Turken gida book1 by janafty - Chapter 36
Turken gida book1 by janafty Chapter 36: Turken gida book1 by janafty Chapter 36. Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu…
3,303 words
Bikin bayan salla da sati uku ne. Yaya Aina ta ce ana jibi biki za mu tafi saboda Matar Baba Aminu magajiya mai yi ce ba ta wuce duk wani sha'anin mu ko ba ta zo ba ƙannen Yaya Muntari za su zo gaskiya tana da ƙoƙari daga ita har Baba Aminun suna da riƙo kan zumunci. Muna cikin hiran ne Marwa ta shigo sai dai ta ce sannanun ku gabaɗaya a ka amsa mata in da na ke zaune ta nufa tana faɗin" Umma Baby ta jiƙa kayanta da ruwa." (Daman Umma ta ke ce mini kamar yadda su Jidda ke kirana.)
Kai na jinjina kafin na ce" To ai sai ta zauna dashi. Domin ban zo mata da wasu kayan ba." Da sauri ta ce" Gwaggo ta ce a cire rigar a shanya kar zazzaɓi ya kamata." Kafin in yi mgana Rahila ta karɓe da cewa" To ba wasu kayan? In sanyi ya kamata fa" Yaya Balki ce ta yi mgana wannan karon da cewa" Sadiya ce fa da tsiyarta. Ba za a rasa wasu kayan su Baby a gidan nan ba."
Yaya Murja na gefe ta ce" Ko ba na ta ba. Ba za a rasa kayan da za ta saka kafin na ta ya sha iska ba." Muna cikin mganar Marwa ta fita sai ga Gwaggo ta leƙo ta na faɗin ita ta ce a cire mata rigar a shanya ta samu wata riga ta ba ma Marwa ta saka mata na amsa mata da to Gwaggo. Yaya Balki ce ke mganar ta ga Marwa ta yi mata girma ne a ido ina mirmishi na ce" Ai na kusa yin suruki in sha Allahu." Yaya Balki ta amsa da Allah ya sa.
"Aina can Marwa ta yi salla gidan Sadiya ne?
Ya Murja ta faɗa ta na mai kallon Ya Aina wacce ta amsa da mata da cewa" E. Tun kafin ta dawo daga makaranta ta dame ni da ni Mama a gidan Umma Sadiya zan yi salla na ce to. Ta na dawowa ta gaya ma Baban shima yana dariya ya ce to yar gidan Umma Sadiya a dawo lafiya." Ina mirmishin jin daɗi na ce" Ai wallahi na ji daɗin haka. Ni da za ku bar mini ita a wajena Ya Aina."
Yaya Balki na dariya ta ce" Topha ƴan mata ba su ishe ki ba ne Sadiya? "Ina fa suka ishe ni. Ban ƙi dozin ba Yaya Balki." Muka saka dariya gabaɗayanmu Rahila ce ta ce" Sai Ya Aina ta baki. Ki haɗa da Jidda ki riƙe gabaɗaya." Ma'u na gefe ba ta ce komai ba ta na latsa wayarta. Ya Murja na sauraran mu amma ba ta yi mgana ba Ya Aina ke faɗin Marwa za ta fara pratical a asibti kuma babanta ba zai bari ba amma don ta riƙa zuwa miki hutu lokaci bayan lokaci ba zai ce komai ba.
na marairacewa na ce" Haba Ya Aina. In kika saka baki zai bari mana." Dariya kawai ta yi ba tare da ta yi mgana ba Yaya Balki ce ke faɗin" Topha! Lalle lamarin Sadiya azimin ne. "Da gaske take yi." In ji Rahila ni kuma na juya ina rantse musu da gaske nake yi.
"To ke in kina son ɗauka shi Yallaɓan na ki na so ne?
Ya Murja ta faɗa tana kallona da sauri na ce" Haba Ya Murja na ɗauka ke mai shaidar Yallaɓai na ne. Ba Marwa ba ko wacce bai sani ba ne na kawo na ce ina so zan riƙe wallahi ba zai ce komai ba. Ballatana ma Marwa shi ya fara cewa ko za mu karɓo Marwa ne ta dawo wajen mu da zama Sadiya? Shi ya sa ma kika ji na yi mgana."
"Oh."
Kawai ta ce ba ta ƙara mgana ba. Yaya Balki ce ta karɓe mganar da cewa" Kuma fa hakane. Yallaɓan na ki ba shi da matsala gaskiya." Rahila ma ta amsa da cewa" Shi da ke son yara. Allah ne dai bai bashi da yawa ba." Ita dai Yaa Aina ba ta ce komai ba sai dai ta na ta mirmishi daga karshe ta kashe mganar da cewa babanta ba zai bari ba ni kuma na ce zan sako Yallaɓai a gaba mu zo tambaya Rahila na dariya ta ce" Shike nan ma an kashe boss ɗin."
Muna ta dariyan mu cikin nishaɗi. Daman fa ko haɗuwa aka yi waje ɗaya Ma'u da Ya Murja sun fi tsame kansu gefe ana hira sai jifa jifa suke saka baki tun ballatana ma in ina wajen. Ni kuma ban damu da su ba in suka sako ni na yi da su in ba su sako ni ba na juya na yi da waɗanda ke yi da ni. Zaitunan Yaya Abubakar tana ɗakin Gwaggo tun da ta zo sai barci kamar wata kasa Yaya Balki ta ce Allah ya sa ba ciki ne da ita ba Ma'u ta kwashe da dariya ta na faɗin" Kuma kamar kin san ta yi yaye ba." Ya Aina ta ce" Kai wannan mata ta Abubakar. Allah ya sauwaƙe."
Ni kuma sai na kada baki na ce" Ku barta ta haihu. Iya rabon ta a duniya fa za ta haifa. " Sai Rahila ta ce kuma gaskiya ne. Gwaggo ce ta leƙo ta ce an kira salla ga ƴayanmu can har sun yi alwala mu ma sai mu tashi jin haka yasa muka firfito domin yin alwala ni ban samu buta ba sai na zauna ina jira Anti ta gama da na ta butan ta bani sai da ta idar da alwalan sannan ta kawo min na amsa ina faɗin" Su Anti an zama yan mata."
Ta na dariya ta rufe fuska kafin ta ce" Anty Sadiya ina goron sallah na." Kai tsaye na ce" Gorom sallah kike so? Sai ta gyaɗa min kai. Ni kuma sai na rausayar da kai kafin na ce" Goron salla ai a gida ake ba da wa Anti. In kina son goron salla sai ki zo gidana ki karɓa. Yanzu ma kin makara salla ta wuce sai dai kuma ta layya in muna raye."
Ita Anti ba ta damu da mgana ta ba cikin dariya ta ce" Kai Anty Sadiya." Nima ina mata dariyan na ce" Ƙwarai Anti. Salla layya in kina son goron salla ki zo gidana da wuri ni kuma sai na cika miki jaka da kuɗi." Gwaggo na bakin famfo tana alwala ta na jin mu ta dai yi mirmishi ba ta saka mana baki ba. "To Anty Sadiya in sha Allahu zan zo. Wannan salla a gidan Umma Ma'u na yi shi ya sa." Ina mata mirmishi na ce" To ai shiken nan na ma san Ma'u ta cika miki jaka da goron sallah ba ki buƙatar tawa ko? Har ga Allah ni a wasa na yi mganar kawai sai gani na yi Ya Murja ta bankaɗo labule ta fito da hijabi a jikinta da alamun ta idar da salla ne kallona ta yi daga sama har ƙasa nima ko cikin mamaki na ke kallonta sai kawai ta daka ma Anti tsawa ta na faɗin ta wuce ta je ta yi sallah sai yarinyar ta wuce ɗakin Gwaggo da sauri. Kamar zan yi mgana sai na fasa na fara tafiya wajen famfo Gwaggo ta taso za ta shiga ɗakinta.
"Ke Sadiya.."
Ya Murja ta yi mini kira cikin gatsali sai na juya ina kallonta cikin mamaki. Ba ma ni kaɗai ba hadda Gwaggo.
"Me ya faru Ya Murja?
Na faɗa ganin kamar tana sakin huci kawai sai ta nuna ni da yatsa ta na faɗin" Daga yau in kina so ki yi min rashin kunya ki zo gare ni kai tsaye ne ba sai kin rakuɓe a jikin ƴa' ta kina gaya min mgana ba. Ba na son rashin kunya." Galala na yi da baki ina kallonta kafin na samu zarafin mgana Gwaggo ta tsawarta da cewa" Murja me kuma ya kawo wannan mganar?
A fusace ta ce" Ba ki ji mganganun da ta ke faɗa ma Anti ba ne? Ta nuna kamar da gayya ne ban tura Anti gidanta ba na tura ta gidan maƙiyarta Ma'u ba. Duk na fahimci mganganunta." Gwaggo ta yi tsaki kafin ta ce" To ni ban ji haka ba. Mganar su kawai suke yi na tsakanin uwa da ƴa." Nan fa Ya Murja ta ce ita fa k a taufau da ita na ke yi. Ƙara nuna ni ta yi da yatsa kafin ta ce" Daman ba tun yau ba kin sha faɗan wai na fi son Ma'u da ke da ita kawai na ke shiri yayana ma gidanta suka sani. To yadda kika faɗan ne domin Ma'u ta fi ki ladabi da biyayya sannan ita ta ja ƴa'ƴana a jiki ke kuma da ba ƙi kaunar su ba ki ja su a jiki ba. Kin ga ko kar ki ga laifin su in ba su je in da kike ba. Gidan kuma Ma'u da ki ke jin haushin suna zuwa yanzu suka fara zuwa. Sai dai baƙin ciki ya kashe ki Sadiya"
"Murja me ye haka don Allah.?
Ya Aina bayan ta fito daga ɗakin Mama itama sanye da hijabi ita da Ya Balki da Rahila. Ma'u dai ba ta fito ba ni kuma tsabar mamaki ma na kasa magana. "Ya Murja Alhajimmu na ciki fa. Gaskiya wannan ba girman ki ba ne. Sadiya fa ba da ke ta ke mganarta ba." A fusace Ya Murja ta ce" Ba za ku gane ba ne. Ni na san ga in da ta dosa. To me ye na damuwa don ƴaƴana ba su je in da ta ke ba. Marwa da kika zaɓa kina so ita ai kin gayyaceta kuma ta je suma in kika nuna kina so su je ɗin za su je."
Sai a lokacin na fahimci haushina ta ke ji saboda Marwa. Kai wannan mata ta ɗoramin karan tsana. Ba na so na yi hayaniya saboda Alhajinmu kawai sai na yi mirmishin takaici kafin na ce" Ki yi hakuri Ya Murja na ga ƙin ɗau zafi har ga Allah ba da wata munafa na faɗi mganar da na faɗa ba. Amma in ta ɓata miki rai Allah ya baki haƙuri. Mganar Anti na zuwa gidan Ma'u ban taɓa sawa a kaina ba domin da ni da Ma'u duk ɗaya ne. Ke ma kuma ina so ki gane wani abu da Anti da Marwa ɗaya suke a wajena ba Bambamci."
Ina gama faɗin haka na juya na wuce wajen famfo ina taran ruwa a buta. Na san dukkansu sun yi mamakin sanyina har sai da Gwaggo ta ce" Shike nan Sadiya kin gama magana. Ke kuma Babba kwabo kin ji kunya tunda har yau Sadiya ta fi ki hangen nesa." Ganin ban kulata ba ya sa ta koma ɗaki fuu. Kuma kowa ita ya ba ma rashin gaskiya a wajen. Sai bayan da na ɗauro alwala na shigo cikin ɗakin ne Ma'u ta ke ce min" ki yi hakuri Sadiya ki fahimci Ya Murja don Allah itama ba da wata munafa ta yi miki mganar ba.'
Kallonta kawai na yi ni kam wani makircin Ma'u ne ban gani ba sai kawai na ce" Bakomai. Ita za ki ƙara ba ma hakuri saboda na ga kamar ta ɗau zafi da ni." Ina gama faɗin haka na saka Hijabi na ta da salla. Bayan na idar sai muka ci abinci na ga dai Ya Aina ta keɓe da Ya Murja na kuma san faɗa ta ke yi mata shi ne na ga ta ɗan saki ranta a raina na ce matar nan me na yi mata wai ta tsane ni ne? Muna cikin cin abinci sai ga Ya Abubakar ya shigo ganin abinci kala kala muna ci ya sa ya ce"Kai. A ina aka samo abinci nau'i nau'i haka kamar an samu sabon restaurant?
Rahila ce ta faɗa masa kowaccem mu ta dafo abinci daga gidanta sai shima ya samu waje ya zauna ya na faɗin" To shi ne ana wannan shagali aka manta da ni? Ni ne fa the head of the family" Ya Balki ta ce" Mun ɗauka Zaituna ta yi maka kyakyawan beta kafin ta fito gida"
Ta faɗa ta na kallon Zaitunan da ke ta cin abincinta jin an taɓo bangarenta ya sa ta yi saurin cewa" Laa shi ya ce in taho ba sai na tsaya na yi abinci ba." Rahila ta ce" Ehem daman na san za a rina." Yaya Aina ke faɗin" Ke kam Zaituna ban san yaushe za ki wayau ba. Ko mu kin ga mun taho ba mu yi girki ba? Ga shaida nan tunda gashi nan kina ci in da kin dafa kafin ki fito mijin ki zai zo ya na neman abinci? Kanta na kasa ba ta yi mgana ba Yaya Abubakar ya wani girgiza kai kafin ya ce" Ƙyaleta Aina ta yi lokaci ne." Daga haka kawai ya miƙe ya ce ya na ɗakin Alhaji a kawo masa abinci. Zaitunan Ya Aina ta tasa ta ce ta saka mai ta kai masa ta na fita Ya Murja ta ce" Mata kamar mai almatsutsai" Ya Aina ta ce" Lafiyan ta ƙalau iskanci ne kawai da ta samu shi Abubakar ɗin mai sanyi."
Ni dai ina jin su ban tanka ba ina ta cin abincina ni shinkafa da waken da Rahila ta dafa na ke ci su kuma su Ya Aina sun ci nawa sun kuma ci na Ma'u ita waina ce da Sinasir. Mganar gaskiya duk cikin mu Mijin Ma'u ya fi kuɗi kowa kuma ya san haka amma duk da haka dukkanmu ba za a ce muna cikin halin rayuwa ba dai dai gwargwado mazajen mu na da rufin asiri. Mijin Ya Murja ne ma sai a hankali domin ya samu matsala can kwanaki an kore shi daga wajen aiki ya fi shekara uku a gida amma dai an ce ya koma shi ya sa Ma'u ta samu dama tana taimakonta ita kuma kwaɗayi ya sa idanuwanta ya rufe. Ni ba na kyautar ganin ido ko ka gode min in na yi niyyar yi maka alheri na yi, in ban yi ba shike nan ba zan yi domin duniya ko kai da zan mawa ka yabeni ba ita kuma Ma'u daman halinta ne ta yi alherin da duniya za ta sani a yabe ta a kuma san tana yi ɗin da son nuna ita fa mijinta na da kuɗi domin in dai Ma'u ta san za a zo gida a haɗu ƙarshen kayanta a kyau da tsada ta ke sakawa. A fuska ba ta nuna wani abu amma ga ni da na san halinta ni na san ta na da halin son a sani.
Yanzu ma muna cin abincin ta na ba da labarin Alhaji Mustapha ya ce zai ba ta jari na miliyan biyar ta fara kasuwanci shi ne take neman shawarammu wata sana'a za ta fara. kowacce na faɗin albarkacin bakinta nima sai na tofa nawa na ce ta saro dogayen riguna da takalma da mayafai na mata ta fara saidawa mu gani ko za su tafi. Sai Ya Aina ta ce yauwa ta ƙara har da atamfofi da kayan yara ni kuma sai na ce kayan yara ta jinkirta tukunna zuwa gaba ta fara da waɗanan dai ta gani yadda kasuwan za ta kaya.
Cikin mirmishi ta ce" Haka ma Shema ta ce. Da ya ke mun yi mganar da ita ta waya. Ya ce dai na tsaida shawara visa na fitowa Egypt za mu je a can zan yo sarin kayan nawa in sha Allahu." Ya Murja ta washe baki tana faɗin" Ma sha Allah. Allah ya sa albarka ƙanwata." Ta amsa mata da Amin Amin. Ita kuma Ya Balki ta ce " Sai ki faɗa ma Gwaggo da Alhaji su suka albarka." Sai ta ce za ta faɗa musu sai mata fatan alheri suke yi nima na yi mata ta re da fatan Allah ya sa a fara a sa'a ta amsa lokaci ɗaya ta na kallona kafin ta ce" Amin Sadiya. Amma fa kema ya kamata ki zo ki fara wata sana'ar zama haka ba daɗi."
Wani abu ya tsaya mini a maƙogawaro. Ma'u ta bala'in raina min wayau. Kuma kawai sai su Ya Balki suka amsa da wallahi kuwa Sadiya. Rahila ce ke faɗin" Ita fa Sadiya Shagon saloon da gyaran jiki take son buɗewa" Ya Balki ta ce" To wannan ai lissafi ne me yawa. Ta dai yi tunanin fara wani abun kafin ta yi ƙarfin da za ta buɗe saloon ɗin." Duk yadda na so na yi mgana sai kuma na kasa. Da na so na mayar mata da martanin mganarta ne sai kuma na yi tunanin ina yi magana za a ce ni ce fitinanniya Ma'u ta yi min mganar arziƙi na maida shi ta tsiya
Sai kawai na kalli Ma'u nima sai na mayar mata da martanin mirmishinta kafin na ce" Kar ki damu ki maida hankali kan naki. Nima soon in sha Allahu Suprise zan ba ku." Sai ta ce Allah ya yarda ta na min wannan dariyan na ta na mugunta. Ya Aina ko sai faman mgana take yi ta na cewa sana'a ita ce mace ko da mijinki na maka komai to ka yi dogaro da kan ka ko domin wata rana. Ya Balki ta ce" Har da ma rayuwa Ya Aina." Rahila ma na ji tana fadin itama za ta fara awo a cikin gida Ya Aina ta ce kasuwanci mai kyau. ita Ya Aina tana saida kayan miya da kayan nau'in ɗanɗanon girki ita kuma Ya Balki tana saida gwanjuna. Ni ce daman ban saida komai sai Rahila Ma'u kuma daman tana nuna mijinta na mata komai sai yanzu ne ta zo da labarin za ta fara na ta kasuwamcin.
"Albishirin ku"
Na faɗa ina musu mirmishi. Na gama cin abinci tuni har na sha ruwa na yi gatsa.
"Goro fari ƙal." In ji Rahila da Ya Balki har suna haɗa baki.
"Nan da kwana uku za mu cika shekara sha biyar da aure ni da Yallaɓai na. Haka ma Rahila da Ya Muntari."
Na faɗa ina musu mirmishi. Ya Balki ta fara cewa" Ma sha Allah. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Kai ashe kun daɗe kamar jiya ne na ke ganin bikin ku fa ke da Rahila? Rahila na dariya ta ce" Sadiya ta na lissafi ni fa mancewa na ke yi. Ko da muka yi shekara goma sai da na ga sun yi walima ne na ce ma Ya Muktar yau auran mu shekaru goma Cif." Ya Aina ta ce" Shekarun suna gudu ba wuya. Allah ya ƙaro muku zaman lafiya da kwanciyar hankali ya raya muku zuru'a." Muka amsa da Amin Ya Murja ma ta yi addu'a muka amsa mata. Sai Ma'u da ta gyara zama tana fadin" Ma sha Allah. Allah ya ƙara ɗankon kauna Mrs Yallaɓai da Mrs Ya Muktar." Ni ce na amsa mata Rahila ta na jin kunya Zaituna ce ta yi karaf ta na faɗin" Sadiya akwai walima ne? Ina mata dariya na ce" Akwai amma ta iya ni da Yallaɓai ce da yara."
Ma'u ta ce" Allah? Ban damu kenan? Ina mata fari na ce" Ai kun gama na ku tunda kun yi addu"a. Ya Aina ta ce" Shi ne ko babban mgana." Zaituna na kallah ina faɗin" Tambayi Rahilan Hubby ƙila za su haɗa mana walima." Duka ta ɗaka min a cinya ta na faɗin" Sadiya ban son wulaƙanci." Kamar zan yi kuka na ce" Wai don na ce Rahilan Hubby shi ne har da duka? Rahila sai kawai ta balla min harara kunya duk ya kamata mu kuma gabaɗayanmu muka fashe mata da dariya. Sai ta ji kunya ta tashi ta fita, ta na fita Ya Balki ta ce" Daga Rahilan har Muntari masu kunya ne." Ya Aina ta ce" Wallahi ba su da hayaniya. Alhajinmu ya sha cewa tabbas an ijiye kwarya a gurɓinta."