Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 43
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 43: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 43. Gyadama Mamie kai yayi yakalli Hameed yamikama Hameed hannu…
4,364 words
Gyadama Mamie kai yayi yakalli Hameed yamikama Hameed hannu dasauri Hameed yarikesa murya Chan kasa Hamad yace "me police sukace?" Girgiza kai Hameed yayi alamun ba update, anatse Hamad ya kalli Ya Mustapa yace "Yaya tell me everything that happened waya kiraka" everything da Security suka fadamai ya maimaita Hamad yayi shiru tareda lumshe idanu kanshi na bugawa sosai yana recalling plate number motar da Mom tazo da ita rannan data zubama Asmeey yaji. Murya chan kasa like a genius yace "DK4615" atare kowa yace "mene!"? Cikin rashin kuzari yace "indai motan datazo dashi last time shine na yanzu toh that's the plate number"bring my laptop Hameed dasauri Hameed yatashi yafice yaje dakinsu yadauko laptop din Hamad yadawo dashi ya kunna yabama Hamad, ahankali Hamad yace "wani yaban hotspot" nan da nan Ya Mustapa yabasa yayi connecting laptop dinsa withing 10min yayi running license plate din yace "got it" dasauri Ya Mustapa yakalli screen din Hamad yace "the car belongs to INUWA RENTAL CAR SERVICES DAKATA" Ya Mutapha yace "but bazasu bamu client Information nasu ba how does this helps with the investigation" dasauri Baba yace "hala sabon layin datayi shita basu tunda bata amfani da line dinta" anatse Hamad dayayi shiru yace "not just that Baba" yayi shiru duk aka kalleshi adakin, anatse Hamad yace "most cars na rental services sunada tracker ajikinsu saisa ba'a iya sace motocin rental services, inhar bata komar da motar ba which I strongly believe data sace Asmeey batada lokacin maida musu da mota, so in this case I will not track her I want to track the car, but…." Yayi shiru duk aka kalleshi Faisal yace "but mene Hamadi!" MAhankali yace "i have to go to rental services din they need to access server dinsu idan inaso na iya tracking car din I know they will never give me access to server nasu saida police warrant" dasauri Baba yace "I'm calling inspector Barau wanda ya dauki case din" yunkurin tashi Hamad yayi ba karfi jikinsa Ya Musty yace "Hamad ka zauna agida u are not good to go" girgiza kai yayi yace "without me u can never find her Yaya i can manage, Hameed hold me" Hameed yakama Hamad yace "kaini na chanza kaya and pray" daki sukaje saida yayi salla ya chanza kaya sannan suka fice all the men akabar matan agida suna kokarin fita adaidaita sahu na sauke Munir da idanunsa sukai ja duk akai parking ana kallonsa Baba yabude mota yafito da sauri yace "Munir" hawaye ya share yace "Baba anga Asmeey"? Ganin Baba bai magana ba kawai yawuce yabude motan Ya Faisal yashiga, Baba ya koma mota aka wuce Faisal yace "mesa kabar school kazo waya gayamaka?" Ahankali yace "Ya Aya! A airport ma na kwana da tun jiya zanzo da safen nan aka samu jirgi" babu wanda yasake magana a rental car din suka hadu da yan sanda nan da nan aka basu access to sever before good 15min dan tracking takes time Hamadi yagano motan a Funtua! Har yan sanda saida sukace Funtua! Komawa motoci akayi gaban Hamadi na fadi he's just praying he will see her in Funtua aka wuce. EPISODE 9️⃣8️⃣
Wato azaba daban daban ne, rannan da Mom ta watsa mata burkono ajiki tadauka bazata tabajin azaba da zafi dayakai wannan ba but yau Asmeey taji azaban da takeji yanzu dama wuka kawai Mom tasaka awuyanta tamata yankan rago she would prefer that a thousand times da abin nan da ake soka nata agabanta! Tayi ihu tayi ihu abin yakaiga kaman muryanta ma yafashe dan ihun baya fita, idanunta hawayen dake fita ciki sun koma kaman jini tsabagren kuka da ihu dan yanda take stretching eyes nata suma sunji ciwo that is wat makes hawayen kaman jini and a bit bloody. Tana wani irin nishi tana kuka tana kallon Mom dake tsaye kusa da Dr cikin wani irin murya da yana fita but ba sosai ba tace "Mommmmm" dan juyowa Mom tayi ta kalleta fuskanta ahade ba rahama ko tausayi, sai ta taka zuwa wajen tace "ba'a ayi suctioning cikin tukunna ba, baki gama chan azaba ba" wani kallon Mom Asmeey keyi kalan kallon da tunda Mom ta haifo Asmeey duniya Asmeey bata taba mata kalansa ba hawaye nabin idanunta jajaye, awani irin hankali agalabaice tace "ban yafe miki ba Mom!" Dummm! Mom taji kalman yadaki tsokan lungun zuciyanta, sai taji kaman she's mistaken ba abinda Asmeey tafada kenan ba, no way Asmeey zata iya gayamata irin maganan nan, wani irin numfashi Asmeey take tanama Mom kallon tsana kololuwa tace "bazan taba yafe miki duka abubuwan dakikamin ba Mom ko Allah nankasheke yana dawo dake bazan taba yafemiki ba!" Mom tawani kwasa mata mari abaki! Jikake tassss! Chinedu yace "Madam Barrister see I go stop oooo on top this pain u are beating this child again!" Bakin Asmeey na jini sabida marin da Mom tamata tace "Mom cikin nan dakika ciremin will hunt you day and night Allah saiya azabatar dake kwatankwacin wanda kikamin!"Wani kyarma Mom keyi tace "bazaki shiru ba saina kasheki wlh!" Asmeey tace "meya rage? Ga wuka chan ki kasheni Mom, Karuwa kawai!" Wani haukacewa Mom tayi takama wuyan Asmeey da duka hannuwanta biyu tashake sosai Asmeey kotari bata iyayi daidai lokacin aka bude kofan dakin aka shigo Fawaz ne daidai Chinedu na zuko cikin cikin wani jini ya ballema Asmeey sai bleeding Chinedu ya firgice shi bata dukan Mom da ake yake bama jinin daya ballema yarinyar yake, yace "Jesus Christ!" Fawaz yayi kan Mom baiyi wata wata ba yadauke Mom da mari ya daga kafa ya kwasheta saita ta buge da gadon akasa kawai yashiga dukanta da kafa yace "matana kike duka jaka kawai" idanun Asmeey na juyawa sosai tana kallon yanda Fawaz ke dukan Mom Chinedu jikinsa na rawa sosai yashiga hada alluran dake tsayar da bleeding yama Asmeey sannan ya yago sanitary pad guda biyar yasa agabanta yashiga kwance kafafunta yasauke kasa, Fawaz yakalli Chinedu yace "u don finish?" Dasauri yace "yes Sir but she's bleeding she's will stop soon" gyadamai kai yayi yaduka yadaga Mom data kasa motsi yayi waje da ita, shikuma Chinedu yazo tawajen hannayen Asmeey ya kwance ya tsaya yana kallon Asmeey da idanunta ke juyawa kaman batasan inda kanta yakeba yayi shiru he's feeling very bad and scared wlh, sai kawai yacire labcoat din ya yar da handglove da nose mask daman jakan bawai yana bukatan wani abu ciki bane duk supply na asibitine yadauki jakan goyon bayansa kawai yafito yaje wajen guard yace "I'm going" duk daganan tsakar gida sunajin ihun Fawaz yana kirban Mom yana cinta yana gindin tsohuwa, Driver yawuce yakaisa dan dama Fawaz yace yagama akaisa.
Ahankali dudda idanunta na juyawa maranta nawani irin mugun ciwo da bata tabajin kalansa ba baihanata ganin wani katon gidan jini kwara daya rak babba akasa ba, wani irin ijiyan zuciya tasauke ta mirgino daga gadon tafado kasa kan tiles din timmmm! Tanaji kaman takara bude wani pampoo ajikinta, jan jikinta tashiga yi cikin all the jini dake tiles din zuwa wajen gudan dake kasa takai hannunta dake rawa tadauka awani irin hankali tadaura kan kirjinta tana wani irin kuka da babu kara takai hannunta tadauki kasan riganta da Mom tayaga tadaura saman gudan jinin data daura kan kirjinta kawai ta kankame dan she understood this is babynta na ciki da aka ciro, wani irin sanyi takeji bana wasa ba kaman ansata cikin freezer dake minus 1 degree Celsius and she's bleeding as well kawai tafara shivering bana wasaba, sanyi daga kai, kafafunta dake abude hannayenta, wuyanta duk shiganta yake, ga azaba tanaji, ga ciwon mara, kara rungume Baby tayi cus tasan itama mutuwa zatayi tana ganin jiri sosai, hakoranta na rawa tana wani irin kadawa ahaka idanunta suka rufe ruffffffff………
Around 9 na safe suka iso Funtua akai daji kusan tafiyan awa daya yan sanda suka kashe sirin na motansu daga nesa suka fara hango gidan duk sai akai parking daga chan nesa daji ne baza'a hangosu ba. Aka fiffito Inspector ya kalli su Abba yace "bamusan su waye agidan ba you guys should stay here harsai mun baku green light" su Baba suka gyadakai gaban kowa na fadi, hoping Asmeey na gidan inspector yakalli yaransa yace "vest on silencer on!" Suka sassaka vest suna saka silencer kan bindigoginsu sannan ya rarrabasu suka shiga tafiya without sound suna zuwa towards the house Hamad kawai yabisu shima Hameed haka, kowama yataho ina no time to waste, is morning two guards ne on duty, 2 suna bacci , biyu kuka sun tafi da Chinedu last night gate inspector yataba security yabude kofa da bindiga hannunsa inspector ya kwashe da yana sumar dashi dayan kafin yayi wani abu suka kwashesa shima all this yafaru babu wani sound duk aka shigo gidan harda su Baba sukaji muryan Fawaz da karfi. "Mayya kawai dayake mijinki na gargajiya yake miki kin nace min kin makale, cini da kyau raguwan banza me kishi da yarta" inspector yanuna flat dayakejin muryan yayi wajen duka suna biyeda shi abaya ahankali yabude kofan flat din aka shiga kawai sai gaban Baba yafadi hakama Munir sabida sound na kaman muryan Mom dasukaji tace "ahhh Fawaz nagaji! Yakuri" daidai inspector yayi wani mahaukacin dukan kofan dakin sukaga Mom tsirara haihuwar uwarta saman Fawaz akan gado da tabaryansa cikin turminta babu anything ajikinta tajuyo atsirace daga ita har Fawaz daya yunkuro da kai yaja daga kwance sun kallo kofa.
Tundaga kan Abba, Kawu, Mustapa, Abdullahi, Faisal, Hameed da Hamad dukansu harsu yan sandan juyawa duk sukayi ganin babban mace kan dan yaro dabai wuce su Hamadi ba tsirara while Baba da Munir nawani irin kallon Mom yayi wani baya zai fadi Munir yataresa da sauri hakan yasa Mom ta tashi da sauri gindin Fawaz na fita daga gabanta tawuce dasauri tadauki dogon riga tana sawa shima Fawaz yatashi abala'in rude Mom tashiga juye juye sai kawai tayi wani kofa data gani da gudu Munir yace "zata gudu" yan sandan duka sukayo ciki suka damke Mom da Fawaz dayake Tsirara Hamad yawani shigo azuciye ture yan sandan yayi yawani kama wuyan Mom yana mata wani kallo yace "ina matana?" Wani kallo Mom tamai babu wani alamun tsoro saidai kunya kawai tace "kai har Kanada mata mahaukaci" sakin wuyanta yayi yawani fizge gun na Inspector yasa akan Mom Abba da kowa sukace Hamad! Inspector yace "Hamad calm down let's handle this properly!" Cikin wata bakan zuciya yana kallon Mom eye cikin eye yace "for the last time Salima! Where is Asma'u?" Sosai Mom ke kallon Hamad gabanta na faduwa sosai ayanda taga idanun yaron wlh he can shoot her and she's not ready to die now hakan yasa kirjinta na bugawa dar dar tace "she's in that flat!" Tanuna flat opposite wanda suke ciki Hamad ya jefar da bindigan yajuya da sauri akabi bayansa harda inspector akabar dan sanda data tare da Mom da Asmeey akai flat din, ahankali Hamad yabude kofan flat din wlh wlh abinda yagani yasa kafafunsa suka kasa motsi suka shiga rawa suna karyewa, Asmeey na kwance kan tiles akasa gawani gadon asibiti gawasu karafuna akasa, ga lab coat duk jini, ga hand glove duk jini, ga kaya harda pant apapparke, ga Asmeey kwance cikin jini daya bushi saidai kyalli kyallin danko da jinin yake, Asmeey looks dead, tayi wani irin fari kaman an samata farin hoda dawani dark kalan kore kore, fuskanta wajajen eye balls nata sunyi baki, exactly yanda gawa ke looking, yanda Hamad yayi kasa haka shima Munir da Baba, Kawu ma yakasa motsi, su Hameed ma haka, da kyar Ya Mustapa nawani irin layi yataka yashiga dakin da namijin kokari. Wajen Asmeey yayi ahankali yaduka yayi kneeling cikin jinin yana kallon yarinyar da babu any breathing sign ajikinta, hannunsa yawani shiga rawa yakaisu yadaura kan hannuwan Asmeey dake kirjinta ta kankame wani tsumma haka daya koma kalan jini yadaura akai, hannunta sanyi kaman kankara, kokarin zare hannun yayi amman hannunwan sun sankare yarinyar ta dade da rasuwa! Awani irin hankali yace "Innalillahi wa innailaihi Raji'un!" Duhu duhu Hamad yafara gani kansa na bubbuga yasoma jin magana sama sama, Abba yayi jarumtar shigowa dakin yazo wajen yace "a'a ina ganin doguwan suma ne Doctor ko"? Yakai hannayensa zai kama na Asmeey dake kirji but hannun yarinyar sun sankare kaman kankara kaman ya fizgo da karfi zasu karye, jikinsa yayi wani kalan mugun sanyi sai yabar hannun, yakai yatsansa wajen hancinta yakara yayi shiru hoping yaji sign na numfashi, babu ko digin numfashi daka fita daga nostril dinta, gabansa nawani irin fadi Abba yadago kanta cus he's not believing this, ahaka kan yataso asankare in that same position wallahi babu rai jikin Asmeey! Ahankali cikin sanyin muryan dake breaking Abba yace "Innalillahi…….wa Innailaihi…….Ra…..Ra…..Raji'un! Kullu Nafsin Za'ikatul Maut!" Flat! Hamad yazube awajen.
INNALILLAHI WA INNAILAIHI RAJI'UN ASMEEY TA RASU!???
ASMEEY TARASU??
HOW IS HAMAD GOING TO LEAVE WITHOUT ASMEEY? HOW????
TA INA YARON ZAI FARA?!
ALLAHU AKBAR MOM SHIKENAN KINCI BURIN KASHE YARINYAR NAN YAU BURINKI YA CIKA!
GA KI GA FAWAZ MOM!!
I AM REALLY CRYING GUYS😭😭😭
SEE YOU SATURDAY 😔 Yayyinsa suka rirrike Hamad, Munir wani irin ijiyan zuciya yake sauke kaman zai shide he has seen dead bodies a school a mortuary and Asmeey looks like one today is the saddest day of his life dayanaji kawai kaman yabi Asmeey yamutu Baba yakasa motsi baitaba sanin he loves Asmeey kaman yanda yakeji yanzu ba ganin gawanta komi na rayuwansa ya tsayamasa chak yakasa komi kallonta kawai yake hoping zata bude idanunta and just look at him once tamai murmushi ko tace Baba with that her simple voice ko tamaima kuka, su karan kansu inspector sun kasa motsi, da kyar Ya Mustapa yamike tsaye anatse tasa hannunsa yazare rigansa na tazarcen shaddan da Dake jikinsa danshi ka'ida kowani kaya yasaka yanasa t-shirt masu kyau da tsada ajiki kawai yazo inda Abba yake rike da Asmeey ya rufamata rigan yasa hannu ahankali ya karbeta daga jikin Abba yace "kumuje I need to take her to any near by hospital for confirmation na dead" basa ita Abba yayi yamike Abba yamike tsaye da kyar şu Hameed duka kama Hamad Kawu da Munir suka daga Baba da kyar suka fito compound daidai officer yafito da Mom da Fawaz Abba ya kallesu saiya dakata yace "Mustapa" Chak Ya Musty dake rike da Asmeey dake lullube ya tsaya Abba yataho wajen yasa hannu ya yaye rigan daga fuskan Asmeey Mom ta kalli lifeless Asmeey hakanan gabanta yayi mummunan fadi Abba yayi wani murmushi mai ciwo sannan yakalli duka yaransa da Baba da babu wani mai kuzari cikin dakewa Abba yace "dukanku nan na isa daku! Na isa nace ayi na hana kada ayi! Yau zan dauki mataki daba lallai yamuku dadi ba amman na isa ne yasa zan dauka banson gardama ko wani yaja dani!" Yakalli inspector yace "Inspector!" Anatse Abba yahada hannu yace "yau rokon alfarma nake gareka nasan aikinku kukeyi, mu ne kuma muka kawo karan nan anan agabanta da abokan aikinka mun janye karan nan!" Ba inspector kadai ba hatta su Ya Mustapa saida ya kalli Abba da ita kanta Mom kirjinta nawani irin bugawaAbba yace "dan wannan yarinyar marigayiyar nan muke fighting har muka bukaci taimakonku dama but tarasu! Inaso diyata should be in peace dabata samu aduniya ba ba'ayita kiraye kirayen sunanta akan wata ba! Asmeey tarasu fada yakare wanda daman dan ita akeyi officer mun janye karan nan munbar matar nan da Allah! Allah baya bacci kuma babu komi! Allahu Azza Wajal! Allah ba azzalumin bawansa bane banso mu yan adam mu nemawa Asma'u hakkinta Allah nafiso ya sakatama na janye korafinnnan kasaki matae nan da yaron, Allah daya bamu yarnan shiya amsa ranka dan haka bakomi munyi imani da kaddara mai kyau mara kyau officer na rokeka da girman Allah kabar case din nan sabida dani da family na bazama muzo police station dinba"Anatse Abba yakalli dukansu dake wajen dake kallonsa yace "kumu wuce mutafi" Musty yafarayin gaba sauran suka bisa abaya Baba da baya iya tafiya da karfi Abba tasama Munir hannu suka rikesa zasu wuce Baba ya tsaya yakalli Mom dawasu kalan idanu sauke kanta kasa Mom tayi jikinta yayi wani irin sanyi cikin rashin kuzari Baba yace "na sakeki saki biyu Salima! Gidan dakika karbe kije na barmiki yau zan kwace yarana dana bari cikin gidan! Har anada banso nakara ganin fuskanki amman kisani cewa bazan taba yafe miki ba har abada! Allah zai tsayar dani dake yamana hisabi rannan gobe kiyama" yayi shiru sai wasu hawaye masu zafi suka saukomai Baba kawai yafashe da kuka yana taba kirjinsa yana shesheka yace "Asma'u!……..hmmm" yawani fuzar da iska yana shesheka yana kallon Mom dake kasa yace "wayanchan karafunan da kika samata ajiki……" Kai! Baba kawai yashiga dukewa yafashe da kuka sosai yakama bakın rigansa yadaura kan fuskanshi yana kuka sosai kaman yaro shi kansa Fawaz saida jikinsa yamai wani iri for the first time dan wlh baitaba sanin yarinyar zata iya rasuwa ba, Abba karan kansa saida ya share hawaye, Munir ma huci kawai yake yana goge hawaye some yan sanda ma saida Baba yasasu kukaTass Baba ya goge hawayensa yace "da yardan Allah sai Allah ya azabtar dake da kalolin karafunan a wutan jahannama sai kuruwan yar nan da abinda ke cikinta sun hanaki zaman lpy Salima! Mun barki da Allah!" Baba yamike ahankali yayi wani luuuu zai fadi babu karfi jikinsa Abba da Munir suka kamasa suka wuce, Inspector ya kalli Mom ya kalli Fawaz ma kusan 1min sai kawai yakalli daya daga cikin boys nasa yace "kwancesu mutafi"Cire handcuff yayi a hannun Mom dawasu Fawaz da guards nasu kawai suka juya suka fice jikin Mom yayi la'asar hakama Fawaz duk suka tsaya charko charko, saida Fawaz yaji rufe gate dinsu sannan yakalli Mom yawani fizgota idanunsa kaman jan gauta yace "how dare you kill matana eh?"Mom nawani kallonsa da bakin cikin zuciyanta yace "we killed her dai together! Stop talking kaman ni kadai nayi kom…….." dauke Mom yayi da mari yace "you are evil Salima! Nayi nadaman ever haduwa dake! Cire ciki baya kashe mata how many yara nasa suka cire ciki! You must have done something to the girl cus kinga bana nan, I hate you! Na tsaneki wlh wlh! You have no more value to me! This is the end of us! Na barki har abada cus wacce tasa nake tareda ke kin kasheni so kin kashe affairs namu"Yawani juya bayan ya barar da ita yayi flat nasu Mom tamike tabisa da gudu ciki tace "when kana gani I don't have anybody yanzu and it's all because of you, shine zakace karabu dani har abada? Wlh wlh baka isaba Fawaz after i dedicated my whole entire life to you shine zakace karabu dani sabida wata kaskantacciyan yarinya ta mutu sai me?" Wani juyowa Fawaz yayi yace "wat did you just call my wife just now?"Cikin karfin hali Mom tace "eh mana ance kaskantacciy……." Kafa Fawaz yasa yawani kwashe Mom jikake kum akasa ta zube kan tiles yawani fara dukan Mom ba kakkautawa da kafa taketa kawai yake da ko'ina yana ball da ita Mom na ihu bana wasaba saida Fawaz ya sumar da ita sannan n yace "guards" da gudu suka shigo yanuna musu Mom yace "take this old witch da belongings nata kuje ku zubar Awani waje I don't care kada ku kara barinta into my house" Daukan Mom wasu sukayi a wulakance wasu suka dauki handbag nata da gyalenta sukai waje da ita shima Fawaz ya shiga shiryawa chan waje aka watsar da Mom kusada motanta akasa Fawaz yafito aka budemai mota ya shiga suka rufe kofan da gate suka wuce.Suka bar Mom asume awajen.Wani hospital dasuka gani anan kan hanya na Funtua suka shiga sukai parking Ya Mustapa dake rike da Asmeey yayi ciki da ta aka karbeta yabisu ciki akai connecting nata da machine dake duba sign of life but unfortunately Doctors sukai confirming Asmeey as BID wato brought in dead.
Hamad Ahankali idanun Hamad da aka bari a mota ke motsi kafin ahankali yabude idanunshi yayi shiru yana kallon saman motan trying to remember abubuwan dasauka faru gama recalling yayi hakan yasa dawani irin sauri ya zabura yatashi zauna yabi inda yake da kallo daidai ya hango Ya Mustapa nafitowa daga asibitin rike da wata a hannunsa datake a lullube da rigansa idanun kowa yayi ja yaga an wuce wajen motan ambulance dawani irin gudu yabude kofan motan yafito yataho wajen yana mika hannu yanaso yayi magana yakasa jiri na dibansa kaman mahaukaci Hameed yafara ganinsa yataho wajen da sauri yakamasa suka shiga tahowa da sauri Ya Mustapa ya tsaya ana bude bayan ambulance din yana kallon Hamad dake tahowa wajen wayyoo Allah sai kawai hawaye yafadomai,Yana zuwa wajen Hamad ya tsaya yakalli Asmeey dake hannun Ya Mustapa yakasa magana yakasa motsi yanaso yadago hannayensa sukahau rawa kawai yafashe da kuka hawaye ya sauko daga idanun Ya Mutspa anatse yace "the hospital confirms Asmeey dead Hamadi! We are going home" Ya Mustapa ya yunkura yashiga ambulance din Hamad yadaga kafa yashiga bayan ambulance din wlh yakasa baida karfi! Innalillahi Wa Innailaihi Raji'un sai kamasa yayyin sukayi suka ijiyesa yazauna yana kallon Asmeey daya kasa tabawa cus shi ji yake kaman ba matarsa bace aka rufe motan su Abba suka koma motocinsubaka shishiga aka dauki hanyar kano Anatse Abba yaciro wayarsa daga aljihu ya share fuskansa, yaciro number Mamie yayi dialing.
Zaune Mamie take a falo tareda Gwaggo da bata dade da tashi ba, da Ammi, da Mama, da Ya Aya, da Ya Aysha kowa yayi zuruuu, Mamie gabanta sai faduwa yake tun fitarsu, wayan Mamie dake kan kujeran ne yafara ringing firgita tayi da faduwan gaba har saida Ammi tace "Ya isa Mamie! Bari na baki wayar"Mika mata wayar Ammi tayi Mamie ta karba ganin Abba ne yasa dasauri tamike tsaye tace "Alhamdulillah Alhamdulilah Babansu Dr ne Allah sa an ganota" kowa yamike tsaye barin Aya da Aya da jikinsu harya fara rawa kafa wayan Mamie tayi a kunne kafin Abba yayi magana tace "anga Asmeey Alhaji?" Shiru Abba yayi yadan sauke ijiyan zuciya cikin muryansa data dushashe yace "eh an ganta!" Wani hamdala Mamie tayi tace "kai Alhamdulillah anga Asm….." saita kasa karasa maganan tuna yanda taji muryan Abba tace "meya sameta? Mesa muryanka yayi wani iri"Ijiyan zuciya Abba yasauke yace "Hamidah inaso ki dubi duka mutanen dake gidan nan farawa da tundaka kan mahaifiyata, kece jagora agaresu da karfin su idan kikai breaking down suma haka dan haka ki Dakar da zuciyanki ki saurareni da kyau" Abba yafadi ahankali ahankali Gaban Mamie na dukan uku uku tabi duka yan dakin ke tsaye ana kallonta harda Gwaggo, wani irin ijiyan zuciya kakkarfa Mamie tasauke tace "ina jinka" gabanta nawani irin faduwa anatse Abba yace "Asma'u tarasu!" Dummmmmm! Haka Mamie taji saukan zancen kaman aradu tai baya zata fadi dasauri Ammi ta tareta Aya ta karbi wayan dasauri tace "Abba nine…..ni…..nine Abba, meya sami kanwata? Abba tell me? What happened to my little sister? Abba wat happened to Asmeey!"Shiru Abba yayi kafin ahankali yace "Asma'u tarasu Aya!" Faduwa wayan yayi daga hannun Aya wayan Mamie ta tarwatse akasa Aysha ta kankame Aya dudda she's expecting abinda ranta dayaga mata but she's not believing it tafashe dawani irin kuka tace "wat happened to my sister"? Gwaggo kaman ta haukace tashiga soshe soshe hannayenta na rawa tace "miya sami Asama na? Ku sanar dani" kankame Aysha Aya tayi tace "our little Sister is no more Asmeey tarasu!" "Innalillahi wa innailaihi raji'un!" Haka Mama da Ammi dake rike da Mamie suka fadi at d same time Gwaggo ta sulale tafadi kujera a sume Mama tai kanta tana kuka, Aya kuka Aysha kuka babu mai lallashin wani Mamie in shock ta rirrike hannun Ammi tace "na zalunci yarinyar nan Ammi" Mamie tawani kalan fashe da kuka tace "shekaran jiya duk kunya kalan na Asma'u saida ta kauda baki dana gayamusu Hamadi yaje chan gidansu ya kwana nan an cika tacemini Mamie dakina bakowa amman dudda haka ban saurareta ba haka na rabasu wallahi harda kukanta rannan, ashe taji ajikinta tafiya zatayi? Mesa nama Asma'u haka? Mesa na zalunceta haka nahanata kebancewa da mijinta? Innalillahi wa innailaihi raji'un how can Asmeey just die? Kodai wasa Abba kenin?"Ahankali Ammi tace "ba'a wasa da mutuwa! Karki kara fadin kin zalunci Asmeey baki mata komi ba banda alkhairi" Mamie takama zuciyanta tace "this is my biggest regret da bazan taba mancewa ba harnima na koma ga Allah! Is this true? Ko mafarki nake? Tayaya Asmeey zata rasu? Innalillahi Wa Innailaihi Raji'un! Yarinyana da kullum nake cikin gidan nan da ita? Banda mai tayani hira sai ita? Idan bamu kitchen tare muna dinning bamu dinning nuna falo muna kallo, I've never meet any girl danake so har cikin tsokan zuciyata kaman Asma'u! Yarinya ce mai shiga rai! Mai tausayi! Ga hakuri! Ga kunya! Ga rashin riko! Ga girmama na gaba da ita! Jiya saida ta rungumeni tace Mamie wlh ina sonki Mamie….."Mamie tafashe dawani irin kuka mai tsuma zuciya, mai daci mara dadi mai sosa rai dakin nan babu wani mai lallashin wani suna ahaka sukaji karan ana bude gate Aya tafara tashi dagudu tabude kofa tafice sauran suka biyota abaya banda Gwaggo dake a sume ambulance dasuka gani yaşa kawai Aya ta duke ta zuba guiwa biyu akasa Aysha ma haka Mamie tadafa bango tana kara kallon motan. EPISODE 1️⃣0️⃣2️⃣
Fiffitowa su Abba sukayi ma'aikatan asibitin suka fito suka bude bayan ambulance din yayyin sukai wajen while Abba yawuce gate wajen aminin nasa daya basa yadin likafanin da ganyen magarya yace "sannu Allah ubangiji ya kara hakuri, bari mubada sanarwa ko masallaci in yaso amata salla bayan anyi la'asar tunda yanzu biyu da yan kai" gyadamai kai Abba yayi ahankali yawuce, su Mamie babu wanda ya iya motsawa saukowa Ya Mustapa yayi yana kallon Hamadi dake zaune just like before yana kallon Asmeey bayako kyafta idanu yasauke kanshi saiya dauki Asmeey ahankali yakalli kanninsa yamusu alamu dasu fito da Hamadi, kama Hamad sukayi suka fito dashi kafafun Hamad kaman sun kamu da shan inna as if they were paralyzed bayama iya motsasu kawai kallon Asmeey da Ya Mustapa yadauka yayi suna tafiya su Mamie da sauran matan na kallonsu is like sun kasa yarda that is Asmeey.