Turken gida book 3 cmplete - Chapter 31
Turken gida book 3 cmplete Chapter 31: Turken gida book 3 cmplete Chapter 31. Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi…
3,318 words
Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi wallahi. Duka halin su ɗaya ba su da adalci sannan butulai ne. In za ka yanki naman jikinka kana ba su suna ci wata rana sai sun nuna ma duniya kai ne mara amfani a wajen su. Ni yau Yallaɓai ya kalla ido cikin ido ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa wai har yana faɗin an targaɗa masa mata a sanadina. Ai na ɗauka yadda ya zo yana cika yana batsewa zai rama mata ne, sai wataƙila ya ji huce daga raɗaɗin taba matar so da aka yi. Ban ga laifin su ba duk mganganun da suka shirya masa in har ya yi amfani da hankalin shi da tunanin shi bai kamata ya fara da haka ba, da sai ya fara yin bincike kafin ya zartar da wata mgana.
Har muka sauka a Dorayi ni kadai na ke cika ina batsewa ina karkaɗa kafa. A bakin titi muka sauka Marwa ta biya shi kuɗin shi da taka da kafarmu muka ta ka zuwa gida. Lokacin ana ta kiraye kirayen sallar isha'i a wasu masallatan anguwan. Ai ban ji wani kukan baƙin ciki ya taho mini ba sai da na ji kafafuwana sun taka zauren gidanmu. Bayan shekaru ashirin da wani abu yau Yallaɓai ya bar mini tarihi. Tarihin ma mai nauyin da na ke jin sa har a cikin zuciyata.
Ni ce a gaba Marwa na bin bayana. Ba wutar nepa amma akwai hasken tocila a tsakar gida sai da muka ƙariso tsakar gida sannan na ga Alhajinmu duke yana alwala. Gwaggo ce ke tsaye tana haskamai da fitila. Ni na yi sallama amma muryata ta shaƙe da farko, sai da na sake yi kamar a tare ni da Marwa.
Gwaggo ta amsa lokaci ɗaya ta nai mai hasko fitila cikin mamaki.
"Sadiya.';
Gwaggo ta faɗa cikin mamaki da har ya bayyana a muryanta Alhajinmu kuma sai da ya idar da alwala sannan ya miƙe yana mai kiran sunana. "Dubu" Kamar yana tantama ɗin ce ko ba ni ɗin ba ce.
"Na'am Alhaji."
Na faɗa cikin karyewan sauti kafin lokaci ɗaya na fashe da kuka. Gwaggo ta ce" Subhanallah ke da waye haka? Alhajinmu kuma duk ya ruɗe faɗi yake yi. "Maimuna kama ta ku shiga ciki. Ba lafiya" Kamar haɗin baki sai ga nepa sun kawo wuta tsakar gidan ya yi haske ɗau.
"Marwanatu."
Alhaji da Gwaggo suka haɗa baki wajem ambaton sunan ta.
"Na'am."
Ta amsa itama a sanyaye. Ai sai Alhajimmu ya kalli Gwaggo itama ta kalle shi Allah kaɗai ya san mai suke sakawa a zuciyarsu amma in zan iya karantar fuskokin su, sun bayyana damuwa tare da mamakin ganin mu a tare a wannan daren.
"Dubu lafiya? Me ke faruwa ne? Me Marwanatu ke yi tare da ke?
"Alhaji ƙafafuwana sun fara rawa. Allah ya sa dai lafiya.'
Gwaggo ta faɗa cikin damuwa.
"Ina fa lafiya. Ba lafiya Maimuna "
Alhajinmu ya faɗa shima a muryansa har ta bayyana damuwa. Muna tsaye ni da Marwa mun kasa mgana, gwara ita ba kuka take yi ba ni kuka na ke yi har yana ba da sauti.
"Shin ba ku faɗa mana abin da ke faruwa ko sai kun sarƙe mana Numfashi da zullumi?
Gwaggo ta faɗa tana ɗan karisowa in da muke tsaye.
"Ke Sadiya bar kuka. Taho mu je abin da ke faruwa.'
Ta faɗa tana riko ni, ina jin ta taba ni sai na faɗa jikinta na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Gwaggo Yallaɓai ne ya ce wai na bar masa gidan sa"
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un.
Gwaggo ta yi salati.
"La'ilahaillalahu."
Alhajinmu ya karɓa.
"Muhamadan rasulillahi."
Gwaggo ta ƙarishe cikin wani yanayi
"Da kika yi masa me zai kore ki da girman ki da kuma daren nan?
Gwaggo ta tambaya daga jin muryan ta za ka san hankalinta ya tashi.
"Ban yi masa komai Gwaggo a kan matar shi ne ya ke son ya wulaƙanta ni." .
Na fada ina shessheƙa. Gwaggo ta na bubbuga bayana alamun lallashi ta ce"Kai jama'a. Me ya sa Yusuf zai haka? Da girmansa? To ita Marwanatu ba na gan ku tare a wannan daren?
"Suna ta zo. Gimbiya ce ta haihu yau suna suka taho daga Rano ɗazu da rana"
Ina jin Gwaggo ta sauke numfashi kafin ta ce" To da sauƙi ai na ɗauka itama wata matsalar ce."
"Umma ce ta ce na taho mu tafi. Mun baro Baby da Yumna na ta kuka."
Marwa ta faɗa kafin Gwaggo ta yi magana Alhajinmu ya ɗan murmusa yana so ya yi magana sai kuma ya yi shuru.
"Alhaji ya ka murmusa? Ka na ji surukin naka da ɗazun nan ka gama yabon sa ya baka kunya ya koro maka y'a kusan shekaru ashirin da aure cikin dare."
"Ho Mata kenan ku dai ba a rabaku da son kai. Ni daman na san ai ta tsuniyar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi ko?
"Ban ga ne ba Alhaji. Kuka fa Sadiya ke yi?
"Duk na ji. Kamata ku shiga ciki bari na je masallaci na dawo sai mu zauna mu yi magana. Allah ya rufa mana asiri.".
Ta amsa da amin ya fice ni kuma Gwaggo ta rike ni zuwa falon Alhaji Marwa ta bi bayan mu. Zama muka yi a saman kujera mai zaman mutum biyu ni da Gwaggo.
"Wai shi Yusuf din ya ce ki bar masa gidan shi!
"Wallahi shi ya ce Gwaggo "
Na faɗa ina jan hanci irin na masu kuka.
"Me kika yi masa da zafi haka? Gaskiya ya ba ni mamaki ai ko mai kika yi masa bai kamata ya yi miki haka ba "
Ina goge hanci ina zayyana ma Gwaggo abin da ya faru ina hawaye ina faɗin" Abin takaici Gwaggo wai ni Yallabai ke kallona ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa saboda tana haihuwan yaya maza ni kuma mata shine ina bakin kishi da ita na kasa hakuri na saka an dakar masa mata shi ne ya zo yana ta faɗa mini mganganu son ran shi daga ƙarshe ya ce na bar masa gidan shi"
Gwaggo ta yi salati ta dire kafin ta ce"oH ni Maimuna. Ashe yarinyar makira ce? Ina ganinta shuru shuru kamar ta Allah. Su suka shirya masa komai, shi kuma laifin sa ɗaya rashin bincike sannan na ga ɓakin sa da ya iya buɗe baki ya ce ki bar masa gida Haba. Ai ba ki cancanci wannan tozarcin ba.'
Uhm"
Kawai na iya cewa saboda zuciyata suya take yi. In ina tuna abin da ya faru.
"Umma ba cewa fa ya yi ki tafi ba. Ke kika ce mai za ki tafi ya ce shi ba zai hana ki ba "
Marwa na ƙura ma ido cikin takaicinta da bakin ciki. Na ma kasa mgana saboda na rasa abin da zan ce mata. Ina tunanin ba ni ce ƙanwar uwarta ba Yusuf Muhammad Inuwa ne.
"Af to me ya rage? Ai duk ɗaya. Mata ai mu haka Allah ya hallice mu, wata ƙila ta fadi haka ne ta gwada zurfin matsayinta shi kuma sai bai ba ta kunya ba, ya nuna mata iya na shi tattalin a kanta ya ce ta tafi ba zai hana ta ba. To ai shike nan bari Alhaji ya dawo sai ya ji shi ne da an tashi hira sai ya ce mijin Dubu dabam ne ina ganin ƙimarsa. To ai yau ga ƙarshen ƙima nan ya kore masa ƴ'a gabanin mangariba da isha'a da girmanta da komai, bai yi miki haka kina da kuruciya ba sai da shekaru suka fara gangarawa."
Gwaggo sai faɗa take yi ni sai na ga ma ta fini ɗaukan zafi. Har a ƙasan raina ban ji daɗin da ma zo gida na buɗe cikina ba amma kuma ai shi ya ja. Da bai yi abin magana ba da ba a yi magana ba. Alwala muka yi ni da Marwa muka yi salla muna cikin sallar Alhajinmu ya dawo shi ya sa muna idarwa Gwaggo ta zo ta kira ni, da man a ɗakin Mama muka yi sallar.
falon Alhajinmu na koma yana zaune ga kwamukan abinci Gwaggo ta jera masa amma bai taɓa komai ba. Duk da ya nuna kamar bai damu ba amma na san ya damu ya kasa yin wani abu ba tare da ya ji damuwata ba. Allah sarki Alhajinmu ina son shi saboda in dai matsala ta tunkaro iylanshi shi baya samun natsuwa sai ya ga ya yi maganin matsalan nan. Dattijo ne mai juriya da jajircewa. Sai a lokacin na ji nadama da tunanin me ya sa na taho gida na ɗaga musu hankali? Da man ban zo ba, ssi wata zuciya ta ce gwara da kika zo a karon farko yau dai Yusuf zai fahimci ba da gidan shi kaɗai kika dogara ba.
"Dubu."
Alhaji ya kira ni kamar yadda ya saba. Ina mai zama gaban shi na tankwashe kafa na amsa masa.
"Na'am ina yini Alhajinmu."
"Lafiya lau. Sai kika baro mini mata can tana kuka?
Kaina na kasa na kasa mgana.
"Bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Dubu. Rukayyatu nawa take da za ta fara karban hukuncin da ba na ta ba? Ba mama take sha ba har yanzu?
"E Alhajinmu."
"Kin ji ko? Me ya sa kika yi haka Dubu? Koda na sanki da fushi ai ban san ki da rashin tausayi ba ko?
"Ka yi hakuri Alhaji na yi kuskure."
"Kin yi kuskure babba. Domin kin ɗauki alhakin ran da bai ji ba, sannan bai gani ba, kar ki ƙara irin haka komai zai faru kar ki yi hukunci a in da bai dace ba. Ina ruwanta? Ta sam ne babanta ya yi miki? To ko domin wata rana ki yi aikin hankali kin ji ko?
"Na ji. In sha Allahu ba za a sake ba."
Na faɗa ina wasa da gefen hijabina.
"Yauwa. In kin baro ita Mai sunan Gwaggon ta ku ita babba ce. Amma Rukayyatu kin ɗauki haƙƙin ta."
Ni dai na yi shuru, saboda sai a yanzu da Alhaji ya sake jadadda mini sannan na sake fahintar ban kyauta ba. Ina jin nonuwana suna cika na san tana can tana rigima.
"Allah ya kyauta na gaba."
Na amsa da Amin shuru na wani lokaci kafin Alhajinmu ya sske kiran sunana.
"Halima."
Tun da na ji haka na san mganar mai girma ce.
"Na'am"
"Me ya haɗa ki da Yusufa har ya ce ki taho gida a daran nan?
Nan da nan na gyara zama cikin natsuwa na warware ma Alhajinmu komai tun daga farko na haihuwan da ta yi ban je barka da wuri da abin da ya faru yau. Har mganganun da muka yaba ma juna na fada masa, ni fa duk a tunanina Alhajinmu zai goya mini baya in ji ɗibar albarkar da Yallabai ya yi mini saboda matarsa.
"An faɗa masa ƙarya da gaskiya daga can Alhajinmu kawai yana zuwa gida ba bincike bai ji ta bakina ba kawai ya fara mini masifa da faɗa kamar zai dage ni."
Na ƙarishe faɗa ina goge ƙwalla da gefen hijabina. Domin ina mai da yadda aka yi hawaye suka kece mini.
Alhajinmu ya yi shuru ni na ma ɗauka ko wani abu ne sai da na dago kaina na ga kallona yake yi na wani lokaci sannan ya gyaɗa kai ya yi wani mirmishin su na manya kafin ya ce.
"Dubu ba dai kina so ki faɗa mini rashin kunya kika yi ma mijin naki ba?
"A'a. Kawai dai raina ne ya baci nima na ma yar masa da martani Alhajimmu."
Sai ya yi dariya wannan karon mai sauti kafin ya ce" Hohoho hausawa suka ce ko shekara ɗari ka yi baka haɗu da mutum ba. In ka fara ganin shi tambayi halin shi, domin hali zanen dutse ko zai iya sauya komai to ba zai iya sauya wannan halin na shi ba." Na yi kasaƙe saboda ina so na fahinci in da maganar Alhajinmu ta dosa.
"Dubu na san ki sarai bakin ki ba ya iya shuru. Kina da saurin hasala da faɗa. Kina so na ce kinyi daidai da abin da kika yi ne? To ba zan ce kin yi daidai ba sai ma na kira sunan ki ki amsa na sanar da ke da kaushin murya da cewa ba ki kyauta ba."
Baki na buɗe ina kallon Alhajinmu. Duk da na san halin shi amma ban tsammaci zai iya cewa wai ban kyauta ba? Me na yi na rashin kyautawar?
"Na san a cikin zuciyarki kina ta tamtaman me kika yi na rashin kyautawa ko? Duk buɗe kunnuwanki da kyau Dubu. Kin yi rashin kyautawa da yawa a cikin duka abin da ya faru. Kuma hukuncin da Yusuf ya so yankewa yana kan daidai ne shima. Tun da ba a gaban shi komai ya faru ba shima faɗa masa aka yi, kuma da bakin ki kika ce daga can gidan abokiyar zaman taki an faɗa masa ƙarya da gaskiya. To ke me ya sa da ya zo gare ki, ba ki zaunar da shi kin faɗa masa gaskiyan abin da ya faru ba?
"Alhajinmu bai ba ni da mar haka ba faɗa kawai yake yi ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba."
"Shi ne kuma yana faɗa kina fada. Har kika yi masa rashin ɗaa da gatsen ko yanzu ya ce ki bar masa gida za ki ta fi ko? To menene abin kuka don ya yi miki abin da kika bukata Dubu?
Ai sai na kasa mgana na dukar da kaina kasa. In Alhajinmu ya saka a ɗaki tun kana jin kana da gaskiya sai ka sare ka fahimci kai ne ba ka da gaskiya saboda irin kalaman da yake amfani da su wajen jawo hankalin mutum
"Ni da ke nan da Yusufa zai ƙara aure na kira ki, a wannan falon kika zauma kamar haka na yi miki nasiha? A cikin duka nasihin da na yi miki wata kalma na yi ta jadadda miki da in kika rike ta zaki rabauta?
"Haƙuri. Ka ce na je na yi ta hakuri wata rana ni ce zan zama mai riba."
"To ashe ba ki manta ba? To me ya sa yanzu kika kasa haƙurin kika kuma kasa rabauta da sakamakon masu hakuri?
Sai kawai na sake fashewa da kuka ina fadin" Alhajinmu na yi ta haƙru wallahi ba ka san hakurin da na ke yi ba ne. Ko wani abu ne suka yi mini da na tuna da nasiharka na ke ma yar da komai ba komai ba. Yau ma ɗin ya ƙure ni ne shi ya sa na tanka masa." Na gama faɗa ina ta jan hanci saboda kuka.
"Du ka na ji kin yi haƙurin a baya amma abin da kika aikata yau duk ya kore wancan haƙurin na ki na baya "
Na ma kasa mgana na buɗe baki zan yi sai na ma yar na rufe. Ni fa na manta ne in dai Alhajinmu ne ba zai taɓa bani goyon baya ba da gaskiyan Gwaggo Alhajinmu na ganin ƙimar Yallaɓai a duk cikin surukansa ya sha faɗa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.
"Kina maganar ke ma da kika haihu ba ta zo ba kaza da kaza ina ruwan ki da wannan? Ke dai ba ki yi don Allah ba ai bai kamata,ki duba ita abin da ta yi miki ba. Ke kin yi mata domin Allah da zaman tare. Ruwanta ne ta ma yar miki da martanin Alheri ko sharri. Ke dai Ubangiji ya yi amfani da zuciyarki kuma ladan ki na wajen Allah. Ba hujja ba ce mijinki ya ba ki umarnin ki je asibiti ki dubata ki yi zaman ki, ki ƙi zuwa kin ga kenan kin saba umarninsa kuma mala'iku sun yi fushi dake matuƙar ba ki nemi gafaran shi ba. Sannan kuma abin da ya faru yau sanadin ki ne, ko da ruwan zam zam ba za ki iya wamke kanki ba tun da kin je wajen sannan waɗanda ke tare da ke ne suka yi hatsiyani ni da ke mun san ke ba ki saka su ba amma ba za mu ƙi gaskiyan cewa a sanadinki suka yi komai."
"Wallahi ni Alhajinmu ban ce kowa ya yi faɗa saboda ni ba."
Na fada ina ƙara rantse masa da Allah.
"Na ce miki ni da ke mun san ba ki saka su ba. Amma shi da sauran mutane in suka ji labarin za su yarda ba bakin ki a ciki! Ki yi tunani ki gani. A wannan gabar Yusufa ba shi da laifi abin da ya ji da shi zai yi amfani."
Ina sharan ƙwallah na ce" Amma me ya sa ba zai yi bincike ba sai ya rufe ni da faɗa har yana ce mini ina da mugun nufi a raina?
Dariya na ga Alhajinmu ya yi kafin ya ce" Dubu ke kika jawo duk zargin da ya yi miki. Me ya sa kika bashi kofar ya fahimci kamar kina jin haushi da haihuwar da aka yi mass? Ki tuna shi ma fa ɗan adam ne yana da zuciya kamar yadda kike da ita. Sheɗan ne ya kawata masa a zuciyarsa amma ina da tabbacin ba haka yake nufi da gaske ba. Ai in da kima da mugun nufi akan matarsa da tun a farkon auran shi zai fahinci haka." Ni sai na ga kamar kawai ina zaune Alhajinmu na ta faman boye laifukan Yallaɓai yana bayyana nawa.
"Har fa ce mini ya yi wai ina kishi da tana haihuwan Maza ni kuma Allah bai ba ni ba "
Na faɗa hawaye na kece mini saboda takaicin kalamansa.
"Haka zai yi tunani haka ma kowa zai yi tunani. Haihuwa kuma na Ubangiji ne daman Allah ya faɗa mana wasu zai ba su maza da mata, wasu mata kaɗai wasu mazan kaɗai wasu ma har su koma ga Allah ba zai ba su haihuwan ba ki godema Allah kina cikin zabaɓɓun Ubangiji. Maganar ita tana yin farar haihuwa ki bar ta da tunaninta, tun da ai shi mijin na ku bai ce ba ya son matan ba duka yana so kuma duka ƴaƴan shi ne. Sai ki roƙi Ubangiji ya baki mai albarka daga Mazan ko daga matan."
Kawai sai na cigaba da sharan ƙwalla domin ni dai Alhajinmu ya gama ƙure duka mganganuna.
"Ki yi haƙuri ki daina kuka ba wai ina goyon bayan shi ba ne a'a ina faɗa miki gaskiya ne a matsayina na adalin Uba. Ba wai don kina ƴ'ata na goyo bayan ki ba, a'a ni ke da shi duka ƴaƴana ne zan yi miki adalci kamar yadda zan yi masa. Ki daina kuka ya isa haka nan ba wani abu ba ne. Kawai sheɗan ne ya shiga tsakani ganin kun kasa samun fahimtar juna."
"Alhajinmu ta ya ya zai fahimce ni?
"Ta hanyar amfani da kalamai na kwantar da hankali kar ki ɗaga sautin ki sama da na shi, na tabbata da kin yi haka da kun fahimci juna.'
"Uhm"
Na sha numfashi saboda na fahimci Alhajinmu ba zai gane karatun kurma ba.
Murmishi ya yi ganin na yi shuru yana kaɗa kai ya ce" Kukan ya isa kin ji share hawayen ki." Ban yi musu ba share hawayena. "Yau kike so ki koma gidanki ko sai gobe da safe? Na kalli Alhajinmu baki buɗe kafin na ce" To kore ni fa ya yi me ya sa zan koma?
"Ashe ba yanzu na gama yi miki nasiha na ganar da ke kuskuran ki ba? To za ki koma gidan auran ki in sha Allahu. Shima ai na san yana can cikin damuwa in bai zo a daran nan zai da safe ina da tabbacin haka"
Kallon Alhajimmu na ke yi na kasa mgana yadda kawai yake da confident a kan Yallaɓai ke ba ni mamaki. Don ba warware masa komai ba! Ai wallahi da ya san wani abu da tuni zai daina wani cika baki a kan shi.