Turken gida book 3 cmplete - Chapter 46
Turken gida book 3 cmplete Chapter 46: Turken gida book 3 cmplete Chapter 46. Ta faɗa har tana ɗaga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da…
3,338 words
Ta faɗa har tana ɗaga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da faɗin"Ok yanzu na ma gano ki. Duk wannan ihun da kike yi cikin ne baki so ta samu ba ko? Ta buɗe baki za ta yi mgana ya hanata ya ɗaga mata hannu yana cigaba da faɗin" Ba sai kin yi magana ba na gano ki baƙinciki ne da hassada dankare a zuciyarki. To bari ki ji na faɗa miki haihuwa yanzu Rabi'atu ta fara sai dai ki mutu wallahi"
"Haba Yallaɓai."
Na faɗa saboda na ga kalaman na shi sun yi tsauri amma sai ya juyo ya balla mini harara kafin ya ce" Ki yi mini shuru kema ai zan iso kan ki." "Topha" Na faɗa a zuciyata me kuma na yi? Gimbiya ta ba ni tausayi ta jawo ma kanta cin mutumci Yallaɓai haka yake ta jifanta da manganganu wai ita kaɗai ce matarsa! Ni me ya sa ban taɓa masa ƙorafi ba sai ita daga dawowarsa ta san abubuwan da suka faru da shi yau? Ta san wani hali ya yini a ciki ba tarba ba kalamai ma su daɗi kawai ta zaunar da shi tana challanging ɗin sa a kan mganar banza! To wallahi in ya ga dama sai ya kwana a duk in da ya ga dama kuma ba wacce ta isa ta hana shi.
"Allah ya ba ka sa'a ka koma gidan su Rabi'atu a ba ku ɗaki sai ka riƙa kwana "
Gimbiya ta faɗa tana tsane hawayen baƙin ciki. Ba ita ba ni kaina wallahi na ji zafin mganganunsa haba wai kamar Yallaɓai ya fara haukacewa. Ni ina ta tsoro ma kar su Khalipa su ta so.
"Ina ruwan ki? In ma a hotel zan ɗauke ta mu je mu kwana wannan duk ba damuwarki ba ce. Matata ce."
Da na so ba zan ƙara mgana ba amma ganin lamarin ya fara lalacewa shi ya sa na sake mgana.
"Don Allah Yallaɓai ka yi haƙiru ke ma Gimbiya ki yi hakuri ku bar mganar nan. Dare ne kar ku ta shi su Khalipa."
Ita dai Gimbiyar ta yi shuru tana ta jan majinar kuka shi ko uban gayyar komawa ya yi ya zauna yana huci shi kaɗai da man ina tsaye ne ban zauna ba sai na ce" Sai da safe" "Dawo nan kema" Ya kira ni a ɗan zafafe, ni fa ban san me na yi masa ba amma na fahimci ba mganar Gimbiya ba da man yau a fusace ya shigo ita kuma kishi ya rufe mata ido ba ta gane ba ta je ta taɓo shi.
"Na'am kana kirana ne?
Wajen zama ya nuna mini a kujeran da ke gefen shi ta zaman mutum ɗaya sai na zauna ina jiran na ji ni kuma me za a sauke mini?
Gimbiya ya kallah kafin ya ce" Da kika kira Sadiya ita ɗin uwa ce ita! ? Daga ni har Gimbiya sai da muka kalli juna sannan muka dawo muna kallon shi saboda mamaki.
"Zugwai-zigwai kin ɗaga waya kin kirata na ce ita din Nene ce?
Dukkan mu mun kasa mgana daga ni har ita saboda ba mu da abin cewa.
"Sadiya ke aurena ko ni nake auran ta? Ni ne shugaba a gidan nan a cikin ku ba wacce ta isa na faɗa muku."
"Ikon Allah"
Na iya faɗa a saman leɓena kamar an turo fa Yallaɓai.
"Kar ki ƙara mini wannan sakarci muna mgana ki je ki kira mini wata wallahi in kika ƙara ranki sai ya ɓaci na ma faɗa miki."
Ya faɗa yana nuna Gimbiya da yatsa, ni ta kalla sai na gyaɗa mata kai alamun ta ba shi haƙuri.
"Ka yi haƙuri."
Ko sauraranta bai yi ba ya juyo kaina ai ni na yi suman zaune tun da yau Yallaɓai ya ke kirana da wata ai na san kuma sai abin da ya manta.
"Ke kuma ki daina ganin ina jin mganarki ki ɗauka ko wani abu na rayuwata sai kin shiga. Ba ruwan ki da tsakani da kowacce a cikin matana. Ki tsaya in da na saka ki, ni ne mijinki ba ke ce mijina da za a ce komai ya faru ki tasani kina yi mini faɗa kamar wani ɗan ki ba. Ba na so na faɗa miki bana so"
"Ka yi haƙuri "
Na faɗa cikin sanyin murya.
"Ban yi ba."
Shima ya ma yar mini a fusace.
"Allah ya huci zuciyarka."
"Amin."
Ya faɗa a ƙufule kafin ya tashi ya shige bedroom har yana bango mana ƙofa. Gimbiya ta kalleni kafin ta riƙe baki tana faɗin" Kin gani ko Maman Jidda? Wallahi ba ƙalau yake ba"
Miƙewa na yi tsaye kafin na ce" Lafiyar sa ƙalau. Da a ce kin ji shawara da duk ba ki jawo ma kan ki tozarci ba, nima da ba ki jawo mini wannan jan kunnen da ya yi mini ba. Don Allah Gimbiya ki daina sakani cikin rigimarki. Ba zan iya da Yallaɓai ba nima kina dai ji ya ce ni ba Nene ba ce ina yi masa shisshigi, in dai kin san ba za ki dinga haƙuri da wasu abubuwan ba nima to ki yi ma Allah ki daina saka ni a ciki."
"Ki yi hakuri." . Ta faɗa a sanyaye to itama ai ta gani yadda ya zauna yana ta yaɓa mana mganganu.
"Na ce miki ki riƙa kauda kan ki. Ba fa komai ne sai ka yi mgana ba. Ki bar shi ya yi ta kai wa daran mana in kin ga za ki iya jiran shi ki jira shi in ba za ki iya ba ki yi kwanciyarki. Ke in ya ga dama duk ranar girkinta ya je can ya kwana me ye na ki? Gidan shi abin da ya dama shi za mu sha, kuma Allah ai yana sama yana kallon shi cikin mu duk wacce ya danne ma haƙƙi sai Allah ya tambaye shi. Duk tsiyar shi ba zai kwana can ba zai dawo kuma yau da gobe ba ta bar komai ba in kika yi haƙuri itama ai wata rana za ta zama ɗaya da mu. Ai mace ce haihuwa za ta fara. Kamar yadda ya ganta ya auro wata rana haka zai ga wata ya auro itama a fara gwagwarmaya da ita ba, ai Namiji ne shi a rayuwar namiji mai ya yi ne da kuma ɗauka da ajiyewa ke dai ki zura ido kawai ki daina ma tanka shi, ki nuna ma kamar ba ki san abin da yake yi ba shi da kan shi zai shiga taitayinsa."
"In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba."
Ta faɗa tana miƙewa itama.
"Ya dai kamata gaskiya."
Ba mu ji ko ƙaran buɗe kofa ba sai ganin shi muka yi kawai a kan mu a falon, ban san ko ya ji manganganun mu ba ko kallon mu bai yi ba ashe ya manta wayarsa a saman kujeran da ya tashi ita ya ɗauka a fusace ya koma ciki ina ganin haka na kama hanyar fita ina yi ma Gimbiya sai da safe, mganganun sa ba su wani dame ni ba Gimbiya ce washegari ta ce ba ta iya barci ba a raina na ce ba za ki yi ba kam nima haka na kwana kuka a ranar da Yallaɓai ya ce ina baƙin ciki da su Khalipa. A cikin zuciyata na ce Gimbiya Welcome to the Game.
Wannan tsiyar da Gimbiya ta jawo ta aka yi ita ta ja mana Yallaɓai sati ya yi daga ni har ita yana yi mana cin mgani ko abincin mu ba ya ci da gani har ita, sai ma bangaren shi da ya turo ma'aikata suka fara ida sa gyarawa ko gaya mana bai yi ba, ni in ranar kwana na ba yan gaisawa ba ma mgana sai dai ya yi ta aikinsa a kan system ko kuma ya yi wasannin shi da ƴa'ƴan shi, nima ko ganin haka na kama kaina ban ga abin da na yi masa na bashi haƙuri tun a falon Gimbiya ban san kuma me ya ke so ba ko so ya ke yi na kwanta masa saboda yana fushi da ni, ni ko na ce a cigaba da tafiya gabar nan ce ya san ni na fi shi kwarewa. Da na fahimci ba ya cin abincina sai na daina ma yi masa ta yi, Gimbiya ta ce itama haka ba ya mata mgana in ta yi masa mgana da kyar yake amsawa. Ita duk ta damu kamta ni fa na faɗa mata an riga an zo matakin da ɗan zaki ya riga ya girma ni Yallaɓai ai ya daina hana ni sukuni da takaicinsa tuni na ke tattara shi na watsar na kama sabgogin gabana. Balle da na dawo da sana'ar hijabai na gadan-gadan ina na gama ta lokacin shi, da man hatsiyar tariyar da bukukuwa ne suka saka na yi sanyi ganin ina so ma na taba jarin kuma ga mutane na so shi ya sa kawai na saka aka ɗinko mini da yawa aka aiko mini da shi.
Gimbiya ko ga shagonta ga aiki amma duk da haka ta zauna Yallaɓai na neman kasheta da haushi. Wai tana faɗin ya fara gyaran bangaren shi bai sanar damu ba na ce ina ruwan ki? Shi da gidan shi da kudin shi? Ni ko a gefen gyalena to da Rabi'atu za ta dawo bai sanar da mu ba ranar ni ba na nan na je gidan Ma'u na duba ta tun da ta haihu ɗin ba ta ƙara lafiya ba lafai lafai ce, Gimbiya kuma tana shago yara suna makaranta danginta suka zo suka yi mata gyaran bangarenta sannan da daddare suka dawo da ita. Ni ina muka sani ba sai dai muka gan su ba kawai ni dai na shiga bangaren Rabi'atun na yi musu sannu da zuwa itama na yi mata sannu duk ta yi wani fari ta rame.
"Ai mun zo ɗazu gyaran bangaren Rabia megadi ya ce duk ba ku gidan"
Kai tsaye na ce ni na je dubiya ne Gimbiya kuma daga wajen aiki ta wuce shago. Kuma ba mu san yau za su dawo da ita ba.
"Ai ko dai tun jiya ma Megidan ya so ta dawo Allah bai yi ba sai yau."
Wato kenan yana sane mu ne dai bai ga damar sanar damu ba ya yi ma kansa ruwa na kawo musu ba su ma sha ba.
"To ga Rabi'atu nan mun san ana ƙoƙari kula da ita Allah ya ba da lada."
Na amsa da Amin Gimbiya sai da suka fito haraba ta leƙo suka gaisa direban da ya kawo su ya kwashe su ya ma yar. Na koma na sake duba Rabi'atun muna ɗan yi hira kaɗan ta ji sauki sai dai ta rame. Ni dai na ga abin mamaki yarinyar nan tana jin diran shigowar mota ni ko ina zaune na ce ina jin Yallaɓai ne ai sai da na yi suman zaune saboda barikin da na gani ganin idanuwa. Yarinyar nan tana zaune amma sai ga ta kwance ta narke kamar ruwa, yana shigowa da man bangarenta ya nufo, yadda ya ganta kwance tana wani lumshe ido ko lura da ni bai yi ba ya nufeta duk ya rufe ya tarairayota jikinsa yana tattaɓa goshin ta.
"Baby me ya faru jikin ne? Kan ki ke ciwo? Ko zazzaɓin ne?
Ya ke faɗa yana taɓa kanta da cikinta ita ko ta narke masa tana shagwaɓa kamar wata jaririya.
"Abba uhm"
Ta ke faɗa har da gutun hawaye, shi kuma gabaɗaya ya ruɗe.
"Me Abba ya yi? Uhm faɗa mini."
"Ba kai ne ba'
Kawai sai ta fashe masa da kuka cikin rawan jiki ya ƙamƙameta yana faɗin"Abba ne ko? To Abba ba zai ƙara ba kin ji ko?
Ɗankari!
Haka na faɗa a zuciyata. Gimbiya ta daɗe tana ce mini yarinyar nan muguwar yar bariki ne ban sani ba, sai yau da ta nuna mini Umma na ke ita kuma Rabi'atu ina zaune tana abin da ta ga dama in shi bai ganni ba ita ai ta san da ni. Zuciyata ta motsa amma ban bari na zubar dakaina a gaban su ba sai na miƙe ina mirmishin ƙarfin hali.
"Mu kwana lafiya Rabi'atu."
Sai a lokacin shi ya farga da ni, ya ɗan yi shock tun da har ya ɗan sake ta, ta bar cinyarsa ta zauna da ɗuwawunta a saman kujera.
"Umma to sai da safe."
Ta faɗa cikin sanyin murya ji na yi kamar ma juya na kamata na yi bugu. Ban taɓa jin kishinta da haushinta irin na yau ba.
"Sadiya da man kina nan zaune?
"Sannu da dawowa."
Na faɗa ban jira amsar shi na bar musu falon, duhu duhu hazo hazo na ke gani kafin na kai bangarena. Na yi shuru zaune ina tunani,ko ma me ya faru yarinyar nan da gangan ta yi, tun da ai ni da ita ne zaune muna hira, raina ya ɓaci kenan ta shirya mini wulakanci ne? Daga abin arziƙi duk abin da ta ga ina yi mata darajan Yallaɓai ne da sauke haƙƙoƙin zaman tare amna ni ai ba ta isa na koma bayan ta ba. Amma tun da ta ce haka mu zuba mu gani, ni ko zan nuna mata na riga ta zuwa duniya ita yarinya ce har yanzu. Ranar raina a bace na kwana ko Jidda ta kira ni a waya ban wani saurareta ba na ce ina jin barci washegari da safe sai ga Yallaɓai ya shigo yana yi mini kame kame ya ɗauka zan nuna masa wani abu ne ya ga bayan gaisuwa kallon musulumci ni ban yi masa ba ma shima ai munafukin ne.
Ko kunya bai ji ba yana faɗa mini Rabi'atu na son tuwo, na ɗauka zai ce ne ni na yi mata wallahi da in na fara faɗa masa mgana sai abin da na manta sai ya taimaaki kan shi ya kira Baby ya saka ta. Asabar ne ba makaranta Tahfiz kuma suna ajin bita ne yau ba ta je ba. Tun da y'arsa ya saka ban yi magana ba na yi shuru kamar zan ce ta je can bangaren nata ta yi mata sai na fasa ganin gogan yana can ya tare. Ranar ko fita bai yi ba har su Adnan gida suka zo suka same shi Gimbiya ko tun safe ta wuce Rano an yi musu rasuwa sai gobe za ta dawo shima Yallaɓai in dacewa zai yi ai ya dace ya je tun da yaron ƙanin Hajiya ce ya rasu saurayi ne ma Gimbiyar take faɗa mini to yarinya ƙarama ta saka shi a gaba har lahadi bai fita ba Baby ya samu tana yi mata wahala ranar ma da na ce ta wuce ta je Tahfiz hanawa ya yi wai ta bari wani sati kawai.
Ban yi magana ba saboda na shirya mafita na. Ranar litini da safe ya fita ya ce mini za su je Rano gaisuwa. Na ce Allah ya tsare ni da man mun tsara da ni da su Munnira Gimbiya gobe za ta dawo ranar bakwai za mu koma tare da ita amma na kira ta a waaya ta haɗa ni da Hajiya na yi mata gaisuwa. Tun ranar nan da na kama shi yana wannan ɓare ɓare jikin ya daina sha mini ƙamshi, ni ko na yi kamar ban ma gane shi ba tare suka fita da Rabi'atun ya sauke ta a makaranta ai ko ta gane ba ta da wayau sai yamma ta dawo gida ban yi kuma abinci da ita ba. Sai ga ta shigo shashena ta zauna ta ɗauka irin baya ne in ce ta shiga kitchen ga abincin ta ga na yi mata kiri ƙiri.
"Umma ba ki yi sauran abinci ba?
Kai tsaye na ce mata yau ban yi girki ba indomie ce Baby ta dafa da suka dawo makaranta. Ba su nan kuma sun tafi islamiya na samu an saka su wata islamiya anan anguwar da muka dawo ba nisa. Su Khalipa da man wajena Gimbiya ta bar su da za ta fi.
"Ki je ko yar indomoe ki sulala ki ci.'
Ta ce mini to, ta tashi ta wuce na rakata da harara ba wai haushin abin da ta yi mini ba ne a'a haushin yadda ba ta raga mini ko don karan da na ke yi mata ba. Na yi kyafci na ce za ki gane ba ki da wayau yarinya. Tun daga ranar na daina ije mata abinci sau biyu tana zuwa tambaya na ce yara sun cinye daga nan ta fahimci dai ba zan ba ta ba ta kama kanta. Sai Yallaɓai ya ce ba ta da lafiya ba ita iya komai amma ranar girkinta su kule ba ka jin motsin su to da man ni ce na ɗaukar ma kaina kuma na yaye Gimbiya da man yar gaskiya ce ba za ta yi ba shi ya sa bai taɓa saka ta ba.
Da Gimbiya ta dawo kamar zan faɗa mata sai na fasa kawai na share saboda kowa ya ji sai ya yi mini Allah ya ƙara. Munnira ta zo ranar jumma'a mganar tafiyar mu Gobe muka shiga wajen Rabi'atu ta duba ta. Da ya ke muna ta knoking shuru ni kuma na ɗauka ko tana salla me tun da bayan mangariba ne sai muka tura kofar tun da a buɗe yake muka shiga abin mamaki ta gyara ɗakin nan tas yana tashin ƙamshi sai na tuna ashe yau gogan yana ɗakin ta ne, sai muka zauna saman kujera muna jiran ta ba ta ji shigowarmu ba sai ga ta fito da wata shigewar riga marabanta da tsirara kaɗan ne. Ko ta yi tunanin shi ne ya dawo ko da man dai haka take yawon ta a ɗakin ta ban mu sani ba da ta gan mu ta ji kunya da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko hijabi ta saka ta fito muka gaisa tana rufe fuska muna fita haraba Munnira ta kalleni kafin ta ce.
"Ke na taɓo ki da mgana. Wai yarinyar nan ne ta kile haka?
Ina dariya na ce" Ras. Ai Namiji ya kilar da ita."
Munnira ta riƙe baki kafin ta ce" Wallahi in ka ganta kamar ka saka mata yatsa a baki ba za ta iya cizawa ba.' Uhm kawai na ce saboda Rabi'atu ta sauya idanuwanta sun buɗe ko na ce yanzu ta san daɗin namiji shi ya sa.
"Kin ga idanuwanta ƙif ƙif na marasa kunya yanzu."
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba.
"Ba shakka Tafida ya ba ta zuma ta ɗanɗana. Sadiya sai ku shirya za ta haɗa kafaɗa da ku yanzu."
"Me ya rage? Ai tama fara haɗawa."
Na fada ina danne abin da ke ta so mini, yarinyar da Yallaɓai ya ce kwana take yi da zazzaɓi ne haka shi ya sa da man ya ce ita ba za ta je Rano ba ni da man na yi masa mgana ne kar daga baya ya ce an ware ta tun da yanzu ba ya so wani abu ya same ta. Washegari su kaɗai muka bar ma gida da yara kaf muka tafi ya ba mu mota Sadi ya kwashe mu, su kuma su Hauwa suna motar gidan Mimisco har da su Anty Bahijja aka yi tafiyar da Mubeenan Musbahu da tsohon ciki har ina ta faɗa na ce kamar dole ta zauna a gida mana tun da cikin ta ya tsufa.
Can muka yini sai dare, Amma mun je gidan Marwa an haɗu ana ta hiran duniya mun haɗu da Sameena ta ce mini gobe ma za ta koma tana dariya ta ce ya ta gan mu da mutuniyar nima ina dariya na ce ta ji wuya ne ta dawo muka haɗa kai don Allah, Sameena na ta dariya ina ta ya ta. Sai bayan isha'i muka koma gida muna mota Jidda ta kirani tana faɗa mini wai Abban su ya kirata ya ce in sun samu break ta zo gida ta duba Anty Rabi:atu ba ta da lafiya sosai. Kamar Jidda ce Yallabai na rufe ta da faɗa ta in da na ke shiga ba ta nan na ke fita ba.