Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 8
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 8: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 8. Two days to salla Yau tun safe shirye shirye ake agidan, Abba is…
2,607 words
Two days to salla Yau tun safe shirye shirye ake agidan, Abba is a very cultured and family man baya wasa da zuwa garinsu babban salla, a kauye suka taso bayan mahaifinsu yayi kudi yadawo dasu cikin birnin Bauchi, so duk salla anan Bauchi sukeyi, rannan salla na biyu kuma sai suje kauye ziyara. Mamie is very busy da shirye shirye, Gwaggo da sai yau ta zauna agida dan tunda aka mata takwara agidan mai jego take zama rainon takwaranta, itama nata aikin take uban kayan da Gwaggo tahada na tafiya zaka dauka bazata kara dawowa gidan ba, a manya manyan gana masgon tahada komi, Abdallah kawai ake jira yadawo da motoci daga service a jejjera komi gobe da safe zasu shiga hanya. Gently yashiga saukowa daga staircase yana sanye dawani wando black sai maroon t-shirt daya zauna ajikinsa da kyau, yasaka pcap black akai sai black shade a idanunshi ya goya black bag pack abaya, he looks damn handsome and huge, babu kowa a falon sai kamshin turaren wuta dake tashi, muryan Mamie dayaji a kitchen yasa yatafi wajen baitaba fita bai sanar da mamanshi zai fita ba, a gefen kitchen din ya tsaya cus baimaso yaga matan dake tayata aiki, murya kasa kasa yace "Mamie!" Dasauri Mami tajuyo jin muryan Hamad, ganin bata ganshi ba yasa takalli matan Ya Mustapa dake wajen tace "ina zuwa Ummi" tafito daga kitchen din ganinshi tsaye a gefe ya shirya tsaf kanshi na kasa yayi kyau sosai yasa tadan tako dab dashi tace "ina zaka Hamadi"? Murya chan kasa yanda dagashi sai Mamin shi zasu iyajin meyake fadi yace "zanje na sama wani cafe software ne dasuka sa nai musu rannan salla zasu bude cafe"murmushi Mamie tayi sosai tace "Masha Allah, Alhamdulillah Allah bada sa'a, Allah yacigaba da kawo maka aiki haka, kayi gudu ahankali kasan titi acike yake sabida salla saika dawo" gyadamata kai yayi yajuya yafice Mamie tabishi da kallo harya fice sannan takoma kitchen. Compound dinsu yafito ya goge machine dinsa yahau kai yatada aka budemai gate yafice, cafe da dan nisa but haka yaje, he install it for them ya nunama Ogansu yanda ake amfani dashi sukai test running akai order from site din sannan Ogan yamai godiya yabiyashi payment nashi 250k ya karba yafito lokacin around 12:50, awani masallaci ya tsaya yayi salla sannan yafito yahau machine nashi wani babban plaza yaje yayi parking sannan yashiga cikin mall na wajen he wants to buy something for Mamie, Abba da Ya Mustapa tunda yau yasami kudi, wajen agogon maza yaje wasu agoguna yazabo masu kyau guda biyu 50k each na Micserah, sai yaje bangaren mata ya tsaya turus yarasa mezai sayama Mamin shi, baitaba sayan wani abu na mata ba, idanunshi ne suka sauka kan set na wani sarka da dan kunne da warwaro is 35k dauka yayi sai ga wani red veil babban gaske hakanan Gwaggo kawai tafado ranshi baitaba really siyama family shi wani abu ba cus baya aiki saidai su subashi kudi, kawai dauka yayi yaga 15k gyalen, yabiya kudinsu 150k, yasa kowanne aka packing daban yafito yasa komi ajakan bayanshi yahau machine nashi sai yawuce shagon dayake sayan turare ya saima kanshi da Hameed sai Ya Abdullahi da Ya Faisal saida yakashe 80k ashagon yarage saura 20k kacal a kudin sannan yahau machine yabiya filling station yasai fuel na 5k a machine sannan yawuce hospital din Ya Mustapa yayi parking yaciro wayanshi yayi dialing number sa wayan na gab da katsewa ya daga yace "Hamadi!" Anatse cikeda girmamawa yace "ina waje Yaya" yana maganan ya katse wayan Mustapa yasan Hamad bazai taba shigowa ba he's even use to it dudda baicemai yazo ba cus bazai taba iya cewa Yaya kazo ba but he knows yana jiransa awaje ne, akwai that respect in Hamad sosai fitowa yayi ya sameshi yana tsaye awajen goye da jaka gawani paper bag a hannunsa na micserah watches yakaraso wajen yace "hope everything is fine with you Hamadi"? Gyadamai kai yayi yadan sauke kansa kasa tareda daga hannu yabashi paper bag din Mustapa yadan kalleshi sannan yasa hannu ya amsa hakan yasa dasauri Hamad yajuya zaihau machine dinsa karaf Ya Mustapa yarikesa yace "ina zaka? Tsaya wat is this? Nawaye?" Kanshi akasa yace "is urs" dasauri Ya Mustapha yaciro akwatin agogon yabude da sauri yace "for me? You got this for me Hamadi?" Daidai agogon ya bayyana is a minimalist agogo brown mai kyau, shiru yayi yana kallon agogon saikuma yakalli Hamadi da kanshi ke kasa yace "an ina kasami kudi Hamadi?" Very low calm voice yace "I design website for one cafe they paid me" dadan fada Ya Mustapha yace "shine bazaka ijiye kudinka katara ba, why are you wasting money? Nacema I need agogo ne?" Har lokacin kan Hamad akasa baice komiba, Ya Mustapa yayi shiru yana kallon agogon he's feeling very emotional cus duka kannensa saidai shi yamusu abu, He's the first one so kwata kwata baitaba tasowa dawani expectation na kannensa sumai abuba, bawai basason juna ba no they're united kawai dai wai wani cikinsu yasayo specific gift yabashi wlh basu tababa sai yau da Hamad yamai so abun ya mugun tabashi he was even speechless saiya kalli agogon saiya kalli Hamad da kanshi ke kasa, gently Hamad yaji Ya Mustapa ya rungume shi cikeda so yace "thank you Hamadi" wani irin kunya ne yakama Hamad kaman zai nutse awajen yadan shiga komawa baya alamun ya sakeshi abinma sai yabama Ya Mustapha dariya, yasakeshi yakai hannu yadanja kunnenshi yace "even a hug from you big brother kunya ko" kanshi na kasa har lokacin bai magana ba, Ya Mustapa yace "thank you Hamadi, nagode" juyawa yayi da sauri yahau machine ya kunna yabar wajen Ya Mustapa yabishi da kallo harya fita daga gate na hospital na su, yasake kallon agogonshi yayi shiru sannan ya maida ya rufe yasa a jakan yawuce ya koma cikin hospital din. Wuraren 2 yakai gida a falo yaga Gwaggo tanacin alalen gwangwani da akayi da sunkai guda 6 da manja ga kaji a gefe ga ruwa ga maltina na gwangwani tana ganinshi ta washe baki tace "oyoyooo Hamadi na yadawo, yaka zokaci abinci" ga mamakinta saitaga yataho, yaune rana na farko datake kiranshi yazo Hamadi yazo, ta shiga mikewa da sauri tana wani Irin murna tace "bara na daukoma cokali" tayi hanyar kitchen zama yayi yaciro gyalenta ya ijiye mata yamike, daidai Gwaggo na dawowa taga bashi awajen but ga gyalen awajen data tashi da sauri ta ijiye cokalin tadauki ledan gyalen tashiga warwarewa tace "menake gani haka? Hameeda zo zo zo taho yau danki yayi abun arziki Hameeda" Gwaggo ta shiga warware gyalen Mami na fitowa daga bangaren Abba tazo Gwaggo tace "kinga Hamadi ya sayamin mayafin salla ni Madina oh dama yaron nan nada kirki da hankali haka dubi mayafin nawa fa" sosai Mamie taji dadi tace "Masha Allah akashe lafiya Gwaggo" Gwaggo tace "ni nasan Hamadi yayi kudi na more ba sauran gantalallun da matansu kadai suke kashema kudiba, jibi abinda yaron da baya aiki ya siyamin na salla banda ke dakika bani atampan codivowel, shikuma Abubakar yamin leshi da atampa gwara gwara likita yamin takalmi amman sauran ko hoda basu sayamin ba, kiga wannan gyale kaman wata Amarya da Hamadi ya sayamin ohh Allah, Allah ka karama yaron nan lafiya ka kuma bashi aiki sabida zamu huta, ahhh zamu huta Madina" Mamie murmushi tayi tace "cinye abincin ki toh Gwaggo" dasauri Gwaggo tace "hakane ungo linkemin ki maidamin ita cikin leda zanje namai godiya kinga ya sayamin mayafin amman kunya ya dingaji harya gudu banmai godiyaba" linkemata Mamie tayi tawuce sama abinta takoma bangaren Abba tana hadamai kayansa tsaf ta gama tafito dakinta ta shiga saitaga yar leda kan gadonta dasauri tawuce ta dauka tabude taga sarka mai kyau da dan kunne da warwaro harda zobe, shiru Mamie tayi saikuma tafito kai tsaye tawuce dakinsu tabude kofa yana zaune akan gadonshi yabude system dinshi ya daura kan cinya yana dandannawa jin anbude kofa yasa yadago kanshi ganin Mamie ce ta maida kofan ta rufe tace "who asked you to spend money like this eh Hamadi?" Sauke kanshi kasa yayi, Mamie tace "I've seen yanda kai aiki for days on this project yauda kagama shine zakaje ka kashe kudinka kaida yakamata akara maka ma kudin so that you will establish something shine kake kashemana eh" kanshi na kasa har lokacin baice komiba, shiru Mamie tayi tana kallon sarkan saikuma ta tako ahankali tazo wajen gadon ta zauna gefenshi tasake kallon sarkan ta kalleshi sai kawai taji hawaye sun zubo mata da sauri takai hannayenta tadaura saman fuskanta ta share, jikin Hamad yayi sanyi sosai ijiye laptop dinshi yayi a gefe yadan juyo yakalli Mamie dake share hawaye har lokacin fuskanta na nuna wrinkles kawai yau saiyaga Mamie shi tafara tsufa sai zuciyanshi yasake yin wani iri, murya chan kasa mai taushi da sanyi da nuna so yace "You've done alot for me Mamie" yadan sakeyin shiru kanshi akasa ahankali yace "I am always troubling you da rashin lafiya" ahankali yace "you're always constantly worried sabida ni" cikin kuka Mamie tace "shine aka cema ka you have to buy something for me? You have to repay me? I'm your mother Hamad I don't need gift sabida kullum ina cikin dawainiya dakai, you're my son Hamadi, it's my duty to take care of duka yarana" dan juyowa yayi yakalleta saikuma gently yakai hannunshi yadaura saman fuskanta ya share mata hawaye yace "don't cry Mamie" hannunshi tarike tana kallonshi tace "promise me bazaka dinga kashe kudin daka samu a aiki hakaba save your money kaji, kai kadai ne baka da aiki, babanku karfin hali ne kawai baida jari yanzu, yayyinka nada iyali duk ta yanda zasukai ga kula dakai wata rana zasu gasa barinma idan yara suka fara tasawa, dama inada niyyan bayan salla zan saida gwal dina na baka saika bude cafe tunda ka iya abubuwa da computer" ahankali yace "Mamie don't sell your gold, just pray for me I can take care of myself and you kinji" gyadamai kai yayi sai kawai sai kawai ta rungumeshi yayi lamoo ajikinta, inhar babu kowa he accept hug din Mamie but da wani zai shigo dakin yanzu zai saki Mamie, sun dade ahaka sannan tadago shi ta kalli sarkan tana goge fuskanta tana murmushi sosai tace "nagode Allah yamaka albarka, Allah yabaka abinda kake nema, Allah yabaka nasara a ayyukanka Hamadi, thank You Hussaini, Allah yamaka albarka" murya chan kasa yace "Ameen" sabida baiso Mami tasani daga baya tamai fada yasa yace "I got wristwatch for Abba and turare for my brothers Mamie" sarai tasan yana fada mata ne sabida kartazo taji daga baya tamai fada, dan shiru tayi chan tace "nawa aka biyaka for aikin dakayi?" Ahankali yace "250k" "nawa yarage yanzu?" Dan shiru yayi chan yace "20k" saikuma dasauri yace "inada wasu kudi a account" shiru Mami tayi tana kallonshi chan ta shafa bayanshi tace "it's okay but next time kada ka kara kashe kudin aikin ka haka duk sun fika kudi sunada tsayayyan aikin yi mai albashi kaji" gyadamata kai yayi, daidai an bude kofan dasauri yafita daga jikinta dudda haka saida Hameed yagani yawani zaro idanu yace "Mamie dama yaron nan na hugging naki ko gizo idanuna kemin" dawani kalan sauri Hamad yatashi zai wuce bayi Hameed yashigo da gudu yarikeshi yace "so you can hug Mami Hamad amman ni baka taba bari nai hugging naka to wlh sainayi yau" yataho zaiyi hugging nashi da sauri Hamad ya fizge kanshi yace "Mamie" Mamie dake dan dariya tace "mehaka Hameed ka kyaleshi please" dariya Hameed yayi yataho wajen Mamie tamikamai sarkan tace "kalli abinda ya siyamin yasami kudi duka ya kashemana" murmushi sosai Hameed yayi yace "kafito daga bayi ina nawa?" Yakalli Mami yace "ga Gwaggo chan takasa hayowa sama tana jiranku itama ta nunamin gyalenta" Mamie tace "bari naje kuhada kayanku ku kuka rage" yace "toh Mamie" tawuce. Fitowa Hamad yayi kana gani kasan wanka yayi but he's still wearing kayan daya saka dazu sabida damuwan Hameed bai bari yadauki wani kaya ba ko kallon Hameed baiyiba yazo wardrobe yadauki jogger da t-shirt yawuce yakoma bayi ya shirya tsaf yafito yajefa kayan daya cire a laundry basket sannan yazo Hameed yace "ina nawa Hamadi" jakan shi yabude yaciro nashi ya bashi yaciro na sauran yayi shi ya ijiye a gefe Hameed was so happy with the perfume sai murmushi yake yace "tashi toh muhada kayanmu" kwanciya kan gado yayi yace "I'm tired" hararanshi Hameed yayi yasauko da box nasu yahada musu kayan tsaf yasama Hamadi kayan zama gida da jallabiya guda biyu da turarukanshi duka ciki da takalman daya saya musu na salla da hula da agogo tsaf da sabulan wanka, yadebi few novels na Hamad ya samai, ka'ida ne duk babban salla a Bauchi sukeyi 7days kuma sukeyi a Bauchi kafin su dawo, gama hadawa yayi yawuce shima yaje yayi wanka. Around 9 yashigo gidan daga mosque Abba yagani zaune kan carpet ga kwalin agogon daya siyamai ga Gwaggo gefensa akasa ta kishinguda da gyalenta amman bacci ya kwasheta tsaresa da idanu Abba yayi ahankali yace "sannu da dawowa Abba" murmushi Abba yamai yace "zonan Hamad" karasawa wajen Abba yayi ya zauna ahankali, Abba ya kalli agogon saiya kalleshi yace "naga abinda ka siyama kowa harda ni Allah yayi albarka, kaima Allah yasa naka yaran su maka abinda yafi haka sannan Allah ya sanyama hanyar nemanka albarka, Allah yakawo tsayayyen aiki" gyadama Abba kai yayi murya chan kasa yace "Ameen Abba" yatashi yawuce sama Abba yasake binshi da kallo sannan yakalli agogon kafin yakalli Gwaggo dake munshari.
Around 7AM Ya Mustapa yazo gidan da matarsa da yaransa biyu Areef and Arfat, shima Ya Abdallah yazo gidan da matarsa da yarsu Amra tasha lalle ta tafi wajen Mamie da gudu tana nunama Mamie lallinta saiga Ya Faisal shima da matarsa ita har yanzu bata haihuba duk suna falo an gama loda kaya tsaf, Hameed ya sauko yana sanye dawani ash color yadi mai kyau Abba dake wasa da jikokinsa yace "Ina Hamadi? Shikadai ake jira" "gashinan zuwa Abba shiryawa yake" gyadamai kai yayi, Hameed yazo ya zauna abinshi bai gaida kowa ba, kusan 10minutes saiga Hamad yana saukowa yana sanye da ash color yadi exactly irin na Hameed sai kamshi yake, yadin yamai bala'in kyau bambamcinsa da Hameed is just eyes, idanun kwalli garesa and it's so obvious kansa akasa anatse yake tafiya daidai cikeda kamala da natsuwa kuma, ya shigo cikin falon calmly yazo gaban Ya Mustapa da matarsa ke zaune kusa dashi kanshi akasa yace "ina kwana Anty" murmushi tayi sosai tace "Alhamdulillah Ya Hamadi ya karfin jikin an warware ko" gyadamata kai yayi yatako zuwa gaban ya Abdallah kanshi akasa anutse yace "ina kwana Anty" cikeda so tace "lafiya lau Ya Hamad ya jiki" bai amsaba yadai gyada kai takawa yayi zuwa wajen Ya Faisal yace "ina kwana Anty" kanta tasauke akasa cus Hamadi ya girmeta she's just 25 amman baida girman kai tace "ina kwana Ya Hamadi" kasa amsawa yayi yawuce gently kusada Mamie duka yayyinshi na binshi da kallo ya zauna, Gwaggo tashigo taci gayu wani bubu da zani da mayafi tasaka na hadari lace tace "mutafi yaufa jajubari akwai go slow" tashi Abba yayi kowa yatashi aka fito Mamie takashe wutan kowani daki ta tofa addu'a duka kulle gidan aka shishiga mota Abba yaje yana sallama da mai gadi yabashi makullin gida da kudade da motoci hudu sukai tafiyan motan Abba sai motan Ya Mustapa Ya Abdallahi Ya Faisal, motan Abba Hamad ya shiga gaba kusada dreban Abba, Abba da Mami suka shiga baya, shikuma Hameed ya shiga motan ya Faisal, Gwaggo tashiga motan Ya Mustapa suka wuce. ** Bauchi