Uwar sadiku complete - Chapter 28
Uwar sadiku complete Chapter 28: Uwar sadiku complete Chapter 28. ‘Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki damu…
4,497 words
‘Allah ne ya kashe kayansa kinga kuwa sai muce Allah ya kawo masu albarka. Kar ki damu Hajiya wannan ba wani bakin abu bane a wajen mace mai haihuwa tunda ma ke kina da wasu yaran wannan ba zai zama matsala ba.’
Nan ya barta da ma’aikatan suna gyarata ya fito waje.
Bayan an gama shiryata aka fito da ita aka bata daki inda likita yace zasu riketa zuwa gobe saboda jininta ya dan hau. Aka nade gawar yaron aka bawa Abba. Bayan ya tabbatar an bata daki sun zauna ita da Yaya Murja ya sanar da ita zai je ya kaiwa Yaya Bello gawar ayi mata sutura sannan ya karbo musu abinci a gida.
Abba yana fita Yaya Murja ta matsa kusa da Zahra tace
‘Kiyi hakuri ki share wannan hawayen, in da rabo sai kiga kin haifi wani amma kina ta kuka sai kace karamar yarinya.’
Cikin shesshekar kuka tace
‘Yaya ya za ayi yaron da bai fi sati biyu ba aka duba aka tabbatar min kalau yake kuma yanzu ace ya mutu?’
Da mamaki Yaya Murja take kallonta tace
‘Hmm! Saboda ke baki taba yin bari bane shi yasa kike cewa haka. Ya za ayi ba zai mutu ba tunda rayuwarsa tana hannun Allah. Ki kwantar da hankalinki wannan ba wani abu bane, ke da kike da yara shida ai sai dai kawai ki cigaba da godiya ga Allah da fatan Allah ya sa wahala ta zama kaffara.’
Ta janyo flask din da tazo da shi ta had a mata shayi mai kauri ta sakata a gaba saida ta shanye. Jimawa kadan likita ya shigo yayi mata allura, kafin ya fita bacci ya fara fuzgarta don haka ta hakura ta kwanta ba da son ranta ba. Yaya Murja ta zauna a kan kujera tana jiran zuwan Suwaiba wadda tace zata biya ta taho da Rahma saboda jinya.
UWAR SADDIKU
Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)
37
Tun kafin Suwaiba ta fito daga gida ta kirawo Rahama, sai dai bata dauka ba. Don haka ta kirawo Innar su Rahman don ta sanar da ita zata zo sai ta dauki Rahma su wuce.
Rahama tana daki a kwance tana kallon wayarta da taga Suwaiba ce taki dauka, haka kawai jikinta ya bata gidan Zahra zasu ce taje ita kuma tayi alkawarin ba zata sake komawa wannan gidan ba.
Tana jiyo Inna ta fara magana da Suwaiba a waya tayi tsalle ta fito tsakar gidan, bayan Inna ta ajiye waya tace
‘Inna na gaya miki ba zan sake zuwa gidan nan ba, wallahi duk wani mutunci da kika ga tana yi idan mutum bai taba yaranta bane. Ni dai gaskiya bana son zuwa gidan nan.’
Inna ta jijjiga kai
‘Hakuri zakiyi, ko iya asibitin ne kije ki zauna da ita in ya so da an sallameta sai ki dawo. Tunda dai kin ga suna kallonki kina yiwa yayyenki irin wannan hidimar, hakuri zakiyi, yanzu Suwaiban zata karaso.’
Haka Inna ta sakata a gaba tana bata baki, ba tare da bata lokaci ba Suwaiba ta zo suka wuce asibitin.
Nan suka zauna a asibitin har magriba. Ana idar da sallar Magriba Abban ya shigo, ya kawo musu abincin dare sannan kuma ya tahowa Zahra da wayarta wadda ta bari a gida lokacin da suka taho asibiti. Suna gaisawa Yaya Murja da Suwaiba sukayi musu sallama suka tafi. Jimawa kadan Abba ya yiwa Rahma sallama ya tafi ya barta da Zahra wadda take ta bacci saboda alluran da ta sha.
Sai da yayi magana da likita kafin ya bar asibitin inda likitan ya tabbatar masa zasu sallameta da zarar blood pressure dinta ya dawo dai-dai kuma ta daina ciwon kai wanda take ta korafinsa tun bayan da ta haihu. …………
Tun a daren Abba ya sanar da Aisha, tayi maganar abincin safe ya sanar da ita Yaya Murja tace za a kai musu don haka ta bari idan yamma tayi sai ta dafa musu abincin dare suje tare su dubota; idan ba a sallameta ba zuwa lokacin.
Ta sanar da mutanen gidansu wanda kafin wani lokaci Hajiyanta ta yiwa Hajiyan Abban waya ta jajanta mata sannan kuma suka sa cewa gobe zasu je asibitin su dubota.
Suma su Yusra tunda Abban ya dawo gida suke ta tambayar labarin Mommy, don haka yayi musu alkawarin gobe ko bai je da su duka ba zai je da wasunsu idan dai ba a sallameta ba. ----------
Sai wajen karfe biyu Abba ya kirawo Aisha ya sanar da ita ta dafa wa Zahra abinci zai zo da anyi sallar la’asar su wuce asibiti. Nan da nan ta fada kicin ta dafa farfesun kaza sannan ta dafa shinkafa ta dafa macaroni tayi miyar dage-dage wadda ta sha nama sannan ta hada coleslaw. Ta sami flask ta cika musu da ruwan zafi saboda shan shayi.
Bayan ya fito daga office ne ya kirawo Yusra ya sanar da ita cewa su shirya ita da kannenta in ya dawo zasu je asibiti, tunda ranar Juma’a ce babu islamiyya. Nan da nan Jummai ta tayasu suka shirya ta tambayesu ko za a dafa wani abun Yusran tace Abba yace Anti Murja ce take kaiwa. ---------
Sai da ya tsaya a wajen Aisha ya ci abinci sannan Aisha ta shirya cikin abayarta mai kyau ta rufe kanta da mayafi mai kalar olive green ta dauki 'yar jakarta sannan suka fito. Suna fitowa ta zare mukullan motar daga aljihunsa tana dariya tana fadin
‘Ka gaji da yawa, bari na tukamu.’
Yayi dariya yace
‘Za dai ayi min wayo a more min mota.’
Itama tayi da dariya.
Suka karaso gaban motar ya bude booth yana fadin
‘Zuba abincin a nan da yara zamu je sai su zauna bayan motar.’
Suka zuba abincin ya zauna a gaban motar ta ja suka fito daga gidan.
Tayi parking a kofar gidan Zahra, Abban ya fita ya shiga don ya fito da yaran.
Gaba daya su sun riga sun shirya don haka yana shiga suka fito yana dauke da Sumayya yayinda yake rike da hannun Ummi ragowar suna biye da shi. Sai da Yusra tayi turus da ta hango Aisha a motar Abba tana tukawa, ya karaso da su duk suka shiga bayan motar.
Rukayya ce ta fara gaida Aisha wadda ta juya tana amsawa, suka suka gaisheta har Yusra saboda Abban ya riga ya shiga motar. Ta ja motar suka kama hanya. Sai da suka kamo hanya sosai yacewa Aishan idan sun zo kan tin gidan gwamna ta tsaya zasu sayi fruit. Don haka suna zuwa ‘yar kasuwar nan da take kusa da Yahuza suya ta tsaya; da hannu ya yafito mai fruit din wanda ya taho da guda. Yayi masa lissafin lemon, ayaba da kuma apple na kusan dubu bakwai yace a saka a leda kuma ya taho da POS machine ya karbi kudin.
Nan da nan mutumin ya juya da hanzari ya dauki leda ya fara cikawa yayinda shi kuma Abban ya gyara zama ya fara laluben aljihunsa don dauko wallet dinsa wadda ATM card dinsa suke ciki. Sai dai ga mamakinsa babu komai a cikin aljihun; ya dan yi tunani yana rike da aljihun ya kalli Aisha wadda take kallonsa yace
‘Kin san na baro wallet din a falo!’
Tayi murmushi tana dubansa, cikin rada tace
‘Kanata santin shinkafata.’
Yayi dariya yayinda ta mika hannu inda kafarsa take ta dauko jakarta, ta zaro ATM card dinta ta mikawa Abban a daidai lokacin da mai fruits din ya karaso dauke da manyan ledodi guda biyu.
Abban ya fita ya karbi kayan ya saka a booth yayi amfani da katin Aisha ya biya kudin sannan ya dawo ya zauna, ta ja motar suka wuce.
Abban ne a kan gaba har suka hau benen da dakin da aka kwantar da Zahran yake, suna biye da shi sai da aka zo bakin kofa saboda ya san Rahma tana ciki ya ja baya yace duka su shige. Ummi ce ta bude kofar suka shige gaba daya.
Rahma da Yaya Murja suna zaune a kan tabarma daga gefe yayinda ita kuma take gefe guda yayinda ita kuma Zahran take kwance a kan gadon tana danna waya.
A hankali ta tashi ta gyara zamanta yayinda suka karasa suka tsattsaya a gefen gadon, ta dan muskuta Yusra ta dauki Sumayya ta dora mata a gefen gadon. Aisha ta karasa shiga dakin da sallama Abban yana biye da ita. Ta wuce ta zauna can daga kusa da Yaya Murja yayinda shi kuma Abban ya ja kujerar da take ajiye daga daya gefen ya zauna.
Ya gaida Yaya Murja da Rahma yayi musu ya mai jiki sannan ya mike ya karasa wajen Zahran ya tsaya a bayan yaran.
Itama Aishan suka gaisa da Rahma da Yaya Murja tayi musu yaai jiki, ta mikawa Yaya Murja kwandunan da suka zo dasu tayi musu bayani. Suka dan cigaba da hira Yaya Murja tana tamabayarta mutanen gidansu.
Bayan ya gama tambayar Zahra jikin nata ya juya yayi wa Yaya Murja sallama ya dubi Aisha yace
’15 minutes, ina jiranku a mota.’
Ya mika mata hannu kamar mai karbar wani abu, ta zura hannu a jakarta ta dauko mukullin motar ta saka masa a hannunsa ya juya ya fice bayan yayi wa su Yaya Murja sallama.
Bayan ya fita Aisha ta mike ta matsa kusa da gadon suka gaisa da Zahran sannan ta yi mata jaje tare da ya jiki. Da kyar take amsa mata tana ta faman harararta don haka itama ba tare da bata lokaci ba ta koma ta zauna.
Suna hira jefi-jefi da su Rahma tana kula da agogon wayarta, minti goma sha biyar suna cika ta yiwa Yaya Murja sallama ta dubi yaran tace
‘Rukayya ku zo muje 15 minutes din yayi kada mu bar Abba yana jira’
Ta fice.
Jimawa kadan yaran suka fice bayan Yaya Murja ta tasa keyarsu. Su Zahra basu dade da fita ba Amina ta shigo, bayan sun gaisa Yaya Murja tayi musu sallama ta tashi yayinda Rahma ta bita don tayi mata rakiya.
Amina ta dubeta tace
‘Na ga mutuniyarki sai wani sheki takeyi tana ta yiwa miji iyayi, na ga ma itace take tuka motar saboda kauna.’
Ta ja tsaki
‘Hmm! Haka Yusra take gaya min ana ta soyayya a hanya. Ki barni kawai Amina! Yarinyar nan ta raina ni wallahi. Na tabbatar da hannunta a wannan haihuwar da nayi babu rai shine ta zo ta nuna min ta kwaci mijinta. Wallahi Amina sai nayi maganin yarinyar nan.’
‘Hmmm! Kinga dai yanzu ki kwantar da hankalinki ki sami lafiya, sai ki san yanda zakiyi ki tattaro kan kudi don kinga akwai wani malami da za a hadani da shi kwanan nan kuma an ce aikinsa babu wasa. Kin san ina ta fama da Abban Asiya ina so na dauki hutun aiki na bishi Abuja yana ta faman gocewa, zargin da nakeyi wata ya ajiye a can shi yasa ko da tsiya-tsiya sai na je.’ Suka cigaba da hirarrakinsu suna shawarar yanda za a yi a sami kudi aje wajen Malami, daga baya Rahma ta dawo don haka suka canza hirar. ___
Kwana daya Zahra ta kara a asibiti aka sallameta, suna dawowa gida Rahma tayi musu sallama ta koma gidansu.
Duk wani ban baki da ban hakuri likitocin sun yiwa Zahra shi domin likita ya tabbatar mata idan ta cigaba da zama da damuwa zata haifarwa kanta da hawan jini na din-din-din, sai dai ita bata ga yanda za ayi ta kwantar da hankalinta ba. Duk wata kulawa Abba yana bata sai dai har yanzu tana ji a jikinta cewa ya san abubuwan da ta shirya kallonta kawai yakeyi.
A hankali tana kara samun lafiya tana cigaba da tunanin hanyar da zata bi ta sami kudi. Bata son ta siyar da babbar saitin gwal dinta amma dai ta fara tunanin sayar da na yaran. Bata son ta tambayi Abba kudi domin bata ga fuska ba duk da komai yana yi mata kamar yanda ya saba sai dai kawai ita din ta kasa sakewa.
Haka dai rayuwarsu ta cigaba. ---------
Kwanci tashi har an kai wajen wata uku da haihuwar da Zahra tayi babu rai, basu samu sun je wajen boka ba saboda har yanzu mahaifiyar Amina a kwance take; domin kusan za a iya cewa ta zama sai dai a kwantar a tayar. Don haka babu halin Amina tayi nisa musamman da yake tana matukar kaunar mahaifiyar tata. Haka ta hakura tana kallo mijin nata yana can Abuja ga shi Asiya tana kawo mata rahotannin cewa yana tare da matan banza a can din amma babu yanda zata yi don ya ma hanata zuwa Abujan gaba daya.
Hankalin Abba ya dawo jikinsa don haka ya nemi kudi ya sake fara business din sa; sai dai wannan karon duk wani abu da zai yi na harkar business din sai idan yana gidan Aisha ne yake yi domin ko wayar abokan kasuwancin nasa baya amsawa idan yana gidan Zahra.
Haka kowa ya cigaba da rayuwarsa. __
Tun tuni aka samarwa Saddiku da Yusra admission a jami’ar Maryam Abacha American University wato MAAUN; Yusra tana karantar Business Administration yayinda Saddiku yake karantar Accounting. Da yake kwanci tashi babu wahala gashi a halin yanzu har suna zana jarrabawar zango na farko wato zasu gama level 1 su shiga level 2.
Tunda suka fara jarrabawa Saddiku yake gayawa Mommy ta karbar masa kudi a wajen Abba naira dubu hamsin zasu hada suyi end of session party. Sai kaucewa zancen takeyi saboda ta san yanzu bata da dama a wajen Abban yayin da shi kuma Saddikun yake sake dagewa da yi mata naci. Haka dole ya sakata tayi masa alkawarin ko da Abban bai bashi ba ita zata bashi ko da bai kai dubu hamsin din ba. Kudaden da take hadawa domin suje wajen boka su kadai ne a account dinta domin ta hada kusan dubu dari biyu; garwar motarta da akayi accident wadda take ajiye a tsakar gida ita take jira ta sami mai siya ta hada kudin sai suje.
Wanna magiyar da Saddiku yake mata a kan kudin party ma ya kara mata kaimi wajen ganin ta dawo da hankalin Abban kansu, bata son ganin yaranta a cikin damuwa musamman Saddikun. ---------
A dakinta ya sameta tana zaune a kan dadduma ta idar da sallar isha’i, bayan ta amsa sallamarsa ya wuce ya zauna a gabanta kamar mai daukar karatu. Ta dan kare masa kallo; zuciyarta tana so ta yarda lallai Saddiku yana shaye shaye; to amma bata ga lebensa da hannayensa suna yin baki ba irin na 'yan wiwi. Abinda bata gane ba shine shi din ba hayaki yake sha ba kwayoyi yake sha masu tsada da kuma dauke hankali nan take. Ya kwantar da kai yace
‘Mommy baki turo min 50k din ba, gobe fa zamuyi final paper kuma ranar Saturday zamuyi party din.’
Tunda ya zauna dama ta san abinda zai tambaya kenan, ta jijjiga kai tana murmushi
‘Ku yanzu ba za ma ku iya tsayawa ku ga result ba kafin kuyi party din idan fa ba ku ci jarrabawar ba.’
‘Haba Mommy, ai duk mun ci. Kin san a ajin wasu foreigners ne don haka ana gama exam kowa zai tafi gida shi yasa zamuyi party din. Kusan kowa ma ya biya mu uku ake jira. Don Allah Mommy ki karba min kudin nan kinga ina cikin organizers fa.’ Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan tace
‘Abbanku yace bashi da kudi kuma ka san idan nace masa party zakuyi ma ba zai bari kaje ba, amma idan kana son 30k ni zan turo maka zuwa gobe idan kuma tayi kadan to sai dai kai kaje ka tambayi Abban.’
Da sauri yace
‘A’a Mommy please ki turo 30k din kawai.’
Suka dan taba hira yayi mata sallama ya fice.
Yana fatan idan ta bashi dubu talatin din daga baya sai ya san yanda zai yi ya takureta ta kara masa ashirin din.
Party suka shirya su uku shi da abokansa, ‘yan ajinsu na Jami’a ma basu san da wannan party din ba. Ya riga yayi alkawarin dubu dari biyu zai bayar gudummuwar party din. Ya riga ya yagi mafi yawan kudin a wajen Abban ta hanyar karyar abubuwan da aka ce su saya a makarantar, a halin yanzu dubu hamsin din kawai yake bukata ya gama hada kudin su je suyi party dinsu. ………..
Babu yanda ta iya haka ta turawa Saddiku dubu talatin daga kudin da take ta faman tarawa, sai dai duk nacinsa ta ki ta kara masa wasu kudin; ta dai gaya masa ya samo makanike ya sayi gawar motarta da yayi accident idan an biyata sai ta kara masa.
Haka ya samo har mutum biyu, sai dai babu wanda ya taya motar a kan dubu dari ma. Domin duk cewa sukeyi ba zata moru ba don har injinta ma ya tashi daga aiki. Haka ta hakura ta sayarwa da na karshen a kan naira dubu sittin da biyar. Wanda a hakan ma yace sai dai su bashi sati biyu zai kawo kudin sai ya dauki motar.
Sai bayan ya tafi Saddiku ya bishi ba da sanin Mommy ba ya karbe naira dubu goma sha biyar a kan ya kai cikon ya dauko motar. …………..
Tun bayan la’asar ya shirya yayiwa Mommy sallama. Ya dauki motarta ya tafi party; motar da tana kallo yanzu ta zama ta Saddiku tunda da tana kokarin ta sa Abba ya saya masa tashi motar amma yanzu ta san bata da wannan damar.
Kamar yanda Abba ya saba bayan magriba ya dawo gidan. A gidan Aisha zai kwana don haka gidan Zahra ya sauka; bayan ya huta suka dan taba hira ita da shi da yaran. Sai da ya dawo daga sallar isha’i sannan yayi mata sallama ya tafi. Kafin ya fita kuma ya sanar da ita idan goman dare tayi Saddiku bai dawo ba tayi masa waya.
Ta san yace mata sun tafi party don haka bata sa rai zai dawo kafin karfe goma na dare ba, don haka wajen tara da rabi ta kulle gidan ta turawa Saddiku message cewa idan ya dawo yayi mata waya tunda ba ciki zai shigo ba a boys quarters dakinsa yake.
Tunda ta kintsa ta kwanta bata farka ba sai karfe biyu na dare; agogonta ta fara dubawa a wayarta taga lokaci.
Nan take ta dannawa Saddiku kira, har wayar ta tsinke bai dauka ba sai kawai tayi zaton ya dawo bacci ne ya kwasheshi tunda ya kwaso gajiya don haka itama sai ta gyara kwanciyarta ta cigaba da bacci. __
Tana idar da sallar asuba ta sauko ta bude kofa ta leko tsakar gidan, so takeyi ta tabbatar Saddiku ya dawo gidan jiya. Ga mamakinta babu motarta a tsakar gidan wanda hakan yake nufin Saddiku bai kwana a gidan ba. Ta fito ta tsaya a kan baranda ta kwalawa Malam Sado kira, da gudu ya taho yana rike da carbinsa da yake wiridi. Bayan ya gaisheta ta amsa tace masa
‘Malam Sado Saddiku bai dawo gidan nan ba jiya da daddare?’
Ya shafa kai yace
‘Bai dawo ba Hajiya sai dai ko nan gaba.’
Ta koma cikin gidan jikinta a sanyaye.
A kan dining table din kasan ta zauna ta lalubo lambarsa a waya ta sake kira, ringing kawai wayar take yi Amma ba a dauka ba. Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta tuno haka yayi mata wancan lokacin da yayi accident. Nan da nan idanuwanta suka cicciko da kwalla; da sauri ta fara laluben lambar wayar Abbansa. Sai da ta zo kan lambar tasa sai kuma ta tsaya ta kasa kiransa; to yanzu idan ta kirawo shi me zata ce masa? Ce mata yayi idan goma tayi Saddiku bai dawo ba ta kirawoshi amma bata yi hakan ba sai yanzu da safe ta kirawoshi tace masa me? To idan fa accident Saddikun ya sake yi ‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.’
Ta fada a fili yayinda idonta ya cicciko da kwalla. Gashi bata san abokansa ba don haka ma bata da lambar ko daya daga cikinsu. Ta tashi jikinta babu kwari ta koma saman, ta zo daidai kofar dakin su Yusra taji motsinsu. Nan dabara ta fado mata; ta karasa ta tura kofar ta kirawo Yusra. A dakin Yusran ta sameta, bayan ta amsa gaisuwar ta tace
‘Yusra yayanki bai dawo gidan nan ba jiya gashi kuma ina ta kiran wayarsa bai dauka ba, ko kina da lambar abokansa da suke party din tare na kirawosu muji?’
Da mamaki Yusran tace
‘Mommy party sukeyi?’
Itama mommy din mamakinta ya karu
‘Au baki sani ba? Yace min end of year party zasu yi shi da ‘yan ajinsu jiya da daddare.’
‘To gaskiya Mommy ni ban sani ba, kuma a abokansa mutum daya nake da lambarsa. Bari na kirawo shi muji.’
Nan ta koma daki ta dauko wayarta ta dawo wajen Mommy din. Ta lalubo lambar Babs wanda dan ajin su Saddiku ne, shima ta sami lambarsa ne saboda yana sonta duk da ita din bata sauraronsa.
Sai da ta zauna a kusa da Mommy sannan ta danna masa kira ta sa wayar a loudspeaker. Yana dauka yace
‘Today is going to be a good day tunda ke kika fara kirana Babe, to ya kike?’
Tace
‘Uhm! Lafiya. Ka san wani abu? Ya Sadik nake nema ka san tun jiya da daddare bai dawo gida ba yace wai ‘yan class dinku suna end of year party shine nake son naji me ya hanashi dawowa gashi Mommy tana nemansa.’
Da mamaki a muryarsa yace
‘Party? Gaskiya ba dai ‘yan class din mu ba sai dai ko wasu friends din nasa, don gaskiya duk mun koma gida ko nima kin ganni a KD.’
Sukayi shiru na dan lokaci, jima kadan yace
‘Amma bari na tambayar miki su Bigi duk da dai na san ba da su bane amma dai idan har guys din mu ne suka shirya party din to lallai Bigi zai sani.’
Sukayi sallama bayan ya sanar da ita idan ya ji wani abu zai kirawota.
Ta dubi Mommy tace
‘Kin ji Mommy!’
Cike da damuwa tace
‘Hmm! Na ji Yusra. Ni haka yace min da 'yan class dinsu don sai da na bashi 20k sannan kuma ya zagaya ya karbe kudin da aka sayar da garwar tsohuwar motata ba tare da ya gaya min ba kuma cewa yayi duk a kan party din ne. To ina ya tafi?’
Jimawa kadan ta sallami Yusran don taje ta shirya mata yara su tafi tahfiz.
Haka tayi ta faman jan kafa cikin matsananciyar damuwa har wajen karfe goma saura.
Wajen karfe goma Abban ya shigo don ya dubasu ita da Yaran. Bayan ya amsa gaisuwar Yusra a falon kasa ya haye saman. A dakinta ya sameta tana kashingide a gefen gado, bayan sun gaisa ya zauna a gefen gadon kusa da kafafunta yace
‘Ya dai? Jikin ko garin na ganki a kwance.’
Ta tashi ta gyara zama sannan ta bashi amsa
‘Uhm, babu ko daya. Hutawa dai nake yi kafin ‘yan gidan su dawo.’
‘Saddiku har ya fice ko? Ai sun gama exam tunda ke bakya hawa motar yau in ya dawo ya bani mukullin motar ya huta yawon ya isa haka, da anyi magana yace zasu je lecture ko kuma zasu hadu suyi karatu.’
Ta dan muskuta
‘Um nima haka na gani, bari ya dawo sai na karbi mukullin motar na boye saboda in zan fita.’
Suka dan taba hira daga baya yayi mata sallama ya fita; yana mamakin Zahra! Tun tuni yake so ya karbe mukullin mota daga hannun Saddiku amma ta hanashi sai tace ita zata kwace kuma bata iyawa. Lokuta da dama yana mamakita, yanda har yanzu ta kasa gane cewa bata tarbiyyar Saddiku takeyi. Shi yasa har yanzu bai gayamata cewa ba zai biyawa Saddiku kudin registration ba sai ya je makarantar da kansa ya ga result dinsu.
Ta kasa gayawa Abba cewa bata ga Saddiku ba kuma ta rasa wanda zata gayawa gashi har sha biyu saura, ta dai yanke shawarar idan aka yi kiran azahar bata sameshi ba zata gayawa Abbansa.
Karfe Sha biyu da kwata wayarta tayi kara, ta dauki wayar kamar wadda aka yiwa dole sai kuma ta ga sunan Saddiku, sai da zuciyarta ta nemi tsayawa lokacin da ta kara wayar a kunnenta. Kafin tayi magana aka ce ‘Hello.’
Ba Saddiku bane yake magana, haka dai ta daure ta amsa. Bayan mai maganar ya gaisheta yace
‘Don Allah ina magana da mahaifiyar Sadik Yusuf ne?’
Cikin hanzari tace
‘Eh, ina Sadik din?’
‘Um gamu nan da su a asibitin Malam Aminu Kano emergency shi da abokansa, suma sukayi tun jiya a wajen party da suka sha kwaya, har yanzu basu farfado ba.’
‘To gamu nan zuwa.’
Ta saki wayar a kan cinyarta daidai lokacin da hawaye ya wanke mata fuska.
Saddiku ya sha kwaya tun jiya ya suma? Yanzu me zata cewa Abbansu, bayan ta gama gaya masa da safen nan Saddiku ya fita.
‘Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!’
Ta mike tsaye, wayar da take ajiye a cinyarta ta subuce ta fadi kasa ta dauke wayar ta ajiye a kan gadon. Ta karasa gaban wardrobe tana share hawaye ta dauko hijabi ta saka sanna ta dauko jakarta a kan mudubi ta dawo ta dauki wayar ta jefa a ciki ta nufi ficewa daga dakin.
Har ta kama hannun kofar sai kuma ta tsaya ta kasa murdawa; to ina zata? Babu mota a gidan kuma Malam Ali baya nan, shi kuma Abban da yake ba a nan ya kwana ba bata ma san ko yana gida ko baya nan ba. Ta juyo cikin sanyin jiki ta koma kan gadon ta zauna ta zuba fuskarta a tafukan hannunta ta sake fashewa da kuka. Bata da wata mafita illa ta kirawo Abban Saddiku ta sanar da shi domin idan ma taje asibitin ita kadai a halin yanzu komai zai iya faruwa.
Ta kama gefen hijabin da yake jikinta ta goge hawayenta, tayi ajiyar zuciya ta laluba jakarta ta dauko wayarta. Ta lalubo lambar Abban Saddiku ta danna kira ta kara a kunnenta zuciyarta na dakan uku-uku. …………
Fitowarsu kenan daga gidan Hajiya shi da Yaya Bello, suka shiga motar Abban suka kama hanyar gidan Yaya Bello inda a can zasu ci abincin rana. Yana zura mukullin motar kira ya shigo wayarsa wadda ajiyeta kenan a kusa da giyar motar; ya fasa tayar da motar ya amsa wayar ya kara a kunnensa. Ba tare da ta amsa sallamarsa tace
‘Abba Saddiku bashi da lafiya yana asibitin Malam a emergency, yanzu Yayan abokinsa da suke tare ya kirawoni ya sanar da ni.’
‘Subhanallah! Accident yayi ko me?’
‘Nima dai ban gane bayanin ba amma dai ba accident bane, nima yanzu zan sami motar haya na wuce asibitin idan kuma kana unguwar sai na shirya mu tafi.’
‘Ina gidan Yaya kiyi zamanki zan je na gani in ya so mayi waya.’
Ya ajiye wayar ba tare da ya saurari amsarta ba. Ya dubi Yaya Bello da yake gefensa ya sanar da shi abinda ta gaya masa, nan yace su wuce asibitin kawai. Don haka Abban ya tayar da motar suka kama hanya.