Kenza eBookz

Turken gida book1 by janafty - Chapter 38

Turken gida book1 by janafty - Chapter 38

Turken gida book1 by janafty Chapter 38: Turken gida book1 by janafty Chapter 38. Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan…

510 words

Kafafuna sun yi sanyi kamar gara ya kama su in na ce zan cire ƙafa zan iya zubewa saboda firgici. Shi ma sai na ga ya tsaya yana kallona amma kuma bai tsawaita ba da sauri ya kauda kanshi. Mirmishi ya ke gayyato ma fuskarshi sai dai ban bari ya gayyato ma kanshi ba ni na fara gayyato ma kaina mirmishi lokaci ɗaya ina faɗin.

"HAPPY 15 YEARS WEDDING ANNIVERSARY YUSUF MUHAMMAD TAFIDA."

Na faɗa ina kallon ƙwayar idanuwanshi. Yadda ban je gare shi domin na rumgume shi ba. Shima bai yi saurin takowa gare ni ba. Ajiyar zuciya ya sauke yana mai ijiye ledojin da ya shigo da su a hannun shi a ƙasa wanda ban san abin da ke ciki ba. Kafin ya ɗago kansa cikin ƙwayar idanuwanshi na ga rauni. Kasala tsoro da wani abu da na kasa ganewa. A kuma yanayin ya kira sunana cikin wata irin muryan da ban taɓa sanin Yallaɓai na da ita ba.

"HALIMA."

Zan iya kirga sau nawa Yallaɓai ya taɓa kirana da sunana Halima, a da in ya kirani ina jin kaina ya yi girma. Amma ban da yau domin sai na ji kamar ya kwarara min ruwan zafin a cikin jikina. Har ina jin tururunshi da hucin shi daga fatar jikina. Sai na ji kamar komai yana sauyawa kamar duk wata kyakyawan alaqan da muka gina ta tare da Yallaɓai tana zangayewa tana komawa ruwa. Kamar kuma ruwan ya fara zuba a ƙasa ya na kwarara da ƙarfin gaske wanda daga ni har shi ba za mu iya tare shi ba.

*Ƙarshen littafi na Ɗaya*

_*Nan na kawo ƙarshen littafi na ɗaya na labarin Sadiya da Yusuf, ba zan ce komai ba domin kun gwadani kun gani, yanzu ma muka tsoma hannu a cikin labarin, ba mu fara komai ba gundarin Labarin na cikin littafi na biyu da na uku, kuma na sanar da ku a manhajar Telegram za mu yi 2,3 ɗin shi, in kuma tsarin VIP ne to mu haɗu a AREWABOOKS, zamu tafi hutu kamar yadda muka saba har sai mun samu adadin mutanen da muke so kafin mu fara, ku yi gayya, ku ba da labarin TURKEN GIDA, ku sanar da wanda bai karanta ba da ya fara domin za a iya barin shi a baya. Wallahi tallahi ina da kyakyawan yakini akan abin da na rubuta kuma ina mai ba ku tabbacin za ku samu labarin nan fiye da hasashenku a kaina, In sha Allahu ba zan ba ku kunya ba, ku biya kudin karatun ku, da zaran kun kai adadi za mu fara kuma ba jira har sai mun dire in sha Allahu. NA GODE*_

*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332.

*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

*Janafty* *25 November, 2024* *17/May/2025*

Readers Also Read