Turken gida book1 by janafty - Chapter 15
Turken gida book1 by janafty Chapter 15: Turken gida book1 by janafty Chapter 15. Gabaɗayanmu muka haɗu a saman dining ɗin ban da Baby da ke can falo ta na…
3,347 words
Gabaɗayanmu muka haɗu a saman dining ɗin ban da Baby da ke can falo ta na kallo. Da kaina na saka ma Yallabai guda biyu na zuba masa miyar da ta ji naman rago Jidda ma ta saka ɗaya ta ce ya isheta nima dai ɗayan na saka saboda na ci abinci a gidan Halima.
"Sadiya ta. Kin yi kyau.''
Haka Yallaɓai ya faɗa yana kallona da mirmishi a saman fuskarsa. Fari na yi masa da ido kafin na ce"Thank you Yallaɓan Sadiya." Jidda na cin tuwon ta ba ta ɗago ba amman ta yi mirmishi. Yallaɓai ya kalleta kafin ya ce"Hajiya Nene ko Umma ba ta yi kyau ba? Da sauri ta ce" Ta yi kyau sosai Abba." Ya na ƴar dariya ya ce"To ai shi ne na yaba kuma sai na ga kamar ta cancanci tuƙwaici ko?
Jai ta gyaɗa masa ta na mirmishi ina jin su ban ce komai ba sai da na ji ya ce"Kar ki damu zan ba ta kyakyawan tuƙwaici" Ɗagowa na yi ina hararanshi kafin na saka kafata na taka masa kafa sai ya janye yana dariya. Jidda dai ta gama cin tuwonta ta ɗauki filet ɗin ta bar mana Falon sai da ta fita na kalle shi kafin na ce" A gaban Jiddan ka ke mganar tuƙwaici?
Kai ya gyaɗa kafin ya ce"To miye a ciki? Ai ba ta san irin tuƙwaicin da kike karɓa ba madam" Wani kallo na yi masa da ya sa sai da ya ƙware yana shan ruwa na yi masa gwalo ina dariya amman sai da na saka hannuna ta bayansa ina shafawa ganin ya sarƙe da yawa. Wani ruwan na sake zuba masa na bashi ya sha sannan ya ɗan lafa masa.
Kallona ya yi kafin ya ce" Ki riƙa bari sai mun shiga ɗaki sai ki yi mini wannan kallon kin ji ko?
Ina dariya ban yi mgana ba shi kuma ya ce" Saboda tsaro ba."
Murguɗa masa baki na yi shi kuma sai ya kaɗa kai kafin ya ce"Murgaɗa da kyau za ki yi bayani ne yarinya in na fara gyara miki service ɗinki har da garambahul." Marairaicewa na yi ina faɗin" Mai jan mota ya tokare boda yau Yallaɓai." Kai tsaye ya ce"ko jan jirgi ne yau sai na gyara miki service ɗin ki." Dariya na yi shi kuma yana faɗin" Yi dariya da kyau." Ni ko na ce to kuka zan yi? Ya na min wani kallo ya ce" A'a shi wannan ki bari sai anjuma."
Kafarsa na taka ina faɗin" Yallaɓai cikin shagwaɓa " Da sauri ya miƙe yana faɗin" Yau wannan shagwaɓar taki ba amfanin da za ta yi miki " Tiolet ɗin falon ya shiga ya wanke bakin shi da hannunshi bayan ya fito ya wuce kan kujera ya zauna ya dauki remot ya kunna TV ni kuma sai na tattara komai na maida kitchen ɗin ina gyara wajen daga can zaune Yallaɓai ya ce.
"Ki zo mu yi hira. Hiran saurayi da budurwansa."
Ina mirmishi na ce"Sadiya da Yusuf ɗin ta ba." Kai ya jinjina kafin ya ce" ko dai Yallaɓai da Sadiyarsa? Na ce ai duk ɗaya. Sai da nima na wanke hannuna da bakina sannan na leƙa su Jidda na ce tara ta yi su kashe kallon nan su je su kwanta in suna da aikin makaranta su ɗauko su yi kafin su kwanta. Jidda ta amsa min da toh sai na rufe musu kofar na dawo wajen Yallaɓai shi kuma sai ya miƙa min hannu na taho ya yi min mazauni saman cinyarsa ina zama ya kishingiɗa nima sai na lafe kaina saman ƙirjinsa ina wasa da tsillin gashin wajen tunda ya cire jallabiyar daga shi sai dogon wando shi kuma sai ya cire min hula yana wasa da gashina gefe ɗaya kuma yana min susan kunni dukkanmu mun yi shuru muna jin bugawar zuciyan juna ga ƙaran tibi da iskar fanka na ƙaɗawa.
Wani farinciki na ke ji. Zuciyata na bugawa da sauri da sauri kamar yadda shima na shi ke bugawa.
"Yallaɓai na."
Na kira sunan shi cikin wani salon da na san ya na kunna shi.
"Uhm."
A saman leɓensa ya amsa min.
"Ina son ka."
"Ina ƙaunarki Halimatuna."
Haka Yallaɓai ya faɗa lokaci ɗaya yana ɗago kaina. Bakinsa na nufa shima sai ya sunkuyomin a tare muka tarbi juna muna sumbatar juna cikin wani shauƙi da muradin junan mu.
*Janafty* *TURKEN GIDA.*
*Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*SADAUKWRWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA (MOMMY)*
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supliments wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*🅿️09*
Mun daɗe muna sumbatar junanmu cikin wani shauƙin da a cikin zukatanmu kawai muke jin tasirin yanayin. Mu ka saki juna lokaci ɗaya kuma muka bi juna da kallo muna sauke numfashi a jejjere.
Mirmishi ya yi mini nima na mayar masa da martanin mirmishinsa. Tallafo kuguna ya yi ni kuma sai na ƙara maƙale hannuwana a a saman wuyansa jawo ni ya yi na sake lafewa a saman ƙirjinsa ina jin yadda ya ke ɗan sauke numfashi kaɗan kaɗan kamar wanda ya yu gudun tsare.
"Yallaɓai.."
Na kira sunan shi bai amsa ba sai ya kalleni kafin ya lakace min hanci da hannunsa guda ɗaya yana faɗin" Uhm" Hannuna na kai saman Sajensa ina shafawa har zuwa ƙasa wajen gemunsa da ya fara fitowa domin yana yawan askewa yana dai barin kaɗan haka ina shafa gemunsa zuwa sajensa ina faɗin.
"Ka san kai ne namiji na farko da ka ruguza dukkan tunanina. Kowa ya san burina na sai na gama jami'a na samu aiki zan yi aure. Amman tashin farko ina haɗuwa da kai ina yar aji ɗaya a jami'a ka susuta tunanina da ya sa na amince da kalamanka na aure ka bayan na yi fatali da mafarkina da burina gabaɗaya."
Na ƙarishe faɗa ina kallon shi. Shima ni yake kallo kafin ya yi mirmishi ya ce" To ni ɗin wasa ne? Kin ga zangaɗeɗen saurayi jikan mutanen Rano. Kin san in kika bari na suɓuce miki samun kamata ai da wahala shi ya sa kika yi amfani da maganar hausawa da suke cewa in dama ta zo maka ka yi amfani da ita saboda wataƙila in ta suɓuce maka har abada ba lalle ka ƙara samun damar ba"
"Allah ko?
Na faɗa ina kallonsa da ƴar dariya. Shi kuma sai ya ɗaga min gira kafin ya ce"Kema kin san gaskiya. Samun jarumi kamata a cikin maza ai da wahala shi ya sa kika yi wuf da ni da sauri kafin ki makara. Ko wata ta yi miki ƴar kafa ba."
Ina dariya ina jan gashin sajensa ya yi shii alamun zafi ya na ƙokarin riƙe min hannu na ce" To me ya sa ka yi ta mini na ci sai da na yi maka kwatancen gidanmu? Kai ma ai kasan in ka bari na subuce maka samun kamata da wahala." Na faɗa ina masa fari, bakina ya sunkuyo ya sumbata lokaci ɗaya ya na faɗin" Ɗan bakin nan na daga cikin abin da ya fara jan hankalina a kanki. Da yanayin mganarki da takun ki. Kai kin iya jan Aji kin ba ma bawan Allah wahala ranar da na koma gida daƙyar na iya barci. A time ɗin bani da burin aure har sai na samu aiki na gina gida na gina kaina amman tun ranar da na fara ganinki kika ruguza mini wannan tunanin. Ke ce silan da ya sa na yi fito na fito da kowa akan aure saboda ai suna ganin ban kai ba me na tara me na ke da shi sannan a tunaninsu na yi yaro a lokacin ba su san a halin da na ke kwana ba ne shi ya sa.'
Ya ƙarishe faɗa yana wani sauke nunfashi ni kuma sai na ƙyalƙyace dariya taya ni ya fara yi yana cewa" Allah. Azumi fa na ke yi duk litini da al'amis ai ya kamata su gane ina son aure. Daga karshe dai na fito musu a Mutum na ce ina son na yi aure saboda ina da karfin sha'awa kuma ina tsoron faɗawa halaka. Nene na jin haka tace ku bar Tafida ya yi auran nan Zuwaira shi ne alherin mu gabaɗaya."
Shi ke tuna labarin a bakinsa amman ni kuma ina hasaso lokacin a cikin idanuwana. Tabbas lokacin an sha gwagwarmaya sosai kafin auran mu amman gashi komai ya zama tarihi. Mun yi aure har da albarkar ƴa'ƴa biyu kuma shekarun sun haura goma sai dai tunawa da abin ya faru kawai a yi dariya ko nishaɗi. Mun cigaba da hirar baya a tsakanin muna yi muna dariya cikin nishaɗi wata magana da Yallaɓai ya faɗa sai da na sauka ƙasan cafet ina dariya.
"Lokacin da kika samu cikin Jidda na faɗa ma kawu Abba da Tariq? Kin san me Abba ya ce? Bai ba ni zarafin mgana ba ya cigaba da faɗin" Cewa ya yi wai ashe dai da gaske ina son aure ashe ƙwan haihuwa ne kunshe a cikina da ba a barni na yi auran nan ba da Allah kaɗai ya san in da za kai wannan ƙwan haihuwan."
Ia riƙe da cikina ina dariya na ce"To sai ka ce musu me? Domin ni a baya bai taɓa faɗa mini sun yi haka da su ba. Shima ƙasan cafet ɗin ya sauko kusa da ni yana faɗin" Me kuwa? Na ce wallahi ai kun kyauta ma kanku da kuka yimin yaƙi kan aurena da Sadiya. Tariq kuma ya ce Allah ya shiryeka Yusuf ban san yaushe ka lalace haka ba."
Ina kallonsa na ce" Gaskiya nima na san ka lalace ni ba haka na aure ka ba." Kansa ya saukar mini a saman kafaɗata yana faɗin" Ke kika lalatani Sadiya. Kika koyar da ni abin da ban sani ba kika buɗe mini baki. Kin san an ce da Namiji ya san mace bakinsa ke buɗewa." Mintsinin hannunsa na yi ina faɗin" Ni kar ka mini sharri. Na koyar dakai ko ka koyar da ni? Na faɗa ina kallonsa sai ya ɗago shima ya na kallona kafin ya riƙe mini hannuna guda ɗaya ya matse cikin hannunsa ya na faɗin" To shike nan na ji mun koyar da juna shike nan? Sai na gyaɗa kai matsowa na yi kusa dashi na matse shi rabin jikina na kan jikinsa ina faɗin" Wai Tarig ɗin sun koma ne? Yana shafa bayana zuwa ƙuguna ya ce" Ina jin kamar sai cikin Weekend ɗin nan za su koma. Faridarsa ma ta ce na gaisheki ranar na sha'afa ne."
Kai na jinjina ina gyara zaman kaina a saman ƙirjinsa lokaci ɗaya ina faɗin" Yallabai. Kayan abinci fa sun ƙare." Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya ce"Bari mu gani zuwa a shiga wannan satin. Sauran da ya rage zai kai mu lokacin? "A'a gaskiya. Ko su indomie duk sun kare lemun su Jidda na makaranta ba ko rabin katan bai kai ba."
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Allah zai rufa asiri. Amman duk kudaɗen hannuna na saka su cikin aikin nan kuma ba a ma gama ba ballatana su yi mana payment amman dai na yi magana da su za su fara ba mu half ɗin in angama aikin sai su cika mana." Ɗago kaina na yi ina kallon shi kafin na ce"To wancan payment ɗin na ku da suka ce tun wancan watan fa? Shuru har yanzu? Ɗan girgiza kai ya yi kafin ya ce"Wallahi kuwa. Kin san yanayin aikin namu ace yau a ce kuma gobe. Sai dai kawai ranar da muka gani ko jiya mun yi mgana da P.A ɗin kwamishina ya dai ƙara bani hakuri kin san sha'anin gwamnati sai haƙuri kawai."
Gyara zama na yi ina kallon shi kafin na ce" Allah ya sa su biya ku a wannan watan" ya amsa min da Amin Amin domin muna cikin bukatar kuɗi mganar asibiti na yi masa sai ya kalleni kafin ya ce" Ranar monday ne ko? Sai na shirya mu je taren ko? Sai na jinjina kai kafin na ce"Allah ya kaimu." Dukkanmu sai muka yi shuru hankalin mu kuma sai ya koma kan TV ɗin da ya ke shi kaɗai tunda hankalimu ba shi a wajen gabaɗaya.
Har na sha'afa da mganar sai na tuna da sauri na kalleshi ina kiran sunan shi.
"Yallaɓai na"
"Uhm"
"Ashe kuma Yaya Usman aure zai ƙara?
"E. "
Haka kawai ya ce mini ba tare da ya kalleni ba. Hankalinsa na kan kallo ni kuma sai na ƙara gyara zama ina faɗin" Shi ne ba labari kuma? "Labarin me? "Auran mana. Ko kai ban ji a bakin ka ba."
Sai a lokacin ya juyo ya kalleni kafin ya ce"Bikin ya zo ne ba ki ji ba? Sai na girgiza masa kai jinjina kai ya yi kafin ya maida hankalinsa kan kallon shi lokaci ɗaya yana faɗin" Ba ma yanzu ba ne. Ina jin sai nan da wattani huɗu sai yarinyar ta gama karatun ta ta dawo tukunna za a yi bikin."
"Au daman yarinyar ba anan take ba?
"E. Ɗiyar ogansa ce a wajen aiki. Tana london ta na karatun masters ɗin ta amman ta kusa dawowa in ta dawo ne za a yi bikin."
Ƙara matsan Yallaɓai na yi domin ina son na ji labari kai tsaye na ce" Ikon Allah. Kuma ya na sonta? Wannan karon wani kallo Yallaɓai ya yi mini da ya sa na yi shuru ina yar dariya kai ya girgiza kafin ya ce"Ban san wannan ba. Shi kaɗai zai iya amsa miki wannan tambayar.".
Ina dariya na ce"Kai ma za ka iya."
Bai ƙara mgana ba sai na kwantar da kaina saman kafaɗarsa ina faɗin" Na yi mamkin da na ji zai ƙara aure. Duk irin yadda suke son juna shi da Anty Zabba'u.'' Yallaɓai dai ya lura da mgana a bakina sai bai biye mini ba sai kawai ya kallleni kafin ya ce" Uhm" Ina shafa kirjinsa na ce"Wallahi. An ce fa ta yi yaji ta na kano yanzu haka. Gaskiya ban ji daɗi ba. Kuma har yau shi Yaya Usman bai zo biko ba ya kyauta kenan?
Yallaɓai ya muskuta kafin ya cire ni daga jikinsa yana kallona cikin buɗe ido ya ce" Sadiya a ina kika ji wannan maganar? Kai tsaye na ce" Yau da na je gidan Halima ta ke faɗa mini fa. Ko ba a yi ba ne? Kai ya girgiza kafin ya ce"Ban sani ba. Domin ni a bakin ki ma na ji wannan mganar."
Da sauri na ce"Au wai ba ka sani ba? An ce ko ba ta a fatakol. Ta dawo kano domin Halima ta faɗa mini bai faɗa mata mganar auran ba sai da aka saka rana da ta ji shi ne ta tada hankalinta ina ga dalilin yajin kenan." Ƙura mini ido ya yi yana kallona nima ko ina kallonsa ban damu ba na cigaba da faɗin" Gaskiya Yaya Usman bai kyauta ba. Bai kamata ya yi ma Anty Zabba haka ba an zama ɗaya an tara iyalai yayansu biyar fa aurensu sama da shekaru ashirin a ji Anty Zabba ta yi yaji saboda zai ƙara aure ai wallahi sai an zage shi duk da ban sani ba ai na san ba ta rage shi da komai ba. Wani lokacin ku Maza ba ku da adalci in za ku ƙara aure a ƙokarin ku sai duniya ta fahimci mace ta gaza ne ya sa kuke son ƙara aure"
"Shi ya ce miki saboda Zabba'u ta gaza ne ya sa ya ke son ƙara aure?
Ya katse mini mgana nima ko na taso masa da cewa" E mana saboda ya yi munafunci miye a ciki in ya na son ƙara aure da ba zai faɗa mata ba sai da mgana ta kamkama bayan ma an saka rana? A hankali ya ce" To ai Ogansa ne ya bashi yarinyar kuma akwai girmamawa a tsakaninsu shi ya sa ya karɓa".
Mamakin Yallaɓai ya kamani yadda ya zauna ya na kare ma ɗan'uwansa..
"Duk da haka dai ai yana so ne ya karɓa shi fa namiji ba a yi masa dole Yallaɓai na. Kuma tun da har ya amsa me ya sa bai zo gida sun tattaunawa da matarsa ba? Tsakani ga Allah bai kyauta ba a ce sai da aka saka rana ya ke gaya mata ko ni ce zan yi abin da yafi nata. Yanzu ta koma gida in an zauna ana mgana sai a ce saboda mijinta zai yi aure ta tada hankalinta ta kasa zaman gidanta ahalin abin ba haka ba ne shi ne bai kyauta mata ya yi mata rashin adalci bai kuma kalli zaman auren su na tsawon shekaru ba"
Yadda na ɗau zafi kamar ƙanwar Zabba'un abin ne ya ɓata mini rai ganin Yallaɓai na nuna abinda ya yi ɗin dai dai ne. Kallona kawai ya ke yi ya ina ta faɗa sai kawai ya juya ya jingina da kujera ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa amman bai yi mgana ba sai ni ne da na gaji na kalle shi ina faɗin"
Yallaɓai ba ka ce komai ba?
Kai tsaye ya ce" Me zan ce! In yi mgana ki ce ina kare masa saboda yana ɗan'uwana ko in ce ita ba ta kyauta ba ki ce sabo da ni Namiji ne ko? Baki kawai na saki ina kallon Yallaɓai ganin kamar ya ɗau lamarin da zafi. Ban gama mamaki ba na ji ya na faɗin" Ke ba ki san abin da ya faru ba kin bi kin zauna akai har kina zargin wani bai kyauta ba a mata da miji ba ka jin bangare ɗaya ka yanke hukunci shin shi kin ji na shi ne! Kin san me ya faru tsakaninsu da ya sa ta yi yajin? Kuma ban yarda Yaya Usman bai faɗa mata ba sai dai in ita ce ta ƙi amincewa tun farko daga baya da ta ga abin da gaske ne sai kuma ta sauya labarin. Mganar yaji kuma ita ce ta ji kunya miye na ta na yin yaji? Auransu shekara ashirin ko sakin ta Yaya Usman ya yi gidan nan ya zama nata. Hakan da ta yi ta nuna cewa ba za ta iya rufa ma mijinta asiri ba ta gwamace ta koma gida ta fallasa komai domin a san halin da suke ciki a yi musu dariya kuma wallahi kanta ta rage ma ƙima in ma tana tunanin ta yi ne domin samun wata daraja ko ɗaukaka in ta yi hakuri wallahi tallahi wata ba za ta zo ta fita ba ba kuma ina kare masa domin yana ɗan uwana ba sai domin na san halin shi adali ne kuma jajircettace ai yana sonta ya aureta ba zai zama domin ta gaza ba ne zai ƙara aure sai domin auran na cikin kaddaran Rayuwansa"
Idona a kan Yallaɓai ganin yana ta rattabo mgana. "Hmm " Kawai na ce kafin na yi shuru shima shurun kawai ya yi yana cigaba da kallon shi ban sake mgana ba ina auna mganarsa a zuciyata ba wani saboda yana ɗan'uwansa sai kuma domin ya na Namiji amman ko Anty Zabba na da laifi shima Yaya Usman ɗin ya na da laifi ni ko kwana za mu yi anan wajen maganganun Yallaɓai ba za su sa na daina ganin laifin Yayansa ba.
Haɗe rai na yi har ina matsawa can nesa da shi kallona ya yi kafin ya yi ɗan mirmishi ya na faɗin" Ni ban kare masa ba. Gaskiya na faɗa miki. Sannan ki cire wannan tunanin na in namiji zai kara aure wai gazawar ta gida ce ba haka ba ne saboda shi aure da mutuwa duk ɗaya ne ba ka sanin lokacin in Allah ya kaddaro maka ne ba yarda za ka yi amman ba nufin ta gida ta gaza ba."