Kenza eBookz

Turken gida book1 by janafty - Chapter 5

Turken gida book1 by janafty - Chapter 5

Turken gida book1 by janafty Chapter 5: Turken gida book1 by janafty Chapter 5. Itama ta amsa da na'am Alhajinmu Sai ya cigaba da faɗin" Kusan dalilin da…

3,342 words

Itama ta amsa da na'am Alhajinmu Sai ya cigaba da faɗin" Kusan dalilin da ya sa na ce ina son ganin ku wannan karon tare da mazajen ku? Dukkanmu muka girgizanmu kanmu kafin mu haɗa baki wajen faɗin"A'a Alhajinmu."

Kai ya gyaɗa kai kafin ya ce"To ba saboda komai ba ne sai dalilin bayan ni kuna da wasu shugabbanin da in kuka yi ba dai dai ba, za su iya yi muku faɗa akan ku gyara kamar yadda ni zan yi muku. Mazajen ku su ne alhakin duka rayuwarku da tarbiyansu yake hannunsu bayan na aura musu ku, shi ya sa wannan karon ganin wannan rigimar da sheɗan ya ba da gudummuwa wajen gina ta a tsakaninku da ta ƙi ci ta ƙi karewa na yi tunanin saka mazajen ku a ciki, saboda ba na so na faɗi na mutu a zaman makokina ke Sadiya da ke Asma'u a ce bakwa yi ma juna mgana akan abin da bai kai ya kawo ba."

Sai ya dakata ya na nazarin mu, dukkanmu kan mu na ƙasa ba wacce ma ta ɗago. Sai ya karkata hankalinshi zuwa ga mazajen mu.

"Yusufa.

Cikin ladabi ya ce"Na'am Alhaji"

"Mustapha."

Shima cikin ladabi ya amsa da Na'am Alhaji.

Sai Alhajnmu ya gyara zama ya na faɗin"Ban sani ba ko kun taɓa sanin tsakanin matayen ku ba a ga maciji? Ma'ana ba sa haɗuwa waje ɗaya su yi rabuwan lafiya? Wataƙila za ku iya fahimtar ba sa shiri da juna amman na san ba su taɓa zama sun warware muku lamarin yadda za ku fahimta ba.

Wannan karon Alhaji Mustapha ya fara faɗin" Haka ne Alhaji. Ban dai san me ya ke haɗa su ba amman Sadiya ba ta zuwa gidana sannan ko haɗuwa muka yi ni da ita in dai ba ni na yi mata mgana ba. Ba za ta yi mini ba, na taɓa tambayan Ma'u ko akwai wani abu a tsakaninta da Sadiya ne amman ba ta ce komai ba"

Ya karishe faɗa yana kallona, nima ko na ɗago muka kalli juna na kauda kaina domin ba ƙarya ya faɗa ba mun sha haɗuwa da shi gidan Anty Bahijja sai na yi kamar ban gan shi ba in har bashi ya yi mini mgana ba.

"Kai fa Yusufa? Ka taɓa fahimtar wani abu?

Cikin girmamawa ya ce"E. Na fahimci ba shiri tsakaninsu. Amman na ɗauka faɗa ne kawai na ƴan'uwa ba mai tsananin da zai haifar da matsala ba ne Alhaji."

Alhajinmu sai ya sauke numfashi kafin ya ce"Kowa ma haka ya ɗauka daga farko farko. Amman suna ƙara girma lamarin na su na ci gaba, tun suna yara har suka girma na aurar da su gare ku, suka hayayyafa suka zama iyaye sun tashi daga yara sun koma uwaye waɗanda ba zan ce ba su san ciwon kansu ba. Sun sa ni tunda Tarbiya ne ma a ƙarƙashin ikon su, daga lokacin ne na fara fahimtar lamarin ya wuce tunanin zai tsaya anan ina tsoron kada su mutu su bar ƴaƴansu cikin muguwar gaban da sheɗan ya kulla a tsakanin su."

Dalon sai ya yi shuru, Alhajinmu kuma bayan ya yi shuru na wani lokaci kafin ya cigaba da faɗin"Ba yau ne na saba sulhu tsakanin Halima da Asma'u ba, tun yan'uwansu na yi musu ban sani ba har ya fi karfinsu suka dangana da ni, na yi nasihan da ban baki sai sun ce sun bari amman ba a daɗewa sai an zo an faɗa mini sun haɗu kuma sun yi faɗa. Wannan zaman saboda dalilin faɗan ne da suka haɗu shekaranjiya a gidan sunan ƴar Rahila. Murja ta zo har gida nan ta na faɗa mini a gaban mutane ke Halima kika yi ta ma yar uwanki ɗiban albarka, ita kuma an ce Asma'u haƙuri take ba ma Sadiya amman dai sun sanar dani faɗan dalilin ita ƙawar Asma'un ce da ta je sunan ƴar Rahilan"

Yusuf ya ce"Subhanallah" Shi kuma Alhaji Mustpha ya kaɗa kai kafin ya ce"Asha. Abu bai yi daɗi ba."

Ni ko kaina na ƙasa a raina ina mamakin Yaya Murja, ko miye riban ta na zuwa ta karantama Alhaji komai?

"Wannan dalilin ya sa na ce zan saka ku a ciki. Gani ga ku zan tambayesu ɗaya bayan ɗaya menene haƙikanin matsalansu da ko da yaushe suka haɗu sai sun yi faɗa? Ko sun manta su ƴan uwan juna ne dangi ɗaya? Ko ke Sadiya kin manta matsayin Asma'u a gare ki ne? Ko ke Asma'u kin manta matsayin Sadiya a gare ki ne?

Ya ƙarishe faɗa ya na bin mu da kallo, kowaccen mu ta kasa ɗagowa saboda nauyin idanuwan Alhaji a kan mu.

"Ke Sadiya ke ce Babba da ke zan fara. Ɗago ki kalle ni"

Ba ni da mafita illa ɗago kaina ina kallon Alhajinmu cikin muryansa a kaushashe da ɓacin rai ya ce"Halima na san halin ki, kina da tsiwa da mgana sannan ke ce daman ko faɗa aka yi dake ko an yi sulhu ba kya hakura ki yi ta gaba saboda daman gaba ba ta yi miki wahala. Ki faɗa mini gani ga Asma'u da mijinki wani irin abu ne Ma'u take yi da ba ki so? Ki faɗa mana sai ta ji ta ba ƙi hakuri ta kuma ɗauki alkwarin za ta daina yi miki saboda ku samu zaman lafiya"

Shuru na yi na wani lokaci kafin na ce"Alhajinmu ba fa ni kaɗai na tsani Ma'u ba. Itama ta tsane ni tun zuwanta gidan nan ba ta sona nima ba zan maka ƙarya ba ba na sonta Alhaji. In kuma ana son a samu zaman lafiya to Ma'u ta daina bin hanyata ni daman ba ta gabana domin na fi ƙarfinta Alhajinmu ka raba tsakanina da Ma'u don girman Allah."

Na karishe faɗa har ina haɗa hannu alamun roƙo, gabaɗaya ni suke kallo har Ma'u sai kawai na ga ta fashe da kuka, ban ko razana ba domin kaɗan daga cikin makircin Ma'u kenan.

Yusuf kuma ni ya ke kallona, saboda ya san halina ina da taurin kai, in na kuma ce na tsani abu to da gaske na ke yi ba na son shi.

"Innalillahi ni ko Sadiya me na taɓa miki a rayuwa da kika tsane ni haka?

Kai tsaye na ce" Ban sani ba. Ke za a tambaya abin da na yi miki kika bi kika addabi rayuwata kina yi mino bita da kulli a wajen iyayena da ƴan'uwana wannan bai isheki ba kin fara yi min ta bangaren dangina mijina wannan bai isheki ba sai kin je kina yamaɗiɗi da ni cewa planning na yi shi yasa har yanzu na ke neman haihuwa ido rufe ban samu ba, har wannan matsiyaciyar ƙawar na ki ta kalli tsabar ido na tana gaya mini mgana."

Na ƙarishe faɗa cikin tsawa domin nima raina ya ɓaci. Tuna abin da ya faru da a gidan Rahila kaɗai kan haifar mini da ƙuncin zuciya.

Daga Alhajinmu har su Yusuf shuru kawai suka yi suna kallon mu. Ma'u ta na kuka ƙaryan da ta saba na yaudaran mutane ta fara rantsuwa ta na faɗin" Wallahi tallahi in kin yarda dani Sadiya ban san a ina Shema'u ta ji wannan labarin kuma, a gabanki na yi mata mganar ban ji daɗin abin da ta yi ba, saboda haka ya sa ko yau ta zo gida ta na faman bani haƙuri ban saurareta ba. Har a waya tana ta kirana ban ɗauka ba domin na faɗa mata ba ke ta tozarta ba ni ta tozarta domin abin da ya yi ki shi ya yi ni Sadiya da ni da ke bamu da bambamci"

Ta ƙarishe faɗa tana shesshekan kuka sai kuma ta kalli Alhaji tana cigaba da faɗin"Alhaji wallahi Allah ɗaya kenan ba ni da wani mugun nufi kan Sadiya. Ina son ta kamar yadda na ke kaunar yar uwata Zainab, ina son ta ƙwatankwacin yadda nake son su Rahila. Amman ban san me ya sa Sadiya ta kasa fahimtata ba, Alhajinmu ko rashin fahimtar da ta faru a baya ta maganar aurena da Yaya Hamza tabbas raina ya ɓaci kuma na ji haushin Sadiya amman har ga Allah daga baya na cire abin a raina ban taɓa kallon Sadiya dashi ba. Ni ko me ya sa zan yi haka? Alhaji Sadiya ce ba ta sona ban kuma san me na yi mata ta tsane ni ba tana hulɗa da kowa Alhaji ban da ni in dai abu ya shafe ni Sadiya tsame hannunta ta ke yi a ciki ba ta zuwa gidana ni in na je wallahi ko bare Sadiya ba ta yi masu abin da ta ke yi mini, in muka haɗu a gida ko gidajen ƴan'uwa Alhaji ko na yi ma Sadiya magana ba ta yi mini ta yi ta gaba da ni. Na zauna ta yi ta tunanin abin da na yi ma Sadiya ta tsane ni amman na kasa ganewa, daga baya sai na fara tunanin ƙila saboda Alhaji ka ɗauke ni ka sanyani cikin Iyalanka ne, ita kuma Sadiya ba ta so wani daga waje ya raɓe ta, sai kuma daga baya na kwaɓi kaina da cewa ai ni ba bare ba ce Alhajinmu ni ma ƴarka ce kamar Sadiya"

Ta faɗa har ta na riƙe kafar Alhaji, tana kuka, gabaɗaya na san ta gama cika zuciyar Alhaji da tausasa kalamanta. Ni ko a raina ban ji na yi nadama ba, kallonta na ke yi ina mamakinta har ta manta mganganun da ta gaya mini a lokacin da aka fasa auranta da Yaya Hamza? Har ta manta?

"Tashi. Tashi Asma'u. Ke kam ba bare ba ce ke ƴa ce kamar Sadiya. Ta shi daina kuka kin ji bari kuka nan"

Ya faɗa cikin sigan lallashi, Alhaji Mustapha har da mika mata wani farin hanky, ya na faɗin"Ki share hawayen ki Ma'u" Ba wanda ya fi baƙanta min rai irin Yusuf har da shi a masu ba ma Ma'u hakuri daman halinta ne ta shirya makirci a raja'a a kanta.

Tsaki na ja mai ƙara kafin na ce" Ke dai Ma'u wallahi an yi baƙar munafuka kuma makira, ke wai kina kuka saboda ki zama abin yarda ni kuma na zama victim kamar ko yaushe ko? Har kin manta? Har kin manta maganar da kika faɗa mini lokacin da aka rushe maganar auran ki da Yaya Hamza? Na ce kin manta? To wallahi kamar yadda baki ƙaunata nima abada ba..'

"HALIMA..."

Alhajinmu ya katseni tare da kiran sunana a tsawa ce, ban kalle shi ba na cigaba da faɗin"Alhajinmu cewa ta yi fa sai ta rama abin na yi mata sai ta kun samini kwatankwacin baƙin cikin da na kunsa mata kuma.."

"Na ce ya isa ko Halima? Ko so kike yi na saɓa miki?

Alhaji ya faɗa ransa ɓace, sai na yi sansarai rai, ganin ya koma ya ba ma Ma'u haƙuri tana shessheƙan kuka. Baƙin ciki da ya tokare mini zuciya ya ta so mini ba kasafai na ke kuka kan abu ba amman daman Ma'u ta saba cin nasara a kaina akan kowa ko da yaushe ni ce victim ita kuma mai gaskiya.

Ban san nima na fashe da kuka ba, sai kawai na miƙe zan fita daga falon ina faɗin" Shike nan ai daman ita mai gaskiya ce ita ce ba ta laifi ni ce fitananniya. Alhajinmu ni fa ƴar ka ce Ma'u fa? Bai kai kamar ni da ka haifa da gudan jinin ka ba."

"Ke ke Sadiya ina za ki je?

Alhajinmu ya fada saboda na juya ina kuka zan fita ne.

"Wallahi zan saɓa miki in kika fita Halima."

Shi ya sa na fasa fita amman sai na coge a tsaye ina sharan kwalla. Ran Alhaji ya ɓaci ya ɗaga murya ya na kiran sunan Gwaggo.

Sai gata ta shigo da sauri ta na sanye da Hijabi a jikinta. Gani na tsaye ina goge idanuwana sannan ga Ma'u na ta shesshekan kuka Alhajinmu na faman ba ta haƙuri.

Cikin mamaki da damuwa a saman fuskarta har kuma ya bayanna a muryanta ta ce"Subhanallah. Alhaji lafiya? Me ya faru ne? Duk da ta san dalilin zaman amman shi dailin koken koken namu ne ba ta sani ba.

Yusuf ne ya tashi daga in da ya ke zai iso in da na ke tsaye amman Alhajinmu sai ya dakatar dashi.

"Dawo ka yi zaman ka Yusufa ƙyaleni da ita."

Sai ya koma ya zauna a inda ya tashi amman gabaɗaya hankalinsa na kaina kamar yadda hankalin Alhaji Mustapha ke kan matarsa.

"Taho min da Halima nan gaba na Maimuna."

Umarnin da Alhajinmu ya ba ma Gwaggo kenan sai ta riƙo ni lokaci ɗaya ta na faɗin" Mu je Sadiya. Mu je Alhaji na kiran ki."

Ban isa na yi musu ba sai na bita har gaban Alhaji ta kuma zaunar da ni a gabansa a kuma in da na tashi, jan majina na ke yi ina ƙokarin shanye takaicina.

Gwaggo ta kalli Alhajinmu kafin ta ce"Daga sulhun ne suka fara koke koke kuma Alhaji?

Bai amsa mata tambayarta ba, sai ma kallonta da ya yi kafin ya ce" Samu waje ki zama, saboda abin da zan faɗa ina so kema ki zama shaida."

Sai Gwaggo ta koma ta zauna a kujeran mai zaman mutum biyu dai dai lokacin da ta ke kallon Ma'u wacce ke ta faman tsane hawayenta da hanky ɗin da ke hannunta. Sannan lokaci ɗaya ta na cigaba da shessheƙan kukanta.

"Ke ma Ma'u ki bar kukan ya isa haka nan."

Ta fada cikin wani yanayi, a cikin ranta tana tunanin komai Alhaji zai yi ba za a taɓa samun daidaito ta bangaran Ma'u da Sadiya ba.

"Halima.."

Kamar daga sama na ji Alhajinmu ya kira sunana a kausashe kuma da karfi jikina da zuciyata suna rawa na ɗaga kai ina kallonsa cikin ɓacin ran da ya bayyana har a saman fuskarsa na ga ya nuna ni da yatsar sa manuniya da ya hana ni ma iya amsa masa kiran sunana da ya yi.

"Yau ce rana ta farko kuma ta karshe da zan ji ƙin ƙara kiran Ma'u da bare, yau ce rana ta ƙarshe da za ki ƙara yi mata kallon wata ba ƴar uwanki ba. Na san halin ki saboda ni na haifeki da gaske ki na da fitina da rashin haƙuri sannan ba ki da yafiya da barin abu ya wuce, sannan kina da nacin faɗa, kowa sai ya manta amman ke zuciyarki ba ta iya mantuwa. "

Ya ƙarishe faɗa da karfi, kamar zai kai mini duka daman Alhajinmu akwai faɗa in ran shi ya ɓaci. Kuma ka da ka ba ri faɗan shi ya faɗo ta kanka domin ba za ka taba jin daɗi ba.

Shi ya sa na ji zuciyata ta karye na fara kuka, kenan har a yau ma Ma'u ce za ta sake yin nasara a kaina?

"Kar na kuskura na kara jin kin danganta Ma'u da bare, ita ba bare ba ce. Jinin ki ce domin in aka tsaga jininta za a ga na ki jinin haka itama in aka tsaka na ta jinin za a ga naki, bari na tunasar da ke abin da nasan ba ki manta ba, ni na saki nono mahaifiyar Asma'u ta kama Asiya ƙanwata ce uwa ɗaya uba ɗaya. Me ya sa kike da tunanin banza ne? Me ta yi miki? Tana bin ki amman kina ƙara nuna mata tsana? Ina ce har hakuri Murja ta ce ta yi ta ba ki kika tafi kina ta cin mutumci? Ke sheɗan ce da ba ki jin bari Halima ko so kike ki zama sheɗaniya a cikin mutane?

Kuka kawai na ke yi, wannan karon kukan da na ke yi ya fi na wanda Ma'u ta yi fidda amon sauti, falon ya yi tsit sai tashin faɗan Alhaji kawai ake ji har Gwaggo tana zaune ne amman ba ta iya dakatar da Alhaji ba.

Ma'u ce ta ɗago kanta tana kallon Alhaji kafin ta ce" Alhajinmu har a waya na kira ta bata ɗauka ba sai na yi mata saƙon murya ta WhatApps bari ma ka ji." Nan da nan ta ɗauko wayarta ta shiga ta duba sai ga shi ta kunna muryanta tarwai ta na fadin"Ki yi hakuri Sadiya da abin da Shema'u ta yi miki. Har ga Allah ban san a ina ji maganar ba. Na nuna mata ban ji daɗi ba na kuma ce sai ta ba ki hakuri saboda haka zan tura mata lambarki sai ta kira ki ta baki hakuri."

Alhajinmu ya girgiza kai kafin ya kalleni ya na faɗin"Ta yi ta ba ki hakuri akan laifin da ba ita ta yi miki ba amman kin kasa hakura. Tabbas na fahimce ke ce sheɗaniya sannan ke ce ke hassada duk abun da ke faruwa."

Ina rawan muryan kuka na kwashi rantsuwa ina faɗin"Wallahi Alhajinmu..."

"Rufe min ba ki, ki kuma tsaya dakyau ki saurareni. Ga uwarki nan ta zama shaida ga mijin ki nan ya zama shaida, daga yau ina mai ba ki umarni a matsayina na mahaifinki, ki ijiye duk abin da ke cikin ranki game da Asma'u ki rumgumi ƴar uwarki. Sannan ki yi zumunci da ita ki je gidanta in abin farinciki ya same ta ki taya ta murna. Sannan ki je a lokacin jaje domin ki ta ya ta jimami. Sannan in ku ka haɗu ke za ki fara yi mata magana, ki bi ta a inda ta ke ku gaisa cikin zumunci da ƙaunar juna. Gargaɗi na ƙarshe a gareki shine ki bi umarnina ya zama wannan shi ne zama na ƙarshe da zan yi a kan wannan mganar, na ƙara faɗa miki ki yarda makaman yaƙin ki ki bi Asma'u sannan ki yi zumunci da ita, in kika saɓa ma ko ɗaya daga cikin umarnina zan yi fushi da ke fushi mai tsananin da ba ki taɓa tsammani ba Halima. Saboda haka in kina so ki rabauta har a ranar gobe ƙiyama ki yi gaggawan bin umarnin da na ba ki."

Alhajinmu na mgana ina jin kamar zuciyata za ta faso ƙirjina ta fito tsabar baƙin ciki tuni kukana ya ɗauke. Saboda ban ga amfanin ina zauna ina kuka saboda Ma'u. Na yarda ta yi nasara a kaina kamar ko yaushe.

Muryanta na rawa na ce"Na ji Alhaji in sha Allahu zan zama mai bin Umarnin ka." Na faɗa ina sauke numfashi saboda na ji kamar numfashina na shirin kwacewa.

Alhajinmu ya gyaɗa kai kafin ya ce" Kin yi kyan kai. Ki sani ko da rana ɗaya na ji labarin kin bambanta Asma'u da Rahila ki sani kin ɓata mini sannan zan daɗe ban iya kallon ki ba, zan daɗe ina miki kallon wacce ta gagare ni."

Da sauri Gwaggo ta ce" Haka ma ba zai faru ba. Sadiya kara ba ma Alhaji haƙuri."

Kaina na ƙasa na ƙara faɗin" Allah ya huci zuciyarka Alhaji. In sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba." Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso mini daga ƙasan zuciyata.

Sai ya saussauta fushin sa jin har Yusuf ya rankwafa ya na neman min afuwa har da Ma'un da mijinta sai Alhajinmu ya jinjina kai kafin ya ce" Bakomai. Na tsorata ne sabo da halin rayuwa. Ka da na faɗi na mutu na bar baraka daga zuru'a ta, na ji daɗin da kika hangi kuskuranki kika kuma yi aniyar gyarawa. Ki yi ma Asma'u sallama ta amsa miki tare da musabaha yanzu a gabana Dubu."

Ban yi musu ba na juya ina miƙa ma Ma'u hannu lokaci ɗaya ina yi mata sallama. Ta miƙo min hannunta ta na yi min wani irin mirmishin da ni kaɗai nasan ma'anarshi lokaci ɗaya tana amsa sallamata tare da sarƙe hannun juna. Ni ma sai na yi mata mirmishi kwatankwancin mirmishin da ta yi mini, ai ba Ma'u kaɗai ita iya bariki ba nima na iya tunda na fahimci ta na cin nasara a kaina ne ta hanyar amfanin da makirci.

"Ki yi hakuri Ma'u. Ki yafe mini sharrin sheɗan ne."

Haka na faɗa ina mai gayyato mirmishi da rahama a saman fuskata, ko ta yi mamaki ba ta nuna ba sai ta waske, kafin ta ce"Bakomai. Na ji daɗin haka Yar'uwata."

Readers Also Read