Turken gida book 3 cmplete - Chapter 36
Turken gida book 3 cmplete Chapter 36: Turken gida book 3 cmplete Chapter 36. To da mam za ta ki ne, me Yallabai ya rasa? In ba ya faɗa ba ba mai ganin sa…
3,318 words
To da mam za ta ki ne, me Yallabai ya rasa? In ba ya faɗa ba ba mai ganin sa ya ce ya kai shekaru arba'in da tara, yana nan a matashin sa, kamar ɗan shekara talatin da ɗoriya. Balle ga ƙudi ga rufin asiri ga iya gayu ga kalamai ta same shi me za ta tsaya jira ban da ta amince?
"Me kika ce?
"Me zan ce?
Na faɗa ina kallon shi.
"Kice koma me za ki ce"
"Ba abin da zence sai fatan alheri. Allah ya tabbatar Allah ya haɗe kawunan mu ya kauda da fitina."
"Amin Amin My Sady. Amma wattanin ukun ba matsala?
"Babu tun da ka shirya."
"Gida ne, kuma in ba su ƙarisa ba zan ce a gyara mata shashe ɗaya ta fara tarewa. In ya so bayan bikin in an gama gyara na ku ke da Daughter sai ku tare a lokaci ɗaya."
Sai na kalle shi kafin na ce" Kana ganin Matarka za ta amince?
"Me ya sa ba za ta amince ba? Ai ba cewa na yi ba za ku tare gabaɗaya ba. Kuma tun da kika amince itama za ta amince in sha Allahu."
Sai na samu kaina da cewa Allah ya sa. Ban ce ina son ganin hoton ta ba amma sai da ya nuna mini a cikin wayarsa.. Ba Yallaɓai da yake matsayin namiji ba har ni mace kyan yarinyar ya dake ni. Tabbas yar maiduguri ce fara ce tas ga gashi har gadon baya ga diri. Masha Allah hancin nan har baka, ga ta doguwa sai dai yarinya ce wannan ko za ta girmi Jidda da ƙadan ne.
"Ta yi kyau. Allah ya sanya alheri."
"Amin Amin. Itama na nuna mata hoton ki."
Ban yi magana ba sai dai ina ta kallon shi.
"Ta ce ganin ki ya fi jin ki."
Ya faɗa yana dariyan nishaɗi.
"A ina take jin labarina?
"A bakina mana. Ai ba za mu hadu mu rabu ba ta ji sunan Sadiyata a bakina ba."
Na yi zuru ina kallon Yallaɓai yana labarin budurwansa cikin nishaɗi.
"Ta ce duk yadda aka yi ina ji dake. Na ce sosai ma ko ita na faɗa mata in har tana so ta kama babbar fada to ta kama kafa dake domin har ni juyanj kike yi "
Ni kaina sai da na yi dariya kafin na ce" Kar ka jawo mini ta shigo da shirinta sabo da ni." "Haba. Ai Rabi'atu ba ruwanta."
"Uhm"
Na faɗa a ƙasan makoshi to wai ba ruwanta Yallaɓai da neman suna.
"Tana ce mini Yallaɓai na ce ta bari kada ki ji ta. Ko a ma'aikatana ba mai kirana da Yallaɓai sai dai Oga ko Injiniya saboda ba na jin daɗin sunan a bakin kowa sai a bakin ki."
"Ai sai na bar mata sunan. Ita ce amarya mu ai mun tsufa."
Na faɗa ina kallon shi hAr na fara tausayin Gimbiya. Domin rawan ƙafan da Yallaɓai zai yi a kan yarinyaa nan, sai ya ce bai yi komai a lokacin auran ta ba.
"Ta ce tana som sunan sai dai ku riƙa kirana ke da ita."
"A'a ni fa na bar mata sunan. Ai na ɗana ina laifi mun sha miya ita kuma yanzu take."
Yana wata dariya nishaɗi kafin ya ce" To ni kuma sai na koma wani suna a wajen ka?
"Ah sunan ka mana."
"Yusuf gatsal?
Ya faɗa yana waro mini ido sai na gyaɗa masa kai ina yar dariya.
"Tab. Ban yadda ba, sannan ban amince da wannan maganar ba. Sai ita ta sauya amma ni ba zan sauka daga kam mikamina ba "
Ni dai sai bin Yallaɓai nake yi da kallo ina jin abin a zuciyata. Yallaɓai na zaunar da ni yana ba ni labarin wata macen cikin jin daɗi da annushuwa. Da bakin shi yake faɗa mini yau na sun fita ne, ya je makaranta ya ɗauke ta sun je shooping daga nan suka biya restaurant suka ci abinci anan ne ya ci wani ferfesun kifi ya lalatamai ciki kwana ya yi yana gudawa. Sai da asuba na bashi sauran flajin ɗin da nake da shi ya samu ya sha guduwan ya tsaya amma har da ciwon ciki shi ya sa da safen bayan ya yi wanka ya fita ya ce zai fara tsaya ta asibiti a ba shi magani. Sannan ya biya makaranta su Baby kafin ya wuce office tun da ya ce mata zai shigo makarantan na su yau.
Har ya fita ya bar ni, ina cikin mamakin manganganunsa jiya, shi kenan kuma tun da ya faɗa mini sai ya samu kofa in dai yana gidana sai ya kawo sanadin da zai yi labarin Rabi'atu. Aikin sa kenan tana gaishe ni na ce ina amsawa, ban san yadda suka kare da ƴan uwan shi ba amma ni dai kawai ya ce mini ya yi magana da Nene, na san da man ba za ta hana shi ba shi ya sa ban matsa sai na ji amsarta ba. Ni dai ban yi taɗin da kowa ba ko su Munnira saboda na kasa iya sarrafa harshe wajen ba da labarin wai Yallaɓai zai ƙara auro zai auro yar yarinya ɗanya shakaf, mu kuma da man tafiya ta tafi jiya ba yau ba. Ko naƙi ko na so ba zan koma kamar Sadiya a jiya ba. Sai dai na koma Sadiya a yau har shekara arba'in da wani abu a duniya. Duk gyare-gyare na ban isa na koma kamar budurwa ko yarinya ba. Dole dai wajen ya saki tun da jiya ba yau ba ne. Itama Gimbiyar ni da ita duk samkal ne, tun da tsere yan mu a shekaru ba nisa sosai itama ai ta kama gidan arba'in. Tun da yana da kuɗi zai buƙaci canji yanayi.
Duk ƙoƙarina na kar ƙarim auran Yallaɓai ya dame ni na kasa. Abin ya tsaya mini a zuciya amma ina ƙoƙarin yakicewa saboda na zauna lafiya. Yallaɓai da bakinsa ya faɗa mini Kawu zai zo za su je su gabatar da kansu wajen baban Rabi'atu. Kuma ya zo sun je ɗin ya dawo yana faɗa mini ya yi musu karamcin amma ya ce su je zai neme su da kan shi. Yallaɓai rawan ƙafa kawai yake yi bai ƙi a ce gobe ma an ɗaura auran nan ba gyaran gida kam tuni ya tsaya bangaren da Rabi'atu za ta fara tarewa ma'aikata suka raja'a duk da namun ma fenti ne ya rage sai tayels da za a sanya amma ita bangarenta har tayels ɗin an saka kaɗan yarage a ƙarisa. Da bakinsa yake sanar da ni in ma an gama da wuri ba zai bari a saka lokacin bikin ya kai wattani uku ba.
Duk wannan bidirin da yake yi ban sam bai sanar da Gimbiya maganar da wuri ba. Na ɗauka yadda ya faɗa mini itama ya same ta sun yi magana ashe bai sanar da ita da wuri ba, ni kuma gani na yi ba hurumina ba ne shi ya sa ban yi azaɓarɓaɓin bakin kiranta in faɗa mata tun da ba ni ba ce mijinta. Kawai sai wayarta na samu kwana biyu tsakani da zuwan su Yallaɓai gaban Baban Rabi'atu.
"Maman Jidda kin manafunce ni."
Haka ta fara ce mini da na ɗauki wayarta da sallama.
"Ikon Allah. Munafuncin mene kuma?
Wataƙila kuka take yi domin tana ta jan hanci.
"Ba ki faɗa mini Daddy aure zai ƙara ba. Sai da kowa ya gama jin magana sannan ya faɗa mini."
"Ai ba hurumina ba ne na sanar da ke. Shi ya sa ma kika ji ban yi miki maganar ba."
Na amsa mata, gaskiya na faɗa mata ba bangarena ba ne.
"Amma ai mun yi magana da ke na ce ki bincika a bangarenki nima haka. Abin da muka sani mu faɗa ma juna me ya sa kika boye mini? Ahalin da bakin shi ya faɗa mini ke ya fara yi ma maganar kafin ma ya sanar da Nene?
Sai na saki baki kawai kamar tana ganina saboda na ga kamar tana neman ta ɗora mini jakar tsaba ne.
"Nima bai sanar da ni ba sai da na ga kiranta sannan na tambaye shi wace ce ya faɗa mini. Ki yi haƙuri in rashin faɗa mikin da ban yi ba ya yi miki ciwo. Na ga ba hurumina ba ne sanar dake shi ya sa"
"Wallahi Daddy bai isa ya auro wannan yarinyar ba. Anty Bahijja ta faɗa mini yarinya ce ƙarama kamar sa'ar Jidda shi ko kunya bai ji ba? Da me muka rage shi?
"Ta ɗan girme ma Jidda gaskiya."
Cikin mamaki a muryanta ta ce" Kin santa ne? "A'a ya dai nuna mini hoton ta na ganta. Kuma ya faɗa mini shekarunta."
Sai kawri Gimbiya ta yi wani jan numfashi kafin ta ce" Da man yana ta cika baki da cewa Ko a lokacin aurena ba ki bashi matsala ba wannan ma yana fsɗi da fahari ba za ki bashi matsala ba. " "To matsalan me? Ai ko na yi kishi da hauka ba shi zai saka ya fasa ba. Sai ma ni na zubar da ƙimata. Kema ina mai baki shawara ki yi haƙuri duk da akwai zafi amma in ka daure sai komai ya zo ya wuce."
"Tab. Wallahi ni ba zan yi munafunci saboda namiji ya so ni ba. Matsala kuma a wajena yanzu ya fara gani."
Kafim na na yi magana ta katse kiranta sai na bi wayar da kallo kafin na furta" Ikon Allah! In na fahinceta ni ce mai yin munafuncin saboda Yallaɓai ya so ni, sai da na yi mirmishi Gimbiya kenan, ni fa ba zan yi tashin hankali da faɗa saboda Yallaɓai zai ƙara aure ba, yadda ban yi a baya ba yanzu ma ba mai sskani na saka kaina a cikin damuwa. Na san ba zai fasa ba kuma a yadda Yallaɓai ke ji da yarinyar nan wallahi Gimbiya ta ce za ta bashi matsala to shi zai iya nesa da ita saboda ya samu masalahan na shi muradin. Tana tunanin ina yin haka ne saboda ya yabe ni, ba ta sanni ba ne ni fa ban yarda na zubarma da kaina ƙima saboda namiji ba, a je dai a dawo suna ne zai yi tambari na bar ma kaina da ƴaƴana abin kunya daga ƙarshe ya yi auran shi to wa gari ya waya? Shi ya sa na koma ga Allah ina faɗa masa damuwa da fatan ya cire mini damuwa da tunanin ƙarim auren da Yallaɓai zai yi. Kuma Alhamdulillah na fara ganin canji.
Yadda ko ƴan uwana ban yi zencen da kowa ba. Haka ƴaƴana kamar yadda ya sanar da su na auran Gimbiya wannan ma ya sanar da su da bakin shi. Jidda jarabawa ma suke yi jibi za su gama za ta dawo gida Baby kuma sun fara Jsce ta gama ajin ukun ƙaramar sakandiri. Duk ta buɗe tantanin budurci ya bayyanar mata. Wancan watan ta fara jinin al'ada gashi ta fi Jidda manyan gabbaina tun ba ta yi wani shekaru nanna sun cika mata ƙirji. Hankalina na mai da kan kula da tarbiyan yayana. Yallaɓai yanzu ba ma gaban shi hankalin shi da duka tunanin shi na kan yadda zai mallaki Rabi'atu ne shi ya sa nake yi masa uzuri.
Ni ko da muka yi magana da Gimbiya ban yi ma ko Yallaɓai zencen ba, nima bai nuna mini a yanayin da suke ciki ba. Shi ya sa nima ban tusa kaina a cikin abin da ba ruwana. Jidda ta gama jarabawa ta dawo gida sai gidan ya yi daɗi na rage kaɗaici, har Yumna yanzu ta fi karsasshin wasa da dawowar Jidda har uban gayyar ma ya yi murna da dawowarta yana faɗa mata gidan ba daɗi da ba ta nan. Ban san me ya faru ba kawai na ga Yallaɓai ya kwaso mini su Khalipa da Anwar, na tamnaye shi lafiya? Ya ce ba komai. Ina maman su? Ya ce mini ta je Rano ta dawo. Ni kuma har ga Allah ban kawo ma kaina tunanin matssla suka samu da zuciya ɗaya na karɓi yaram gidan sai ya zama active saboda ɗan hayaniyarsu in sun tafi makaranta Jidda da Baby suna gida, in sun dawo gidan ya sake rikicewa da wasannin su tun ballanta Yunma da Yallaɓai ya gama ɓata ta da mugun wasa.
Kwana uku tsakani ranar wata laraba Munnira ta kira ni a waya tace ko ina gida na ce mata ina gida. Sai ta ce mini gata nan zuwa, da maganar mu ba a daɗe ba sai ga ta tun da na ganta na san da magana. Na kuma san bai wuce labarin auran Yallaɓai da suka samu labari. A daran jiya yake faɗa mini Baban Rabi'a ya neme sa yau zai je su sake ganawa. Ina kuma da tabbacin ya gama binciken shi ne zai ce ya turo magabantan sa. Tun da Yallaɓai ba shi da abin ƙin daga asalin shi har rayuwarsa duk da ɗan adam tara yake bai gama cika goma ba.
"Kwana biyu ke da Hauwa kun ɓoye?
Na faɗa lokacin da na shigo falon, da man ina cikin bedroom ɗinna Jidda ta sanar da ni zuwanta.
"Wallahi ya gida?
Ta faɗa tana ɗaukan ruwan da Jidda ta kawo mata na gora ta zuba a kofi ta fara sha sai ni kuma na zauna gefenta ina faɗin" Ya yara? Kwana biyu ba mu haɗu ba."
Sai da ta gama shan ruwa ta dire kofin a saman centetr table ɗin dake falon sannan ta ce" Uhm ke ce ai kin ɓuya. Yanzu ma dalili ne ya sa na neme ki."
"Wai auran Yallaɓai?
Na faɗa ina dariya.
"Au ashe ma kin san abin da ya kawo ni."
Ina mata murmishi na ce" Na san dai yanzu shi ke trending."
"Uhm wai ashe Yallaɓai aure zai ƙara ba ki sanar da mu ba Sadiya?
"Wallahi na kasa iya faɗa ma kowa. Amma na bari in an saka ranar sai na kira ku mu yi maganar."
"Da gasken gasken dai auren zai ƙara?
Ta faɗa cikin tantama.
"Ya wuce wai fa. Yau ma yace mini zai sake komawa Baban Rabi'atun ya sake neman shi."
Na faɗa ina kallonta.
"Sunanta kenan? Rabi'atu?
"E. Yar maiduguri ce amma an riƙeta anan Kano. Yarinya ce ƙarama ajinta ɗaya ma jami'a."
"Duk a ina kika san wannan labarin?
"A ina kuwa? A bakin uban gayyae mana."
Na faɗa ina dariya sai Munnira ta gyara zama tana faɗin" Ba Shakka." Sai kuma ta yi shuru. "Ke a ina kika ji? Na tabbata dai maganar ba ta fita ba sosai."
"A bakin Jamila na fara ji, sannan jiya da daddare labari ya kawo labari Nasir ke faɗa mini. Ashe wai har sun samu matsala da mutuniyarki?
"Wac ce?
"Gumbiya mana."
Sai na ware ido kafin na ce" Subhanallah da shi Yallaɓan? Munnira ta yi dariyan mugunta kafin ta ce" Wai ita ana dole ba zai yi mata kishiya ba. Ta manta ke ma da ita aka yi miki kishiyar? Wanzami ba ya son jarfa"
"Me ya faru ne! Ni wallahi ban sani ba. Na ga dai ya kwaso mini yara ya kawo mini da na yi magama sai ya ce bata nan ta je Rano."
"Af yaji ta yi "
"Yaji?
Na faɗa ina zaro ido.
"Wallahi faɗa suka yi a yadda Nasir ya ce shi Ya Tafidan ya faɗa massa. Tun da ya faɗa mata zai ƙara aure ba su samu fahintar juna da zaman lafiya ba ranar kawai ta saci wayarsa ta dauki lambar yarinyar ta kirata ta yi mata zagin kare dangi. Ashe yarinya yar gari ce ta yi recording yana zuwa ta kunna masa shi kuma da ya dawo sai ya hau ta faɗa shi ne ta miƙe yana faɗa tana faɗa daga ƙarshe zai bar mata ɗakin ya ce ta ja masa riga har tana yaga masa, ta kuma ci kwalan shi ta ce in dai ya rantse sai ya yi auren nan da wannan yarinya ita kuma sai ya sake ta. A cewar sa ya yi ta ƙi sakin shi sai ya fizge kan shi ya ture ta gefe ta faɗi shine ta hau kuka wai ya daketa akan wata banza gari na wayewa ta tafi Rano har yau ba ta dawo ba shi kuma ya ce ba zai je ya yi bikonta ba tun da abin da ta yi rashin tunani ne."
Tagumi kawai na yi na ma kasa magana. Sai da na ce mata ta bi a hankali. Amma sai take ganin kamar ni ina goyon bayan Yallaɓai ne.
"Na je Gwammaja jiya har Nene ba ta saka baki a maganar ba ta ce Gimbiyar ce ba ta kyauta ba.. aure ya ce zai ƙara ba wani zunibi ba"
"Ina su Anty Bahijja?
"Ohom musu. A bakin Suwaiba na ke jin Mimiaco ce kawai da Nene ke bayan Tafida. Anty Maimuma da Anty Bahijja duk yan bayan Gimbiya ne kar a yi mata kishiya."
Ban san ina dariya ba sai da na ga ina ƙyaƙyatawa.
"Wato kar a yi mata kishiya tuj da ta su ce? Ni da bare ce ai suna gaba gaba wajen ba shi goyon bayan ni ya yi mini ko?
"To da man. Ai ni farinciki na yi da zencen ƙarin auren na. Lokaci ya yi da Gimbiya za ta ɗanɗana abin da kika ɗanɗana ta ji in da daɗi."
"Wallahi. Welcome to the Game."
Na faɗa ina dariya har muna tafaww. Ba wai ina murna ba ne amma dai na ji daɗi a kallah dai za su san cewa yau gare ka ne gobe ga wanin ka jibi ma a kanka ne zai faru.
Muna tare da Munnira har bayan la'asar sanman ta tafi, Yallaɓai da wuri ya dawo ya yi wanka aka saka manya kaya ana ƙamshi ya tafi. Tun kafin ya dawo ya kirani a waya da albishir ɗin Baban Rabi'atu ya ba shi da man ya tura magabantan shi. Murna kamar Yallaɓai zai yi hauka da ya dawo haka ya rumgumeni cak kuma ya ɗagani yana juyi da ni a tsakiyar falo gaban yara. Ni dai na daki kafadan shi ina faɗin ya sauke ni. Ai na ga abin mamaki haka ya bi su Jidda ɗaya bayan ɗaya yana rumgumansu cikin farinciki.
"Abba me ya faru ne? Ko ka samu wasu kudaɗe ne?
Jidda ta faɗa tana dariya.
"Abin da na samu ya fi kuɗi daraja My Jidda. Ƙaramar Anty zan sake kawo muku."
Daga ita har Baby shuru suka yi kamar ba su gane ba.
"Jidda Baby, aure zan ƙara. Baban Antynku ne ya ce na turo da magabatana."
"Allah ya sanya alheri Abba"
Jidda ta faɗa cikin natsuwa its ko mara kai Baby sai ta fara tsalle tana faɗin" Abba yaushe bikin? "Ba zai ɗau lokaci ba? Ya faɗa yana shafa kanta falona ya kaure da ihun su har da su Khalipa da ba su san me ake ciki ba. Yumna ya ɗaga sama yana mata wasa kafin ya kalleni yana faɗin" Rabi'atu ta ce ita fa Yumna za ki ba ta." "Ba dai uwata ba kam! Na faɗa da iya gaskiyata sai ya fara dariya.
"Jidda zaki ba ta ko Baby?
"Jidda ai ɗiyar Gimbiya ne. sai dai ko Baby ko Khalipa."
"Ta fi son mace ta ce mini. Kin san tana ganin hotin su a wayata. Ita dai Yumna take so."
Ni tsabar mf zumuɗin Yallabai ya sa ban samu amsa masa ba. Abinci ma bai ci ya ce ya ci a can wai an kawo Baba ya ce sai ya ci shi kuma ya kasa yi masa gardama su Baba manya. Ina so na yi maganar Gimbiya ina jin tsoro kar ya ce na yi shisshigi, ganin yana cikin farinciki yasa na yi kumdunbala na yi masa maganar amma sai ya shashantar da maganar da cewa na ƙyaleta za ta dawo.
"To ko za ka je ka dawo da ita ne? Ka yi mata uzuri kishiya fa zaka yi mata?
Kawai ya taso mini kamar ni cw na yi masa laifin