Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 3

Uwar y'an mata complete - Chapter 3

Uwar y'an mata complete Chapter 3: Uwar y'an mata complete Chapter 3. *************** Zaune su ke a falon wanda ya kacame da hayaniya da surutu,duk abinda…

4,436 words

*************** Zaune su ke a falon wanda ya kacame da hayaniya da surutu,duk abinda suke kamar Ammin su bata falon, domin idan da sabo ta saba da ƙiriniyar su, haka ta ke tamkar Alkalin babbar kotu hakan t a gidan, matukar su na nan.Rabon dambe yin hukunci duk aikinta ne,shiyasa ba ta damu da harkar yaranta ba, itama tana gefe tana danna wayarta tare da cigaba da online business ɗinta.

********Umma zaune yayinda su Nabeela su ka zagayeta sai fad'i banza fad'i wofi ake cikin farin ciki,saboda Umma macece mai son wasa da jikokinta bata iya zama idan ba tare da su ba,Tun ranar da taje gidan su,suna dawowa daga makaranta, da su ka sameta gidan, shi kenan suka kwashe dukan su suka biyota gidan ta,Ɗanliti direba anan ya ke zuwa ya ɗauke su zuwa makarantar boko da Islamiyya.

Duk dare sai Umma tayi masu tatsuniya tare da koya masu azancin magana da sauran su ,Daman abinda su ke so kenan, irin abincin gargajiya masu daɗi na gidan wanda ake yawan yiwa Umma daga ɗan wake da shinkafa ko kwaɗon zogale,ɗan tsunbul da sauran na'ukan abincin gargajiya wanda mafi yawa basa cin su idan ba a gidanta ba,wannan yasa suke jin daɗin zaman gidan,Ba aiki ba faɗa saɓanin inda Ammi da batada mai aiki shiyasa komai dasu take idan su na gidan.Amma gidan Umma suci Karen su ba babbak.Sai dai Umma sam bata bari suyi faɗa kuma ba'a wasa da sallah kasancewar ko agidan su, hakan suke tafiyar da rayuwar su,shiyasa basu ɗauki hakan a matsayin takura ba.

**********Yaya Zillah...Yah Zillah...kina jina fa to!uhmnnnn ba aiki bane ki zo mamma na kiranki... Inji Tasi wanda ke ƙwance a kafufun karima yana shan ƙanƙarar zoɓo, tub'ure da baki ta fito daga ɗ'akin tana fad'in mamma gani! da karfi tamkar zata daki kariman.

Oh ni k'yasu Allah ya rabani da ke lafiya!kada watarana garin takaici na ki dakeni...Inji karima tana duban Zillaziya.

Ai wallahi duk ranar da ta dakeki sai munyi kuli-kulin kubura da ita,Ni da Yaya Safara'u Inji Tasi yana hararen Zillaziya cike da raini, ya ƙ'ara da cewa ƙatuwar banza wanda batason aiki gani nan Namiji nike amma na fiki amfani a gidan man,kedai gaki ko abinci baki iya ba!ko kunun banza naki ba zai shayu ba!ga ƙazanta ana sati ba'ayi wanka ba!Idan ma kinsani ki daina bleaching dan Ranar da kikayi wanka duk dattin jikinki zai zubar da hasken naki na Mai....

A fusace ta shure shi!ƙafin ya ƙarasa maganar...Tace sai na karye ka, in fashe bakin nan naka marar mutunci ko dan kaga na ɗaga maka ƙafa ƙwana biyu?hannu ta ɗaga ta tafkeshi...karima hanata tare da faɗin ke dakata! bana son iskaci in kiraki bazaki saurareni ba, dan ya faɗa miki gaskiya sai ki dakeshi to Kar na k'ara gani.....Mamma baki ga yana min rashin kunya ba? yayi maki ke ba yimin kikeyi ba? Ai a gurin ki ya gani daman gurin hawa wurin sauƙa.

Dariya Tasi yayi tare da mata gwalou takalminsa yasa ya futa daga gidan yana fad'in ƴar wahala ta tashi mai zaman banza,to masu sun bar maki gidan, ki jiƙa abinda kin ka ajiye ki sha...nayi maƙota in samu na Rana.

Aikin kenan ɗan yawon maulan Abinci, ai gwara Ni da Kai,Yace na gane ba na abinci ba na man bleaching ga hannu da ƙafa sunyi baƙi kuma lahira wuta bal-bal....Takalma ta wawura ta bi Tasi har ƙofar gidan tana zagin sa, wanda tuni ya gudu bata same shi ba! ƙwafa tayi Tace ka dawo in ga wanda zai rabani da kai ɗan iskan yaro.

Inda karima ta dawo tayi tsaye tare da riƙe kugu Tace ke kuma gani ai kece ke ɗaurewa Tasi da Safara'u gindi a gidan nan, suna min rashin kunya!To duk sai nayi maganin su,idan ma banda ƙaddara me ma zanyi dasu a matsayin ƙannai na! 'Ya'yan takalawa dasu, ɗiyan buzu mai shayi da mai dawo,Ni naji haushin kasancewar wai Buzu ne uba na gwara ke,amma kin cuceni kinci amanata da yanzu Alh.Basi ne mijinki babban ɗan kasuwa inda kin aure shi lokacin da yake nemanki da yanzu sai dai in ci in sha a ɗauke min ƙwanika, sai gashi garin ruwan Ido kin auri matsiyaci wai ma buzu!Ni banga abinda kinka gani gareshi ba! da ace zaki ɗauki shawarata da kin kashe auren nan, kin auri wancan ko da magani,Bazaki samu matsala daga garemu ba, dan bana baƙin cikin zama Agola a ko'ina indai da mauƙo,idan ba haka ba! Duniya zan shiga inda Ali Nuhu zanje yasani film inyi KUD'I nagaji da zaman TALAUCI da takaici kina ganin ko sukuni banida tun lokacin da mai na ya ƙare! Ga matsiyatan samarin nan basu sakin komai sai firar banza!Tsaki tayi tare da hamma Tace Allah wadaran aikin takaici kullum cikin yunwa, Inda gidan Baba Basi ne, sai dai muyi plushing da Naman kaji..."

Karima mutuwar zaune tayi, duk da idan da sabo ta saba da cin mutuncin Zillaziya amma na yau yafi na ko yaushe, wato rashin mutuncinta ma sai gaba yakeyi.... wasu hawaye suka gangaro mata, A zuciyarta tace "Tabbas annabi ya yi gaskiya,yadda kayiwa naka sai anyi ma"Hannu tasa ta share Tace na gode Zillaziya,amma zauna kiji akwai maganar da na kiraki muyi mai muhimmancin gaske idan na gama sai muci bura uban juna a gidan nan Ni da Ke.

Tsaki tayi tare da harararta tace kamar wani abin kirki za'a ji, yanzu hakan gulmar matan layi ne tunda shi ne aikinki....

Mari ta watsa mata a fusace Tace ke kinci kan kazar gidan mai gari! nayi gulma saboda samu take bani dan ubanki Buzu mai shayi,ba da abin Alheran gulma nake ciyarda ku ba?Da ban yawon layi da ina zan samu shinkafa ko ƙanzon da kuke ci,sakarai marar mutunci,ni zaki cima zarafi marar hankali,tara miki nake karki hasala ni fa!yanzu sai nuna miki naki wasa ne, kije ki tambaya fagge kowa yasan wacece karima Mai dawo da nono,Idan na ƙara jin bakinki sai tumurmusaki kamar yadda nake wasan majaujawa da rawanin ubanki.

Ki bani hankali kiji abinda Zan fad'a maki shashasha....

To zillaziya Tace tare da sosa fuskarta inda tasha hannun Mamman ta,kuma ta duba sam ba alamun wasa yanzu shiyasa tayi hankali.

MORE COMMENTS MORE POST IDAN KUMA BA'AYI BA,ZAN MAYARDA SHI NA KUƊI...DABARA TA RAGEWA....

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

Home of Brilliant Writers forum

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA TAKWAS DA TARA_

INA MATA IYAYEN GIDA,ƳAN KASUWA DAMA MASU SAYEN ƊAYA?KU ZO GA DAMA TA SAMU, @5 STARS FASHION TRENDS 👝🥻SUN ZO MUKU DA KAYA NA KECE RAINI,NA ƘASASHEN DUNIYA DA NAN GIDA NIGERIA,DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI,AKWAI LACES,SHADDA,ATAMFA,GYALE,JIKA,ZANNAN GADO,MATERIALS DA DAI SAURAN SU.

GA MASU BUƘATAR KAYAN MU ZASU IYA ANTAYO WANNAN LINK MATA ZALLAH👇🏿👇🏿👇🏿

https://chat.whatsapp.com/IEUdOSV8nGTECNWaJnB2dy

DAN ALLAH KARKI SHIGO IDAN KINSAN BAZAKI SAYE BA.

*********************** Zillaziyya ce zaune ɗaram kam kujera ƴar tsuggune da ke tsakiyar gidan, tana zizara ƙwalliya,ita kuma safara'u kayan miya take jajjagawa, Mammah na ƙwashe tuwon dawa,

Sai da ta kammala shirin ta tsaf, kana ta sanya Riga da Siket na atamfar su na Sallah don dai su ne masu dama acikin suturarta,su ma wanda Hajiya Maryam ke basu ne ga sallah.

Mayafin da ta aro gurin ƙawarta ƴar lubancy ne ta yafa tana rangwaɗa ta ce"To Mamma ni na tafi, Karima ta dubeta ta ce " Kin dai ji duk abinda na faɗa miki,Kar kije ki nemi guri ki zamanki, magariba tayi maki gidan nan!manyan mutane ba'a masu rawar kai,kuma baka nuna kai ƙerarre ne,kinsan idan ba da dalili ban damuwa da yawonki amma yanzu da anyi garaje, sai ya canja wata mafarkin mu da shirin mu duk za su rushe....Mamma ai da shidda na yamma tayi zan dawo, ina zanyi sake ai min sakiyya wasu na nema basu samu ba, nikam tunda na samu ai bazanyi wasa da Alhajina ba Inji zillaziya tana wani fari da ido tare da hararan gefen da ƙanwarta safah ta ke tana aikin ɗaura sanwar miya.

Tsaki Safara'u tayi ta ce" Allah wadaran naka ya lalace...ta ci gaba sa aikint. To 'yar baƙin ciki mai bakin jaba shirunki sheri maganarki guba, ai duk lalacewar Masa tafi kashin shanu, Alhamdulillah aƙwai farin jini ga farin fata, ba irin ki ba baƙa mai baƙar zuciya,da baƙin jini mai baƙar aniya to ahir ɗin ki ni Zillaziya na gawurta ba dai ke ba yarinya oh!zamani hooo....jininka ma sai yay ma baƙin ciki,dama ance makashinka yana tare da kai,to tun yanzu anyi walkiya duhun dare ya haska na gano ki,kina min hassada ta Allah ba taki ba.

Karima tsaki tayi ta ce "to kaji masu bakin magana kuyi tayi haihuwar masifa! sannan ta tashi ta fara ɗauke ƙwanonin tuwonta fuskarta a murtuƙe.

Safara'u ta ce"Mamma kiyi haƙuri kunsan duk yadda akai da jaki sai yaci kara,ta dubi yayarta ta nunata da yatsa ta ce"Ke kuma ba komai, na gode ma Allah da yayi ni baƙata, kuma na tsaya a baƙar, ke fa? gaki da farin naki amma kina shafa man bilitin dan rashin godiyar Allah,kinga ke ƙone ciki da bai,Sannan da ki ke zancen baƙin jini to sai me? Ai ba gareni farau ba!Ke da keyiwa samari magani dan su son ki fa?ko wanga Alhajin ai baice yana so ba, sai ya zo ya gani ne tunda saboda tsabar farin jinin naki yasa za'a maki Auren haɗi, ba na nagani ina so ba.

Har Zillaziya tayi kukan kura inda safah,sai ita ma ta tashi a fusace tare da kinkimou ƙwanon da tagama gyaran kayan miya da shi, tana faɗin Wallahi duk kin ka tab'a ni sai na maki wanka da ruwan nan, mai kayan aro kawai,ba ka da abin ƙarya sai ka ɗaukarwa kanka ita ƙwaɗayi dai mabuɗin wahala,

Ƙwafa zilla tayi, zaki gane shayi ruwa ne sai na miki mugun wulaƙanci duk kin kaje gidana, cin arziki mai ƙaton baki wawuya kawai!Komai zaki faɗi dai ki fa gwara ni ina Sallah, kefa? ba Sallah bare Salati jahila.

Karima ce ta dawo gurin a fusace!ta jefi zillaziya da takalmarta nan ta ke tayi waje da gudu, tayi tafiyan ta, Safara'u ko ranƙwashi tayi ma ta tace" ba na hanaku faɗan nan na tonon sililin ba,kudai kullum sirrin gidan nan naga mutanen layi,sai nayi maganin ku tunda na gane abin ya wuce gona da iri,.Safaah inda Mamma ta nufa tana bata haƙuri,ta ce" kinaji fa tana cemin mai baƙin jini...To safah dan Zillaziya ta fad'a miki hakan shi ne me? ko ni nan bacewa hakan ba! bare ke kina gani ke kawai nake jin sanyin ki a gidan nan, ba mutunci ne da ita ba,to ke meyasa za ki dinga biyewa halayen ta?

Mamma Allah ya shiryeta,In sha Allahu zan daina biye mata tunda baki so, Tace to Amin, yafa koɗaɗɗen mayafinta tayi, tare da shura tsinkakkin takalmanta ta fita tabar gidan kamar yadda ta saba da yawon mak'otan ba dare ba Rana.

********** Duk wani tunani da dabara ba wanda Alhaji Bello baiyi ba don ganin ya samu hanya mai sauƙi da zai fad'awa Halima zancen ƙarin Auren sa, da Hajiya Babba ta bashi umurni,Amma ya kasa abokin shi Hashim ne ya turo a matsayin wakilin sa, shi ma yace ba zai iya ba.

A gefen Hajiya Halima ma ba laifi duk da bata san wainar da ake toyawa ba,amma kuma ta fahimci Alh.Bello yana cikin damuwar da ya hana duk wata kafa da zata iya fahimta,gashi sai ƙara sanya yaran ajikinsa yake, yana kulawa da su kamar da can baya.Ita ma lallaminta yake tare da nuna mata soyayya sai dai ta ƙasa gane manufarsa shin wannan sauyin lamarin da gaske ne? Tabbas jikinta na bata akwai dalili domin ruwa baya tsami banza. Fatan ta Allah yasa ya canja ne kamar yadda yake.

Ci gaba da kula da gidan da tayi da yaranta,Amma har yanzu a zuciyarta maigidan ne take ji, Addu'oin da ta saba dasu na tsari ba dare ba rana wanda ya zame mata jiki su ke ƙwaranyowa a bakinta.

******** Tun da Umma ta dawo daga gidan Hajiya Arziki taji abin duniya ya dameta,don kuwa tabbas Hajiya Arziki abin tausayi ce,shiyasa tayi koƙarin kiran layin ƴaƴanta su Musa amma duk bata samesu ba, Hawayen ƙunci su ka zubo mata ta ce"Hasbunallahu waniemal wakil, Allah na gode ma,Allah ka ganarda yaran nan su dawo su riƙi mamansu,ka ƙara shirya min Habibuna.Tunani da nazari ta dinga yi,saboda su Nabeela sun koma gidan su, shiyasa taji wata irin kewar yaran tana damunta,don a duniya idan an cire Habibullah a rayuwarta to jikokinta ne na biyu idan da na ukun su bazata wuce Juwairiyya ba surukarta. domin ita ce ta zame ɓata ƴa maccen da Allah bai bata ba.Tana ƙaunar jikokinta da surukarta kamar yadda take son Alh. Habibullah.

************* Hajiya Babba ce ke danna waya tare da karata a kunne,bayan an ɗaga ta ce Alo ɗan Inna kana Ina?

Da ladabi yace ina shago Hajiya, an wuni Lafiya?

Lafita qlaw,To ina son ganin ka,yau ne ranar haɗuwar ku da wannan yarinyar da na maka bayaninta Zillaziya ƴar gidan ƙawata Karima.

Numfashi ya sauke kamar Hajiyarsa na gabansa, ya wani ɓata fuska! kana ya yarfe hannu,yace to Hajiya sai nazo....

To shi kenan Allah ya kawo kasuwa mai Albarka,ina so ka d'auko atamfa da leshi me mayafi masu kyau,zan haɗa turaruka da ƴan kayan ƙwalliyar ƴan mata sai ka riƙa mata,kasan yanzu mata sai da amshi idan kana so kasaye zuciyarsu da ta iyayensu.

To Hajiya ba damuwa,yace tare da kashe wayarsa,Tsaki tayi ta ce" Allah ya shirya ka ɗ'an Inna, ba zan lamunce ganin hakan ba...mayyar mace duk ta shanyeka ba ka da katabus a gidan ka duk abinda *UWAR 'YAN MAATA* ta fad'a ya zauna a rayuwarka,dole inyi maganin ta, in har ina raye ba zan tab'a barin Halima tayi yanda takeso ba a gidan nan, daga nan Hajiya Babba ta tashi ta shiga bedroom ɗinta tana faɗa sa zagin Halima da yaranta take.

Gaskiya fans na kusa mai da buk ɗinnan na kuɗi dan na gane baku comments idan kun karanta.

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

~Home of Brilliant Writers forum~

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA;_

~'YAR MUTAN DIKKAWA~ 😍

_BABI NA GOMA DA SHA ƊAYA_

******************* Gab da magriba Alh.Bello ya ƙaraso gidan Hajiya Babba,da sallama fuska ba walwala ya shiga katafaren falonta, mai launin kore da fari,hakimce take saman kujera ta ɗaura kafafuwanta saman ɗan tebutin da ke gurin, fuskarta na kallon ƙatuwar talabijin ɗin bango da ke manne a ƙayataccen falon, ta mayarda hankalin ta ga kallon shirin zamantakewa, da akai kusa kammalawa a tashar Arewa 24.

Wuri ya samu ya zauna tare da faɗin sannu da hutawa Hajjiya,waigowa tayi gefensa tana murmushi ta ce D'an Inna...Kai ne na ɗauka mai aiki ce dan na aiketa,yaƙe yay ya ce na lura kina son shirin nan,kin ga sai yanzu na samu sararin fitowa daga shagon, Bakomai haka ake so, Allah ya ƙara ba da kasuwa mai Albarka,bari naje na ɗauko maka sakon,tashi tayi tana dariya ai wannan shirin yana da kyau kaga Binta gwadaben da Hajiya Aisha suna fafatawa,hankalinsa ya mayar kan talabijin yana Hajjajo har kin san su,Bedroom ɗin ta nufa,nayan ƴan mintoci sai gata ta fito ɗauke da ledojin masu manyan rubutu da aka rubutawa Sahad Store,ta bashi ya amsa yana godiya tare da tashi,ya ce to nikam dai zan koma sai da safe da fatan ba wata matsala ko?

Eh ba matsalar komai idan ma allura zata tono garma,to daga wurinka ne gurbi zai ɓata sha,dan bana son asamu tangarɗa ko ɗaya a tafiyar nan, Ɗan Inna ni dai burina kayi aure ko zan huce taƙaicin haihuwar ɗa namiji,sunkuyar da kznsa yay yace bakomai in shaa Allah,Ta ce "Ya banga atamfa da leshin da nace ka ɗauko ba?

Na haɗa su Hajiya su na mota,na tafi. To shi kenan Allah yasa adace daga nan ta dinga jera masa Addu'oin samun nasara,har ya isa parking place ya juyo yace Hajiya yaya sunan yarinyar ma?zaro ido tayi tare da fad'in na karbi Salati ni Meri yanzu Ɗan Inna har sunan nata baka haddace ba?Tsaki tayi da yanayin bacin rai tace" Zillaziya."

Ganin Hajiya ta sauya ya sanya shi sakin ransa yay murmushi kana yace to Hajiya sunan nata ne na ƴan gayu ba wanda muka saba ji bane,amma yanzu na rike Zillaziyat....Dariya Hajiya Babba tayi har sai da hauren ta na makka ya bayyana tace" Yawwa ko kai fa ai gani ya kori ji ƴar gayu ce, sai dai kaje idan ka isa ƙofar gidan ka kirani sai na kira ita Karima,sai aturo Zillaziya dan ba'a barin su fita,kai ba dai kirki ba kam gasu da tarbiyya,kai inda ba dan talauci yay masu atishawar tsaki ba,ai da yanzu su ne ƴaƴan masu shi dan tsaf rayuwar su ta bariki ce ga alkunya.

Shiga yay motar sa dan ya gaji da sauraranta ya ce"Hajiyata sai kin jini nan ya rufe motar sa, Hajiya na d'aga masa hannu cikin Jin ɗadi,mai gadi ya wangale get nan Alh.Bello ya bar gidan ya kama hanyar unguwarsu,masallacin ƙofar gidansa ya tsaya domin gabatar da sallar magriba.

************ Bayan sun gama sallar magriba kamar yadda su ka sa ba basu tashi daga gurin sai sunyi azkhar idan an gama kuma a fara karatu kafin Isha.

Ko yau hakan ne, sun gama azkhar Ammi ta zauna yayin da ƴaƴanta su ka kewayeta su na ɗaukar karatun Alkurni Mai girma, da sauran littafan addini.

Sun ɗauki kusan rabin awa suna karatun daga bisani Ammi ta fara masu nasiha da sauran lokacin da ya rage musu.

Ƙara gyara zaman su sukayi musamman Nabeela da yake yanzu girma ya kawo hakan Aysha da Yaseera,Nana Khadija da Fatima ne matasan 'YAN MAATA acikin su.Shiru su kai suna sauraron Ammin su.

Malama Juwairiyya (Ammi) ta ci gaba da faɗin yau kamar yadda na faɗa maku jiya, zanyi maku nasiha a kan *MATSAYIN WANDA YA ZAGI MAHAIFANSA(IYAYE)*

```Zagin iyaye Musamman a cikin wannan zamani, namu kun ga abu ne mai sauƙi, wanda mafi yawan mutane basu ɗauke shi a bakin komai ba,Ina so kusani ba wai sai kun buɗe baki kun zagi Iyaye ba, ba, A'ah idan ma ka zagi Iyayen wani matuƙar bai rama ba, to tamkar ka zagi naka Iyayen ne,Idan kuma kowa ya rama zagin to kowa ya zagi nasa iyaye.Sannan ku sani idan har mutum ya kuskura ya zagi iyayen sa ta kowacce fuska ko siga,to kuwa mummunan albishir shi ne ya shiga babban haɗari,tun nan duniya.

Idan Kuma ya shiga ɗakin kewa(kabari) to a nan ne zai yabawa aya zaƙinta!Dan haka mu kula kunji ƴan Albarka.

Domin Annabi (S.A.W) ya ce"Duk wanda ya zagi iyayen sa, to za'a dinga saukar masa da ruwan wuta!a cikin kabarin sa tamkar yadda ruwan sama ke zuba(Waiyazubilla!)

Haka Annabi Muhammad (S.A.W) yace,Ranar da aka yi isra'i dani naga wasu mutane a cikin wuta an rataye su, ga bishiyar wuta!sai na cewa mala'ika jibirilu su waye waɗannan?sai ya ce"Su ne waɗanda su ke zagin iyayen su maza da iyayen su Mata a lokacin da su na duniya. ``` Numfashi Ammi ta sauke tare da duban fuskokin yaran dan takaranci yanayinsu da yadda nasihar tayi tasiri akansu, agogon wayarta ta duba sannan ta koma kai dubanta garesu,duk jikin su yay sanyi hamdallah tayi, sannzn ta ce"In sha Allah anan zan dasa aya,Allah yay muku Albarka,dan lokacin sallar Isha yayi sai ku tashi muyi sallah.

Ina fatan kun ji faɗar ma'aikin Rahma,ko ba komai zagi tsakanin musulmi da musulmi abu ne mai muni a wani gefen Annabi ya Kira shi da fasikan ci ne.Dan Allah kuyi hattara kunji yaran kirki.

In shaa Allah Ammi zamu kula Inji Nabeela

Aysha Tace Ammi zan fad'awa ƙawayena na school da suke da d'abiun zagi.

Yasira ta amshe tace" nima na tsorata Allah ya yafe mana"

Amin khadija da Fatima su ka ce idonsu yay jajur su na dab da zubda ƙwallan tsoro!

Ammi ta ce "Allah ya yafe mana dukan mu.

Haɗa baki sukai gurin fad'in Amin.

Daga nan su ka ta da Sallah.

*************** Safara'u ce ta sallame sallah tana lazima ta shafa addu'a,duban 'yar uwarta tayi wacce tun ɗazu take cika tana batsewa,ta ce "Yah Zillah kiji tsoron Allah kina fa zaune gurin nan akai magriba da Isha, baki komai kuma bakida lalurar fashinta da ranki da lafiyar ki har lokacin sallah biyu su wuce kina nan kina game ɗin maciji...Nasan a halin yanzu haushi na ki ke ji,ko naso in fita daga sabgarki bana iyawa don hannunka baya ruɓe ka yanke ba!hallakar da ke tunkararki ko ince kike ciki a yanzu na ke jiye miki,A islamiyar da na ke zuwa ina jin wa'azin masu wasa da sallah dan Allah ki kula...

Tsakin da Zillaziya tayi ne ya katse zancen Safara'u da ta fara cin abinci... Tace"Sannu ƙanwar mallam ɗiyar liman surukar shehi,ke safah in tambayeki idan na mutu kina da gadon kabari na ne?Ina ruwanki da makomata!Balle abin dunya ya dameki yay miki zafi!?Meye naki a cikin sha'ani na da rayuwata!Kinga kabarinki dabam nawa daban dan haka ki fita idona in rufe bana son sa ido da shiga sharo ba shanu,wato har kinsani ma idan ina fashin sallah ko banayi tunda abin a jikinki yake fita,to naƙi nayi sallah kice wuta jahannama kalidina fiha abada zani....

Wa'yazubillah lallah na tabbata jahili baya da maraba da dabba...inji safara'u.

Wai meye ne ina Sallah kun dameni har ina rafkanuwa?yanzu hakan na kasa gane raka'a nawa niyyi,Allah dai ya ga niyata magariba,wato kun fara sana'ar taku ta faɗa?to sai ku k'asa kowa ya kwashe rabonsa har ni...'yan jakkar Uba!Inji karime wacce tayi tsaye bakin ƙofar ɗakin tana hararen su.

Safara'u ta ce" Mamma daga fad'an gaskiya sai alheri ya zamo sharri...to ance ana son gaskiyar taki? banza kawai da baki san ciwon kanki ba marar zuciya!Inji Zillaziya tana hararen safah

Tashi safah tayi tare da ɗauke ƙwanon abincinta tana tanɗe hannu, Ta ce" Allah ya baki haƙuri, Bana so idan haƙurin ta mutu me zan samu? Ta bi bayan safah da harara sannan ta dubi Karima Tace" Mamma wai shi wannan Alhajin ba zai zo ba?tun magariba nake jiran sa amma shiru ba labari....Tsaki tayi Ni wallahi ina gudun yace" ya fasa gashi kaf YAN MATAN unguwar nan na labarta masu wani Alhaji mai kuɗi zan aura...sannan kinga ƙwalliyar nan da limcy makeover tayi min ta naira dubu biyu ce bashi tayi min idan yazo ya shafa min in biyata,akan kar ta goge shiyasa banyi Sallah ba, idan yazo ya gani daga baya ko gobe ne nayi,Kinga na haɗu ko har fa wani turare ta fesa min ga fuska mai hana gumi,shafa fuskar tayi tare da yiwa Mamman ta fari da ido,sannan ta ajiye madubi wayarta ta ɗauka ta duba,hannu ta aza aka ta ce" Allah ka agaza min Alhajina ya taho dan limcy ko ƴan sanda tana ɗauko min akan kuɗinta bata da kirki ...Mamma dan Allah kima Hajiya Babba filashin kice Bai tahou ba!

Dallah rufe min baki sakarya sai hauka ki ke,to uban waye yace kije ai maki ƙwalliya bashi da ƙyaunki da fasalinki kamar a wanke goma a shafa, zakice a fenteki hakan kamar kura, Ni haushin ƙwalliyar nan nake ji dubeki kamar biranya....Dariya Safara'u ta ƙyalƙale da ita Ta ce" Ahaf ai garin neman gira a rasa ido Mamma,har na tuno da wani labari, akwai wata amarya da tayi irin ƙwalliyar ga, ango na zuwa yaji tsoro wai ya aza fatalwata nan wurin partyn ya saketa ya cika wando da iska ya fece.... Zillaziya najin hakan ta antaya da gudu bakin randa tasa sabulu ta dinga wanke ƙwalliyar zuciyarta na bugawa tare da godewa Allah da Bai kawo Alhajinta ya ganta hakan ba,ka da ita ma hakan ta faru da ita. Safara'u ko dariya ta dinga ƙwasa har da riƙe ciki,a ranta tace"wanda baiji bari ba yaji hoho tunda Zillah taƙi sallah ai kuwa ta rasa ƙwalliyar."

Karime Tace yo su manyan mutane ma ina ruwan su da wani ƙwalliya? Ai ba duk gero ga tuwo ba,don abincin wani gubar wani maza ki hanzarta gyara fuskarki, na san zai zo tunda Meri ta bani tabbacin hakan sannan kisan me zaki dinga fad'a masa? ina so ki ari kalaman kirki ki ƙwanta masa kamar ladidi ƴar gidan liman kinga dabi'unta da maganarta duk irin su zakiyi,saboda idan har ka iya zance ka ɗarar ma ƙwantace.

Safara'u dai tayi tsaye tana duban ikon Allah.

Zillaziya Tace,to Mamma duk na gane kuma na haddace, Allah ya Kai damo ga harawa.

MORE COMMENTS MORE TYPING GUYS I LUV U LODI-LODI IN GODIYA MASOYA

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:33 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI,TSARAWA,RUBUTAWA_

*ƳAR MUTAN DIKKAWA*

*BABI NA* 12/13

Haƙiƙa ina jin daɗin comments ɗin ku Allah yabar ƙauna,👇🏿 Fateema(Ummee) Ta ce" Aunty Nabila kiwa Allah ki mn typing naga xuwan Alhaji 😂 kuma buk dinn yana birgeni gaskia ina daukar abun koyi sosai musamman xaman su ammi a wnn page din Dan nima yau nasihar da xanma yarana kenn dama nima muna karatun bayan magrib nasiha ce bana musu kuma itama kin dora ni a hanya nima kuma yarana ammi suke cemin infact dai lbr na ddi gaskia kuma akwai gyaran tarbiyya sosai sakallahu khair🙏😍🥰."

*INA GODIYA.*

*********************** Daga masallaci Alhaji bai zame ko'ina ba,sai ƙofar gidan Buzu mai shayi,yaro ya samu domin ai masa sallama da Zillaziya.

Yaron na shiga yaci karo da Karima da ke ƙoƙarin komawa ta leƙa waje,kiciɓis tayi karo shi ya ce"Maman su Tasi wai ana sallama da Zillaziya...kan ya rufe baki da gudu ta fito daga ɗakin,caraf Karime ta sharɓe hannunta ta riƙe,sannan ta dubi yaro Ta ce"To Iliya je ka kace masa tana zuwa maman ta,fita Iliya yay daga gidan.

Zillaziya ta dubeta ta ce"Mamma ki sakeni!meyasa zaki riƙeni bayan ba wanda zuciyata ke mararin ganin irin sa,na ƙosa idona yay tozali da ruwan maliyar zuciyata mai naira...Dallah sakarya rufe min baki,shi kenan daga aikowa kiranki ki fita?Ba wani jan aji so kike ya gane mun matsu?Kin ga aro ƙaton Hijab ɗinnan na Sarafa'u kisa gwara fitar farin kije masa da shigar ƙwarai,idan kuma an dace sai ki dinga bayyana masa surarki ya ga zubin da Allah(SWT) yay miki."

Hijab ta sa har ƙasa ta fita daga gidan,bayan ta haddace kaf huɗubar mammanta har na ta salon,ta gilashin mota ya hangota tana tafiya kamar hawainiya,ƴar caras da ita matashiyar budurwa siririya, hasken farin wata ɗan daren sha uku ya haska masa fuskarta,ƴar fara kyakkyawa....Sallamar da tayi yasa ya buɗe mota ya fito yana amsawa,har ƙasa da gurfana kanta a sunkuye tana rufe fuskarta da hijab ta gaida shi."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull