Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 25

Uwar sadiku complete - Chapter 25

Uwar sadiku complete Chapter 25: Uwar sadiku complete Chapter 25. Ya juyo ya dawo cikin falon ta biyoshi a baya tana mita

4,475 words

Ya juyo ya dawo cikin falon ta biyoshi a baya tana mita

‘To kai kuwa Baba ka kyalesu mana, tunda yana da kudin.’

Ya zauna sannan ya bata amsa

‘Ba zan kyalesu ba! Yusufa ai danuwana ne kuma idan yaransa suka lalace dole abun ya shafi zuri’armu. Da ma wasu nutsattsun yara ne da sai ace, musamman shi Saddikun. Bari su gama a nan din tukunna muga hankalinsu.’

‘Ai shikenan, Allah ya bada sa’a.’

--------

Tunda ta dawo daga gidan Yaya Bello Abba yaga yanda take cika tana batsewa ya san bata sami yanda take so ba, don haka ya kawar da kai kamar bai ganta ba. Haka ta karasa wunin tana ta faman kunci, tunaninta ma yanda zata gayawa yaran musamman Saddiku wanda yake ta faman murna yana gayawa abokansa wadanda yanzu yawanci suna level 2 cewa shi Dubai zai tafi kuma ba zasu rigashi gama degree ba.

Sai dai shi Abban yaji dadin wannan hukuncin kawai dai yana mamakin yanda tafi shakkar Yaya Bello fiye da shi.

Bayan Sallar isha’i ne suna zaune a falon sama har yaran suna hirarsu, Yusra ce ta shigo da sallama daga falon kasa. Kujerar da take kusa da ta Abban ta zauna, bata jima da zama ba tace

‘Abba wai yaushe zamu yi jarrabawar ne? Wadda kace zamuyi don samun admission a Dubai din.’

Ya kalleta

‘Oh, Mommy bata gaya muku ba ko? Ai an fasa zuwa Dubai din, na yanke hukunci da ke da Yayan naki kuyi first degree a nan BUK in ya so idan kun gama sai ku tafi duka kasar da kuke so don yin second degree. So yanzu idan result ya fito BUK za a nema, daman kin ga ita kuka cike a JAMB form ko?’

Nan take idonta ya ciko da kwalla, Mommy wadda take zaune a kusa da shi ta tashi ta shige dakinta. Yusran ta zumburo baki

‘Abba! Haba Abba, don Allah Abba ka bari mu tafi.’

‘An gama magana Yusra, nan din ma degree zakuyi irin na can so babu wannan zancen. Amma nayi miki alkawarin idan dai kika fita da first class to in Sha Allahu ko ban biya miki ba zan nemar miki scholarahip ki je UK ma kiyi masters kinga na can ya fi daraja.’

Ta share zafafan hawayen da suka gangaro kan fuskarta, ta tashi ta shige dakinsu na sama ba tare da tace masa komai ba. Ya bi bayanta da kallo yana jijjiga kai, ya san abun da haushi amma bai ji dadin yanda tayi masa hakan ba sai dai ya san wannan din dabi’ar uwarsu ce. Ya cigaba da hirarsa da suaran yaran, sai daga baya suka tashi kowa ya tafi makwancinsa.

Tun kafin gari ya waye Yusra ta sanar da Saddiku abinda Abba yace, nan da nan ya rikice. Ya sami Mommy a dakinta ya sa mata kuka; yana tsugune a gabanta Yusra ta shigo ta zauna a gefen gado kusa da Mommy din. Ta kalli Saddikun ta kawar da kai, tace

‘Mommy don Allah ki yiwa Abban magana mana, wai me ma yasa zai canza magana bayan an gama maganar nan?’

Taja tsaki ta kawar da kai

‘Wai ubanku ne Bello yace ba zaku je Dubai din ba sai dai BUK, nima babu yanda banyi dasu ba don jiya ma da safe da na fita gidan Bellon naje. Yace wai a barku saboda tarbiyya, ko kuma tsabar bakin ciki ne oho! Tunda yaransa BUK sukeyi to dan kowa ma yayi BUK.’

Saddiku ya dubi Mommy yace

‘Wallahi Mommy na dade da sanin mutumin nan dan bakin ciki ne, ina ruwansa tunda ba da kudinsa za a je ba?’

Yusra tace

‘Uhm! Yanzu ai sai ya zuba ruwa a kasa ya sha tunda zamu zauna muyi BUK kamar yaransa. Mtsewww! Na tsani dan sa ido wallahi.’

Saddiku ya dora hannuwansa a kan gwiwar Mommy yace

‘To yanzu Mommy babu abinda zaki iya yi a kai?’ ‘Da zan iya da tuni nayi, ka san shi da bakin taurin kai.’

Ya dafa kansa da hannuwansa biyu

‘Amma gaskiya ya cuceni Mommy, duk friends dina na gama gaya musu zan tafi Dubai amma gayen nan ya sa aka fasa. Allah ya isa wallahi.’

Tace

‘Ka barni da shi, zan yi maganinsa kwanannan.’

Nan suka gama hirarrakinsu suna ta zagin Yaya Bello. Daga baya suka sanar da Mommy cewa idan hakane ta yiwa Abban magana su in ba za a kai su Dubai din ba to sun fi son Maryam Abacha University. Duk da bata san yanda zai dauki wannan zabin nasu ba amma tayi musu alkawarin zata yi iya yinta taga a kalla sun sami nan domin ko babu komai dai kada suyi Jami'ar da ‘yayan Bellon suke yi wato BUK. __

Kwanci tashi har an fara yiwa azumi lissafin abinda bai fi wata daya ba. Zuwa yanzu duk wanda ya ga Aisha ya san tana da damuwa, sai dai duk yanda ‘yan uwanta suke so su rabata da gidan Yusuf ta ki yarda. Suna nan dai ita da Amira, duk da bata rasa komai ba amma rashin ganin Abban yana damunta. Ko a hanya bata ganinsa, kusan kamar ma dai suna rayuwa a mabanbanta duniyoyi. Bata taba fasa addu’a da sadaka ba, ga addu’ar karya sihiri wadda kullum sai tayi kuma Hajiya ma sai ta yi ta aiko mata da ruwan. Tun tana lissafin kwanaki har ta gaji ta daina; abinda ta rike kawai shine Allah ya amsa addu’arta lokaci kawai ake jira. ………..

Ranar Juma’a ce kuma da yake ta kama ranar hutun aiki Zuwaira, Zainab da Aisha da Zahida gaba daya su da yaransu sun hallara a gidan Hajiya. Don haka sai kaiwa da kawowa akeyi, Farha da Abdallah wanda yake shirin zana common entrance suma suna nan a cikin dangi. Mijin Zahida ne ya bawa Hajiya kujerar Umra wadda zasu tafi cikin azumi don haka kowa murna yakeyi.

Can wajen karfe biyar na yamma lokacin kowa ya fara shirin tafiya Yaya Abubakar shima ya shigo tare da babban yaronsa Abulkhairi. Bayan sun gaisa ya dubi Anti Uwani yace

‘Anti Uwani family meeting kuke yi ne aka wareni?’

Tayi dariya tace

‘A’a wa ya isa ya wareka? Nan da ka gansu duk dadin baki suka zo su yiwa ‘yar uwata zata tafi Umra su samu ta tafi dasu ni kuwa ina kallonsu da ni zata duk a Nigeria zamu barsu.’

Yayi dariya yace

‘Ai kuwa a Nigeria zaku barsu Anti Uwani don kema da taki kujerar nazo.’

Zahida tayi caraf tace

‘Allah Yaya da gaske.’

Ya daga kai

‘In Sha Allah na ma gama biyan kudin sai su tafi tare, nima don dai ban dade da komawa sabon office bane da dani za a.’

Nan take Zahida ta zabga guda, kafin ta dire Yaya Zainab ta harareta tace

‘To sarkin bidi’a, da an yi motsi sai ki kama wani nanannen hanciki.’

Suka kyalkyale da dariya.

Nan suka hau sabuwar murna gaba daya. Hajiya ma sai tafi Anti Uwanin murna domin sai da ta matse kwalla saboda jin dadi. Haka ta dinga sakawa Abubakar albarka tana addu’a Allah ya kara masa arziki.

Haka Anti Uwani ma sai ta rasa inda zata saka ranta don murna, tayi ta sa musu albarka tana musu addu’a. Ta matsa kusa da Hajiya ta dafa ta tace

‘Yaya, Yaya Kinga dana ko? Na rasa bakin godiya Yaya. Tunda kika haihu ban taba kukan rashin haihuwa ba, kullum godewa Allah nake da bai bari na sha wahalar goyon ciki ba kika sha mana wahalar ke kadai kika haifo min ‘yaya. Gashi nan kinyi shuka sai girbar alkhairi nakeyi hankalina kwance.’

Hajiya tayi dariya tace

‘Naga alama kam to ina binki bashi kenan na wahalar nakuda.’

Suka sa dariya gaba daya

‘In Sha Allah idan naje sai nayi dawafi sannan nayi miki addu’a Yaya; yanda kuke so na Allah ya soku fiye da haka kuma Allah ya karramaku fiye da yanda kuke karramin.’

Ta fara share kwalla, Zahida ta dafa bayanta yayinda Hajiya tace

‘To ga ‘yarki nan baure sarkin kuka zata tayaki muna murna zaku saka mu kuka.’

Suka sa dariya gaba daya.

Ana idar da sallar Magriba duk suka watse suka bar Aisha da Amira wadanda sai bayan sallar isha’i zasu tafi.

A nan falon Hajiya suka ci abinci suna ta hirarsu, sai da aka idar da sallar isha’i suka tashi tafiya. Lokacin Farha tayi bacci don haka Abdallah da Anti Uwani suka rakosu farfajiyar gidan. UWAR SADDIKU

Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)

34

Babu yanda Zahra ta iya, tana ji tana gani aka fasa kai yaran Dubai karatu. Ta dai samu ta karfin tsiya ta takura Abban ya amince zai saka su a Maryam Abacha University. Yayi magana da Yaya Bello shima ya amince da haka, tunda dama abinda yake gaya masa shine ya kasance yaronka yana kwana a gida har sai ka ga yanayin fahimtarsa a rayuwa tukunna. Don haka nan da nan aka fara shirin shiga MAUN.

Sai dai kawai ta yiwa kanta alkawarin sai ta kai Yaya Bello wajen boka don ta fuskanci tunda yanzu dan uwansa ya kara kusanci da shi to lallai hukuncinta zai ci gaba da cin karo da nasa. Yanda take jin yanzu ta sami Abba a hannunta bata jin zata sake bari ya subuce mata, duk wata hanya da zata bi sai ta bi don ta tabbatar babu wanda ya sha gabanta a wajen Abba. Domin a yanzu ma gani takeyi kamar Abban yana bawa Yaya Bello wasu kudade ne. __

Tun lokacin da ta gane aikin boka yayi tasiri take kula da motsin Aisha, musamman ta sami mai aikin gidan commissioner wadda dattijuwa ce take sa mata ido tana kular mata da motsin Aishan. Tana so ta san lokacin da Aishan zata bar gidan. Zuwa yanzu kusan watanni goma an sanar da ita Aishan tana na; ta kasa gane wanne irin naci ne wannan. Miji baya kula ki amma ace ba zaki bar masa gida ba? Ta dai bata daga nan zuwa babbar Sallah ta san in Sha Allahu zuwa lokacin ko bata gaji ba to tabbas kudin hayar gidan zai kare.

Maganar boka ta tuno da ya ja layi guda biyu yace mata tafiyar Aisha da Yusuf mai tsawo ce; yanzu haka tsawon kenan kuma in Sha Allahu sai ta ga karshen wannan tafiyar. __

Kwanci tashi har azumi ya karaso; duk wani abu da Aisha take bukata na azumi haka ta dauki Amira suka je suka siya, kuma da yake Yaya Abubakar ya san halin da take ciki ranar da aka ga watan azumi sai ga sako ya aiko mata. Buhun shinkafa, dankalin bature, doya, kifi da suga haka aka kawo mata.

Ranar goma sha takwas ga watan azumi jirgin su Hajiya zai tashi tare da Aisha. Ranar sha biyar ga wata ta shirya suka tafi gidan Hajiya ita da Amira; bayan ta kwashe duk wani abu mai amfani nata saboda bata barwa kowa ajiyar gidan ba. Sai da ta kulle ko ina tayi addu’a sannan suka fito, har zata saka kwado a gate din ta tuna duk wanda ya zo yaga kwado daga waje ya san babu kowa a gidan don haka sai ta fasa saka kwadon kawai ta kulle da mukullin. Babu wanda take harka da su a kan layin don haka bata bukatar yiwa kowa sallama, ta ja motarta suka bar unguwar.

Ranar da aka dauki azumi na sha takwas da safe Aisha da kanta ta dauki Abdallah da Farha ta kaisu gidan Umma, kakarsu ta wajen Uba. Ba karamin dadi Umma taji ba don dama sun dade basu je mata kwana ba. Sukayi sallama a kan sai bayan Sallah idan ta dawo zata zo ta daukesu. Da yamma jirginsu ya tashi sai kasa mai tsarki, tana tsakiyar Hajiyanta da Anti Uwani. ____

Ranar da aka kai azumi na ashirin da biyar Baba Salamatu wato mai aikin gidan commissioner ta shigo gidan Zahra. Lokacin yara duk sun tafi masallaci sallar asham sai Jummai wadda take aiyukanta a kichin yayinda Mommy din take hutawa a falon sama. Bayan sun gaisa da Jummai ta hau saman ta kirawo Mommy.

Nan da nan ta sauko saboda ta san akwai labari tunda Sala ta zo. Bayan sun gaisa tace

‘Hajiya ina ga kanwarki dai ta bar gidan na fa.’

Ta ji dadi sosai a ranta, amma sai ta waske tace

‘Allah Sala, ko dai unguwa ta tafi.’

‘Kai gaskiya ba unguwa ta tafi ba Hajiya. Don Kinga fa tun azumi na kusan goma na daina ganin motsinta, almajiran ma da suke zama kofar gidan jiya sun tabbatar min bata nan don farkon azumi kullum da magriba sai ta basu sadaka amma yanzu an kwana biyu basu ga motsi a gidan ba.’

Ta dan yatsina fuska

‘Allah sarki, to na gode Salamatu. Dan jirani ina zuwa.’

Ta karasa tana mikewa tsaye, ta haye sama ta barta a nan. Jimawa kadan ta sauko ta zauna a inda ta tashi, ta mikawa Salamatu naira dubu tana fadin

‘Ga abun sadaka kya sayi ko dan sabulu.’

Nan da nan ta washe baki da addu’a tana ta faman godiya, tayi mata sallama ta fice. ……….

Cikin walwala suka tashi ranar idi, nan da nan aka shirya yara kowa ya sha kwallaiya. Karfe takwas saura Abba ya fito ya zuba su a mota suka wuce masallacin idi.

Kafin su dawo an sauke tuwon Sallah.

Sai da kowa yaci ya koshi sannan Mommy ta ware na makota, Jummai ta dauka suka tafi tare da Nana da Ummi. Gidaje uku suka kai, gidan commissioner ne na karshe kuma shine cikon na hudun. Bayan sun gaisa da matarsa wato Dr. Maimuna wadda ake kira Mama suka bayar da tuwon, aka juye aka basu kwanukan da kuma tukwici.

Salamatu ta dauko kwanukan ta biyosu suna ‘yar hira da Jummai kamar zata yi mata rakiya. Kasa-kasa suke yin maganar don haka Ummi da Nana da suka wuce gaba basa jinsu. Salamatu tace

‘Wai ni Jummalo amaryar gidanku auren ya mutu ne?’

Jummai tace

‘Babu mamaki fa, don na manta rabon da maigidan ma yayi rabon kwana da ita; ko ba ayi shekara ba an kusa. Ina ga sakinta yayi ko kuma dai wata matsala aka samu.’

‘Gaakiya da alama, tunda kin ga ta bar gidan fa tun farkon azumi. Yanzu haka dai auren ya kare. To ko Uwar dakinki ce ta kar auren ne?’

Ta dan zaro ido

‘Ke salamatu! To ni ban sani ba in kin shiga gidan kya tambayeta.’

Ta tabe baki

‘Au na manta ke fa ba a sukan uwar Saddiku a gabanki ko. To ku gaida gida.’

Tayi musu sallama suka wuce.

Tun daga wannan lokacin gulma ta fara yawo a unguwar cewa Abba ya saki Aisha.

Bayan da su Nana suka dawo ne kuma Malam Ali ya kwashesu da tuwon gidan Hajiya suka tafi kai mata. Mommy ta riga ta gayawa Yusra cewa idan Hajiya ta tambaya Ina abincin gidan Aisha tace tare suka yi don haka suna ajiye tuwon ma kafin a tambaya Yusra ta cewa Hajiyan

‘Tare sukayi tuwon da Mommy da Anti Aishan.’

Ta yashe baki

‘Ai gara hakan ya fi.’

Bata jin dadi sosai saboda ciwon diabetes wanda tun goman karshe ya tasar mata saboda an hanata azumi tace sai tayi, don haka ta san ba cin tuwon zata yi ba. Nan ta bawa Yusra umarni ta kaiwa Anisa ta ajiye a kicin. Ta gyara kwanciyarta ta kara muryar rediyonta yayinda su kuma yaran suka fito tsakar gida suka cigaba da hidimominsu. _

Bayan Sallah da sati daya su Aisha suka dawo Nigeria; tayi sallah kuma tayi addu’a a kan Allah ya karya wannan kulli da aka yi tsakaninta da mijinta, sannan kuma ta roki Allah ya saka mata ko ma waye yake mata wannan zaluncin kuma Allah ya toni asirin me yi mata hakan.

Tabbas ta sami natsuwa kuma ta dawo da wani sabon karsashi na zaman jiran lokacin da wannan asirin zai karye, in Sha Allahu ko zata rabu da Yusuf to ba yanzu ba sai dai idan ya dawo hayyacinsa yace ta tafi to tabbas a lokacin zata tafi.

Kwanansu biyar da dawowa Aisha tana hutawa a gidan Hajiya; an dauko su Abdallah duka ta basu tsarabarsu har sun je gidan ‘yanuwanta yawon zumunci.

Suna zaune a rumfar da take farfajiyar gidan suna hirarrakinsu, Hajiya ce a kashingide a kan tabarma yayinda Anti Uwani ke zaune a kusa da ita. Ranar laraba ce don haka Farha da Abdallah suna islamiyya. Aisha ta fito daga cikin gidan bayan tayi musu sannu da hutawa ta zauna a kusa da Anti Uwani. Bata dade da zama ba ta dubi Hajiya tace

‘Hajiya gobe ni da su Abdallah zamu je gidan Yaya Zainab, daga nan zan dauko ‘yata ranar Juma’a sai mu koma gida.’

Sai da Hajiyan ta tashi zaune sannan ta bata amsa

‘To Allah ya kaimu goben. Baku yi magana da Yayanki bane?’

‘Tun last week dai da yazo, ranar da muka je gidansa har muka taho bai dawo ba kuma da ya zo nan shekaranjiya bana nan, amma idan bai zo ba zan kirawoshi kafin mu tafi.’

Tayi gyaran murya tace

‘Uhm! To ai munyi magana ba zaki koma gidan Yusufa ba tunda ko kin koma dake da wadda bata da miji duk daya kuke. Ki zauna a nan, ba zamu kashe miki aure ba, duk lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya zo ya daukeki ku koma.’ Tuni idonta ya cicciko da kwalla tace

‘Hajiya don….’

‘Ba shawara na zauna yi dake ba, idan ke baki san ciwon kanki ba mu muna kishinki. Na gama magana babu inda zaki koma har sai Yusufa ya zo nan da kanshi sai ku tafi.’

Da kyar ta bude bakinta tace

‘To.’

Ta tashi jikihta babu kwari ta koma cikin gidan, kai tsaye dakin Anti Uwani ta wuce ta fada kan gado ta sa kuka.

Tana shigewa Anti Uwani ta dubi Hajiya tace

‘Yaya don Allah ku bar maganar nan, ku bar yarinyar nan ta koma gidanta tunda ita ta ji ta gani. Idan tana can ma sai tafi dagewa da addu’a amma yanzu idan an rike ta a nan ba zata nutsu ba tunda ta fi son can din. Idan babu hali ma ni sai na koma can na dinga tayata zaman zuwa lokacin da komai zai warware.’

‘Uwani ki kyaleta, ai ba sallamarta mukayi ba kawai don mun mata aure.’

‘Ni dai Yaya gaskiya ki barta ta koma, shima Abubakar din zai zo ya same ni.’

Bata saurari Hajiyan ba ta tashi ta bi bayan Aishan.

Kai tsaye dakinta ta wuce don ta san a nan ne zata sameta. Ta zauna a gefen gadon ta dafa bayan Aishan tace

‘Yi hakuri Shatu, Abubakar din zai zo ya same ni. Wannan abun ba komai bane face jarrabawa kuma da izinin Allah zai wuce, mu da muka je har kasa mai tsarki muka roki Allah a kan wannan lamarin ai ya kamata a ce mu barki ki zauna a dakinki zuwa lokacin da komai zai warware.’

Ta share kwallarta da zanin gadon ta mayar da kanta ta kwantar a kan cinyar Anti Uwani sannan tace

‘Gara na zauna a can ni dai, kuma ina ji a jikina wannan matsalar ta kusa zuwa karshe in Sha Allah. Kuma Anti Uwani ita matarsa so take na bar gidan kin ga yanzu idan ta bude ido taga bana nan ai ta ci nasara ko?’

‘Kada ki damu ki cigaba da shiri in Sha Allahu don ranar Juma’ar zaki koma, idan ma sun ki saurarata har gidan baffanki zan je na kirawoshi ya mayar dake don na san ba zai goyi bayan wannan aika-aikar ba.’

Haka ta dauki lokaci tana lallashinta. ………..

Washegari da yamma suna zaune sai ga Baffa, Suhail ne babban yaronsa ya kawo shi saboda shi tun tuni ya hakura da tuki saboda baya gani sosai daga nesa, don haka idan zai fita sai ya jira yara.

Bayan sun gaisa da Hajiya da Anti Uwani yace

‘Kwana biyu, kin san idona ya ki ina ta so nazo na ganku to yara duk kowa ya bazama nema babu lokaci.’

Tace

‘Babu komai Baffa, ai dama komai lokacine. Allah ya kara lafiya ya ja kwana.’

‘Amin ya Allah.’

Suna nan zaune suna hirarrakinsu Aisha da su Abdallah suka shigo, sun dawo daga gidan Anti Zainab.

Bayan ta gaida Baffa yace

‘Yanzu kika zo Shatu da magaribar nan, ba kya gudun kiyi dare a hanya? Ya maigidan naki? Ina fatan dai komai ya warware.’

Ta sunkuyar da kai tace

‘Lafiya kalau.’

Anti Uwani tace

‘Ai tunda muka dawo daga Umra dama bata tafi ba.’

‘Garin yaya? Ina fatan dai ba matsalar nan ce ba.’

Hajiya tace

‘Itace dai har yanzu babu wani cigaba, don shi yasa ma nace ta zauna a nan idan ya dawo hayyacinsa ya zo su tafi.’

Da mamaki Baffa yace

‘Ikon Allah! Ko da yake malamin da na sa yake addu’a ya gaya min abun zai iya daukar lokaci amma komai daren dadewa zai yi karshe.’

Ya kalli Aishan yace

‘Shatu da kinyi hakuri kinyi zamanki a can tunda ance min an baki mai tayaki kwana, jarrabawa ce ta ubangiji kuma idan kina can din ai sai abun ya fi saurin warwarewa.’

Ta sunkuyar da kai, Anti Uwani tace

‘To ai Yayan ce ta hanata komawa ita da Abubakar, amma ita ai tana son ta koma gidanta kuma nima na goyi da bayan hakan an dai fi karfinmu ne kawai.’

Baffa ya kalli Hajiya yace

‘Gaskiya a barta ta koma Hajiya, ai hakuri akeyi. Kuma wannan abun in Sha Allah zai warware in Sha Allah.’

Ya kalli Aisha yace

‘Ki koma Shatu kiyi zamanki, sai dai idan shine yace ki tafi to tabbas muma ba zamu barki ki zauna ba. Amma yanzu hakuri zakiyi ki zauna gaba daya mu cigaba da addu’a.’

Anti Uwani tace ‘Dama gobe tace zata koma, tunda an yi haka in Sha Allahu goben sai muje na rakasu ita da Amiran.’

Baffa ya dubi Hajiya yace

‘Ayi hakuri Hajiya in Sha Allah komai zai wuce.’

‘Um,shikenan Baffa. Dama gani nayi tana can tana zama kamar me zaman kanta shi yasa nace ta dawo gida, amma in Sha Allah goben zata koma.’

‘Yauwa.’

Aishan ta tashi ta wuce daki inda su Abdallah suke can suna wasansu.

Hajiya da Anti Uwani kuma da Baffa suka karasa hirarrakinsu, sai dab da magriba Baffa yayi musu sallama ya tafi. Yana fita Hajiya ta dubi Anti Uwani tace

‘Kun sami yanda kuke so ai sai kije ku fara shiri ke da ‘yar taki ko?’

Ta mike tana dariya tace

‘Eh, bari muje mu hada kayanmu ai zaman aure ba wasa bane kuma kowa da jarrabawarsa.’

Ta wuce daki tana dariya.

Cikin daren nan Anti Uwani ta taya Aisha suka hada kayanta. Washe gari Juma’a wajen karfe goma suka kama hanya tare da Anti Uwanin suka tsaya suka dauki Amira sannan suka wuce.

Sai da suka gama gyara gidan tsaf sannan Anti Uwani ta hau mota ta koma gidan Hajiya, ta bar Aisha da Amira.

Gaba daya Aisha ta manta basu siyo burodin karin kumallo ba gashi kuma basu da indomie a gidan. Don haka da safe wajen karfe takwas da rabi Aisha ta bawa Amira kudi ta siyo musu burodi da kwai su karya.

Tana fitowa daga gate din gidan su kuma su Yusra sun fito daga gidansu zasu tafi tahfiz don ranar aka koma hutu. Yusra ta balla mata harara, ita kuwa tayi dariya ta dagowa Rukayya hannu wadda ta mayar mata da murmushi ta daga mata hannu itama. Ta wuce ta barsu a nan Yusra tana ta faman hararar Rukayya. --------

Tun bayan da ta haifi Sumayya bata sake yin wani tsarin iyali ba, ba wai ta damu da haihuwar bane amma tabbas a halin yanzu idan ta zo ba zata Hana ba. Duk da har yanzu Aisha bata haihu ba amma dai tana so ta haifi da namiji sannan Kuma tana so ta cika gidan da ‘yaya.

Tun cikin azumi take jin jikinta babu dadi, lokacin da ya kamata tayi al’ada har ya wuce bata sha azumi ko daya ba don haka zuwa yanzu tana da yakinin ciki ne da ita. Lafiya kalau take daukar ciki ta haihu don haka ta yanke shawarar ba zata je asibiti ba har sai cikin yayi wata hudu, zuwa lokacin idan aka yi scanning za a iya gaya mata mace ne ko namiji.

Tun kafin yaran su tafi tahfiz Jummai ta zo, don haka suma tafiya ta sallami Jummai da ayyukan da zata yi mata ta haye sama ta kwanta a dakinta. Bata Dade da kwanciya ba Shima Abban yayi mata sallama ya wuce gidan Hajiya.

Yana fita bacci ya kwasheta.

Bata farka daga wannan baccin ba sai wajen Sha biyu da kwata lokacin da yara suka dawo daga tahfiz wanda shigar Sumayya da Ummi dakin shine ya farkar da ita. Bayan sun gama yi mata sannu da gida tace su sauko wajen Jummai su ci abinci sannan su kunna TV suyi kallo. Suna fita daga dakin ragowar yaran ma suka shigo sukayi mata sannu da gida sannan suka fice Yusra ce ta karshen shigowa ta sami waje a gefen gadon ta zauna, ta dubi Mommy din wadda har yanzu take kwance tace

‘Mommy kika ce matar Abba ta tafi?’

Cikin halin ko in kula tace

‘Eh, tun cikin azumi ma kuwa.’

‘To gaskiya Mommy ko dai bata tafi ba ko kuma ta dawo don gaskiya yau na wannan mara kunyar ‘yar tata ta fito daga gidan, don har hannu ma ta dagowa Rukayya.’

Ta tashi zaune ta kalli Yusra yayinda mamaki ya bayyana a fuskarta

‘Ikon Allah, to dama tana nan ko kuwa dawowa tayi?’

‘Ina ga dai Mommy azumi taje tayi a gida shine ta dawo.’

Ta jijjiga kai

‘Um! To shikenan idan kin sake ganin motsi a gidan kiyi min magana.’

Ta amsa sannan ta tashi ta fice daga dakin.

Duk da Yusra ta san cewa uwarta tana bin malamai amma bata san itace tayi abinda Abba ya daina kula Aisha ba, ba wai ta dauka bin malaman kuskure bane. Hasali ma a wajenta shine dai-dai tunda Mommy tace tsari ne ake nema musu. Lokacin da taga Abba ya daina kula Aisha tayi zaton asirin da Mommy tace musu ta yiwa Abban ne ya karye shi yasa ya manta da ita, don haka yanzu da ta ganta tsoro take ji kada ta sake yiwa Abbansu wani asirin duk da ta san Mommy a tsaye take a kansu. Yusra tana fita daga dakin ta gyara zama ta kafa tagumi; Aishan nan wai me take nufi ne? Kusan shekara guda miji baya zuwa inda kike amma kin ki fita daga rayuwarsa? Wannan din wanne irin naci ne? Gashi zuwa yanzu matan unguwar da take harka da su sun fara tambayarta labarin Aisha a kan sunji a unguwa cewa auren Aishan ya mutu; duk da dai ta gaya musu itama bata san me ake ciki ba domin da ta tambaya ma Abban yace kada ta sake yi masa maganar.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull