Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 34

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 34

Turken gida book 3 cmplete Chapter 34: Turken gida book 3 cmplete Chapter 34. Da farko ta ɗan yi ɗari ɗari, amma daga baya da ta ga na nuna kamar ma wani…

3,352 words

Da farko ta ɗan yi ɗari ɗari, amma daga baya da ta ga na nuna kamar ma wani abu bai faru ba sai ta saki jikinta. Amma ban ƙyaleta ba sai da na yi mata maganar da man kuma na yi alƙwarin ko ba jima in dai muka haɗu sai na fada mata gaskiya. Ce mata na yi a duk abin da za ta yi to ta riƙe gaskiya da amana. Ta sani Allah na sama yana ganin ta, in har ta nufi wani da sharri to ta sani ƙaiƙayi na iya komawa kan masheƙiya. Sai ta fara kame-kame da cewa wai ba ita ce ta faɗa masa abin da ya faru ba kawai dai ya zo ya ganta tana kuka ga targaɗe a hannu shi ne ya fusata tana ta dai ƙoƙarin kare kanta na ƙarya ahalin ni da ita mun san ba gaskiya ta ke faɗa ba.

"Magana ai ta wuce. Da man na ce sai na faɗa miki gaskiya. Ki sani ni tsakani da Allah na ke zaune da ke ban taɓa nufin ki da wani sharhi ba. Ruwanki ne ki gyara alaqata da ke a zuciyarki ruwanki ne ki cigaba da ɗaukata tun farko. Amma ni dai ba zan fasa zama da ke tsakani da Allah ba sannan ba zan fasa mutumtataki a matsayin ki na matar mijina kuma uwar yayansa ba."

"Na gode in sha Allahu zan gyara. Don Allah ki yi haƙuri "

"Ba komai. Ban riƙe ki ba, koma na ƙullaceki a baya na yafe miki. Ni da ke ba mu isa mu hana kan mu jin kishin juna ba tunda kishi gaskiya ne. Amma in ya taso mana mu koyi yadda za mu sarrafa shi akan mu. Allah ya ba mu zaman lafiya."

Ta amsa Amin duk ta ji kunya ni kuma abin da ke zuciyata na faɗa mata. Tare muka yi ma tuwon shinkafar da na yi mana da daddare muna yi muna ɗan hira jefe-jefi a bakinta ma na ke jin Nene ta yi zazzabi kwana biyu na ce ban sani ba ai da na je na duba ta. Da Yallaɓai ya dawo da daddaee ya ji daɗin ganin mu tare gwanin ban sha'awa. Ranar girkina ne saboda haka na yi kwalliya yar caras da ni ina tashin ƙamshi. Tare muka yi dinner gabaɗaya har yaran cikin farinciki abin da ba mu taɓa yi ba.

Ni ban faɗa masa wani abu ba shi ne muna falon shi tare ya kallemu ni da ita yana faɗin" Na ga chanji daga gare ku na ji daɗi kwarai." Sai ta ce masa ai ni ce na yi mata nasiha kuma ta ji za ta gyara in sha Allahu. Ya yi ta washe baki yana jin daɗi ya taso ya rumgumeni yana sumbatana a ƙuncina na ture shi ina hararan shi.

"Ke ce jagoran mata na ko a gidan Aljanna Sadiya ta. Ni da duk abin da na mallaka duka na ki ne."

"Har wannan gidan?

Na faɗa ina dariya. Sai ya gyara zama a hannun kujeran da nake zaune ya ce" Wannan gidan da abin da ke cikin shi ai ya zama na ki, yau ba fata nake yi ko mutuwa ko rabuwa ba wanda ya isa ya fidda ke daga cikin sa. Sai dai ni ki kore ni ma domin kin cancanta." Ina dariya na ture shi ina faɗin"Bana son daɗin baki." "Wallahi da gaske na ke yi " Ya faɗa yana ƙoƙarin ya dawo ya zauna kusa da ni sai na tashi na koma kusa da Gimbiya na zauna.

" Ni za ku haɗe ma kai?

Ya faɗa yana kama baki ni da ita muka haɗa baki wajen fadin" E ɗin." Muka faɗa a tare muna dariya sai ya koma ya zauna akan kujeran da na tashi yana faɗin" Za ku neme ni yara "

"Yara?

Na faɗa ina kallon shi sai ya zare mini ido yana faɗin" E yara ko kun girme ni ne? Sai na yi shuru tun da na fahimci yana jin magana ne. Saboda jin daɗi sai wajen goma ya tafi kai su gida da ya dawo bayan mun kwanta sai da ya yi mini maganar.

"Na gode Sadiyata. Don Allah ki cigaba da haƙuri. Ba ki ji farincikin da na ji ba lokacin da na gan ku tare da Daughter ba"

"Uhm"

Kawai na iya cewa domin sai na ga kamar Yallaɓai na sane a duk wasu iskancin da Gimbiya ke yi. Me ya sa ba zai mata faɗa ba? Sai ni ce zai yi ta nanata ma in yi haƙuri da ita, ita ba zai ce ta yi haƙurin ba. Ni dai na yi masa yaƙe kawai ban nuna komai ba, sabo da kauda maganar sai na yi masa maganar zazzabin da aka ce Nene ta yi kwana biyu. Sai ya ce mini ta ji sauƙi ne shi ya sa bai faɗa mini ba amma na bari weekend sai na shirya mu je da yara mu gaishe ta na amsa masa.

Haka ko aka yi ranar lahadi muka je Gwammaja tun safe muka yini. Da man su Baby sun yi hutun Tahfez saboda gabatowar azumi, Nene ta ji sauki amma jikinta ba karfi ina gidan sai ga Halima wataƙila saboda idanuwan Nene ne ya sa ta gaishe ni, nima saboda mahaifiyarta na amsa. Ni saboda ita a bangaren Maman farko na yi yini na, sabo da ba na son abin da zai haɗa ni da yarinya. In ta neme kawo mini wargi ba zan ɗauka ba. Muna gidan har dare tun da Yallabai ne ya kawo mu sannan shi ya ce zai biyo ya ɗauke mu. Motata a gida na barta. Tun la'asar Halima ta tafi gida shi ya sa na koma ɗakin Nene, duk da ba ta fito fili ta furta mini ta ji maganar hatsniyar da muka yi a gidan sunan Ammar ba a maganganunta na san jirwaye take yi mini mai kama da wanka. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali, ya ishi mai hankali wanka.

Ta yi ta ba ni haƙuri ne, tare da nuna mini na cigaba da haƙuri ina kauda kai. Sannan ta gangaro kan maganar Halima ta na nuna mini na yi hakuri da ita akwai yarinta a tare da ita, da ta ji labari ta yi mata faɗa sosai tun rashin kunyar da ta yi mini na farko. Ni dai ban ce komai ba illa to, amma ina ganin beken Nene, Haliman ce yarinya? Mata da mijinta da yayanta ai ta san abin da take yi. Na dai nuna ma Nene komai ya wuce amma a ƙasan raina na kudiri niyyar ba zan bi ƙanwar miji ta samu damar cin kasuwa a kaina ba. Ni ko yayar miji na ga tana tozartani kama kaina nake yi ballanta ita ƙaramar alhaki.

Mune sai goman dare Yallaɓai ya biyo muka tafi gida. Mu dai mun tsaya mun ci tuwo shi kuma sai da na dafa masa Tea da Indomie ya ci kafin ya kwanta. Sabgogin gaba na kawai na cigaba da yi ga matsowar azumi, shi ya sa na saro inears da yaawa wannan sallar har da mayafai da takalma na yara da manya. Yallabai ya ba ni 100k rance a cewarsa zan biya shi in na haɗa ribata na ce na ji na karba da shi na samu na ganganɗa na ɗinko hijabai diffirent ɗinki kala kala sama da hamsi suna gida sai dai da an saka oder na saka a leda na naɗe Baby na taya ni muna sawa a jaka ko a leda. Tun da Jidda na makaranta sai Baby ke taimakona yanzu. Kuma Alhamdulillah, ana siya sosai ina samu ga Jidda ma tana saka mini a status tana yi mini talla har yan makarantan su sun ce suna so. Irin mata yan dapertment din su, akwai wata ma course ɗin ɗaya sannan ɗakin su ɗaya Ummu Salma Hamza ɗiyar Iyan zazzau ne na garin zaria itama akwai ƙoƙari kamar Jidda shi ya sa suka fara ƙawance shima ɗin sai da Jidda ta neme shawarata ni kuma na faɗa ma Yallaɓai na ce ya saka a yi masa bincike kan yarinyar kar ya zo ta shiga jikin ɗiyarmu ta cutar damu.

Shi ya bincika kuma ya ce yarinyar ta fito babban gida masu tarbiya. Jin haka ya sa muka ba ma Jidda izini ta saki jiki da ita, to ita ce ta siya hijabai sama da kala ashirin kaloli dabam-dabam. Ni kuma sai na ba ta kyautar ɗaya da dogon wando da sikat da pant saboda kyautatawa mai son ɗiyata. Cikin saƙon Khaleesat na saka musu sakon su can gidan suka je suka karɓa. A lokacin suka fara test ni dai addu'ata ko da yaushe Allah ya tsare mini yarana Jidda kuma ina yi mata fatan sa'a da nasara. Yallabai kuma yaƙini gare shi a kan Jidda da cewa in sha Allahu za ta saka shi alfahari wata rana.

Cikin haka muka shiga watan Ramadana, Jidda sai kusan salla ta dawo gida hutun na su ma na sati ɗaya ne ana fice salla ta koma saboda suna shirye-shiryen fara jarabawar farkon zangon karatu. Mu dai muna gida muna bin su da addu'a sai da suka gama jarabawa suka samu hutu ta dawo gida, duk ra rame sai ɗan wuya da tsawo. Yallabai ya yi ta faɗa wai kar ta saka ma ranta karatu ta mutu saboda naci. Ta riƙa hutawa tana cin abinci, dawowar Jidda na sake saka mata ido ko zan ga wani canji ban ga komai ba sai ma girma da hankali da natsuwa da Jidda ta kara. In ina kallonta sai na cika da alfahari na ce Ubangiji ka gama yi mini komai tun da ka ba ni Jidda. Baby ce dai wannan ko aure ta yi na tabbata sai na rika yi ina kwaɓa mata. Shegen rawan kai ne da surutu gare ta.

Kafin su koma Ummu salma Hamza ta kawo mata ziyara takanas ta zaria. Direba ya kawo ta a ranar kuma suka koma, ni kaina har da ni a masu yi ma Ƙawar Jidda Hidima. Itama na ganta mai kyau da ita age mate ɗin Jidda ce, ita ta fi Jidda haske da kiɓa amma tsawon su ɗaya. Itama a zuwan da ta yi na fahimci tana da natsuwa sosai. Har Yallabai sai da Jidda ta kira shi ya dawo gida ya ga Ummu Salma suka gaaisa ni kuma ta ba ni mahaifiyarta muka yi waya. Ta ce mini tana shigowa Kano, za ta neme ni wata rana na ce in sha Allahu. Amma ta ce na karɓi lambarta a wajen Ummu sai na kirata na ce in sha Allahu. Ta kawo ma Jidda Atamfa da mayafi, sai Baby ta kawo mata doguwar riga har Yumna an kawo kayan wasa tun da ta san sunansu a baki. Nima da za ta tafi na ba ta hijabai biyu na ce ta kai ma mamanta. Sai turaren wuta da na jiki sauran nawa ne na kwashe na ba ta, Jidda daman ta yi cincin da donut ta kwashe mata aka yi raffing. Yallabai kuma 20k ya ba ta tace karɓa ya zare mata da cewa shi mahaifin Jidda ne. Kuma duk wanda yake aminta da Jidda ya tabbata shi din uba ne gare shi, shi ya sa ta karba ta duka har kasa tana godiya. Muka rakata har waje, direban daman da ya kawo ta, tafiya ya yi sai da za su tafi ya dawo. Ni da kaina na yi ma Jidda alƙwarin itama za ta je har gida wajen Ummu salma. An ce tuwon girma miyan shi nama.

Kafin babbar salla suka koma makaranta. A lokacin na yaye Yumna, da na biye ma Yallaɓai to ba zan yaye ta ba. A cewarsa wai ba ta gama yin ƙwari ba yarinya bukekiya tana yawon ta ko'ina, tuni na cire ta a nono tana da wattani sha bakwai cikin na sha takwas. Da wajen Ma'u zan kai ta yayen, tun da ita ta yi mini magana. Har Marwa itama ta yi nacin na kai mata Yumna yaye. Ma'un da muke kusa na yi niyyar na kai mata ita ta yayeta kwatsam sai muka wayi gari da rasuwar mijin Baaba. Ma'u na can Kura mu ma mun je mun kwana ɗaya mun dawo har Amina dake Kaduna ta taho. To Allah ya sa dai ita ce uwar yayen Yumna ita tafi da ita Kaduna a can ta yi babbar salla. Tun tana rigiman Umma Abba Baby har ta gaji ta haƙura tun da akwai yara a gida. Yallabai ya gaji da korafi na ɗauki hakkin yarinya ya haƙura shima.

Sai da ta yi wajen wata biyu sannan Amina ta dawo da ita. Yumna ta ɗan rame sannan ta kara girma sun kawo ta da sha tara na arziki ita da mijinta Yallabai na ta fadan wai na tura musu ɗawaniya. Na ce na ji ba komai ai ƙanwata ce in ta yi mata ba ta faɗi ba. Rayuwa dai alhamdulillah tana tafiya cikin farinciki. Yallabai yanzu fa na neman ya sha kwana. Kuɗi kawai yake facaka har mota ya sauya wata jeep ce itama mai tsada. Adnan ya faɗa mini da muke hira da shi za ta kai miliyan huɗu daga nan na yi shuru. Sannan ya bude shagunan sai da kayan gini, komai na na'uin gini akwai, kofifi, interlock, simnti, kayan aikin tiolet, kwano, ba abin da babu a wajen ƙasan wajen kuma ya saki shagunan masu aski da wasu yan kasuwan sun kama sannan ginin gidan shi ya yi nisa har an yi linfter an saka kankare tuni yanzu ma rufe yace mini ake yi, an ma kusa gamawa da ya nuna mini a hoto. Sai ina ta mamakin gaggawan da yake yi a kan ginin nan sai da na yi masa mgana.

"Ina so ne ko ba ku tare ƙarshen shekaran nan ba to a farkon shekaran 2023 mu tare a sabon gida in sha Allahu."

"Allah ya amince mai girma Md."

Na faɗa ina dariya har ina jinjina, saboda maganar gaskiya Allah ya buɗa ma Yallabai kwangolili ne wasu na jiran wasu malam. Kuma in dai aka bashi kwangila ya yi shike nan duk wanda ya gani sai ya yaba yace a haɗa shi da shi sillar gasikiya da amana da aiki ba ha'in ci. Mu kan mu mun shaida Mijin mu na da kuɗi yanzu, abinci sai dai mu yi kyautarsa. Duk wani abu na daɗi muna ci, suturu kuwa na kece raini muke sawa mu da yayanmu. Ba mu ba har iyayen shi ma yana yi musu nima ba abinda zan ce masa sai godiya. Ya ba ni kuɗi na kai gida ya kai kayan abinci komai fa sai godiya. Da shi da Kawu sun yi ma Tariq fintikau shi duk cikin su ba shi da ƙarfi tun da aikin Gwammati yake yi. Su kuma yan buga buga ne da man.

**** BAYAN WATTANI HUƊU.

A watan october 2022 Baaba ta gama idda sai ga shi karshen ta dai gidanmu ta dawo da zama ita da sauran ƙannen Ma'u su Zainab. A ɗakin Hajiya Dubu su Ya Hamza suka gyara mata daman tarkace ake sawa a ciki. Baaba duk ta yi laushi kamar ba ita ba, ni ce wai za mu zauna muna hira da ita har muna dariya abin da ban taɓa tunanin fatuwarsa ba. Datti ya samu aiki a NNPC reshen jihar kaduna har an saka masa rana zai yi aure zai auri wata abokiyar karatunsa tun suna KAsu ba ta yi aure ba har ta yi masters tana aiki itama. Duk kuma a kusan lokaci ɗaya aka saka musu ranar aure tare da Adnan, wanda shima ya fara aiki a ma'aikatan Yallabai a matsayin Engeanaring na karatu.

Tuni ginin gidanmu ya yi nisa ko na ce cikin kashi uku an yi biyu saura ɗaya. Tun da ko wancan satin da hanya ta bi da mu ni da Ma'u da su Ya Aina na ɗauko su a motata mun je gaba da in da gidanmu na mu yake, gaisuwa yayar Zaitunan Ya Abubakar ne ta rasu muka je mata gaisuwa. Na bi da su ta gidan har sauka ma muka yi suka gani, Mun shiga ciki ma'aikata ne sama da ashirin suna aiki, wasu sun sanni suna ta faman gaisheni waɗanda ba su sanni ba suna faɗa musu matar injiniya ce.

Mun iske suna ta saka inteelock na tsakar gida. Wasu na ciki ɗakunan suna yin filista, wasu na ma an gama ana saka kofofi daman POP da wearing din wuta ana gama rafta Yallabai ya ce an yi su. Na ga har fulawoyi aka shushuka a gidan har sun girma daman Yallaɓai akwai son shuke-shuke a gida. Ya Aina da Ya Balki suna santin girman gidan da kyan shi, Ma'u ko har da guzarin kasar wajen da yake tana da ƙaramin ciki sha take yi wai ta yi mata daɗi.

Muna tafe a hanyar komawarmu Ɗorayi Ya Murja ta ce"Gidan nan da girma yake. Amma na ga shashi huɗu ko aure Baban Jiddan zai ƙara? Ya Balki tace" Ni ma abin da zan ce kenan bayan shashin Sadiya da na abokiyar zamanta nata ga biyu nan kusa da juna."

"Nima fa ina ta mamaki."

In ji Ma'u dake gidan Gaba su suna can baya ne.

Ina dariya na ce" To Allah masani. Mu ma dai haka muka gani da na yi magana ya ce ɗaya na shi ne ɗaya na baki. Daga karshe yace ga shi da yara maza ya yi awadace ne."

"Uhm ya dai ce muku ne amma da wahala bai ƙara ko dayan ba ne ballanta yanzu da giyar kudi ke ɗiban shi "

In ji Ya Aina ni ko na saka dariya ina ba su labarin diramasu da Gimbiya.

"In Yau Yallaɓai ya ce zai yi aure ai akwai yaƙin duniya na uku shi da matarsa."

"Ta yi ta gama. In dai ya yi niyya sai ya yi."

In ji Ma'u ita da ta ga zahiri, ga amarya har ta haihu, itama an zama daya da ita.

Ni dai ina ta dariya har muka kariso gida, Rahila ba ta je ba, ba ta da lafiya ta ce sai gobe za ta leko, muna gidan har bayan la'asar muna ta hira da Baaba da Gwaggo. Har a raina ban kawo ma Yallaɓai aure yanzu ba, ba kuma don ban ji a raina zai ƙara ba amma sai don ina ganin wataƙila akwai sauran lokaci. Sai dai me? Sai na fara ganin canje-canje daga wajen shi, yana yawan kafa-kafa da wayarsa a kwanakin nan. Abin da a baya bai dame shi ba in ba aiki zai yi a ciki ba ko an kira shi ta yini a in da take bai taɓa ba ya fi amfani da laptop ɗinsa a kan wayarsa

Amma a kwaanakin nan Yallaɓai na kan wayarsa har murmishi zan ga yana yi wani lokacin, na rasa me ya ke dubawa ko kuma me ya ke karantawa? Sannan wata rana in yana gidana zai dawo ya yi wanka ya ci uban gayu ya fita in na yi magana sai yace akwai mutanen da zai gani ne. Ni kuma samin shi da jama'a da hulɗodi sai ban damu da fitan na shi ba amma a kwanankin na fara zargin Yallaɓai yana yin wani sabon abun da bai saba yin shi ba, sannan ranar ma Yumna na wasa da wayarsa da ya ijiye a saman kujeran falon sa ya shiga tiolet, sai na karɓa abin mamaki na san code ɗin buɗe wayarsa date ɗin aurenmu ne, amma sai na gwada ya ƙi buɗewa kenan ya canza. Da ya fito ya ga wayar a hannuna ya ɗan yi wani iri, da sauri kuma ya karɓe wayarsa ni kuma sai na ce masa Yumna ce za ta yi masa wasa da shi na karɓa Tambayarsa na yi ashe kuma ya sauya code ɗin buɗe wayarsa.

"E na sauya."

Bai kuma faɗa mini abin da ya sauya da shi ba sai da na tambaye shi.

"Date ɗin ranar da na buɗe ma'aikatana ne."

Haka kawai ya faɗa daga nan kuma ya koma ya zauna ya cigaba da duba wayar tashi. Har yana wani mirmishi na yi kasake kaawai ina bin sa da kallon mamaki amma na kasa magana.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull