Uwar y'an mata complete - Chapter 4
Uwar y'an mata complete Chapter 4: Uwar y'an mata complete Chapter 4. Ya ce"Haba ƴan mata,tashi mana daga nan sukayi musayar gaisuwa,nan ya ƙara gabatar…
4,438 words
Ya ce"Haba ƴan mata,tashi mana daga nan sukayi musayar gaisuwa,nan ya ƙara gabatar mata da abinda ya kawo shi,ya ƙara da cewa"Zan aureki ba dan matata ta gaza ba,sai dan wani dalili,ina son kisa ina son matata ina ƙaunarta haka ni uba ne,ina ƴaƴana ina fatan idan kin shiga ki kama girmanki agurin su,don nasan mommynsu zata kama girmanta a gurinki,zaman lafiya na ke so ba hayaniya ba,bana son raini,bana son rawar,ina son mutum mai nutsuwa mai aiki da ilimi,Sannan ina ga ba lallai bane in ƙara dawowa ba,komai ake ciki zakuji daga gurin Hajiyata,don ita zata ƙarasa neman auren,saboda ina da abubuwa masu muhimmanci da dama a gabana a ƙarshe ina muna fatan alheri.
Murmushi wanda yafi kuka tayi, jingina jikinta da motar tayi don jikinta ya yi sanyi,a hankali ta buɗe bakinta da sigar ladabi ta ce"A gaskiya Alhaji naji daɗin kalamanka matuƙa,wannan ya nuna min ni da yayata munyi dace,dace mafi tsafa arayuwa,na samunka a matsayin abokin rayuwa,Yayana samun namiji mai mutunci da kirki wanda yasa darajar uwargidan a gaban idon duniya sai an tona,samun namiji mai iya yabon matarsa ta cikin gida agaban wacce zai aura sai antona,Haƙiƙa kai jarumi nagattacce wanda ya cancanci a kirashi da namijin duniya,na gode Alhajina ina farincikin amsata da kaiyi a matsayin mata,duk da nima ko mafarki ban taɓa zaton ko tsammanin da kai zan rayu ba,ina roƙon Allah dafa mana yadda kabi Umurnin Hajiya ni ma nabi umarnin Mammana Allah yabamu ƴaƴa masu Albalka da zasubi umurnin mu.
Kai Amin a gaskiya Zillaziya na yaba da ɗabi'unki ya ce" ya na kallonta."rufe idon ta tayi da tafin hannunta har kasa naji kunya tana murmushi,agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya duba ya ce"To ni zan koma ki gaida Baba Kariman,Ungo wannan ya ce"A lokacin da ya buɗe mota ya ɗauko kayan har da kuɗi ya bata."
Ɗan ja da baya tayi cike da tsoro tana kallonsa,ta ce"A'ah Alhaji Mammana ta hanani ƙarɓan kuɗin kowa don ta ce"zata yanka mu idan mu ka amsa,dan Allah ka barsu an gode."
Ki amsa ki faɗa mata ni na baki ba roƙa ki kai ba...maza ki karɓa nace,amsa tayi tana godiya sannan ta wuce shi ma yabar ƙofar gidan bayan sunyi musayar lambobin waya.
A zauren gidan ta buɗe leda kuɗi ta gani da yawa,da batasan ko nawa ne ba,zara tayi ta boye a kugunta,sannan ta shiga gidan tana ƙwalawa Karima kira,da gudu ta fito daga ɗakin ta rungumeta,ta ce"Mammah anyi nasara ya ce"ya gani ya yaba kuma yana so,kai haba kunga rawar zillah kunga rawar zillah gafa rawar karime tace ta dinga tiƙar rawa tana karkaɗa kugu,Safara'u da Tasi waje suka fito suna kallon rawa sukeyi Zillaziya nayiwa Mamma liƙi da ƴan dubu dubu.Safarau tace kai jama'a kallo ya kuma sama,Tasi yace akwai shoyki yau a gidan nan.
Bayan sun gama Zillaziya ta labartawa Mamma komai,daga nan akai kasafin kuɗi kowa ya kama tashar sa,duk da ba haka zillaziya taso ba amma bata damu saboda ta ɓoye wasu akan tasan halin karima,sannan sai da tace a ɗebe kuɗin limcy aka bata,ranar gasassun kaji da fanta aka ci a gidan aka ƙwanta,Bawan Allah Buzu yana kan teburin shayi baisan wainar da ake toyawa ba,dan a shagon yake ƙwana sai da rana ya ke zuwa ya leƙo su ya basu ɗan biredi da abinda ya sauwaƙa."
************* Bayan duk sun kammala komai har sunyi shirin ƙwanciya,sai kawai ta tsinci kanta da son sanin ina ya tafi?Mirginawa tayi gefen sa, a maimakon ta ga yay bacci sakamakon ya rigata kwanciya,sai dai idon sa yana dubin saman d'aki ga alama yana wani tunani ne.
Bugun zuciyar ta ya tsananta!hasashen ta kenan gaske ne,tashi tayi tare da tab'a shi,ba alamar motsin sa S shiyasa ta shafa fuskarsa da hannunta mai d'auke da mayataccen k'amshin turarukan Zainab Bukar(Bittal Hajj Incence) Firgigit!ya sauke dara daran fararen idon sa a kanta ba tare da yay magana ba.
Gyara murya tayi cikin sigar damuwa!Ta ce"Yallabai meke faruwa?Tun d'azu na k'asa sukuni,zuciyata tana raya min akwai abinda ke damun ka tun jiya,Abin ya bani mamaki bayan magrif ban gan ka kamar yadda ka saba dawowa, sannan na kira ka kusan sau bakwai ba ka d'auka ba!Dan Allah ka fad'a min damuwar ka Abban Zeenat ko zuciyata zata samu sarari,ko idaniya na za su samu damar runtsawa,gangar jikina ya samu hutu.
Idan da sabo ya saba da tausasan kalaman matarsa Halima,sai ma yanzu ya tuna ya ga kiranta lokacin wayarsa na mota sanda yaje inda Zillaziya.Ajiyar zuciya yay zahiri ya kalleta ya ce"ki kwantar da hankalin ki Ummin Mima ba abinda ya faru,ko da kika kirani ina da wani uzuri kuma wayan yana mota sai da na zo gida na ga kiran kiyi hakuri na sha'afa ne ban miki bayani ba...
To ina ka tafi ne? Inji Halima tana masa kallom tuhuma,gaban shi ya fad'i dole ya fad'i gaskiya domin ya tsani k'arya.
Yace"Halima ina son ki bani aron hankalinki da tunaninki,daman akwai maganar da na ke so muyi da ke,A gaskiya ko da ki ke kirana ina kofar gidan su Zillaziya...Wacece ita? meye alaƙar ku? me kaje gidansu?Duk ajere Halima ta jero masa tambayoyin.
Yace "ki saurara mana da farko ba sai nayi miki bayanin wacece Hajiya Babba ba,to ta bani umurni nan da wata Daya in auri wannan yarinyar Zillaziya ƴar gidan ƙawarta Baba Karima!har ga Allah banyi niyyar maki abokiyar zama ba,don ajiye macce fiye da Ɗaya baya daga cikin tsarina kawai dan Hajiya ta tilasta ni ne zanyi,ya k'ara gyara murya tare da kamo hannayen Halima da ke hawaye!yasa cikin nasa tare da share mata su,ya tausasa muryar sa yace"Halima bana son tashin hankali shiyasa ƙarin AURE baya Cikin tsari na,zanyi domin bin umurnin uwa kuma na ɗaukar maki Alk'awari Ni Bello ba zan tab'a wulakanta ki ba,bare na ba da kofa wacce zan auro ta raina ki,abin da nake so ki ɗauki girmanki,haka yarana ina son su, ba zan ƙara cutar da ku ba,Dan Allah kiyi haƙuri ki yarda da wannan kaddara...
Kukan ta ne ya fito fili,murya a disashe Ta ce"Tabbas wannan ita ce kaddarata, kuma na amsheta, na rungumeta ni Halima mai taken *UWAR 'YAN MAATA* gashi sanadin su za ayi min kishiya.
Duban sa tayi tare da goge kwallah!da ke kwaranyo mata tana sheshsheƙa Ta ce"NA GODE Bello Allah ya baka ikon adalci a tsakanin mu na yarda kabi umurnin Hajiya Babba amma ina da sharad'i.
Duban ta yay yace wanne sharad'i?Ta ce "Bana goyon bayan ka raba wani sashe a gidan nan ka ba Amaryar ka,ko dai kai mata gininta ko kuma ka raba mana sashe. Murmushi yay yace "an gama ranki ya daɗe ba damuwa bane,sannan zan baki kuɗi ku sayi duk abinda kuke buk'ata ke da yaran nan. kuma ki rubuta min komai da ake buk'ata a gidan nan.
Had'iye fushinta da b'acin rai tayi ta dubeshi sannan tayi murmushi ta ce'' Ban buƙatar komai na hidimar gida aƙwai,amma zan duba abinda mukeso, a zuciyarta sai nanata sunan takeyi"Zillaziya ta ke.
Daga nan ƙwanciya tayi tana sharb'ar gawaye tare da tuna rayuwarta da Bello da Hajiyar sa tun farko har ƙarshe ace yanzu saboda tana haihuwar 'YAN MAATA zasu juya Mata baya, shi kuma gogan sai rarrashin ta yakeyi wanda takeji a ranta tamkar yana zuba mata tafasasshin ruwa a zuciyarta.Gajiya da sauraren tayi a ƙarshe, bayi, ta shiga tayi Alwala tana fitowa ta tada Sallah nafilfili ta dinga jerowa tare da karatun Alkurni mai girma,tana Addu'oin neman tsari da kariya daga sharrin zuciya da mugun kishi.Tana zaune gurin tana lazimi har alfijir ya keto bata runtsa ba,sanyin asuba yazou mata da sanyi da sauƙi a zuciyar ta,Sallar asubahin tayi,A lokacin taji wasai,Azkhar tayi ta shafa daga nan ta fad'a gado wani Bacci mai dad'i ya saceta.Shi ma Alhaji Bello da ya tafi sallah ya yi ta Addu'oin neman zaman lafiya,bayan ya dawo ya bi lafiyar gado da katifa .
*****************
Washegari.
Da misalin k'arfe goma da rabi na safe, duk zaune ahlin gidan su ke, a gurin da aka tanada domin cin abinci.
Ba komai ke tashi ba, sai ƙarar cokulan da su ke amfani da su,Babu mai magana illa kira'ar Sheik Sudais da ke tashi kad'an a cikin falon.
Cikin ƙwanciyar hankali su ka dinga karin kumallon na safe,har su ka gama,daga nan Khadija da Fatima su ka ƙwashe ƙwanukan,yayin da Abbu da Ammi su ka koma falon da zama,Nabila goge teburin tayi tsaf, Aysha da Yasira dukan su a k'asa suka zauna ana kallon Africa t.v 3, Wa'azin Sheik Ali Isha Pantami mai ratsa jikin su ke sauraro aka rayuwar Barzaq(Rayuwar da mutum zaiyi acikin kabari bayan ya mutu)Duk Hankalin su ya ɗunguma ga dubin ƙatuwar talabijin ɗin, ba mai motsin kirki bate magana,saboda tashin hankali tabbas rayuwa abin tsoro ce,kuma mutuwa,rayuwar kabari,tashin ƙiyama duk gaskiya ne,basu ji k'arar bud'e k'ofar ba.
Sai sallamar ta da sukaji...Abbu da Ammi ne suka amsa atare...Da gudu 'YAN MATAN su doshi 'yar dattijuwar kakarsu su na fad'in oyo yo Umman mu... Dariya tayi sosai sannan Tace" ai na ɗauka ko baku tashi bane?"
Da ladabi Ammi tace"a ah Umma hankilin mu ne Kan wa'azin shiyasa ba muji ba afwan Umman mu tana murmushi tare da kamo hannun surukarta ta zuwa harabar falon.
Zaunawa Umma tayi akan kujerar zaman mutum uku, su kuma dukan su ka zube a gaban ta ana gaishe-gaishe cikin jin daɗin ganinta.
Cike da k'aunar jikokinta da iyayen su Umma ke magana tare da jan yaran wasa,nan fa falon ya kaure da dariya. Ammi ce ta fita jim kad'an sai gata ta hadowa Umma abin karyawa,ta ajiye Umma godiya tayi tare da kinkimou 'yar ledarta da ke cikin jikkarta Ta ce" ungo waɗannan Juwairiyya kayan yaji da daddawa ne nasa Atine ta daka maki yanzu sai su lalata ƙamshi falon nan, Da farin cikin ta karɓa tana godiya"Umma bakya gajiya waɗancan ma basu ko ƙare ba,ga wasu Allah tufa asiri."
Abbu yace Amin, gaskiya Umma mun gode gasu da daɗi yana dariya. Tace ba komai Allah maku Albarka.
Amin sukace nan ta ɗauko wata Leda, Tace" ke Nabila ga naku awara da fara an soya, sai ku haɗa da kan ku,nasan zakuce Atine bata iya irin naku ba, shiyasa nace mata iya suya,Kuma kar in ga kun cika yajin nan.
To Umma,mun gode Nabila Tace" Da azarbabi su na murna, madafa nufa ,aka gyare awara tsaf da mai da yaji da kabeji da komai aka dawo falo Ana kwaɗayi,Dariya Abbu ya dinga yi musu yana faɗin sarakunan ƙwaɗayi har ƙwari(fara)zasuci daga nan ya ce "shi zai fita,a dawo lafiya su kai masa Ammi har k'ofar falon ta mishi rakiya tare da manyan Addu'oin neman tsari kana ta dawo aka ci gaba da cin awara da fara,sai hira kaure gwanin sha'awa."
************
Cikin sa'a wayar ta shiga ta fara ruri,can aka d'auka
Gyaran murya karime tayi Tace" Alo Hajiya Meri...Ni ta Karime."
Tsaki Hajiya Maryam tayi har sai da Kariman ta jiyota, sannan ta k'ara da cewa duk yadda Akai da jaki sai yaci kara!
"Karime Tace kina jina Hajiyata..."
Murmushi tayi cikin iko da gadara kamar Karima na gabanta,tare da d'aura k'afa ɗaya kan ɗaya ta ya gi naman kaza bakinta ya cika Ta ce"Eh....Karime Ina ji.
"Kut...kut.....Karime ta haɗiye yawo domin har ta ayyana ko me ƙawarta ke ci,Tace" Ina kwana?
Lafiya kalaw,Inji Hajiya Babba.
Karima Ta ce" Daman bugowa nayi in fad'a miki jiya dai d'ana yazo kuma har sun Dai-dai ta da ita ƴarta ki Zillaziya,Ya kuma faɗa mata yanzu komai yana hannunki,to shi ne Tace" Bakomai itama a faɗa miki ta yarda,kinga yanzu sai a turo ai maganar aure.
Dariya Hajiya Babba tayi tare da kurb'a lemon da ke gefenta Tace "Ai nasan ya zo dan Nice na turo shi,sannan kamar yadda naga ya dace in taimaka in haɗa shi da Zillaziya hakan zan ganin dacewar na turo magabatansa ba sai kin fasalta ba."
Washe Baki Karima tayi tare da sosa ƙeya Tace"Ahhhh to Hajjaou ai ba komi muna godiya."
Hajiya Babba Ta ce"Karki damu kedai ki fad'a mata ta rage azarɓaɓi da rigima dan wallahi ɗ'an Inna baya son rashin kunya, zai iya cewa "ya fasa!kin san kema hakan rayuwarki ta ke,hakan kikayi garin rigima da shigewa samari har kika hadou da ɗan Buzu mai shayi garin ƙaƙabe ƙaƙabe ƙwaɗayin madara ya kai ki toooh kija mata kunne...''
B'ata rai!Karime tayi tare da d'auke wayar a kunnenta Tsaki tayi da cizon yatsa, sannan Ta ce "To Hajiya zan fad'a mata,ai komai ya wuce ki daina tuna baya Meri dan Allah aini yanzu naga izinah.
"To Allah yasa hakan,shi kenan In shaa Allah zanyi magana da ƙannaina zasu zo ayi maganar daman ina son nan da mako uku ai a gama komai,sai ki sanarda Buzu."
To yayi Hajiya Allah ya shiga ciki, Na gode ƙwarai,sai na shigo jibi,Inji Karima tana lasar baki."
"A ah kiyi zamanki kawai zanje gidan ɗan uwana jibi, idan buƙatar ganinki ta taso ai ni zan kiraki ki zo...Inji Hajiya Babba.
To shi Kenan Hajjaou sai na jiki.....To yay Hajiya Tace tare da datse Kiran.
Ci gaba da cin naman kajinta tayi tana kora ruwa,tana masifa wato shi talaka ba zai tab'a canjawa ba!in dai akan ƙwaɗayi abin duniya ne, kizo ki min me?Ba inda zani bana son harkar ƙauyanci azou a b'ata min gida da wari!Sai meta Hajiya takeyi ita kad'ai.can sai ga mai Aikin ta shigo tana kwashe kwanukan da ta gama cin abinci,ruwan wanki hannu ta kawowa Hajiya Babba a tasar silba ta wanke hannunta,tare da gogewa da tissue.
Kallon ta ci gaba da yi tana dariya tare kwak'ule haurunta da tsinke kwak'ula.
Karima ko ta na gama wayar, da Hajiya Babba ta baiwa Zillaziya wayarta,ranta a b'ace!Tace" Wallahi sai kinyi nadama Meri!Bari dai Zillaziya ki shiga gidan sai ai mai kankat duk wannan mulki,iko,da wulaƙanci sai na rama nima,muyi wasa tare ai ƙurciya tare dan kawai dare ɗaya Allah ya yi naki baturen sai ki canja,har da shirgin wulakanci kamar ba tare mukayi rayuwar budurci ba!
Kiyi haƙuri mamma nima naji duk abinda take faɗa,kuma wallahi na sha alwashin ramamaki duk iskancin da Hajiyar Alhajina ke maki!
Bakomai akwai ranar kin dillaci Inji Karima,sannan ta d'auki tabarya ta ci gaba da sussukar geron ta da zatayi gumba.
'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍
Share
Post
Comments [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄 *NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*
~Home of Brilliant Writers forum~
```LABARI TSARAWA RUBUTAWA HAK'K'IN MALLAKA```
*'YAR MUTAN DIKKAWA*
BABI NA 14/15
*Wannan shafin kacokam kyauta ne,ga masoyan UWAR ƳAN MAATA.*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*
************************
Kasancewar bata wani sami baccin kirki ba,a daren jiya shiyasa batayi saurin farkawa da wuri ba,wajajen ƙarfe goma da mintotoci ta farka,a gurguje ta faɗa bayi tayi wanka,sannan ta kimtsa.
Saukowa tayi daga saman benen zuwa ƙasa jikinta ba k'wari,komai baya mata daɗi,a zuciyarta ta ci gaba da maimaita kalmar; Innalillahi wa Inna ilaihir raju un!"
Wani daddaɗan ƙamshi ya fara dukan kofofin hancita,bata san lokacin da ta lumshe ido ba,shakka batayi daga madafa ƙamshin ke fitowa,shiyasa ta wuce kai tsaye,ko da ta shiga tsaye tayi tana hamdala ga Allah,fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa inda su ke,su na ganinta su ka rungumeta suna mata ina ƙwana."
Wani daɗi ya lulluɓeta ta amsa masu,Zeenata ta janyo hannunta tana faɗin Momy duba kigani har mun kammala abin kari,Sudat tace"Momy ci kiji yay daɗi kinsan nafi yaya iya girki,Khallesat ta amshe Momyna duk fa nafi su aiki dan ma kusani idan tace"ya yi daɗi nice mai magin hannun."
Dariya tayi kana ta dauki cokali ta ɗanɗana komai tana lumshe ido har da tanɗan ludayin miya tace"Kai gaskiya aikon ku yana kyau komai ya yi daɗi,Allah ya ƙara zaƙin hannu yay maku Albarka....Eaaaaah sukace duka tare da rungemeta su na dariya,Tace gaskiya kun kyauta ina can ina bacci yau na makara."Zeenat ta ce momy inda ma baki tashi daga yanzu kija zamanki ki huta duk yanda kike koya mana aiki mun haddace mu zamu dinga maki...."Saudat ta amshe gaskiya ne."
Murmushi tayi ta dubesu kana ta ce"to muje a jera a teburin cin abinci,har ta ɗauki doyan da ƙwai Khaleesat ta karɓa,Momy je kawai ki hakimce komai yana zuwa,yau fa bazaki aikin komai,dariya tayi ta ce"To na gode."
Sai da su ka kammala jera komai yadda ya dace,sannan su ka nufi ɗakin su,wanka su kayi sannan aka shirya ƙananan da basu iya wanka ba,tufafi kowa yasa ya fito tsaf sai ƙamshi suke,inda ta ke zaune suka sameta Salima da Salma da Sareena su ka hayeta ana mata ina ƙwana.
Tashi tayi domin kiran Alhaji tana shiga ɗakin sanyin Ac da daddaɗan ƙamshin turaren sa ya daki hancinta,da sanyin muryarta mai kama da sassanyar sarewa ta masa cikakkiyar sallama wato ; Assalamu Alaika.
zaune ta sameshi yay wanka ya sha shadda jinin kare ya kafa hula wacce tayi dai-dai da shigar sa,ba ƙarya ya yi kyau,amma damuwa ce fal ɗauke a fuskarsa,zaune kawai yake yana nazarin duniya,kallonta ya yi tabbas ta masa kyau,kuma tausayinta ne aransa sai dai ba yadda zaiyi da abinda ya gagari wuta!"Wa alaiki Salam Iwar Alheri,ya furta tare da sakin fuska."
Murmushi sakar masa ta ce"Ko dai ka manta sunan nawa Yallabai?"Ai UWAR 'YAN MAATA shi ne yafi dacewa dani kuma a yanzu har koyaushe sunan yana matukar burgeni,ina jin daɗin a kirani da shi in amsa, don 'Ya'ya maata Rahma ne,kuma Alheri ne sannan jin daɗi ne,a wani zubin kuma hutu ne."yanzu dai muje k'asa abincin yana jiran isowar mai gayya uban gayya Abban Ƴan maata.
Dariya Alh.Bello yay a zuciyarsa yana mamakin halayenta, kamar ba ita ce da kuka ba daren jiya,amma yau kamar bata san da zancen auren ba, tayaya ma tayi saurin hak'ura tun wuri hakan...? shi fa shiyasa yake ta zullumi hankalinsa ya tashi yana jin tsoron haɗa ido da ita,amma gashi ta basar....To ko daman haka kishi ya ke? Ba mai bashi amsa,shiyasa ya juya akalar tunanin sa gefe,ya dubeta yace"To muje daman na kammala shirina yanzun nake son in fito in ɗebi girki nan,me aka dafa mana yau?
Ai yau ƳAN MATAN gidan nan su ka dafa ina nan ina bacci,wucewa tayi gaba tana karairaya yana biye da ita kamar wani sahorami, yana kai kice zamuci jagwalwale anya zan iya ci? dariya tayi Ta ce"idon ka da harshenka su ne zasu gane maka."
Inda aka tanada na Musamman domin cin abincin iyalan gidan,su ka nufa cikin farin ciki.Yaran su ka samu duk a zazzaune kan kujeru cif su Tara,Alhaji da Hajiya su ka zauna nan su ka kammala su goma sha ɗaya."
Gaida Daddyn su sukayi,da murna ya amsa masu yana washe baki,abin mamaki dan yaushe rabon su da su ga hakan har sun manta."Da wasa ya ce"anyi kuwa yau zan ci abincin nan naku?Zeenat ta ce Daddy ai ya yi daɗi,Uhummmn to bari muji cokali ɗaya ya kai bakinsa yay murmushin jin daɗi yace"Lallai yau kunci kyauta wannan daɗin...Daga nan dai ya dinga jansu wasu tare da raba masu kuɗi,su na jin ɗaɗi,har su ka kammala cin abincin nan yace"su shirya yau yawo za'aje."
Sun ji daɗi sosai mota biyu suka cika aka ƙwashi hanya sai sahad akai sayayya kamar ba za'a daina ba,duk abinda suke so tun daga Mommy har kan auta Sareena kowa sai da ya darje,daga nan aka wuce celebrity park akai ciye-ciye da lashe-lashe yunin ranar dai Alhaji Bello yana tare da iyalan sa ko kasuwa da shagunan sa na cikin gari bai leka ba."
Ana can wurin yawon shaqataw, sai da yamma lilis su ka dawo gida a gajiye,nan aka bud'e sabon babin shagali gwanin sha'awa.
**************** BAYAN MAKO BIYU
Zuwa yanzun Hajiya Babba ta gama duk wani shirin da za'ayi na auren D'an Inna(Alhaji Bello) da Zillaziya,Don ta tura kawunnansa sunje neman Auren a gidan Buzu Mai shayi anyi maganar auren da ƙannan Karima,dan Buzu cewa yay dole sai anje ƙasar su,Ita kuma Karima ta ce"Ba zata saɓo ba,don in Hajiya Babba taji zancen Buzu biyu babu za'ayi dan haka tasa ƙannanta su ba da auren,Akai komai har rana an yanke nan da wata ɗaya za'a d'aura dan Hajiya Babba ta ce"Ba'a buƙatar komai amarya kawai ake so."
Gefen Alhaji Bello ba dama, don a yanzun wani sabon so da ƙauna matarsa da ƴaƴansa yake ji,tare da tausayin su,jikinsa na bashi duk sauyawar da yay a baya ba banza ba ne,don kamar yana da nasaba da Hajiyarsa,tun da tayi masa maganar aure ya yadda ya daina jin wannan abubuwan a kansu. "Komai sai da ya sauyawa Halima na ɓangaren ta da na yaran,a cikin sashen sa na k'asa ne ya warewa amarya ɗaki ɗaya da falon mai wurin cin abinci da madafa."Ita kuma Hajiya Halima daman tana ɓangarenta sama da ƙasa ita da yaran da Alhaji.
Hakan da yayi ya yiwa mata daɗi don amarya dai tana iya ƙasa,kuma a ganinta gefen amarya ko rabin sashen yaranta baiyi ba,bare nata sashen,A zuciyarta cewa tayi" An dai samma Amaryar ne kawai"Kar a mutu ba'a shuka ba"Duk sai taji damuwar ta rage,dan gidanta yana hannunta, cikin ƴan ƙwanaki sai shirin auren akeyi sai kuma Allah ya yaye mata komai,dan kuwa har haske da jiki tayi ba kamar kwanakin baya ba duk ta rame ta lalace sanadin saka Auren a rayuwarta.
Amma yanzu wasai ta ke jin ta dan komai Alhaji Bello yay mata har kud'in jari ya ƙara bata don duk ya faranta ranta mata ta ƙwantarda hankalinta,shiyasa ta d'auki aniyar faranta ran mijinta da yaranta yadda bazata bar wata kafa ko ɗaya da wata zato ta samu gurbi a zaman su."
Gefen Zillaziya abin nema ya samu,"Wai an baiwa mayya raino"Sai wani kauɗi take acikin unguwar su ba wanda baisan zata auri Alhaji Bello ba,har ƴan kore ta samu masu take mata baya,ta sauya ƙawaye ta nemi pan k'arya dasu ta ke."Cikin gidan su ma yanzun ita ce sarauniyar da ke mulkin Buzu mai shayi da Karima dan ita ke faɗa aji,suma iyayen a biye su ke da ita,saboda kud'in da ta ke samu a gurin Alhaji dan baya zuwa inda take ita ce ke kiransa awaya kullum,kuma dabara ta roƙeshi kuɗi ya turo yaronsa a kawo mata,to fa dasu ne ta ke basuwa ana sayen abinci da sauran avubuwa,cikin ɗan lokaci ta sayawa Karime ledar ɗaki, idan ya bata zanna da lesi sai ta ɗinkawa mɗMamma da Safara'u."
Su Safara'u anyi laushi an zama ƴan abi Yarima asha kiɗi,don idan kiɗa ya canja salon juyi sauyawa yake ,duk da har yanzun tana fad'awa Zillaziya gaskiya, amma kuma idan tafara sara tana duba bakin gatari, don ita ma adinga damawa da ita."
Har yaran unguwar kowa da Aunty Zilly ake kiranta domin chocolates da alawa take raba masu dan kawai ta nuna ita wata ce, ƙawayenta ma da Hajjaou su ke kiranta ko matar Alhaji,hohoho sai taji dad'i tana ƙara rawar kai, yanzu kam Zillaziya ta kasance tararuwar unguwar fagge, da zarar an fad'i sunanta an santa,wannan abin yana matuƙar burgeta."
******************* Kamar yadda ta ke kawowa musu ziyara lokaci zuwa lokaci,hakan shima ya tattara nasa iyalan,don ance"Yaba kyauta,tukuici duk da ziyara aikin alheri ne kuma abu mai kyau ne,sannan ba'a gajiya da shi don sakamakon aikata alheri yana gurin Ubangiji."
Basu tsaya ko'ina ba sai gidan Umman sa, a cewar sa yau dukkan su har shi kansa inda Umman zasu yuni.
Farin cikin maras adadi Hajiya Umma ta samu kanta aciki, ganin Abbu da Ammi da su Nabeela dukan su a gidan.
Da murna su ka zauna ana musayar gaisuwa sai hira ake da raha,nan Umma tasa mai aiki ta sake d'aura wani girki na gargajiya tuwon acca da miyar taushe."Tun da ga ƙarin masu ci sun zo musu a bazata, Ammi(Juwairiyya)ta shi tayi ta fad'a madafa tare da taimakon ƴar aikin ta Umma, sai aiki su ke suna fira,Umman ce ta samesu ita ma ta haɗa miyarta da kanta irin ta tsoffin mata.
Bayan awa uku da rabi, aka gama dafa abincin har da zoɓo da komai,sai falon ya gauraye da daddad'an ƙamshin ga man kuli da man shanu, da Daddawa da kayan yaji sun wadatu a miyar."
Cin abincin ake ana ta zuba santi ,Abbu da Ammi har da ƙari bare su Nabeela,Aysha,Yaseera, Khadija da Auta Fatima ba'a magana."Nabeela har da faɗin Umma miyar nan tayi amma kince tun safe kika ɗaura sai zuwan mu kika haɗa gaskiya ta ɗauki lokaci "
Umma Ta ce "Ai hakan ake miya ana so ta d'auki lokaci tana nuna Yan mata, ba irin naku miyan ba na zamani ina gani a talabijin wai miya minti talatin an gama to ina dadin yake?Yo ko gardin Naman ya gama fita ne?bare kayan ɗanɗano su bayyana kansu, kyawon miya a d'aurata tun safe wajajen goma sai sauketa zuwa azuhur komai ya gama nuna ya had'e."
Dariya Nabeela tayi Ta "ce kai...Umma ai acikin waɗannan awowin anyi anyi abinci kala biyar....oina laifin awaya ɗaya."
Ammi Ta ce "Ai Umma bazasu iya haƙurin hakan ba,shiyasa ake abinci ba kai ba ƙafa, ni daga yanzu ma zanyi koyi da ke Umma duk da girkina yana cin lokaci amma zan ƙara wani."
Abbu dariya yay yana tand'ar hannu domin in da sabo ya saba da cin girkin Umman mai dad'i amma ba ƙarya miyar yau tafi ta koyaushe, duk ko Juwairiyya ba baya ba gurin girki dace biyu yay a duniyar abinci."
More comments more typing.....
'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄
💄💄💄💄💄
*NA*
*NABEELA DIKKO*
*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*
_Home of Brilliant Writers forum_
_LABARI_ _TSARAWA_ _RUBUTAWA_ _HAK'K'IN MALLAKA_
```'Yar mutan Dikkawa```
BABI NA 16/17
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._
************************ Lokaci sai tafiya yake yayin da ƙwanakin ƴan Adam suna shuɗewa,rana da mako sun wuce,har Allah ya kawo ranar...Abu kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba,domin jama'a da dama sun shaida da ɗaurin auren Alh.Bello Balale da Amaryar sa Zillaziya,a babban masallacin jumma'a,wanda ya samu halartar manyan ƴan kasuwa da ƙososhin gwamnati."Sai da babu mutum ko ɗaya daga dangin Buzu,ƙannan Karima ne su ka shige gaba ga komai."Anyi hidindimu an kashe kuɗi sosai wanda duk a bakin aljihun Alhaji suke fitowa."
Farin ciki a gurin Hajiya Babba da Karima ba'a magana sai murna ake,da yamma lilis aka raka amarya gidanta in da aka tanada domin ta aka wuce da ita,ƴan uwan Hajiya su ne ruwa da tsaki agurin tarbon Zillaziya wacce a zuciyarta ba'a iya misalta abubuwan da ke ciki."Komai an gyare tsaf an zuba kaya na mutunci kowa sai fatan alheri yake."
"Ƙawayen amarya sun sanyata agaba sai tsiya suke mata,faɗi banza faɗi wofi,ita ma bakinta gareta da ance mata caaas...zata ce aaaasss,sun sha hira da santin gidan, sun jira shigowar Ango da Abokan sa,amma basu ba labarin su har dare ya yi,shiyasa su kai sallama da ita,kowa ya watse akabar Amarya kad'ai a ɗakin tana jin haushi.''