Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 10
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 10: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 10. Wuraren 11:30 Asmeey tafarajin munsharin Gwaggo sosai ahankali…
3,691 words
Wuraren 11:30 Asmeey tafarajin munsharin Gwaggo sosai ahankali ta lallaba ta sauka daga gadon batare datai making sound ba tana rike da veil nata a hannu tazo wajen kofa kaman barauniya tabude kofan ahankali tafito tana maida kofan tarufe tajuya da sauri tana tafiya ahankali ahankali sadaf sadaf tana warware gyalen tana kokarin yafawa danta rufe gashinta tai wajen kofa daidai takai kofa tasa hannu zata bude kofan taji saukan zazzakan murya that is so calming and soothing a kunnuwanta. "Where do you think you're going"? Amahaukacin firgice tajuyo karaf suka hada idanu da Ya Hamadi dake zaune a dinning ga laptop gabanshi da bottle water a gefe ya tsareta da crazy eyes nashi kawai saitaji ta dimauce jikinta yayi wani iri, she couldn't stand his gaze at all tama kasa magana gabanta sai faduwa yake sai kawai tajuyo ta wuce hakanan saita sake samun kanta da so ta kalleshi dago idanunta tayi kaman mara gaskiya ta kallonshi hada idanu sukayi mugun faduwa gabanta yayi tabude kofan dakin Gwaggo da sauri ta shiga daidai Ya Mustapa na shigowa da ledan magani a hannunshi dinning ya wuce ya zauna yana kwalama Asmeey kira. "Asma'u Asma'u" daga ciki Asmeey tace "na'am" fitowa tayi ganin Ya Mustapa a dinning a yasa taje wajen ta tsaya gefensa batare data yarda ta kalli inda Ya Hamadi yake ba, magunguna guda biyu yaciro yace "2 2 zakisha, duba fridge idan akwai ice kisa a kumatunki karya kumbura idan babu kisa ruwa a leda yayi kankara zuwa anjima" gyadamai kai tayi tawuce kitchen shikuma yatashi yakalli Hamad dake aiki yace "good night" gyadamai kai yayi Asmeey tafito da bottle water ganin babu Ya Mustapa duk sai taji wani iri magungunan tadauka daga dinning tawuce dakin Gwaggo da sauri.
WAYYO ASMEEY💔💔 AFADI GASKIYA MAMIE HAMADI YA SIYAMA ICE CREAM KO ASMEEY?? 💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
M SHAKUR TA IYA LITTAFI🤩🤩 THANK YOU ALL FOR READING🤩 GAYAMIN ME KIKEFI SO GAME DA THIS BOOK +2347012181461
EPISODE 1️⃣1️⃣
Tana shiga cikin dakin Gwaggo ta maida kofa tarufe ta jingina da kofan hannayenta biyun dake rike da bottle water da magani duka ta daura kan kirjinta dake bugawa nonstop, why is her heart racing sabida Ya Hamad? Saikace yauta fara ganinshi toh kodan bai taba mata magana bane? Anytime sukazo salla ma hardly take ganinshi dan baya shiga mutane, wani zubin daga ranan dazasu zo sai rannan salla take kara ganinshi, takai almost 2min tsaya awajen sannan tawuce ta zauna bakin gadon tabude maganin tabude ruwa tasha, at first batason magani but dukan Mom yasa ta koyama kanta shan magani da kanta, cus drawer su na daki Baba na ijiye musu basic magunguna haka irinsu paracetamol, Ibuprofen maganin ciwon mara da first aid kit she learn to take care of kanta, kallon gadon tayi yanda Gwaggo ke maka uban minshari abinta ta rakube ta kwanta gefe dudda ga uban space tai shiru gabanta sai faduwa yake she wanted to go back to side nasu hakan zaisa laifinta yaragu gashi an hanata fita anan and she knows, Mom tasan ba'a side nasu ta kwana ba, hannunta takai saman kumatunta da taji yana mata zugi takai hannunta saman cikin nata shima dake mata zugi saitai shiruuu hawaye ya gangaro mata bata taba iya bringing kanta to ask her self maisa Mom is always beating her? Mom bata tausaya mata, Mom hit her kaman she's not her Mom, tana son Mom but Mom bata sonta, dazu data rungume Mamie she wished Mom ta rungume haka, hawaye ta kara sharewa ahaka tagama tunane tunanen ta bacci yayi awon gaba da ita. Around 1:00 yagama abinda yake dan har Abba saida yashigo still bai gamaba kashe system dinshi yayi yadan kalli kofan dakin Gwaggo saikuma ya mike tsaye ahankali yawuce kitchen freezer yabude yadauki ruwan data saka dayaga yayi kankara yadauka yadauki bowl yasa, yasa wasu ruwan a freezer incase zatai amfani dashi gobe, yafito daga kitchen din yana tafiya ahankali yawuce gaban dakin ya tsaya yayi dan jimmm, hannu yadaga yadaura kan kofan yayi knocking kadan he could hear minsharin Gwaggo daga wajen, sake knocking yayi ahankali but still shiru yasake yin jimmm, ataushashe cikin yar kankanuwan murya dake ratsa mind yace "Asma'u!" Firgigit Asmeey tafarka tabude idanunta dan har cikin zuciyanta taji yanda aka kirata, da muryan bacci dake a hargitse tace "uhnn na'am" dan jimmm Hamad yayi, kusan 10seconds sannan calmly dan yasan bacci take karya firgitata yace "open the door" tashi tayi daga gadon dasauri ta sauko batare datama san dankwalinta baya kanta ba bata da kayan bacci anan so gown din atampan ne ke jikinta ta taho wajen kofan kai tsaye tasa hannu daya tabude kofan while dayan hannunta nakan idanunta tana murzawa sabida bacci, sauke gentle eyes dinshi Hamad yayi kan fuskanta she's not even looking at him sosa idanu take sabida bacci, idanunshi yadaura kan lafiyayen hadadden kitson da aka mata dayayi kyau sosai da sauri yasauke kanshi ya maida kan fuskanta for the second time ahankali yace "Asma'u!" Dasauri ta dago kanta takalleshi tana janye hannunta daga kan idanunta da suka kada sabida bacci ga kumatunta daya kara ja inda aka mareta gabanta na faduwa sabida yanda yakira sunanta, tsareta da idanu yayi na kusan 10secs dukansu babu wanda yayi magana this time around shine yafara janye idanunshi daga kanta yamika mata bowl da ruwan ice ke ciki yace "put this a fuskanki" bowl din itama ta kalla saita gyadamai kai ahankali tasa hannuwanta kan bowl din zata amsa sai bai saki ba hakan yasa tadago kanta ta kalleshi ganin bai sakin mata ba, hada idanu sukayi yanda taga yana kallonta yasa ta sauke kanta kasa da sauri har lokacin hannuwanta nakan bowl din tana jira ya sakin mata, cikin yar kankanuwan murya da ita kadai zata iyajin maganan sa Hamad yace "next time if anyone tries to slap you use your hands or elbow ki kare fuskanki," dan dago kanta tayi tadan kalleshi har tsakiyan zuciyanta takejin muryanshi dakeda bala'in dadi, ga kamshin dayake yi daya cika wajen, bawai fuskanshi ko expression nashi shows he care bane but his words are so deep a heart nata that translates as he cares, baiso yaga kumatunta sunyi jan mari, sauke kanta kasa tayi sannan ta gyadamai kai ahankali tace "tom, thank you 4 d ice cream Ya Hamad" sakin mata bowl din yayi ta hanyar jaye hannayenshi daga kai yajuya da sauri kaman wanda yaji kunya murya ciki ciki yace "Mamie na siyama not you" yawuce dinning da sauri hakanan saita kasa komawa ciki ta tsaya awajen kaman an kafata he looks so cute, godiyan datamai ne yabasa kunya? His shyness is charming, laptop dinshi ya dauka daya kashe da ragowan ruwan bottle water daya rage yajuyo hada ido sukayi da sauri tajaye nata idanun gabanta na faduwa takoma cikin dakin da sauri ta maida kofan tarufe, dauke kai yayi yawuce yakashe wutan parlour kafin yayi stairs yashiga dakinsu Hameed yayi nisa a bacci, ijiye komi yayi yafada bayi yafito daure da alwala, dadduma ya shimfida yayi nafila sannan yatashi yazo yahau gadon ya kwanta ahankali.
Tana maida kofan tasake jingina da kofan tayi shiru duk wani motsinshi a parlour tanaji harya gama kashe wuta sannan tajuyo yarufe kofa dan bakajin walking step nashi what is wrong with her? Tayi maganan ahankali, wucewa tayi gaban gadon ta zauna tadauki kankaran ta daura saman kumatunta but saitaji sanyi da sauri tacire ta ijiye a bowl din tana kallo, sake dauka tayi takai kumatun kusan 3secs ta ijiye takasa jure sanyin sai kawai ta ijiye bowl din ta kwanta sai tunanin Ya Hamad take da yanda yakirata Asma'u da maganan daya mata muryanshi is so soothing she can't even explain and so calm gawani irin natsuwa da kwarjini da haiba da tunda take bata taba ganin namiji mai kalansa ba ga idanu kuma kwallin dayake sawa namai bala'in kyau ahaka bacci yayi awon gaba da ita.
Wajajen 4:30 na asuba Gwaggo ta farka tana kunna wuta takalli Asmeey data dukunkune tace "ke ga jin sanyi amman kin kasa tashi ki dauki abin lulluba" sauka tayi daga gadon ta wuce drawer taciro bargo tazo tabude ta lulluba mata sannan tawuce bayi tace "bari na barta tadan kara bacci nasan taci bakar wuya a hannun muguwar uwarta" salla Gwaggo tafito tayi tanakan dadduma tana kallon Asmeey data kudundune a bargo harkai saijan charbinta take around 6 tafada bayi tayo wanka tazauna ta cicciro abubuwan shafe shafen ta tafara shafawa masu wired kamshi abinda yatada Asmeey kenan tabude idanunta tana yaye bargon ta tashi zaune ahankali tace "Gwaggo meke wari" kallonta Gwaggo tayi zata zageta sabida yanda take kiran manta na wari tabuga salati. "Oh Innalillahi wa innailaihi raji'una billahillazi idan uwarki bata rokeki gafara ba sai Allah ya soyata a jahannama, kalli suntumemen kumatu kaman an zuba yeast" dasauri looking confuse Asmeey ke kallon Gwaggo dake surutu but ganin yanda take kallon fuskanta yasa gently takai hannunta saman kuncinta da Mom ta mara saitaji ya kumbura takai dayan hannun ta shafa na bangaren dama is normal hannunwanta kansu sai sukayi kaman ta daura daya a tudu daya a flat surface sai kawai ta tashi da sauri tawuce bayin Gwaggo tana bude kofa ta tsaya turus tana kallon madubi yanda kumatunta na haggu ya kumbura kaman tana ciwon hangum ko ciwon hakori harda wajen lips da jaws nata saitai looking kaman ba'ita ba tai wani irin muni a idanunta wani irin sosa mata rai abin yayi batasan sanda ta duka tafashe da kuka sosai ba like she's feeling super hurt, takai kusan 30min abayi Gwaggo tace "wai harna gama shiryawa tsaf nasaka kayan salla bazaki fito kiyi salla ba" da kyar ta tashi idanunta sunyi jazur tafito kanta akasa tasaka hijabi tai salla tana idarwa ko azkar batayi ba ta mike yafada gado taja bargo har saman kanta Gwaggo tace "yau naga ikon Allah tashi kije kiyi wanka yanzu zanje chan dakinku na karbo kayan sallanki mutafi masallaci" taushe bakinta tayi bataso Gwaggo tasan tana kuka ta danne tace "bazanje ba" tsuki Gwaggo taja tamike tace "nadawo dakin nan bakiyi wanka ba sai an jimu agidan nan" tawuce tafita. Wajajen 7:15 Gwaggo tadawo da leda a hannunta wanda Ramla tahada mata komi da zata saka dan ka'ida rannan salla kowa kayan da Abban Kano ya dinkama kowa yake sawa ganinta har lokacin akan gado gashi masallacin dasuke zuwa 8:00 ne salla yasa Gwaggo tace "au baki tashi ba bari kigani" kayan ta ijiye tafito falo tana rapkama Abba kira. "Abubakar Abubakar, Madina kai Abubakar" koda Abba yabude yashiga saukowa Mami biyeda shi ya shirya tsaf cikin manyan kaya da malunmalin ga agogon da Hamadi ya siyamai wrist nashi Mamie ma tasaka lace mai kyau ta saka sarkan da Hamadi ya siyomata shima Hameed yashiga saukowa yayi bala'in kyau cikin shaddan sa sky blue da akamai jumper da aiki mai kyau. Abba yace "Gwaggo lafiya" rai abace tace "kaga nida Asama ne takemin bori uwa nice na kumbura mata fuskan, wanka takiyi wai bazata masallaci ba sabida uwarta ta nakasa mata barin fuska" wani kallon takaici Abba yama Gwaggo sai kawai yawuce dakin Mamie tabisa Gwaggo tabi Hameed dake kamshi tace "kawa Allah sammin turaren nan daka fesa dake kamshi ja'iran chancewa tayi wai wari turarena yake" Hameed yace "dama bakisan tsami turarenki yake ba Gwaggo" haderai waggo tayi tace "nidai zaka tsammin ko bazaka tsammin ba"? Daidai Hamad yafito cikin exactly kalan kayan Hameed da sunmai bala'in kyau yana saukowa daga stairs Hameed yace "turarensa ne ki tambayesa" tsayawa Gwaggo tayi tana kallonsa yanda yake tafiya a natse tace "Oh Allah ka nunamin auren Hassan da Hussaini, kai Allah yama Hamadi natsuwa inama haka Hameedu keda natsuwa" rai abace Hameed yace "me kikace"? "Uban ka nace" ta amsashi tana murmushi tana kallon Hamad daya hada fuska.
Abba ne yafara shiga dakin da sallama yace "Husna" dawani irin sauri Asmeey ta tashi dan gidan nan kap bataga wanda baya girmama Abba ba shine babba har Baba respecting Abba yake sosai kuma ya manyanta yaye bargon tayi ta tashi ta zauna tace "na'am Abba ina kwana" daga Abba har Mamie kumatunta sukabi daya kumbura gashi tai kuka sai idanunta suma suka tashi karasowa wajen gadon Abba yayi yace "subhanallahi Doctor bai baki magani bane?" Ahankali tace "yabani nasha amman yace nasa kankara jiya nafara sawa sai nayi bacci bansa da kyau ba" tana maganan sai hawaye suka sake fadomata ta share da sauri ta sauke kanta kasa asanyaye Abba yace "ya isa tashi kiyi wanka muje masallaci Doctor sai kara dubaki" gyadama Abba kai tayi ta tashi ahankali tawuce bayi Abba yawuce yafita duk zuciyanshi ba dadi Mamie ma haka suka fito duk an shigo su Ya Mustapa kowa yaci gayu Abba ya kalli agogon hannunsa yace "inaga masallacin 8:30 zamuje ko na 9 Doctor ahmm please kaduba yarinyar nan kumatunta ya kumbura" dasauri Ya Mustapa yace "batasa ice bane" Mamie tace "tafara wai sai tai bacci" Abba yabi duka yaran nashi da kallo sunyi kyau sosai kallo saya Hamad yama Mamie yaga sarkan saya sayamata Abba yasa agogon Ya Mustapa ma yasaka agogon daya sayama hakan yamai dadi sosai.
Bata wani jimaba tafito ta zazzage ledan harda cream Ramla tasa mata sharp sharp tasa kayan atampan da Abba yamusu mai kyau gold atampa mai blue ne embellish an mata riga da skirt da suka zauna ajikinta sosai, bata daura dankwali ba hijab kawai ta saka ta fesa turare tasake kallon madubi she feels pathetic she feels down she's feeling like the most ugliest girl in the world zuciyanta yayi baki kirin ba dadi ta daga hannuwanta takalli lallinta da duk sun gwalje nothing is right about her banda kitso da dinki she's having a very very dark salla sai kawai taji tana kunyan ama ganta gashi batada nose mask anan adakinsu akwai daga waje taji Mamie ta kirata. "Ma'u kingama" ahankali muryanta na cracking tace "eh" takalmin sallanta wanda yake hill gold mai kyau sosai very expensive shoe tasaka sannan taja wuyan hijabinta gaba sosai sannan takama hijab din tagaba tarufe kumatun tazo wajen kofa kanta akasa tafito ahankali kowa na falon har Abba kallonta suke banda Hamad dayayi kaman baimasan wani abu na faruwa ba Abba da baison wani yayi maganan fuskan yasata kuka yace "toh kumutashi muje muje muje Husna" Hamad yafara tashi kai tsaye yawuce kofa abinsa yabude yafice, Gwaggo takoma daki taciro gyalenta ja ta yafa wanda Hamad ya siyamata tace "billahillazi banga wanda yakaini kyau agidan nan ba yau" fitowa sukayi sukai wajen motocin gidan da an wanke gasu Nana da Ramla duk an fito suma sanye da irin kayan dake jikin Asmeey, Ramla sai kallon, ahankali ta tsaya gefe daya wajejen taki zuwa wajen su Ramla Munir daya fito daga flat dinsu yana sanye da shadda hadade tasha guga idanunshi akan sister shi yafara sauka yanda yaganta ita kadai tajawo hijabi gaba da sauri wajenta yafara zuwa ya tsaya yadan leka fuskanta yace "mehaka Ya Asmeey kin rufe fus….." kasa karasa maganan yayi lura da kumburin fuskanta sai yayi shiru yana kallonta ahankali yace "na dauko miki nose mask?" Gyadamai kai tayi da sauri yajuya yakoma flat dinsu daidai Mom na fitowa daga flat din tareda Mama dasu Ammi mugun bugawa kirjinta yayi Mom ce kadai bata sanya kayan da Baba yamusu ba wani HKG atampa ta saka ta daura designers after dress akai ta zuba gwalagwalai awuya da hannu tana tafiya kaman she owns the floor rawa hannuwan Asmeey yafara tajuya tana kokarin zata zagaya ta bayan motan Ya Mustapa yace "Asmeey" arude ta juyo yakalli Hamad ya mikamai key sienna motan Baba yace "all the children su shiga this sienna drive them, get in Asmeey" dasauri kafin Mom ta iso wajen tawuce, ta shiga chan last roll na motan Ramla itama tashigo tazo ta zauna kusa da ita sauran kannensu suka shiga motan kowa na shiga motan Mom ta iso ta gaisa da kowa aka amsata banda Baba daya shige mota abinsa Mom tawuce ta shiga motanta Mama ta shiga tareda ita, Mamie ta shiga mota daya da Ammi da Gwaggo Hameed ya jasu Ya Faisal yaja matayensu shikuma Ya Mustapa yaja su Abba Munir yafito yazo ya shiga gaban motan Ya Hamad yashigo ya rufe motan Munir yajuyo yaba Yusra nose mask yace "mikama Ya Asmeey". Black glass Ya Hamad yasaka yaja motan duk akabar gidan, hannu Ramla tasa ta karbi nose mask din tajuyo tamikama Asmeey da ke kallon gefe daya ahankali tace "Asmeey take" juyowa Asmeey tayi batare data kalleta ba tasa hannu zata karbi nose mask din dasauri Ramla tarike hannunta hakan yasa Asmeey ta kalleta da rinannun idanunta sosai Ramla taji she's feeling guilty barinma kumatunta data gani sai taji tai nadama taruwa hawaye yayi a idanunta murya chan kasa tace "I'm sorry Asmeey kiyakuri kinji" shiru Asmeey tayi tana kallonta tana tuna abinda tamata jiya tayi kokarin fizge hannunta Ramla tarike muryan Asmeey na rawa sosai tace "ki sakeni" ta madubin gaban motan Hamad ya kallo bayan, yaran ma duk suka juyo Ramla tace "kice kin hakura tukunna" ranta na tafarfasa tabude baki zatai magana takasa tashiga kokarin fizge hannunta, Munir da iya shiganma yar uwanshi yace "Ya Ramla ki saken mata hannu" ahankali Ramla tace "hakuri nake bata" cikin tsiwa Asmeey tace "bazan hakura ba and baruwana dake kifita harkana you lied kince nace miki wawiya and I never said that, ai yanzu you are happy ko daman kince nasaba shan mari a kumatu kema zaki karamin kumatun is swollen I hope you're satisfied niki sakeni" tafashe da kuka sosai datake rikewa sake kallonta Hamad yayi ta madubin sai kawai ya dauke kanshi ya maida kan titi Ramla ta rungumeta da sauri tana kuka itama tace "Asmeey dan Allah kiyakuri I'm sorry for whatever I said jiyan nan kiyakuri kinji" shiru Asmeey tayi sai chan ta gyadamata kai Ramla tace "tsaya na samiki nose mask din" hannu rasa ta sharemata fuska sannan tasa hannunta a hijabin tasa mata nose mask ahaka sukakai mosque kashe motan Hamad yayi Munir ya sauko yabude musu duk suka shiga fitowa gabanta sai faduwa yake tadan kalli gaban motan ganin Ya Hamad na zaune dauke kanta tayi da sauri tafita daga motan ahankali daidai Mom na zuwa wajen dawani irin sauri tadawo cikin motan hakan yasa Hamad yajuyo hada idanu sukayi dauke kai tayi da sauri sannan tafita daidai su Mom sun wuce tabi baya ya sauko yarufe motan suka wuce sahu tayi gefen su Gwaggo Mom nadaga chan.
Sallame sallan sukayi kaman ance tadan juyo karaf suka hada idanu da Mom wani kallo da Mom tamata ita kadai tasan meaning dinshi cikinta wani kuka yayi dasauri ta sauke kanta kasa tashi Gwaggo tayi tace "kumuje Billahillazi yunwa nakeji dabino na yana mota shi zanci" hannunta Ramla takama tace "muje" ahankali ta mike dasauri tabi Ramla suka wuce Mom tamata wani kallo ganin kallon data mata dazu baisa ta tsorata tace a motanta zata koma gıda ba ko gaisheta ina kwana batayi ba tafarfasa zuciyanta yashiga yi suka wuce itada Mama.
Wajen motarsu sukaje suka jingina suna jiran Ya Hamad da Munir ganin Mom na zuwa wajen wani kalan dukewa tayi ta tsugunna dan kafafunta sun kasa daukanta ko kallonta Mom batayiba tawuce wajen tata motar abinta tashiga ta kunna tana duke ahaka saiga Ya Hamad da Munir suna zuwa ahankali Ramla tace "tashi muje" Tashi tayi Munir yabude musu motan duk suka shiga tunda ta shiga motan tai shiru dudda anata hira but Mom kawai zuciyanta ke kawo mata şundan bata lokaci kafin sukai gida parking akayi saukowa sukayi ahankali tawuce flat dinsu Ya Hamad yadan kalleta yadauke kai mazan suka wuce wajen raguna dan tanka su Mamie kuma suka wuce backyard daidai zata shiga flat dinsu Gwaggo tace "zonan Asama tunda komawa inda ake neman kasheki kikeso kiyi" Dan waigowa tayi ta tsaya Baba dayake tsaye kusa da Gwaggo yace "badake ake magana ba" juyawa tayi tayi hanyar flat dinsu Abba Mom data fito daga mota takalli Baba dayayi kaman bai ganta ba zata wuce flat Gwaggo tace "eh aje acire kaya afito ayi aiki" ko kallonta Mom batayiba. Kananun yaran gidan tea aka shiga basu Ammi tace "Ramla kutashi kuje kuda su Nana ku jera carpet a tsakar gida da kayan abinci anan za'aci" tashi duk sukayi, Asmeey na shiga dakin hijabin ta cire ta zauna ahankali tana zare nose mask daga falo taji Gwaggo tace "kifo Asmeey an saku aiki" tasan aikin already hakan yasa tadauki gyalenta na dakin blue ta yafa akai tadan zazzago dashi tafito slippers data gani so well kept anan side na chair a falon ta zura kafafunta aciki sun mata yawa Ramla dake kallonta tace "jiya da daddare saida nazo na ganki but Ya Twins bansan ko Ya Hamadi ko Hameed bane" da zuciya daya Asmeey tace "maisa kwallin?"Gwaggo dake zaune ta buga salati tace "Hamadi kike cewa maisa kwalli Asmeey ai gashinan yana jinki"? Dawani irin sauri daga Asmeey har Ramla suka juyo daidai yagama saukowa daga stairs gashi bakajin footstep nashi, arude tajuya zata fice gabanta na faduwa calmly yace "my flops" chak Asmeey ta tsaya saita sauke kanta ta kalli kafafunta da sukai dan firit a takalmin, awani irin hankali tajaye kafafunta daga ciki sannan ta sauke kanta sadaf sadaf tafita ahaka Ramla tabita suka shiga warware carpet suna shiryawa a compound din ga pillows sun jefa anyi setting sannan suka tafi backyard su da matan yayansu nafito da abincin da aka dafa daban daban kusan 45mins aikin ya daukesu su Baba kuma an gama gasa musu some part na layyan dasukayi duk akazo aka zauna dan cin abinci Mama tace "bari na kira Maman su Aya". 💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣2️⃣
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈
CHAT ME UP DON SHIGA wa.me/+2347012181461 EPISODE 1️⃣2️⃣