Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 7
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 7: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 7. EPISODE 7️⃣ Baba na falo dukansu suka shiga gaidashi yakalli…
3,306 words
EPISODE 7️⃣ Baba na falo dukansu suka shiga gaidashi yakalli Asmeey yace "meke miki ciwo yanzu?" Ahankali tace "bakomi" yakalli Munir yace "kaifa"? Shima ahankali yace "bakomi Baba" Baba yace "okay kuje ku gaida Maman ku tana ciki" dukansu gaba daya suka wuce kitchen Mom na tsaye cikin kitchen din tana directing yan aiki duka suka shigo suna gaidata she answered dukansu banda Asmeey da Munir, tace "Ramla bring crete na egg from the store" Ramla tace "to Mom" tawuce store, ahankali Hamda tace "mezanyi Mom" kaman bada ita ake magana ba Mom tace "Hannatu sa ruwa a doyan nan wannan yayi kadan" ahankali Munir yace "Mom kiyakuri" kaman bada ita sukai magana ba Mom tace "yauwa ruwan yayi hakanan hannatu daura akan wuta amma yaran nan tea kuma su Yusra" Ramla tafito ta ijiye egg din Mom tace "zaki iya tafiya" tawuce ta tafi su suna tsaye Mom tacigaba da abinda ke gabanta kaman bata gansu ba kusan 10min suna tsaye awajen Baba daga falo yace "Asmeey Munir kuzo nan" juyawa sukayi suka fito daga dakin sukazo falo Baba yakalli Asmeey yace "jekisa kaya I will take u to hospital kafin naje aiki"gyadamai kai tayi tawuce Baba yamike yawuce sama, Mom na tsaye a kitchen din wayanta yayi kara takalla "Ki sameni a side naki" takaranta sakon Baba. Anatse takalli Hannatu tace "cigaba ina zuwa" tawuce sama falonta tashiga dakinta Baba baya ciki hakan yasa tawuce dakinshi dake side nata tabude kofan yana zaune akan gadonshi tamaida kofa tarufe ahankali tace "ina kwana Alhaji" ranshi a masifan bace yanunata da hannu yace "Salima akan yaranan nan ni da ke wlh wlh zamu samu matsala zan sabamiki sosai! Yarana sune rayuwana you know that! You know how much I love yarana! Why? Akanme zaki dinga azabtar dasu? Munir namijine yanada those manly features in him Is not proper ki dinga dukansa agaban kanninsa, he's not a child he's 20yrs, akwai other ways na hukunta yara not by beating! Mesa kin cika saurin hannu? Kinga tabon da kikama Asmeey a jiki? Wat is wrong with you Salima? Mesa kin cika zafi? For God sake Asmeey is a gurl aure zatayi gidan wani zata haka kikeso aganta da tabo abaya? Me amfani kalan wannan zuciya taki?Kowa yasanki da masifa yaran gidan nan babu wanda baya tsoronki! Ki kiyayen mini yara! Ki kiyayesu! Wlh wlh duk randa kika kara daga hannu kika daki ko Asmeey ko Munir Allah sai kinga tsananin bacin rai na wlh kuwa, idan sun miki laifi give them punishment Munir zaki iya sashi share compound ya wanke all cars na gidan nan I will not talk, Asmeey ma you can give her any punishment, duk randa kika kara tabasu san zabamiki Salima" Baba yayi maganan da karfi, kallonshi Mom tayi dudda ranta abace amman sai ahankali tace "hmmmm Alhaji kenan! Stay out of this please, ba ruwanka da yanda zan hukunta yarana, kuma wlh sai sunji ajikinsu especially Asmeey dataja da authority dina" Baba na mata wani kallo yace "I can lay down my life for yarana especially Asmeey! Kiyi kuskuren kara tabamin yara kiga"yajuya yafice fuuu dan ranshi yabaci jiyama sabida kar yayi abinda zaiyi nadama daga bayane yasa baizoba Mom tabishi da kallo yana fitowa afalo yaga yaran yawuce, fuskanshi ahade ya shiga mota driver ya jasu ko 1hr basu bataba suka dawo gida yace "Munir shirya katafi school" gyadama Baba kai yayi yawuce dakinshi Baba yakalli Asmeey datagama zuru zuru yace "jeki kwanta kihuta" gyadamai kai tayi ta tashi tawuce saida yajira Munir yafito sannan suka fice tare, Asmeey na shiga daki kawai tasami gefen gado ta kwanta Ramla ta kalleta duk jikinta yayi wani iri tace "nakawo miki abinci?" Girgiza mata kai Asmeey tayi, Ramla tai shiru tana kallonta bata taba furta maganan nan a fili ba sabida tsoro but anya Mom ce ta haifi yaran nan especially Asmeey, Mom treats the girl kaman wata abokiyar fadanta yar adawanta, Asmeey na tsoro mamanta har cikin kayan cikinta, she just wants to understand something why is Mom like this? Menene abinso a yarka tadinga tsoronka kaman taga mala'ika? She's too small to understand ne ko akwai wani abune why do Mom hates Asmeey? Wlh da itane Ammi kemata abinda Mom kema Asmeey da tuni ta gudu tabar gidan nan, dan ijiyan zuciya kawai ta fuzar saita zauna ahankali gefen Asmeey, hannunta takai ta dafa kafadanta murya chan kasa tace "Asmeey" dago kanta Asmeey tayi ta kalli Ramla sai kawai ta fashe da kuka ta kifa kanta a kirjin Ramla tace "Ya Ramla I'm a bad daughter I hurt my Mom, bai kamata na tsaya inata sauraron abinda Munir yaketa fada gama da Mom ba, a good daughter bai kamata ta tsaya and listen to any magana ko kalamai marasa kyau akan mahaifiyarta ba, and nadinga tarema Munir da zata dakeshi i didn't even know why I did it kawai yabani tausayine, banso ta dake shine, da Mom ta daki Munir gwara ta dakeni, he said all he said out of anger but ai Munir is a good boy, he always care for me he shares everything he has with me" ahankali Ramla tace "konine bazanso adaki Munir ba, stop crying hakanan, Mom zata hakura ya isa, you are hurting yourself Asmeey" ijiyan zuciya kawai take ita kadai tasan yanda takeji a zuciyanta, maganganun Mom sun zauna aranta waye ita zataja da authority Mamanta? Was she trying to show Mom tafita son Munir bayan Mom ne ta haifeta? She is feeling so bad and guilty, ahaka baccin da batayi last night ba ya kwasheta ajikin Ramla, Ramla ta kwantar da ita she's feeling very bad even though sunada different mothers but sunason junansu regardless saisa ma Baba ke hada yaransa waje daya su kwana kuma kusada dakinshi. Tashi tayi ahankali tafito daga dakin tawuce dakin Ammi tabude kofa, Ammi na zaune a falonta wani wa'azi takebi a Sunna tv Ramla ta shigo hakan yasa ta kalleta dasauri ta maida kofan tawuce wajen Ammi ta zauna kusada ita dab sai kuma tayi shiru Ammi tace "menene? Meya faru?" Kaman bazatai maganan ba takasa rikewa murya chan kasa tace "Ammi mesa Mom batason yaranta especially Asmeey kaman yanda ke kike sona?" Tsareta Ammi tayi da idanu tace "idan gulma yakawoki tashi kibarmin daki" kaman zatai kuka tace "wlh Ammi Asmeey tausayi take bani sosai, Ammi kinga ke baki dakinmu baki kwana tareda mu, I use to see wat she's going through kullum, Ammi idan Mom tabata manya manyan files din nan nasu na kotu idan yarinyar tazo bata iyaba ko bata gama abinda Mom tasata ba kaman zata zare kaman zata haukace wani zubin har zawo takeyi wlh kaman zatai hauka, Ammi all of us zamuyi bacci banda ita sabida she's trying to read duka abinda mamanta tasata, saisa most of the time saina tashi nabar dakin cus idan ina kallonta zuciyana breaking yake wat kind of mother is Mom Ammi? Why is she making her daughter go through so much pain? And Asmeey can't react sabida she feels abinda Mom kemata is okay and is normal, Ammi batada lokacin kanta sabida Mom kanta ba kitso sabida Mom, time din dazata zauna ta kula da kanta takasa sabida tunanin files din Mom, what kind of mother is Mom eh Ammi?" Murmushi Ammi tayi tace "the best mother but mai worst approach, Allah ya kyauta ke banson maganan baruwanki kicire idanunki akansu yanda nakeyi dake dasu Yusra ba dole ne sai Mom tayi haka da nata yaran ba so mind your business" hawaye ne yataru a idanun Ramla ahankali tace "Ammi please ki gayama Baba azaban da Asmeey is going through cus bai sani ba, Ammi the worst part is Asmeey can not even show cewa she's sad! Wlh bantaba ganin sad young girl kaman Asmeey ba, waya babu any social media sai watsapp, waya babu any contact saina sisters nata da yan gidanmu, friend kwara daya Mom tahana, ba saurayi, school Mom takasa ta tsare ita ke kai yarinya tadawo da ita, Ammi wlh I hate Mo…." Wani kallo da Ammi tamata yasa takasa karasa maganan, strictly Ammi tace "tashi kifita daga dakina" ahankali ta mike tawuce tafita daga dakin. Around 11 Asmeey ta farka gently ta tashi zaune har zazzabi zazzabi takeji bathroom nasu ta wuce tahada ruwan zafi sosai tai wanka tajuya tana kallon bayanta ta madubi da sheda tako'ina sunyi ja abunka da faran fata, ijiyan zuciya ta sauke sannan tafito tazauna gaban madubi tadauki mai tafara shafawa tana cikin shafa man taji wayanta na ringing har mantawa take tanada waya, da sauri ta juyo akan gadon taga wayan hakan yasa ta tashi ahankali tasa hannu ta dauki wayan tana kallon number which is new, ganin sabon number ne saitaki dauka anata kiranta chan wayan yasake ringing tana dagawa taga Mom dasauri ta dauka kirjinta na bugawa sosai ahankali tace "Mom" Strictly Mom tace "when did you become deaf and dumb? Are you blind da bakiga anata kiranki awaya ba? Fawaz ne call him back kuyi magana" gyadama Mom kai tayi kaman tana gabanta tace "t…toh" Mom ta katse wayan dailing number tayi back harya katse ba'a dagaba sai number yakirata back ahankali tadaga tace "Hello Mom tace nakiraka" shiru akayi kaman ba mutum adayan bangaren hakan yasa Asmeey tace "hello" cikin wani husky voice yace "da Mom batace ki kiraba da bazaki kiraba?" Ahankali tace "eh" anatse yace "why?" Ahankali tace "sabida Mom forbid me from talking to kowa banda my family" dan murmushi Fawaz yayi muryanta bala'in dadi, yadan murmusa yace "ai nima yanzu I'm part of the family since I'm going to be your husband!" Hakanan Asmeey taji gabanta yafadi dumm! Takasa magana kawai tunaninta ya tsaya chak, Fawaz yace "Mom choose me to take care of her last baby gurl, I'm your husband to be Asma'u" abu taji ya tsaya mata awuya sai taji kaman kuka takeji saikuma takasa, murya chan ciki yace "I love you Asmeey" sauke kanta kasa tayi this is the first time wani ke gayamata yana sonta, anatse Fawaz yace "zan dinga kiranki wifey daga yanzu" shiru still tayi ahankali yace "I will be going to London gobe it's a 2days trip idan nadawo I will come and see you okay Wifey" shiru tayi jin batayi magana ba yasa yace "are you there" rasa abinda zatace yasa tace "wayana zai mutu my battery is low zansa charge" dasauri tacire wayan daga kunnenta ta katse ta yarda wayan tareda kifa kanta agado tana sauke ijiyan zuciya. Kusan 3mins tayi ahaka sannan ta tashi tawuce wajen wardrobe nasu tabude wani atampa taciro gown tasaka green yamata so simple a jiki tasaka hijab sai kawai tahau kan dadduma. Around 3 Mom ta shigo gidan kashe motanta tayi ta shigo falo Ramla tace "Mom sannu da zuwa" ko kallonta Mom batayiba tawuce daki abinta Ammi tafito daga dakinta takalli Asmeey datagani gaban dakinsu tana kallon bangaren Mom sai kawai tazo tawuceta ta tafi dakin Mom kai tsaye tasa hannu tabude kofan da sallama Mom na zaune tana kokarin ciro iPad mata daga cikin jakanta ganin Ammi saita tsaya tana kallonta Ammi ta maida kofan tarufe tazo ta zauna kan kujeran dake facing na Mom anatse tace "Maman Aya nasan maganan dazan miki ba lallai ta miki dadi ba, sannan ba hurumina bane but all I know shine d'a na kowa ne! Asmeey da Ramla da Munir duk daya suke awajena" Ammi ta danyi shiru sannan ta kalleta ido cikin ido tace "Salima yaran nan mune muka haifosu amman kisani amana ne su agaremu wanda Allah yabamu rannan gobe kiyama Allah zai tambayemugame dasu, hakkinsu na kanmu, idan muka cutar dasu Allah zai saka musu sannan zai hukuntamu! Kene mahaifiyar yaran nan kinsan me kike musu kinsan ya fushinki yake aransu, nasan sun miki laifi but yanda kika sharesu is torchuring them, tun jiya they couldn't eat sabida ke! They couldn't sleep sabida ke, Asmeey tun jiya takasa saka lafiyayyen abinci abakinta same with Munir dudda Babansu yatasashi agaba yatafi school tun safe, I'm sure ba lallai yama gane abinda ake koyarda su a makaranta ba! Gabaki daya yaran kin barsu agantale duk sun zama wani iri, idan ciwon zuciya ya samesu ko hawan jini I'm sure you will not forgive yourself Salima! It's okay for us mothers to be angry but kinfi kowa sanin mai fushinki yakema yaran nan I don't even know wat I'm doing her but seeing them is breaking my heart, what is so big dazakima Asma'u kalan tabon da hala yaran dazata haifa nan gaba zasu gani a jikinta? Aganina me wacce zatai fada ne da duk wanda zaiyi inflicting such pain ajikin yarki mace ba ke kimata dakanki ba, wallahi Allah zai tsayar dake akan yaran nan, amman kiyakuri idan na shiga huruminki" Ammi na maganan ta tashi tawuce kofa tabude tafita, Mom tabita da kallo ranta ya dagule, yau Aya da Aisha duk saida suka kirata kuma tasan Babansu ne yakira ya sanar da su, kafafu ta kada tai dan ijiyan zuciya ta sauke anatse tace "Lami" da sauri yar aikinsu Lami tashigo dakin anatse tace "gani Hajiya" "kiramin Asmeey" Mom tafadi atakaice hakan yasa Lami tafice. Asmeey na zaune kan gado idanunta sunyi jazur Lami tabude kofansu tace "kizo Maman ki na kiranki Asmeey" dasauri Asmeey ta mike tsaye ta gyadamata kai gabanta faduwa yake, tafito tana tafiya ahankali tawuce side na Mom ahankali tabude kofa, babu kowa a falo hakan yasa tawuce bedroom din tai knocking da sallama daga ciki Mom tace "come inside and lock the door" kofan tabude ahankali babu kowa a dakin gadai kofan bayi a bude maida kofan tayi tarufe tasa lock ta tsaya awajen, daga bathroom Mom tace "zonan" wajen bayin Asmeey tayi gabanta na faduwa sosai taje gaban bayin ta tsaya, Mom na tsaye wajen tap ga bucket tana tara ruwa tama Asmeey wani kallo tace "zonan" wani irin nishi Asmeey tafara tana kallon Mom, yanda kirjinta ke motsi zaka dauka fashewa zaiyi sai kawai hannayenta suka fara rawa jikinta ma haka takasa magana, tadan shigo ta gaba gaban bayin sai kuma taji knees nata sun kasa daukanta tadafa bango zatai kneeling bakinta na kokarin furta magana. "M…..Mo….Mom…." Taku daya Mom tayi tazo wajen tasa hannu tawani fizgota cikin bayin Asmeey zata tsala ihu Mom ta bugata da bangon bayin takai hannayenta kan wuyanta ta shaketa da bala'in kyau idanunta na kadawa tace "because of you mutanen da basu kai komi ba, in educational level i think NCE gareta but tanada audacity da zatazo tana gayamin maganan banza ana cewa Allah zai tambayeni sabida ke, kedin banza da wofi, Babanki bai kwana anan ba dudda yana bangarena and still yabiyoni yacimin mutunci akanki this morning, are you showing people ina making naki sad eh? Are you showing mutane I'm hurting you"? Girgixamata kai Asmeey tayi tana tari idanunta sunyi ja kaman zasu fito, Mom nawani irin kallonta tace "nina haifoki and I can kill you babu abinda zai faru, Shegiya wulakantacciya sabida ke anata kirana, wani daraja gareki Asma'u dan Maman ubanki" wani Irin kyarma tafara idanunta na juyawa kaman zata mutu ganin haka yasa Mom tasaketa Asmeey ta zube awajen tana wani irin tari tana bankarewa tana dukan wuyanta, Mom ta tsaya tana kallonta zuciyanta na tafarfasa sai kwai ta juya ta sunkuci bucket na ruwan datake tarawa ta daga ta juye akan Asmeey tai wani irin ihu da baya fitowa sosai Mom tace "Shegiya jaka kawai duk sanda akamin magana akanki sai kinji ajikinki" zata ijiye bucket din sai kuma ta daga bucket din ta shiga bugama Asmeey tana rafka mata duk ta inda ta samu Asmeey na wani irin kuka tana kare fuskanta da hannayenta akasan bayi, Mom ta jefar da bucket din daya fashe tajuya tafita daga bayin tarufe bayin tana huci sosai. Kaya tawuce ta chanza sannan tafita daga dakin tawuce kitchen dan yauma Baba na side nata. Kusan 1hr tana akasan bayin ahaka sannan ta dafa bango ta lallaba ta tashi ta zauna ta kankame jikinta, this is the reason jiya she tried to protect Munir cus bataso Mom tafaramai Irin wannan dukan gwara ita ayita mata dan tama fara sabawa, sosai takejin sanyi but unless Mom ce tazo ta budeta bata isa ba tafito da kanta ba, wani irin zama tayi kaman almajira tana kallon window bayin hawaye na fita daga idanunta kadan kadan har wajajen 5:30 na yamma sannan taji an shigo flat din. Tana wajen akazo aka bude kofan bayin dasauri takalli Mom jikinta na rawa muryanta baya fita sosai tace "I am sorry Mom" wani kallo Mom tamata ta daka mata tsawa tashi kicire kaya, zabura tayi tamike tsaye da kyar tana dafa bango ta shiga cire kayan Mom na kallonta hawaye sake kwararo mata daga idanu sukayi Mom tace "yayyinki basu taba ja da dokana ba and look at them they're living a very fruitful life, I will say this to you for the last last! The next time zan ce kiyi abu ki kiyi, na hanaki abu kikiyi, konace kiyi abu ki kiyi wlh wlh zam share sunanki daga cikin yaran dana haifa Alhamdulillah bake kadai gareni ba" daidai tacire rigan yarage sauran pant and bra hannayenta duk ciwo sabida yanda tadinga kare fuskanta dasu da Mom na bugamata bucket, Mom ta mata wani mugun kallo tace "ko ina zakikai girman nono oho jaka kawai saina kaiki an ciresu cus suke saki feeling kaman kin girma bakisan zan iya tattakaki ba kokinkai shakera dari, juya nagani" juyawa tayi Mom tabi bayan nata da kallo duk shaida na dukan shekaran jiya juyawa tayi takoma daki chan ta dawo da magani a hannu ta bude tafara shafamata tana fada tace "kunyi waya da Fawaz"? Gyadama Mom kai tayi alamun eh, Mom tadanyi shiru chan cikin kakkausan murya tace "I choosed him for you! Shizaki aura, shi kadai ne namijin dana yarda dashi in your life kuma bance you should get distracted da soyayya ba, tsakani ki dashi biyayya, your top pariority shine ki gama Law school da good grade, sai bayan kin gama law school zan turashi yaga Babanku asa rana ko ayi biki kinakan NYSC ko bayan NYSC so ki saki jiki dashi yarone mai tarbiya i choosed him for you jiya nina kirashi kotu dan yazo ya ganki dudda ya sanki tun kina little gurl, sister shi kawar yayanki Aya ne u remember right?" Gyadama Mom kai tayi jikinta har sannan rawa yake Mom tace "shima I told him banso yayi distracting naki da soyayya focus on your goals am I clear" ahankali tace "yes Mom" Mom tace "all the files dana baki gobe zaki bani summary kowani case I don't bloody care how u will do it, get out of my bayi" dasauri ta dauki riganta tadan juyama Mom baya tana maida riganta Mom na kallonta kusan Asmeey tafi yayyinta duka nono har Ramla datake gani tanada shi, ina zatakai nono haka God she's just turned 21 batason hakan ko kadan, wucewa tayi tafita daga bayin tana tafiya kadan kadan tafice gwanin ban tausayi tana fita Munir na shigowa da sauri tayi gefe zata wuceshi yakama hannunta chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yana kallonta yace "why did u cry? Did Mom beat u again? Are your clothes wet? Ruwa ta watsa miki?" Fizge hannunta tayi da sauri ta kakalo murmushi tace "bayi na wanke ma Mom yes I cried but sabida ta hakura, jeka bama Mom hakuri kaima Munir" Dan Jim Munir yayi yana kallonta tausayin Asmeey yakeji sosai hakan yasa ta turashi ganin yana kokarin magana yawuce side na Mom itama tawuce.
ABINDA MOM KEYI TA KYAUTA?????
COMMENT DANAKE GANI TAKO'INA YASA NA KARA MUKU💃💃💃💃💃 💫UWA KO UKUBA💫
✍🏻M SHAKUR
LOOKING FOR INDA ZAKU SAMI TURBAN, HEAD BAND, HAIR BEAD, AND BABY CLOTHES AND BACK TO SCHOOL ITEMS FROM GA MOMMY JUNIOR COLLECTION 💃
https://chat.whatsapp.com/DKwIcG6u9OL1LolCjvOmJC
EPISODE 8️⃣
KANO