Turken gida book 3 cmplete - Chapter 33
Turken gida book 3 cmplete Chapter 33: Turken gida book 3 cmplete Chapter 33. Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne…
3,303 words
Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne da kiran Jidda yana cewa ta ba ni haƙuri, ba ma wannan ba yaran mu fa yanzu duk motsin mu suna ankare damu ji dai Jidda da na ke ganinta shuru shuru ashe tana ankare da komai. Wayar da muka yi da ita sai na ji zuciyata ya ɗan sauka Ina cikin ɗaki Marwa ta zo, ba ta wani daɗe ba amma ssi da na zuba mata doya ta tafin ma Kawu da shi tun da yana so amma ya ce ba za su tsaya ba akwatinta ta ɗauka na raka ta har haraba na ba ma Afra 1k na ce ita 500 Abadalla ma haka tana ta mini godiya. Kawu daman a can waje ya yi parking ɗin motar shi.
Yallaɓai na neman shiri da wuri ya dawo ana yin sallar mangariba ya siyo mini fura da kayan marmari ban sake masa gwiwa ba amma dai na karɓa kadahan kadahan. Lokacin na yi wanka abinci kuma daman farar shinkafa na dafa da daddaren ina da sauran miya, saboda na san muna faɗa sai na ji gayu na tsuke cikin riga da wando ina tafe mazaunena suna kaɗawa. Ai da ƙyar ya fita sallar isha'i yana dawowa ina ciki Yumna na wajen Baby ya ritsani yakulle kofa.
"Sadiya so kike yi na haukace a kan ki ko?
Ina tssye lokaci ɗaya ina ninke darduman da na idar da salla a kanta na ce" Sai dai in matarka ce za ta haukata ka. Amma ni Sadiya ai ban kai wannan matsayin ba.' Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji ya ruƙumƙume ni daga tsayen yana mai faɗin" Ki yi haƙuri ki yafe mini na yi kuskuren da na zo na yi miki magana cikin fushi. Am sorry please."
Na yi banza da shi, amma dai ban yi ƙoƙarin kwace jikina ba. Ya juyo da ni muna kallon juna ya saka hannu ya zare mini hijabin jikina yana bina da wani kallo duk ban yi masa mgana ba.
"Kike cewa ba ki isa ba Sadiya ta? To wai wata kuma isar kike so na nuna miki da za ki san ni a wajena kin isa kin iss. Ke ɗin isa ce kafin ma isar ta iso."
A tsume na kalle shi kafin na ce" ai ka gama nuna mini isata tun da jiya ka ce na bar maka gida.' Sai kawai ya riƙo hannuna duka buyin cikin na shi ya matse yan faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannun shi. Lokacin da kika ce in na ce ki tafi za ki tafi na faɗa ne domin na ga zaki iya tafiya ki bar ni Sadiya? Sai na ga wai kin tafi? Lokacin da kika fita wallahi ji na yi kaina ya yi wani girimgirim Sadiya na shiga tashin hankali. Me ya sa za ki yi mini irin wannan gatsen fisabillahi"?
"Gatsen me? Kai ka ce na tafi ba za ka hana ni ba."
"Na gwada ne, na gwada ki na ɗauka kema a wasa kika faɗa "
Kallon sa na yi ina wata dariya kafin na ce" Wasa? Ni ka ga wasa a magana ne." "Wallahi ban gani ba. Kin ba ni tabbaci jiya. Ni dai kar ki ƙara yi mini irin haka bana so. Sai ki saka ai zuciyata ta buga." Na buɗe baki zan yi magana ya haɗe bakin mu waje ɗaya yana tallafo kaina na yi masa tsaye ƙiƙam shi ya sa sumbatar ba ta yi armashi ba.
"Ki tallafe ni ma Sadiya ta."
Ya faɗa cikin karyewan sauti a yanayin shi kaɗai da na kalla na san tallafan yake so.
"Me zan maka? Yara na falo fa?
Ƙamƙameni ya yi yana faɗin" Na kulle ɗakin ba za su shigo ba " Ganin ina kallon shi ya sa kamar zai yi kuka ya marairaice mini yana faɗin" Don Allah I need you sosai." Sai na kasa musa massa ya ja na ya yi zuwa kan gado yana mai ƙamkame hannuwana. Duk yadda na so na basar da shi na kasa Yusuf ne fa? Yusuf ɗin da na sani tun yana matashin sa. Sai kawai nima na tallabe shi, na saki jiki na ba shi abin da yake so.
Bayam mun natsa tun kafin mu kai ga wanka ina saman ƙirjinsa ya rumgumeni yana faɗin" Ki yi haƙurin kin ji ko? Ke mai hakuri ce ki ƙara akan na baya. Mimisco ta kira ni , Suwaiba ma duk sun sake yi mini bayani na gamsu. Itama Daughter zan yi mata faɗa kowa ya yi hakuri domin a zauna lafiya kin ji" Na yi kamar ban ji ba sai da ya ƙara faɗn" Kin ji ko?
"Na ji."
"Ba ki yafe mini ba ko?
"Uhm"
Sai ya sumbaci goshina kafin ya ce.
" Ina kaunar ki."
"Ina sonka Yusuf ɗina."
Na faɗa ina sake rumgumoshi kamar na saka shi a aljanma haka ya ƙamƙameni yana faɗin
"Na gode Abar ƙaunata Ubangiji ya bar mu tare har mutuwa. Mutuwan ma ta ɗauke mu rana ɗaya" Ina mirmishi na amsa da Amin. Mun so mu shagala sai muka ji kukan Yumna a kofar ɗaki tana kiran sunana.
Uma "Uma.
Ni da Yallaɓai muka kalli juna muka kwashe da dariyan nishaɗi.
*Janafty**TKGB3016*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
Shike nan faɗan mu ya ƙare ni da Yallaɓai amma lokaci bayan lokacin in muna zaune da ya yi magana zan kalle shi na ce" Ni ai Yallaɓai ka ga ƙarar mini da ruwan kaina. Ni da ka kalla ido cikin ido ka ce mini ina da mugun nufi akan matarka. Wallahi na kasa mantawa da wannan maganar" In na faɗi haka sai ya marairaice yana lallashina shi a dole sai na manta duk kalaman da ya yi amfani da su a kaina.
"Me ya sa ba ki mantuwa ne Sadiya? Maganganun da na faɗa cikin fushi kema kin san ba a son raina ba ne. In ma na ce kina da mugun nufi ai kaina na yi mawa. Tun da tsawon shekarun da muke tare da ke ban amfana da komai ba sai alheri. Ki yi haƙuri don Allah ki daina dawo da maganar da ta wuce." In ya faɗi haka sai na tura masa baki na ce" Uhm, ai ka san da haka ka manta ka yi ta manganganu."
"Ki yi mini afuwa ki yafe mini. Halin ɗan adam ne na ajizanci."
Haka ya kan faɗi in na ta da maganar kuma ba wai ban yafe ba ne na yafe amma na kasa mantawa in na ga yana yi mini rawam ƙafa sai na kalle shi na tuna masa maganar. Tun yana lallashi da sake ban hakuri watarana ma shuru yake yi mini amma ya kan ce Allah na sama yana gani kuskure ne ya yi kuma ba wanda ya wuce ya yi kuskure. Har cewa ya yi sharrin sheɗan ne ranar ina ta tsintsira dariya shi kuma sai ya yi fuska yana hararata.
Kwana biyu kamar na manta da maganar kawai ranar yana gidana da daddare muna falon muna kallo, Yumna ta yi barci tana ɗakin su Baby, sai za mu kwanta zan je na ɗaukota. Wani American film muke kallo daman sune fina finan Yallaɓai ni kwata kwata ba sa burgeni sabo da shi ne ma na ke kallo, in ya ga na yi shuru sai ya yi ta mini bayani iyakata Umh da Hmm to ni bai san ba na son wannan bayanin ba, da zai ƙyale ni da na ji daɗi amma ba zai gane ba ni kuma ba na son na kushe ƙokarinsa. Yana cikin ba ni labarin film din ne ya gangaro kan karatu shi ne ma yake faɗa mini ya nemi gurbin PHD a Universty of Ibadan har ya samu.
Baki na buɗe kafin na kalle shi ina faɗin" Lalle Yallaɓai can Ibadan ɗin za ka koma? "A'a ai online ne karatun sai in za a yi jarabawa zan je." "Allah ya ba da sa'a." Ya amsa da Amin Amin. "Saura ni Yallaɓai maganar komawata master" "Ina za ki je da Yumna? Ki bari ki yayeta sai ki koma."
Na kalli Yallabai shima ya kalleni, ai yadda ya ga ina kallon shi ne ya sa ya yi dariya kafin ya ce" Wallahi da gaske na ke yi. Zan hana ki komawa makaranta ne? Ko Daughter na faɗa mata in har za ta koma ni ba ni da damuwa." Shuru kawai na yi masa na ma kasa mgana ina zencen makarantana yana kawo mini zencen wata matar shi, tsaki na so na yi sai na fasa kar ya ce na raina shi yana magana ina yi masa tsaki.
"Kina yayeta in sha Allahu sai ki koma. In kuma lokacin na sake yin ajiya shike nan sai ki jira ki sake haihu ki yaye sai ki koma."
Ai ban san na kai ma kafaɗan Yallabai duka ba ya kauce yana dariya. "Me na faɗa? Ba ki son haihuwan ne yanzu? "Ban sani ba." Na faɗa ina tsumewa, Rumgumoni ya yi yana faɗin"Sorry tsokanarki fa nake yi, ke ba ki san wasa ba? "Ni ka ƙyale ni, ni ai na gama haihuwa da kai, ni da ka ce ina da mugun nufi a raina game da kai da matarka."
Na faɗa ina kallon shi, da sauri ya sake ni, ni na faɗa ne a wasa amma sai na ga ya wani daure fuska.
"Yi haƙ.."
"Sadiya."
Ya katse ni da kiran sunana a fusace kafin na amsa ya nuna mini yatsa yana faɗin" Ba na ce ki bar tado da wannan mganar ba? Me ya sa ba kya jin magana ne, ko so kike yi ki ɓata mini rai hankalin ki ya kwanta ko? To shike nan kin ɓata mini rai kin ji daɗi."
Ya faɗa yana ture hannuna da na ɗora a kan cinyarsa. Ya mike na yi saurin kama hannun shi guda ɗaya.
"Sorry"
Na faɗa ina leƙen fuskarsa, tun da ya kauda kai ne ya ki dariya sai na jawo shi ya faɗo gefena na sumbaci ƙuncinsa ina ƙara faɗin" Am sorry Yallaɓai na."
Lumshe ido ya yi ya buɗe kafin ya kalleni har muryan shi ta sauya." "Me ya sa kike haka ne Sadiya? "Ba zan ƙara ba" "Shike nan ni ba zan yi kuskure kuma na zo na gyara daga baya ba? Na ba ki hakuri kin ce kin hakura to dawo da maganar kuma duk na mene ne? Ni fa mijinki ne, ke matata ce da soyayya ce ta kawo mu a wannan karnin, kina yi mini laufuka, kafin ma ki roƙe ni nake yafe miki saboda ba na son mala'iku su yi fushi da ke. Amma ke me ya sa in saɓani ya shiga tsakaninmu magana kaɗan bisa kuskure sai ki ma yar da shi makami a kaina? Ko don kin ga ina lalacewa a kanki da ban baki shi ya sa kike yi mini yanga?
Sai na kasa mgana saboda maganganun shi sun sanyaya mini jiki.
"Ka yi haƙuri wasa nake yi."
"Wannan maganar ba abar wasa ba ce. Ki bari kar ki ƙara ta yar da ita raina ba ya so. In kika ƙara zan kai karan ki wajen Alhajinmu."
Da sauri na kalle shi gira ya ɗaga mini kafin ya ce" Da gaske na ke yi. Kin fara kular da ni da mganganun ki." "Yi haƙuri ni dai. So kake yi ka sa Alhajinmu ya daina misali da mu.? "Tun yaushe? Ai kin gama karya mini wannan record ɗin a gaban Alhaji. Fisabillahi abin da kika yi ba ki kyauta mini ba."
Na tura baki kafin na ce" To ba kai ka ja ba. Cewa ka yi na fita ba za ka hana ni ba."
"Kuma kika juya kika tafin ko kunya?
Ya faɗa yana kallona ni kuma sai na juya masa baki, caraf ya kama bakin nawa ya ja, na yi ɗan ƙara ina buge hannun shi. "To kar na tafin? Na nuna maka muna da gidan uba muma" "To ai kin makara. Domin Alhajinmu ya fi sona a kan ki." "Na ga alama." Na faɗa ina rike baki shi kuma yana yi mini dariya.
"Haka fa Alhajinmu ya zaunar da ni ina faɗa masa abin da ka yi mini ina kuka amma shi yana koro mini jawabin laifina ne a fakaice yana yabon ka."
Na karishe faɗa cikin mamaki, Yallabai ya kwashe da dariya yana mai rumgumoni cikin nishaɗi, muka yi baya shi ya jinginar da kansa a jikin kujera mai zaman mutun huɗun da muke zaune ni kuma ya yi ma kaina da jikina masauƙi a saman kirjinsa.
"Wallahi na yarda Yallaɓai Alhajinmu ya daɗe yana yin ka."
"Tun a ranar farko da na fara ganin shi nima na ji kamar mahaifina. Ba ƙarya ba ne yana ƙaunata nima ina ƙaunarsa sosai na ke ganin girmansa saboda shi ɗin adalin Uba ne sannan dattijo ne."
Ina ta mirmishi jin yana ta yaɓon mahaifina.
"Na je gabansa ina mai neman afuwa na yi miki laifi. Amma ni yake sake ba ma haƙuri da Amana. Ya ce Yusufa ka yi hakuri da Duhu ka cigaba da hakuri da ita akan wanda kake yi a baya. In ta yi maka laifi ka yi mata hukunci cikin natsuwa bayan ka yi bincike. Saboda shi yanke hukunci cikin fushi yana kawo dana sani. Kin ga dai afakaice ya yi mini nasihan na daina saurin yanke hukunci cikin fushi ba tare da bincike ba."
Ya faɗa yana wasa da gashin kaina da na yi tsifa ban yi ri ga na yi kitso ba.
"Kawu ya yi ta kambama dattakon Alhaji. Na ce ai bai ga komai ba ni ne zan bashi labarin Dattakon sa." Sai na ɗago ina kallon shi, sumbatar lebensa na yi kafin na ce.
" Na gode."
"See your mouth kin gode mene! Nima Alhaji mahaifina ne so ki daina yi mini godiya kuma duk abin da na faɗa akan shi kyakyawan hallayan shi ne."
Na gyaɗa kaina ina faɗin" Gaskiya ne. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon kwana." "Amin ya yi tsawon ran da zai ga takwaran shi in sha Allahu." Sai na kalle shi kafin na yi magana ya rigani da cewa. "Ina so na yi ma Alhajinmu Takwara Sadiya." "Uhm me ya sa ba ka yi masa a wannan haihuwan na Gimbiya ba?
Mirmushi ya yi har ina jin sautin mirmushin. Kafin ya ce" Zan iya yi masa ba wanda ya isa ya ce don me. Amma na fi so takwaran Alhajinmu ya kasance Dubu da Yusufa ne iyayen sa. Sai ya fi soyuwa a wajen ki da wajen Alhajinmu." Girgiza kaina na yi kafin na ce" ba ka san Alhajin mu ba ne. Ko ni ko Gimbiya duka ba zai bambata mu ba." "Duk da haka dai. Hausawa suka ce abin cikin ƙwan ai ya fi ƙwan daɗi." Dariya na yi shima yana taya ni,na ƙara rumgume shi ina faɗin.
"I love you Yallaɓai na."
"I really like you Sadiya ta "
Na ɗago ba zato kawai ya haɗe bakin mu, yana sumbata na. Sai nima na rumƙumƙume shi da hannayena na zagaye da su zuwa maransa ina shafawa. Hannu ɗayan kuma na saman kirjinsa ina masa wasa. Ban ɗauka za mu zarce ba sai da na ga Yallabai na sabule mini ƙaramar rigar da jikina da sauri na riƙe masa hannu ina kallon shi.
"Ina so.
"Mu yi a falo."
Ya faɗa ararrabe saboda a lokacin ya ɗan kai sama can yana buƙatar matallafiya.
"Yara fa? Kar su shigo."
Sai ya tashi yana layi, ya je ya rufe mana ƙofar falo ya kashe wutar amma bai kashe kallon ba. Tun yana tafe gare ni ya cire farar vest ɗin jikinsa ya yi kuma fatali da dogon wandon dake jikinsa, kaina ya ƙariso ya jawo ni a saman kujera mai zaman mutum ɗaya ya zaunar da ni a saman jikinsa muna masu kallon juna.
Ƙura mini ido ya yi da ɗan hasken Tibin da ke falon idanuwansa sun juye sun yi ja sannan sun ƙanƙance.
"Sadiya ta."
"Uhm"
Na faɗa a ƙasan makoshi.
"Ki agaza miniiiii"
Ya faɗa cikin wani yanayi sai da tsikar jikina ya tashi da gudu na haɗe bakin mu waje ɗaya shi kuma hannayen shi na kara kaina wajen raba ni da yar ƙaramar shimin dake jikina. Ba ka jin komai sai tashin nunfashin mu sama sama.
Gaskiya Yesterday was cool. Na faɗa a cikin raina jiya nan mun yi nishaɗi da ni da Yallabai mun gamsu da juna fiye da tunanin mai tunani. Yallabai na ƙarshe ne wajen sarrafa ma mace da jan ragamar tunaninta in ta shiga hannun sa. A jiya nan haka ya ruka juyi da ni kamar waina ni ma ba a bar ni a baya ba na yi ƙoƙari sosai wajen faranta masa rai. Sai wajen ɗayan dare muka koma ɗakin mu bayan na je na ɗauko Yumna. Da asuba kuma a tiolet ya yi ɓarnan ruwan shi, ina ya bari ya bari amma bai ji ba sai ya ɗaga ni sama sai ji na yi kawai ya baƙunce shi, ban ɗauka har a tiolet lamarin zai ba da armashi ba sai da ya nuna mini hanya. Kai jama'a ni dai na faɗa muku Yallaɓai duniya ne wallahi."
Ni dai tun da faɗan mu ya kare da Yallaɓai na manta da maganar Rahila sai da ta zo gidana na tuna na yi mata zencen me ya haɗa ta da Ya Muntari? Magana ta kawo magana na ba ta labarin artabuna da Yallaɓai, har dalilin da ya sa na ji batun su ita da Ya Muntari Shi ne take faɗa mini kan wata budurwansa ce da ya ke kashe ma kuɗi, tana ɗauke masa hankali, ai ni na yi suman zaune kar ka raina namiji. Ya Muntari da nake gani sumu sumu kamar na Allah ashe kwallo ne.. Rahila na hawaye tana faɗa mini irin tashin hankalin da watsttatsiyar yarinyar nan ta saka ta a ciki. Ta hargitsa mata gida ba zaman lafiya ita da Ya Muntari, ta daina wanka ta daina mgana ta daina girki shine da ya gaji da magiya ya kawo ƙaranta wajen Alhaji.
"Tabdijam amma dai Ya Muntari bai da kunya."
Rahila ta jinjina kai kafin tace" Dakyar na samu ya rabu da ita .Kuma ba shi da ƙudin auranta amma tana cinye masa kuɗi daga waje."
Ni dai har Rahila ta tafi ina ta kambama lamarin a ƙasan raina. Wai Ya Muntari tabdijam! Ban taɓa tunanin haka daga gare shi ba. Ai daga nan na daina raina wayan namiji. Yana fama da rayuwarsa amma yana ɗebe ma kansa aiki. Allah dai ya kyauta. Yadda ni kaɗai na sani sai ban furta ma kowa ba amma na yi ƙoƙari sosai wajen taimakon yar uwata ta dawo cikin hayyacinta da shawarwari da jikina kuma da Aljihuna. Lokaci kaɗan kuma ta manta ta dawo kamar ba ita ba. Maza maza mutanen mu.
***
Tun bayan abin da ya faru ba mu ƙara haɗuwa da Gimbiya ba sai da ta yi arba'in ta zo gidana kuma ina da tabbacin Yallabai ne ya matsa mata tun da shi ya kawo ta da kan shi. Da sunan an kawo mini Ammar na gan shi. Ban nuna komai ba na yi musu kyakyawan tarba, gidana ta yi yini tun safe har dare har yara da suka dawo makaranta nan Salisu ya kawo su tun da mamansu ta na gidana.