Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 21
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 21: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 21. Baba na zaune dakin Gwaggo, Ammi ta shigo, Aya ta shigo, Gwaggo…
2,625 words
Baba na zaune dakin Gwaggo, Ammi ta shigo, Aya ta shigo, Gwaggo na zaune daketa washe baki, Mamie ma haka, Baba yace "Aya na aurar da Asmeey!" Dasauri Aya ta kalli Baba tace "Baba Asmeey"? Gyadamata kai yayi yace "ba'a dade da daura aurenta ba anan masallaci sabida inaso jibi su Yaya da Gwaggo suka tashi wucewa su tafi da ita" ahankali Aya da gabanta ke fadi tace "waye mijin Baba"? Murmushi Baba yayi yace "Hamadi!" Murmushi Aya tayi saikuma tayi wata cute dariya sanin Hamadi sarkin kunya takalli Mamie tasake murmushi Mamie ma haka, Baba yakalli Gwaggo yace "Gwaggo bance ki fitar da zancen nan ba Asmeey y'ata ne nakuma aurar da ita na sanar da Baffan ku Aya Alhaji Mahmood hardashi wajen daurin aure, zuwa gobe idan Asmeey tadan sami karfi da kyau zan sanar da ita, kafin kitafi inaso keda su Ramla ku hadamin kayanta tsaf da credentials nata da komi nata zaku iya ciremata kaya kala biyu da zata saka gobe da shi jibin tayi tafiya, sauran zansa akai mota yau din nan dasauri Aya tace "toh Baba" Ammi tayi murmushi tace "Allah sanya alheri Mamie" Mamie tace "Ameen Ameen nagode" dan hira sukayi Aya sai wani dadi takeji.
Ranan sai yamma Ya Aya tatafi sai alokacin Asmeey tafara jin damuwa bataga Mom ba tana nan saita fara tunane tunane Ya Hamad ma tadanyi shiru saita kalli kofa shima bata gansa ba duk saita farajin ba dadin Munir ya shigo yana wani murmushi yahayo gadon yace "Asmeeeyyyyy" dan hararansa tayi tana turo baki tace "sunana kake kira kai tsaye" dariya yasake yi yace "I am just happy sabida ke" "ni?" Asmeey tadan tambayashi dasauri yace "wai Nana" dan murmushi Asmeey tayi bata kara magana ba tadaura kanta kan pillow tana kallon yanda yake taba wayansa yana Instagram sai kawai Mom tasake fadomata arai tace "Munir Mom na side dinta?" Yana jinta Munir yayi banza da ita hannunta mai lafiya tamika ta taba Munir tace "Munir Mom fa"? Batare daya kalleta ba yace "kije takarasa karya dayan hannunki duka kinga saiki huta" shiru tayi bata sake cewa komiba kanta na kan pillow tana kallon wayansa tashiga lumshe idanu ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Sai wajajen 11 nadare yashigo gidan kawai dan kar ace this and that ne da yau yakoma Kano sabida kunya shigowa gidan yayi yahayo sama zai shiga dakinsu Abba yace "Hamad" dago kansa yayi yasauke yace "na'am" wucewa yayi gaban dakin Abba daya shiga yabisa abaya Mamie na zaune tana kallon wani shiri da akeyi a tv takalli Hamad din daya kasa kallonta kasa akasa yace "Mamie ina yini" "sannu da dawowa" Mamie ta fadi, Baba yadauki bandir na 1k din yadago yace "gashi dazu Baba yazo nemanka yabaka bakanan, sadakin Asmeey ne karike mata idan tadan sami lpy saika bata lokacin muna kano" kallon kudin yayi saiya kasa karba yasake sauke kansa kasa Abba yace "ha'a wai ba sako nake baka ba koko cewa nayi kudin naka ne? Kudin matarka ne karba kaje ka ijiye" yana ahaka kansa akasa kaman mai tsoro yadaga hannuwansa yamikama Abba duka biyun yakasa dagokai saura kadan Abba yayi dariya yasamai kudin a hannu Hamad ya karba kaman flash yajuya dasauri yafita daga dakin, dakinsu yawuce ahankali yabude kofan bakaramin dadi yaji dayaga Hameed na bacci ba shigowa yayi yamaida kofan yarufe yatafi wajen akwatinsa yaduka yasaka kudin achan kasa sannan yatashi yafada bayi yafito yahau kan dadduma sannan yadawo gadon ya kwanta yayi shituuuu ahaka bacci am yayi awon gaba dashi.
Surutun Gwaggo ma yau yasake tadata daga bacci bude idanu tayi ahankali Gwaggo na saman kanta tana tafamata uban yawu a hannu wai addu'a take dauke hannunta tayi tana turo baki Gwaggo tace "bazaki bari nagama miki addu'a ba bakiga kin denajin zafi ba" ahankali tace "ni har yanzu zafi yakemin" baki Gwaggo tasaki tace "ahhhh lallai kin dace da Hamad dan bakin halinku daya Asama, ohh ni Allah baya amsan adduata kenan ko bakina baida tsarki" tashi tashigayi Gwaggo tace "wai bazaki zauna najarasa ba" ahankali tace "ni fitsari nakeji" tawuce bayi Gwaggo tabita da kallo tace "hartadan fara kumari" zaki iya tsarkin da hannu daya konazo namikin tsarkin?" Juyowa Asmeey tayi ta kalli Gwaggo tace "huu'um" Gwaggo ta kwashe da dariya tace "ai shikenan jeki abinki nima daman nayi maganan ne amman ina tunanin warin dazan shaka idan kin hada da kashi" maida kofan tayi dasauri ta rufe tafito da alwala tazo tahau dadduma ahankali take salla da hannun.
Yauma haka aka wuni agidan Hamad baya nan only God yasan ina yake zuwa ansan he will definitely do that so babu wani cikin bothers dinsa daya nemesa. Yau all through Gwaggo na dakinta hakan yasa Asmeey takasa zuwa wajen Mom but zuciyanta na zuci zucin tunanin Mom, sai bayan Isha'i Gwaggo tasa Mamie takamata ta kaita kasa dantai bacci da asusuba zata tashi tahada kaya tunda Allah baiyi zuwansu kauye ba sabida ciwon yarnan Asama. Sallama Baba yayi hakan yasa Asmeey tadago kanta ganinsa yasa tashiga kokarin tashi dasauri Baba yakarasa wajen gadon yakai hannunsa yadagata yana saka mata pillow abaya yace "sannu ya jikin"? Ahankali tace "dasauki Baba" zama yayi bakin gadon yana facing nata yakai hannunshi ahankali yadauki hannun nata da aka kulle yana kallo yayi shiru fuskanshi yayi wani iri kasan he's hurting hakan yasa gently Asmeey tace "Baba bayamin zafi yanzu wlh" dan kallonta yayi har yanzu fuskanta bai dawo daidai ba kana ganinta kasan taci duka wlh, sai yaji kaman Allah zai kamasa for all the pain she went through, Asmeey is the most beautiful daughter dayake dashi mai kyawun hali da hakuri da biyayya she's going through this pain duk baisani ba and yana gidan, ijiyan zuciya ya sauke yace "mesa baki sanar dani kalan dukan da Mamanki ke miki ba"? Dan zaro idanu tayi tace "Mom bata wani dukana Baba sai once in a while kawai idan na bata mata rai ne"lumshe idanu Baba yayi yabude yace "naga jikinki Husna, i saw duka dukan, i saw hands naki" sauke kanta kasa tayi da sauri lips dinta yashiga rawa chan tace "nike mata laifi Baba" ajiyan zuciya Baba yasauke anatse yace "Asma'u" hakanan taji gabanta yafadi tace "na'am Baba" ahankali Baba yace "jiya da rana bayan sallan azahar na dauramiki aure da cousin dinki, Yayanki Hussain, Hamad!" Wani wawan faduwa gabanta yayi dasauri takalli Baba gabanta na bugawa beyond measure dan har Baba saida yagani yasa hannu yakama hannunta anatse yace "I dont know mesa mahaifiyarki kemiki abinda take miki but ban haifeki dan wani ya kashemin ke ba and Munir ya sanar dani komi dan yajuyo maganan datake gayamiki adaki kan tamiki miji da yanda tazage yan uwana harda kiran mijin naki mara aiki da abinyi"Baba yace "amatsayina na mahaifinki ni da Yayana muka hada aurenki da Hamad" kawai sai hawaye sharrr ya sauko daga idanun Asmeey tasauke kanta kasa tanaji kaman mafarki take Baba yace "sadaki dubu dari nabawa mijin naki yarike miki kudin kukaje kano zai baki, gobe da izninin Allah zaku tafi Kano aduk sanda komi yazama daidai za'a tsara lokacin da za'a kira mutane ayi yinin biki wato walima, dazu nasaka yayarki Aya tahada kayanki tsaf itada Ramla ankai mota" Baba yasauke ijiyan zuciya yana kallon ya da take share hawaye Baba yace "iya abinda nasani shine kin gama university Asma'u, zancen zuciyanki law school lies a tafin hannun mijin naki sabida shine keda iko dake, idan yaga dama yabarki kije idan yaga dama yahana shine mai iko dake yanzu" Baba yasake yin shiru sannan yakai hannunsa yakama hannunta ahankali yasake daura dayan hannunsa saman kanta yace "Asma'u nasan yanda kikeda tarbiya da natsuwa mijinki Hamad for now baida wani tsayayyen aiki, ki zama mata mai tsoron Allah da kaunar mijinta domin Allah, kada ki takuramai da siyan abubuwan kyalekyalen duniya siyamin kaza, siyamin kaza, ki zama mai godiyan Allah kiyakuri da abinda ya iya samu yabaki, kada kice dan kinga matan yayyinsa da kaza sai kema yamiki kaza, wata rana sai labari shi arziki na Allah ne, kuma yana bawa duk wanda yaso, Hamad nada kwazo zai kula dake iya gwargwado, iya karfinsa kuma kinji" gyadamai kai tayi tafashe da kuka maganganun namata wani iri, Baba yace "Hamad baida gida, yanzu kukaje kano a flat din Abba da Mamie zaku zauna kafin agama gina flat dinku, Abba Yayana ne kuma matsayin mahaifina yake bazai taba bari ki cutu ba hakama Mamie, ki kula dasu Asmeey kinga sun soma gajiyawa jiki ya tsufa ki zama mai taimaka musu da abubuwa da dama tundaga kan girki da sauransu kinji Asma'u" Baba yasa hannu yaciro wayanta da Ramla takawo mai dazu yace "ga wayanki nan nacire sim naki nada zan ijiye wajena zuwa nan gaba, nasaka miki wata SIM card danake dashi ki dinga amfani dashi, Asma'u ina sonki nayafe miki duk wani abu dakika tabamin da Wanda na sani da wanda ban sani ba sannan ina neman yafiyanki ina matsayin mahaifinki but i couldn't protect you kalleki yau Asma'u kiyafema Babanki kinji" dawani sauri Asmeey ta rungume Baba tana kuka murya kasa kasa tace "Baba bakamin komiba baka tabamin komiba dan Allah kadena rokona Baba" tafashe dawani irin kuka, Baba yadagota yakai hannu yashare mata fuska yace "I am sure babu wanda zai kara dukanki agidan Yayana, Mijinki, Yayinki da Abba will shield you Asma'u thank you for being a good daughter to me, me rufama iyayenta asiri, mai hakuri da juriya da kwazo, ina alfaharin zama mahaifinki" kara rungume Baba tayi tana kuka, Baba yayi murmushi yana shafa bayanta yace "go and start a new life kinji"? Dagowa tayi ahankali takalli Baba tace "Baba Mom tas…."? Baba bai barta ta karasa maganan ba yace "mahaifiyarki mahaifiyarki ce har abada Asma'u but kaman yanda banda wani iko akanki yanzu itama batadashi kina karkashin Hamadi yanzu ba muba kinji" gyadama Baba kai tayi gabanta na faduwa ita kadai tasan ya zuciyanta ke mata sai wajejen 11 Baba yabar dakin ta kwanta tai shiru tana kallon sama jitayi bakinta ya bushe dasauri tatashi zaune da kyar takalli side drawer tabi duka dakin da kallo babu bottle water da dane data kira Mamie but hakanna saitaji tanajin nauyinta bamataso su hada ido, ahankali tasauka dagakan gadon tamike tsaye tunda Baba yafita bataji any motsi ba maybe kowa yayi bacci tunda gobe zasuyi tafiya, daya daga cikin gown din Ya Aya tasaka red mai botura agaba ya tsaya mata a gabada guiwa but baikai har kasa ba, babu dan kwali akanta ko hula, rigan short hand garesa, slippers tasaka tabude kofan ahankali tafito tana tafiya, hannunta always feels kaman kaya sabida nauyi ko na daurin da aka matane oho, staircase tahau tasauka a first matakalan da kyar tana shirin sauka na biyu…. "Ina zaki?" Chak Asmeey ta tsaya sabida muryan Ya Hamad dataji da kamshinsa duka at the same time, wani kalan nauyi taji tajuyo balle ta kallesa yau, sai kawai tasauke kanta kasa lips nata yahau rawa kaman yar baby tace "ruwa zanje kitchen na dauka" murya ciki kaman baiso yayi magana yace "go inside, I will bring it for you" gyadamai kai tayi still taki kallonsa ta taka bene dayan data sauka akai tahayo nan falon sama tawuce dakin Mamie, Hamad dake sanye da joggers ash color yana sanye dawani black t-shirt dayamai bala'in kyau yawuce yasauka kasa, kitchen ya shiga yadauko bottle water marasa sanyi guda biyu yahayo sama, kofan dakinsu yakalla sannan yawuce dakin Mamie ahankali yabude kofan batare daya bar door din yayi kara ba ya shiga ciki. 💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 2️⃣2️⃣
Hakanan gaban Asmeey yawani fadi ganin Ya Hamad yashigo dakin yamaida kofan yarufe kawai yau saitaga Ya Hamad yafi koda yaushe mata girma, saitaga yamafi Ya Mustapa tsayi da cika, maida kanta kasa tayi dasauri ganin zai juyo, juyowa yayi yadan kalleta tana zaune bakin gadon kanta akasa, yatako yafara zuwa sai kawai Asmeey tafara wasa da fingers nata she's just so nervous and tense jikinta namata wani iri harya karaso gaban gadon ya ijiye gora daya kan side drawer hannunta Asmeey ta mika dakedan rawa zata karbi dayan bottle dake hannunsa sai taji shiru bai bata ba. Dan daga kanta tayi kadan ganin bai bata ruwan ba, budemata goran ruwan yake idanunsa nakan ruwan da fararen hannunsa kumbunansa agyare gwanin ban sha'awa, maida kanta kasa tayi ahankali, bude ruwan Hamadi yayi yakalleta tareda mika mata calmly kaman wanda baisan yanda ake daga murya ba yace "take" hakanan kawai saitaji hannunta na rawa she's trying to control it takasa tashiga mikamai hannun yana kallon hannun samata bottle din yayi a hannun ta karba tadawo dashi jikinta still hannun rawa yake tadaura kan cinya tarike trying tadan natsu cus she's shaking too much and she doesn't know why, kusan 3secs tayi ahaka kafin ahankali takai ruwan baki tasha da dan yawa sannan tacire abakinta tamikamai hannu yakawo zai karba ta dauka ya amsa kawai tasaki, goran yafadi akasa dasauri ta kalla tace "sorry bansan bak…." Ta sauko daga gadon zatai tafiya ruwan yajata zata zamiye tai baya dawani irin sauri Ya Hamad yariketa ta hanyar kama waist nata da kafadanta tadan shigo jikinsa bawani sosai ba yana kallon floor din batare dayama lurada abinda yayi ba kawai tashi tsigan jikinshi yayi sosai dasauri ya kalleta itama Asmesy ta kalleshi gabanta na faduwa asanyaye eyes nawa nawani shinning, her body is so warm da yanajin warmth din a hannunsa dake waist nashi ga idanunwanta tana kallonshi dayaji cikinsa yafara juyawa da sauri yacire hannunsa daga waist nashi dana shoulder nata atare dukansu suka sauke idanunsu Hamad yadan koma baya kadan, dasauri takoma baya adan daburce tajuya zara wuce, murya kasa kasa yace "ina zaki"? Asanyaye tace "mop zan dauko" juyawa yayi yace "don't worry" wucewa yayi yabude kofa yafita bai jimaba yadawo da mop, Asmeey tamikamai hannu zata amsa sai kawai yawuceta yashiga gabanta yafara goge ruwan Asmeey ta tsaya tana kallonsa adan sace takasa denawa, he's so calm! He's kind, and yanada good heart, gashi da tausayi, and he's respectful! Dago da kansa yayi suka hada ido dasauri ta sauke kanta kasa kaman wata munafuka, jingina mop din yayi abango ahankali yasa hannunsa yadanja zanin gadon ya gyara yasa hannu yayi dusting dudda babu any dirt agadon sannan yadan matsa gefe batare daya kalleta ba ahankali yace "zoki kwanta" gyadamai kai tayi ta taho ahankali ta shiga kwanciya da kyar yadan tsaya yana kallonta saikuma ya matso gadon dasauri ta kalleshi kallonta shima yayi right in the eyes dawani irin sauri ta lumshe ido, bargon yadauka yana rufa mata saiya sauke gaze nasa kasa yajuya dasauri yadauki mop daya jingina a bango kafin chan kasa kasa yace "good night Husnah!" Wani kalan runtse idanu Asmeey tayi da karfi tanajin wani iri ajikinta, the way he called that name Husnah sai kawai taji no one does it better than him, saitaji tafison ana kiranta Husna than Asmeey ma, bude kofa taji yayi hakan yasa tadan bude idanunta kadan daidai yana fita juyoda kansa yakarayi da gudu ta runtse idanun sai taji yafice ya maido kofan yarufe ahankali. Bude idanunta tayi tana sauke wani irin ijiyan zuciya she's feeling some wired movement ajikinta especially her tummy kaman butterflies na tashi, murya chan kasa tace "yanzu ni Matar Ya Hamad ce? Matarshi Matarshi?" Sai kawai tawani kankame bargon murmushi takejinyi but saitakiyi, wani dan karamin waje in her heart is happy she's his wife batamasan mesa hakan ba ko menene dalilin ba, but the rest of her heart is just fear tana mamakin tayaya Mom ta yarda da aurensu da Ya Hamad cus batason mutanen kokuma Mom bata yarda ba Baba yamata auren? Or maybe Mom ta yarda sabida abinda Fawaz yamata? Sai saka take tana warwara ahaka bacci yayi awon gaba da ita. *