Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 35

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 35

Turken gida book 3 cmplete Chapter 35: Turken gida book 3 cmplete Chapter 35. Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da…

3,320 words

Na ɗauka ni kadai ce na fahimci Yallaɓai na yin wasu baƙin abubuwa. Sai da Gimbiya ta yi mini magana a chart, da man tun bayan faɗan da na yi mata muke yar daɗi da ita in ma wani abu ne ya shige mata duhu akan mijinmu za ta kira ni mu tattauna.

"Maman Jidda."

Na amsa mata lokacin Allah ya sa ina online itama haka.

"Kin fahimci Daddy na yin wani abu a boye wanda ba ya so mu sani!?

Sai na ce mata ban fahimta ba, saboda ko na ce na fahimta ba ni da hujja tun da ban ji ba, kuma ban gani ba.

"Me kika gani? Me ya sa kuma kika ce haka?

Sai na rubuta mata tambayoyin na tura mata sai na ga tana yi mini Vn Yana shigowa da sauri na buɗe.

"Maman Jidda Daddy na yin wani abu gaskiya. Yanzu fa kafa kafa yake yi da wayar sa kuma a da ba haka yake yi ba. Maman Jidda Daddy fa yanzu sai ya kai 1 na dare yana online sai ka rasa da wa yake yin charting da na yi magana sai ya ce wai da abokan hulɗarsa ne. Sannan sai ya rika yin wanka ya ci gayu ya ɗau mota ya fita sai dare yake dawowa ni fa gaskiya na fara ji a jikina anya anya kina ganin ba wata ce can a waje ta fara ɗauke masa hankali muna nan zaune ba mu sani ba."

"Hmmm."

Kawai na tura mata na ma kasa magana. Ashe dai ba ni kaɗai na lura da wani abu na ɗaukan hankalin Yallabai a kwanakin nan ba.

"Ki yi magana. Ke ma kin fahimci haka,?

"Nima na fahimta amma na kasa gane me ya jawo haka."

Na amsa mata

"Kin ji ko. Wallahi mu tashi tsaye da bincike kar muna zaune wata shegiya ta ɗauke masa hankali.'

Sai kawai na ce mata to zan bincika itama a ɓarayinta ta bi komai a sannu sai ta amsa ni da to, wai har da cewa ta sanni da sanyi wani lokacin wannan karon ba abin yin sanyi ba ne sai kawai na tura mata dariya.

A ranar da muka yi magana yana gidan Gimbiya ne sai washegari da zai dawo gidana ya saba dawowa da wuri, amma yau har goman dare bai shigo ba na gaji da jiran shi kuma na kira shi bai ɗauka ba. Kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tun da ni ban saba kiran ta haka ba. Baby ce daman ke jiran shi kan maganar JSSCE ɗin ta na makaranta ta ƙi yin barci daga ƙarshe da ta gaji da jira dole ta kwanta.

Ba Yallabai ya shigo ba sai sha ɗaya saura. A yanayin da ya shigo mini ba na lafiya ba ne. Toilet ya faɗa yana faɗa mini cikinsa ya lalace. Wayarsa da babban rigan sa ni ya bari da su tunda ni ce na tarbe shi.

Na shiga bedroom ɗin mu da niyyar na ijiye masa wayar da key ɗin mota sai rigan shi. Ina shirin ijiye masa wayar a saman gado kira ya shigo. Gabana ya faɗi ras! Ganin sunan mai kiran RABI'ATU BUK."

Har ta katse na kasa daina kallon wayar. Kaf a tunanina ban tunano wata yar uwan Yallaɓai mai wannan sunan ba. Ban gama mamaki ba gur! Saƙonta ya shigo wayar daga sama na ja na fara ganin abin da ta rubuto.

"Yallaɓai na ka isa gida lafiya? Mun gode...!

Daga nan sai saƙon ya yanke, jiki na rawa na watsar da rigar hannuna ina ƙoƙarin gwada buɗe wayar amma na kasa. Wata zuciyar ta ce Sadiya ki natsu ki yi aiki da hankali. Sai kawai na ijiye ma sa wayarsa nan saman gadon na zauna a gefe na ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya ina girgizawa.

Mintina biyar sai ga shi ya buɗe kofar bedroom ɗin ya fito yana nishi sama sama.

"Cikina kawai ina hanya ya karta. Ina zuwa sai gudawa kina da ko pulajin ne Sadiya?

Ya faɗa yana dafe cikinsa. Lokaci ɗaya yana ƙarisowa gabana yana kuma ƙoƙarin cire rigar jikinsa.

"An kira wayarka. "

Ya kalleni a ɗan tsume yana cire rigan daga shi sai farar vest.

"Ta kuma turo saƙo."

Sai kawai ya tsaya yana ksllona. Nima ina kallon fuskar shi yanayin shi ya nuna tsoro amma sai ya yi dakiya irin ta maza.

"Rabi'atu ce ko?

Ya faɗa yana kallona.

"E ita ce"

Na faɗa ina kallon shi, shima yana mai kallona sai kawai na ga ya yi murmishi. Mirmishin da na ji ya soke ni a ƙasan zuciyata.

*Janafty**TKGB3017*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX

Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka. 09069067488. +234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

"Da man na san za ta kira."

Ya sake faɗa lokaci ɗaya da ƙwatanƙwacin irin mirmishin da ya yi a farko lokacin da na ce an kira wayarsa.

Gabana ya sake faɗi ras! Ba tunanin komai na kawo ba sai tunanin Yallaɓai ko dai ya fara bin mata ne? To ni dai ban san wannan yarinyar ba sai yau amma shi a yanayin da ya nuna kamar ya jima da sanin ta. Sannan fuskarsa ta bayyana asirin zuciyarsa na yadda take da muhimmaci a wajen shi koda bai furta da fatar baki ba.

"Yallaɓai."

Na faɗa jikina na rawa tare da zuciyata ban san ma na sauke kafafuwana daga harɗe sun da na yi ba sai da na ji suna karkawa, tare da dukan junansu saboda tsoron tunanin da ya shige ni yanzu nan.

"Na'am."

Ya faɗa yana mai kallona fuskarsa ba alamun wani firgici ko nadama.

"Me ya faru?

Ya faɗa yana mai sake kure ni da ido, sai na ga kamar yana neman raina mini wayau bayan ya san abin da ya faru amma kuma yana sake kallona yana tambayata me ya faru?

"Wa ce ce Rabi' atu?

Na fada da sigar tambaya amma a rarrabe saboda fargaban amsan da zan ji ya faɗa mini. Ni fa cikina har curewa ya yi waje ɗaya nima ina jin kamar in na yi motsi zan iya barkewa da zawo saboda zullumi.

"Wata ce ba ki san ta ba."

Ya faɗa yana sauke rigar hannunsa a saman gado. Sai kuma ya saka hannu ya ɗauki wayarsa yana dubawa. Mirmishi yake yi alamun yana karanta saƙon nata ne. Ban san ina da wannan ƙarfin ba sai da na ganni tsaye kan ƙafafuwana lokaci ɗaya kuma na saka hannuna da ƙarfi na fizge wayar daga hannun shi.

"Wace ce Rabi'atu Yusuf ina tambayan ka kana faɗa mini wai ban santa ba. Wace ce wannan yarinyar ehe?

Na faɗa ina mai ɓoye wayar a bayana sannan cikin ɗaga murya nake maganar. Ni fa na gama tunanin kaf na haɗe shi waje ɗaya Yallaɓai ya fara neman mata a waje shi ya sa yanzu ba shi da lokacin mu. Innalillahi Wa'inna alaihirraju'un. Nake nanatawa a cikin zuciyata lokacin da na ga kawai ya kalle ni amma bai yi magana ba.

"Yusuf wace ce Rabi'atu? Kar dai a ce abin da zuciyata take zargi akan ka gaskiya ne?

Na faɗa ina jin zufa na taruwa a saman hancina tsabar tashin hankalin da nake ciki.

"Me zuciyarki ke tunani na a kaina Sadiya?

Ya faɗa hankalin shi a kwance har yana karya hannayensa a saman kirjinsa alamun bai damu da yanayin da na shiga ba.

"Yusuf neman mata ka fara yi? Mu har ka gama moran mu ka fara hango matan bariki?

"Subhanallah wannan mganar bai da ce ba Sadiya. Allah ya tsare ni da aikata ɓarna. Ban yi da ƙananun shekaru ba sai da girma ya kama ni Sadiya?

Ya faɗa a yanayin muryansa da ɗan bacin rai kaɗan. Domin har yana sauke hannuwan shi ya nufe ni da su yana faɗin.

"Taho mu zauna na yi miki bayani."

Da sauri na ja baya domin ni kawai idanuwana suna hango mini Yallaɓai wasa yake son yi da tunanina shi ya sa.

"Na saurare ka? Me za ka faɗa mini? Tun farko me ya sa da na tambayeka wace ce ita ba ka faɗa mini ba?

"To mun bar ɗakin nan ne kika ga ban faɗa miki ba? Da man ko ba ki gani ba ina da shirin sanar dake a kwanakin nam."

Sai kawai na saki baki ina kallon shi, a gefen gado ya zauna hankalin shi kwance.

"Na ce ki taho dai ki zauna mu yi magana."

Ya faɗa yana nuna mini gefen sa, sai na ɗauke kaina kafin na jijjiga jikina ina faɗin" In ba ka yi lalacewa kana matashin ka ba, yanzu da ka haɗu da yar iska yar bari.."

"Ya isa haka Sadiya."

Ya ɗaga mini murya sannan ya ƙara da ɗaga mini hannu abin da ya hana ni ƙarisa maganar da na ɗauko.

"Me ya sa kika kasa shaida na ne Sadiya? Ashe ba za ki iya rantsuwan a kan bayan ku da kuke gonakin da Ubangiji ya hallata mini ba, ba zan iya shinshinar gonar da ba mallakina ba ne? A she ni ba za ki iya mini wannan shaidar ba?

"Ɗan Adam mai sauyawa. Tun ballanta jinsin Namiji. Me ye kake ɓoye-ɓoyewa in ba wata yar bariki ka samu a waje tana ɗauke maka hankali ba?

Na katse shi nima ina taso masa sai kawai ya yi shuru amma ya kalleni yadda na firgice da zargina shi ya sa sai ya gyaɗa kai kafin ya ce" Ko dai mu jinsin maza muna sauyawa amma ba sauyawa ta wannan bangaren ba Sadiya. Ba maganar yar bariki kuma ki daina faɗa, ba ki san wace ce Rabi'atu ba, sabo da haka ki daina danganta da sunayen banza."

"Ƙarya na yi. Wace ce ita in ba yar bariki me bin mazan wasu a titi ba?

"Ba ita ce ke bi ni ba. Ni ne ke bin ta Sadiya."

Ya faɗa yana kallona. Kamar an iska ya wuce ta gefen kunnuwana haka na ji kamar sautin wani abu ya wuce. Shuru na yi ina kallon shi, shima ni yake kallo.

."Me ha kan ke nufi?

Na faɗa ina mai raba bakina saboda rawan da ya fara yi mini.

"Sadiya Rabi'atu ba karuwa ba ce sannan ba ƴar bariki ba. Yarinya ce da ta fito daga gidan tarbiya da dattako."

Ni fa duk ba nan na ke so ya je ba. Matsayinta a rayuwarsa na ke son sani.

"Ni na ganta na ce ina son ta."

Sai na yi ma Yallaɓai zuro kamar na warke makanta.

"Kuma AURANTA zan yi in sha Allahu "

Shike nan ƙurungus kan kusa. Ni gabaɗaya na sha'afa idanuwana sun rufe na manta cewa bayan biyu. Ubangiji ya ce su cike huɗu in har za su yi adalci, na sha'afa da cewa bayan mu akwai guraben mata biyu, tunanina da zuciyata kawai suna hasko mini Yallaɓai ya fara neman matan bariki saboda yana da kuɗi. Su kuma matan bariki da man in har kana da kuɗi shike nam za su tallata maka ƙofar lalacewa. Na manta yadda ya aure ni ya kuma auri Gimbiya. To watan wata rana in ya yi ra'ayi zai iya auro wata ko wasu ma biyu bayan mu. Na manta ko na ce ban ɗauka yanzu ba ne. Kamar yadda auran shi da Gimbiya ya shammace ni haka labarin wannan auren ma ya sake shammata na.

Na kasa motsi daga in da nake tsaye. Zuru kawai na yi ina bin Yallaɓai da kallo shi kuma ganin haka sai ya taso ya zo ya kamani ya zauna da ni a gefen gado sannan ya kuma ya zauna a gefen har yana dafa kafaɗata hannunsa na rito a wajen kirjina.

"Bayanin da nake so ki zauna na yi miki ne tun farko kika kasa zama ballanta ki fahimce ni."

Ya faɗa yana mai kallon fuskata. Nima shi nake kallo, na tuna ni ce nan na sha cika bakin cewa in Yallaɓai ya tashi kara aure ba zan damu ba domin ni ya gama yi mini kishiya, Gimbiya ce ke da wannan ƙuncin ba ni ba, ban tabbatar ma da kaina kishi sunan shi Kishi ba sai yau, domin sai na ji wannan ƙullutun abin da ya taɓa tsaya mini a ƙahon zuciya a daran da na samu labarin Yallaɓai ya auri Gimbiya. Irin shi ne na ji ya tokare mini zuciya. Ya yi sanadiyar rufe bakina da kassara sauran kuzarina.

"Ba ki ji komai ba Sadiya ta?

Ya faɗa yana leƙen fuskata. Kamar an ƙwato numfashina haka na ji na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan na kalli Yallabai. Sai ga ni jiki a sanyaye ina mai mikar masa wayar sa, ya saka hannu ya karɓa.

"Ka yi haƙuri ban san haka maganar take ba."

Na faɗa cikin sanyin murya. Sai na ji kwarmin idanuwana suna cika da kwallah. Sai ya fara dariya yana faɗin" Me ya faru? Ni ba ki yi mini laifin ba ni haƙuri ba na ji daɗi da kika zama mace ta farko da kika fahimci ina boye miki wani abu."

"Gimbiya ma ta sani."

Na faɗa ina kallon shi, sai ya kalle ni cikin mamaki. A hankali na warware mishi yadda muka yi da ita. Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Allah Sarki ƴan mata na. Ina son ku wallahi." Ai ni ko jin sa ban yi ina cam na tafi duniyar tunani. Aure. Aure fa Yallaɓai ya ce zai ƙara, in a da ina raba shi da kwana biyu ne yanzu fa sai dai kwana huɗu. Kai innalillahi.

Haka nake faɗa a ƙasan zuciyata. Gabaɗaya jikina ya yi sanyi kamar an yi mini duka.

"Da man lokaci na ke jira na same ki mu yi maganar nan. Wallahi tallahi ban da ke ko Nene da yan uwana ba su san da labarin Rabi'atu ba."

"Nima ai ban sani ba, ba ka faɗa mini ba sai da na gani da kaina."

Na faɗa kamar zan yi kuka sai ya rumgumo kafaɗata yana faɗin" Allah shi ne shaida na. Niyyata cikin satin nan na ke da niyyar faɗa miki, kin san ba ni da wata abokiyar shawara sama dake. Ni da ke mun kai wani matakin da ba zan iya ɓoye miki komai ba, da man na ce sai na yi magana da ke sannan zan je na yi magana da Nene."

"Uhm"

Kawai na faɗa domin na kasa magana ko na ce ba ni da ta cewa ne kwata kwata kamar an shafe manganganun dake cikin ƙwaƙwalwata.

"Da gaske na ke yi Sadiya ta "

Ya faɗa yana wasa da yatsun hannuna guda ɗaya da ya kama ya riƙe.

"Ko da gaske ne ni na isa na hana ka ƙara aure ne? Ai kamar yadda ka yi na farko ban iya hanawa ba wannan ma sai dai na sake yin maka fatan alheri."

"Na san baki isa ki hana ba. Amma ai kin isa na yi shawara da ke ko?

"Sabo da mene?

Na faɗa ina kallon shi.

"Saboda ke kin zama TURKEN GIDA na. Ban isa na zartar da wani hukunci ba tare da na nemi shawaran ki ba. Duk da ba ki isa ki hana ba amma kin isa ki nuna mini abin da nake ƙoƙarin yi in mai kyau ne ko akasa sa, Sadiya kina da wata daraja mai girma a zuciyata da na ke girmama manganganunki. Na ke kuma kambama tunanin ki a kaina. Na tabbata ke mai adalci ce mai kau da kai mai haƙuri da hangen nesa. Kamar yadda kika saba ba ni shawara da zuciya ɗaya yau ma ina da yaƙinin da zuciya daya zaki ba ni dukkan shawarwarin da na ke son samu daga gare ki"

Koda a ce daɗin baki ne na Maza to ni dai wallahi ya yi tasiri a kaina, har ban san ina ta mirmishi ba kaina ya yi girman da na ji ashe nima na isa a wajem mijina ban sani ba.

"Da gaske Yallaɓai na?

Na faɗa ina yi masa mirmishi duk da a ƙasan zuciyata nauyi na ke ji, amma bai hana daga can sama wata tsoka ta jin daɗi ta motsa mini ba.

"Haba. Kike tantama? Ke ce fa mafarin Yusuf, ke ce da shi a shekaranjiya da jiya har da yau. Bayan iyayena ke ce macen ta farko da zan nuna da ta yi ma rayuwata hidima. Ki sani ke ɗin ta musamman man ce a wajena. Anan ƙarƙashin nan na ke jin tarin hidimarki a gare ni "

Ya faɗa yana taɓa wajen zuciyarsa da hannuuwana da ya riƙe, sai gani kamar shashasha ina ta dariya da mirmishi.

"Na gode da Martabawa Yallaɓai."

"Nima da na gode da hidimantawa My Sady"

A tare muka kalli juna sannan muka yi mirmishi sai na faɗa jikinashi ya rumgumeni cikin rumfar hannayensa masu zame mini garkuwa a koda yaushe.

"Wata shawara kake buƙata daga gare ni?

Na faɗa ina kwance a saman ƙirjinsa. Sai ya dago ni muna kallon juna kafin ya riƙe dukka hannayena guda biyu ya fara faɗin.

"Rabi'atu yar maiduguri ce amma zama ya kawo ta nan Kano. Akwai Baffanta a nan garin ƙanin mahaifinta kenan bayan rasuwar mahaifinta shi ya karbeta ta dawo hannun shi tun tana JSS3. Ga shi yanzu har tana karatu anan BUK ajin ta ɗaya."

"Ina jin ka."

Na faɗa ina kallon Yallaɓai domin ganin yadda ya natsu kamar Nene ce a gaban shi ba ni ba.

"Mun fi wattani biyu da haɗuwa. Kuma ni dai yanzu ina matakin na gabatar da kaina a wajen Baban nata ne."

"A ina kuka haɗu?

Na samu kaina da yi masa wannan tambayar Saboda ni dai a sanina ba ruwan Yallaɓai da yan mata amma sai ga shi ya zaunar da ni yana ba ni labarin budurwa.

"A bakin BUK new site. Na je yi ma wani abokin karatun mu murna ya samu koyarwa a wajen shi ne bayan na fito na haɗu da ita tare da ƙawayenta su biyu."

"Sai ka rage musu hanya ko?

Na faɗa ina kallon shi sai ya fara dariya kafin ya ce" E. Ranar alhamis ne, daga cikin makaranta za su je gida Weekend. Sai na rage musu hanya na kai ƙawayenta gida itama na kai ta daga baya."

Sai na samu kaina da yin mirmishi kawai.

"Kuma suka yadda suka shiga motarka ba su san ka ba?

"Ni na yi ta bin su ina yi musu magiya."

Ya faɗa mini gaskiya da na ji da man ban tambaya ba. Da man bayan ni akwai wata macen da Yallaɓai zai iya yi ma magiya! Kin manta da Gimbiya? Wata zuciyar ta tunasar da ni.

"To kin ji yadda muka haɗu da Rabi'atu"

Sai na kalle shi, na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai ji daɗin faɗin sunan wata mace ba, sai ga shi a gabana yana kiran sunan wata macen cikin shauƙi da muradi.

"A hostel take zaune kenan?

"E. Can take zaune sai bayan sati uku take zuwa gida Wekeend"

"Can kake zuwa taɗi kenan?

"E to wani lokacin. Amma har gidansu ina zuwa."

"Can Maidugurui?

Sai ya zaro mini ido kafin ta ya ce" Gidan Babanta dake Kano dai, Maiduguri wataƙila sai mun je ɗaurin aure."

Sai na jinjina kai na ma kasa mgana. Yallaɓai ya riga ya gama tsara komai shi da yarinyar.

"Kana son ta ne haka sosai?

Sai ya fara sosa gira. Sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko ba ka faɗa ba labarin zuciyarka fuskarka ta bayyana mimi. To ita nata sonka kamar yadda kake son ta?

"Ofcourse. "

Sai muka kalli juna sai ya rage zumudin ya dan saussauta murya kafin ya ce" Na ce mata bana som auram ya wuce wata uku ta ce ta amince."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull