Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 26

Uwar sadiku complete - Chapter 26

Uwar sadiku complete Chapter 26: Uwar sadiku complete Chapter 26. Tabbas dole ta koma Doguwa; tunda dama akwai maganar Yaya Bello da take so a rabashi da…

4,467 words

Tabbas dole ta koma Doguwa; tunda dama akwai maganar Yaya Bello da take so a rabashi da Abban. Dama azumi ne ya hanata zuwa da aka sallace kuma bata da aiki sai bacci saboda cikin da take dauke da shi; ko da yake lokaci zata saka taje gidan Amina su tsara yanda za ayi don watakila ma Aminan zata iya zuwa mata Doguwan.

Haka ta karasa wunin ranar tana tunanin mafita. --------

Ita kuwa Aisha tunda ta dawo gidanta sai ta sake mayar da hankali wajen addu’a, ranakun aiki taje aiki ta dawo ranakun Asabar da Lahadi kuma sai taje islamiyya. Rashin kulata da Abban yakeyi yana damunta sai dai da yake dinkin mayafai da takeyi yana rage mata zama haka nan sai abun yayi mata sauki;kuma ta samu ana sayen mayafan sosai don haka kusan kullam cikin aiki take Amira tana tayata. ---------

Ranar Alhamis ce don haka yara babu islamiyya da yamma, tun safe ta gayawa Saddiku kada ya fitar mata da mota don zata fita da yamma amma ga mamakinta sai da ya fita; koda yake yanzu ta kula ko sauraron maganarta baya yi, yanda yayi niyya haka yake aikatawa. Malam Ali yana kawo yara daga makaranta tace ya tsaya zai kaita unguwa don haka nan ya zauna ya jirata.

Saida ta gama abinda takeyi tayi sallar la’asar sannan ta fito suka kama hanyar gidan Amina.

Duk da gidan Amina bai kai girman na Zahra ba amma shima ya tsaru, domin maigidanta ma ya fi Abba Saddiku dukiya. Cikin walwala ta sauketa ta ajiye mata lemo da cake sannan suka gaisa.

Bayan sun gaisa Aminan ta dubi Zahra wadda damuwa ta bayyana a fuskarta tace

‘Ya na ganki duk kinyi yaushi ne kawata, meye labari?’

Ta tabe baki ta kawar da kai

‘Mtseww, wallahi kin san na ce miki Aisha ta tafi gidansu ko?’

‘Eh kwarai kuwa.'

‘To wallahi yarinyar nan ta tattaro kayanta ta dawo.’

Ta rike haba tana mamaki

‘Ikon Allah, to amma dai Abban bai ce komai ba ko?’

‘Bai ma san da ita ba komai normal, kawai dai bana son zamanta a gidan ne. Nifa na fi so ace babu igiyar aurenta a wuyansa shine kawai zan huta.’

Ta dafa cinyarta

‘Ki daina damuwa, ki bawa banza ajiyarta kawai tunda dai maigidan yana hannunki. Kuma na gaya miki aikin bokan nan ba zata iya karyashi ba ko waye malaminta a garin nan.’

‘Hmm! Kin san kuma da maganar Yayansa da nace miki yana mun shisshigi, duk da dai na sa Yaron Malam yayi min aiki amma dai naga alama aikinsa bai yi ba. Ni wallahi Doguwan ma nake son zuwa don dai kawai cikin da yake jikina ne ya sa bana son zuwa.’

Ta dan zaro ido

‘Ciki uwar Saddiku? Lallai matar nan himmarki tana da yawa.’

‘To na sani ko shine namijin da nake ta nema, ai kin ga dole na tattala.’

Ta mika mata hannu suka tafa

‘Da kyau kawata. Nima wallahi ina son zuwa Doguwa saboda mijin Asiya, ya fara kawo mata wargi gara na nema mata taimako. To amma gaskiya sai an dan kara kwana biyu, in kina so idan na shirya sai muje ko kuma na tafi da sakonki mu gani ko zai karba. Sai dai shi kinsan fa baya aiki da sako sai dai kai da kake da bukata kaje da kanka, kuma gaskiya ba zan baki shawarar zuwa wajen nan da ciki ba.’

Ta dan yi tsaki

‘Wallahi nima abinda nake ji kenan, to amma bari mu gani a kwana biyu tunda ma yanzu babu wata major matsala.’

‘Gaskiya dai. Idan kuma wani abun ya taso ai sai kiyi maleji da Yaron Malam tunda shi ko ta waya zaku gama komai.’

Suka karasa hirarrakinsu sai gefin magriba sukayi sallama Zahra ta shiga mota Malam Ali wanda yake jiranta ya mayar da ita gida. Haka ta hakura ta cigaba da rainon cikinta tana fatan ya zama namiji; tunda ko babu komai yanda bokan nan yayi mata alkawarin babu wanda yake maganar Aisha. Domin har dangin Abba ma babu wanda yake maganarta kamar ma babu ita, kuma tana da yakinin kwanan nan kudin hayar gidan zai kare ta san dole Aisha ta tashi tunda babu mai biya mata.

UWAR SADDIKU

Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)

35

Duk yanda Aisha ta kai ga son boye damuwarta game da rashin ganin mijinta abun yana mata wahala; lokuta da dama ta kan kwana tana kuka. Wasu lokutan kuma idan ta yi sujuda da nufin ta roki Allah sai kuka yaci karfinta, haka zatayi mai isarta sannan ta dago daga sujudar. Tana zuwa aiki da islamiyya ga kuma cinikin mayafanta amma duk wannan bai isa ya debe mata kewar mijinta ba.

Yau din ma haka ta tashi cikin yanayi na damuwa, gashi ranar hutu ce don haka babu aiki kuma gashi da wuri Amira ta fita saboda ana bikin babbar kawarta; don haka ita kadai ce a gidan.

Duk yanda ta so ta kawar da damuwar daga ranta abun ya faskara, haka tayi ta faman aikace-aikace, har aikin ma da batayi niyyar yi ba. Sai wajen karfe biyu ta gama goge gidan, ta dauko tsumman ta fito ta wanke a faffon tsakar gida ta shanya. Har ta kama hanyar shiga gidan sai kuma ta zauna a kan dankalin da fulawoyi suke ciki; ta karewa tsakar gidan kallo kamar mai neman wani abu.

Haka kawai kuma sai ta ji kamar ita kadai ce a duniyar; ya za ayi ace tana zaune a gidan mijinta amman saboda Zahra babu mai kulata? Makota gaba daya basa harka da ita gashi mijin ma yanzu ya daina kulata. Ta manta rabon da a buga mata gate don daga ita sai Amira suke rayuwarsa, sai dai da yake duk sati sai Anti Uwani ta kawo su Abdallah. Ta share zazzafar kwallar da ta zubo a kan fuskarta. Tabbas ba zata taba yafewa Zahra ba da ma duk wani wanda yake da hannu wajen sakata a wannan halin.

A da ta yiwa kanta alkawarin zata zauna tayi jiran har mijinta ya dawo hayyacinsa amma kawo yanzu bata sani ba ko zata iya cika wannan alkawarin. Domin zaman ya fara isarta, ta fara rasa walwala gaba daya tunda komai ya daina bata farin ciki. Tabbas bata san zuwa yaushe zata iya jira ba amma dai ta fara tunanin yiwuwar ta koma gidan Hajiya kawai ko jiran ne tayi a can.

Ta share hawayenta lokacin da ta tuna la’asar ta kusa kuma bata ma yi azahar ba, ta mike cikin sanyin jiki ta shige cikin gidan domin yin sallar azahar. ___ Da yake tazarar dake tsakanin karamar Sallah da babbar Sallah babu yawa har har an fara lissafin babbar Sallah.

Kamar yanda ya saba haka yayi wa kowa kayan Sallah; baiyi maganar Aisha ba wanda wannan ya kara kwantarwa da Zahra hankali ta kara sakankancewa lallai aikin boka na Doguwa ya kama.

Sa ya siyo da rago daya wanda aka yanka Uwara Saddiku tayi yanda take so da shi cikin walwala. Cikinta ya fara girma domin ya shiga wata na hudu don haka ba da ita akayi aikin suya naman ba, masu aiki ne su uku sukayi. Sai dai kawai tana zaune daga gefe a kan tabarma tana nuna yanda take so ayi. Haka suka gama aikin suka tattare mata naman aka saka a cikin gida.

Ita kuwa Aisha tun ana i gobe Sallah suka tafi gidan Hajiya, a can aka yanka mata ragonta aka gyara aka soya. Saida suka gama yawon Sallah lokacin bayan Sallah da kwana biyar sannan suka koma. Haka rayuwa ta cigaba. __

Ranar Talata ce tana zaune a staffroom, bata da aiki a daidai lokacin don haka take ta faman duba wayarta tana kallon status; daga kan wannan ta koma kan wannan. Suna ta wucewa har tazo kan status din Anti Karima, matar Yaya Bello.

Hotuna ne na yaronta na uku wato Yusuf wanda suke kira Adil, daga kallon hotunan zaka gane bikin sauka ake yiwa Adil din wanda tabbas ta tuna kamar wancan satin ta ga hoton katin gayyatar bikin saukar a status din Yaya Saratu. Daga rubutun da Anti Karima tayi a status din ne kuma ta gane saukar hadda yayi; tayi murmushi tana kallon hoton zayyanar dake hannunsa.

Idan taga yaro ya haddace alkur’ani tabbas yana bata sha’awa kuma tana alfahari da su domin Abdallah da farha ma tana fatan su haddace izu sittin.

Ana cikin bikin Sallah ta gani a status din Anti Karima an kawo kayan auren Asma’u yayar Adil din, ta manta dalilin da ya hanata koda waya ne ta yiwa Anti Karima tayi mata barka. Lallai yanzu ya kamata taje gidan nan don ba zata ma iya tuna rabonta da su ba, ko babu komai dai ya kamata taje mata murnar auren Asma’u da ake shirin yi kuma da saukar Adil din. Nan take ta yanke shawarar ranar asabar idan ta tashi daga islamiyya zata je gidan tunda dama karfe sha daya suke tashi kuma ranar Amira tana da lecture har karfe daya; don haka daga islamiyya sai ta wuce gidan Yaya Bello daga can ta tsaya ta gaida Hajiya sai ta wuce ta dauko Amira.

Ta dan gatsina fuska a lokacin da tayi tunanin zuwa gidan Hajiya; bata son zuwa gidan Hajiya saboda yanda Hajiyan takeyi mata wanda ya sa Anisa ma da take gidan bata ganin girmanta don ko gaisheta bata yi. Ta tuno zuwanta na karshe gidan wanda bayan ta gaisa da Hajiyan haka Hajiyan ta tashi ta shige daki ta barta, itama Anisa da mai aikin Hajiya suka shige kicin suka barta ita kadai a falon Hajiya. Saida ta gaji da zama sannan ta taso ta fito kuma babu yanda bata yi ba Anisan ta kirawo mata Hajiyan tayi mata sallama taki; sai ce mata kawai tayi tayi bacci kuma idan tana bacci ba a tashinta. Haka ta hakura ta tafi tana mamakin dalilin da yasa suke mata wannan kiyayyar. Kusan zata iya cewa kaf ‘yan gidan su Abba Yaya Bello ne kawai da iyalansa suke zama da ita yanda ya kamata.

Ta kawar da tunanin ta cigaba da latsa wayar tana hakurkurtar da zuciyarta a kan haka zata hakura taje gidan Hajiyan, in ya so ta dauki dan rakiya daga gidan Yaya Bello watakila abun yayi mata sauki. ……….

Tun ranar Juma’a ta tanadin alkur’ani izu sittin da turaren mai kamshi da agogon hannu wanda ta saka a leda a kan zata kaiwa Adil. Da tayi tunanin zata dafawa Hajiya funkason alkama da farfaesun kifi to amma gaskiya bata son ta sha wahala taje su lalatar da abincin basu ci ba don haka ta yanke shawara gara ta sayawa Hajiyan tuffa da kayan shayi irin wanda ya dace da masu ciwon suga ta kai mata.

Ranar asabar suna tashi daga islamiyya ta wuce gidan Yaya Bello.

Tana tsayar da motarta a bakin gate din gidan yaran gidan suna dawowa daga tahafiz; tun daga nan yaran suka fara gaisheta, bayan ta amsa suka nufi cikin gidan a tare. Suna tafe tana yiwa Adil murnar haddar da yayi.

Cikin girmamawa Anti Karima ta karbeta, Muhammad da Asma’u wadanda basu je tahfiz ba suka gaisheta sannan Asma’u ta kawo ruwa da lemo. Suka zauna ita da Anti Karima a falo sunata hirar yaushe gamo, daga baya kuma aka janyo akwatunan kayan auren Asma’u aka bude mata ta gani tana ta sa albarka.

Anti Karima ta dubeta tana daga mata kayan tace

‘Kinga yanzu saura wata uku da kwana goma bikin.’

Da murmushinta tace

‘Allah ya nuna mana, kice abun ma ya matso.’

Jimawa kadan Aishan ta dubi Anti Karima tace

‘Anti to me ake shiri? Akwai wani anko da za ayi don gara na karbi nawa kafin na tafi.’

Ta kama haba ta bude baki

‘Tab, ai Abbansu baya son anko babu ma wanda ya isa yayi wannan zance. Kina ji event center ma yace ba za aje ba wai a nan gidan zamuyi gaba dayan bikin. Har yanzu faman lallabarsa nake yana burtsewa; tunda kinga gidan ai ina muka ga filin yin biki idan banda rigimarsa.’

‘Gaskiya dai Baban su Muhammad da ya bari munje event center din. Amma fa kin san duk abun suna ne ko a nan din aka yi kalau za a gama shike nan, ai albarkar abun ake nema.’

‘Hakane.’

Suka cigaba da hirarrakinsu.

Sai wajen sha biyu da kwata sannan Aisha ta mike zata tafi. Ta nemi wanda zai rakata gidan Hajiya aka ce Asma’u ta shirya suje, don haka ta dan zauna tana jiran Asma’u ta kintsa.

--------

Kamar yanda ya saba duk ranar da babu aiki da safe yake tafiya gidan Hajiya, idan rana tayi sai ya wuce gidan Yaya Bello inda a can zai ci abincin rana. Ba zai koma gidansa ba har sai anyi sallar Magriba. Duk yanda Zahra taso ya daina zuwa gidan Yaya Bello ko kuma a kalla idan ya je ya daina dadewa abun yaci tura. Tunda yace mata a can yake cin abincin rana ta fara zargin wani abun suke barbada masa a abincin shi yasa ya kasa rabuwa da su.

Sau biyu tana turawa Yaron Malam kudi yayi mata aikin da zai raba Abban da Yaya Bello amma ko sauyi bata gani ba. Daga karshe Yaron Malam din ya sanar da ita aikin ba zai yiwu ba domin mutumin da ta bayar da bayaninsa idan sun tashi zasuyi aiki ko ganinsa basa iya yi. Sosai abun ya bata mata rai amma babu yanda zatayi tunda tana tsoron zuwa Doguwa da cikin jikinta; musamman da yake sau biyu tana yin scanning a gurare daban-daban kuma duka biyun sun tabbatar mata namiji take dauke da shi; bata son wani abu ya sameshi.

Haka ta hakura ta daga musu kafa, amma tayi alkawarin idan ta haihu da zarar tayi arba’in zata je Doguwa duk sai tayi maganinsu ko waye malamin Yaya Bello bai isa ya mallake mata miji ba.

Yau din ma bayan ya gama cin abincin safe tana kallonsa ya shiryo ya fito, tun safe take masa korafin bata jin dadi da nufin ya fasa fitar amma bai ma kulata ba. Kawai sai ya sanar da ita idan da matsala tayi masa waya sai ya dawo. Da kyar ta bude baki tayi masa a dawo lafiya shi kuwa ya amsa ya fice ya kama hanya lokacin wajen karfe goma.

Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce don ya san a yanzu Yaya Bello yana can, domin tunda diabetes dinta ya tashi da azumi da kanshi yake zuwa yana bata abincin safe da na dare. Sosai suke lallabata saboda bayan diabetes din kuma to tana yi musu rikici irin na tsufa domin ko abincin ma idan ta ga dama sai tace sai taci abinda likita ya hanata ci. Haka dai suke ta fama.

Lokacin da Abban ya shiga gidan Hajiya ta gama cin abincinta, suna zaune dai a falo suna hira ita da Yaya Bello. Nan ya zauna suka cigaba da hirarrakinsu gaba daya.

Can zuwa shabiyu lokacin har Hajiya ta fara gyangyadi a falon, sukayi mata sallama domin ta samu tayi baccinta. Suna fita suka nufi gidan Yaya Bello a motar Abba tunda shi Yaya Bello bai zo da mota ba. __

Lokacin da Yaya Bello da Abban Saddiku suke shiga gidan Yaya Bellon yayi daidai da lokacin da Aisha suke fitowa tare da Asma’u yayinda Anti Zalihan take biye dasu tana yiwa Aisha sallama da godiya.

Kana shiga gate din gidan dan karamin farfajiya ne inda daga nan zaka shiga wata kofar mai irin siririn soron nan sannan ka fada tsakar gidan. Kasancewar kofar falon baki wanda take a farfajiyar farko a rufe take sai Yaya Bello ya wuce gaba suka nufi cikin gidan ta wannan soron.

Suna daf da kaiwa karshen soron Aisha ta sako kai Asma’u na biye da ita. Ganin Yaya Bello ta tsaya ta fara kokarin kaucewa ta bashi hanya ya shige, tana shirin rage tsawo ta gaisheshi ta hango Abban Sadik a bayansa.

Take ta manta da gaisuwar da take niyyar yi ta bi shi da kallo baki a bude. Ta kusan shekara biyu rabon da ta ganshi kamar haka, ya dan yi kiba amma kuma ya kara tsufa. Yanda take binsa da kallo shima haka yake binta da kallon.

Yaya Bello ne ya katse musu kallon yace

‘A’a! Aisha. Sannu da zuwa.’

Ta kauda kanta ta rage tsawo ta gaishe da Yaya Bello. Bayan ya amsa ya juya bayansa ya dubi Abba yace

‘To kai kaga amarya ta biyoka fa.’

Kamar bai ji abinda yace ba ya bude baki a hankali har yanzu idonsa a kan Aishan cike da tsananin mamaki yace

‘Aisha! Daman nan kika dawo?’

Ta kawar da kai ta dan share kwallar da ta fito daga idonta, a dai-dai lokacin Asma’u ta koma cikin tsakar gidan ta zauna a kan kujera domin jiransu.

Cike da mamaki Yaya Bello ya fara binsu da kallo daya bayan daya yana kokarin ya fahimci abinda yake faruwa. Ya gyara tsayuwa yace

‘A’a! Me yake faruwa ne? Me yake faruwa ne? Ya zaka ce nan ta dawo bayan da na fita ma bata zo ba.’

Kafin ya bashi amsa ya kama hannunsa ya dubi Aishan yana nuna mata cikin gidan yana fadin

‘Mu koma naji abinda yake faruwa, kunata kallon juna kamar wasu baki.’

Ta bude baki zata yi magana yayinda Yaya Bello ya janyo Abban suka nufi cikin, bata da wani zabi don haka ta wuce gaba suka bita a baya domin idan ta tsaya wajen ma ba zai isa su wuce ba.

A falon suka ci karo da Anti Zalihan ta mike tsaye tana fadin

‘A’a, kin tsintosu Aisha.’

Babu wanda ya amsa mata don haka ta matsa Abban Sadik da Yaya Bello suka zauna a kujerar zaman mutum uku yayinda ita da Aishan suka zauna a kujerun zaman mutum daya. Yaya Bello ya dubi Aishan yace ‘Aisha me yake faruwa ne, kamar mamakin ganin juna kukeyi ke har kina share kwalla. Me yake faruwa ne?’

Bata sami bakin bayar da amsa ba saboda hawayen da take ta faman tokarewa ne ya kwace ya wanke mata fuska gaba daya, ta sa hannu ta fara share hawayen.

Cikin tsananin damuwa da mamaki Yaya Bello ya gyara zama yana dubansu daga wannan ya dubi wannan. Yace

‘Yusufa wai me yake faruwa ne? Kayi min bayani.’

Ya sa hannu ya goge fuskarsa yana muttsike ido kamar wanda ya tashi daga bacci, a hankali ya bude baki yace

‘Yaya babu komai fa, na dai dade ban ga Aishan bane kawai.’

Ya dubi Aishan wadda ta sunkuyar da kai tana share hawaye yace

‘Ikon Allah! To yaji tayi ko rabuwa kuka yi amma baku sanar ba.’

Gaba daya su suka yi shiru kowa yana ta faman zare ido, itama Anti Zulaiha sai kallonsu take tana mamaki don bata ma fahimci kan zancen ba. Yaya Bello ya katse shirun ya dubi Aishan yace

‘Aisha me yake faruwa ne? Ya sake ki ne ko me ya faru?’

Ta share hawaye tace

‘A’a bai sake ni ba, ya dai kusa shekara biyu bai zo gidan da nake ba shi yasa muka dade bamu hadu ba.’

Yaya Bello ya sake shiga rudani, ya kalli Aishan ya kalli Yusuf din. Aisha ta sake share hawaye, ta bashi labarin yanda abubuwan suka faru. Binta kawai yake da kallo yana mamaki. Ya dubi Abban Sadik din yace

‘Yusufa kai kuma kana auren mace kawai sai baka ganta ba kuma ba zaka nemeta ba?’

Ya share gumi yace

‘Wallahi Yaya ni kaina har yanzu ina mamaki, don ni sai yanzu ma fa da na ganta na tuna da ita. Na kasa gane me yake faruwa ma gaba daya wallahi.’

‘Ikon Allah! To ni kaina ma ban fahimceku ba. Amma Yusufa ya za ayi ace kai da matarka kuma ga gidan da take kusa da daya gidan amma kace wai ka kusa shekara baku hadu ba. Wannan din wacce irin rayuwa ce?’

‘Wallahi Yaya nima sai yanzun nake mamaki, kamar ma gaba daya mantawa nayi da wani bangaren na rayuwata. Gaba daya ma na kasa ganewa.’

Sukayi shiru kowa da abinda yake ransa. Jimawa kadan Anti Karima tayi gyaran murya tace

‘Gaskiya Abban Muhammad ni ina ga ka kirawo Malam Sama’ila tunda yau asabar watakila yana gida, domin wannan abun yayi kama da aljannu ko shaidanu. Gara ka gane kan komai a dauki mataki kafin su bar nan su sake komawa ruwa.’

Yace

‘Hakane gaskiya, bari nayi masa waya na san yanzu zai shigo in sha Allah.’

Ya dauko waya ya kirawoshi, yace masa yana bakin titi zai fita amma yanzu zai dawo.

Sukayi shiru suna jiransa.

Jimawa kadan Yaya Bello ya kasa hakuri ya kirawo Muhammad yace masa ya fita waje da zarar Malam Sama’ila ya zo su shigo tare. Yana fitowa suka hadu suka shigo ya nuna masa falon.

Bayan sun gaisa Abban Muhammad yayi masa bayanin abinda yake faruwa, ya rufe da

‘To Malam Sama’ila abun ne naga kamar na mutanen boye, to shine nace gara ka zo muji ko da akwai abinda za a taimaka da shi.’

Yayi shiru yana jijjiga kai, jimawa kadan yace

‘To gaskiya Alhaji wannan bayanin da kayi min ya fi kama da sihiri, Allah ne ma ya takaita abun. Watakila kai din kana da wata kariya ko kuma gidan naka na da makari shi yasa da suka shigo suka ga juna. Tunda idan ban manta ba lokacin da na yiwa Asma’u rukiyya na baka taimako kala-kala naka da na yaran.’

‘Hakane. To yanzu ya za ayi Malam? Na iya barinsu su koma gidan don ni gaskiya ina tsoron su koma su sake mantawa.’

Suka sake yin shiru na dan lokaci.

Jimawa kadan Malam Sama’ila yace

‘Akwai Malam Audurahmanu, kai ka san shi ai wanda yake zuwa mana limancin sallar dare da azumi. Sai dai shi a unguwar koki yake, shine ya kware a aikin sihiri ni dai ka barni da rukiyya idan aljani ya bayyana a jikin mutum.’

‘To ai sai mu tashi muje in dai zamu sameshi yanzun.’

‘Zamu sameshi tunda ko baya gida makarantarsu kusa da gidan ne’

Yaya Bello ya dubi Abban Sadik yace

‘To kaji ai sai ka tashi muje ko?’

Cikin sanyin murya ya amsa ‘To Yaya, yanda kace.’

Gaba daya suka mike suka fito, har sun kusan fita Yaya Bello ya koma yacewa Anti Karima

‘Ina ga ki dauko mayafi muje saboda ita Aisha din kya zauna da ita.’

Don haka ta saka hijabinta suka shiga motar Abban Sadik Yaya Bello ya tuka suka kama hanya.

A makaranta suka sami Malam Audurahmanu, babu dalibai don an tashi ‘yan islamiyya don haka ya nuna musu aji suka zauna.

Bayan Malam Sama’ila yayi masa bayani ya tambayi Aisha itama tayi nata bayanin, shi kuwa Abban Sadik da aka tambayeshi ma kasa bayanin yayi; abinda yake tunawa kawai shine ya dade bai ga Aishan ba kuma ya san bai saketa ba. Malam Audurahmanu ya dubi Yaya Bello yace

‘Ina zuwa.’

Ya fita daga ajin.

Jimawa kadan ya dawo dauke da robar ruwa karama guda biyu da kuma wani mai a 'yar roba kamar ta Robb. Ya mikawa Aisha robar ruwan guda daya yace ta shanye, ta kalli Anti Karima ta daga mata kai don haka tayi Bismillah ta shanye. Ya mikawa Abban Sadik din dayan yace shima ya shanye, ba tare da wani musu ba ya shanye.

Ya dubi Yaya Bello yace

‘Ayoyin karya sihiri ne, sune matakin farko za a sha na kwana bakwai.’

Aisha tace

‘Ni dama tunda abun ya faru kullum sai na tofa ayoyin na sha sai dai a ruwan fanfo ne ba na zamzam ba.’

Malam yace

‘Ma Sha Allahu to shi ya sa ma abun baiyi wani tasiri sosai a kanki ba, karanta min ayoyin naji.’

Nan take ta karanta masa ayoyin ba tare da wani kuskure ba.

Yana murmushi yace

‘Ma sha Allah, in dai kika rike wannan babu wani sihiri da zai yi tasiri a kanki, ko yayi ma na dan lokaci ne tunda Allah yana jarraba bawa da abinda ya so.’

Ya mikawa Abban Sadik ‘yar robar hannunsa yace ka lakaci wannan ka shafa a kanka. Ya karbi robar ya rike amma ya kasa ko budewa, jujjuyata kawai yakeyi yana kallonta. Kafin yace wani abu Yaya Bello ya karba ya bude, ya lakaci man da yake ciki ya muttsike a hannunsa ya cire hular Abban Sadik din ya kama kan nasa ya shafe masa man tas. Nan da nan idonsa yayi ja ya fara neman birkicewa, Malam Sama’ila da yake gefensa ya dafe shi ya fara karatu.

Ba a fi minti biyar ba yayi atishawa ya dawo dai-dai. Ya goge gumin da yake fuskarsa, Yaya Bello ya mika masa hularsa ya saka yana ta faman satar kallon Aisha wadda suke zaune a gefe daya ita da Anti Karima.

Malam Audurahmanu ya mike yana fadin

‘Bismillah Malam Bello.’

Ya bi bayansa suka fice.

Sai da suka shiga ofishinsa suka zauna sannan Malam yayi gyaran murya ya dubeshi yace

‘Wato Malam Bello sihiri ne aka yiwa dan uwanka don a rabashi da mai dakinsa, aljanine aka saka masa wanda gaba daya yake hanashi tunawa da ita. Saboda yanda aljanine yake tare da shi kuma duk ma wanda ya so ya tuna masa ita to ba zai yarda su hadu ba. Amma Allah ya kawo makarin abun tunda ka ga wannanan man da ka shafa masa a kansa kamshin mutuwa yayiwa aljanin don haka ba zai sake dawowa ba. Sai dai da yake yana da wata matar kuma ga maganganun da ta gayawa wannan din za a iya cewa itace tayi wannan aika-aikar; duk da dai bai halatta a zargeta ba domin shaidanu makaryata ne. Amma yanzu idan kun tafi to a barshi ya cigaba da kwana gidan ita waccan din, zan bayar da ruwan tofi da zai dinga sha tsawon kwana bakwai kuma da addu’oi. Sannan a samu ko shi ko wani a dinga karanta bakara a dakin da yake kwana. In Sha Allah bayan kwana bakwai din sai ku dawo sannan sai ya koma rabon kwana kamar da.’

Yaya Bello ya jijjiga kai yana mamakin yanda Zahra zata yi haka, tunda yake bai taba jin matar da Hajiya take yabo kamar ita ba, don ko matarsa da ita aka fara aurowa Hajiya bata sonta kamar yanda take son Zahra.

Nan suka koma ajin, bayan sun koma ya sake yi musu bayani gaba daya kuma ya gaya musu kada su zargi kowa balle a sami wata sabuwar fitna don shaidanu haka suke so.

Ya basu umarni suje su cigaba da addu’a komai zai dawo dai-dai, ya sake bawa Aisha hakuri sannan sukayi sallama suka tafi. Sai da suka fito sannan Aisha ta tuna da Amira, take ta buga mata waya tace ta zauna ko a library ne ta jirata nan da awa daya zata karaso.

Gidan Yaya Bellon suka koma inda sai da sukayi Sallah suka ci abinci sannan Aisha tayi musu sallama ta ja motarta ta tafi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull