Kenza eBookz

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 47

Turken gida book 3 cmplete - Chapter 47

Turken gida book 3 cmplete Chapter 47: Turken gida book 3 cmplete Chapter 47. "Ko hutu kuka samu ki tafi gidan Ya Hamza ma ji kin kamo hanya kin dawo sai…

3,348 words

"Ko hutu kuka samu ki tafi gidan Ya Hamza ma ji kin kamo hanya kin dawo sai na ci uban ki Jidda. Saboda kawai duba Rabi'atu sai ya ce ki bar karatun ki taho! Gaskiya Yallabai ya fara samun matsala."

Ita dai da ba ta san mafari ba hakuri ta ba ni ta ce wai ta faɗa masa suna ma test ne, bayan mun gama wayar na kalli Gimbiya ina faɗin" Kin ji mijin ki ko Gimbiya? Ta yi uhm kafin ta ce" Wallahi ni dai ina tunanin ba haka nan ta bar sa. Ba ki ganin yadda ya ke fita hayyaci a kanta ne? Wai Jidda ta zo dawo makaranta kawai saboda ta duba yar gold? Da wani abun ne ya taso tsaye zai yi ya ce ba za ta zo ba amma da ya ke yar gold ce ya ce a zo a duba ta mana."

Ni takaici ma ya hana ni mgana, ko da muka isa gidan yana bangarenta shi dai ya zo ya yi mana bangajiya ban da ita ni Gimbiya ta ma ce mini ko gaisuwa ba ta yi mata ba da a ce da ne zan yi mata mgana yanzu ko kiɗa ya sauya shi ya sa rawa ma ya sauya. Shi kuma gogan bai nuna mata abin da ya kamata ba. Yadda bai nuna mini ya kira Jidda ba nima ban nuna masa na ji aikin da ya yi ba. Sai da kan shi ya zo yana ce mini Jidda ta so ta zo gida amma tace suna test a raina na ce ta so ko ka so, ya na neman ya riƙa kashe ma Baby karatu saboda matarsa kawai sai ya ce ta zauna ta yi ma Rabi'a girki ne ga an yi sau ɗaya sau biyu ana uku na ce ba zai yuyu ba.

"Ba zai yuyu ba kika ce Sadiya?

Ya faɗa da safiyar lahadi sun shirya Sadi na jiran su zai kai su Tahfiz wai Baby ta zauna ta je bangaren Rabi'atu ta yi mata shara sannan ta tambayeta abin da take so ta dafa mata yarinya ta ce hadda za ta je tana bita yau amma ya ce ta haƙura ai jiya ta je.

"E gaskiya ba ta yuyuwa ka kashe ma yarinya karatu kawai saboda bukatar matarka. Yallabai ta ɗauko wata daga can garin su ko ka samo mata wacce za ta kula da ita fakat kenan."

Sai ya kasa mgana ni ko na yi masa mai gabaɗaya sai na ce" Kuma ni ban ga aikin da zai gagareta ba ai ba ta ciwo tun da ta iya ji da hidimarka to za ta iya ji da hidimar kanta da gidan ta ma" Tun da ya ji na faɗi haka ya kiyayi tsayar mini da karatun yarinya ban san ko maganar da na yi masa ba ne, ko da man sun tsara hakan sai ga wata yarinya an kawo kamar za ta ɗan girmi Baby ƙanwar Antyn ce ta yi candy aka kawo ta taimaka ma Rabi'atun ta bakin Gimbiya ta ce da man akwai wacce za ta taimaka man aka bar shi yana ta faman wahala. Tun da ga lokacin kowa ya samu lafiya ta warke tun da yanzu laulayin ya bi jiki amma tun da makira ce a ko da yaushe nuna masa take yi tana cikin ciwo saboda ya lalace a kanta.

Mubeena ta haihu amma aiki aka yi mata da nagudan ya taso mata ni Musbahu ya kira uku na dare na ce ya zo gida ya ɗaukeni tun da ba zan iya driving ba. Yallaɓai na ɗakin Gimbiya a waya na kira shi sai ga shi ya fito, da man ina haraba ina jiran Musbahu yana zuwa bayan sun gaisa kawai ya ɗauke ni muka tafi, muna asibitin har safe ba ta haihu ba kan yaro ya jirkice suka ce aiki za a yi mata Musbahu ya saka hannu. Bawan Allah duk ya ruɗe sai da Adnan ya zo yana bashi baki. Da safen Yallaɓai ya zo shi ya biya ma kudin aikin da aka yi mata an samu nasaran fito mata da yaron ta namiji ƙato mai kama da uban shi. Ba ni na koma gida ba sai da na ga ta farfaɗo y'anuwanta sun zo suna ta mini godiya domin ni ce na tsaya a tare da ita har ta samu kanta na ce ba komai Musbahu da Mubeena sun ɗaukeni da daraja shi ya sa nima nake daraja duk abin da ya shafe su. tun da kuma aka yi haihuwar bana zaune kullum sai na je asibitin kwanan ta huɗu suka koma gida to can ma gidan haka nake sintiri , suna an ɗaga sai sati biyu kan lokacin maijego ta ji sauki. Y'anuwanta sun ce za su dauketa bayan suna da Musbabu ya nemi shawara ta na ce ya barta ta je gidan kamar gobe ne.

An yi suna yarinya ta ci sunan Hajiya iya Hafsat. Musbahu ya yi ƙoƙari ya yi abin da kowani uba zai yi raguna biyu aka yanka mata Ya Usman ya siya ragunan sunan. Mun sha suna har Nafisan katsina ta zo da Safiiya ni da man mune yan gaba gaba Gimbiya da wuri ta zo har yara da suka dawo makaranta na saka Sadi ya kawo su, Amaryan Yallaɓai sai yamma ta zo daga makaranta saboda kuma tuƙo kanta ta yi ba ta yi dare ba da dokar megidan ban da tukin dare. Wannan kan gaskiya ne daga ni har Gimbiya in muka fita da mota muka kai dare ba mu dawo ba haka zai yi ta kira yana mana faɗa. An yi suna lafiya an watse bayan suna da kwana huɗu yanuwanta suka ɗauketa zuwa gida sai dai ya riƙa zuwa yana ganin ta. Ni dai na yi mata atamfa da kayan Baby iya karfina. Sai da ta gama wanka za ta dawo ne Musbahu ya zo da kanshi ya ke faɗa mini abin arzikin da Yallaɓai ya yi masa ni ban ma sani ba cewa ya yi ya tashi daga gidan shi ya yi ƙarami ya bashi gidan da na taso ya zauna a ciki ya bar masa na wajen na shi sai ya saka haya a ciki. Kai na yi masa murna kuma na san Yallaɓai ya yi haka saboda ni, domin ko kwanaki da ya ce zai saka haya magiya na fara yi masa ina son gidan nan bana so na ga an bama wani can bare gwara na gida.

Da na yi ma Yallaɓai godiya hararata ya yi kafin ya ce" To ya zan yi? Gidan nan ji kike yi da shi kamar me. In na ce zan siyar ki ji haushina in na ce haya ma kice aa. Shi ya sa sai na yi tunanin gwara na ba ma Musbahu shi sai ya bar mini na shi, tun da na ga in shi ne zaki ji daɗi yaron ɗakin ki ne"

Ina ta dariya ban yi magana ba wai zan ji daɗi yaron ɗaki na ne kuma na ji daɗi sosai. An je an yi ma gidan fenti da gyare-gyare Mubeena ta dawo, ta kuma zo har gida ta yi mini yini ita da Anna(Hafsat) daga baya nima na je gidan na da wuri sai na ke ganin kamar zan waiwaiya na gan ni ina shiga ina fita a gidan wasu shuɗaɗdun al'amura ba za su taɓa shuɗewa ba, saboda a gidan nan abubuwa da dama sun faru sai dai godiya tun da yanzu mun samu cigaba ne. Kowa ya ji labari sai ya yi ma Musbahu murna tun da ya samu cigaba gidan shi kuma Yallaɓai ya saka yan haya.

An gama gyara shashen Yallabai falo ɗaya ne da bedroom uku. Ni har mamaki yawan bedroom ɗin na yi da na tambaye shi cewa ya yi ba ruwana na jira mana na gani. Sai na kama bakina. Ya yi shirin shi har kayan funitures ya siya ya gyara bangaren shi tas kuma kowani ɗaki ya saka gado, wato dai wulaƙanci Yallaɓai ya ƙaro ashe wai kowacce ranar girkinta da ɗakinta in kin fita ki rufe ranar da kike da miji ki zo ki gyara ku kwana da miji in kin fita kina da key dinki ki rufe. Ranar da ya ta ramu yana faɗa mana na kasa haƙuri sai da na yi dariya.

"Na zama abin dariya ne?

Ya tambaya a daƙune ganin ya ji haushi ya sa na ce" Ni tsarin ne ya ba ni dariya wai ranar girkin ki da key ɗin turaka ki je ki gyara in kin fita ki rufe" Shima sai da ya yi dariya kafin ya ce" Maganin ƙorafi na yi. Kowa da turakanta magana ta ƙare." To ni dai ko rawan jiki ban yi ba tun asali na tsani turakan miji wallahi, Shi ke nan Yallaɓai ya fara buɗa jiki in kina da girki sai dai ki bi shi har dining ya saka a bangaren na shi duniya sabuwa. Ni fa ranar girkina mantawa na yi na yi barci a bangarena da safe na tuna tsarin har abinci a can za ki haɗa masa ke fa can za ko tare sai kin fita girki ni ko na ce ba zan iya ba ya'yana fa. Yallaɓai ya ce to na yi ta kwana a bangarem nawa shi dai ya gama bin kowacce daƙinta tana yi masa yanga.

Ina gani Rabi'atu da Gimbiya ana gogawa. In suna da turaka aka kasa zaune aka tsaye. Rabi'atu in ranar ta ce ƙamshi turare har haraba. Ita da Salima kanwar Antyn tasu su zage a yi ta girke-girke. A sauya zanin gado a yi wannan a yi wannan haka itama Gimbiya sai suka koma suna gasa shi ko Yallaɓai na jin daɗi sun zaɓi dakunan su ni na karshe suka bar mini, na san dai in dai ranar girkina ne da safe zan je na gyara ko na saka Baby ta gyara na kuma shiga ɗakin na gyara na wanke tiolet a bangarena na ke yi abinci na kwasa na je na jera masa bana yin wannan rawan jikin na su to Allah na tuba wani kuma dare ne jemage bai gani ba ai sai daran mutuwarsa? In muka kwana da asuba nake gudawa bangarena sai dai in zai fita ya biyo ni ranar har ce mini ya yi in bana son kwanan nan ne na faɗa masa.

"Aa kawai dai ban saba ba ne wallahi ina jin wani iri."

Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" Gwara ma ki saba malama turaka yanzu kika fara zuwa." Shuru kawai na yi, ni bai san ban wani damu ba ta kaina na ke yi, duk da wannan rabawan da ya yi bai hana an samu matsala ba Gimbiya ta ce Rabi'atu tana ɓata kitchen da falo ba ta gyarawa haka take fita tun da can take girki, saboda da daga Rabi'atu sai ni ne daga baya abin ya birkice ni na dawo farko, sai Rabi'atu sai Gimbiya, rigima sosai sai da ya tsawarta musu da cewa zai kori kowa a turakan na shi sannan aka zauna lafiya bayan an yace kowcce ta zo ta ɓata waje ta gyara kafin ta fita ni ina gefe ban shiga ba ina ruwana na yi magana ya ce ina yi masa shissshigi. Na koma gefe na zama yar kallo tsakanin Rabi'atu da Gimbiya ne suke ƙwama film acikin gidan nan wani abun ma kamar ka yi ta dariya wani abun kuma hauahi ka ji kamar ka yi ta dukan su.

Cikin Rabi'atu har ya fito wata biyar amma ya yi girma sosai. Har ni kaina ina mamaki, sai da ta yi scan Yallabai ya zo bakin shi kamar zai kai kunne yana faɗa mini an ce yan biyu ne a cikin Rabi'atu mace da namiji. Sai a lokacin ya ke faɗa mini wai maman Rabi'atu yan biyu ne namijinta ya rasu ne. Labarin yan biyu Rabi'atu za ta haifa kusfa kusfa Yallaɓai ya kai labarin nan da man fa yana da shegen surutu da faɗi ba a tambayeka ba. Gimbiya ko ta ce ya dai bar murna domin likita ba Allah ba ne, shi ko ina ruwan shi yana ta shirin haihuwa kamar an ce gobe ne ballanta yanzu da kuɗi suke huda shi ai komai ma zai yi. Haka nan muke zaune muna gungura rayuwar mu, ba a sati Gimbiya da Rabi'atu ba su yi tsiya ba, kuma duk fa kan turaka da miji, ni wallahi har na gaji da baa su haƙuri na saka musu ido, kuma in dai aka yi sai Gimbiya ta zama mara gaskiya saboda ta cika ƙorafi da mgana ita kuma Rabi'atu wayau da bariki da haka take cutar da ita ba ta sani. Ni dai ba mai yi da ni Yallaɓan ma kan shi isata yake yi na tattara shi na bar musu ranar har mgana ya kwaɓa mini wai ya fahimci na koma gefe yanzu na yaye shi kamar ba mijina ba, ba na damuwa da al'amuran shi.

"Ba haka ba ne. Gani na yi bayan ni kana da biyu irina masu kula da kai."

Hararata ya yi kafin ya ce" Wato ina da biyu! Ai ko goma ne ina nan a matsayin mijin ki kuma dole a ce ma mijin iya Baba."

"Dole ne wannan"

Na faɗa ina masa dariya ganin ya shaƙa sai kawai ya jinjina kai yana faɗin"Na gano ki wato kin gama cin moriyar gangan za ki yada ƙwaron ta ko? Dariya har ina faɗowa daga kan kujera. "To wallahi ba ki isa ba." Yallaɓai da karfi hali shi wai a dole ban shiga ana kishin sa da ni ba a raina na ce ba kuma zan tusa kaina ba, ai ni tun da na yi karatun namiji na daina ta yar da hankalina a kan shi. Ya gaji da mitan shi ya haƙura domin ni kam ta kaina na ke yi, haƙkin shi dai ina ba shi ina iya bakin kokarina amma ba na rawan jiki da na ƙafa a kan shi. Na gama yin wannan tun a baya yanzu duk abin ma ya fita kaina. To jiya ai ba yau ba.

Siyayyya kayan haihuwa komai biyu aka siya dangin Yallaɓai kowa uwar biyu yake kiran Rabi'atu da shi har Nene fa in ta kira waya sai ta ce ina uwar biyu? Na ce lalle duniya juyi juyi yanzu uwar biyu ce a layi ba mai farar haihuwa ba. Cikin Rabi'atu na wata bakwai ya yi ƙasa ga shi ya girma yana rinjayan ta, ba ta aiki komai da man daga kwanciya sai in za ta shiga makaranta ya ma hana ta driving shi ya ke kaita ko Sadi, Salima na nan tare da ita tana kula da ita amma da wannan ƙaton ciki ba ta fasa zuwa turaka ba tana ganin ƙya shin ta haƙura har sai ta haihuwa na ce yar wahala kawai in dai namiji ne ke ce a baya ba shi ba. Danginta sun yi maganar a al'adansu gida za ta koma ta haihu megidan ya ce bai amince ba da kan shi ya zo yana faɗa mini na ce Allah ya kyauta ban san yadda suka ƙare ba daga baya ya ce mini in ta haihu an yi suna za ta je can Maiduguri ta yi wanka tun da sun matsa a raina na ce to ni ina ruwana? In na yi magana ya ce ina yi masa shisshigi ni dai iyakata Allah ya kyauta da Allah ya raba lafiya.

Ciki na kai wata tara ta daina fita ko'ina saboda ta yi nauyi ba sai an faɗa maka ba kana ganinta sai ka ce amma dai yan biyu ne acikin nan ko? Saboda girman shi ya yi yawa gaskiya Rabi'atu ta zama ɓukekiya ciki ya ma yar da ita babban mace. Edd ɗinta bai gama cika da kwana goma ba aka yi mata aiki ta haihu a wani daran jumma'a. Da ya kama 13 Nov. 2023. Ni Yallaɓai ya taso ina barci lokacin da ta fara naguda da man cikinta na shiga wata tana ya tara mu ni da Gimbiya ya ce zai riƙa kwana a bangaeen Rabi'atu saboda cikinta ya shiga watan haihuwan shi, ni dai ko a jikina na ce Allah ya ba da sa'a. Gimbiya ce ta ɗan nuna ba ta yadda ba ya shi ba yardanta yake bukata ba shi ya sa ba ma amfanin mganar tun da abin da ya yi niyya ba zai fasa ba.

Ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi mata C.S an fito da jarirai biyu mace da namiji. Kwana muka yi zaume a asibitin nan ni da Yallabai da Salima sai da safe aka fito da ita sannan ya kikkira jama'a ya sanar da su. Da safen na koma gida ni na ke ma faɗa ma Gimbiya da yara Rabi'atu ta sauka an samu yan biyu. Su Baby suna ta murna, Sai da huta can da yamma na koma asibitin Gimbiya ta ce mini sai gobe za ta je shago za ta leka. Ko da na je asibiti ta cika makil da dangin Rabi'atu da na Yallaɓai su Anty Bahijja ana bakin gadon mejogo ana ta yi ma jarirai hotuna. Faɗi take yi an yi haihuwan da ba a taba yi a gidan Tafida ba haka ta yi posting ma a status. Shi kan shi angon ƙarnin ya kasa sukuni ina jin all contact ya yi wajen tura sakon an yi masa haihuwa saboda yadda yake yini amsa wayoyin yan barka. Washegari tare muka koma da Gimbiya da yamma da yara ai ko ta sha mamakin ganin su Anty Maimuna ana ta rawan ƙafa a gabanta ma sun sake faɗa an yi ma Tafida haihuwan da ba a taɓa yi masa ba ta cika ta yi fam har tana ba su amsa da cewa sai dai a kira su da ƙannen su Khalipa Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya ba aure gare ta ba ta san ita kanwarta ce dukan tsiya za ta yi mata suka bar Gimbiya da tura baki tana ƙwalla ni dai ban tofa ba amma da man na san wata rana itama za ta ji irin abin da na ke ji a can baya.

Kwanan Rabi'atu shidda a asibiti aka sallamota suka dawo gida. Yayenta biyu sun taho daga Maiduguri da kanwar babansu Yakumbo ita za ta zauna da ita har bayan suna. Gida fa sai kamshin masu jego, an shirya suna gagarumi tun da haihuwa ce da ba a taɓa yi ba. Kuma mun ga haka mukan mu kowaccen mu 100k Yallaɓai ya ba mu ni da Gimbiya na fitar kayan suna. Jidda ma ta zo gida lokacin ai dole ta zo Yallaɓai fa haka ya dinga kiranta wai ta zo gida ta ga k'annenta yan biyu. Kuma yara sun ci sunan Sulaiman da Aisha. Ya cika alƙawari ya yi ma Alhajinmu takwara. Alhajinmu ko har gida ya taho barka ya kuma turo Gwaggo. Tun da an yi ma ubana takwara ai dole na ware kudi na yi hidima cikin kuɗin da ya ba ni ne na siya ma yaran riga da pampers uwar kuma atamfa na yi mata. Gimbiya dai kayan jarirai kawai ta yi ni kuma ba ni da da man zillewa Yallabai ya gama yaɗa ma Duniya Alhajinmu ya yi ma takwara shi ma can Alhajimmu ya gama yaɗawa shi ya sa kaf yan gidanmu sai da suka zo barka na nesa su Amina suka kira waya.

Sa guda Yallaɓai ya gada da raguna biyu, shagalin suna abinci ma daga reataurant aka dafo shi. An yi kayan rabo su robobi jaka memo da hotunan yara, Jidda dai ta yi kayan fulawa su cake da donut uban kuma ya ba da kuɗi ta yi har da cake, Rabi'atu kuma ta shiga ta fita da kayan alfarma. Ni dai kala biyu na saka da man ina da su Gimbiya ko da man tana da sutura ina tunanin ba ta yi ma sabon ɗinki ba. Yan uwansu na Maiduguri ba su zo da yawa ba gaskiya saboda nisa sai dai dangin Yallaɓai ne suka cika gidan har da mai kiɗan kwarya su Halima suka kira suka cashe, wata zabiya cikin masu kiɗan ƙwarya tana waƙe mai jego.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull