Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 1

Uwar y'an mata complete - Chapter 1

Uwar y'an mata complete Chapter 1: Uwar y'an mata complete Chapter 1. [11/9, 8:31 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

4,428 words

[11/9, 8:31 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

2021

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_Bismillahir Rahmanir Raheem._

_GABATARWA;Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki,Salati mai ɗimbin yawa zuwa ga manzon Rahma,da Alayensa da sahabban sa._

_TSOKACI;Wannan labarin k'irk'irarre ne banyi domin wani/wata ba duk wanda ya ga yayi dai_dai da rayuwar Arashi ne_

*SADAUKARWA; GA UWA TA GARI, KUMA MACEN KIRKI, HASKEN ANNURI ME HASKAKE ZUCIYAR AL'UMMAH, GINSHIK'I, GARKUWA GA RAYUWAR 'YA'YAN TA, ALLAH YA SAKAWA UMMANA MAHAIFIYATA DA ALHERAN SA, ALLAH YA SA AYI KYAKKAWAN K'ARSHE, ALLAH YA BIKI DA HALAYENKI NA ALHERI MAAH, K'AUNAR KI TANA BUGUN ZUCIYA TA, MALAMA JUWAIRIYYA MUH'D KGW (MADAWAKIN KEBBI)MRS ALH AMINU ADAMU DIKKO, ALLAH YAƘARA NISAN ƘWANA DA SOYAYYA IYAYENA ABIN ALFAHARI NA, NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFI GAREKI AMMINA, DA DUK WATA UWA MAI 'YA'YA MAATA ARZIKIN GIDA.*

_GAISUWAR BAN GIRMA GAREKU MASOYANA A DUK INDA KUKE A FAD'IN DUNIYAR NAN._

_BABI NA D'AYA_

***************** Cikin ƙunci da baƙin ciki Hajiya Halima ta ƙarasa saman Alahaji, domin kiransa kamar yadda aka umurce ta!tana haura saman tana zubda ƙwallah! da tunani barkatai aranta, sai kai kawo maganganun da Hajiya ta fad'a mata suke a ƙwaƙwalwarta, masu kama da harshen damo...Cin mutunci da habaici tare da arashin da Hajiya ta ƙare zayyano mata, zafin da take ji a zuciyarta yasa gumi ya fetso mata saboda maganganun sun mata ciwo.

Ƙofar ɗakin ta dinga bugawa a hankali,domin gudun matsala,jim ɗin da taji ne yasa ta tura ƙofar a hankali bakinta ɗauke da sallama, daga can cikin ɗakin ya amsa,muryarsa da karfi ba tare da ya waigo ba,, ya ce"wai waye ne?"

Muryarta na rawa!ta ce" Ni ce Alhaji."

Ke wa....? ya tambaya

Share ƙwallah tayi tare da nazarin irin wannan tasko da wulakancin domin sarai yasan ita ɗin ce domin yaran basa gidan, Sai dai haɗiye yawun ta masu ɗaci! tayi kuuuut!sannan Ta ce"Halima."

Tsaki...ya yi a cikin ɗakin, kana ya ce" shigo a gajarce!" Jiki ba ƙwari tayi tattaki daga falonsa na sama zuwa uwar ɗakin,

Kawar da kansa yayi gefe, domin ya tsani ko da kallonta. ya ce"ya akayi UWAR 'YAN MAATA?''

Gabanta ya faɗi, da ƙunar rai!ta dubeshi ta kawar a ranta tana tunanin kenan shi ma yabi sawun danginsa,iska mai zafi!ta furzar daga bakinra, Ta ce" Abban Zeenat daman Hajiya Babba ce ta zo, shi ne ta ce" na kiraka, tana k'asa."

Washe Baki yayi ya ce'" Aaaah muna da manyan baƙi kenan a gidan nan, agogo ya ɗaura a tsintsiyar hannunsa, sannan ya kafa hular sa ruwan k'asa, da sauri ya ƙarasa shirin sa tsaf, hasken sa da kyau tare da kwarjinin sa tuni suka ƙara bayyana.

Ido ta zuba masa kamar kar ta ɗauke, cike da so da ƙauna,domin rabonta da ta sanya shi a idonta tsawon mako ɗaya kenan,domin idan ya fita shago tun safe baya dawowa sai cikin dare, saɓanin ƙa'idarsa ta da dayake dawowa da yamma lis.

A cikin ƴan ƙwanaki ya sauya idan ma ya daeo sama yake hayewa, batare da ya lalubota bare yaran ba abinda ya dame shi da su,don ya daina kulawa dasu kamar da can baya,duk da tana ganin kamar karan tsaye ne da akai ma rayuwar su, shi ne yay tasiri a kansa.

"Ke wai Halima wacce irin mayyar mata ce!? Ya katse mata tunani..... Tabbas Hajiya Babba tayi gaskiya,lallai ke mayya ce! saboda tuni nima na gano hakan,haka kawai ki dinga kallona? kallo na ƙurulla! Ai wannan kallon ko addini bai yarda da shi ba, daman ta faɗa min cewa"saboda maitarki duk kin lashe ƙwayaƙwayin haihuwar 'ya'ya maza da ke ƙwance ajikina, kin lashe su tatas, shiyasa sai haihuwar ƴaƴa mata kikeyi!To Allah yayi min tsari da maitar ki, daga nan ya wuce fuuuuu yayi waje yana mita."

Kuk ya zo mata a bazata, tana sheshsheƙa, ta ɗaga hannaye sama tana jero Addu'oin tsari da agaji agurin ubangiji tare da nemawa yaranta tsari daga bakin Hajiya da dangin mijinta duka, don ta daɗe da ƙonewa ciki da Bai,ko'ina babu daɗi.

Wani tunani ya zo mata shiyasa da sauri ta juya ta bar bedroom ɗin, ƙasa ta sauka! jikinta har rawa yake da sassarfa ta ƙarasa gurin fridge, ruwa da lemo ta ɗauko masu sanyi ta ajiye a gaban Hajiya, zuba mata tayi a ladabce ta dire a stool, Hajiya sai fira takeyi ita da tilon ɗanta acikin farinciki, shi ma da murna yake magana da Hajiyar ta sa, Alhaji Bello Babale kenan.

Ko kallon arziki Halima bata ishi Hajiya ba Ta ce"Wato sai yanz ki ka ga damar kawo min ruwan in sha, cimakar gidan ɗana ma kina baƙin ciki da in moreta?To sannu Gimbiya uwar marowata!"

Tsaki Hajiya tayi tare da zabgawa Halima wata harara!ta watsar, zama tayi gefen Alhaji Bello a tsorace!

Wani kallon banza yayi mata kana ya cigaba da magana da mahaifiyar sa,Lemon Hajiya ta kai bakinta ta kurɓa ta dubi Halima duban takaici!

Tace "Dakata ɗan Inna da maganar da kake...shin ita wannan matar ta ka batasan ta ba Uwa da D'a wuri suyi sirri ba? Wannan mannewa hakan har ina?Yau ko naga ikon Allah, Ni Meri ana nemaan shata min layi tsakani na da d'ana kamar akwai wanda ya haifa min shi .....!

Wata kunya ta lullub'e Halima, nan ta sunkuyar da kanta ƙasa!tana wasa da zobenta zinari da ya samu mazauni ɗaeam a ƙaramin farcenta, wata kasala taji ta ma kasa ko da motsin kirki.

Alh.Bello yace" ke Sadiya bamu gurin zanyi magana da uwata!"

"lallai kam uwar da ta iya haihuwa faɗi mata dai, ba masu Haihuwar asara ba!Inji Hajiya.

Da sauri Halima ta tashi kamar ta kife, ta nufi D'akinta tana rusa Kuka!kan makeken royalbed ɗin ta faɗa sai da ta darji kuka sosai,gefen zuciyarta yana faɗa mata ta tafi gidan su,ta wurgar da ƙwallon mangwaro ta huta da ƙudaji...wani gefen na zuciyarta kuma yana jiye mata aikata hakan,Anya zata sabou? tayaya zaki bar yaranki mata,to waye zai kula da su!?shi zuciyarta ke raya ma ta.Karfa kiyi gudun gara ki fad'a zago! goma ta lalace garin gyaran ɗ'aya Direban da ke ɗauko yaran daga makaranta ne, ya danno hancin motar Bus fara mai kyau da tsada. A cikin gidan suka shigo bayan ya tsaya ya kashe inji ɗinsa,Yara maata farare,kyawawa ne suka dinga fitowa daga motar, daga matasa ƴan sakandare, firamare,da kuma 'yan noziri. Hanyar da zata sada su da cikin falon gidan suka nufa, shiga sukayi kowanne rataye da jikarsa,da ƙwandon Abincinsa ga hannu,Zeenat da Khaleesat ne a gaba,sai Maryam(Mamu) da khaleesat, Bilkisu ne a baya,Hajaru da Halima hannayen su a sarke suna dariya, sannan yara sosai acikin su, wato Saudat,Salma,da Sareena.

Da sallam su ka shiga falon, da fara'ar su da zummar suyi Ido biyu da maman su sai dai Kash!Hajiya(kakar su) ita suka gani nan take suka sauya fuska!A hankali suka jero layi kowa na gaida Hajiya Babba...Hajiya Sannu da zuwa,Hajiya Ina yuni,Sannu Hajiya..."Hajiya ta dinga fad'i sannun ku,kallon Maryam tayi Ta ce"Takwarata Inna issa Mai laboji...zo nan inda Hajiya mamun taje tana tunzurar baki duk cikin yaran mamuh kawai Hajiya keyi ga shi ita kuma mamu ta tsani Hajiyar,Saboda masifar ta,Kuma ko a yaran gidan maamu tafi kowa tsiwa da rashin tsoro.

Cigaba da gaida Hajiyar sukayi suna wucewa ɗakinsu,Ita Kuma yawwa take faɗi, caaan Tace Kai na gaji da amsa gaisuwar.Ku barni na huta! tunda har yanzu baku ƙare shigowa ba!Baki Maamuh ta tunɓure, ta tashi daga wurinta tabi bayan ƴan uwanta tana gunguni.

Alhaji Bello kam sai kallon yaran yakeyi zuciyarsa cike da ƙaunar su,Domin shi kam Akan su komai Yana iya yi, Kuma Bai ragesu da komai ba. Hajiya ta dubi Bello da jin haushi Ta ce" Kai D'an Inna meye abin kallo a nan? har da murmushi?Tsaki tayi kana Ta ce" Yara sai kace an saki gargen Akuyoyi gasu Nan ba adadi duk kala Daya ba sauyi! sunyi wani layi sai kace an tattaro yara Mata na unguwar Nan kaf!Ace macce Daya tal ta dinga haihuwar diya Mata har Tara. Ai da ban yiwa tufkar hanci aka juye mata mahaifar ba!To da yanzu Allah kad'ai ya San iya adadin matan da zata haifo,Da Hamsin ko d'ari Koma matan duka duniya da sukai saura zata zubo, tun da mahaifar ta, ta iya Mata ce kuma ba kanta kamar kaza..'Nifa har haushi kake bani irin yadda kake nuna kulawar ka Akan fekakkin yaran nan.gwara Mai sunana Domin Naga ta d'auko Ni sosai uban kowa Bata Tsoro!Sauran Nan duk na tsane su jinin mayu."

Gyaran Murya yayi Cikin sigar rarrashi ya ce"Hajiya Babba ai hannunka baya ruɓewa ka yanke,yaran nan duka 'ya'yana ne Kinga dole na kula da su da duk abinda zasu buk'ata a rayuwa.

To naji Amma ka dai ji duk abubuwan da na fad'a maka!Babu canji ba nawa!Cikin kwanan nan Ina so ka shirya Nan da shekara D'aya labari ya sauya.Inji Hajiya Babba tana kokarin mayarda madubinta a fuska.

To Hajiya duk yadda Kikace hakan za a yi, NAGODE.Alhaji Bello yace Yana rufuwa Hajiyar baya.Har Bakin motarta ya rakata,Inda direban ta ke zaman jiran fitowar ta .Shiga tayi ta hakimce a Bayan motar tana Danna iPhone 11 dinta Sannan su ka wuce.

Shi ma motar sa ya fad'a Yana tunanin magangannun da suka tattauna da Hajiyar sa,Wani Abu yaji ya daki zuciyarsa Nan Hawaye ya dinga kwaranya a tudun fuskar sa,Sitarin motarsa ya daka!Da tunanin Duniya ya k'arasa babban shagonsa da ke Kan titin Ahmadu Bello way.

**********Kusan tsawon minti biyar da shigowar sa falon gidan.Amma yayi tsaye tare da hade hannayensa a kirki,ledojin da ya Shigo da su a gefen sa,Sai kallon salihar matarsa da yaran yakeyi,wacce ke tsakiyar yaranta Mata biyar tana koya masu karatun Alkurni Mai girma da sauran littafan addini.

Wani sanyi yaji a ransa,Babu abinda ke masa Dad'i sai yadda Juwairiyya ke karatun littafin Allah kamar balaraba.Haka yaran na Amsawa da zagin Muryar su.

Da farin ciki ya iso inda su ke Yana masu sallama.Amsawa Ammi tayi da fara'ar ta tana Masa Sannu da zuwa.Yaran ma kansa sukayo duka Suna Fadin Marbaan Abbunmu tare da karbar kayan.

Dariya yayi tare da musabaha da yaran, Nan ya Basu tsarabar su amsawa sukayi Suna Godiya,Ammi ma karbar nata tayi tana Sanya Albarka. Yaya Nabila ce Babba acikin su Nan ta zauna ta raba alawar da cakuleti ta baiwa k'annanta Aysha sai Yasira sannan Khadija da Kuma Auta Fatima,Dakin su suka nufa da littafan su Domin yayarsu ta daura masu karatun Daga inda Ammi ta tsaya,Kamar yadda Malama Juwairiyya ta tsara masu a Kullum.

Bayan sun fita Ajiyar zuciya Abbu yayi sannan ya dubi Ammi.......Yace.....

Kubiyoni Domin Jin Cigaban labari.

Comments din ku zaisa Naga dacewar k'arasa typing labarin.

Bati neh👌🏽 ba na KUD'I ba, bakin ku shi zai saya maku littafin ta hanyar suburbudou min zafafan comments.

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:31 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA BIYU_

**********Ganin basu ga Mommyn su a falon ba shiyasa su na sauya tufafi suka nufi ɗakinta.

Da sallama sunka shiga momynmu mun dawo daga makaranta. Sai dai sheshsheƙar kukanta suka jiyo murya adisashe ta amsa,tana kan gadon sai hawaye ta ke gogewa da kar su fahimci tana kuka!Da sauri Zeenat ta isa gareta tace Mommy lafiya? Ya naga kina kuka?Maryam (Maamah)tace ai kin san Yaya ba zai wuce wancan tsohuwar ba ita ce ta zagi momyn ko yau kenan!

Tsaki Zeenat tayi tace ni wallahi na tsani matar nan kamar mutuwa ta!Mama dan Allah kiyi hakuri...Bilkisu tace in shaa Allah watarana sai Hajiya Babba tayi dana sani!Saudat tace yaya kuna ganin akwai ranar da zata saduda?Tabbas akwai ranar inji Khaleesat,sai Bilkisu tace to Allah ya nuna mana....Ameen ya rabbi salma tace tana goge ƙwallah!Daga nan dai ysu ka dinga baiwa Mommyn su haƙuri, wasu akan gado sauran tsaye su na ta faman rarrashinta.

Ajiyar zuciya tayi tare da duban su daya bayan daya kaf acikin su ba maƙosa,amma a hakan kakarsu ta ke kyamatar su saboda kawai su na 'YAN MAATA.

Da ƙyar tace naji kunji,na haƙura muje ku ci abinci, kafin malamin ku yazo,rungumeta sukayi gabaɗaya suna dariya, saboda ta daina kukan!Sareena har da kwallah hakan salma da saudat su na faɗin Mommy idan kina kuka mu ma zamuyi muna sonki kece ke son mu,kamo su tayi, tare da laƙuto masu kumatu tace Daddynku ma yana son ku kunji, yanzu muje kar mallam ya jira ku,gaba tayi rike da hannun sareena yayin da sauran yaran ta su ka mara mata baya cike da farinciki da ƙaunar mommy.

A ƙofar gidan wani kangon gida,tace a dakata,gidan wata ƙawarta tun zamanin budurci,Shiga tayi gidan...Da fara'ah matar ta tarbeta tana faɗin a'ah maraba da Meri yau kece a gidan namu?

Ɓata fuska Hajiya Babba tayi tace baba Karima ina gidan?Ai wannan sunan gida ne!ƙara kallon karima tayi da gidan sama da ƙasa tayi dariya har sai da hauren ta na makka ya bayyana,Tace kango dai ba gida ba,ta mallam buzu mai shayin ƴan gayu.

Ɓata fuska Karima tayi,tace shigo kin wani tsaya,ba dole in tsaya ba inga matsugunni kai talauci baiyi ba inji Hajiya Babba.

Haba meri wannan ai wulaƙamci ne bana son haka gaskiya, Karime tace a ɗan hasale,Ke ni kinga bani ko jin daɗin sunan ga da kike kirana wai meri!kice Hajiya maryam mana.Dariya Karima tayi tace lalle duniya sabuwa maye baya ganin wutar gutsunai,hmnnnnn inda ba'a san asalin kaza ba, to maryam mu shiga daga ciki,A ah ko nan ma ya isa inji Hajiya Babba dan ta gano inda ƙawarta ta nufa.

Kujerar roba Karima ta aza mata sannan ta zauna da kyankyami,tana wani hurar hanci tare da gyara zaman gilashin ta da ke manne a fuskarta,Karima tace Meri waaai na manta maryam ya gida? kin san sabo turken wawa sai da haƙuri domin na saba.

Hajiya Babba watsar da zancen tayi tace lafiya ƙalaw ya yaran duk suna ina ne?

Karima tace sunje gidan gwaggon su Baraka basu dawo ba,

Allah sarki daman a hanya nake nace bari na biyo kai tsaye mu gaisa, sannan gobe ko jibi idan kin samu dama sai kije gidana zamuyi wata magana da ke inji Hajiya Babba

Karima tace to Hajiya Maryam in shaa Allah zan zo, ko yanzu da baki zo ba ko kirana kikayi a waya ai zanzo nan take.

Murmushi Hajiya Babba tayi sannan ta zuge zip din jikarta dubu biyar ta lissafo ta baiwa Karima, jiki na rawa ta amshe tana godiya, nan Hajiya ta wuce har kofar gida karima ta rakata tana godiya da zummar gobe zata zo tun safe.

*******Juwairiyya na gode miki a bisa tarbiyya mai kyau da kika baiwa yarana,Zuciyata na riskar farin ciki da jin dadi a duk lokacin da naga 'Ya'yana Maata da Allah ya bani, bani jin akwai ranar da zanji bana sonki ko kuma abin da ya fito daga gareki. Da ke da yaranmu kune bugun zuciyata ina ƙaunarku a raina Allah yay muku Albarka.

Tafarkin addinin Islam da kika daura su ma abin alfahari ne,haƙiƴa na yadda mace tagari ita ce take haifo yara nagari, domin anyi walkiya gari ya haska, gashi na hango zaɓina a matsayin mafi dacen zab'i a duniya. Wanda babu irin sa Allah ya saki aljanna, sarauniyar maata,uwar gida ran gida haske annurin idaniyata maman Nabeela da Fatyma uwar Aysha da Khadija Ammin Yaseera Allah ya ƙara nisan kwana ya barmu tare inji Abbu yana dariya

Ammi dariya tayi tare da rufe fuskarta cikin jin daɗi tace na gode ya sahibi ai dama duk abinda ka shuka shi ne zaka girba...Ka kasance matashi nagari shiyasa Allah ya baka macce tagari wacce ta zamo uwar yaran ka nagari duk da suna mata, Amma baka taba nuna masu wani abu ba wanda mafi akasari mutane suka jahilta,Domin a iya tunani na ƙasa gane aibun haihuwar ƴaƴa mata a ganina da mazan da mata duk ɗaya ne,sai dai muyi addu'a Allah yabamu nagari masu albarka wanda zasu mana biyayya,Allah mun gode ma da kyautar da kai mana, hakika ina alfahari da kai mai gida takobi zaki gagara gasa Allah ya barmin kai ya raya mana zuriya.

Ameen macen kwarai,ai yara masu albarka ake nema ba bambancin jinsi ba Allah yasa musu albarka, su kuma masu halin zaɓen haihuwa Allah ya shiryar da su,nikam sam bana cikin su, domin nasan komai na Allah ne.kuma duk dangina suna son yarana to meye damuwa ta?Inji Abbu yana murmushi.

Babu ita yallabai na Ammi tace tana murmushi ita ma, Abincin da zasuci ta ɗauko ta ajiye a tsakiyar katafaren falon, nan ta zuba a babban faranti,su Nabeela ta kira, nan kowa ya wanke hannunsa aka fara cin abincin tuwon shinkafa da miyar taushe wanda kabewa,nama da kifi da agusi ya walwatceta,Abincin su ka dinga ci tare da kod'a girkin na Ammi su,sai dariyar Abbu suke wanda ko damar magana bai samu ba akan daɗi...lemon abarba da kankana Ammi ta hada kowa kofi ya ɗauka ya sha. Sai sannan Abbu ya samu damar fadin Alhamdulillah Ala kulli yaumin.

Had'a baki sukayi daga Ammi har yaran gurin fadin Masha Allah.

More comments More typing Idan ba'ayi ba zan mayar da shi na kuɗi👯🏽‍♀️

*YAR MUTAN DIKKAWA CE* [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA UKU_

*GORON JUMMA'AH* _Ina taya d'aukacin jama'ar musulmai murnar zagayowar ranar jumma'ah Allah ya sadamu da alheran sa Aamin BARKAAH DA JUMMA'A_

~Tunatarwa Kada mu manta da karatun suratul juma'at,Khahfi,Ikhlas,Salatin manzo,Istigfari da Hailalah~

************************ _WASHEGARI_

Tunda ta sallame sallar asuba ta ke cikiniyar d'aurawa yaranta abincin su na kari,da wanda zasu tafi makaranta da shi,Zeenat,Khaleesat da Saudat su ne 'yan maata acikin yaran shiyasa suke taya sauran ƙannansu shiri, har suka sa tufafin su na makaranta,

Duk wannan didimar ta kula da yaran ita kaɗai keyi sai manyan acikin su da ke tayata,Bayan sun karya kowannensu jikka da ƙwandon abincinsa suka ɗauka suka fice daga gidan sai kewar mommynsu suke,Addu'ar dawowa lafiya mommy Halima tayi masu, sannan ta dawo ta cigaba da ayyukan gidan kafin mai gidan ya sauko daga saman sa,Kasancewar gidan na da yawa shiyasa Halima ke famar aikin gyaran sannan ta daura girki ga kula da yaranta,ga shi Hajiya Babba ta hana a dauko mai aiki a gidan bare ta taya ta aiki, a cewarta waai ai duk 'YAN MAATA ne a gidan sai suyi aikace-aikacen.Wannan dalilin ne yasa Hajiya Halima ke matukar shaan ayyuka a gidan musamman yanzu da hutun yara ya kare su ka koma makaranta,Domin idan suna hutu ta riga da ta raba masu ayyuka kowa da wanda yakeyi.

********************** Da misalin karfe sha d'aya da rabi da minti uku zaune ta ke a uwar dakin ta tana lazimi da salitin manzo da hailala bayan ta gama sallar walha(Dhuha) da Azkhar,Tana cikin addu'a ta jiyo sautin muryar da ko a mafarki tajita zata gano mai ita,Tana sallama.

Shafa addu'ar tayi kana ta tashi,Da sauri ta ƙarasa falon,murmushi ya bayyana a fuskarta tace sannu da zuwa Umma ina ciki ina sallah Bismillah zauna,An tashi lafiya?

Wacce aka kira da Umma ne tayi dariya tace Lafiya kalau,Juwairiyya. Haba biri yayi kama da mutum...Nikam naji shiru nace ba dai bacci ba yanzu da safen nan.

Umma baccin dai ma nakeji tun safe idan na tashi bana kwanciya,Inji Ammi tana hamma.

Umma tace to ku sassautawa ibadar nan hakan juwairiyya Addini fa sauki gareshi,kuyi tashin dare, sannan tun kafin asuba kuyi rakatanil fijir,Bayan asuba kuma kuna zaune har gari ya waye,Kowa ya fita aiki ke kuma kin koma zaman ibada, haba rai nason hutu ina laifin kinyi Walhan nan sai ki ɗan ƙwanta ki huta!Uhmnnnnn Allah ya sa mudace.

Aameen Ammi tace, tana murmushi da jawabin umman nasu.

Duk ina mutane na, ko sun tafi makaranta?Har manyan.

Eh...umma duk an fita kafin a dawo,Inji Ammi

To yau ina nan har sai sun dawo inji dalilin da yasa aka daina zuwa inda nake har tsawon mako biyu.

Lallai umma sunyi laifi...Ni dai ina gefe...Domin na san ba su da mafita inji Ammi tana dariya.

Umma dariyar takeyi tace barni da yan karen ga ma hade da su anjuma...Am umma bara na hadou mana abin kari kafin na daura sanwa,tunda ma kinzo sai ki zaba mana abincin da zan dafa da rana,tun dazu nake tunanin me ma zan dafa?

Ai kuwa da wake da mai da yaji zaki dafa mana, sai ai mana hadin ganye inji umma tana murmushi yayin da ta cire hijab dinta.

To shi kenan umma, haka za a yi. daga nan madafa Ammi ta nufa, shayi mai kauri ta hada da kwai da dankalin turawa, duk ta lodo su a ture nan suka zauna ta hadawa umma na ta sannan ita kuma ta hada nata, su ka karya suna fira,

Bayan sun kammala kwashe kayan tayi ta nufi madafa,Nan ta daura sanwa,Umma ce ta sameta madafan har da tilasta ta waii dole itama sai ta tayata aikin,Ammi dai gyaran wake ta bata da aka zuba,Kuma Umma ta nace akan ita zata hada hadin ganyen,Ba domin Ammi ta so ba,Ta barwa umma. su na aiki a madafa su na fira da dariya abin su gwanin sha'awa tamkar ba uwar miji da suruka ba.

**************** To karima kin dai ji dalilin kiran ki,Ina fatan bazaki watsa min k'asa a ido ba!Inji Hajiya Babba tana kallon kawarta karima.

Numfashi karima ta sauke tace Haba Meri wanda ke kan dutsin ai baya tsoron wasan jifa,wallahi naji dadin wannan magana kuma na yarda na amince ina goyon bayan ki,Ai da ka aifi matar gwamna gwara gwamna ka aifo domin ko an ki ko an so da uwar gwamna za a kiraka,ba da uwar matar gwamna,wannan ai shirme ne naji ana fadin da ka aifi gwamna gwara matarsa,Inaaa ai bazata sabo ba!Dan haka kinyi min dai-dai.

Murmushi Hajiya Babba tayi wacce ta hade acikin wani mayen leshi da akai mata bubu,ga zobba da murjani da awarwaro masu tsada da ta zuba,ta sha jan lalle abu ga farar mace yayi mata jajur...Ta wani hakimce acikin lumtsuma luntsuman kujerinta irin ma masarauta,Kafafuwan ta saman tutumi tana fuskantar katuwar talabijin din ta, ta bango....Ta dubi karima tace to yanzu karima ke nake sauraren duk yadda akayi sai ki kirani.....

Amshe zancen tayi to Hajiya maryam babu matsala!nifa ta gefena ba wata damuwa ai abokin kuka!ake fad'awa mutuwa na san komai a nan.

Kedai kiyi yanda nace ai ba don tsawo akan ga wata ba,shawara abu ne mai amfani kuma tana bukatar lokaci.Inji Hajiya Babbba

Karima tace haka ne kuma nan ta dinga cin naman kaji da lemon roba,wanda Tani mai aikin Hajiya ta ajiye mata,Ci takeyi tana kora fanta da faro kamar mahaukaciya

Yake Hajiya tayi tare da girgiza kai tace Aah sarki karima kice an dade ba a hadu ba?Wallahi ko Hajiya bari ke kam kinji dadi ki goge baki da cinyar kaza ki kuskura da fanta Allah dai ya kai giwa inji karima tana ya gar naman kaji .

Dariya Hajiya Babba tayi har da kifewa tace Allah ya rabawa kowa da cutar talauci....Amin karima tace tana gyatsa!Nan ta tattara sauran naman ta zuba ajika tace to Hajiya ni zan koma.

'Yar aiki Hajiya ta kira da sauri tani ta shigo,Tace Hajjaju gani... kije daki na ki dauko min dubu biyu to Hajiya,Tani tace da sauri ta bar falon.

Kudin ta kawowa Hajiya,Tace karima gashi ki hau adaidaita,Amsa karima tayi tana godiya,Tani...Na'am Hajiya,Ki karowa kura nama bai isheta ba sai akaiwa yara...Karima washe baki tayi tace ina ko nama ga isar kura meri tunda ba da shi aka haifota ba ita ma daga sama ta samu idan Allah ya baka dama sai ka dama mu ma wataran idan da rabo sai mu zamu in Allah yace Inji karima tana murmushi

Naman Tani ta mikawa karima ta karba sannan ta wuce tana farin ciki,Tsaki Hajiya tayi tace Shin talaka ko'ina sai ya nuna Hali....Tani dariya tayi tace kwarai kuwa Hajjajou.

More comments

More typing

'YAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA HUƊU_

_Jinjinar ban girma ga masoyan UWAR 'YAN MAATA, Hajiya Halima ta ce,A gaishe ku,Haka Hajiya Babba ta ce tana nan daram mai hali baya fasawa_😅

```Godiya Ga jama'ar gidan'Yar mutan Dikkawa novels place,da UWAR ƳAN MAATA FANS,Da Only Nabila's fans group,ban manta da ku ba yan gidan Nabeeha novels group da Hubby group duk ina godiya da comments din ku a cigaba da suburbudouwa ni kuma ba zan gaji da sanbadou maku ba.``` ******************** Cikin shirin sa tsaf ya sauko daga saman sa, sai ƙamshi ya ke zubawa, Domin Alh.Bello Babale ba baya ba,fagen ɗaukar wanka da ƙwalliya,yayi kyau matuka kallo ɗaya ba zaka fasalta masa haihuwa tara ba, kai tsaye. Idan ka dubeshi zakace shekarunsa basu kai talatin da ɗauri ba,Kamar wani ɗan sha tara haka yake kullum.

A falon ya sameta tana kallon sunna t.v,Kyakkyar mace mai dagargazajjen jiki lukuta da ita zubi da tsarin dirinta mai kyau ne, launin ja da ɗourawa shi ne zubin fatarta,duk da shekarunta bazasu wuce talatin da uku ba, amma gata caƙwai kamar budurwar da bata haihu ba,sai ƙamshi takeyi kamar wacce zataje gasar ado,kallon ta yayi tare da lumshe ido...Har ya ƙaraso inda ta ke.

Tashi tsaye tayi da girmamawa tace Alhaji barka da fitowa,an tashi lafiya?

Lafiya law Halima,na tashi lafiya, yace a gajarce

Alhamdulillah...Tace

Briefcase ɗinsa ta amsa, ba musu ya sake mata...Nan tace ga breakfast can a dining yana jiran mamallakin sa.Kamar yace,A'ah sai kuma yayi murmushi domin daga jiya zuwa yau akwai tunanin da yakeyi akan Halima,shiyasa ya fice ta na biye har inda aka tanadar masa da abincin sa,ajiye jikarsa tayi a ɗayan kujera,sannan ta duƙufa da haɗawa Alhajinta abin karyawa.

Zaune tayi gefen sa tana murmushi a lokacin da yake cin abincin...ga ƙamshin turarenta da nashi ya gauraye sai ya ba da wani daddad'an kamshi na musamman.

Cokali Alh.Bello ke aunawa a bakinsa wani na bin wani tare da lumshe idon sa tabbas abincin Halima na dabam ne, kuma idan yace zaiyi masa yaji! to yunwa zata samu muhalli a rayuwar sa.Saboda dad'insa da d'and'anon sa na dabam ne,Halima ruwan gora ta zuba a kofi ta baiwa Alhajin a baki ya shaa,Zuciyarta fal da farin ciki domin ta ga alamar rayuwar su ta da Alhajin ta kamar zata dawo yanda ta ke,Ya ci abincin sosai sannan ya tashi yace to madam ni zan wuce shago Ina son na zaga sauran kantunan Naga abinda ke wakana....Narkewa Hajiya Halima tayi tace gaskiya Baby nifa kamar kar ka tafi sai ku barni Ni kad'ai a gidan,But neman halal ne Allah ya tsare,ya kiyaye min kai, Allah ya baka sa'a da nasara da kuma kasuwa mai Albarka.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull