Turken gida book1 by janafty - Chapter 37
Turken gida book1 by janafty Chapter 37: Turken gida book1 by janafty Chapter 37. Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba…
3,348 words
Ranar yini muka yi ana ta hira a yi daɗi a yi tsiya bayan mangariba Gwaggo ta ce Alhajinmu ya ce kowacce ta yi shiri ta koma gidanta yinin ya isa haka. Jin haka yasa muka fara shiri saboda tun da Alhaji ya yi mgana to dole fa kowa ta kama hanya. Ni dai Yallaɓai na kira sai ya ce bari a yi sallar isha'i sai ya zo mu tafi gida. Ma'u ta fara tafiya Alhajinta ya zo ɗaukansu ita da yara haka ya yi mana yayyafim kuɗi goron salla damu da ya'yanmu ban sam kuma nawa ya ijiye ma Alhaji da Gwaggo ba. Su suka tafi da Zaituna da ƴaƴanta za su sauke su a gida daga can na ji Ma'u na faɗa ma Gwaggo za ta biya gidan su Shema'u. Kafin ya zo daman Ma'u ta sanar da Alhajimmu da Gwaggo mganar jarin da ya ce zai ba ta su ka yi ta masa godiya da saka albarka. Nima da Yallaɓai ya zo mun je gaban Alhaji na faɗa masa nan da kwana kaɗan auran mu zai cika shekara goma sha biyar da ni da Rahila.
Alhajinmu ya yi mirmishi kafin ya ce" Ma sha Allah. Shekaru goma sha biyar masu albarka da tarin albarka zuru'a. Allah ya ƙara haɗa kawunanku. Haƙiƙa Yusufa da Muntari sun cika ƴaƴa tunda duk tsawon wannan shekarun ba su taɓa kawo min ƙaran ku da sunan kun yi musu wani abu ba hakan ma abin alfaharina ne. Allah ya yi muku albarka ya bar ku tare har jikokin ki." Kan mu na ƙasa ni da Yallaɓai muna ta amsawa da Amin Amin. Gwaggo na gefe ta na ta saka albarka kafin ta ce" Jiya ba yau ba. Allah ya ƙara muku zaman lafiya. Na tuna da Mama itama shekarunta a ƙasa kenan Allah ya jiƙanta ita da Hajiya gabaɗaya." Muka amsa mata da Amin Amin da za mu tafi shima Yallaɓai ya ba ma yaran su Ya Murja goron sallah Marwa dai ta ce za ta bi Ya Aina zuwa gida amma jibi za ta dawo. Yallaɓai ya ba ma Alhajimmu kuɗi da Gwaggo amma ban sam ko nawa ba ne. Daga nan muka yi musu sallama ya ɗauke mu zuwa gida.
Sai da muka koma gida har mun yi shirin kwanciya muna rumgume da juna Yallaɓai na shafa gashin kaina ya ce.
"Sadiya ta."
"Yallaɓai na"
Na amsa masa cikin so da ƙauna. Sai kawai ya ce" Gani na ke yi kamar jiya jiya muka yi aure sai ga shi wai mun kusa cimma shekaru goma sha biyar da aure cikin yan kwanaki ƙalilan masu zuwa." "Nima haka na ke ji a zuciyata." Haka na faɗa masa na ke jin kamar jiya muka yi auran ashe shekarun sun tafi. Ƙara kamkameni ya yi kafin ya ce" Har yanzu ba ki sauya daga Sadiyar da na fara sani yar shekara sha tara ba." Nima ina mirmishi na ce" Kai ma har gobe baka sauya min a wannan gwarzon matashin da na aura a shekaru ashirin da bakwai ba." Sai kuma muka kalli juna ta cikin duhun ɗakin da ɗan hasken da ya kan shigo ta window ɗin cikin bedroom ɗin kafin ya sumbaci goshina ni ma sai na maida masa martani na sumbaci kumatunsa kafin mu koma mu kwanta yama ƙamƙame dani kamar za mu koma abu ɗaya.
******
Wed.13 JULY 2015.
Rana ta ƙara zagayowa ranar da a irinta ne aka ɗaura mana aure ni da Yallaɓai a irin kuma ranar ne muka zama miji da mata. Jiya Yallaɓai ya dawo domin tun washegarin ranar da muka dawo daga Ɗorayi ya je kaduna sai jiya da daddare ya dawo. Kuma yau tun safe ya fita saboda Nene ta kira shi a waya tana son ganin shi. Bai ko tsaya a gida ya ƙarya ba ya fita wanka kawai ya yi. Su Jidda sun koma makaranta tun jiya sun tafi gidan ba kowa sai ni kaɗai Marwa ba ta dawo ba amma na kira Saude na ce ta zo ta ta ya ni mu gyara gidan.
Na ba da a yi mana cake babba sannan a gida na ce zan yi mana zoɓo muna da sauran naman sallah na ce kawai sai mu yi amfani dashi bayan haka na yi dambun nama da yawa ya na nan. Kawai dai yar walima ce daga ni sai mijina sai ƴa'yana.
Saude ta zo da wuri tare muka gyara gidan ko'ina muka turare shi da turaren kamshi. Saude na saka ta dafa farar shinkafa tunda ina da miya da na yi a frigde sai na koma ɗaki na ɗau wayata na kira telanmu domin na ɗinka wani material mai kyau saboda wannan ranar na tuna masa yau zan yi amfani da shi sai ya ce zai aiko min da shi anjuma kaɗan. Sauran kazar da na siya wajen Surayya Halin yau na ce Saude ta ɗumama ta kai mini falon yara ni kuma sai na kunna data na shiga ina ganin saƙonni.
Na ga group ɗin gidanmu ana ta tagging ɗina ina shiga sai na ga Ma'u ce ta sanar da Anniversery ɗin mu ana ta yi mana fatan alheri ni da Rahila da Ya Muntari. "Mrs Injinya Allah ya ƙara dankon ƙauna." In ji Yaya Auwal shi kuma Ya Hamza tagging ɗina ya yi kafin ya ce" Yallaɓiya an gangara a bautar ubangiji.. Allah ya zaunar da ku lafiya." Haka suka yi ta ma Ya Muntari shaƙiyanci wai ɗankwali ya ja hula. Nima na shiga ina amsawa cikin farimciki. Na je na yi status amma ban saka hoto ba na dai saka Alhamdulillah! Sannan sai na rubuta"
"Shekaru goma sha biyar cikin farinciki Alhamdulillah."
Duk da ban yi caption ba sai aka fara mini mgana ta private ana mana addu'a yawanci duk yan makarantar mu ne da muka yi BUK tare waɗanda na ke da lambarsu.
Sai Adnan ɗin su Yallaɓai da ya gani ya ce min" Ma sha Allah Happy Wedding Anniversery Mrs Yusuf Muhammad Tafida." Musabahu ma haka ya ce mini" Ma sha Allah Allah ya ƙaro danƙon kauna ta Yallaɓai" Duk na amsa su. Sauran dai su Anty Bahijja ban ga sun gani ba. Zuwa na yi na zaƙulo hoton Rahila a waya na ranar sunan ɗiyarta da aka ɗauka na saka a status ɗina na c
" Happy 15 years Wedding Annivesary Mrs Muntari Amini yashe(Hubby)" Sai na ƙara da emojin rawa da murna da dariya. Ina ta dariya saboda na san in ta gani sai ta yi mgana Ya Hamza ya fara gani kawai sai ya yi tagging ɗin status ɗin da cewa.
"Ina na ki hoton?
Ina dariya na ce ni ban da hoto ya ce ban isa ba. Kowa sai ya ce wai ina hotona da na Yallaɓai tunda na saka na Rahila. Ganin sun dameni ya sa dauko hoton da ranar idi ne ma Marwa ta ɗauke mu da wayata ni da Yallaɓai yana tsaye ni kuma na jinginar da kafaɗata a saman kafaɗarsa. Shi waya ma ya ke yi bai san ana hoton ba ni kuma ina mirmishi. Hoton ya yi kyau sosai yana sanye da farar shadda mai babban riga sai dai ya cire babban rigan. Ni kuma na saka leshi mai ruwan haske akwai zanen marun a jikin leshin sai ya haskani gabaɗaya. Ina mirmishi shi kuma Yallaɓai ya ɗan sunkuya yana kallona aka ɗau hoton shi na saka a kasan hoton sai na saka.
"Barka da shekaru goma sha biyar cikin Aminci, soyayya, sadaukarwa a gare ka ya amintattace na. MRS HALIMATUSADIYA YUSUF MUHAMMAD (YALLAƁAI NA)" Na ƙara da gayyar emoji kafin ka ce kwabo duk yan gidanmu sun ce na tura musu a group ɗin gida na tura hotunan tuni har sun sakamu a status daga ni har Rahila ni a bayan wannan sai na saka hoton Jidda da Baby shima da wannan sallan aka yi musu na yi mgana a ƙasa da cewa.
" A shekaru 15 da auren mu ga albarka da Ubangiji ya yi mana nan. Allah ya raya ku HAUWA'U YUSUF MUHAMMAD(Jidda) DA MAIMUNATU YUSUF MUHAMMAD(Baby)."
Kowa sai addu'a ya ke yi. Har ta Ma'u sai da ta ce na tura mata itama ta saka ta yi mana addu'a na amsa mata ko da bai kai zucci ba.
Na duba Yallaɓai ba ya online na kuma kira layin shi ba ta shiga. Sai kawai na tura masa test massages.
"Happy Wedding Anniversy Yallaɓai na"
Na jira na jira amman bai turomin amsa ba sai na yi tunanin ƙila Network ya sa bai shiga ba. Da ya tafin na kira shi na ji ko Jikin Nenen ne ya tashi sai ya ce mini yanzu ya iso gidan lafiyanta ƙalau sai hankalina ya kwanta.
Na yini cikin farincikina ina ta amsa wayoyin yan' uwa da abokan arzuƙa har mutanen fatakol Anty Zabba ta kirani ta na min fatan alheri Haka Munnira Hauwa dai wayar ta ya lalace ba ta sani ba. Amma har Nafisa Muhammad Sani mun yi mgana da ita, sauran yan gidansu Yallaɓai duk waɗanda suka ga status ɗina mun yi mgana hatta da Halima Autar su Yallaɓai amma ban ga Anty Bahijja ko Anty Maimuna sun gani ba Mimisco dai tana online amma ba ta duba ba.
Ban damu ba, na cigaba da harkokina. Saude sai wajen uku ta tafi gida ni kuma salla kawai ke ta da ni a inda na ke Yallaɓai har lokacin bai dawo ba na kuma kira shi ta shiga bai ɗauka ba na ƙara kira shuru sai can ya turamin saƙon zai kirani ya je wani waje ne ni kuma sanin sabgoginshi sai ban damu ba. Na cinye sauran kazar hadin uwargida duka na sha gumba sannan na sha kayan marmari ranar ko abinci ban ci ba har Jidda suka dawo makaranta daman na gaya musu in Yallaɓai ya dawo da daddare za mu yi walima Jidda ta ce" Umma waliman mene? Ina mirmishi na ce" Na cikar mu shekaru sha biyar da aure ni da Abbanku."
Da ya ke ta na da wayau sai ta ce" Umma Allah ya bar ku tare." Na amsa da Amin Baby kuma sai tsallen murna ta ke yi, ko kafin mangariba har ɗinkina an kawo min daman kunshin sallar da na yi bai fita kitso kuma daman bai dameni ba ƙara gyara kaina kawai na yi, na saka Jidda ta ƙara gyara gidan ta kunna turaren wuta. Ina da bloons na ma Baby ne jidda ta kama min muka hura su na ɗaura su a falon mu wajen guda ashirin kala kala. Sai falon ya yi kyau sai bayan mun yi sallar mangariba sannan mai cake ta aiko mini dashi da kwatance sai gashi a gidana ta online na siya ƙanwar wata mate ɗina ce da muka yi Buk ce ke yi. Sannan na siya ma Yallaɓai gift wani agogo mai kyau 25k shima a wajen wacce muka yi BUK na siya daman kayan maza take saidawa na saba siyayya a wajenta in dai zan siyam Yallaɓai wani abu na gift wajenta na ke siya.
Bayan mun idar da salla mangariba muka ƙara kawata falon a center table na ijiye cake ɗin sai muka zagaye shi da voul na nama da dambun nama cake, da donut sai lemuka da ruwa. wajen ya yi kyau muna gamawa na ce Jidda ta kashe hasken falon in an ji motar Yallaɓai yana shigowa sai a kunna daga nan na ce su je ta yi wanka ta yi ma Baby na ce su saka dogayen rigunan da na siya musu yan kati ita na Jidda riga da wando ne. Baby kuma doguwar riga ce kala ɗaya na siya musu mai kalan baƙi da fari.
Nima na shiga bedroom ɗina na tuɓe na faɗa Tiolet na yi wanka amma a ƙasan raina ina tunanin ina Yallaɓai ya je? Ko kaduna ya je? Ya ce zai kirani amma shuru har na fito wanka ina wasi wasi. Daman na yo alwalata ana kiran isha'i na kabbarta salla bayan na idar ne na zo na zauna gaban madubi na tsantsara kwallya mai ƙayatarwa. Na gyara gashina na sake shi baya na yi ɗauri mai kyau ɗinki riga ds sikat ne sun kamani sun yi mini cif a jikina haka na yi ma kaina barin turaren humra ko'ina na gifta ina tashin kamshi na saka wani takalmina baƙi mai ɗan tsini kaɗan ina tafiya ya na ɗan ba da sauti kaɗan ƙwas! Ƙwas
Falon yara na shiga na gansu sun yi kyau suma. Jidda ma ta ce" Umma kin yi kyau" na ce na gode sai na ja su muka yi ta ɗaukan hotuna sun ɗan yi ma duhu saboda dare tare muka zauna sun kunna cartoon ni kuma waya ce a hannuna ina ta kiran Yallaɓai wayarsa a kashe tun ina duba agogo ina saran dawowar Yallaɓai har na sare Baby ta gaji har ta fara barci ita kanta Jiddam ma barci ta ke ji.
"Umma Abba bai dawo ba?
"Yana kan hanya in sha Allahu."
Na faɗa mata cikin karfin hali. Tashi na yi na fara zagayen falon ina yi ina duba agogon wayata. Tara da rabi ta yi shuru sai hankalina ya tashi na fara tunanin ba lafiya goma na yi na ce bari na kira Nene na ji ko yana can ai kuma ya san da ina gida ina jiran shi. Na latso lambar Nene kenan zan kira sai kira ya shigo mini na ɗauka Yallaɓai ne jikina na rawa na koma na zauna sai dai kuma sunan wacce ke kira ne ya sa sai da gabana ya faɗi Ras! Haka kurum na ji kamar ba alheri ba ne ya sa ta yi min wannan kiran karfe goma na dare.
"Ma'u ce.'
Jikina sai ya kama rawa har ta katse ban ɗauka ba. A ƙoƙarina na kira Nene amma ba ta bari ba kawai sai ga wani kiranta ya ƙara shigowa cikin dauriya da shahada na ɗaga kiran
"Ma'u."
Na faɗa kafin ma na yi mata sallama. Sai ta amsa mini cikin yanayin muryanta amma cikin farinciki.
"Na'am Sadiyar Yallaɓai."
Yadda ta faɗi sunan ne sai na ji ban yarda da ita ba. Kafin na samu zarafin mgana ta cigaba da faɗin" Na san za ki ce kira cikin daren nan ko? . Da sauri na ce" E ina fatan lafiya." Sai da ta yi wata irin dariya kafin ta ce" Lafiya sumul. Murna cika shekaru sha biyar da aure na kira na yi miki sannan tare da ba ki wani kyakyawan albishir."
Sai kawai na ji zuciyata ta tsinke amma sai na ɗaure cikin karfi hali na ce" Na gode. Ina jin ki wani albishir ne wannan da ba za ki iya jiran safe ba ki ka kira cikin daren nan?
Tana dariyan nan na ta na mugunta ta ce" Ba na so wani ya rigani ne. Na fi so ki fara jin wannan albishir ɗin daga bakina." Juyawa na yi sai na ga Jidda har ta fara barci daga kan kujera sai kawai na miƙe na buɗe kofar falon Yallaɓai na shiga na maida ƙofar na rufe a cikin duhun nan na lalubi kujeran dining na ja na zauna ina faɗin" Uhm ina jin ki Ma'u."
"Zan kashe wayata yanzu. amma ki kunna data ki hau whatspp na tura miki saƙo."
Ko kafin na ce wani abu ta kashe wayarta. Ni fa na gama sakankancewa daman ba alheri Ma'u za ta nuna min ba. Amman ban taɓa tunanin ganin abin da na gani ba. Jikina na rawa na buɗe data saƙonni na shigowa amma ba ta su na ke ba Ma'u na ke nema ina ko ganin ta tura mini abu kamar hoto na faɗa hannuna na rawa na danna sama yana buɗewa. Wallahi tallahi yana buɗewa ne amma kamar yana buɗewa da gudun numfashina ne.
Yana gama buɗewa na ji kirjina ya amsa. Kaina ya sara, hannunawana sun fara ƙarkawa saboda jikina da zuciyata suna rawa ne a lokaci ɗaya a lokacin idanuwana sun firfito ba domin na ji mamakin abin da na gani ba ne. Sai domin ban taɓa tsammacin shi a lokaci kusa haka ba. Ina wannan rawan jikin da na zuciyan kiran Ma'u ya sake shigowa ban ɗauka zan samu kuzarin ɗaukan wayarta ba amma sai gashi na ja na ɗauka na kuma ƙarata a kunnina duk da yadda zuciyata ke gudu da sauri da sauri.
"Ina fatan kin ga irin kyakyawan albishirin ɗin da na ke so na gaya miki ko Sadiya?
Runtse ido na yi zuciya na fat fat! Amma sai wata zuciyar ta ce Sadiya kar ki bari a ga gazawarki daman shi Ma'u take jira kamar an dake ni na dawo hayyacina sai na saki wani mirmishi wanda ya fi yin kuka daɗi na ce" Haba ai kin makaro Ma'u domin Yallaɓai ya riga ki yi mini wannan albishir ɗin'
Shuru ta yi domin ni na san ta yi mamakin jin kalamaina. Ban bari ta ƙara mgana ba na ce" kin yi gaggawa Ma'u da kin jira da ni da kaina zan kira ki na faɗa miki Yallaɓai YA ƘARA AURE"
Ban ƙara ba ta wata damar mgana ba na cigaba da faɗin" Walimar da na shiryama ma a gida saboda Anniversary ɗin mu ne da kuma taya shi Murnan ƙaruwan da ya samu na aure."
Ina gama faɗin haka kit na kashe wayar saboda sai na ji kamar santsi na ja na ina shirin na sumulmiyo daga kan kujeran da na ke zaune. Sai na kama jikin kujeran da hannuna ɗaya na ƙanƙame jikina ba inda ba ya rawa. Zuciya ta da tunanina sun tsaya waje ɗaya cak na kasa yin ma wani tunani. Ji na ke yi kamar ina zaune ne amma jiri na ke gani shi ya sa na ƙamƙame kujeran da na ke zaune amma ban san lokacin da na ji na sulmiyo ƙasa ba. Sai ga ni zaune a kan mazaunaina a ƙasan tayel ina kokawa da numfashina wayata ta yi zaman dirshan a kan jikina na saka hannunawa da suke rawa na ɗauka na buɗe na koma whatpps na shiga kan sunan Ma'u ina kallon hoton da ta tura mini sai a lokacin na lura da in da Ma'u ta ga hoton.
Sunan Anty Bahijja ne a saman sreenshoot ɗin da ta yi, sannan hoton na GIMBIYA CE(SAUDATU) tsohon hotona kamar ma a gidanta na Abuja ne kafin mijinta ya rasu. Tana tsaye a falon gidanta a lokacin ta na mirmishi ta saka wata doguwar riga ne a hoton. Abin da ya fi ɗaukan hankalina shi ne kalaman da aka yi amfani dashi a ƙasan hoton.
"Allahu Akbar alƙawarin Allah ya tabbata. Congratulation Mrs Yusuf Muhammad(Tafida)."
An ce wai ka yi ma hawaye rahama ne. Sai yanzu na amince da wannan mganar, na kasa jin kuka ya taho mini ma idanuwana sun ƙeƙashe. Shi kenan ta faru ta ƙare an yi ma mai dami ɗaya sata. Daman shi ne suprise da Yallaɓai ya ke ta faɗin zai ba ni? Lalle ko na karɓi kyakyawan suprise. Ban san lokacin da ya shigo gidan ba domin ban ji ƙaran buɗe get da shigowar motar sa ba ba. Sai da na ji lokacin da ya ke saka ɗan makulli yana ƙoƙarin buɗe kofar falon kamar an jani an mikar dani tsaye sai ga ni a tsaye a kan kafafuna. Wayata kuma tana jimƙe a hannuna. Ya buɗe kofar kenan ya shigo ni kuma sai na fara takawa ƙwas ƙwas ina ji jikina na rawa amma na daure na isa ga makunnin wuta na kunna dai dai yana ƙoƙarin ciro wayarsa daga aljihu domin haska fitila.
Haske ya gauraye falon. Ya bi ko'ina da kallo dai dai lokacin kuma wasu daga cikin bloons ɗin da na saka afalon suka fashe ji ka ke yi tus! Tus! Sai da ya ɗan waiga sannan ya juyo yana sauke kallon shi a kaina dai dai ni kuma ina tsaye a gaban shi na harɗe hannayena a bayana. Na ƙasa takawa zuwa gare shi, saboda sai na ga kamar ba Yallaɓaina bane kamar wani ne wanda ban saba dashi ba, sai na ke jin kamar wannan Yallaɓan yanzu akwai wata tazara da ya shimfiɗa a tsakanimu daga yau.