abin da ya faru da gayya ne ke ce kika shirya komai."

"Uhm"

Kawai na iya faɗa na kashe wayar. Daman ai ba ta kaunata tun marin da na yi mata na kore ta a gidana ni na san tana neman ranar ɗaukan fansa a wajena sai yau ta samu dama ai sai ta yi amfani da damarta da kyau da kyau.

Ina nan zaune Yallaɓai bai kirani ba har aka fara kiran sallar mangariba. Daga Marwa har Baby ba su neme ni ba nima ban nemi kowa ba. Tiolet na faɗa na yo alwala na so na ta yar da salla. Ina cikin yin salla na ji shigowar motar Yallaɓai da ƙaran buɗe get sai da gabana ya faɗi. Ya shigo falon farko ina tahiyar ƙarshe ina jin sa yana kirana suna da karfi daga ji ran shi a ɓace ya ke.

"Sadiya"

"Sadiya"

Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe.

"Na'am. Ina salla ne lokacin da ka shigo."

"Me Daughter ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta?

Baki na buɗe ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buɗe bakina sai kuma na yi shuru kawai.

"Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani ɗan iska?

Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce" Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka?

"Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da ya ke kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faɗamini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. Saboda ke an targaɗa mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode."

Ya faɗa cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai.

"Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf?

Na faɗa ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa.

"E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji hauahi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi."

Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah.

"Na ɗauka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba."

"Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da Daughter amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri."

Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga na yi ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce"Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda."

Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba.

"Ni kike faɗa ma haka Sadiya?

"An faɗa maka sai me? Kai waye? Mijina! Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin" Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekari sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iyawa aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar dakai ko garke Gimbiya za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yunma ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka."

"Sadiya."

"Yusuf"

Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buɗe murya na kira sunan shi yana huci ina huci. Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba.

"Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki."

Ya faɗa yana sassauta muryan shi,

"A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.'

Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai.

"Kar ƙi kara ce mata Banza."

"Na ce banza a banza Yusuf don Allah ka dauki mataki in ka isa."

Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna.

"Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci?

Na faɗa ina zare masa ido.

"Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya."

Ya ɗan fara saukowa tun da ya daina ɗaga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su.

"Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi?

Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi.

"Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ?

"E. Ina so na gani. "

Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce" Ni kike tsarewa cikin gadara kina faɗin na ɗau mataki akan sadiya?

"E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba sai me.'

Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido.

"Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne."

"To ki tafin ma who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya."

Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce" Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci."

Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce.

"Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko?

"Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.!

Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buɗe kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma. Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faɗin" Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa."

"Umma..amm"

"Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata."

"Zan zo."

Ta fada tana zakuɗa goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye. Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa. Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce" Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana? Ki jira har sai ya kai ga haɗa ki da jami'an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa."

Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannuna na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce" Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karba ba!

"Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba."

Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin" Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe "

"Sadiya."

Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk dauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.

*Janafty**TKBB3N15*

Lokacin da na fito daga gida na san ba ni da kuɗi a tare da ni amma hankalina bai tashi ba sai da muka kai titi. Sannan na fahimci daga ni sai kayan jikina da hijabi na fito. Takalmin kafata na silafas ɗin cikin gida ne, tsabar a yanayin da na fito ba mai daɗi ba ne. Marwa na kalla da ke biye da ni, ga Afra sai ƙananun kuka take yi tana faman jijjigata.

"Marwa kin fito da ƙudi?

Na tambaya ina jan majina. Saboda tun fitowarmu har bakin titi hawayena bai tsagaita ba.

"E na ɗauko ƙaramar jaka ta"

Ta faɗa tana nuna mini jakar sai na sake jan hanci irin na masu kukan nan, mun ɗan jima kafin mu samu Adaidaita muka shiga na ce Ɗorayi zai kai mu.

Muna tafe shuru sai kukan Afra ni dai ina ta goge hawaye lokaci bayan lokaci ina jin nono na yana zuba kenan har yanzu Yumna ba ta daina kuka ba. Sai na ji tausayinta kamar in koma in ɗaukota amma kuma gwara da na barta shima ya ji in da daɗi.

"Umma."

Marwa ta kira sunana tana kallona, nima da rinanun idanuwana na kalleta.

"Me ya faru?

Ganin ta ƙura mini ido amma ta kasa mgana.

"Umma me ya sa kika taho? Da kin tsaya kun fahimci juna da Kawu "

Wata uwar harara na jefa mata sai ta yi saurin kama bakinta ta yi shuru.

"Kika sake yi mini maganar shi zan kwasa miki mari Marwa."

Na faɗa ina huci ni kaɗai har ya yi mini wannan tozarcin kuma take tunanin na zauna mu fahimci juna? Mutumin da ya ce na bar masa gida ai ya gama magana.

"Ke ko a ranki ba ki ji haushin tozarcin da ya yi mini ba. Amma kina maganar wai da ban taho ba na zauna mu fahimci juna. Tun da ke a yanayin da kika gan shi kin ga alama yana buƙatar hakan."

"Ki yi haƙuri Umma "

Ta faɗa a sanyaye amma ni sai na ji kamar ana hura ma ɓaçin raina wuta ma na cigaba da faɗa ta in da nake shiga ba ta nan nake fita ba, saboda ni gani nake yi goyon bayan Yallaɓai take yi ni kuma tana ganin laifina domin na bar masa gidan sa kamar yadda ya buƙata.

"Umma da kin taho da ko Yumna ne?

"Ba zan taho da ita ba ɗin. Lokacin da ya auro ni ai ba da ita Alhajinmu ya haɗo masa ba. Su zauna gidan ubansu nima gidan nawa uban za koma."

"Umma tana ta kuka fa"

"Ke zan ci ubanki fa Marwa in ba ki ƙyale ni da waɗanan mganganun naki ba. Kina ƙara tunzarani."

"Allah Ya ba ki haƙuri"

Ta faɗa tana sunkuyar da kai kamar munafukar tsabar yadda ta ba ni haushi kamar na kai mata duka.

"Namiji ya yi maka irin wannan wulakancin kuma don ba ka da zuciya sai ka cigaba da zama? To ko ke Kawu ya yi ma haka ni uwarki na ba ki Umarnin ki baro mishi gidan shi ki dawo gida domin ya san ubanki na da gida ba a daji ya auro ki ba."

Ba ita kaɗai har mai Adaidaitan sai da ya juyo yana kallona na haɗe rai ina harare harare.

"Hajiya a dai yi haƙuri. Rayuwar auran yanzu duk ɗan hakuri ne."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull