Kenza eBookz

Uwar sadiku complete - Chapter 29

Uwar sadiku complete - Chapter 29

Uwar sadiku complete Chapter 29: Uwar sadiku complete Chapter 29. Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan a…

4,481 words

Ita kuwa Zahra yana ajiye wayar ta dora hannu aka ta sake rushewa da kuka; shikenan a gaban Yaya Bello za a yi mata wannan tonon asirin, ya sami dalilin da zai shiga rayuwarsu ita da yaranta ya hanasu jin dadi.

Sai da tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita halin da ake ciki, duk da bata gaya mata cewa kwaya Saddikun ya sha ba.

Sukayi sallama a kan idan taji abinda ake ciki ta sanar da ita. …………

Har suka isa asibitin Malam Aminu Kano babu wanda yace wa dan uwansa wani abu; shi Abba yana ta mamakin to Saddikun da aka ce masa dazu ya fita meye zai sameshi har a kaishi emergency kuma ace ba accident ba yayinda shi kuma Yaya Bello yake kallon hanya yana nashi nazarin.

A kusa da emergency din yayi parking suka fito suka shiga, sai dai suna shiga kuma ya rasa wanda zai kama. Don haka ya janyo Yaya Bello suka dawo waje ya kirawo Zahra ya tambayeta wanda zasu nema; bayan ta sanar da shi ya ajiye wayar ya kirawo lambar Saddikun sanna suka nufi komawa cikin emergency din.

Yana shiga ya hango wanda yake waya da shi; yaro ne matashi wanda ba zai wuce shekaru ashirin da biyar ba zuwa da shida. Da hanzari ya karaso wajen su Abban,bayan sun gaisa ya mikawa Abban wayar Saddiku yana fadin

‘Ga wayar Sadik din.’

Ya karba yana fadin

‘Wai me ya samesu ne?’ Cikin damuwa yace

‘To ni dai abokinsu ne ya kirawoni kuma a hotel na samesu wai party sukeyi shine suke competition aka wanda yafi shan kwaya da yawa zasu bashi kudi 250k. Su ukun da suke kwance a nan su suke shan kwayar shine da sauran suka ga sun sume duk suka gudu sai abokinsu daya ya kirawo ni ya gaya min don harda kanina a cikinsu. Shima yana gaya min ya gudu, don yanzu ma likitocin tambayar da suke shine a gaya musu sunan kwayar da suka sha don su san irin abun da ya dace suyi musu amma ni ban sani ba; abokan nasu kuma duk sun kashe waya. Gasu can dai su uku a kwance a sume an dai musu allura.’

Yaya Bello yace

‘Subhanallah!’

Matashin da yake yi musu bayani yace

‘Likitan da yake duba su yana wancan office din, ku zo mu karasa sai kuji daga bakinsa.’

Yaya Bello yaja hannun Abban Saddiku wanda ya kasa wani katabus suka bi bayan yaron.

Bayan ya gabatar da su a wajen likitan shima likitan irin bayanan da yayi musu ya sake basu, ya dora da

‘Matsalar itace bamu san irin kwayar da suka sha ba. Shi daya yaron da ya farfado yace sunan kwayar flash dayar kuma rod, a lussafinsa shi kwaya uku ya sha yayinda su kuma suka sha biyar ko shida. Muna bincike kuma muna jira su farfado mu sami ainahin sunan kwayar domin shine zamu san irin abinda ya dace muyi musu.’

Suka yiwa likitan sallama bayan ya sanar dasu idan sun farka za a mayar da su sashen kula da kwakwalwa.

Bayan sun fito daga ofishin suka karasa inda Saddikun yake; yana nan a kwance babu alamar wani motsi a tare da shi idan banda numfashi da yake futarwa a hankali. Suka kare masa kallo Yaya Bello yace

‘Allah ya kyauta.’

Ya janyo hannun Abban Sadik wanda yake binsa kamar mutum-mutumi suka fito bayan sun yiwa yaron godiya sun sanar dashi cewa suna nan a farfajiyar asibitin idan an bukaci wani abu.

Akwai dan waje daga gefen emergency din da kujerun siminti na zama, nan suka je suka zauna. Suna zama Abban ya zuba fuskarsa a tafukan hannunsa yayinda shi kuma Yaya Bellon ya zauna kusa da shi yana nashi nazarin ba tare da yace komai ba.

Sun dauki kusan minti goma haka kafin Abban Sadik ya sauke hannuwansa ya dubi Yaya nasa cike tsananin damuwa yace

‘Allah ya sauwake.’

‘Amin ya Allah.’

‘Wallahi Yaya ban san yanda aka yi Saddiku ya zama haka ba. Kusan mutum uku ne suka yi min magana a kan na binciki yaron nan, don malaminsu na secondary school ma kai tsaye ya gaya min cewa yana shaye-shaye. Amma duk yanda naso na dauki mataki a kai uwarsa ba zata bari ba domin wasu lokutan ko bari na ganshi ma bata yi. Gashi ko an kama shi da laifi ta iya kare shi, wasu lokutan ma kamar shashantar dani take ta mantar dani al’amarinsa. Yanzu ka ga abinda ya faru ko Yaya? Da anyi mata magana sai tace wai ana so a hadani da shi.’

Yaya Bello yace

‘Sha’anin mata ne sai hakuri. Yanzu jira zamuyi ya farfado muji daga bakin likitocin yanda za ayi a taimaka masa don ba zamu barshi haka ba.’

Cikin kunan rai ya cigaba

‘Ka ga tunda har ya kai ya shiga gasar shan kwaya kenan ya dade yana yi har ta bi jikinsa, kuma ma kudi har naira dubu dari biyu ina suka samo su? Ni dai ban taba bawa Saddiku naira dubu goma ba ma ba balle dubu dari biyu ko fiye. Ina ya sami wadannan abokanma?’

Suka cigaba da tattaunawa Yaya Bello yana kwantarwa da Abban hankali yana gaya masa za a samu ya bari in Sha Allahu.

Wajen karfe biyu suka jiyo kiran Sallah daga nesa, Yaya Bello ya dafa Abban yace

‘Ba muyi Sallah ba ai gara mu lekashi sai mu nemi masallaci muyi Sallah ko.’

Suka mike gaba daya.

UWAR SADDIKU

Written by Sakina Yazid (Innar su Amal)

38

A nan asibitin suka zauna, sai waya Yaya Bello yayi gida ya sanar da su Asma’u taje ta bawa Hajiya abinci.

Tun shigowarsu abokin Sadik din ya bawa Abban mukullin motar Sadik din ya sanar da shi hotel din da sukayi party din inda a nan motar take. Don haka suna nan zaune ya kirawo wani yaronsa Shamsu yace ya zo ya sameshi a asibitin. Da yake lokacin da suke wayar Shamsun yana court road ba tare da bata lokaci ba ya hawo Babur ya karaso ya samesu. Mukullin motar Mommy din ya bashi ya sanar da shi inda motar take, yace yaje ya dauki motar ya ajiye masa ita a wajensa zai nemeshi. Sukayi sallama ya hau babur dinsa ya kama hanya.

Bayan an idar da sallar la’asar su Abba suka koma inda Saddiku yake kwance. Zuwa lokacin daya yaron wanda ya rigasu farfadowa har an canza masa daki yana tare da iyayensa. Shi kuma daya yaron kanin saurayin da su Abban suka tarar mahaifiyarsu ta riga ta zo inda ta yiwa likitan bayanin tana so su sallameshi zuwa gobe don ita da yaran zasu bi jirgi zuwa Lagos daga can zasu wuce Dubai hutu; tana so likitan ya rubuta mata medical report idan sun je can likitocin zasu sake duba yaronta.

Bayan ta gama bayanin suka gaisa da Abba suka jajantawa juna, likitan yayiwa su Abban bayanin cewa su Saddikun ma yanzu sun farka don haka ana bukatar a samo madara su sha sannan za a canza musu daki inda za a cigaba da kula da lafiyarsu.

Ba tare da bata lokaci ba Abba ya fita ya siyo madarar ya kawo, da taimakon ma’aikaciyar jinya Yaya Bello ya daga Saddikun wanda har zuwa lokacin idonsa yake a rufe ya dura masa madarar aka samu ya sha kadan.

Zuwa karfe biyar da rabi sun dan kara farfadowa domin shi Saddiku har yana kiran Mommy yana wasu zantuka da ba a gane me yake fada. Nan aka turashi a gadon jinya aka mayar dashi wani dakin a sashen kula da kwakwalwa. Aka saka mishi drip kuma aka sake yi masa allurai.

Bayan likitan ya fita Abba ya zauna a kujerar dake ajiye a dakin yayinda Yaya Bello ya tsaya a daidai kan Saddikun yana tofa masa addu’oi.

A hankali yayi shiru ya daina surutun, Yaya Bello ya dawo ya zauna a kujerar dake kusa da wadda Abban yake kai. Ya dubi Abban yace

‘Ko Zahran za a sanarwa saboda a sami wanda zai zo ya kwana da shi mu samu muje gida zuwa safiya ko?’

Cikin sanyin murya yace

‘Eh ba zan ma kirawota ba don bana jin zan iya saurarenta yanzu. Namiji dai ya kamata a samu ko kuma ni din in an jima sai na dawo zuwa safiyar mu gani.’

Yaya Bello yace

‘Ba za ayi haka ba, gamu da samari a dangi. Ko wajen su Jamilun Inna ai za a sami mai kwana da shi ko kwana nawa za ayi. Kuma ma yanzu ina ga Muhammadu zan kirawo ya taho musu da kayan bukata ya zo su kwana da shi tunda ba abu ne da ake so ya baza dangi ba ayi ta faman cewa yana shaye-shaye.’

Kafin Abban ya bashi amsa ya kirawo Karima ya sanar da ita halin da ake ciki, yace ta bawa Muhammadu kudin mota kuma ta zubo musu abincin dare ta bashi abun shimfida suna jiransa idan ya zo sai su tafi.

Muhammadu shine yaron Yaya Bello na farko wanda zai bawa Saddiku kamar shekaru hudu, don a halin yanzu shi yana ajin karshe a Jami’a inda yake karantar aikin jarida.

Nan suka zauna har zuwa lokacin da Muhammadu ya iso sannan sukayi masa sallama suka tafi. -----------

Tunda Abban Saddiku ya fita ya sanar da ita gasu a asibiti kuma shima bai san me ya sami Saddikun ba don baya cikin hayyacinsa take cikin matsananciyar damuwa. Gashi Abban ya ce kada ta sake ta zo asibitin sannan kuma ya ce ta daina damunsa da waya idan ana bukatar wani abu a wajenta zai nemeta. Haka ta kasa sukuni kuma ta rasa me zata cewa yaran da suke ta faman tamabayarta ko bata da lafiya; don haka kawai sai ta biye musu a kan bata da lafiya sannan kuma Yaya Sadik ma bashi da lafiya yana asibiti Abba ya kai shi.

Har la’asar tana rike da waya tana jiran shigowar kiran Abba ko kuma ta ji shigowarsa gidan amma shiru. Hankalinta ya kara tashi don haka ta sake kiran Yaya Murja ta rushe da kuka. Cikin firgici Yaya Murja tace ‘Subhanallahi! Zahra Saddikun mutuwa yayi ne kike kuka haka? Ki gaya min me ya faru.’

Cikin shesshekar kuka tace

‘Yaya nima ban sani ba Abbanshi yana can tare da shi kuma yaki yayi min bayani har yanzu shiru, cewa ma yayi kada na sake yi masa waya sai ya dawo.’

‘Ikon Allah! To kiyi hakuri mana, na san tabbas da mutuwa Saddiku yayi da yanzu kin ji labari ai lafiya ce take buya akasinta baya buya. Kiyi hakuri zuwa lokacin da zai dawo gidan sai mu ji.’

Suka ajiye waya.

Jimawa kadan kuma Yaya Murja itama ta kasa nutsuwa saboda yanda Zahran take kuka, don haka nan da nan ta barwa abokiyar zamanta girkin da yake nata ta kama haryar gidan Zahra.

A dakin ta sami Zahran suka zauna tana ta bata baki; sai dai har zuwa lokacin Zahran bata gaya mata gaskiyar abinda ya samu Saddikun ba. Ta dai sanar da ita cewa lafiya kalau ya fita abokinsa ya kirawota yace bashi da lafiya har sun kai shi emergency. Don haka suka zauna suna jiran Abban ya dawo ko ya bugo waya. Har Magriba ta kawo jiki bai dawo ba don haka Yaya Murja tayi mata sallama ta tafi nata gidan a kan duk abinda taji ta sanar da ita, sannan kuma idan dare ya kara yi Abban bai dawo ma ta sanar da ita sai ta gayawa Yaya Muhammad ya nemeshi.

Ta tafi ta barta zuciyarta fal damuwa. ---------

Suna fita daga asibitin suka sami masallaci sukayi Sallar Magriba sannan suka wuce ya sauke Yaya Bello a gidansa.

Ya ji dadi matuka da Allah ya sa ba a gidan Zahra zai kwana ba don yanda zuciyarsa take tafasa baya jin zai iya saurara mata; domin duk halin da Saddiku ya shiga laifinta ne.

Ba zai kirawo wannan abun da jarrabawa ba domin sakaci ne kuma ya san da laifinsa a ciki; to amma me yasa Zahra take katangeshi daga yiwa dansa tarbiyya? Shi din me ya rufe masa ido yaki ya jajirce? Tabbas Zahra itace ta san kulle-kullen da ta dade tana yi a kansa kuma baya jin zai iya yafe mata idan ta lalata masa yara.

Kai tsaye gidan Aisha ya wuce; ta gama abincin dare ta jera a table gidan yana ta kamshin turare.

Kallo daya tayi masa ta san cewa akwai damuwa a tare da shi. Bayan ya amsa sannu da zuwanta ya dubi dining table yace

‘Kin gama abinci ko? Yunwa nake ji.’

‘Na gama, zaka sake kayan ko sai ka ci abincin?’

‘Hakane, bari ma na fara yin wanka.’

Yana fitowa daga wankan ta zuba masa abincin wanda tuwo ta dafa da miyar agushi, ya ci ya koshi ba tare da yace mata komai ba. Bayan ya gama ya taso daga table ya dawo gaban TV, ta kwashe kwanukan sanna ta hado shayi ta ajiye masa. Ya dauki remote ya kunna TV a daidai lokacin da ta zauna a kusa da shi tana kallonsa.

Ya kalleta yayi gajeren murmushi yace

‘Ya ake ta kallon fuskata kamar ana karanta littafi?’

Ta mayar masa da murmushin tana wasa da gashin kansa tace

‘Na ga kamar ka shigo da damuwa ne shine tunda ba a gaya min ba nake kokarin karantawa, tunda ka san an ce labarin zuciya a tambayi fuska.’

Yayi murmushi.

Nan ya bata labarin abinda ake ciki, sosai ta jajanta masa sannan tace

‘Kuma ka ga maganar Yaya gaskiya ne, idan aka samu ya farfado gaba daya akwai rehabilitation centers inda idan ka biya zasu ajiye shi tsawon wani lokaci a dorashi a kan magunguna da therapy har a samu ya rabu da shan kwayar. Sai dai fa su yawanci gaskiya a can ake kwana kamar boarding school.’

Ya kalleta cike da damuwa

‘To ya za ayi, ai dole a kaishi tunda idan na barshi a gida uwarsa ba zata bari a yi masa abun da zai bata masa rai ba.’

‘Amma fa babu uwar da zata so ace danta yana shaye-shaye, ita din ma na san idan kayi mata bayani zata gane kuma zata so a rabashi da mugun abu. Ka dai yi mata bayanin tunda ko babu komai yana bukatar addu’arta.’

‘Hmmm!’

Ya mayar da hankalinsa ga kallon TV din yana shan shayinsa.

Bayan ya kurbe shayin ya ajiye kofin, ya dauki kafafunsa ya dora a kan cinyar Aishan tare da gyara zama. Ta muskuta ta fara matsa masa kafafunsa tana yi masa tausa domin ta san idan yayi mata haka abinda yake bukata kenan. Sai wajen karfe tara da rabi sannan ya tashi yayi sallar isha’i wadda bai samu yayi a masallaci ba saboda gajiya. Bayan ya idar ya dauki mukullansa yayi mata sallama a kan zai je gidan Zahra ya dawo.

Yana fita itama ta tayar da Sallah. ---------

Tana kwance a dakinta ta jiyo shigowarsa gidan, nan da nan ta taso ta fito falon sama don ta tareshi.

Yaran duka sun yi bacci sai Rukayya da Yusra wadanda suke zaune a falon kasa suna jiran suji halin da Yayansu yake ciki kafin su kwanta. Bayan ya amsa sannu da zuwansu ya nufi saman.

Suka biyoshi a baya Rukayya tana fadin

‘Abba kwantar da Yayan aka yi?’

Yace

‘Eh, sai zuwa gobe zasu sallameshi watakila.’

Yusra tace

‘Abba wai me ya sameshi?’

Baya son ya amsa wanna tambayar don yana ganin bai dace ya ce musu dan uwansa shaye-shaye yayi ba. Ya kada kai yace

‘Zuwa yayi gidansu abokinsa suka sha lemo wanda yayi expiring ba tare da sun sani ba shine suka sami food poisoning shi da abokansa biyu.’

Yana cikin bayanin suka shiga falon saman don haka Mommy taji lokacin da yake maganar food poisoning, sai da tayi ajiyar zuciya saboda yanda ta dan sami nutsuwa; to da me yasa bai yi mata bayani ba ya barta cikin damuwa?

Suna karasa shiga cikin falon ya cewa su Rukayyan

‘To tunda an ji inda Yaya yake sai aje a kwanta ko?’

Suka yi masa sai da safe itama Mommy din suka yi mata sai da safe suka shige dakinsu na na saman domin kwanciya bacci.

Suna shigewa ta mike ta bi bayan Abban wanda ya nufi dakinsa tana yi masa sannu da zuwa. Bata sani ba ko ya amsa ko bai amsa ba, ta dai san bata ji yayi magana ba sai dai da yake bata ganin fuskarsa bata san yanayin da yake ciki ba.

A tare suka shiga dakin, ya wuce ya ajiye mukullan hannunsa a kan mudubi sannan ya janyo ‘yar kujerar da take gaban mudubi ya zauna yayinda ita kuma ta zauna a gefen gado suna fuskantar juna. Tace

‘Ya jikin Saddikun? Naji kanacewa yara food poisoning ne, wanne irin abinci suka ci?’

Kallonta kawai yake a fusace wanda ita kuma take mamakin dalilin da yasa yake kallonta kamar itace tayi poisoning Saddikun. Ta dan bata rai ta kawar da kai , yace

‘Ai nima nan zuwa nayi na tambayeki abinda Saddiku yaci ya sami poisoning din?’

Mamakinta ya karu yayinda ta kara shan kunu saboda yanda ta kula yana so ne kawai ya raina mata hankali. Tace

‘Ya zaka tambayeni bayan kaine kaje wajensa?’

Yayi kwafa yace

‘Ko da yake ba ma wannan ya kamata na tambayeki ba, dazu da safe da na tambayeki Saddiku me kika ce min?’

‘Ce maka nayi ya fita, kuma ai a lokacin ya fita din ko ka ganshi ne a gidan bayan nan?’

Ya jijjiga kai saboda yanda take bashi mamaki, ya rasa yaushe Zahra ta kware a karya haka. Yace

‘Ban gashi ba, amma bari na sake tambayar watakila zaki fi ganewa. Jiya a ina Saddiku ya kwana?’

Gabanta ya fadi yayinda tayi sauri ta waske; sai a lokacin ta gane inda ya dosa. To ana maganar yau ya za ayi ya dinga tamabayarta jiya. Tana jin motsin kwayar idonsa a kan fuskarta domin ya ki ya daina kallonta wanda hakan ya saka ta kasa sukuni. Bata da wata mafita domin ta tsani yanda yake warware duk wata karya da ta yi masa ba tare da bata lokaci ba. Ta saci kallon fuskarsa suka hada ido, ta sake shan kunu sannan tace

‘Yace min zasu yi party na end of session, kuma na ga tun a secondary suke irin wannan party din shi yasa ban zata da wani abu ba. Shine yayi dare ni kuma bacci ya kwashe ni ban sanar da kai ba.’

‘Shine kika nuna min ya dawo kuma a gidan ya kwana? Ba ma wannan ba; kin zama kece uwarsa kece ubansa shi yasa kika bashi kudi kuma kika bashi izinin ya tafi party kika bashi mota yaje yayi abinda ya ga dama ba tare da ke da shi kun nemi izini na ba tunda dama kin nuna masa ni din bana son shi?’

Bata da bakin magana don haka ta sunkuyar da kai tayi shiru, so take kawai ya gama wannan hayaniyar tasa ya gaya mata abinda ya samu Saddikun da kuma halin da yake ciki. Ya fuskanci ba zata yi magana ba. Yayi murmushin takaici yace

‘To ina yi miki murna Zahra, saura kadan ki hallaka Saddiku domin jiya da kika boyemin kika bashi kudi da mota ya tafi party zuwa sukayi suka sha miyagun kwayoyi wadanda jikinsu ba zai iya daukan wannan yawan ba. Wannan shine ya janyo su ukun suka sume aka samu aka kaisu asibiti. Tun jiya basu farfado ba har zuwa lokacin da na barosu a asibitin, sai dai mu cigaba da addu’ar Allah ya tasheshi lafiya tunda likitocin sun tabbatar ya dade yana shaye-shayen kwayoyi.’

A firgice take kallonsa da baki bude, kafin ta sami kalaman da zata gaya masa ya mike ya dauki mukullin da ya ajiye ya nufi kofar. Sai da ya kama hannun kofar ya juya ya dubeta yace

‘Kuma ban baki izinin zuwa asibitin ba, idan kuma kin ki ji to zaki sha mamaki.’

Ya murza hannun kofar zai bude tayi sauri tace

‘To shi da waye a asibitin?’

Tana nufin ya gaya mata domin ta samu tayi waya taji halin da yake ciki tunda ta kula shi din ba zai yi mata bayani ba. Cikin halin ko in kula yace

‘Shi da mutane ne. Sai da safe.’

Ya fice kafin tace wani abu ya bar mata gidan.

Take hawaye suka wanke mata fuska.

Wannan wacce irin musiba ce ? Yanzu dama da gaske ne ake gaya mata Saddiku yana shaye-shaye amma yaron nan yana musa mata? Yanzu ya zata yi? Gashi Abban ta kula wulakanci kawai yake yi mata domin yaki yayi mata cikakken bayani. Gashi bata ji ya shigo da mota ba, to ina motar tata da Saddikun ya fita da ita?

‘Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun.’

Ta fada a fili lokacin da tambayoyin suka fara yi mata yawa a ka. Anya kuwa wannan abubuwan da suke faruwa babu sa hannu a ciki? A ce Saddiku yana shaye-shaye sannan kuma gashi Abbansa ya juya mata baya yanata faman yi mata wulakanci?

Ta share hawayenta yayinda ta mike ta fice daga dakin, wayarta zata dauko ta kirawo Yaya Murja ta sanar da ita. A falo ta zauna a kan kujera ta dauki wayar tata, har ta budo lambar Yaya Murja sai kuma ta tuna cewa bata shirya sanar da Yaya Murja cewa Saddiku shaye-shaye yakeyi ba. Musamman da yake taba yiwa Yaya Murja korafin yanda mutane suke faman gaya mata cewa Saddiku yana shaye-shaye. Tun a lokacin Yaya Murja tace mata ta bincika sosai kuma ta sanar da Abbansa, har ma ta ce ta tura mata shi domin idan ta gan shi ko zata iya fuskantar wani abu a tattare dashi. Ko maganar bata yi masa ba balle ta bincikeshi don a lokacin gani take kawai kiyayya ce da hassada tasa ake mata haka. Sai daga baya ta samu ta tsara Yaya Murja.

To yanzu idan ta kirawota me zata ce mata? Nan ta ajiye wayar ta kifa kanta a kan kujerar ta sake fashewa da sabon kuka.

Haka ta kwana cikin matsananciyar damuwa; tunaninta daya hannu aka saka mata a al’amuranta take ta shiga matsala kuma ko wanene sai ta rama.

Mutum biyu take zargi; Aisha wadda dama duk itace silar rikita mata gidan aurenta wanda a baya yake cike da kwanciyar hankali da kauna, sai kuma Yaya Bello wanda sosai take zarginsa a kan al’amarin Saddiku tunda ta kula yana bakin cikin yanda yaransa basu da gata kamar yanda Abban yake kulawa da yaranta, tunda shi baya iya bawa nasa yaran gata kamar yanda Abban yake bawa nasa.

Tabbas sai ta rama; tunda daman yanzu account dinta ya fara nauyi. Sarkar Rukayya ta gwal kawai zata bayar aje a sayar shikenan da zarar Amina ta sami dama sai suje wajen malamin da ta samo musu tunda itama a halin yanzun tana da tata matsalar. …………

Ko da gari ya waye ranar aiki ce don haka Abba ya shirya daga gidan Aisha suka fice gaba daya ba tare da ya je gidan Zahra ba. Ya riga ya san babu abinda suke bukata kuma ya yi waya da Malam Ali ya riga ya kai masa yara makaranta.

Babu yanda Aisha bata yi ba ya barta ta rakashi asibitin itama ya hanata, sai dai ta hada breakfast inda ta soya dankalin bature da sauce din kaza sannan ta zuba musu ruwan zafi a flask ta bashi ya kai musu. Yana fitowa ya sayi kayan shayi ya wuce asibitin. Da sallama ya tura kofar dakin ya shiga.

Muhammadu yana zaune a kan tabarmar da ya shimfida yana kokarin hada musu shayi da ragowar ruwan da ya zo da shi jiya. Ya ajiye kofunan da suke hannunsa ya tari Abban ya karbi kayan hannunsa ya ajiye. Bayan Abban ya amsa gaisuwar sa yace

‘Likitan ya zo ne Muhammadu?’

Yace

‘Bai zo ba, nurse din ce ta shigo tace yaci abinci zata dawo ta bashi magani.’

‘To ga abinci nan ka zuba muku ku ci, bari naje na sami nurse din.’

Yana fita ya sami waje ya zauna, basu dama yayi suci abinci sannan ya samu yayi magana da Saddikun kafin likitan ya shigo.

Sai da ya basu kusan awa guda sannan ya dawo dakin, lokacin sun gama cin abincin har nurse din ta bawa Sadik maganinsa. Sun gama cin abincin, Saddiku yana zaune a kan gadon yayinda Muhammadu yake zaune a kan tabarmar yana karatu. Bayan Abban ya amsa sannu da zuwansu yace

‘Kana da lecture ne yau Muhammadu?’

Yace

‘A’a, sai gobe ne zamu yi test shi yasa nake karatu. Yau ba zan shiga makaranta ba.’

‘Allah ya bada sa a.’

Ya karasa ya zauna a gefen gadon Saddikun. Muhammadu ya dauki litattafansa ya mike yana fadin

‘Abba bari na zauna a nan waje na cigaba da karatun, idan ana nemena Ina nan.’

‘Ok to kada kayi nisa don yanzu zan tafi.'

Ya ji dadin hakan don dama so yake yayi magana da Saddikun, wanda tun bayan da ya cewa Abban Ina kwana ya sunkuyar da kai bai sake dagowa ba. Sukayi shiru na dan lokaci babu mai magana, shi Abban yana kallon Saddikun yayinda shi kuma ya sunkuyar da kai ya kasa hada ido da Abban nasa. Jimawa kadan Abban yayi gyaran murya yace

‘Sadik me yasa kake son ka kashe kanka?’

Ya dago kai idonsa cike da kwalla, suna hada ido da Abban yace

‘Kayi hakuri Abba.’

Ya sake sunkuyar da kansa yana share hawaye.

Abban ya jijjiga kai yace

‘Likitane ya duba ka Saddiku, nurse din da ta shigo ta baka magani bata wuce sa’arka ba sai dai ko ta baka shekaru biyu zuwa uku, kalli yayanka Muhammadu yana karatu don ya zama dan jarida, ni da na haifeka public administration na karanta shi yasa kaga na kai matsayin da na kai. Amma kai Saddiku ka zabi zama dan kwaya, ka tara kayan maye ka sha ka fita daga hayyacinka shi kenan abinda kake so Saddiku.’

Cikin kuka yace

‘A’a Abba kayi hakuri.’

‘Ka daina bani hakuri Saddiku, baka yi min laifi ba. Kanka ka yiwa laifi kuma kayiwa Allah laifi. Ya baka rayuwa kuma ya baka dama ka zama abun alfahari ga al’umma amma ka zabi shaye-shaye.’

Sukayi shiru na dan lokaci, Abban yace

‘Wa ya baka kudin zuwa party?’

‘Mommy.’

‘Tun yaushe kake shan kwaya?’

Ya sunkuyar da kai yayi shiru na dan lokaci, jim kadan yace

‘Tun ina SS 2.’

‘Ka san yanzu jikinka ya saba ba zaka iya rayuwa babu kwayoyin da kake sha ba saboda ka zama addicted ko?'

Bai iya amsawa ba kai kawai ya daga don ya san hakan ne.

‘Ina son ka Saddiku, ina son kayi rayuwa a hayyacinka kaima wataran ka zama wani ka tara naka family din cikin nutsuwa. Akwai makarantar da zasu taimaka maka ka daina shan kwaya amma fa makarantar kwana ce, idan likita ya sallameka daga nan can zamu wuce. Idan Allah ya sa ka rabu da addiction din a wata shida sai ka fito ka cigaba da karatunka.’

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull