Kenza eBookz

Turken gida book1 by janafty - Chapter 16

Turken gida book1 by janafty - Chapter 16

Turken gida book1 by janafty Chapter 16: Turken gida book1 by janafty Chapter 16. Taɓe baki na yi kafin na ce" Haka kuke nunawa shi ya sa muka ɗauka haka…

3,315 words

Taɓe baki na yi kafin na ce" Haka kuke nunawa shi ya sa muka ɗauka haka ɗin ne." Na faɗa har ina hararan shi sai kawai ya yi yar dariya kafin ya ce"To ke miye naki a ciki! Tun da ba ni ne zan ƙara auren ba." Ina mele baki na ce" Da nawa a ciki tunda mace ce ƴar uwata kuma muna aure a zuru'a ɗaya."

Kawai sai ya fara mini dariya na kalle shi ina faɗin" Na zama abar dariya ne? Hannu ya ɗaga sama kafin ya ce"Ko ɗaya gani na yi har matsawa kika yi daga kusa da ni. Ni ne Yaya Usman ɗin? Tabe masa baki na yi sai ya fara matsowa kusa da ni yana faɗin" Yanzu dai Yaya Usman bai yi ma Zabba'u adalci ba ko? Mata ban san me namiji zai yi ya iya muku ba. Auran su sama da shekaru ashirin bai yi tunanin ƙara aure ba sai yanzu. Da ace ya ce zai yi a farkon auren su sai a ce daga yin aure zai ƙara mata kishiya in ya bari sai ta ɗan sha miya sai a ce sai da ya ga ya sun gama wahala tare ya yi kuɗi zai saka mata da kishiya in kuma ya bari ta manyanta sai a ce ya ga ya gama moran ƙuruciyanta zai ƙara mata kishiya. Mara adalci butulu duk kalaman ku ne. Na rasa ko wani yanayi ne na kishiya zai taɓa zama dai dai a wajen ku.'

Kafin ma ya ƙariso na yi saurin miƙewa ina faɗin"Ba wannan yanayin domin ba macen da ke son zama da kishiya. Ko a gidan Annabin Rahama matansa sun yi kishi ballatana mu."

Shima miƙewan ya yi yana yar dariya kafin ya ce" To wai an ya ni za ki bari na ƙara auran nan? Wata uwar harara na wurga masa kafin na ce" Ai na san ka na da ra'ayi. Allah ya ba da sa'a. Ta zo mana tunda ba kaina za ta zauna ba "

Na yi wucewata na barsa nan tsaye sai ya biyo ni yana dafani kamar irin yadda ƙawaye ko abokai suke yi "Ba yanzu ba. Sai na zama mai kuɗi lokacin kin zama Gwaggo sai na auro yar shilla mu ƙarishe rayuwarmu tare ko? Da gwiwan hannuna na tokare masa ciki ya yi gefe yana dafe cikinsa fita na yi daga falo ina mai buga masa ƙofa. Bai biyo ni ba sai da ya tsaya ya kashe kayan wuta gabaɗaya ni daman ɗakin yara kawai na leka na ga sun yi barci sun bar wuta akunne Jidda ta bar littafanta nan ƙasa barci ya ɗauke ta. Ta shin ta na yi ta koma saman gado ni kuma sai na kwashe littafanta na ɗora mata saman drower ɗin su na tashi Baby ta je tiolet ta yi fitsari sannan ta dawo na kwantar da ita na sake tofa musu addu'a na kashe musu wuta na rufo ƙofar ina fitowa muka haɗe da Yallaɓai na dauƙe kai na ƙarisa wajen makashin wuta na kashe duhu ya bayyana. Na ji takunsa ta baya na ban anƙara ba na ga ya ɗagani sama yana nishi nishi. Wuntsila kafa na fara ina faɗin" Ni ka sauke ni"

Na faɗa ina tura masa baki, shi kuma ya na faɗin" An ki ɗin" Wuntsila kafa na yi da sauri muka yi baya kamar zamu faɗi shi ya sa ya sake ni yana dafa bango. Dariya na saka masa saboda akwai duhu har bayansa na bige bango. "Wassh.." Haka ya faɗa, ni kuma sai na kwashi gudu ina jin sa ya na faɗin" Sadiya ki tsaya anan wajen." Ƙofa na buɗe na gudu bedroom ɗin mu ina faɗin" In kana da karfi ka kamani.".

Ina shiga na kashe hasken ɗakin duhu ya bayyana ya na shigowa ya fara kiran sunana ni kuma ina danne dariyata. "Yarinya in na kama ki za ki sha wuya fa."

Motsina ya ji ya fara laluɓata ina gudu muna zagayen gado daga karshe mune har saman gado. A ƙarshe dai Yallaɓai ya yi nasaran kamani ina ta dariya gabaɗayanmu muka baje kan gado muna sauke numfashi. Muna kuma kallon juna acikin duhun ɗaki ni ce na ganganra na hau jikinsa na rike masa duka hannuwansa biyu na duka ina sumbatar bakinsa. Shima ya na tayani daga karshe. Da ya ke ya fini karfi tuni ya ƙarbi ragamar lamarin ya mirgina da ni na dawo ƙasan sa shi kuma ya kama ni a hannu tuni muka lula cikin irin ta mu kyakyawan duniya ta ma'aurata irin mu masu marmarin juna da muradi a kullum.

*****

Washegari ta kama jumma'a ne. Yara sun tafi makaranta Yallaɓai kuma an kira shi ya fita office tun safe sai ni kaɗai a gida. Tara na safe Saude ta zo yau gyaran kitchen na ke jin yi sai na ce ma Saude ta gyara sauran ɗaku nan ni kuma sai na gyara kitchen. Ina can ina gyaran wayata na ɗaki ana ta kira ban sani ba. Da ya ke Saude iyakarta gyaran falon farko da na biyu sai ɗakin yara da kitchen sai wanke tiolet ni na ke gyara ɗaki na da kaina sai haraban gidan bayan kwana biyu ko uku haka.

Ni na ce ta shiga ɗakin da na ke sauke baki da ke kallon Bedroom ɗina ta gyara mini sai ta ji kamar ana ta kiran wayata sai ta ruga kitchen ta na cewa" Anty na ji kamar ana kiran wayarki a ɗakin ki." Sai na sauke Towel din da nake goge gogen na nufi cikin ɗakina sanye na ke da riga doguwa amman iyakarta gwiwata da kaɗan kwalliyar safen da na yi ma Yallaɓai ne kafin ya fita.

Ina zuwa na ɗau wayata da ke saman gado na yi mamakin ganin kiran Ya Auwal har sau uku shi da kira ɗaya ya ke yi shi da Yaya Hamza in kin zo kin ganni sai ki kira su daga baya ganin kiran sa har uku sai na ji tsoro ina shirin bin bayan kiran shi sai kuma ga kiran shi ya sake shigowa da hanzarin na ɗaga.

"Yaya Auwal"

Haka na faɗa cikin fargaba daga can bangaren da sauri na ji ya ce"Sadiya kina asibitin ne? Ya jikin Alhajinmu na mu?

Cikin mamaki da rawan baki na ce" Wani asibiti ku. Kuma? Alhajinmu ba shi da lafiya ne? Cikin mamaki ya ce"Ba ki sani ba! Dazun nan Yaya Abubakar ya kirani ya ce Gwaggo ta kira shi a ruɗe Alhajinmu ya faɗi. To mun sake mgana ya ce ga shi sun isa asibitin mun rabu kan zai sake kirana amman shuru kuma na yi ta neman layin sa ban samu ba."

Cikin tashin hankali na ce"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Wallahi ban sani ba. Ba wanda ya kirani Ya Auwal."

"To ki yi maza ki shirya. Ki kira ki wayar Gwaggo ki ji asibitin da suke kin ji ko?

Sai na amsa masa shima ya ce daman suna shirin tahowa ne da ya bari sai gobe asabar amman tunda ga wannan matsalan suna nan tafe in sha Allahu. Muna gama mgana hankalina tashe na kira wayar Gwaggo ba ta ɗauka ba sai na kira ta Yaya Abubakar amman ba ta shiga ba sai na kira Rahila ita na sameta abin mamaki suna asibitin tare da Ya Muntari shi ta ba ma wayar ma ya faɗa min asibitin da suke.

Hankalina duk ya tashi Alhajinmu na da hawan jini amman ya daɗe bai tashin masa ba sama da shekaru biyar. Bayan rasuwan Mama ne ya kamu da hawan jinin. A gaggauce na yi wanka na shirya na kira Yallaɓai ina faɗa masa ya ce gashi a hanyar Rano amman zai dawo da wuri mu haɗu a asibitin. Saude na bar ma gidan na ce ta dafa musu sauran taliyan da ta rage ita da su Jidda. Ta kuma tsare min gida har in dawo Alhajinmu ke asibiti ba lafiya.

Cikin yar damuwa ta ce" Sai kin dawo Anty. Allah ya bashi lafiya" na amsa mata da Amin tsabar sauri sai da na fita na tuna jakar da na ɗauka ba kuɗi a ciki sai da na koma na sauya wata jakar fitar ta sauri ce kayan jikina doguwar rigar atamfa ce sai na saka dogon hijabi Jalbab. Adaidaita na tara zuwa asibitin na kuɗi ne ban ƙara razana ba sai da na kira Rahila ta ce suna Emergency a firgice na tambaya aka kwanta ta mini

Duk da ina cikin firgici na yi mamakin ganin kaf ƴan gidanmu a wajen kowacce da mijinta har da Ma'u Alhajinta da su ake shiga ana fita. Yaya Aina ce kawai ba mijinta a wajen amman har da Mijin Yaya Balki da na Yaya Murja. Yaya Abubakar da zaituna suna wajen. Ga Rahila ga Ya Muntari. A ƴan ɗakin mu ba kowa tunda Amina na kaduna ƙila ba ta sani ba ni ce kuma a cikin su ba wanda ya kirani amman sun iya kiran Ma'u saboda tsabar munafunci.

Raina ya ɓaci da haushi shi ya sa daga su har mazajen na su ba wanda na ce ma sannu. Ina ji Rahila na kiran sunana na wuce zuwa in da Gwaggo ke zaune na duka ina gaisheta ta amsa min cikin kulawa da casabaha a hannunta.

"Ya jikin Alhajinmu Gwaggo? Kai tsaye ta ce" Da sauƙi sun ce jininsa ne ya yi sama sosai nunfashin dakyar ya ke fita amman sun saka masa Oxygen yanzu ba daɗewa." Ido na zaro ina faɗin" Innalillahi." Sai tadafa kafaɗata kafin ta ce"Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu Alhaji zai tashi."

Sai na jinjina mata kai ina maida kwallar da ta kawo mini mutuwar Mama kawai na ke tunawa.

"Gwaggo shi ne ba a samu wanda zai kirani ya faɗa,mini ba? Yanzu ɗin ma ba domin Yaya Auwal ba da ba zan sani ba kenan? Cikin lallashi da damuwa ta ce" Ki yi hakuri hankula a tashe suke. Abubakar kawai na kiran suma yan'uwan na ki ki yi musu usuri sun shiga ɗimuwa" Sai ban ce komai ba amman a raina na ce a dimuwan aka kira wanda ake so.

Ba bari a shiga in da Alhajinmu ya ke Yaya Abubakar ne kaɗai da su Ya Muntari ke zirga zirga. Zama na yi kusa da Gwaggo ba wacce ma na kallah balle in yi mata sannu har Yaya Abubakar ban gaisar ba sabida ya bani haushi har da ya ganni ya na ce min" Ke sai yanzu kika iso? Cikin gatse na ce" E. Sai yanzu aka faɗa mini" Hankalinsa ya yi can bai ma jini ba Rahila ce ta zo ta zauna kusa da ni muka gaisa Yadda ta ga na haɗe rai ne ya sa ba ta jani da magana ba.

"Hala Yallabai baya nan ne? Kai tsaye na ce"Lokacin da na ji labarin abin da ke faruwa ya fita" Sai ta yi shuru kafin can ta ce"Ki yi hankuri ni kaina hankalina ya tashi na manta da kiran ki." Wani kallo na yi mata amman ban iya mgana ba.

Muna nan zaune jugum jugun har wajen azahar sai da aka cire ma Alhajimmu iskar Numfashi tun da sun ce numfashinsa ya daidai ta. Sannan suka maida shi ɗaki na musamman da Mijin Ma'u ya biya duk na ji Yaya Abubakar na faɗin Yaya Hamza ya turo kuɗi shi da Yaya Auwal amman kuma mijin Ma'u ya biya komai. Ina kallo suna ta yi masa godiya su Yaya Murja har tana faɗin" Allah ya saka masa da alheri ba domin alherin Ma'u a gare shi ba yaushe har zai riƙa yi mana Hidima haka? Ma'u ƙi kara yi masa godiya kin ji ko" Sai ta amsa da toh kawai. Ban yi wani mamaki ba sanin halin su balle Yaya Murja akwai son abin duniya ita kuma Ma'u in ta fahimceka ta san yadda za ta riƙe sosai.

Sai bayan an kai shi ɗaki na musamman ne aka bar mu muka shiga yana barci amman Alhajinmu duk ya rame ya faɗa. Daga gani ya daɗe da ciwo a jiki bai faɗa ba an ce mu bar shi ya samu hutu sosai sai muka fito dukkanmu zuwa kofar ɗakin muka zauna saman kujerun wajen. Mijin Ma'u ya yi ma Gwaggo sallama zai tafi ita kuma ta tafi raka shi. Sai bayan sun wuce ne Ya Balki ta kalleni taba faɗin" Sadiya ya gida? Ɗazu kin zo hankula ba a kwance suke ba ba a gaisa ba."

Sai na ɗan saki fuska muka gaisa buɗe bakin Yaya Murja sai cewa ta yi" Duk da haka ta ganmu amman ta fi ƙarfin ta ce mana sannu." Nima sai na kalleta kafin na ce"Saboda me zan ce muku sannu? Kun ware ni a cikin dangi ba wacce ta iya kirana ta faɗa mini halin da ake ciki sai Ya Auwal dake Abuja ne ya kirani ya faɗa mini. " Yaya Balki ta ce"E ba a kyauta ba to ki yi hakuri. Nima Ma'u ce ta kirani ta faɗa mini ta ce itama Yaya Murja ce ta faɗa mata.'

Shekeƙe na kalle su kafin na taɓe ba ki na ce"Ai da ya ke Ma'u ce ake son ta sani an kirata an faɗa mata ba shikenan ba." Rahila na taka min kafa wai in yi shuru cikin masifa na ce"Sai kin ƙi faɗan gaskiya! Wa na ke tsoro? Gwaggo ba ta nan ta na ciki wajen Alhajinmu. Ya Muntari ne a wajen ya kirana sunana ya na faɗin" Asibiti ne fa nan ba gidan biki ba. Ku bari ku koma gida mana."

Yaya Murja kuma sai ta taɓe baki ta ce"To daman ai mun san baki tsoron kowa mara kunya. Hassada ce da kishi saboda ta ga Ma'u ta riga ta zuwa. An ce ki yi hakuri kuma sai ki na neman gaya mana mgana" Anty Aina ta tsawatar ta ce a bar mganar ni ko ba na barin ta kwana na ce"Allah ya tsari Sadiya me Ma'u ta mallaka a duniya nan da ni ban da shi sai na yi mata Hassada! Ai ba ta kai ba tukunna dai."

"Zan fa ci ubanki Sadiya ni ba tsaran ki ba ne wallahi."

Zan sake mgana Anty Aina ta daka min tsawa ta na faɗa min" Wai ba na ce ki yi shuru ba ne Sadiya? Kaina na kawar gefe ina kaɗa kafata cikin bacin rai. Yaya Balki ta ce"Ita Yaya Murja saurun fusata ita kuma Sadiya rashin kunya. Alhajinmu na kwance ba lafiya ma ba za su fasa ba."

"Ba za su fasa ? Me ya faru?

Yaya Abubakar ya faɗa yana ƙariso wajen tare da Ma'u sun jero Ba wanda ya yi mgana sai Zaituna.

"Sadiya ce da Anty Murja suke cacan baki."

Yaya Abubakar ya kalleni ya kalleta kafin ya ce" Me ya faru? Anty Balki ce ta maida masa yadda aka yi kawai sai ya juyo yana kallona kafin ya ce" Ni ne nan na kira Murja na faɗa mata na kuma ce ta kira Ma'u da sauran ta faɗa musu. Tun da sun ce ki yi hakuri sun yi kuskure ba shike nan ba? Ko ke shikenan ba a baki hakuri ki hakura?

Ko kallonshi ban yi ba sai da na ji ya ce"To kar ma ki fasa. Ke daman ba ki son zaman lafiya ko da yaushe cikin ƙananun mganganu kike." Ɗagowa na yi ina kallonsa cikin ɓacin ran dake cikin idanuwana shi kuma sai ya juya yana ma Ya Muntari mgana.

"Ka na ji suna hayaniya ba ka tsawarta musu ba?

Kai tsaye ya ce" Na yi mgana sun ki ji shi ya sa na kyale su. " Kawai sai ya juya ya na kallona kafin ya ce" Duk wacce ta san hayaniya ya kawota ta tashi ta ƙara gaba. Mu lafiyan mahaifimmu muke nema ba tashin hankali ba."

"Ka yi hakuri ya Abubakar. Sadiya kema don Allah ki yi hakuri. Har ni na kira wayarki ba ta shiga."

Ma'u ta katse surutun na shi. "To kin ji ma." Ya faɗa ya na kallona dakyar na iya danne ɓacin raina na kalli Ma'u ina faɗin" Ya wuce." Sai ta yi mini mirmishi na mayar mata da yake. Kusa damu ta zauna amman gefen Rahila. Shuru kawai na yi ina danne yanayina ni fa daman da Yaya Murja da Yaya Abubakar haushin su na ke ji tun kan abin da ya faru. Kuma har gobe na san suna bayan Ma'u ne. In da suka ijiyeni nima nan na ijiye su.

Kiran wayar Yallaɓai ya sa na tashi na bar wajen. Yana tambayanta ya jikin Alhajinmu na faɗa masa da sauki da yadda ake ciki. "Allah ya ƙara sauki muna idar da sallar jumma'a zan taso kin ji ko? Ban da damuwa ok? Sai na gyaɗa masa kai kafin ya cigaba da faɗin" Yara fa! Ina kika kai su? "Suna gida tare da Saude." Sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Sai na dawo."

Da haka muka yi sallama. Ganin har azahar ta yi sai na fita haraban asibitin na tambayi wata nurse masallaci sai ta nuna mini. ga mata nan suna alwala mazan dai ina ga waje za su fita su samu sallar jumma'a nima sai na bi bayansu na yi alwala muka shiga masallaci na yi sallah na zauna ina addu'o'i bayan na shafa sai na kira wayar Amina sai ta ce minI ita Yaya Aina ta kira ta faɗa mata mijinta baya nan amman in ya dawo in sha Allahu suna tafe gobe na ce Allah ya kaimu.

Muna waya Khaleesat na kirana bayan na katse sai na kirata jikin Alhaji ta tambaya na ce da sauƙi ya na barci ita ke faɗa min suna hanya na yi musu fatan isowa lafiya. Na daɗe a masallaci sai da Rahila ta kirani ta ce ko na tafi ne? Na ce a" a ina masallaci.

"Oh mu ai nan muka yi tamu sallar. Ki zo ga su Baba Aminu nan sun iso."

Sai na ce mata gani nan zuwa. Ji fa har mutanen jihar katsina sun ji labari sun iso amman ni ana raina min wayau. Kuna ina da tabbacin cikin su ne wata ta kira su ta faɗa musu. Na fito daga masallacin zan wuce bangaren dakin da Alhajimmu ya ke na ci karo da Baaba Asiya ta na ta neman ɗakin kamar ma ta na kiran waya ne ƙila Ma'u take kira sai na ƙarisa wajenta ina faɗin" Baaba."

Sai ta juyo ta na kallona fuskarta kadaha kadahan kamar yadda muka saba karɓan juna tun bayan faruwan rushewar auran Ma'u da Yaya Hamza da na zama ni ce sila."

"Yauwa. Ma'u bari ma ga Sadiya na gani."

Daga haka ta katse wayarta. Da yar jaka a hannunta da kayanta a ciki.

"Sannu da zuwa Baaba"

"Yauwa dai."

Sai na mika hannu zan karɓi jakar sai ta hanani ta wuce gaba tana faɗin" Ina ne ɗakin da aka kwantar da Yaya Sulen? Ban damu ba na wuce ina faɗin" Ciki ne." Ba tun yau ba ni na san ta tsane ni ita da yarta. To nima dai ɗin ba wani son su nake yi ba shi ya sa ban taɓa damuwa ba matar da na san ba ta ƙaunar uwata ina zan taɓa ganin farinta. Ta bakin Hajiya Dubu da ke yawan faɗin" Asiya ki daina wannan dabi'un naki karki tsufa kuma tsufar ta zo ta yi miki gardama." Allah ya jiƙan Hajiya Dubu da gafara. Mutuwarta da mutuwar Mama sai nima na mutu zan iya mantawa da su.

Muna tafe ina gaba ta na baya har zuwa ɗakin da Alhajinmu ya ke. Baba Aminu ne ashe da Baba Sani suka zo. Ma'u na ganin uwarta ta yi wajenta tana mata barka da zuwa. Ban ƙara ta kan su ba na isa wajen su Baba Aminu ina gaishe su.

"Lafiya lau! Dubu ce? Sai na ansa musu domin kaf gidan su Alhajinmu ba mai kiran sunansa sai dai Dubu saboda na ci sunan Hajiya Dubu ce kuma ita ɗin mai Daraja ce ta matsayin uwa a wajen su.

Readers Also Read