Kenza eBookz

Turken gida book1 by janafty - Chapter 4

Turken gida book1 by janafty - Chapter 4

Turken gida book1 by janafty Chapter 4: Turken gida book1 by janafty Chapter 4. Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki…

3,359 words

Sai ta kawo mini sannan na kalle ta ina faɗin" Ki ɗiba abinci ki ci sai ki zo ki wuce gida kin san kina da makaranta." Da toh ta amsa min ta wuce kitchen ta diɓo taliyan ta zo ta zauna a kasa ta na ci, ba hira muke yi ba sai ni ce ma ke mata tambayoyi.

"Babanku ya dawo?

Sai ta ce min a'a sai na girgiza kai kawai, lagos ya ke zuwa kwadago in ya tafi sai ya yi rabin shekara bai dawo ba ya bar iyalansa da wahala. Ni na riga ta tashi, na tafi da filet ɗin hannuna da kofi zuwa kitchen na saka a sink ɗin wanke wanke. Leda na samu na buɗe drower ɗin cabinet ɗin kitchen ɗin na auna mata shinkafa tiya biyu sai taliya da maracaroni da na diɓar mata tunda nima abincin nawa ya yi ƙasa.

Bedroom na koma na ɗauko mata 2k daga cikin jakata sannan na dawo falon lokacin ta gama cin abincin sai na ce ta wanke hannu ta zo. Ina zaune ta zo ta zauna gabana ta na faɗin" Ga ni Anty" Ledan na tura mata gabanta lokaci ɗaya ina mika mata kuɗin hannuna ina faɗin"Ki kaima mamanku kin ji ko? Ta karɓa tana faɗin"An gode Allah ya saka da alheri." Na amsa da Amin ina faɗin"Ki yi sauri ki hau mashin ne biyu ta kusa." Sai ta amsa minI, tare muka fita saboda zan rufe gida tana fita na maida gidan na rufe na dawo falo ina kallo, film ɗin horror ne ya ɗauki hankalina sai da aka gama shi amman za a yi part 2 ɗin shi. Uku na rana na koma ɗaki na kwanta sai barci ban ta shi ba sai huɗu da rabi, sai na yi alwala na yi sallah na ga tunda huɗu ta wuce sai kawai na ce bari na yi azkar ɗina.

Ni kaɗai a gida kamar mayya na matsu su Jidda su dawo sai shidda suka dawo saboda biyar da rabi ake tashin su kafin ya je ya ɗauko su shidda ta yi tunda makaranta boko da isalamiya ne. Dawowarsu ne ya sa na fito falo suna bani labaran makaranta suna cin abincin, Baby ce mai surutun Jidda irin Babanta ne tana da sanyi sosai ba kamar Baby ba. Suna gama cin abinci suka sauya kaya zuwa na gida. Unform ɗin Jidda ta ce za ta wanke na ce yamma ta yi, tunda suna da guda biyu ta bari zan wanke musu gobe da safe

Tare muka yi sallar mangariba, muna idarwa a ƙaramin falo muka fara karatu. Jidda na suratul maryam ne Babby kuma tana ƙasa ƙasa sai da suka biya na jiya na ƙara musu sannan muka yi azkar tare. Muna gamawa sai muka miƙe muka yi isha'i tunda an kira. Muna idarwa na bar su a falo suna kallo ni kuma na shiga kitchen na dafa ma Yallaɓai tea daman na dafa masa farar shinkafa tunda shi taliya ba ta dame shi ba, ina gamawa na shiga wanka ina wankan ma na ji shigowar motar Yallaɓai.

A gurguje na shirya cikin riga da wando, wandon plazo ne mai buɗewa ta kasa. Rigar kuma Top ce mai wuya ta kama jikina sai na gyara gashin kaina na tufke a tsakiya na saka wata hula mai love a saman kaina kalan pick . Tsakiya babu komai, kwalliya na yi kamar yadda na saba na saka jan baki na kamar yadda na saba. Na ji ƙaran bude ƙofa ganin bai shigo ba ya sa na san ya shiga tiolet ne. Ba jimawa sai gashi ya shigo da sallama ina zaune a gefen gado ina bin shi da mirmishi bayan na amsa sallamarsa.

Hannuwana ya buɗe minI na tashi da sauri na faɗa masa ya rumgumeni. Nima sai na ƙamƙamesa ina fadin"Barka da dawowa Yallaɓai na." Ya na shinshina ƙamshin humran dake jikina ƙasa ƙasa ya ce" Uhm. I like it." Ɗagowa na yi muna kallon juna kafin na ce'Me? Yana mini wani kallo ya ce"ƙamshin ki mana." Far na yi masa da ido kafin na ce"All is yours" Kumatuna ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka." Na amsa da Amin. Ruwan wanka na ce zan haɗa masa ya yi wanka sai ya ci abinci. Shi kuma sai ya ce"E. sai mu ta fi wajen kiran Alhaji ba"

Gyaɗa masa kai na yi ba tare da na yi mgana ba. Sanda ya shiga wanka ni kuma na je haɗa masa abinci bayan ya fito ya sauya kaya zuwa wani yadi riga da wando ɗinkin zamani. Falon farko mu ka je saman dining ya ci abinci su Jidda kuma suna ƙaramin falo Bayan mun gama ba mu tsaya ɓata lokaci ba ya ce na saho hijabi mu ta fi, daman na fito da Hijabin jalbab mai ruwan ƙasa har ƙasa sai na saka takalmina iri ɗaya da wanda Yallaɓai ya saka daman tare ya siya mana.

Na ce musu Jidda su kula da gida za mu je gidansu Gwaggo mu dawo. Baby taa saka rigiman sai ta je Babanta ya tsaya yana lallashinta da zai siyo mata ice cream sannan ta yarda na ce in za su kwanta su kashe komai za mu fita da key da toh Jidda ta amsa da yi mana a dawo lafiya. Sai da muka fita da motar sannan Yusuf ya koma ya rufe get ɗin Sannan ya dawo muka kama hanya mun ɗauki hanya kenan na kalle shi kafin na ce" Na gwada kiran ka yau ban same ka ba."

Hankalinsa na wajen tuƙi ya ce"Nima na kira ki ban same ki ba." Sai ya kalleni kafin ya ce"Me ya faru? Kai tsaye na ce"Kan mganar komawata Abu shika ne, Uncle Abba bai ƙara kiran ka ba? Sai a lokacin ya tuna ya ce"Kash! Ya kirani amman shaf na manta ba mu yi mganar ba. Amman bari yanzu zan kira shi."

Ni ya miƙa ma wayar ya ce na kira shi, Kawu Abba daman ya saka masa da na kira sai na saka a speaker har ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.

"Kawu barka da dare."

Shuru bai yi mgana ba.

"Uncle Abba barka da dare"

Wata murya a dakushe ya ce"Yusuf in ma bashi kake nema na kuɗi ba ni dashi wallahi. Wanda ma nake binka EFCC ne za su ƙwatar mini haƙƙina."

Daga ni har Yusuf sai da muka kyalƙyace da dariya. Ni ce na ce"Haba Uncle Abba ba amana yanzu sai ka kai mini Yallaɓai EFCC? Jin muryata ya sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce" Sadiya? daman kina kusa? Na amsa masa da e, sannan muka gaisa dashi. Shi kuma sai ya bige da faɗin"Yallaɓan nan naki ya ci bashina kamar gadon ubansa yaƙi biyana. Gwara babbar hukuma ta shiga ciki, in na je gaban manya sai a saka sanayya a ciki gwara a kame shi ko amansu ne sai ya yi."

Yusuf na dariya ya ce" Na ci fa halas, abin da ya yi Nene shi ya yi ka fa Kawu Abba." Kai tsye ya ce"Ko? To ai ko ita Nenen ta ci kuɗina sai ta biyani ballatana kai."

Ni dai ina ta dariya ganin sun sarƙe da gaddama shi Yusuf ya na faɗin ya ci halas kawu na fadin shi ba ƙanin Uban shi ba ne na uwarsa ne bashi da gadonsa. Zungurin kafar Yallaɓai na yi sannan ya yi gyaran murya yana fadin"Sadiya ta ce a yi maka tuni ka yi mganar da Dr Fadil ɗin? Kawu Abba dagacan bangaren ya ce"Kash na manta. Amman bari na kira shi na ji yadda muka yi zan kira ka."

Sai ya kashe wayar, dai dai Yusuf na faɗin" Kina ganin komawarki can da ganin likitan ba damuwa? Sai na gyaɗa mai kai ina fadin"E, ba matsala can ma ƙwararru ne. Tunda na yi ta nan ban dace shi ne aka ban shawara na gwada can ɗin." Sai ya jinjina kai, bai yi magana ba sai ni ce na cigaba da faɗin"In ina da appoitment na ganin likita tun ana gobe zan je zariya na sauka gidan Ya Hamza bayan na gama ganin likitan sai na dawo."

Kai tsaye ya ce"E hakan ma ya yi. Allah ya sa a dace." Na amsa masa da Amin. Mun shiga anguwan ɗorayi kawu Abba ya sake kira ya ce sun yi mgana da abokin nashi Dr Fadil shi likita ne a bangaren zuciya amman ya ce ya yi ma wata Dr Nayami mgana musulma ce amman ba bahaushiya ba ce, ya ɗan yi mata brief na matsalata ta ce zuwa sati mai zuwa za ta iya bani appiotment in har ya tabbata zai kira Kawun ya sanar dashi.

Jin haka ya sa sai na ji daɗi kamar na je ta shaida mini zan iya sake samun wani cikin haka na riƙa ji. Daidai lokacin Yallaɓai na gyara parking a kofar gidanmu da ke anguwan Ɗorayi.

*TURKEN GIDA LITTAFIN KUƊI NE, BOOK 1 ZAI ZO A MATSAYIN KYAUTA. BOOK 2,3 KUMA ZAI ZO A MATSAYIN NA KUƊI, KU BIYA KUƊIN KARATUNKU #1k NE KACAL, AKAN MANHAJAR TELEGRAM TA WANNAN ASUSUN BANKIN 9069067488 JAMILA UMAR OPAY, KO TUNTUƁA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* 09069067488. 08032773332.

*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN DA KE SAMA. MUN GODE*

*Janafty* *03/10/2024* *TURKEN GIDA.*

*Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty*

*SADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z

*🅿️03*

Gidanmu na nan a farko layin shiga anguwar Ɗorayi. Yanayin fasalin gidan babba ne sannan tun daga waje za ka fahimci tsarin gidan na tsohon ɗan boko ne. Domin Alhajinmu kafin ya yi Ritire(Ritaya) sai da ya riƙe mukamin babban darakta na kamfanin wuta na jihar kano(KEDCO). Bayan kasancewarsa manomi. Kuma gidanmu na da ga cikin rukunun gidajen da suka daɗe a anguwar tun da sama da shekara ashirin duk da ko mu kanmu muna da wayau lokacin da muka dawo gidan tun a wancan lokacin zamani na kwance. Sai dai yanzu lokaci bayan lokaci yana samun ƴan gyare gyare da kwaskwarima daga su Yaya Hamza.

Ni na fara fitowa daga Motar. Yallaɓai na kuma an kira wayarsa ya tsaya a mota ya na mgana. Kofar gidan namu tar da hasken wuta gabaɗaya ma anguwa akwai hasken ƙwakwayen da suke kofar gidajen wasu mutane dake cikin rukunin anguwan ta Ɗorayi.

Gidanmu na ke kallo ina tuna wasu shuɗaɗɗun al'amura da suka faru damu a cikin gidan masu daɗi da akasin su. Yallaɓai ne ya katse min tunani da cewa" Kin ga ko na manta ɗazu musabahu ya zo offishina ya bani saƙo ya ce in ji Yaya Muntari mijin Rahila."

Sai a lokacin na ɗago ina kallonsa ya fito daga mota ya na nuna min kullin abu a baƙar leda, yadda ya ga na taɓe baki ya sa ya san tabban nasan da saƙon.

"Bar shi a motan kawai."

Bai yi musu ba sai ya koma cikin motar, ina hangensa daga waje ya buɗe akwatin motar ya jefa sannan ya fito yana ƙoƙarin rufe motar hasken wata mota da ke tunkaromu ta kashe mana ido daga ni har shi sai da muka saka hannuwammu muka kare fuskokin mu dashi.

"Kai. Waye wannan da ba zai rage filita tunda ya shigo cikin anguwa ba."

Na kasa magana ne saboda mamakin ganin motar ba wucewa ta yi ba, kusa damu itama ta gyara parking, tun kafin ma na ciki su fito na shaida su waye tun daga cikin motar akwai hasken fitila.

"Ma'u ce.."

Haka na faɗa a cikin raina dai dai san da ta buɗe murfin mota ta fito shima mijinta ya fito daga can bangaren direba.

"Alhaji Mustapha ne, da Ma'u ashe."

Yusuf ya faɗa ya na sakin mirmishi, na kalle shi wani abu ya yi mini tsaye a zuciyata. Lalle Alhajinmu wato zaman yau bayan ni da Ma'u har da gayyar mazajen mu kenan?

Kara haɗe rai na yi, ganin Ma'u na nufoni shi kuma Yusuf ya nufi Alhaji Mustaphan shi adole ya ga ɗan'uwan mijin yayarsa. Ƙaramin tsaki na ja dai dai lokacin da Ma'u ta ƙariso kusa da ni ta na faɗin"Sadiya kema Alhajinmu ya kira ku ne ke da Injiniya?

Ta faɗa lokaci ɗaya ta na ɗora hannunta saman kafaɗata. Sai na ji kamar ta ɗora min cuta da sauri na kauce ina yi mata wani irin kallon ke ki kiyayeni. Ita kuma ta na bi na da wannan munafukin mirmishin nata na yaudara.

Ƙoƙarin sake matsowa kusa da ni take tana yi min mirmishinta da ba alheri a cikin sa. Tsaki na ja mai karfi na juyawa na fara tafiya zuwa ƙofar da za ta sada ni da cikin gidanmu na ji muryan Ma'u da ɗan karfi ta na faɗin"Haba Sadiya. Ke shike nan abu ba ya wucewa a wajen ki? Na yi ta ba ki haƙuri fa?

Sai da na kai kofar gidan sai na juya ina kallonta sai na ga har su Yusuf ma sun dawo da hankalunsu kan mu, dariyan gefen ba ki na yi. Ni ai sai dai na rubuta littafi guda akan maƙircin Ma'u daman ta yi ne domin hankulansu ya dawo kan mu, shigewata cikin gida na yi ina ji Yusuf na kiran sunana na yi masa banza na yi shigewata na bar su nan ƙofar gida.

Dogon korido ne mai ɗauke da ɗakuna uku na waje, biyu suna rufe ne sai guda ɗaya ne a buɗe. A raina na ce kila Datti ya zo gida ko kuma an yi baƙin maza daga Yashe ko Yan tumaki. Ban gama mamaki ba sai ga Datti ya fito daga cikin gida sai muka ci karo da juna.

"Datti.."

Na kira sunan shi, sai ya kalleni domin fitowarsa daman hankalinsa na kan wayar hannunsa. Daga shi sai baƙin wando da farar singileti.

"Yaya Sadiya? A daran nan?

Ya faɗa yana kallona, jiyo muryoyinsu Yusuf suna ƙokarin shigowa ya sa na raɓa ta gefensa na wuce, ina jin sa ya na tambaya ta.

"Ke kaɗai kika zo? Ina Yallaɓan da su Jidda?

Ko juyowa ban yi na faɗa tsakar gidanmu da sallama. Gwaggo na Madafi na kuma nasan shayi ta ke dafama Alhajinmu da tun tasowarmu nasan ba ya iya barci sai ya sha wannan ruwan zafi. Ita ta amsa min sallamata tana kuma leƙowa muka ci karo da juna tsakar gidan tar yake da hasken gulop.

"Maraba da Hajiya Dubu."

Sai na sa ki mirmishi ina faɗin"Kai Gwaggo ni dai wannan tsohuwar ta mutu ba ta bar mini gadon komai ba sai na sunan ta." Gwaggo na dariya ta ce"Ka ji min ƴar nema. Ai ko ita ta bar miki gado tunda ta bar miki gadon suna mai daraja irin Halimatussadiya."

Ya na iya?. Domin in dai Gwaggo ce ta riƙa sharhin sunan kenan da kawo tarihi. Gaisheta na yi cikin girmawa ta amsa ta na faɗin"Na gan ki ke kaɗai ina shi Yusufan? Na rausayar da kai kafin na ce"Ga shi nan shigowa."

"Oh. To ina yaran suke? Ko can gida kuka baro su?

Ban amsa mata tambayarta ba. Sai na bige da faɗin"Alhajinmu na ciki ne Gwaggo? Na faɗa ina kallon ƙofar falon shi da na hangi hasken wuta.

"E. ya na ciki tun ɗazu ya dawo. Zaman jiran ku yake yi. Domin nima sai yanzu ya ke yi min taɗin kuna tafe ke da Ma'u"

Ta na dire maganarta sai ga sallamar Ma'un ban tsaya ba ni kuma na kara sauri zuwa falon Alhajinmu. Da nesa kaɗan dashi ɗakin Gwaggo ne shima akwai hasken wuta daga cikin ɗakin, kusa da shi kuma ɗakin Mama ce a sakaye, daman in dai ba mu ne muka zo gida ba, ɗakin Mama yana yini a sakaye ne Ɗakin na kallah ta window ya yi duhu alamun an kashe hasken ɗakin gabaɗaya ƙwallah suka taho min na yi saurin shanyewa amman a fili sai da na furta" Allah ya yi miki Rahama Mama."

Lokaci ɗaya na cire takalmina akofar ɗakin Alhajinmu na shiga da sallama a bakina.

Alhaji Sulaiman Abubakar Yashe(Alhajinmu) na zaune a saman kujera mai zaman mutum biyu cikin jerin kujerun da suka yi ma falon kwanya. Falon da na girma sosai shi ya sa sai kujerun suka zama a can tsakiya. Alhajinmu ba tsoho ba ne, ko na ce yanayin jikinsa na ɓoye shekarunsa. Ya mori jiki saboda bashi da kiɓa tun zamanin samartakansa har kuma girmansa. Dattijo ne wankan tarwaɗa, mai matsaikacin faɗin fuska da furfura ta gama zagayewa. A shekarunsa zai iya haura 65 amman kuma ba zai ga za 67 ba.

Cikin yanayin maganarsa da zafin murya irin ta Alhajinmu ya amsa min sallamata.

"Amin wa'alaikis salam. Dubu ce tafe?

Sai da na ƙarisa gabansa na zauna ina faɗin"Ni ce Alhajinmu barka da dare." Yana yar dariyansu ta manya ya ce"Barkan mu dai. Yana ganki ne kaɗai ko Yusufan ya na waje ne?

Ko kafin na samu zarafin magana Ma'u ta yo sallama ta shigo bayan ta kuma mijinta ne Alhaji mustapha da Yallaɓaina Injiniya Yusuf.

Itama gaban Alhajin ta zo ta zube ta na gaishe shi, ni dai na matsa can gefe na jingina da kujera suma su Yusuf nan kasan cafet ɗin da ya malale ɗakin suka samu mazaunin zama cikin girmamawa suna gaishe da Alhajinmu ya amsa cikin sakewa da dattako, sai ya karkata kansu yana tambayan su aikinsu da sauran harkoki.

Ni kuma kaina sai na dukar da kaina ina duba wayata ganin har tara na dare ta gota da kaɗan. Ita kuma Ma'u sai ta tankwashe kafa kamar mutuniyar kirki kanta na ƙasa ban san abin da ta ke yi ba.

Shigowar Gwaggo ɗakin dauke da shayin Alhaji ya katse hiran ta su, ta miƙa masa a wani ƙaramin mug ya karɓa ya na faɗin"Na gode Maimuna. Allah ya yi albarka" Ta amsa da Amin. Sannan ta juya suna gaisawa da su Yusuf tunda da suka shigo ta ce su shiga itama ga ta nan zuwa.

"Ma'u ya gida ya yara? Ina su Alhaji karami?

Gwaggo ta faɗa ta na kallon Ma'u. Ita kuma sai ta ɗago ta na faɗin" Lafiyan su lau Gwaggo na baro su gida tare da Zainab"

Gwaggo ba ta yi shuru ba sai ta kara cewa" Ya gajiyan ku? Kun sha suna. ke ce kawai daman da Sadiya ba ku biyo ta nan ba ranar sunan" Gum na yi da bakina saboda daman in dai Ma'u na magana ba na saka baki, can na ji ta na ce ma Gwaggo wai mun yi dare ne shi ya sa ba mu biyo ta gidan ba.

Shi kuma Alhajinmu sai da ya yi rabin da shan shayinsa sannan ya kalli su Yusuf ya na faɗin"Ban yi muku ta yi ba, ko Maimuna ta haɗa muku shayin ne?

Alhaji Mustapha ne ya yi saurin cewa" Mun gode Alhaji." Yusuf dai bai yi magana ba saboda na ji an kira wayarsa bai ɗauka ba ina jin sai ya sakata a silet.

Ficewa Gwaggo ta yi daga Falon zuwa ɗakinta. Ta bar mu daga mu sai Alhajinmu sai da ya gama shan shayinsa sannan ya kalleni yana faɗin"Dubu kai kofin can madafi"

Ya faɗa yana mika min mug ɗin hannun shi da ya gama shan tea, sai na miƙe da sauri na karɓa na fita zuwa tsakar gida na tura kofar madafin tun da har Gwaggo ta sakaya ban ijiye ba sai na diɓi ruwa a katon botoki mai murfin ɗin dake cikin madafin na tara a sink na wanke shi, tunda madafin gidanmu ya daɗe da komawa na zamani na kife kofin saman cabinet ɗin kitchen ɗin sannan na fito na sakaya shi kamar yadda na ga Gwaggo ta yi.

In da na tashi nan na koma na zauna. Sai sannan Alhajimu ya gyara zama ya na sanye da jallabiya mai ruwan madara kansa ba Hula sai furfuran da suka masa kwanya daga kansa suwa gemunsa da sajensa.

"Ma sha Allah, na ji daɗin yadda bayan na kira ku kuka amsa kirana. Allah ya yi muku albarka gabaɗaya."

Muka amsa da Amin gabaɗayanmu. Alhajinmu ya kalleni sai ya kira sunana da sai irin haka mgana mai muhimmanci ya ke kiran sunana bayan Dubun da yan kirani.

"Halima.."

Sai na ɗago na kalle shi lokaci ɗaya ina mai amsawa.

"Na'am Alhajinmu."

Sai ya karkata kan Ma'u itama ya kira sunanta.

"Asma'u.."

Readers Also Read