Turken gida book 3 cmplete - Chapter 45
Turken gida book 3 cmplete Chapter 45: Turken gida book 3 cmplete Chapter 45. Sai ya fara dariya wanka ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi'atu…
3,366 words
Sai ya fara dariya wanka ya yi bangarena ya shirya. Ya ce zai sauke Rabi'atu a makaramta zai wuce office tun ɗazu Musbsbu ke kiran shi akwai waɗanda ke jiran shi na yi masa fatan dawowa lafiya. Bayan fitan su na rana na leƙa Gimbiya ta sha dai kuka amma dai an warware kaya. Ni dai na sake jadadda mata ta yi haƙuri in tana so ta zauna lafiya. Ranar girki ma duk Baby ta yi mana itama nan shashena ta ci abinci muna tare da ita har dare sannan ta kwashi yaran ta suka koma bangarenta. A ranar Yallaɓai ys ƙarishe kwanan shi a ɗakin Rabi'atu washegari ya dawo ɗakina ya yi kwana biyu sannan ya koma na Gimbiya. Ni ban san halin da suke ciki ba na ɗauka komai ya daidaita ashe ba haka ba ne, Yallaɓai dai na kwana a bangaren Gimbiya in ranar girkinta ya zagayo shima a falo kuma baya jin abincinta baya mgana da ita daga gaisuwa sai gaisuwa. Ni ban sani ba sai da ta zo tana kuka tana faɗa mini na ce ta sake bashi haƙuri amma duk da haka bayan kwana biyu ta dawo ta ce mini ba abin da ya sauya.
Jin haka da zuciya daya na ce zan yi masa mgana amma in ɗauko magamar yadda ya fara yi mini ihu a saman kaina ne na san cewa Gimbiya ta gama ɓata ma Yallaɓai rai ya gama jin haushinta shi ya sa kallonta kawai yake yi.
"To tun da ta baka hakuri ka haƙura mana? Shi kenan ita ba za ta yi kuskure ka ba ta da mar gyarawa ba?
Kawai sai Yallaɓai ya ce tun da ni ce Nene na yi masa faɗa saboda na ce abin da yake yi bai kyauta ba Allah zai kama shi.
"Ki bari Ubangijin nawa ya kamani amma ba ke ba."
Zan sake magana ya ɗaga mini hannu.
"In kika sake tare ni da mganar da ta shafi Gimbiya wallahi zan kai ƙaran ki wajen Allah. Haba kin dame ni? Kin fi sanin abin da ya kamata ne? Ko sai na ce Allah ya isa ne sannan za ki ƙyaleni da wannan mganar ne?
"Allah ya ba ka haƙuri. In sha Allahu ba zan ƙara mgana bam"
"Better for you."
Tun da ya yi mini haka na koma gefe itama Gimbiyar na faɗa mata tun da ta bashi hakuri ya ƙi haƙura ta fita batun shi in ya gaji zai seuko da kansa na faɗa mata nima irin tijaran da ya yi mini daga faɗan gaskiya. Gaskiya ne yanzu Yallaɓai ya zama masifaffe abu kaɗan sai ya fara faɗa yana yi ma mutane ihu. Maganar gaskiya Gimbiya ta ba ni tausayi duk ta rame ta saka ma kanta damuwa kuma Mimisco washegarin ranar da ta zo ta saka aka zo aka tafi da mota aka aka gyaro ta dawo kamar sabuwa. Kamar ma wani abu bai same ta ba Yallaɓai da kan shi yake sake koya ma Rabi'atu mota duk da iya amma hannunta bai faɗa ba, sannan abin da na ɗan fahimta Rabi'atu ta fara raina Gimbiya ba ta jin kunyar kallonta cikin ido kuma ba ta jin kunyarta kamar farko domin akwai rana tana shashena Gimbiyar ta shigo wallahi ba ta gaisheta ba sai da na yi mata mgana. Da man abin da na kr gudu kenan yarinyar nan ta zo ta fara raina ta, ba ta da yadda ta iya.
Ban san ta in da mganar abin da ya faru ya zaga dangin su Yallaɓai ba. Amma na fi tunanin Gimbiyar ce ba ta dandara ba ta fidda mganar. Sai ga Munnira ta kirani tana ba ni labarin jiya ta je Gwamnaja Anty Bahijja tana ta masifan wai Gimbiya mahaukaciya ce za ta jama Tafida asara ita sun lura kishinta na hauka ne da man shima ina ta jiye ma Gimbiya kar ta kai wannan lokacin sai ga shi da kanta ta zo har falona tana kuka tana faɗa mini Anty Bahijja ta je ta same ta a shago sai abin ta manta ba ta faɗa mata. Wai har tana cewa in haukan ta ya tashi ya tsaya a kanta kar ta sake gigin taɓa kayan Tafida tun da ita ba ta da hankali.
"Allah ya kyauta amma ni na san irin wannan ranar za ta zo"
Haƙuri na yi ta bata tun da ni kam ba ni da yadda zan yi da su Anty Bahijja nima ai haƙuri na ke yi da su. Na ji daɗi dai Gimbiya ta fahimci duk da tana na su akwai wani wajen da za su iya nuna mata Tafida ne ya fi kusa da su kuma tun ba a je ko'ina ba ta fara ganin haka har kuma lokacin Yallaɓai bai sauko ba ni na ba ta shawara ta kira Baba Tafida ta faɗa masa komai shi ya tako har gidanmu ya hada su ya yi musu sulhi mu ma ya tara mu ya yi mana faɗa. Dalilin zuwam Baba Tafida ys sa Yallaɓai ya sauko ya dawo yana sauraran Gimbiya amma ta ɓarar da alfarmanta mai yawa a wajen Yallaɓai motar da ta gama faɗa a kanta tana ji tana gani Rabi'atu ke hawa motarta tana zuwa makaranta, tana kuma shiga gari da abin ta amma ita miji ke jin haushi har Rabi'atu tana ɗaukan Gimbiya a mai yi mata hassada tun da na san za ta faɗa ma dangin ta kuma kowa da maganar da zai kawo mata Balle na ga tana da ƙawaye suna biyo ta gidan ni dai ba ruwana nawa ido ne tun da mijinta bai hanata tarkacen ƙawaye ni a wa? Iyaka dai in sun zo za ta kawo su har bangarena su gaisheni abinci ma ni nake ba su wani lokacin tun da in dai tana makaranta ni ke dafa abinci da ita ba kuma wanda ya sakani ni na saka kaina ganin wata rana sai yamma take dawowa ta gaji ba za iya wani girki ba shi ys sa nake yi dafa abincin da ita. Mota kuma Yallaɓai ya ce bai siya ba in Gimbiya ta isa faɗan ya sa ya siya. Na ce ta yi shuru ta ƙyale shi, sai yanzu ne Gimbiya ke son dawowa jikina ta makara amma duk da haks ban gwasale ta ba. Ina ba ta shawara kamar yadda zan ba ma kaina kums ni daga ita har Rabi'atu daya na ɗauke su.
*****
Mun yi azumin watan Ramadana mun yi salla. Jidda ta dawo gida salla amma ana fice sallata koma saboda za su fara jarabawa. A bayan salla muka muka yi auran Anti yar wajen Ya Murja Kaduna muka kai ta muna gama nata muka faɗa ma Firdausin Ya Balki. Ita kuma Funtua muka kaita auran gida babanta ya yi mata. Duk fa mun zama iyaye girms ya kams mu tun da mun aurar mun kai ga jikoki ma. An saka ma zainab ƙanwar Ma'u rana itama dangin mahaifinta a can kura ne za su aurar da ita ga ɗan katsina. Lokacin da muka yi sha'anin Rabi'atu ba ta nan ta tafi Maiduguri ganin gida, Gimbiya ce kawai ta zo mini biki da ƙannenta har da Maryama da muka taba samun matsala. Yanzu sai gaisuwar mutumci ina anfanin to rigima? Har su Munnira duk na ce su saki tun da itama ta saki a cewar Munnira wai da ta ga uwar bari ba, domin abin mamako har su Anty Bahijja yanzu Rabi'atu na zuwa gidajensu lafiya lau kamar ba su ne masu taya Gimbiya a dawa ba.
Da ta dawo daga maiduguri tazo da tsaraba ba wamda ba ta ba shi ba, ni kaina turaren wuta har ina kyautar shi.Yarinyar an yi mata huɗuban kyauta yadda za ta siye kowa to haka take yi ko Gwammaja za mu je ba za ta zuwa hannu rabbana sai ta riƙe ma su Nene wani abun. Cikin lokaci kaɗan Rabi'atu ta yi farimjini a dangin Yallaɓai wai har Anty Bahijja wata rana a ɗakin Nene mun je gaisheta ni da Gimbiya da yara ta zauna tana yabon Rabi'atu tana faɗin yarinyar akwai hankali sai daga baya ta yi ma Tafida uziri shi ya ga abin da ya gani. Har Nene yabon ta take yi in ta zo gida nan ta yi wannan ta yi wannan har kunshin su na yan maiduguri take zuwa na musamman ta ƙun sa ma Nene a kafa da hannuwana duk wani abinci da ta san Nene na so in za mu je za ts yi ta je mata da shi, wani abun ma ni ke faɗa mata. Mimisco da man ba ruwanta ko ita tafaɗa ta ce Yarinyar nan tana da wayau ta san dubarun zaman duniya. Kuma ita ba ta ware kowa ba, kowa na ta ne, har su Suwaiba haka take girmama su shi ys sa cikin lokaci kalilan kowa ya san Rabi'atu har mazan fa in suka zo gidan haka za ta yi ta musu rawan jiki. Yallaɓai ko sai jin daɗi yake yi yana fahari Gimbiya ko sai kuka da nadama ba ta da yadda za ta yi ƙaramar yarinya ta zo ta sha gabanta.
Muna gidan Halima za ta zo ba ta shiga shashen Gimbiya ba ta yini a bangaren Rabi'atu ba abin da ba ta bata in dai ta gani ta ce tana so za ta ce ta ɗauka. Ni dai ta so ta sake shigowa jikina na ce nahi. Ai kin ci taliyar ƙarshe amma dai muna gaisawa sannan in ta zo gidan tana shigowa mu gaisa ni ce ba na sakar mata. Da baffan Rabi'atu ya je makka shi da Antyn ta, Har Nene da su Maman farko sun samu tsaraba Yallaɓai Jallabiya da Darduma da casbaha da dabino da ruwan zam+zam. Ni kaina an siyo mini abaya yara ma kowa da na shi har Jidda dake makaranta Gimbiya ma ta samu abaya. Ni kaina wayon yarinya na ba ni mamaki sumu sumu da ita ashe ta san abin da take yi.
Su Anty Bahijja ko duk an bi su da dabino da ruwan zam-zam suna ta taɗin suna jin daɗi. Ni dai ban damu ba da duk abin da take yi ba lokacin ta ne ta yi wata rana ba za ta yi ba mu kan mu ai duk mun yi wannan bin a farko muka gaji muka haƙura Gimbiya ce ke damuna kuma na faɗa mata ta yi haƙuri amma fa ba ta da yadda ta iya da Rabi'atu. Wacce ko zazzaɓi Nene ta yi kaf yan gidan su sun zo duba ta. Na cen maiduguri su kira waya me ya sa Yallaɓai ba zo so ta ba?
Nan da ya samu hatsari Allah dai ya tsare buguwa ya yi a hannu sai gocewa a ƙafa haka suke tururuwan zuwa duba shi danginta na nan Kano na can ko suna ta kiran waya. Kamar ta goya Yallaɓai haka take ki da shi, biyayya take yi masa ko abi za ta ba shi sai ta rusuna ni fa ina gefe ne amma ni kaina na san yarinyar nan bariki kawai take gwada mana. Ni kaina zuciyata na motsawa ballanta Gimbiya? Ga shi kaumar yaran mu take yi kamar ita ta haife su an ce mai ɗa wawa. Har ta su Khalipa yanzu in dai tana gida suna bangarenta ita kenan ba su abubuwa suna ciye-ciye an ce mai ɗa wawa Yallabai gani ya ke yi a kan Rabi'atu xai iya faɗa da kowa. In Jidda za ta koma makaranta ba ta zaune ba ta tsaye sai ta ga ta koma ita ce kawo mata wancan ta ya ta wancan kuma duk ya gani kuma wallahi hakan yana tasiri. Baby ko daman ta zam yar ɗakin ta ko gidansu muka je wani abu ya faru ita da danginta kamar si goya mu. Itama in ta shiga damu dangin haka za ta daraja su. Maganar gaskiya sai dai ƙin gaskiya amma Rabi'atu tana da hallaya mai kyau. Ta bakin Gimbiya ta kan ce an yi ma Yallaɓai surkullrn yan maiduguri ya ruɗe kan yarinya na kan yi dariya na ce ba surkulle sannu ciwon kai ne kawai.
Mun yi babbar salla Rabi'atu ba lafiya ashe ciki ne. Yallaɓai kamar bai taɓa haihuwa ba Gimbiya baƙuwa a harkan mu ai mun zama yan gari. Haka yake kiran waya yana faɗa ma mutane Rabi'atu na da ciki. Tarewa gabada ya yi a bamgarenta yana kula da ita tun da laulayi take yi mai zafi, Ni ko duk abin da yake so a yi masa ni zai kira itama in tana son wani Umma kaza Umma kaza, na roƙi Allah ya cire mini kishin nan na hauka shi ya sa da ni ake renon cikin Gimbiya ko sai dai kuka a ɓoye in ta yi magana cibi ya zama ƙari lokacin da ya tare a bangaren ta yi magana da cewa ai muna gida ɗaya ba sai ya tare a wajemta ne zai kula da ita ba buɗe bakin Yallaɓai sei cewa ya yi ya tare ɗin sai ta hana shi ganin ya harzuƙa ya sa na shiga tsakani na lallaɓa shi ita kuma Gimbiya na ce mata ta yi bamza da shi duk abin shi dai ba zai dauwama a wajen ta ba.
Gimbiya faɗa mini take yi ba za ta iya jarumta na ba. Ba za ta iya juran ganin Yallaɓai na rawan jiki akan wata na da ciki ba. Na ce gwara ma ta saba domin yanzu aka fara. Wataƙila bayan Rabi'atu ma ya ƙaro wata itama ta zo tana gasar haihuwar to ya za ka yi in ba ka yi haƙuri ba?
*Janafty*
*TKG320B*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani. 09069067488 +234 706 234 9732
Rawan jiki da ɓare-ɓare kam Yallaɓai na yin shi a kan cikin Rabi'atu ga shi cikin na ta ya zo da laulayi ga shi ba ta son cin abinci in ku ka ga yadda Yallaɓai ke lalacewa a gaban yarinyar sai kun yi mamaki. Ni kuma duk abin da ta ce tana so haka zai marairace yana roƙo na domin na samar mata, ni kuma tausayi take ba ni ko bakomai nima uwa ce, wani lokacin kuma Baby yake sawa dafe-dafe nan Gimbiya dai ya san ko giwan wake ya sha ba zai tunkareta ba domin ba ma yi za ta yi ba iyakarta da Rabi'atu sannu Allah ya ƙara lafiya.
Kwanciyarta asibiti biyu sannan ta ɗan samu kanta sai da ta koma gida ta yi satuttuka. Antynta ta ɗauke ta ganin wahalan da take sha, Yallaɓai ya so ya hana na dakatar da shi da cewa ya barta a gidansu a kula da ita. Ya bari ɗin amma fa can yake tarewa in ya dawo daga aiki sannan ya dawo gida ya zaunar da ni yana bani labarin in na ga Rabi'atu sai na yi mata kuka ta rame kaza kaza, ni har gajiya na ke yi kamar a kanta aka fara samun ciki su 'ƴaƴan gidan ba a gaban sa aka samu cikinsu ba daga sama ya gan su, duk dauriyata sai da ya riƙa motsa mini zuciya. Tana gidansu sau biyu yana sakani muna zuwa duba ta ni da yara Gimbiya dai an tashi zuwa sai ta ce ba ta da lafiya duk da ya san ƙaryanta ne ba ya matsa mata sai ni. Ni dai na yi sakacin da gabaɗaya Yallaɓai ya gama raina ni in dai akan lamarin matansa ne ko abu ne ba zai tunkari Gimbiya ba sai ni. Saboda ina yi masa kara shi kuma hakan sai ya bashi damar ya rika cin ko wata kasuwa a saman kaina , yanzu kuma lokaci ya kure mini na yi sakacin da ba zan gyara komai ba tun farko da ban bashi fuska zan iya ɗauka ba da wataƙila nima zai shakkar tunkarata da sha'anin matarsa kamar yadda ya ke jin shakkar tunkaran Gimbiya.
Ba ni kaɗai ba dangin shi ma sun ta sintirin zuwa duba ta zuwan mu na ƙarshe can na ga Halima ta yi baje-baje kamar a falon Nene ban yi mamaki tun fa yanzu ai Rabi'atu uwar ɗakin ta ce. Gimbiya ta ɗauka bayan ita ba wata macen da Yallaɓai da dangin sa za su yi ma rawan jiki saboda samun ciki sai ta ga ma suna abin da ya fi wanda suka yi mata a baya. Sai ta sha mamaki domin tun cikin na ƙaramin sa Yallaɓai ya gama tsara in mace ne ga sunan da zai saka Aisha in namiji ne kuma Alhajinmu zai yi ma takwara zai yi zai yi kaza har na haddace su a kaina.
Gimbiya ta yi ta ƙunci in an yi wani abu da ya bata haushi ta same ni da mganar na gani ko? Na ce na gani mana amma ban nuna na ji ko na gani ba itama in ta yi haka sai ta zauna lafiya. Amma ba ta ji shawarata ba kafin Rabi'atu ta dawo gida sai da suka yi tsiya akan ranar girkinta yana kai wa dare a can. Ta ga fa nima har ranar da yake ɗakina abin da yake yi kenan amma ta na gani ban ma na nuna na gane abin da yake yi ba, amma ita da shegen kishi ta yi masa mgana har tana saka ni a ciki wai na faɗa masa gaskiya ba ya adalci tunda yana jin mgana ta.
"Tana gidan nan ma rashin adalci yake yi mana Maman Jidda. Ba ta gidan ma ba zai daina ba."
Ina zaman zamana a bangarena ta kira ni a waya sha ɗaya saura na dare. Na ji dawowarsa ba daɗewa ni na ma ɗauka wani abu ne ya same shi amma sai na iske shi zaune fuskar nan kamar hadari ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a saman kujera yana karkaɗawa alamun yau fa akwai masifa in Gimbiya ta cigaba da zungurin sa.
Kallonta na yi, Baiwar Allah ta yi masa kwalliya da fa zafi ka zauna jiran miji har sai ka siƙe sannan zai dawo. Amma yanzu in na ce bai kyauta ba daga ni har ita zai iya cewa mu bar masa a gidansa a yadda dai yake zaman taƙama nan yana kaɗa kafa ji yake yi yana daidai da koma wacece.
"Fisabillahi yana kyautawa? Sai ya je ya shantake? Tun ƙarfe nawa na gama shirina ina jiran shi? Ni ban hana shi zuwa ba amma sai ya yi abin na shi da tunani a ciki.'
"Ok wato kina so ki ce ba ni da tunani ko Saudatu?
Ya faɗa yana daga zaune, a ɗan kuma fusace domin ni fa na daɗe ban ji yana kiran ta da Daughter da ya saba ba itama tuni Daddy ya kama kan shi Babansu Jidda ne ko Abban Khalipa.
"Ni ban ce ba amma dai na ce ba ka yin tunani in za ka yi wani abu."
Kawai sai ya yi wani mirmishi na san in ya tashi magana ba zai faɗi mai daɗi ba ita kuma ta harzuƙa za a iya yin abu mara kyau.
"To ke kiyi haƙuri don Allah. Zuwa gobe in hankula sun kwanta cikin tsanaki sai ki nuna masa in da bai yi daidai ba sai ya gyara."
"Ba zan gyara ba."
Ya katseni a fusace na yi jage ina kallon shi sai kawai ya miƙe kamar zaki ya fara nuna Gimbiya da yatsa kafin ya ce" Ke wai me ya sa kin raina ni ne! Komai abin kishi ne a wajen ki? Rabi'atu ba ta da lafiya na je gidansu na dubata na shigo kin yi tunanin ki ce mini ya mai jiki.? Matata ce fa ke kuma y'ar uwan ki ce fa?
"Aa ni wallahi ba yar uwata ba ce. Ta tsaya iya dai matsayin matarka dai."