Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 20
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 20: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 20. Baba yakalli Mom yanuna mata files na hannunshi yace "Salima ni…
3,274 words
Baba yakalli Mom yanuna mata files na hannunshi yace "Salima ni zaki kwacema gida? Gidan mahaifina? Shi zaki maida naki sabida kinga banda sani kan harkan makaranta kaman ke? Salima tunda na aureki nataba cutar da ke? Makarantan nan da abinda kika zama yau is all thanks to me nina saki kikai karatun da kudina? Gidan nan banawa bane eh nasan ninasai filaye kusan uku na hada na karama gidan girma nayi renovation saisa yan uwana suka bar gidan yadauki sunana a paper da komi ba nasu sunayen amman hakan baya nufin nine mai gidan nan gabaki dayansa Yaya na ciki, Kawu na ciki, mahifiyarmu Gwaggo na ciki, this house is gidan gado da mahaifinmu yabari, Salima kin maida gidan da babu zufanki ko daya ciki naki sabida makarantan da karatun da kikayi na ilimin mallakan abinda babu zufanka aciki ko shi karatun lawyer?" Baki Mom ta tabe tace "kanka akeji Baban Aya! Shekarun mu talatin da aure munada diyar 27yrs shine zaka sakeni yanzu? Ni zaka saka? Maisa baka sakeni tun ina yar yarinyataba sai yanzu zakamın sakin rashin mutunci kace na tattara na barmaka gidanka, is something wrong with u?Akwai wani level da ake kaiwa a aure da wlh miji bai isa yasaki matarsa ba, Baban Aya baka isa kasakeni ba wlh! Zama daram babu inda zanje! Gidanku bawai na kwace to sell it kowani abu bane no it's just lave-rage, idan kanason gidan ku na gadon nan u want to protect it at all cost to ka zauna dani zama daram inba hakaba get ready kahakura kaima da gidan gadonku" Ijiyan zuciya Baba yasauke yana girgiza kai yace "fine gidan nan ba kirike, Alhamdulilah ni da yan uwana ba dukiya ko wani abun duniya ne agabanmu ba kirike gidan bazan taba kaiki kotu kona tsaya yakanki sabida gidan nan ba, but just know this dagayau ke ba matata bace! Me and you are complete strangers! Babu any hakki naki akaina u are on your own, I don't know you dagayau Salima, gidankuma gashi duk yanda kikeso kiyi dashi gado ne kici, kin nunamin kalanki ba yarmu kadai kika tsana ba yau kin nunamin nima you've always hated me, baki sona ko daya Salima inhar kin iya kin amfani da ilimi da wayau kika yaudareni nayi signing takardun gidan nan only shows me baki taba sona ba, kaman yanda bakison mahaifiyata da yan uwana kije bakomi, take" ya ijiye mata files din akan table yawuce yafita Mom tabishi da kallo kirjinta na bugawa feeling very bad a zuciya, she thought Baba would beg her yace ya maidata just to save gidan, itafa she cares so much about that name tag na marraige Mrs Salima Muhammad S Turaki, her name, her status is her identity! Marraige is power! But karfin hali da taurin kai yasa taki magana tasan laslas he will come back to her ta cigaba da shan shayin zuciyanta na tafarfasa kasa daurewa tayi ta tashi tabude kofa tafito dakinsu Asmeey tawuce tabude kofan babu kowa ciki kirjinta ya shiga tafartafasa yana suya kaman an zuba kwalbati.
Sauka tayi kasa yaran harsun gama breakfast sun fice waje Gambo kawai ke falon tana gyarawa tace "barka da saukowa Hajiya" ko kallon Gambo batayiba tawuce hanyar dakin Munir kai tsaye tabude kofan bai dade da tashi ba yayi wanka shiryawa yake yana kokarin saka rigansa na shaddan dayasa Mom tabude kofa tashigo dakin fuskanta a murtuke tana kallonsa, daukekai yayi daga kallonta dan bala'in haushinta yakeji rai abace Mom tace "baka iya gaisuwa bane ko bakinka ciwo yake"? Rigansa yakarasa sawa da kyar murya ciki ciki yace "good morning Mom" tsaresa Mom tayi da idanu yanda yajuya abinsa yana daukan agogonsa yana kokarin sawa tace "Aya na gidan nan har yanzu?" Da kyar yace "eh" kallonsa Mom take tace "okay yayi mata kyau, jeka kiramin Asmeey" batare daya kalleta ba yace "bazata iya zuwa ba" Mom jitayi kaman Munir ya watsamata garwashi ajiki amsan daya bata wat the hell! Ita Munir ke amsawa haka? Karasawa wajensa tayi tawani juyodashi tana kallon kwayar idanunsa da kyau tace "mekace yanzun nan Munir"? Sosai gabansa ke faduwa amman ya dake ya danne tsoron yakuma daure yaturo mata baki sosai cikin tsananin jin haushinta yace "nace miki bazata iya zuwa ba Mom" tassss! Mom ta yanka masa mari mai rai da lafiya tace "such insolence! Are you sick upstairs? Ni kakema magana gatse haka without respect? Are you talking to your Mom like this Munir?" Azuciye Munir yace "yes Mom namiki cus you are not the type of mothers da aka suffanta dake shiga aljanna" Munir yahau huci idanunsa na tara hawaye yanama Mom wani kallon tsana da rashin tsoro irin na yara, eyes nashi na looking kaman yana hararan Mom, Mom tace "ohh kayi girma ko Munir ni kake harara with those eyes kaman na aliens? Zakaci ubanka yau" tayi maganan tajuya tana neme neme abinda zata dakesa dashi taga charger laptop dinshi kawai tadauka ta cire ta taso tana linkewa tayo kan Munir dake kallonta har lokacin kawai tadaga wayan zata chaulamai rike wayan yayi azuciye yafizgo saida Mom tabiyosa kaman zata fado kansa dan kafafunta yau suna ciwo tadake tana kallonsa tace "dambe zakai dani Munir"? Yanama Mom wani kallo yana turo baki yaki magana, Mom takalli wayan tace "sake wayan nan, ka sake wayan nan nace" Munir yaki saki sai huci yake kaman zai rufe Mom da duka wlh, kana ganinsa kasan kawai dan Mom mahaifiyarsa ce da wlh saiya kaita kasa yau sabida yanda yakejin haushinta kuma ya zuciya, Mom ta bala'in girgiza ganin Munir is becoming fearless yanzu, tadake tace "is because of salla sannan kasa kayan salla da kaga other side of me" tai maganan tana yarda wayan kasa ta matsa gefe tanunamai kofa sounding super serious tace "wuce kaje ka kiramin Asmeey" azuciye Munir yana daga murya dan yasan dukanta zatayi tazo yace "bazanje ba!" Yanda Mom ta girgiza saida kafafunta sukai rawa saura kadan tai baya ta hana kanta dan kar Munir ya lura yadena tsoronta, Mom ta daki kirjinta tana huci kaman zata kama da wuta tace "Munir nike aiken ka kake cemin bazaka je ba?" Azuciye yace "I will not call Asmeey for you so that u will end up killing her completely cus she's sick and her hand yayi breaking and you sent her with the man daya mata haka, wlh wlh wlh Allah yasa Baba yarabaki da Asmeey har abada" zabura Mom tayi tayo kanshi zata kaimai mari chak Munir yarike hannunta gamgam azuciye yarike hannun so baimasan ya matsema Mom hannu sosai ba kaman zai karya, Mom kaman zatai ihu yanda ya chapke hannunta amman ta daure tana kallonshi tace "dambe zakai dani Munir eh? Ni uwarka dana haifeka zakai dambe dani? Okay beat me" ta fizge hannunta tace "beat me nace tunda kadawo dan iska shaye shaye kafara ko? Saisa har kake ganin u can beat me, Wlh wlh I will deal with you nina aikeka kaki ko, zakaga abinda zan maka" Mom tajuya fuuu tayi kofa tabude tafice dasauri Munir yabude bayinshi yashiga kawai saiya fashe da kuka sosai yana kallon hannayensa, he's very angry with Mom but kuma he's hurting yanda yarike mata hannu and wlh a lokacin zuciyanshi har rayamai yake yama tura Mom tafadi akasa, yanaji itama ta karye especially a hannu sabida takasa dukansu dagayau, sabida yanda yakejin haushinta, da kyar yahana kanshi hankadata da hannunta daya rike, he just hates her sabida yanda tasan waye Fawaz ta aika Asmeey dashi, dayayi raping nata fa? Dawazai auri Asmeey? Tazama bazawara kenan fa, yakai kusan 4min abayin yatashi ya wanke fuskansa yafito sai kawai yaji baimason fitan daman fidan wani friend nashi zaije sai kawai yakarasa yasamak kofansa key yahau gadonsa ya kwanta. 💫UWA KO UKUBA💫
✍🏻M SHAKUR
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈
CHAT ME UP DON SHIGA wa.me/+2347012181461 EPISODE 2️⃣0️⃣
Ramla ce tashigo dakin Mamie da kayan Asma'u na salla, Ya Aya takarasa shafa mata mai dakuma magungunan da Ya Mustapa yabada adinga samata ajiki wajen duk wani tabo na duka dake jikinta, jikinta duk ciwo fuskanta bai sabe ba, tayi ja tana zaune da towel da hannunta karyayye, Aya tadauki jakan taga kayan salla ne tace "Ramla simple kaya zaki kawo or even better dauko jakan dana ijiye mata agaban wardrobe naku na jiya wannan ledan" dasauri Ramla tace "toh"tajuya tafice, Aya ta kalleta tace "kinkicin komi you have to eat kona miki noodles"? Gyadama Ya Aya kai tayi alamun eh, Aya tace "ohh har yanzu baki dena son indomie ba toh shikenan, meyake miki ciwo yanzu"? Ahankali tanuna hannunta, Aya tace "zai dena sannu ko, Aysha ma zatai magana dake takira dazu bari na kirata" gyadamata kai tayi, Mamie tashigo dakin da tray na shayi mai kamshi tace "kisha shayin nan Asmeey yana helping da healing kashi sosai" Aya tace "Mamie wai baki gajiya by now bai kamata kina all this work serving namu abinci ba" dan dariya Mamie tayi tace "Wlh I'm use to it, to yara maza gareni Aya dole nine zanyi serving nasu abinci, da Allah yabani mace da tuni duk bana abubuwan nan, Ma'u ya hannun yarage zafi"? Gyadama Mamie kai Asmeey tayi, Mamie tace "sannu kinji wai ina kayanta sanyi na shiganta" Aya tace "Ramla taje takawo" Mamie tace "toh bari naje naba yayyinku abinci" dasauri Aya tace "Mamie kibarshi bari naje na basu" dasauri Mamie tace "no zauna da Asmeey" tana fita Ramla na shigowa taba Aya ledan tace "ina zuwa" tafice Aya tabude kayan wani simple english gown taciro black ne tawuce wajen kofan ta rufe da key sannan tadawo tadagata pant tafara bata akunyace tashiga sawa Aya ta taimaka mata sannan tabata gown din tasaka yamata kyau gown din Aya tai murmushi tace "kinga yanda gown din yamiki kyau" tadauki tea tabata a right hand nata dakeda lpy tace "zauna toh bari naje makiki indomie" Ya Aya tafice yarage saura ita kadai adakin, dakin tabi da kallo hakanan kawai taji tsoro yakamata dasauri ta mike hannun data rike tea dashi na rawa kaman zata kabar da tea ta shiga tafiya dasauri da kyar tabude kofan daidai Ya Mustapa na shirin shigowa ta tsaya chak tana numfashi yace "Asmeey menene give me the tea" yasa hannu ya karbi tea yana kallonta yace "bakowa adakin ne?" Gyadamai kai tayi tace "Ya Aya taje kitchen" gyadamata kai yayi yace "muje" juyawa tayi ahankali ta shiga ciki ta zauna bakin gadon hannunta ya dauka yarike yace "yana hurting sosai"? Girgizamai kai tayi daidai Ramla na dawowa dakin yace "stay with her Ramla bayan kinyi breakfast I will come back namiki fixing drip" ta gyadamai kai dakinsu Hameed ya leka yaga dukansu sunyi wanka suna bacci maida musu kofan yayi yarufe yawuce dakin Abba inda nan Mamie take yanzu yayi knocking tareda sallama ya shiga.
Around 1 Abba yafito yana sanye da tufafi mai kyau da babban riga da hula yataho dakinsu Hamad bude kofa yayi Hameed yagani zaune kan gado yayi alwala yace "bazakaje masallaci bane" adan kunyace tuna abinda yama Abba dazu yace "Hamad nake jira yana alwala a bandaki" daidai nan Hamad yafito Abba yace "kumuje" turare Hamad yawuce ya fesa yana sauke hannun rigansa sannan yataho Hameed biye dashi suka fito sauka sukayi suka fito tsakar gida Baba suka hango shima yasha manyan kaya masu kyau ya kafa hula yana gaisawa da Yayan Mom da aminansa guda biyu dake wajen sai kuwa ustazun yaran gidan dan babban malamin bai sami daman zuwa ba.
Masallaci suka shiga aka tada salla sukayi ana sallamewa da 2mins Hameed yatashi zai fice Abba yace "koma ka zauna" zama yayi kusa da Munir dake gefensa, Abba yakalli Hamad dake zaune kusada Ya Mustapa dake azkar sannan Ustaz yacire Mic daga wuyanshi yakashe duka, babban aminin Baba yafara bude wajen da addu'a kowa ya kallesa yace "tom babban aminina ya gayyace ni dan nazo nan nabada auren diyarsa Asma'u" atare gaban Hamad da Hameed da Munir da sauran yayinsu suka buga, rawa hannun Hamad yafara gently yaji saukan hannun Ya Mustapa akan hannunsa dasauri Hamad yadago kansa yakali Ya Mustapa hawaye harsun taru aciki yasauke kansa da sauri kasa, Baba ya kalli Ustaz yace "Bismillah Akaramakallahu" gyaran murya Ustaz yayi yace "Masha Allah ayau mun taru anan domin muzama shaida akan auren daza'a daura tsakanin Hussain Abubakar wato Hamad" dawani irin sauri Hamad yadago kansa kirjinsa ya buga shima Hameed dudda he felt relieved but he was shocked dayaji sunan Hamad, Munir yawani irin jin dadi harda wani motsi kaman zai kwaso shoki Hameed yamai wani annoying look ya natsu yana murmushi, Ustaz yace "da yarmu Asma'u Muhammad Sani, anyi duban jini da sauransu?" Ya Mustapa yace "Hamad AA ne, blood group O negative zai iya auren kowa" Ustaz yace "Masha Allah" nan yacigaba da daurin aure tsakanin Hamad da Asmeey akan sadaki dubu dari Baba ya fiddo da kudin yabiya duk su Abdullahi da Faisal dasu Hameed are in shock cus basu san da maganan ba kawai aka shafe, Abba yace "kawo goron da sweet Doctor" tashi Ya Mustapa yayi sai alokacin ya saki hannun Hamad da kawai ya sauke kansa kasa kirjinsa sai bugawa yake, baimasan wat he is feeling ba, Ya Mustapa yashigo da goro one bag da sweet aka bude aka rarraba Aminnan Baba suka amsa suka sa albarka sukai sallama suka tafi, Yayan Mom Alhaji Mahmood yace "toh ni ku nunamin sirikin nawa ba gane yan biyun nake ba wanne ne Hussein wannene Hassan?" Baba yayi dariya yanuna Hamad yace "gasa nan" sai kawai Hamad yaboye fuskansa a guiwa gwanin kunya sai kace wata Amarya mace, zokaji dariya a masallaci hatta Ustaz saida yayi dariya da su Ya Faisal ma haka shima Hameed saida abin yabasa dariya dudda he's in shock, Munir harda rike ciki dan wlh Ya Hamad kaman wata mace abinda yayi sosai fa ya kife fuska a knees. Baba yakame tasa dariyan yace "surukinka akwai kunya Alhaji Mahmood" Yayan Mom yace "ahh ai nagani to Masha Allah, Allah yasa albarka, ga Asma'u dai mun baka amana, mun yarda dakai cus nasan waye mahaifinka tun muna yan samari kafin ya koma kano" Baba yace "kwarai" Abba ya jinjina kai, Alhaji Mahmood yace "zama da mata sai hakuri saikuma anakai zuciya nesa dan haka ina maka fatan alkhairi bari naje Alhaji ma'assalam" yamika musu hannu yana gaisawa da kowa Baba ya bisa dan yanaso yayi magana dashi yajuyo yakalli Munir dake dariya yana washe baki uwa Aj'ı aka daurama aure yace "kai zonan" tashi Munir yayi yabisa da sauri. Ustaz yamike yayi sallama da Abba yafice, Abba yatashi yadan kalli Hameed daya sunnar da kansa yana sosakai na rashin gaskiya Abba yace "muna komawa gida za'akai kudin aurenka gidansu ita wacce kakeso din tijararre" yawuce yafita, Ya Abdullahi yatashi yana kallon Hamad dahar lokacin yakifa kansa kan guiwansa yace "ango, ango, ango Hamad" Faisal yace "wuhuhuuuu sai amarci ina gayamaka Ya Abdallah" zokaga dariya harshi Ya Mustapa saida yadan kyakyata amman a fuske, Hameed yataso shima yace "ku tsaya kuje Yaya" duk suka tsaya suna kallosa yace "yanzu kowannenmu zai dauki topic ne dazai koyamai kan zaman aure, ni Hameed his twin brother i will take him kiss and hug" zokaga dariya, Ya Faisal dan sune sako dagashi sai su yace "as yayan ango I will teach him tarayya" wani kalan tashi Hamad yayi tsaye da duka hannunsa a fuska zai fice suka rikeshi suna ihu. "Angooo Angooo" kaman zai fashe da kuka Ya Hamad har lokacin hannayensa nakan fuska yace "Yayaaaaa" Ya Mustapa na dan dariya ciki ciki yazo ya karbesa yace "dalla ku cikasa wai mehaka kuna abu kaman yara"Hameed yace "damafa yadan kyasa harda siyamata ice cream" kaman Hamad zaiyi kuka yace "ni banso" yajuya yafita daga masallaci zasu bisa Ya Mustapa yataresu yace "wai sai kun sakashi kuka zaku huta? He's in shock let him be" Ya Abdullahi yace "Ya Doctor wai ya akayi Abba ya chanza"? Ya Mustapa ya harari Hameed yace "wannan mara kunyan yanada babe so karya wahalan da Asmeey that is already going through alot shine aka hada da Hamad, once we get to kano zamu mai gini a compound a flat da zasu zauna" Ya Faisal yace "but Ya Doctor tayaya Hamad zai fara rayuwa da mace ku baku gansa ba? I'm still worried for Asmeey fa, cus can heeeeeee?" Suka wani bushe da dariya, Ya Mustapa yayi shiru but duk sun gane maganan sa, Ya Mustapa yace "well all I know is he's a man, komujima komu dade zamuga yaransa" Hameed yayi wani ihun iskanci yace "Yaya kaga dan Allah nima muna komawa kano washe garin rannan kuje gidansu Zee wlh Yaya nakai 2more months banyi aure ba zaku iya rasani washhh" kunnensa Ya Mustapa yakama yace "kaiko naughty boy" ihu Hameed yayi yana dariya yace "sorry Yaya Sorry" Ya Mustapa yace "lemme warn you tundaga yanzu naga ka takurama Hamad koka samai ido ranka sai ya baci and that goes for dukanku" yasaki kunen Hameed yanuna Faisal da Abdallah da duk ke gimtse dariya, yace "allow him to get close to matarsa, banda sa'ido you know yanda Hamad yake wlh na kamaku in anyway ranku zai baci" Faisal yace "Yaya bazan samai ido ba but wlh Yaya curiosity wan kee me I just want to see yanda Hamad zaiyi coitus" Zokaga dariya Hameed harda faduwa akan dadduma cus ya dauka shi kadaine dan iskan ashe Ya Faisal ma dan iska ne, infact yama fishi iya iskanci is the way he said coitus that killed him finish, duk kawai yanda Hamad zaiyi abu akeso agani, Ya Mustapa yakallesu da Faisal da Hameed sai kuma ya kalli Abdullahi dayaga shima rike dariya yake da kyar hannuwansa har zabura suke sabida yanaso ya tuntsure da dariya yace "ohhh hardakai Yayansu akeso aga coitus"? Ya Abdallah yawani bushe da dariya yana kama cikinsa yace "Ya Musty sorry, sorry, is not my fault, to Hamad din namune wlh ko mace bata isa tanuna mai kunya ba, ni I can't wait to see his wife with belly maybe aruwa zatasha, yaron da a bayi yake chanza kaya yayi wanka how he go do the thing now? With clothes on or off"? Zokaga dariya su ukun kaman mahaukata, ganin suna nema susa shima yayi dariyan babba dashi 40 something years kawai Ya Mustapa yajuya yafice daga masallacin yace "yan iskan yara" sunma manta duk a masallaci suke zama sukayi ciki suna gulma suna bude babin Hamadi. 💫UWA KO UKUBA💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣1️⃣ KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈
CHAT ME UP DON SHIGA wa.me/+2347012181461
EPISODE 2️⃣1️⃣
Tsaf Baba ya sanar da Yayan Mom Alhaji Mahmood abinda ke faruwa tundaga kan zancen fyade, wanda already tun jiya ya sanar dashi awaya dakuma zancen karbe gidan gadonsu datayi, ran Alhaji Mahmood yabaci yanaso yaje yasameta Baba ya hanasa yace "yabarta tayi yanda taga dama da gidan" sundanyi magana kafin yawuce shima, Baba yawuce yatafi.