Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 9
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 9: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 9. Flat dinsu ya shiga zuwa dakinsu da babu kowa, ko ina Hameed yayi…
4,441 words
Flat dinsu ya shiga zuwa dakinsu da babu kowa, ko ina Hameed yayi oho?Bayi yafada yayi wanka yafito daure da towel yawuce yasa key a kofan sannan yabude akwatinshi kayanshi yaciro komi yasa a wardrobe Hameed yasamai duk abinda yake bukata ya shirya tsaf sannan yaciro laptop dinshi daga bagpack ya kunna yana zama kan gado saikuma yayi jim kafin yakalli wayanshi dake gefenshi sai kawai yadaga wayan……. Gwaggo na zaune anan falo tana surutu duk wani abinda yafaru a Kano yaran nan take bama labarinshi ko gajiya batayi ba, yaran suma sun zagayeta anajin dadin labari harda na takwaran da aka mata wayanta yahau ringing da sauri ta taba wayar dake cikin lalita akasan zanin tace "yooo wa yake kirana ko su Munarin Kauye ne"? Warware zaninta tashiga yi tasa hannu taciro wayan daga lalita takalli screen din kaman ta iya karatu tace "tohh wannan lamba ce batada suna" ta danna dauka takai wayan kunnenta murya ciki ciki akufule Hamad yace "kuma karki kira sunana! Yarinyar chan batai lalleba" yana maganan ya katse wayan Gwaggo tace "wace yarinyar? Ham…." Saikuma tai shiru da sauri tuna yace karta kira sunansa, tashiga bin yaran da kallo daya bayan daya tana sauke wayan daga kunnenta kawai tazare idanun ta mike tace "duk kutashi kuzo ku nunamin kunshin sallan ku daya bayan daya"faduwa gaban Asmeey yayi dake zaune kusa da Ramla cus tasan Gwaggo taga batai lalle ba she will cause trouble tai maza ta mike zata wuce Gwaggo tace "zonan kafin na cimiki mutunci Asama" tsayawa Asmeey tayi tana boye hannunta abaya, Gwaggo tace "mehaka naga kafafunki farare tasss kaman na zabiya! Jibi yara anan ku takwas gasu Hajar hudu ku shabiyu, maza sunsha aski mata sunsha lalli banda ke sai kace yar riko" har lokacin Asmeey taki nuna hannunta ahankali tace "Gwaggo makaranta zani bayan salla saisa an hana lalli a makarantar" dakuwa Gwaggo tamata ta daga murya tace "kinci mai garinku da makaranta yo ko kirista suna zuwa hutun salla balle ke musulma ke baki gajiya da boko sai kace uwarki iyyee? Kinada tabbacin zakiga sallan badi? Babban salla guda hannayenki da kafafu fari sol kaman aljana ina masu lallen wuce ki kiramin su Amina idan basu tafi ba, ke ko sun tafi sai an kirasu" wucewa Amina tayi da gudu ta tafi, Asmeey gabanta na faduwa dumdumdum tace "Gwaggo dan Allah ni bazanyiba ni ki barni" tai stairs da gudu Gwaggo tace "kiramin ubanku Munir" dan shima Munir na falon, tsayawa Asmeey tayi tajuyo da sauri ta kalli Munir daidai yawuce abinshi da sauri Hamda ta sauko tazo wajen zatai magana Baba ya shigo ga Amina da masu lalle da kitso sun shigo falon suma, Gwaggo na daga murya sosai tace "Muhammadu Sani tun kana dan kankani kataba ganin salla tazo da bansa kunshi ba?" Dasauri Baba yace "a'a Gwaggo" cikin fada Gwaggo tace "toh wani dalili zaisa kaf cikin yaran gidan nan Asama ce mara kunshi sai kace wata bare wannan mukai baki ai sai ace mun tsaneta ne ba yar gidan bace" kallon Asmeey Baba yayi da sauri ta sauke kanta kasa zaiyi magana sukaji muryan Mom cikin harshen turenci tace "you know she's going to Law school bayan salla Alhaji that's why"kafin Baba yayi magana Gwaggo tace "to yar boko ke duk inda kike saikin nuna mutanen dake wajen basusan komiba kene kikasan komi, ke ba abin kunya bane yarki ta fita daban cikin sauran yara? Komi boki komi boko da boko za'a lahira dazaki hana yarinya yin adon salla? Yin ado da salla sunna ce danko Annabi tsira cewa yayi ranan salla musa kaya mafi kyawu muyi ado mai kyau amman ina zakisan haka sai ilimin yahadu kika sani bana arabi" Mom zatai magana strictly Baba yadaga mata hannu hakan yasa tai shiru, cikeda girmamawa Baba yakalli Gwaggo dake huci yace "Gwaggo kiyikuri yanzu za'a mata" cikeda rigima Gwaggo tace "ai gamasu lallin nan na aika Amina taje ta kirasu anan gabana za'a mata kafin yar boko ta zaga tahanata yi kekuma zauna da shegun idanunta masu kama dana jemage" tanuna Asmeey da atsorace tadan dago kanta ta kallo Mom data mata wani mugun kallo, da sauri ta sauke kanta kasa Mom tajuya daga sama zata koma daki Gwaggo tace "saukowa zakiyi kije kema kisa hannu abayan gida ayi aiki ba daraja kikafi sauran dake wajen ba bakina kima kika fisu ba dan sunfimini ke so dubu" wani kallo Mom tama Gwaggo saikuma ta kalli Baba daya mata kallon baison rigima tayi abinda tace yajuya yafita itama Mom din badan taso ba ta sauko tawuce tafita, Gwaggo tabita da harara, ran Munir fess kaman ya rungume Gwaggo dan dadi aka shiga yima Asmeey lallen dake cikin tsananin tashin hankali duktai zuru zuru sauran yan uwanta harda Munir suka zagayeta suna kallon yanda ake lallen Munir harda matsar da kanninsa baya karsu gwaljema yayarsa lalle, kana ganin Asmeey kasan hankalinta baya jikinta Gwaggo ta buga tsaki tace "Allah yahadaku da jarababbiyan uwa ga yara har yara Allah yabata inba haukan bama yarinya haka kaman Asama wani yahanata yin lalle ba abun tai fada dashi bane amman ita ke hanawa da kanta yarinya kyakkyawa haka son kowa kin wanda yarasa" itadai Asmeey ta saukar da kanta kasa. After magrib aka gama lallen gabaki daya both baki da ja, ta kwanta anan kan doguwan kujera dan ba halin salla suna kallon film tareda sauran yaran, Gwaggo kuma ta fita tsakar gida wajen su Baba tana magana dasu ganin an gama lallen, bude kofa akayi aka shigo Ya Mustapa ne da sauri yaran sukai wajenshi suna gaidashi Ramla ya kalla yace "come here Ramla" dasauri Ramla ta taso taje wajen kofa dayake, jakunkunan ice cream din hannunshi yabata yace "gashi ki raba muku" gyadamai kai tayi dukansu sukai godiya yawuce yafita Ramla tashiga rabon ice cream din na supreme manyan robobi tanaba kowa nasa, tazo gaban Asmeey hakan yasa Asmeey tace "kibani strawberry" Ramla tarike last strawberry tace "nawane shi vanilla zan baki" dasauri Asmeey tace "ai kafin ki dauki strawberry nace miki ni shinakeso" Ramla tace "to baza'a bayar ba" kallon Ramla Asmeey tayi cikin ido sai kawai ta dauke kai tace "ki hada duka ki shanye banso" ran Ramla baci yayi jin abinda Asmeey tace, cikeda masifa tace "ohh kullum akaina ne kikeda bakin rashin kunya ko"? Dasauri Nana tace "Ya Ramla kiyakuri" tashi zaune Asmeey tayi daga kwancen ta harari Nana tace "wayace kisa baki? Da ke akayi?" Akufule Ramla tace "wai ba Baba yace kidenamin rashin kunya ba? Dani kike magana kaman kinyi da sa'an ki? You're a rude stubborn girl wawiya kawai" ran Asmeey yabaci jin zagin da Ramla tamata tace "ni dai ba wawiya bace" hannu Ramla tasa ta dungure mata kai saida Asmeey takoma baya tsabagen yanda Ramla ta dunguruta tace "okay nine wawiyan kenan? Ki kara magana kiga wlh sai kinsha mari akan kumatun nan naki daya saba shan mari"dasauri Yusra tai wajen kofa tabude tafice ganin Ya Ramla da Ya Asmeey na chachan baki akan ice cream…. Ganin bataga su Baba ba yasa tai wajen motoci inda taga Ya Mustapa tsaye tareda Ya Hamad tai wajensu tana haki tace "Yaya ga Ya Ramla chan da Ya Asmeey suna fada a falo sabida ice cream" "because of ice cream"? Ya Mustapa ya maimaita, gyadamai kai tayi tana zaro idanun gulma tace "she prefers strawberry itakuma Ramla tace vanilla zata bata tace bataso shine Ya Ramla tashiga dungure mata kai tace mata wawiya wai zata mareta akan kumatunta da suka saba shan mari" Ya Mustapa yace "wuce muje" binta yayi zai wuce daidai nan sai ga Mom data zagayo daga backyard tashiga flat din hakan yasa Ya Mustapa yace "ga Mom chan tafi kawai bari basai naje ba" wucewa yayi yakoma inda Hamad yake tsaye dan shi baiyi motsi ba daman. Mom na shiga dakin tagansu suna chachan baki hade giran sama da kasa tayi yaran kowa yayi tsit kaman anga dodanniya gaban kowa na faduwa harda ita Ramlan ganin Mom, maida kofan Mom tayi tarufe takaraso falon yaran kowa na komawa baya, Ramla ta kalla strictly tace "what is going on here"? Ice cream na hannunta Ramla ta nuna mata tace "Mom Ya Mustapah ne yazo yabani ice cream yace narabamana, kingani nabama koya shine nazo naba Asmeey this Vanillah agaban kowa agaban yaran nan tahaumin rashin kunya harda cemin wawiya wai kawai dan ban bata strawberry b……" Kafin takarasa maganan Asmesy ta tari numfashinta muryanta na rawa tace "wlh Mom karya takemin itane tafara cemin wawiy…….." tassssssss! Mom ta dauke Asmeey da lafiyayyen mari da saida ta ijiye kafafunta na lallen kunshi akasa saman tiles hands nata suka kwalbe ajikin chair, ita kanta Ramla saida kirjinta yabuga bata taba kawowa Mom zata daki Asmeey over this silly ice cream issue ba, idanun Asmeey harwani baki sukayi gashi a left side Mom tamata marin inda tamata dazu da safe, Mom namata wani mugun kallo cikin kakkusan murya tace "is this tarbiyan dana baki? Are you stupid kike kiran yayarki dake gaba dake makaryaciya! Are you stupid Asmeey!" Mom ta daka mata tsawa da saida falon ya amsa idanun Asmeey sukai jaaa ga duka kannenta awajen, she felt embarrassed, baki tabude zatai magana amman kuka yasa ta kasa magana cus tana bude baki zata fashe da kuka ga kanninta awajen, Mom dake huci sosai tana kallonta tace "okay I'm talking to you kin sauke kanki kasa ni ga shashasha eh?" Dago kanta tayi ta kalli Mom sai kawai jikinta yahau rawa ganin idanun Mom tace "so….s……" saikuma sorry yakasa fitowa sabida kuka, ran Mom yayi masifar baci tawani fizgo gaban rigan Asmeey haka yarinyar ta taso fuuuu kafafuwanta sukai daba daba akasa skirt nata ya sauka kan black lallin Ramla naso tabata hakuri cus she's regretting telling Mom amman tsoro take ahada da ita, Mom tashiga daga murya tana jijjiga Asmeey yace "don't you know how to apologize Asmeey ko saina daddakaki zaki bada hakuri" rawa bakinta yashiga yi idanunta sunyi fiki fiki sun kankance daidai lokacin Gwaggo tabude falon ta shigo tundaga lallin da taga ya kwalbe akasa ta shiga kallo da yanda Mom tarike yarinyar tana kallon yanda hannayen Asmeey da jikinta ke kyarma kawai Gwaggo ta kurma mahaukacin ihu tana bude kofa da saida gidan kap ya amsa. "Ihuuuuuuuu zatai kisan kai jama'a ataimaka zatai kissan kai!" Tundaga su Mamie da Ammi dake backyard dasu Ya Mustapa da Hamad dasu Baba dake masallaci harda Ustaz da su Ya Hameed saida aka fito da gudu ana yowa flat din jin ihun Gwaggo, Mom ta dauke kai daga kallon Gwaggo dake ihu babu ko dar a zuciyanta ta shake wuyan rigan Asmeey dake kyarma tace "I said apologize now!" Ta daka mata tsawa ahankali cikin muryan ban tausayi jikinta na rawa sosai tace "so….so…sorry" "Sorry Wa ne"? Mom ta sake dauketa da mari a same kumatu for the second time mercilessly, Gwaggo tai ihu ta taho tana ture Mom tace "wai ke yarnan bataki bace ko yar riko ce?" Mom dako gezau batayi ba da tureta da Gwaggo keyi tana rike da Asmeey tace "speak!" Bakinta na wani kalan rawa tace "so……sorry Ya Ramla" daidai lokacin su Ya Mustapa na shigowa falon Ya Hamad biyeda shi, awani kalan zuciye Mom ta hankada Asmeey saitin center table dake tsakiyan falon da mugun karfi sai kasa tamugun buge da center table din a gefen cikinta daidai kan idon Baba dasu Mama da kowa hadda matan su Ya Mustapa, Mom tajuya fuuuu tawuce stairs Baba kawai yayi mutuwan tsaye yakasa magana ganin yanda Mom ta buga yarsa da center table mugun buguwa ma, Gwaggo ganin yanda yarta sandarewa tayi ta kankame awajen cike da mamaki kowa na falon was freeze har ita Mama yar fadan Mom, Mamie ce ta iya motsi cikin kowa takarasa tsakiyan dakin ta duka tasa hannu ta dago Asmeey data kasa motsi idanunta har lokacin duhu duhun mari suke mata, ahankali Mamie tace "Ma'u sannu tashi, kinji ciwo"? Jikinta na wani irin kyarma totally destabilize ga lallen da aka mata ya dame duka har center table yabaci shima da lallin da sauri ta girgizama Mamie kai har lokacin bata gani da kyau ga kunya yagama kasheta ga jikinta rawa kawai yake, tajuyo tana kokarin neman Mom dabata gani a falon ba kowa na kallonta, ahankali Mamie tace "Doctor zoka dubata" dasauri Asmeey ta kalli Mamie jikinta na rawa yana kyarma amman takakalo murmushi muryanta ciki ciki yayi rauni tace "babu abinda kemin ciwo ai ban buge ba" dasauri Yusra tace "duk Ya Ramla taja Mom ta daketa and she lied cus Ya Hamad ai bata cemiki wawuya ba kene kika kirata wawiya because of ice cream" ran Ammi taji yabaci tashigo tsakar falon tace "are you the reason aka daketa haka? Ramla do you even love your sister? Kalli kumatunta, kalli lallinta, kalli yanda jikinta ke bari, bakida imani ne Ramla ke ba mai marba Asmeey ice cream bane bakene babba ba? Wace kalan muguwa ce ke"? Tadaga hannu zata daketa Abba yace "dakata! Karki daketa!Yarane ba'a raba yara da irin kananun fada haka musamman wajen rabo amata afuwa, Husna" da sauri Asmeey ta kalli Abba idanunta sunyi firfirr ba hawaye tace "uhmmm na'am Abba" magana Abba zaiyi but sai yayi shiruuu ganin yanayin yarinyar yace "kaita ta wanke hannayenta da kafafun Maman Doctor, Nana ku gyara inda yabaci da lallen" yunkurin dagata Mamie tayi tace "tashi muje" Asmeey takasa tashi bakinta zaiyi magana sai kawai ta kasa sai hawaye yataru a idanunta ta juyar da fuskanta irin na neman inda zata saka kanta dinnan Mamie ahankali tace "zo Asmeey come" Mamie zata kamata Asmeey zata fita daga jikinta takasa da sauri ta shige jikin Mamie duk yanda takeso ta daure ta danne takasa tafashe da kuka sosai jikin Mamie mara kara sai shesheka da jikinta dake motsi irin kukan nan mai taba zuciya tana huci mai bala'in zafi a jikin Mamie, Baba ya yunkura zai wuce sama Abba yarikemai hannu alamun no dan yaga yanda Baba ya zuciya kuma babu kyau hukunci acikin fushi hakan yasa ya tsaya, Munir yawuce ahankali wajen ya tsugunna kusa da Mamie da Asmeey ke jikinta yadaga hannunsa yadaura saman bayan Asmeey yayi shiruu idanunsa sunyi jazur, ahankali Hamad yajuya yafice daga falon yarufo kofa, Gwaggo da sai alokacin tadawo daidai tace "toh wlh wlh tunda dai abinda akema yarnan agidan nan kenan zan tattarata natafi da ita, kuma dagayau tabar shashin nan, idan uwarta ta isa tazo inda nake ta tabata, bantaba ganin muguwa Uwa irin mahaifiyarta ba, wlh kekuma sarai ai kinsan halin uwarta koda tamiki laifi ai sai ki rufamata asiri ba yar uwarki bace? Kuma ai kina sane ai haushi takeji ansata tayi lalli alhalin tahana ba dole ta dirketa ba, ga lallin nan tasa yabaci hankalinta ya kwanta, Mara Imani da idanunta kaman na mutan da, saisa Allah yahanata tsayi kaman in kifeta da kwando, muguwa dunkulen magi kawia ai gajeren mutum akwai bakin hali" Gwaggo na fadin haka ta karaso takama hannun Asmeey dake jikin Mamie tace "tashi muje" fitoda ita daga jikinta Mamie tayi tace "tashi kuje Asmeey" idanunta akasa taki kallon kowa ta kasa tashi, rai abace Baba yace "badake ake magana ba tashi" ahankali ta tashi da dauriya da kyar, Gwaggo tariketa tajawota aka mammatsa suka taho Ya Mustapa yabi yanda ke tafiya da kallo dakuma gefen cikinta suka fice sai kawai Mamie itama tabisu abaya haka sauran matayen, Mama kuma tawuce sama abinta wajen Mom danta bata hakuri Ya Mustapa yajuya yafito kowa ma yafito. Flat din su Mamie Gwaggo tashiga da ita har lokacin fada take sosai dakin dake kasa tawuce dan ita duk dakunan kasa nakowani flat nata ne cus duk inda taga dama take kwana tabude tashiga tace "wuce kije ki wanke hannunki" wucewa tayi ahankali ta shiga bayin ta maida kofan tarufe takarasa wajen wash hand basin tadaga hannuwanta da akama lalle duk sun gwalje both baki da jan tai shiru sai kawai hawaye suka sauko daga idanunta tabude tap din ta wanke hannayen tasss and lallin yayi mata bala'in kyau inda ta gwalje ne yayi wani iri, lallin yayi dan ja, Kuka takeso tayi but saita hana kanta gabanta har lokacin faduwa yake, Mom sai fadomata take arai bazata taba kwana anan ba sabida kar ran Mom yabaci zata bari Gwaggo tai bacci saita tafi wanke, kafafunta tayi suma tass ta dauro alwala dan batai salla ba ta kalli kumatunta da sunyi jaa sosai abunka da fara ko yaya aka mareta kalan fatar fuskanta saiya chanza towel na bayin tasa ta tsane fuskanta sannan tabude bayin tafito Mamie tagani tsaye kusa da bayin tace "alwala kikayi?" Dasauri ta gyadama Mamie kai tana kakalo murmushi tace "eh banyi salla ba shizanyi yanzu" Mamie na kallonta tace "babu abinda ke miki ciwo?" Gyadama Mamie kai tayi Gwaggo tace "wannan ai ko zata mutu bazata fadi ba uwarsu yanda kikasan ta tsafesu ni zoki salla muje falo muci abincin dare yunwa nakeji"dan takowa Mamie tayi dab da ita gently takai hannunta ta daura saman kumatunta dayayi ja tana kallon idanunta, wlh tunda Mom ta mareta koda yanzu tai alwala tasa ruwa a fuskanta bataji sanyin dataji kaman sanyin dataji yanzu da Mamie ta daura hannunta kan kuncinta ba sai jikinta yayi sanyi sai taji jikinta ta ciki yadaina radadi cikin murya mai sanyi dakuma so Mamie tace "ya isa! Calm down zanma Mamanki magana dakaina kinji, next time koma menene karkima nagaba dake rashin kunya, kinfi kowa sanin mahaifiyarki macece mai bama yaranta tarbiya yanda yakamata bata yarda danta ko yarta ya taka na gabansa ba, next time respect Ramla kinji no matter what don't talk back at her just like yanda Mom bazata bar su Yusra ko su Nana sumiki rashin kunya ba kema bazataso kima na gabanki ba, but ya isa okay" gyadama Mamie kai tayi idanunta na cicciko da hawaye, ahankali Mamie takai hannunta gefen cikinta tace "wajen namiki ciwo nasa Doctor yakawo miki magani?"Girgizamata kai tayi tace "a'a bayayi" Mamie tace "to yi salla abinki" Gwaggo taja tsaki tace "wlh takara taba yarnan tagani yo ita ubanwa naga tana girmamawa? Girmamani take? Mata sai girman kai jitake tafi kowa sabida tayi boko, bokon da agidan d'ana tayi kuma da kudinsa banza kai shashasha muzuba ni da ita zan nuna mata matsayinta" Mamie dai tawuce tafita Asmeey ta dauki hijabin datagani kan gadon wajen tasaka tai salla magrib da isha'i ma da akayi Gwaggo da tunda tafara salla take kallonta tace "kiwa Allah Asama kitashi kicire hijabin nan muje muci abinci cikina sai kuka yake" tashi tayi ta cire hijabin tawarware mayafinta tasa aka yadan sauko mata shoulder Gwaggo tai gaba ta biyota abaya su Ya Mustapa duk suna falon Ball ma suke kallo a tv falon da Ya Abdallah da Ya Faisal da matarsa ke basa abinci, shi kadaine be ciba sai Ya Hameed shima.
Hameed yakalli Asmeey fuskanshi ahade yace "kawomin ruwa" hararansa Gwaggo tayi tace "bazata kawoba bakaga kalan dukan data gamaci ba" tabe baki yayi yace "inda sabo ai tasaba yanzu" wani mugun kallo yayyinsa sukamai, yadanyi murmushi, haushin Mom yakeji sosai aransa, he hates the woman wlh sabida yanda take da duka, da girman kai da fadinrai, haka su Ayah suka wahala a hannunta shi besan me Baba yagani ajikinta take zaman aure da irin matar nan ba, wucewa fridge Asmeey tayi a kitchen tana tafiya ahankali tasa ruwa a tray da cup tafito dashi tazo falon kanta akasa tazo gabanshi ta ijiye. "Gashi Yaya" zata juya Mustapa yace "zonan" faduwa gabanta yayi ta gyadamai kai tazo gabanshi babu wasa kan fuskanshi like a big brother yasa hannu a aljihunshi yaciro wayanshi ya kunna flash yanuna mata gefenshi yace "sit" zama tayi ahankali Gwaggo tace "yauwa dubamin ita" hannunshi yadaura saman kanta ya juyar da fuskanta yana haska kumatunta Mamie ma tafito ta tsaya kansu sannan yasauke wayan yace "inda kika buge namiki ciwo?" Girgizamai kai tayi tace "a'a Yaya" hannunshi yakai ahankali yataba gefen cikin ta saman riga da kyau jin wajen is not hard yadan sauke ijiyan zuciya yana kallon yanda take runtse idanu she need drugs, hannunshi yacire dan murmushi yamata tareda shafa kanta yayi cikeda kauna ta dan uwa yace "it's okay okay don't fight with ur sister again, i will buy another ice cream for you gobe" Abdallah yace "wani flavor kikeso nima zan siya miki" Faisal yace "akan strawberry flavor tayi fada nima zan siyamata gobe" Hameed yadan harareta yace "sweetthooth kawai i will also buy for you" murmushi kadan tayi feeling so loved, ahankali tace "nagode Yaya" Mamie tayi murmushi tana kallonta Gwaggo tace "sauko muci abincin" Ya Mustapa yace "jekici abinci zan fita nakawo miki drugs" tashi tayi zuwa kujeran da Gwaggo take ta zauna suka faraci tanadan jin nauyin yayyinta dan ba koda yaushe take ganinsu ba, but kuma tana sonsu sosai sunada kirki sosai and suna son kanninsu suma.
Parking yayi ahankali tareda kashe motan ya kalli paper bag dake gefen sa kan kujera yayi jimmmm sai kawai yatashi yakai hannu yadauka tareda bude kofan yafito yarufe yafara tafiya zuwa flat nasu ko kadan baisan yayyinshi kowa na falon ba hakan yasa kai tsaye yabude kofan yashigo tsayawa yayi ganin kowa harda Mamie duk a falon ga Gwaggo da Asmeey datai tsuri gefen Gwaggo ana kallon ball Baba ne kawai baya falon, duk juyowa akayi ana kallonsa banda Asmeey da tana ganin shine ya shigo ta maida fuskanta tv, ganin yanda kowa kallonshi yake yasa da sauri yaboye abun hannunshi abaya yajuya dasauri zai fita daga falon Mamie tace "Hamadi!" Chak ya tsaya hakanan gaban Asmeey yafadi batare data dauke kanta daga tv ba, Mamie tace "ina zaka daga shigowan ka? Ina kaje ban ganka ba tun dazu? Come" dan jimm yayi sai kawai yasa hannu ya maida kofan yarufe yahade rai kanshi akasa yafara takowa zuwa wajen Mamie Mamie tabi paper bag din da kallo tace "meka sayo?"Agefenta ya ijiye paper bag din da sauri batare dayace komiba kawai yajuya kowa na falon yabishi da kallo yawuce stairs, Gwaggo tace "mara mutunci meya kawo miki banda ni? Koni ba mutum bace" Mamie tasa hannu tabude paper bag din fari ba logo ajiki kawai saita dago kai takallo sama harya shige dakinsu sai kawai tasa hannu taciro ice cream a babban cup strawberry da akai breaking cone da chocolate da so many orishirishi ciki ga cokali takalli Asmeey da idanunta ke tv tace "Ma'u gashi yayinki yasayo miki ice cream" kowa na falon saida mamaki ya kashesa barin ma Hameed daya wani zaro idanu irin na gulman nan, Asmeey ta kalli Mamie saita kasa tashi ta amsa Gwaggo tace "tashi ki amsa Hamadi ya siyamiki yaga kinci bakar duka uwa jaka" tashi tayi zuwa wajen Mamie akunyace tasa hannu takarba ice cream din Mamie tace "kije daki kisha abinki" batai musu ba tawuce dakin Gwaggo tana kallon ice cream din daya dadada mata rai, dan satan kallon sama tayi kafin tabude dakin Gwaggo ta shige. Gwaggo tace "Doctor kaika aikashi ya sayo abin ne?" Girgizamata kai Ya Mustapa yayi ya mike tace "bari na sayo mata magani" su Abdallah suma sukama Mamie sallama suka fice flat nasu. Hakan yasa dasauri Hameed yatashi yazo wajen Mamie cikin whispering yace "Mamie Hamadi buying ice cream for a gurl this is unbelievable" hararanshi Mamie tayi tace "munafincinka yakesa Hamad baya shiga harkan kowa cus u give meaning to anything me dan ya sayama Asmeey ice cream? Ba agabansa taci duka ba yanada tausayi" Hameed yana wani murmushi yace "Mamie kodai kodai he he…." Tallabemai keya Mamie tayi tace "kaga saida safe" ta tashi tana murmushi tayi stairs abinta ta shige dakinta shima yatashi yace "bari naje na sami dan iskan nan" dakinsu Hameed yabude Hamad baya ciki it seems yana bayi kayan jikinshi yarage dagashi sai singlet da boxer yazo gaban bathroom din ya jingina da bango yayi folding hands nashi yana jiran yafito, kusan 5min yayi awajen Hamad ya bude kofa yayi wanka yana sanye dawani ash color joggers da white t-shirt na polo mai kyau ga kayan daya cire abayi a hannunshi, hada ido sukayi da Hameed dakemai wani kalan kallo da sauri ya dauke kai ya fuske yafito zai wuce karaf Hameed yasha gabansa yace "wat is that you did earlier?" Chak ya tsaya batare daya kalleshi ba yace "I don't know wat u are talking about" dariya ke neman kufcema Hameed yace "karya kake munafuki why did u buy ice cream for Asmeey?" Tambayan kaman zaisa ya nutse akasa sai kawai yama juyama Hameed baya kaman zai kara komawa bayin Hameed yarikeshi ya fashe da dariya cikeda iskanci yace "so you are in love" watsar da kayan hannunshi yayi akasa yace "stop Hameed leave me alone" tsabagen son yakureshi Hameed yace "to kaida bama kasan ya ake sex ba how would you be intima……" wani kalan tura Hameed yayi da karfi kaman zaki yawuce da sauri ya sunkuci laptop dinshi zai fice daga dakin Hameed yadaga murya yace "google wat is sex and start learning tun yanzu kafin asami matsala bayan aure" da sauri Hamad yafita yana bugo kofan me Hameed zaiyi inba dariya ba dariya haryana faduwa gaban bayi is not like Hamad baisan sex ba but he can swear baisan yaya akeba wlh kuwa kunya irin na Hamad daban ne aduniya, he hates maganan banza, he hates looking at abubuwan banza ko iskanci ko tsiraici ko maganan kiss baiso ayi a inda yake yanzu sabida dan maganan nan zai iya harsu koma Kano yadena zama dakin nan kenan yadinga avoiding nashi, ba lallai yanason Asmeey ba bama ya tunanin tsokanane kawai yasan tausayi yarinyar tabashi yasayo mata ice cream kaman yanda suma sukace zasu saya mata, da kyar yagama dariyan yaduka ya kwashe kayansa yaje ya ijiye masa yafada gado abinsa sai bacci. Babu kowa a falo hakan yasa yawuce dinning kawai yama ijiye laptop dinshi yawuce kitchen yadauko ruwa yaja kujera ya zauna yabude ruwan yasha yana sauke ijiyan zuciya sannan yafara aiki. Almost 30min shi kadai afalon yana aiki aka bude kofan aka shigo hakan yada yadago kanshi karaf suka hada ido da Ramla wacce tana ganinshi taci burki gabanta na faduwa hakanan cikin duka yayyinsu ba ita kadaiba all of them sunfi shakkan Ya Hamadi cus babu wacce yake wasa da ita babu wacce ta taba ganin hakorinsa baitaba mata magana ba, gashi yanada kwarjini wani kallo yamata dayasa batasan sanda ta sauke kanta kasa ba tace "uhnnn dama…..daman wajen Asmeey nazo" bayabo ba fallasa yace "get out!" Har tsakiyan kanta taji muryanshi kusan tunda tasan Ya Hamad this is the first maganan dayake mata wlh kuwa gyadamai kai tayi tace "tom saida safe Yaya" tajuya tabude kofa tafice.