Uwa ko ukuba complete by m shakur - Chapter 44
Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 44: Uwa ko ukuba complete by m shakur Chapter 44. Har saida Ya Abdullahi yazo yana rikeda ita kawai saiya wuce…
3,924 words
Har saida Ya Abdullahi yazo yana rikeda ita kawai saiya wuce falo yayyin suka shigo yakalli Munir yace kuyi clearing kujerun nan waje daya dasauri Yayyin suka shiga aiki aka kawo tabarma aka shimdida kan carpet din Ya Mustapa yasauke Asmeey ahankali dan fuskanta yafito Aya ta duke awajen Aysha ma haka Munir yawani kalan fuzar da iska, Abba yashigo dakin yakalli matan yace "dan girman Allah kudena kukan nan, Mamie ke zaki shirya yarinyar nan ga matan liman nan zuwa ta taimaka kuma is not time for cry kuma Asma'u addu'a" daidai Matan Liman na sallama tana shigowa aka matsa mata Abba yace "me ake bukata Malama Khadija"? Anatse tace "ruwan dumi, bucket, gloves, turare, shi ganyan magaryan da likafani, auduga, sai ku maza zaku fita dan Allah mata kuje kusa lullubi mala'iku na zuwa irin wajen nan" ahankali Abba yasa hannu yadago Ya Aya yace "Aya haka zakiyi? Kece babba fa, wazai lallashi Aysha kalli Munir fa haba Aya! Ina imanin ki" cikin wani irin murya tace "Abba Abba kasan menake ji Innalillahi Abbaaa" tama kasa magana, Mamie ta goge fuska ahankali tace "bari na dauko" tawuce sama anatse tafito musu da hijabai mazan sukakai Gwaggo dakinta Ya Mustapa yamata allura cus she's sick, Mazan duk suka fice Hamad yakasa motsi hakan yasa aka barsa, wani kalan zama yayi gefen kofan falon kaman mahaukaci, su Mamie kowa yasaka hijabi suka matsa gefe Mamie tadauko komi Ya Musty yayi knocking tazo ta karbi glove a hannunsa takoma tana kallon Asmeey ruwan dumi aka samata ajiki sannan gently Malama Khadija takarbi hannun Asmeey luckily suka sauko Mamie ta dauke tsumman gyalen dake kirjinta sai Mamie taga gudan jini dukansu sukai shiru suna kallo hawaye yacika idanun Mamie, kafin ahankali tasa hannu ta dauka ta ijiye kan tsumman a gefe wani kalan cirema yarinyar kaya suke da ko su basa ganin jikinta balle yan falon, pads dunma aka ciro that are completely soaked da bloody yadawo so bloody ma not like a pad kowa kawai na kuka……
Anatse Hameed yaciro wayarsa ganin yayyinsa kowa yakira matansa ya sanar dasu Ayuba yakira Ayuba ya dauka, muryan Hameed duk ba dadi ahankali yace "can you bring Zee to gidanmu Yubs?" Jin muryansa yasa Ayuba yace "okay but why is ur voice like this?" Dan gyaran murya yayi yace "my brother just lost his wife" Ayuba yace "twin dinka Hamad?" Gyadamai kai yayi yace "yes" Ayuba yace "ohh my god! So sorry Allah jikanta bari naje" ok ya katse wayan, Hameed yayi dialing number Zee harya katse bata dauka ba ana biyu tadaga tace "Hello" dan lumshe idanu yayi murya chan kasa yace "how is your body?" Ahankali tace "Alhamdulillah!" Anatse yace "Asmeey tarasu Zee!" "Innalillahi wa innailaihi raji'un! Baby mene kace!" Zee tafadi hankali tashe, ijiyan zuciya yasauke yace "Ayuba will come pick you up, kibar mutanen dake gidan, kisa hijab har kasa" gyadamai kai tayi tana fashewa da kuka tace "okay" dan tana son Asmeey sosai, Asmeey itace wacce taci burin zama da ita agidan nan cus sauran matan yayin sun girmesu itada Asmeey sune yara….
Almost 30mins aka dauke matan yayyin duk sukazo, saiga Zee itama motansu yayi parking awaje da mutane ke nan karasawa Hameed yayi yabude mata kofan baya ahankali tafito idanunta sunyi jajir suka hada idanu fitowa tayi shima Ayuba yafito gida Hameed yanuna mata da idanu hakan yasa ta shiga ahankali yabita abaya har wajen kofa suka bude an gama yima Asmeey komi fuskanta akadan bari awajen tayi kyau tai haske mai kyau ga auduga a nose nata da kunne, Malama tadan kalli Hamad dake inda yake tun dazu kaman mahaukaci tace "Mijinta Hamadi Mahifinta yan uwanta mahaifiyarta kuzo kumata addu'a kafin arufeta duka" babu wanda ya iya motsi, dayake duk sun shigo, anatse Munir yatako yazo saiya duka yakalli Asmeey yayi wani huci ya dunkule hannuwansa yasake fuzar da iska murya chan kasa yace "I never knew dead could be this painful, Ya Asmeey you are the best Sister I've ever had! I'm sorry I couldn't protect you as much as I should! Allah ya gafarta miki, Allah yabaki aljanna Firdaus, Na yafemiki kome kikamin even though babu abinda kikamin sai alkhairi, Allah yahadamu a Aljannatul Firdaus!" Yan dakin sukace Ameen, yawuce yatafi yana jan rigan jikinsa yadaura kan fuska yana hawaye daya kasa daurewa. EPISODE 1️⃣0️⃣3️⃣
Baba yataho ahankali yayi shiru yana kallon Asmeey na kusan 1min sai chan yace "I just wish Allah zai bani second chance arayuwan nan sabida na gyara kura kuren dana miki Asma'u and protect you better! I've not done abubuwan daya kamata nayi as your father, I'm part of the reason why kika rasu! Asmeey ki yafemin! Kinyafemin" yayi maganan hawaye na fitowa daga idanunsa yace "Allah ya gafarta miki Asma'u! Allah yamiki Rahama!" Yatashi ahankali yawuce, Ammi takalli su Aya dake kuka tace "saiku" da kyar Aya ta tashi takama Aysha, sukaje wajen Aysha nawani irin kuka Ya Aya takalli Asmeey saita sauke kanta kasa tace "seeing you covered in white sainaji ina kunyanki! For the first time ever nai realizing I've never ever been a good sister to you Asmeey! Tsoron da baida amfani yasa I couldn't do anything about situation naki and watch you suffer over and over again, kiranki banayi sabida an hanani, gidana baki taba zuwa kin kwana ba sabida an hanani" tafashe da kukan nadama tace "I wish Allah zaiga zuciyana yaji tausayina yabani second chance dake Asmeey I will show you wat being an elder sister means, that love dakike nema from matar chan(Mom) i will give u the love of a mother Asmeey na! I am sorry I'm sorry Asmeey! Wlh I was nothing but a bad sister to you! Munir is the only good person among us! He did wat we couldn't do for you wato stood by you, Asmeey I'm sorrryyyy" Aysha ta kankame Ya Aya dan she's speaking abinda ke zuciyanta dukansu biyun were never good to Asmeey bawai sun tsaneta bane but tsoron Mom yaşa they couldn't shower little sister su da love datai deserving from them suka fita rayuwanta, tashi Ya Aya tayi tadaga Aysha data tashi da kyar tace "I'm sorry Asmeey! Allah yamiki rahama" Zee kuka take haka su Anty Asiya, Abba yakalli Hamad saiya kalli Mustapa da Hameed alamun su daukesa su kaisa, dukawa gaban Hamad Ya Mustapa yayi yace "Hussain!" Kallonsa Hamad yayi, anatse Ya Mustapa yace "time to say good time! Zokama matarka addu'a" wani kalan kallon Ya Mustapa yake kaman bai gane maganan sa ba Ya Mustapa yakamasa Hameed nasaka hannu suka kaisa wajen suka zaunar dashi, zama Hamadi yayi yana kallon Asmeey yayi shiruuu na kusan 2min, sai kawai yakama hannunsa yakai baki yasa yatsunsa abaki yana tauna kumbansa kaman wanda yasami tabin hankali yana kallonta kuma but kumbuna yakeci kowa yayi shiru masu kuka na kara sautin kuka natse Abba yace "rufeta Malama mukaita waje amata salla" ijiyan zuciya Malama tasauke Hamad yabata tausayi takai hannunta ahankali taja farin Yadin dake wuyan Asmeey zata rufe fuskanta kaman saukan aradu dawani irin zafin nama da gudu Hamad yawani sunkuci Asmeey for the first time yariketa gam ajikinsa ya rungumeta tsamtsam yace "Husnahhhhhhhh!" Yakara kankameta yana saka fuskansa gefen wuyanta ya kankameta sosai yawani fashe da kuka yace "Asma'ul Husnahhhh!" Yafashe da kuka ba kakkautawa yace "I can never let you go! Saidai abirnemu tare! Wat is me without my Husnah! Asmeey kene rayuwana! Asmeey don't leave me kiji tausayina! I will sink and sunk and lost and lostt and lostttt and everything without u, Asmeey karki bari su rabamu Asmeey" yacirota daga jikinsa yariketa a hannu yana kallonta, yakai hannunsa yazare audugan hancinta Abba yace "Hamad!" Amman kaman badashi akeba yawani shafa fuskan Asmeey yana wani irin kuka yace "ke kadai nataba so in my life! I will never ever hurt you again! I will make you happy! We will be parents again! Asmeey I've been a good husband! Give me another chance to give you my full love! Husnah dan Allah karki rasu ki barni! Come back sai we die together rana daya kinji! Asmeey mexanyi arayuwan nan babu ke eh"? Diddiga hawayensa keyi a fuskanta sosai yasake maidata jikinsa yace "I will never leave u again even now saidai akaimu tare! Husnahhhhhhhhhh" Yafashe da kuka mai tsuma rai ita kanta Malama saida tai kuka, cikin wani irin muryan kuka Hamad yace "I love you Asma'u! I love you Asma'u! I love uuuuu……" shiru yayi sabida ijiyan zuciyan dayaji a kirjinsa danya rungumeta, kyafta idanu yafara kaman mahaukaci saikuma yashiga cirota daga jikinsa ahaukace yace "Yaya tayi numfashi!" Kowa ya kallesa Abba yace "Hamadi it's okay batai numfashi ba tarasu Asmeey" dawani irin sauri yace "wallahi tayi numfashi Yayaaaa" duk sai akazo harda Munir Ya Mustapa ya duka yana kallon Asmeey, Baba ma yazo Mamie ma haka da yayyinta kowa jikinsa na rawa, anatse Ya Mustapa yace "she's not breathing! Daukomin stathoscope a mota na Faisal" Da gudu Faisal yafice Musty yakai yatsansa yadauka kan jijiyan wuyan Asmeey but he's still not feeling any pulse, daidai Faisal na shigowa yabasa karba yayi da gudu yasa a kunnensa ahankali yakai yasaka ta cikin wuyanta yadaura kan kirjinta dasauri yakalli Hamad da jikinsa ke rawa yace "Mamie abamu bargo da kayan Asmeey her heart is beating but very slow we need to put her in ICU withing 20min komu tasata finally" kai zokaji kabbara Hamad yawani fashe da kuka kowa na Allahu Akbar! Allahu Akbar! Mazan sukai waje Malama na kabbara Mamie ta karbi Asmeey daga hannun Hamad aka cire likafanin wani simple gown aka samata Hamad ya karbeta yafito gudu kawai yake akai mota da ita yashiga ya kankameta akahau sharara gudu mazan waje na kanbara kowa harda yan anguwa ana Myrna ana doguwan sumace sai asibiti.
Kafin suyi parking about 10 doctors dukansu abokan Ya Mustapa ne na jiransa da Nurses da gado da abubuwan CPR aka dauki Asmeey sai ciki su Hamad dasu Abba harda su Mamie dan kowa yabiyosu banda matan yayin suna asibiti aka zazzauna while Hamad na gaban dakin da aka shiga da ita yana leke kaman zai zare, almost an hour Doctors sukayi akan Asmeey ana ceto rayuwanta akai shocking heart nata countless time kafin luckily tafara breathing sannan aka ma jikinta abubuwa na disinfection cus ba'asan lafiya tools da aka mata evacuation dashi suke ba, all the doctors are saying this is miracle Allah ne kawai yadawo da yarinyar data daina numfashi for hours she needs to be in ICU for 24hrs, Hamad yana wajen yaga anfito da Asmeey ga oxygen a hancinta yabisu da gudu su Baba suma duk suka taso Ya Mustapa yatare Hamad yace "you can't see her now but she's alive Alhamdulillah!" Dukawa Hamad yashigayi ahankali gani yake sujjada kadai is not even enough to thank Allah for this favor dayamai but still saida yayi kowa yazo wajen ana hamdala Mamie na kuka sosai. Ya Mustapa yace "yanzu tana ICU nobody can see her or ama barsa ya shiga wajen sai bayan 24hrs an fito da ita" Dasauri Hamad yace "but how is she Yaya?" Dan ijiyan zuciya Ya Mustapa yasauke yakalli duka family nasa kowa is anxioussun basa tausayi yace "all I can say for now is she's out of danger but bansan Yaya zata tashi ba! Just pray for her! Kumata addu'a sun mata evaluation naciki without any sedative or any magani nothing nothing ko bayan an gaman babu wani magani a system nata daya nuna tashi wallahi Allah ne kawai ya dawo ma yarinyar nan da rai! Just pray for her, duk ku tafi gida ku dawo gobe" Dasauri Hamad yace "I will stay here Yaya" kawai yawuce yayi wajen ICu yazauna kujerun wajen yana kallon dakin da Asmeey ke ciki, Abba yace "are you sure zata tashi lafiya? Kafada mana gaskiya tunda baya wajen nan?" Ahankali Ya Mustapa yace "akwai high probability zata shiga state of shock! Due to fear and pain, she might also loose her mind so just pray for her"
Duk gyadamai kai sukayi yace "kuje gida za'ayita zuwa muku barka I will be here da Hamad" duk suka gyadamai kai dudda babu wani mai so yaje gidan but suka tafi. EPISODE 1️⃣0️⃣4️⃣
Wuraren 8 nadare Mom ke farkawa sabida haushin karnuka datakeji ba kakkautawa, kadan kadan take bude idanunta karnuka tagani dudda akwai duhu wajen but akwai hasken wata ga idanun karnukan dake kyalli sabida dare suna kallonta, sun zazzago da harshe, su kusan uku suna wani nishi suna dalalar da yawu dake sauka kan fuskanta da wuyanta, wani irin mugun faduwa gabanta yayi batasan sanda tawani yunkuro kaman mahaukaciya ba ta taso firrrrrrrr, jakanta datagani tadauka ta buga karnukan dashi duk suka koma baya tamike dasauri tasa hannu tana gudu tana kokarin ciro key mota kare daya yawani biyota kaman zaki yakai bakinsa kafanta ya ganna mata cizo a kafa, ihu Mom tayi ta fizge kafarta daidai tana ganin key tabude mota ta shiga tarufo da gudu ta kunna motan taja karnukan na haushi sunabin motan Mom nawani irin nishi na azaba kafanta na zugi tafito gari tawuce wani asibiti tai parking tashiga ciki da sauri, suka wanke mata kafan tabiya kudi ta dauki hanyar kano that night still kafanta ciwo yake Tahir taje ta kwanta batare datai wanka ba, tun safe ba salla, tai shiru jikinta ciwo yake sosai da kafan dayasha bandage gabanta sai faduwa yake Asmeey kawai sai fadomata arai take, deep down tanajin wani iri a kasan zuciyanta dataga yarinyar ta rasu, damuwa ce? Tadamu ne Asmeey tarasu da gaske? But ai tafi kowa son yarinyar ta mutu tuntuni mesa yanzu abin ya tsaya mata arai? Son Asmeey take? Damuwa da Asmeey tayi? Yarinyar da sanadinta Fawaz yake mata iskanci? But how could even Fawaz do this to her? Asmeey is not in the picture he should've made her his queen? How is she going to leave without him?" Shiru tayi she's really thinking about Fawaz but kuma kawai sai Asmeey takara fado mata arai, ahankali ta kwanta agado tai shiru tana kallon sama tana tuna sanda ta haifi yarinyar! Asmeey is one daughter ayaranta da starting from small take sonta! Asmeey na son mahaifiyarta! Lokacin nan she can't keep her da mai raino taje office Asmeey bata zama ga kiwuya, idan ko Mom ta taso daga aiki tazo daukanta wajen mai raino Asmeey na hangota zata fara murmushi tana dariya tana tsalle tana chap clap clap. Mom tayi da short smile da bamatasan tayiba, tacigaba da tunani, Asmeey yaran nanne that are very clingy koda yaushe tanaso taga tashige jikin Mom, kota rungume Mom, kota taba Mom, kota kama hannun Mom, itakuma tundaga kan su Aya she hates clingy children, ta tsani yara su dinga mammanne mata da sauransu, she hates it with passion saita tuna rannan da Asmeey tai lamo ajikinta danata duba kyasfi abayanta dakuma rannan da Asmeey tanata kallonta tace mata mene tace Mom I love you! Wani abu Mom taji yazo ya tsaya mata akan zuciya data rasa menene shi but abun is not making her feel happy about rasuwan Asmeey and at dsame time she's not feeling sad wani neutral feeling takeji at d same time kuma sai tunanin yarinyar take wato Asmeey! Takasa denawa kuma, Lema Mom taji akan fuskanta dakuma sauri takai hannu ta taba jin hawaye yasa taja wani tsaki. "Mtswwwwww like seriously?" Tawani tambayi kanta cike da tunkaho da girman kai, tace "Asmeey nakema kuka oh please! I'm just sad because of Fawaz ne and zaisani!" Tayi shiru still tacigaba da juye juye takasa natsuwa takasa jin dadin rayuwanta Asma'u kawai ta tsaya mata arai gari, bata taba taita tunanin Asmeey like today ba jikinta duk yayi wani la'asar, she's feeling something azuciyanta, gashi fuskanta sai jikewa yake da hawaye da ba ita keyinsu ba tana gogewa, sai ganin fuskan Asmeey takeyi, tadamu but she's angry akan mesama ta damu Asmeey is not worth tai occupying space na zuciyanta, wlh bata runtse ba duk sai zazzabi yarufeta ga kafan da kare ya cijeta dake mata radadi tawuce ta shirya komi tai wanka tafito tai checking out taje ta maida motan suka kawota airport tahau jirgi sai Bauchi.
Asibiti tafara zuwa aka duba kafanta akace ba'a kashe mata dafin da kyauba saida aka mata allura uku kafin tawuce gida tana shiga saitaga gida hatta mai gadi babu shi flat dinsu empty babu kowa, gadai komi all funitures na nan but all the children basanan, tawuce dakunan su an kwashe akwatinansu da sauran su Baba da gaske yake? Jitayi duniya yamata zafi this big house ita kadai? How? Tayaya zataji dadin gidan nan ita kadai? Tayaya zata fara rayuwa cikinsa just she?. EPISODE 1️⃣0️⃣5️⃣
Komawa gida sukayi daga asibitin jama'a sai shigowa ake harda mutanen dabama su sani ba ana musu barka ana kuma mata addu'an samun lpy, saida mutane sukadan ragu sannan Mamie tama samu natsuwan ganin Zee da kanta ke kasa dan kunyan kowa take murmushi tayi tace "Zainab" ahankali Zee tace "Mamie sannu da dawowa Allah bama Asmeey lpy" murmushi Mamie tayi tace "jiya tashin hankali yasa ba'a fara biyo dake nan ba, sannu da zuwa kinji Allah miki albarka" akunyace tace "Ameen" Asiya tace "meza'a dafa Mamie?" Anatse Mamie tace "kun manta al'adan mu duk sabuwan Amarya ke zaba" Asiya tace "hmmm wlh tashin hankali yasa na manta komi, meza'a dafa miki Zee?" Akunyace Zee tace "anything"…. Dudda bawai hankalin kowa yagama kwanciya bane but 60% na danuwan kowa yatafi saura 40% which is lafiyan Asmeey, Alhaji Mahmoud Yayan Mom yazo cus Baba yakirasa tun sace Asmeey da Mom tayi yakirata yafi a kirga wayanta baya shiga, koda ya iso Baba bai boyemai komiba har affairs nata da Fawaz Alhaji Mahmoud was shocked to bone marrow yace "yaron datake fasikanci dashi takeso ta aurama diyarta wani kalan jahilcin jahillya period ne wannan?" Alhaji Mahmoud ya tambaya kunyan Baba yakamasa yadaima kowa gaisuwa yatafi kafafunsa ba karfi, wajajen Takwas na dare Ramla da duka kanninta dawani babban manager business din Baba suka iso kano dan Baba ya aikasa yakawosu ya yanke shawara zai dawo kano da zama kusada yayansa da Asmeey saikuma bude Sana'a anan kano sannan zai dinga zuwa Bauchi yana duba sana'ansa tanan, zai sayi gida anan, Munir zai nemamai transfer zai maida yaron Egypt kawai yakarasa karatunsa anan ita daman Aysha a Abuja take aure sunadai zuwa Bauchi hutawa itada mijin, Aya ne kawai ke aure a Bauchi, he's relocating back here he will never make that mistake ever again he will protect all yaransa especially Asma'u yayi regretting actions nasa, he's going to be a better father hence forth.
Kawu aranan da daddare yama Mama saki daya Mama kaman zata haukace yace tabar gidan tadauka za'a roki Kawu wlh babu wanda yacemai anything let her serve the punishment inba hakaba bazata taba daina gulma ba, it's high time adena letting everything go in the name of zumunci, washe gari da kansa yakaita airport ta tafi shi bayau zai tafi ba. ****
Wlh at a point saida Ya Mustapa yafara jin tausayin Hamad cus the only thing dake dagasa daga gaban ICU dinnan is salla daidai da ruwa babu acikin shi abinci babu, babu abinda bai kawomai ba Hamad bayaci, yatashi suje office din nan ina baya tashi yana zaune gaban ICU nan yana kallon Asmeey ta glass dako motsi batayi connected to machines ga oxygen a hancinta. Ga wajen sanyi sabida AC wuraren 2 nadare Ya Mustapa yazo wajen rikeda wata yar bargo haka bamai girma ba da coffee mai zafi a hannunsa ijiye coffee yayi ya warware bargon yaduko ya yafama Hamad daya dago jajayen idanunsa da sauri dan baima lura da Ya Musty ba ya rufamai, maida kansa yayi kasa Ya Mustapa yazauna kusada shi yadauki coffee yabasa yace "have this" kin karba Hamad yayi ya girgizamai kai cus bamaya iya magana, Ya Mustapa strictly yace "wlh zan koreka from this hospital idan baka amsa kasha ba ha'a!" Ahankali yasa hannu ya amsa yayi shiru yana kallon roban coffee din hawaye na taruwa a idanunshi saiya fuzar da iska daga bakinsa mai zafi sai hawaye yafadomai dasauri yakai bayan hannunsa ya share yasake fuzar da iska batare dayayi magana ba kana ganinsa kasan zuciyansa cike yake da bakin ciki, hawaye suka sake zubowa ahankali Ya Musty yakai hannunsa yakama kafadan Hamad da karfi hakan yasa gently Hamad yakai dayan hannunsa yadaura kan hannun Ya Mustapa dake kafadansa yarike yana fuzar da iska yana wani kalan gyadama Ya Mustapa yakai hawaye na saukowa bakinsa nawani irin rawa yace "I…….I……lost….." saiya kasa magana sabida yanda abun ke masa ciwo sai kawai yawani irin juyowa ya rungume Ya Mustapa da kyau, is as if yanzu ne yake asalin kuka all those moment ba kuka yayi ba cikin wani irin murya yace "I lost my little……ba…..by….." yanda jikin Hamad ke rawa yana kukan kasan abun ba karamin ciwo yamai ba Ya Mustapa felt it sosai, bayansa yashiga shafawa, murya chan kasa Ya Mustapa yace "I know it's painful but ka dauke sa as kaddara daman Allah ya kaddara cikin bamai zama bane pray Allah yasa mai ceton kune, and just because you guys lost this baby doesn't mean bazaku sake samun another one ba, da izinin Allah zaku samu wani cikin soon ma dazaran Asmeey ta warke, I will make sure the best gynecologist ta dubata to makesure Asmeey is okay evacuation da suka mata baiji mata wani ciwo awani waje ba everything is going to be fine kaman ba'ayiba Hamadi".
EPISODE 1️⃣0️⃣6️⃣
Ahankali yace "but as a husband you need to learn how to be strong, Hamadi you are not that little boy autan gidanmu da zaka dinga yawan kuka kaman da noo! It's time yanzu kaima ka kula da naka responsibility din and be a man kaima ka lallashi family ka, look at you please Asmeey ta tashi ta ganka in this condition ai she will deteriorate, Hamad dole namiji yama kansa zuciyan maza and learn to be strong for family shi, the one in pain physically and mentally and emotionally is Asma'u cus ita aka dauke, aka azabtar, aka kwakulo cikin dake cikinta ba ahaka idanunta biyu duk wani azaba daka sani ta sha kai kawai you are feeling the pain a zuciyanka ne sabida soyayyan dakake mata da babynku imagine kanajin pain this much then how will Asmeey's pain be like?" Ya Mustapa yadanyi shiru yace "idan yarinyar nan ta tashi mu gabaki dayanmu bamuda wani effect on her but youuu! Hamadi taganka looking this messy lost da this kumburarrun idanu Asmeey will be completely shattered so put yourself together and give this poor girl the support dabata taba tunanin zata samu ba! Trust me second chance Allah yabama all of us to do better in protecting kanninmu yaranmu matanmu we had countless time and chance to save this girl but gani muke ai mahaifiyarta ne look at today, so we should do better, Hamad don't ever make mistake na neglecting matarka hold her close taji sauki kubar garin nan start life naku afresh, start all over and be the best husband to her cus she deserves it give this girl the love she's craving for, fill up that void in her heart, be that man da she will wish idan akwai hundred life time she wanna spend it with u kaji"? Gyadama Ya Mustapa kai yayi ahankali yanajin wani karfi Ya Mustapa yace "take your coffee dasafe zakaje gida wash up change and comeback okay" gyadamai kai yayi ahankali yakai coffee bakinsa yafara sha Ya Mustapa ya tsaresa da idanu. ***