Turken gida book 3 cmplete - Chapter 32
Turken gida book 3 cmplete Chapter 32: Turken gida book 3 cmplete Chapter 32. "Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi…
3,269 words
"Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi amanarki dai dai da rana ɗaya bai taɓa kawo mini ƙaran ki ba. Ko da yaushe ya zo gaisheni godiya yake yi mini yana yaba miki. Duk da na san kina saɓa masa shina haka amma bai taba fada mini saɓanin alherin ki ba. Ya zauna dake cikin daɗi da rashin sa. Kema ai ba ki taba kawo mini ƙaran sa ba sai yau. To na yau ɗin ma duk kishi ne shi ya sa ban ɗauke sa wani abu mai girma ba. Ki koma gidanki ki daidaita da mijinki domin yana yi miki kara ba domin komai sai domin yana son ki. Ki je ki ba shi haƙuri ki kara haƙuri Mai hakuri in ya yi ta shan haƙuri ba ya kiɓa lokaci ɗaya amma watan wata rana zai zama giwa in har ya koshi da hakuri"
"Ki yi hakurin kin ji ko? Ki koma ki cigaba da Biyayya aure. Domin Aljannarki tana a karƙashin diga digin mijin ki ne Dubu. In kin yi masa biyayya ki rabauta. In kin saɓa masa ki taɓe. Ni ba ruwana na riga na sauke haƙƙin Ubangiji na in kin bauɗe na faɗa miki gaskiya."
Na yi shuru ban yi magana ba kaina na ƙasa amma na daina kuka.
"Kin ji ko?
Ya sake faɗa yana kallona sai na gyaɗakaina kafin na ce" In sha Allahu Alhajinmu na gode Allah ya ƙara girma." Ya amsa da Amin kafin ya cigaba da faɗin" Da dake da Rahila ne na ke yawan kafa misali da ku. Na kan ce tun da na aurar da ku ba ku taɓa tada mini hankali da korafin mzajen ku ba. Sannan suma ba su taɓa kawo mini maganar sharrin ku ba sai alheri. Amma sai ga shi a wancan satin nan in da kike zaune Muntari ya zauna yana karanta mini wani abu daga cikin na ƙuntata da Rahila ta ke yi masa ya kasa haƙuri ya kasa tanƙwasata sai da ya karya kaurin nan ya zo gabana yana faɗa mini na kira ta na yi mata faɗa. To kema ko sati ba a yi ga ki nan zaune kina kawo mini suka akan mijin ki, ke da Rahila kuna so ku ba ma misalina kunya ne?
Da sauri na ce" Ba za mu ba ka kunya ba in sha Allahu Alhajinmu."
"To na ji daɗin haka. Allah ya sa. Allah ya yi muku albarka addu'ata a koda yaushe ya zaunar da ku lafiya sannan ya yalwata ma mazajen ku samun su yadda za su riƙe ku bisa gaskiya da amana." . Na amsa da Amin kafin na yi tambayar da ke sosa mini rai.
"Alhaji me Rahilan ta yi ma Ya Muntari?
"Ina ruwan ki? Wannan tsakanina da ɗana ne. Ya faɗa mini kuma na sauke haƙƙi na kirata a wannan falon na yi mata faɗa ta yi mini kuma alƙawarin ta daina. Kamar yadda kema ba zan yi taɗin nan da kowa ba itama ba zan zo ina faɗin rashin kyautatarwarta ba. Ni kamar alƙali ne shi kuma alƙali ana son shi da gaskiya da rike sirri "
"Ai ni za ta faɗa mini Alhaji"
Na faɗa ina mirmishi shima mirmishin ya yi kafin ya ce" Wannan shima dai duk tsakanimku ne. In ta faɗa miki ba ta yi laifi ba. Domin tare kuka tashi kuka girma, akwai sirrukan masu yawan da zaku tattauna a tsakaninku na yan uwa."
"Haka ne Alhaji."
"To kin gani. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya. Tashi ki je ki samu wani abu ki ci sannan ki kwanta da safe ki koma ɗakin mijinki ki tallafi yayanki. Ke da kika kusa kai ga suruki Dubu amaryata da na saka ana can jami'a ana ta karatu ko?
Ina dariya na amsa masa" E Alhaji amma ai ta ce ba ta ssku ba auranku na zoɓe ne."
"Manta da ita, ga matata ta gaskiya me zan yi da ta roba? Amma dai ina nan ina jiran ta a falon nan ta kawo mini suruki na ga ko na fishi dogon hanci."
Me zan yi in ba dariya ba, da man shi Alhaji dariyan ya ke so na yi. Ya sallame bayan ya ce na ce Marwanatu ta zo su gaisa ita da wannan yarinyar na ta mai kukan tsiya duk ta cika masa kunni. Na fita ina dariya na koma ɗakin Gwaggo na iske su suna ta hira na faɗa mata saƙon Alhaji sai ta sunkunci yarta ta fuce tana faɗin" Shi ta ke jira ya lallasheta." Bayan fttan ta Gwaggo ba ta matsa mini sai ta ji yadda muka yi da Alhaji ba amma dai na faɗa mata zan koma saboda Yumna.
"E gaskiya ya kamata baiwar Allah na san za ta sha kuka."
"Wallahi Gwaggo Nonuwana har sun fara tasawa."
"Wayyo sannu. Ko za ki sha panadol ne in kin ci abinci."
"To Gwaggio"
Ita ta kawo mini abincin Tuwo ne miyar kubewa bushasshiya. Na ci da yawa muna hira ban gama ba Marwa ta dawo ta ce ma Gwaggo ta je ta ba ma Alhaji Tuwo kafin ya suma saboda Yunwa.
"Ai da man ke ce kika tsayar da shi, amma shi uwarhaka ai ya koshi ya kwanta."
Muna ta dariya ta fice ta bar mu, Marwa ta zauna muka ƙarishe cin tuwo da ita ta fita da kwamukan ta ɗibo mana ruwa na sha mgani da shi. Akwai katifa a ɗakin Gwaggo ita Marwa ta shimfiɗa za ta kwanta ni kuma na ce ina gado Na yi mata sai da safe ganin waya a hannunta sai na yi tunanin mijinta za ta kira. Har na juya ta kirani.
"Umma."
Na juyo ina kallonta.
"Za ki koma ko?
Sai da na yatsina fuska kafin na ce" Alhaji ya matsa. Zan koma gobe in sha Allahu." Sai ta kama murna. Na yi shigewata na bar ta. Kayan jikina na cire, na samu wata rigar Gwaggo ta makka ce Ma'u ta kawo mata ita da daɗewa lokacin da mijinta ya koma. Gwaggo a lokacin ta ce ba ta so wai na yara ne muka matsa mata ta karba. Ashe za ta yi mini amfani ita na zuba mai taushi har kasa na ɗaure kaina dakallabi na haye gadon Gwaggo. Na daɗe ban yi barci ba kewan gidana kewar 'ƴayana da mijina. Su suka taru suka yi mini rufdugu na yi ta juye juye sai can barci ya kwashe ni har ina makara sai da na ji Gwaggo na kiran sunana.
Sannan na iya tashi na je na ɗauro alwala na yi salla nonuwana sun yi mini nauyi sun kwana a ba tsotsa ina jin kamar zazzaɓi zai kama ni amma haka na fita na share tsakar gidan nan tas na haɗa wamke-wanke Marwa ta karba sannan na je na gaida Alhajinmu ƙara jadadda mini yake yi da na ƙarya na shirya na koma gidana. Ni dai ba ni da ta cewa daman ai dole na koma ko domin Yumna amma a kasan zuciya ina cewa ba don halin Yallaɓai ba shima.
Ɗumamamman tuwon jiya muka ci da safe, na ƙara shan panadol na kwanta da niyar na dan runtsa barci ya sarkeni, tun wajen tara na kwanta ni ce sai wajen sha ɗaya na tashi. Shima ɗin tada ni Marwa ta yi wai tana faɗa mini ga su Kawu nan.
"Wani kawun?
Na faɗa ina mitsike idanuwana masu cike da barci
Kafin ta samu zarafin magana na ji kukan Yumna ai da sauri da diro daga saman gadon Gwaggo a ƙofar falo muka ci karo da Baby ɗauke da Yumna tana ganina ta rumgumeni tare da Yumma tana faɗin" Umma mun yi kewarki jiya. Yumna ta kwana kuka Abba ne ya yi ta lallashinta yana ta ba ta tea" A zuciyata na ce da kyau na ji daɗi da ya ɗanɗana. Ture Baby na yi baya kaɗan ina karɓan Yumna wacce ke ta miƙo mini hannu tana faɗin Uma.
Da sauri na karɓeta na rumgumeta ni da ita muka sauke ajiyar zuciya kamar mun shekara ba mu ga juna ba..zama na yi a saman kujera na fara ba ta nono. Allah sarki baiwar Allah ta karɓe da sauri tana sauke numfashi. Ina shafa kanta ina mai jin tausayinta. Sai na ga an yi mata wanka itama Baby ta yi wankanta.
"Ba ki je makaranta ba?
"Umma mun fa makara. Abba bai yi barci da wuri ba sai 7:30am muka tashi fa."
Ta faɗa tana kirga mini da hannunta.
"Uhm wa ya yi ma Yumna wanka?
"Abba mana. Ni kuma na yi da kai na shi ya soya mana doya da kwai Umma."
"Ya kyauta."
Na faɗa ina jinjina kai Marwa na kalla ganin tana ta shiri alamun kamar ta yi wanka ne.
"Gida za ki leƙa?
"A'a tafiya za mu yi"
"Ke da wa?
"Ni da Kawu mana. "
Sai ta ga na yi shuru ina kallonta sai ta yi dariya kafin ta ce" Umma ni da Baban Abadallah."
Sai na ware ido kafin na ce" Ya zo ne?
"Ya zo tun dazu tare muka zo da shi da Abba."
Baby ta fanshe ta sai na fara tunanin ko wa ya faɗa ma Kawu ko kuma dai ya zo ɗaukan Marwa ne bai san abin da ya faru ba sai yau.
"Ni ba ruwana. Nima da safen nan ya ce mini zai zo Abban Jidda ya yi masa waya akan kum samu matsala."
"Uhm"
Kawai na ce na cigaba da ba ma Baby Nono Jidda na ta yi mini surutu na yi kamar ban jiba. Wayata na gida ban san adadin waɗanda suka kira ni ba. Ba daɗewa muka ji muryan su a tsakar gida sai ga Gwaggo ta shigo da hijabinta tana faɗin"
"Ki ta so ta..'"
Ganina a zaune sai ta ce" Au ashe kin tashi? To maza ki shirya ga mijinki can na jiran ki." Baki na tura kafin na ce" To ban yi wanka ba zan tafi Gwaggo " "Ba gidan ki za ki koma ba? In kin je can sai ki yi. Maza tashi kafin Alhaji ya ji ya leƙo da kansa kin san halin shi." Ba ni da yadda zan yi haka nan na yanke ba ma Yumna Nono Gwaggo ta karɓeta tana yi mata wasa.
Kayana na je na saka na ɗauko hijabina na saka. Baby tuni ta fita wajen babanta Marwa na yi ma magana ko yanzu za su wuce ta ce zai kaita gida ta gai da Ya Aina. Amma kafin su wuce za ta biyo gidan tun da akwai kayanta a can na ce mata toh. Na karɓi Yumna hannun Gwaggo na shiga yi ma Alhajin mu sallama.
"Allah ya yi miki albarka. Mijinki ya yi ta bani haƙuri sharrin shedan ne Allah ya tsare na gaba.'
Na ce Amin sannan ya yi ma Yumna wasa, har yana ba ta 500 ya ce kuɗin zance ne. Na karɓan mata ina masa godiya. Koda na fita kofar gida suna jikin motar Yallaɓai shi da Kawu suna mgana amma kowannen su da motar shi ya zo. Baby na cikin mota da alamu ni suke jira.
Ba domin Kawu ba wallahi shigewata mota zan yi amma saboda shi na tsaya ina gaishe shi.
"Lafiya lau Surukata. Ashe kuma abin da wannann mara mutumcin ya yi miki kenan?
Sai na kasa magana amma na kauda kaina bana son ma mu haɗa ido da Yallaɓai.
"Ai da kin kirani wallahi sai na shigar miki. Amma ko yanzu na yi mata faɗa na ce kuma ya gode ma Allah ma ya samu surukai na gari in wani ne Alhaji ai ko kallon sa ba zai yi ba. Maimakon haka ma sai ya karrama mu, muna bashi haƙuri muma yana ba mu."
Nan ma na yi shuru kaina na kasa, Yumna ce ma ke miƙa ma Yallabai hannu tana faɗin Aba da sauri na janyeta ina ƙara haɗe raina.
"Ki yi haƙuri kin ji ko? Fushi ne da shedan suka yi tasri a kan shi amma ya tuba ya ce ba zai ƙara ba."
Sai na ɗan kalle shi ta gefen ido kansa na ƙasa yana ɗan mirmishi kamar ba shi ne ya yi mini wulakanci ba jiya.
"Ba komai. Allah ya kyauta na gaba.'
Suka amsa da Amin gabaɗaya. Shi ya buɗe mini gaban mota na ƙi shiga na faɗa baya kusa da Baby. Mun tafi muka bar Kawu anan amma ya ce za su biyo kafin su wuce. Muna tafe a hanya yana ta kallona ta madubin gaban mota ni ko na yi cuɗun ciɗun da fuska bai ga fuskar ma wata mgana ba. Haka muka isa gida ni ko jiran shi ban yi ba na yi wuce wata cikin gida. Ya biyo ni har ɗaki yana so ya yi mini magana na bar masa yarsa nan saman gado na faɗa tiolet na banko masa ƙofa ai ban fito ba sai da na ji ƙaran jan get alamin ya fita sannan na fito ina jan tsaki.
Sai da na yi wanka sannan na duba gidan. Kitchen dai ya sha kyau Baby na saka ta gyara shi ta goge da falon su. Falon Yallaɓai ko ta kan shi ban bi ba girki ma doya na ce Baby ta fre mana ta sulala mu ci da mai da yaji sai bayan azhar na duba wayata. Hauwa da Munnira sun kikkirani da Rahila sai Suwaiba. Munnira na fara kira ba ta ɗauka ba sai na kira Hauwa. Ita ke faɗa mini Mutaƙka ya yi fata fata jiya akan abin da ya faru, ni tsabar haushi ban san lokacin da na ce.
"Ku fita hanyata ku fara aminta da Gimbiya shine faɗan na su."
"Wani irin magaana ne wannan? Ai ba su isa ba. Shima ai na faɗa masa ba zai yuyu ba sai ya ce wai shi bai ne na rabu dake ba amma na daina wulakanta Gimbiya saboda ke Ya Tafida ya ce ba ya jin daɗin haka."
"Kar Allah ya sa ya ji daɗin mana.'
Na faɗa cikin ɓacin rai, ban faɗa mata na je gida har na kwana ba amma na faɗa mun hau ramar da ba ta da ganye mun fado a jiya da daddare ni da Yallaɓai.
"Kai Gimbiya ba ta ji daɗi ba. Ta haɗa karya da gaskiya.'
"Daga shi har ita in sun fasa sun raina Ubangijin su.'
Sai da na faɗa sannan na rufe baki ina waige-waige ni kaɗai sai da na yi dariya Hauwa ma sai da ta dara."
"Haushi take ji kuna tare da ni, ba ma ita ba har su Anty Bahijja ma. Kuma sai dai su mutu wallahi.'
Hauwa ta ce kwarai mun daɗe muna mgana kiran wayar Munnira ne ya katse mu. Ta ce mini Ashe ta koma tun safe,Marwa fa? Na ce mijinta ya zo ɗaukanta ta je gida ta dawo.
Munnira zage-zage ta dinga yi tana faɗa mimi hauka hauka ta yi ma Nasir jiya ya zo yana ce mata ita ke hassada fitina tsakanin matan Yaya Tafida." "Ai ko jiya ya ga tijara. Na fashe kamar tayagas faaa faaa. Haka nake yi ta in da na ke shiga ba ta nan nake fita ba. Ai daga karshe sai ya dawo yana bani haƙuri."
Ina dariya na ce" Duk haka suke suna da son kan su. Amma ba su da laifi abin da Yallaɓai ya faɗa musu. Za a ce ke ce ke da fitina ya ja miki kunne." "To ai ba shi kaɗai ba hadda su Anty Bahijja, a group ɗin gidan su je ki gani sai abin da suka manta ba su fada mana ba, na fara ma yar da martani Mimisco ta kira ni ta ce kar na sake magama shi ya sa na yi shuru."
"Au kuma?
"Wallahi kunna data ki sha kallo."
Ba musu na yanke wayar na kunna data. Sai da na bari saƙonnin duk sun gama shigowa a group din gidan su Yallabai Iyalan Marigayi Muhammad Inuwa02. Mata ne kaɗao sai mi surukai a ciki mazan suna can na farkon. An yi ta cin kasuwa akan mu har Yayar Gimbiya da ba ta zo ma sunan ba, tana ta mganar cewa ba za su yarda da duka ba ko su Anty Bahijja su ɗau mataki ko su su ɗauka da kan su.
Ita ko yar kanzagi Anty Bahijja ta ce ai Tafida tuni ya ɗauka mataki dukkanmu an ja mana kunne. Anty Maimuna ta fito ta ce ba lafin kowa ba ne sai ni Munnira ta ce ko gobe yarinya ta sake mata rashin kunya sai ta mata dukan tsiya. Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya Nasir zai ji, group ya koma faɗi in faɗa har sun jj labarin abin da ya faru. A cewar Jamila ta ce Gimbiya da bakinta tafaɗa mata ni da su Munnira taron dangin muka yi mata ita da yan uwanta Suwaiba ta yi taggin ta ce ƙarya ne tana wajen ta yi Vn wajen mimtina sha tana bayanin abin da ya faru ni ina fara ji ma haushi ya sa na kashe gabaɗaya.
An yi manganganu har Ant Zabba ta tanka ta ce in dai har gida muka je muka dake su ba mu kyauta ba.. amma ya kamata a yi bincike domim a samu sulhu. Mimisco ta tawatar ganin abin na nemen ya zama rigima ta ce kar wanda ya ƙara mgana. Ba ni da damar ma yar da martani shi ya sa na yi shuru. Kafin ma na kashe datan sai ga kiran Mimisco na ɗauka muka gaisa sannan ta tambayeni abin da ya faru duk na zayyane mata, ta ce gaskiya suma ba su kyauta amma Munmira ma ba ta kyauta da tun farko ba ta tanka su ba. Ta yi mini faɗa sosai ta ce bai kamata ina barin ƙananun abubuwa suna shan gabana ba. Na yi gaba fa sai dai a biyo bayana. Na ji daɗin magana da ita shi ya sa duk cikin yayyen Yallaɓai Mimisco na dabam ce a wajena. Ta ce ko an buɗe gidan kar na tanka ma kowa na yi shuru kawai itama amsa ce. Nan take na yi mata alƙawarin ba zan yi magana ba ta yi mini godiya muka yi sallama.
Mun gama wayar kenan ina shirin ajiyeta bayan na kashe data Jidda ta kira ni kwana biyu ba mu gaisa. Bayan gaisuwa da tambayan makaranta ta kira sunana.
"Umma."
"Na'am Jidda."
"Me ya faru tsakanin ki da Abba ne?
Cikin mamaki na ce" Me kika gani?
"To ya kira ni yanzu ba daɗewa yana faɗa mini ya yi miki laifi kina fushi da shi na kira ki na baki haƙuri"
"In ji baban na ki?
"E Umma. Don Allah ki yi masa haƙuri ba ki ji muryan Abba ba duk ya damu."
Sai na yi mirmishi kafin na ce" Bayan nan bai faɗa miki komai ba? Bai faɗa miki laifin da ya yi ba?
Tana dariya ta ce."Umma ba sai ya faɗa mini ni dai kawai ya ce kina fushi da shi na kira ki na ce ki yafe masa ki kula shi."
"To."
"Don Allah Umma."
"Na ce to ko?
Na faɗa a ɗan hasale.
"To ai Umma na san halin ki ne yanzu sai ki fara gaba da shi, yana mgana kina yin banza da shi. Allah Abba abin tausayi ne fa Umma in dai a kan ki ne."
"Ƙaniyarki Jidda."
Na fada ina danne dariyata itama dariyan ta ke yi.
"Ke har kin san abin tausayi a kaina? Zan ci mutimcin ki fa"
"Wallahi Umma in ba ki yi masa mgana da ya ganki duk sai ya ruɗe"
"Sai anjuma Jidda"
Na faɗa mirmishi, jin tana yi mini shaƙiyanci.
"Umma a duba mini my Abbana don Allah."