Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 2

Uwar y'an mata complete - Chapter 2

Uwar y'an mata complete Chapter 2: Uwar y'an mata complete Chapter 2. Murmushi Alh.Bello yayi yace Aamin my Halimcy...Har sun kai kofar fita falon cikin…

4,500 words

Murmushi Alh.Bello yayi yace Aamin my Halimcy...Har sun kai kofar fita falon cikin jin daɗi da soyyaya sai Halima tace uw Alhajina ina zuwa minti biyu,Da sauri ta nufi madafa,Wata hadaddiyar kula ce ta dauko dayan hannunta rike da flask cikin basket mai zip,ta kawo inda yake tsaye yana jiranta...Ya ce menene tace samosa neh wannan ruwan shayin na'a na'a ne, na had'a maka,idan kaji yunwa kafin na aiko abincin rana sai kaci, kasan bana son ulcer ta kama min kai..."

Dariya yayi yace nagode Allah yayi miki Albarka Halima, Allah ya ƙara kare mu daga sharrin miyagun shaidanu,wallahi ina sonki amma wataran sai naji na tashi da jin haushin ki,Ina jin duk duniya ba wacce na tsana kuma bana son gani kamar ke.

Numfashi ta sauke ranta a jagule!da Jin maganarsa!Da k'yar ta iya saita nutsuwarta,washe bakinta tayi tace Ameen Abban Mamaah,Ni kaina nasan ba haka kake dani ba,zuwan abu ne amma Allah ya shiga tsakanin mu da duk damuwar mu.

Yace ba daɗi amma ki ƙara haƙuri zan kula,To in shaa Allah, jiki asanyaye domin a zuciyarta ta tsorata kuma ta gasgata zancen sa, saboda haka yake yau mutum gobe ba mutum ba,Amma addu'ah makami ce kuma maganin komai.

Har mota ta rakashi tana masa adawo lafiya,Tace Alhaji karka manta Addu'ar da Manzo (S.A.W) ya baiwa 'yan kasuwa irin ku masu SANA'A wato ;" ```LA'ILAHAA ILLALLAHU, WAAHDAHU LAA SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU, WAA LAHUL HAMDU, YUYYII WAAYUMUTU WAA HUWA AYYUL LAA YA MUTU, WAA HUWA ALAA KULLI SHA'IN QADIR.

MASHA ALLAH MAR'ATUSSALIHA NAGODE IN SHA ALLAH ZAN DINGA KARANTA TA A DUK LOKACIN DA ZAN B'UDE SHAGO KO KAYAN SANA'ATA. ``` Inji Alhaji Bello Babale,Yana duban Halima.

Murmushi ta mayar Masa Mai sanyi,ita ma

Da murna yabar gidan nasa zuciyarsa wasai,Ya nufi kantin sa. Halima ma ba laifi da farin cikin ta Koma daga Cikin, kowa da abinda yake rayawa a zuciyarsa.

*WAIWAYE....* Alhaji Kabiru Balale shi ne ainihin sunansa mazaunin garin kano ne a unguwar fagge,Yana da mutunci sosai Baki ne wulik ainihin bakane, Dan kasuwa ne sosai wanda yayi suna a garin kano fannin kasuwanci,Yana da manyan kanti a kasuwar kwarai da kuma unguwannin garin,Su biyu ne iyayen su suka haifa shi da kanin sa saminu bayan iyayen su sun rasu daga baya shi ma saminu ya rufa masu baya.Shiyasa Alhaji Babale ya kasance maraya kuma shi kadai bayada kowa duk danginsu sun mutu,Domin zuriyar su suna da k'aramcin haihuwa kowa 'ya ko d'a d'aya yake haihuwa a tarihin ziriyar su kuma nan da nan iyayen su da kakanni sun mutu.

Alhaji Babale ya auri Hajiya Maryam wacce akafi sani da (meri Mai dawo) A wancan lokaci itama tana rayuwa a cikin fagge kuma idan za'ayi lissafin manyan 'yan tallar dawo da nonon a unguwar fagge, to meri tana cikinsu ita da aminiyarta karima wacce sukewa laqani da KUD'I ko na waye(Sai kin ci)Meri da karima makota kuma tare sukayi tashen budurci da tantiranci acikin unguwar Domin har gefe suke da shi na Marasa mutunci,Ba ta'addancin da basuyi Kuma Basu tsoron kowa har kirari da wak'a unguwar fagge take da shi Saboda sun shahara a garin na kanon dabo.

Sanadin sayen furar da Alhaji Babale keyi gurin meri har soyyaya ta dinke a tsakanin su,Iyayenta sun ga dan kasuwa mai kudi basu tsaya bata lokaci ba akai aure daman daga Babale har meri basuyi boko ba sai muhmadiya wanda shi ya fi ta ilimi sosai a gefen addini.

Sun d'auki tsawon lokaci kafin su sami rabo wanda har malamai meri ta fara bi dan kawai ta samu haihuwa ta ci gadon Babale ko bayan ransa.Cikin ikon Allah ta samu ciki bayan watanni tara ta haifo santalelen d'anta wanda yaci sunan kakan sa uban Babale wato Bello shiyasa suke kiran sa da (D'an Inna) tun da ya tasa mahaifinsa ya turashi kasuwa a hankali Dan inna ya iya kasuwanci amma akan ya nace yana son boko shiyasa baban sa ya saka shi makaranta,Yayi firamare da sakandare a shekarar da zaije jami'a ne Alh.Babale ya rasu,Wannan dalilin yasa ya cigaba da kasuwancinsa ya ajiye zancen karatu domin daman wannan shi ne burin marigayi mahaifinsa.

Bello fari ne kyakkyawa mai kakkauran jiki,yana da tsayi da manyan ido,ga shi da saje suma ce luf kwance a kansa,mutum ne mai tsafta da kyankemi kuma marar so magana,yana da kwarjini sosai.

A hankali ya dinga kula da meri wacce ta dawo Hajiya maryam ya gina mata katafaren gida a jan bulo sannan ya zuba mata 'yan aiki,Mai gadi,Direba da kuma Tani mai aikin abinci.Yana son mahaifiyar sa sosai kuma sanadin sa yasa har yanzu ba ta kara aure ba,saboda ko taso tayi Bello ke hanata a cewarsa shi bazai amince tayi aure ba,kasancewar macce mai son kudi da daula da cin dadi kuma tana samu shiyasa ta watsar da maganar aure tayi zamanta tana cin duniyarta da tsinke,ta ci ta shaa ta zuba ajikinta.

Maryam wacce Alh.Bello ke kira da (Hajiya Babba) da sauran 'yan uwanta tana da masifa da son wulakanci sannan tana da kyauta amma kuma alokacin da ta baka a nan take ma gori ko wulakanci shiyasa idan ba mai zuciyar kaji ba,Ba mai karfin Halin cin abin hannunta.

Bello ya hadu da matarsa Halima a makarantar da ya shiga ta degree wanda ake zuwa ranakun karshen mako(Saturday/sunday)Daga nan soyayya ta kullu a tsanin su har su ka kammala karatun su,Halima tana ilimi ga kirki da hakuri kuma kyakkyawa ce jinin fulanin Adamawa zaman aiki ya zaunar Iyayen ta kano,su na na zaune a tarauni 'yar masu kudi ce sosai kuma ta taso acikin gata kasancewar yayyenta maza uku ita ce auta kuma macce acikin su,Sunan Mahaifinta Alh.Musa mamanta kuma Hajiya Saudat,sai yayyenta Halidu,Haruna da Hamza.

Anyi auren Alh.Bello da Hajiya Halima a bisa soyayya da kuma amincewar iyayen su.Kusan shekara daya da rabi babu motsin komai nan Hajiya Babba ta dinga zarya neman taimakon Haihuwa a cewarta kila Halima juyace bata haihuwa,ta manta da waye Ahlin Bello, domin da haihuwar ta wadace su da ita ma ta kara daga dayan Amma maye baya ganin wutar gindinsa.

Auren Bello da Halima ya zamo na arziki Saboda tun Auren ta komai ke hab'aka,ta ko'ina arzikinsa da na kasuwancin sa ya b'ude,Har katafaren gida ya Koma ginawa Mai Kama da sumfarin waje,suka Koma a G.R.A,Manyan kantuna ya b'ude ya zuba Yara,Hajiya ma ya gyare Mata gidan ta sai Sam barkah.

Watarana Halima ta tashi da zazzabi bayan anje asibiti nan likita ya tabbatar da tana da ciki nan fa murna ta mamaye kalbin Bello da Hajiya,So da kauna da kulaw babu wanda Halima bata gani a gefen dangin mijinta da iyayenta musamman Hajiya Babba kamar ta hadiyeta dan so,Wata tara cip ta aifo zeenat daga nan duk shekara sai ta haihu ga shi ko tayi planing bayayi tana ciki tana haihuwa babu tsaiko har ta haifo 'ya'ya MAATA tara a duniya.Ba tare da sanin ta ba Bello ya shirya da likitan su akacire mata ma'haifa kamar yadda Hajiya Babba ta tsara musu yadda za'ayi shiyasa suka cewa Halima wani sabon tsarin iyali ne daga kasar waje sai anyi aiki a hakan ta yarda. domin ta tsani kuma ta gaji da irin tsagwamar da su Hajiya Babba ke ma ta.

Saboda tun da Halima ta fara haihuwar mata,Dan kawai bata samu D'a namiji ba, shi kenan uwar mijinta ta daina sonta ta juya mata baya,Har yaran ta tsane su da hakan har danginta suka maara mata baya,shiyasa Halima ta zamo mujiya a cikin su ita da yaranta duk da Allah yayi masu baiwar kyau gaba da baya amma a hakan ake kushe su dan kawai su na maata ita kuma har suna suka saka mata suna kiran ta da shi wato *UWAR 'YAN MAATA*

Babu kalar wulakancin da Hajiya batayi mata a hankali da zuga ta yau da kullum har Alh Bello ya fara daukar karatun mahaifiyar sa shima yabi sahunsu sai dai shi kam yana son yaran wataran kuma har su nuna tsanar su yake amma bai ragesu da komai ba ci,sha,sutura,da duk lalurorin su dana ilimin su.A kullum mahaifiyar Halima k'ara jaddada mata takeyi akan tayi hakuri ta dage da addu'a watarana sai labari kuma ta cigaba da amsa sunan *UWAR 'YAN MAATA* da su ke kiranta da shi,Domin mata rahama ne, Mata haske ne,Mata arziki ne.Wannan ke sa Halima taji komai ba komai ba sai domin zuciya batada k'ashi.

A cigaba da zafafan comments labari mai dad'i ya na zuwa........

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE* [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers Forum_

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA BIYAR_

*Ba abin mamaki bane,dan mutum ya canja sheƙa,saboda haka mu zamanto masu fahimta mai kyau,za'a haifi mace a gidan su, kuma ta girma a gidan wasu,Allah yasa mudace Amin.*

```Wannan Shafin naku ne ƙawayen Arziki``` ```Hubby Hussain (Amarya) Hassana Danlarabawa,

Khadija Uthman,

Fadila lamidou sai

Ayshetulumaira (maman Khalil)

Rabi Sidi, Nabeeha Ameenu tawa

Nabila lady &Nabilancyluv

Duk Na gode da kulawa Allah yabar Zumunchi Amin, Ina maku son so fisabilillah ``` *********************** Alh.Garba D'an K'asa shi ne sunan mahaifin Alh.Habib D'an K'asa,Mahaifiyar sa Hajiya Zainab mutuniyar kirki ce Suna Zaune Lafiya mijinta har lokacin da mai rabawa ta raba, Marigayi Garba ma'aikacin gwamnati ne ya rike muƙamai da dama kafin ya rasu,yana da ilimin Addini da na zamani,yana da ƴaƴa hud'u a duniya duk maza,Habibullah,Hamisu, Halilu, sai Abbakar. Bayan rasuwar Alh.Garba da shekara ɗaya, watarana gobara ta tashi a gidan cikin dare inda tayi sanadiyyar mutuwar Hamza,Hamisu da Halilu lokaci ɗaya, Hajiya Zainab ma sai da tayi jinya domin ita kad'ai ta fita.

A lokacin Habibu yana kudu wurin bautar k'asa, komai su Hajiya Zainab basu fita da shi ba, bayan rayuwarta da tasamu yayin da rayuwar 'ya'yanta uku wuta ta cinye su kurumus. Hajiya ta shiga tashin hankali har ta nemi zaucewa akan abinda ya faru,bata baccin rana bare na dare,yaranta ke gani yayin da su ke kururuwar neman agaji suna ambato wayyo Umma wuta!Umma wuta ta kama jikina!Umma wuta...."Wannan shi ne abinda ta ke tunawa da shi.

Da ƙyar aka shawo kan matsalar ta, da taimakon Habibu wannan yasa ya kasance shi kad'ai agurinta kuma yana kula da Umma (Hajiya Zainab) sosai.

Lokacin da ya samu aiki a ma'aikatar (ministry of education) ne, akan yana Albashi mai tsoka ga sabgogin da yake samu shiyasa ya ginawa Umma gida,sai suka tashi daga gida Haya domin gidansu na da ya ƙone ƙurmus. hakan su ka cingaba da rayuwar su har Allah ya had'a shi da Juwairiyya Mukhtar, tana kirki da ilimi 'yar gidan manyan mutane ce mahaifin ta yayi suna sosai mazauna garin kaduna ne, Unguwar Rimi gidan su yake ta karanci (Islamic studies) a jami'a shiyasa take da ilimi sosai,Sunan mahaifiyar ta Hajiya Ruƙayya tana da yayye Isma'il, Abdulllahi sai ita Juwairiyya sannan Nabiha da Fauziyya.

Juwairriyya kyakkyawa ce wankan tarwad'a mai tsayi da Jiki,bayan sun shafe shekara ɗaya da haɗuwa kuma soyayya mai tsafta ta ɗinke a tsakanin su,daga nan magabata suka shigo har kawowa auren su da aka ƙulla yadda addini ya tanadar.

Juwairiyya ta sunyi aure da Alh.Habibullah yanzu kusan shekaru goma huɗu, Suna da yara biyar duk Mata Nabila,Aysha,Yaseera, Khadija sai Kuma Auta fatima, su na zaune Lafiya ita da mijinta da Kuma surukarta da duk sauran dangin mijinta.

Macece Mai fara'ah kyauta da kuma son Alheri,abin hannunta baya had'a ta da kowa ga ta tsafta da rikon Addini,Hakika duk inda za a lissafa Mata nagari to Malama Juwairiyya zata zo a sahun farko,har islamiyya ta ke da ita ta kanta Wanda take zuwa da dare ita da yaranta Suna koyarwa Kuma gwamnati ta d'auki nauyin biyanta sanadin kokarin ta. Sannan mamba ce a kungiyar kare haƙƙin mata da sauran su.

Arziki da buɗi sai ƙara gangarowa yakeyi a gidan Alh.Habibulah (Abbu)Domin har ƙarin girma akai masa shiyasa ya samu damar tura kuɗaɗen sa a jihar Kebbi, inda Aminin sa Alh.Yusuf Waziri domin a dinga yi masa aikin shinkafa. Saboda jihar ta Kebbi jihace mai Albakar ƙasa da albarkokin albarkatun noma, musamman garin ARGUNGU wanda ya kasance garin noman arziki, dan kuwa idan shinkafa kakeso to kazo Argungu kai da yunwa sai bad'in bad'ad'a, a zahiri shugaban k'asar nijeriya Muhammad Buhari da kansa ya jinjinawa garin tare da basu Lambar girma a fagen noma tushen arziko,don su ne haziƙan manoman NIGERIA.

Alh.Habibullah yana aikin gona, a gefe kuma ya b'ude gidan sayarda Man fetur mai suna ( *'YAN MAATA PETROLEUM*) da gidan ruwan gora ( *JUWAI TABLE WATER*) da kuma Gidan bololuwa ( *UMMA BLOCKS*) yanzu hakan ta ko'ina Alh.Habibullah Yana samu,mutum ne mai son kasuwanci duk da yana aiki amma ya riƙe sana'oi,shiyasa ya ƙara samun buɗi. ya tamfatsawa Umma sabon gida ya saka 'yan uwanta na k'auye da ƴan aiki, Kasancewar Umma Yar Yola ce mahaifinsa ne ɗan jihar ta kaduna.

Da gidan sa zuwa gidan na Umman sa ba nisa, duk a Sultan road kaduna,suke zaune ba wata matsala sai jin Daɗi da san barka.

*CIGABAN LABARI...*

A ƙofar ɗan rukub'abben gidan ta mai napep ya ajiyeta,fitowa tayi tare da d'auko jikkarta,ta sallame shi sannan ta wuce cikin gida.Da sallama ta shiga.

Wata matashiyar budurwa ce da ke durk'ushe gaban murhun da ke hayaki,tana faman hura wutar ne ta waigo tare da amsa sallamar idonta yayi jaa saboda hayaki tana taje majina,Tace Mamma har kin dawo?

Eh Safara'u na dawo sannu da aiki ita Gimbiyar tana ciki ko?

Eh...mamma tana can tana ibadar ta Bacci ta ke, yanzu hakan na tasheta yafi a kirga tayi sallar azahar amma tayi biris Inji Safara'u.

Ajiyar zuciya Karima tayi Tace ita ta sani,jeki d'auko min faranti...Washe Baki Safara'u tayi Tace mamma kice kin yo Mana samuwa gidan manyan gari,Sosai ma kuwa yarinya me kika Daura halan?Fara da Mai da yaji...Yar kullum Safara'u Tace a lokacin da ta d'auko faranti acikin ƙwadon da suke ajiye mataccin ƙwanonin su,da ke tsakiyar gidan saboda ko store babu bare kicin agidan,ɗaki ɗaya ne sai bayi duk na ginin laka.

Amsa Karima tayi tare da zubawa a farantin ta k'asa Kashi uku Tace ki dauka tunda wancan Bacci take sai ki ajiyewa Tasi'u nasa nasan yanzu zai dawo daga makaranta ungo Wannan fanta ce kowa Daya.Amsa Safara'u tayi Jiki na mazari yawun ta na tsinkewa, Tace wai yaushe rabo mamma?Dariya Karima tayi Tace sha kuruminki yarinya kinyi kusan ci har ki ture!Ni kinga yanzu hakan ko kin gama gare-garencan ba cinta zan ba, Saboda naci naman kaji da lemon kwalba na ƙoshi,wannan kuma na cikin jikka da dare zanci abina in ƙwanta, yau bana Jin zan iya cin komai a rayuwata bayan naman kajin nan da lemon kwalba.....Dariya Safara'u tayi Tace duniya sabuwa mamman mu, kina shagali to a Ina zakici wannan nikam dai mamma!?Me kikewa sauri safarah?zaki ji.

Cikin Bacci ta jiyo Muryar Mamma da Safara'u suna dariya wanda sautin maganar su ke nuna bakinsu a cike yake, tunanin tayi biredi yau aka samo agidan ake ci,Tashi tayi tana hamma cikinta sai kugi yake saboda tsabar yunwa,Domin ba isasshen abinci suke samu ba, bare su ci idan anci na dare, na safe gagara yake, haka idan anci na safen sai na Daren ya gagara, wataran sai mamman su tayi surfe ko dawon kuɗi suke samun na gari ko ƙanzo,

Tafiya takeyi kamar zata karye,har da tangaɗi don yunwa! tana fitowa ƙofar ɗakin taci karo da su zaune suna cin naman kaza,murza idonta tayi kardai mafarkin da takeyi kullum shi ne har da tana a farke! B'ude idon ta ta sakeyi tare da haɗiye yawu,dariya Karima tayi tana kallonta Tace ke Zillaziya b'ude idonki Ras a faranti kaza ce ba mafarki kike ba!A suƙwane ta zo ta zauna tare da b'ude kafafuwanta Wuuuuf ta ɗauke cinya ta kai bakinta, ta fara ci,ƙwace farantin Safara'u tayi Tace,kinga matsalar ki Yaya zillah! wallahi ke azzaluma ce bakida lissafi amfaninki ɗaya ki ci, amma idan aiki ne kece abaya sai dai ni baiwarki inyi!To kasonki da na Tasi ne kika haɗe hadamammiya!

Ke Bana son rainin hankali, ki sake min farantin to...Zan gyara kason na d'auki nawa...Inji zillaziya wacce ta cika Baki da nama...Safarau Tace ba zanyi ba,halin ki ne ban sani ba...ko yanzu ai kinci kuma bazaki rabon na gaskiya ba! Safara'u ta karashe maganar tana fizgar kafar kaza.

Mamma ki Mata magana zan ɗauketa mari akan naman nan wallahi... Inji Zillaziya a fusace!

Karima Tace ke Safara'u sake Mata...ke Kuma kiyi rabon tsakani da Allah nasan ki da zalinci Tom.

Tuɓure Baki Zillaziya tayi Tace to mamma zan ƙwatanta!

Kinji ko mamma...Inji Safara'u tana hararen Zillaziya,daga nan fad'a ya kaure a tsakanin su har da dambe akan Naman kazar,Ƙarshe fad'a karima ta dinga masu ta raba naman da kanta,sannan suka dawo ga cin naman suna hararen juna!

Karima Tace to ku ƙwantar da hankalin ku in dai naman kaji ne, ku kusa fara daina fad'a akansa, zan sanarda da ku wani labari Mai Dad'i.......

MORE COMMENTS MORE POST

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA BAƘWAI_

***************** BAYAN MAKO ƊAYA

Yau ta kamar ranar Assabar, ba Boko sai Islamiyya shiyasa Umma ta tattara su Nabeela domin suyi mata rakiya,bayan sun dawo daga makaranta, gidan 'yar uwarta Hajiya Arziki suka nufa, wacce ke zaune a Jan bulo ta kanon dabo.

A lokacim da su ka isa sun sami tarba ta musamnan a gurinta, Nabeela da su Aysha suka dinga jero mata gaisuwa a ladabce,murmushi Hajiya Arziki tayi da jin daɗi ta amsa, tana mai jan su wasa da raha,Ta ce "Kai Barkallah yanzu Haj.Zainab duk yaran gurin Habibullah ne?Umma Ta ce" ƙwarai kuwa, kin gansu ziƙa-ziƙan 'YAN MATAN TUSA tana dariya, tuɓure baki Yaseera Ta yi, Ta ce" kai Umma wane na tusa Khadija ta amshe Ƴan mata dai,nan Hajiya Arziki ta kawo masu ruwa da kayan motsa Baki.

Bayan sun jiƙa maƙoshin su Hajiya Arziki ta dubesu ta ce" ikon Allah ke da jikokin nan na mu gwanin sha'awa gaskiya kun burgeni,wai har yanayin shigar ku kala ɗaya,duba jikinta Umma tayi ta ce kai Haj.Arziki ni na dai saka ne dan ra'ayi na amma ban kula da leshina ya yi ruwa da atamfar su ba da bazan sa ba, Nabeela ta tuntsure da dariya tana faɗin Umma ai wayo mu kai maki, sai da muka ga kalar lace ɗin,shi ne muka saka atamfar mu irin kalar sa, kinga dai munyi ankon, murmushi Fatima tayi ta ce Ummana ki barsu Yaya ko yanzu kin caresu ina super Holland zata kama ƙafar wannan lace mai tsada....Ƙwarai kuwa kedai Autalele shiyasa nake sonki,domin ke tawa ce,Haɗa baki sukai Umma mu fa ba naki bane?Dukan ku nawa ne amma Auta ta musamman ce.Hajiya Arziki kamar tayi hawaye don ta samu abin kallo, a zuciyar ta tana tunano ina ma ace ni ce da jikoki na hakan?

Haj Zainab tana fira da yaran har ta jehowa ƙawarta tambaya amma shiru, Ta ce Arziki...Arziki...Arziki..firgigit tayi ta amsa, Zainabu me kikace?

Yaran ta duba da murmushi ta ce jikokina dan Allah ku koma daga falon can na farko,zanyi magana da Haj.Zainab yanzu za'a kawo muku abin ci.

Umma ta dubeta ta ce wai Lafiya naga kamar kina cikin damuwa?

Hawayen da ta ke ƙoƙarin shanyewa ne su ka gangaro mata ta ce lafiya ba lafiya ba Zainabu.

Haba! ai komai ya yi zafi!maganin sa Allah, me zaisa ki zubda hawaye hakan?ya kamata ki godewa Allah, dubi cikin irin ni'imar da ki ke ciki mana...Inji Umma da damuwa.

Hawayen da ke zuba Zainabu daga zuciya ta ne, ba daga ido na ba, bare na shanye su,kin san kusanci da igiya babu kamar turke...To haka kusanci na dake yake, babu wanda nake faɗawa damuwata daga Allah sai ke aminiyata kuma jinina abokiyar ƙurciyata.

Zainabu Ina cikin damuwa mai yawa, fiye da wadda kika sanni da ita a baya,yanzu abin ya tsananta har na fara tunanin wannan baƙar ƙaddara zata samo ajalina! kinga rabona da insa Isah,Ibrahim Musa,Samaila da Kabir a idona har na manta!

Ashe haka wata haihuwa ta ke?meye amfanin jin daɗin nawa?meye amfanin daular?meye amfanin rayuwar da nakeyi?Ace ina da 'ya'ya maza har biyar amma ganin su yayi min wuya bare abinda suka haifa!

Kinga shi Alh.Isa yana Dubai zamansa da iyalansa,shi kuma Dr.musa yana India shi ma sai Engr.Kabir shi yana can London, Ambr.Ibrahim yana China, shi kuma Brr.Sama'ila da yake nan Nigeria,a Abuja fa amma ba zuwa yake ba.

Kin san komai duk yaran nan ni ce na haifesu,kuma tun bayan mutuwar uban su nake faɗi tashi akansu,duk abinda na tara akan karatunsu ya ƙare,yanzu da ya kamata in more inji daɗi su, shi ne suka zaɓi matan su akaina,su na ƙasashen waje zamansu. Har ɗiyayyakinsu ban sani ba,wai yaransu basu son zuwa Nigeria, da matansu, iyakacin su rayuwar turawa sun manta dani uwar su....goge ƙwallah tayi ta ce sai dai kira a waya ko aiken kuɗaɗen Abin ci tsakanina dasu tamkar waɗanda su ka ajiye abar kiwo wai ni Arziki zasu wulaƙanta! Na Abujan ma yana shekaru bansa shi a ido ba!yanzu hakan ba zan iya lissafo miki sunan ƴaƴansa ba duka,sai dai in gansu a hoto,Ni da jikokina amma basu sanni ba!Kuma basu damu da ni ba, dole nayi kuka domin na haifawa uwayen wasu 'ya'ya.

Ina da labarin dukkan matan su iyayen su, na cikin daula har 'yan uwan su ke zama gidajen yarana!kowacce surukata gidan da iyayenta ke ciki yafi gidan nan nawa duk kyaun ga nashi,amma bai kai na iyayensu ba, Kinga kuwa su ne na haifawa,tabbas na yarda da maganar nan da ake cewa"Da ka haifi gwamna, gwara ka haifi matar sa" don gashi na haifi mazan amman suna can cikin duniya suna bautawa matan su da danginsu, gani ni uwarsu in gansu ma ya zame mani aiki.....Muryarta ta dinga rawa ta fashe da kuka...Ta ce duba kigani ke da jikokin gwanin burgewa,ni nawan ƙyamatata suke basa ko son gani na, basu sanni ba!wai an waye...kaico ni Arziki ni nayi haihuwar banza...

Dan Allah kiyi haƙuri Arziki na san yaran nan basu kyauta ba!amma karki masu baki Inji Umma wacce idonta ya cika da ƙwallan tausayin ƴar uwarta.

Ya bazanyi kuka ba Zainab!? ai suje gasu ga duniya, makaranta ce mai zaman kanta,ni dai nasan tuwo sunan sa tuwo! tun da sun zaɓi matan su akaina ni ma na barsu har abadaa...ko wannan gidan da nake zaune da kuɗaɗen da su ke turo min ina zaman kaɗan daga kuɗina da na kashe masu ne,kuma har abada ba zasu taɓa biyana abinda nayi masu amma ba komai watarana mai allura tilas ya duƙawa masaƙi...

Ke dai yanzu ki ƙara haƙuri dan Allah Arziki,mu ci gaba da addu'a Allah ya ganar da su muhimmacin ki a gurinsu, A gaskiya Al'amarin su na bani mamaki yana kuma damuwata,ace dukan su halin su ɗaya tamkar wani haɗin baki, nayi iya ƙoƙarina don na fahimtar dasu muhimmancin tahowa inda kike amma sai suce yanayin aiki ne, shi fa Musa har ce masa nayi yazo ya ɗaukeki ya mayarda ke Dubai din tunda naga ita Amina tana da kirkinta, ita har kiranki tanayi ku gaisa,shi ne yace min to In sha Allah zaizo, Shiru sauran ma yanzu kinga ko na kirasu basu ɗauka domin sun san tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi,Amma mu ciga ba da addu'a kin san ba'a yanka da wuƙar da batada kaifi, Addu'a ita ce makami duk abinda zamuyi,ki cire damuwa kada hawan jinin ya tashi.

Ba komai Zainab na gode daman idan akace ɗan gata sai an fassara da ɗan banza, ko ban zagesu ba duniya zata zagesu,Allah ya shirye su.

Amin Umma ta ce daga nan mai aiki ta kawo musu Abinci suka fara ci su na taɓa fira,Umma sai ƙara ƙwantarwa da Hajiya Arziki hankali takeyi,su Nabeela kallo suke tare da labari da mai Aikin Hajiya.

Larai mai aiki sai dariya take basu har su ka kammala cin nasu abin cin.

D su ka fito kayan atamfa da laces da shaddodi da turare da sabulan wanka masu tsada,Hajiya Arziki ta cika masu leda da su.

Godiya sosai Umma da su Nabeela sukayi mata har ƙofar get, inda Direban su yake tayi masu rakiya suka wuce sannan ta dawo gida tana tunanin nata yaran da jikokin ta.

*************Da yamma Hajiya Halima na garden din gidan zaune tana Azkar din yamma kamar yadda ta saba sai ga Salma tazo ta ce" Maama kizo Inji Abba kuma fa harda Daddynsu Ahlan... murmushi Halima tayi ta ce ohhhh Alh.Hashim ne yazo,yau a gidan nan lallai muna da manyan baƙi to muje.Amma karki ƙara faɗin Daddyn Ahlan kema Daddynki ne bana son rashin kunya kinji...Eh mama kiyi haƙuri Inji Salma

Falon Mai gidan ta shiga kai tsaye da sallamarta da fara'a ta gaisa da shi tare da nufar fridge Lemo ta d'auko masu da cups suna ƙara gaisawa.

Tace Alhaji yau kaine kodai ɓatan kai kayi? ya gida yasu maman Ahlan? kwana biyu duk kum ɓoye? Dariya yayi, duk lafiya suna gaida ke, ya yaran nan?Ta ce lafiyan su Lau...Dubin mijinta tayi Ta ce zyallabai Barka da hutawa... murmushi yayi yace barka dai uwargida ran gida,Alh Hashim yace bata laifi ko ta kashe ɗan Amarya, dariya sukayi dukan su..."

Bayan sun d'auki lokaci su na fira abinci ta zubo masu nan suka ci har da santi ita kuma alokacin ta basu guri.

Alh.Hashim yace a gaskiya Alh.Bello ina ganin mutuncin Halima, dan haka ba zan iya fad'a mata abinda ya kawo ni gidan nan ba!Sai ka fad'a mata domin Waƙa a bakin mai ita tafi daɗi..nidai banga aibunta ba, ga girki na garari mai daɗi,Ina ma zan dinga dibar irinsa a gidana ?Don kasan ni an wuceni gurin auren macen da ta iya girki,komai bata iya ba na ƴan aiki nakeci kuma ba so nake ba don ba wani biyan buk'ata.

Amma ka dubi Halima,ga tsafta, ƙwalliya,iya girki,iya magana,fara'ah da tarbou jama'a gata koyaushe ita da yaranta duk da suna mata amma fesfes,banga ta inda ta gazaba dan batada mak'osa,duk inda aka shiga,amma saboda wani dalilin banza ka juya mata baya,Ba kai mata adalci ba,ka tuna tun bakayi arzikin nan ba hakan,ta ke tare da kai, har kawowa yanzu. haka kawai dan Allah bai bata haihuwar D'a namiji ba ku dinga ƙuntatawa baiwar Allah...Wannan ba hujja bace Karka manta gidana Yara uku gareni mata namijin ɗaya tal daga gareshi Kuma haihuwa ta tsaya...Amma kai Allah yayi ma arzikin har ƴaƴa tara maimakon ka gode masa sai ka dinga kushewa...ka nuna ga zaɓinka.

Ba haka bane Hashim umurnin Hajiya Babba ne, ba nawa ba,sannan ai ina kula da yaran nan fiye da zatonka ko ita Halima ba da son raina bane watarana nake mata wasu abubuwa,In Sha Allah nayi Alk'awari ko nayi Auren ba zan wulaƙanta uwar ƴaƴana ba!Nidai ka taimakeni ka fad'a mata zancen ƙarin Auren nan Dan Allah......

Idan babu comments ba post 🙅🏽‍♀️ 'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

BABI NA SHIDDA

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull