Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 5

Uwar y'an mata complete - Chapter 5

Uwar y'an mata complete Chapter 5: Uwar y'an mata complete Chapter 5. Wasu Hawayen baƙin ciki suka zubo mata a fuska!wanda ta daɗe tana shanyewa agaban…

4,421 words

Wasu Hawayen baƙin ciki suka zubo mata a fuska!wanda ta daɗe tana shanyewa agaban ƙawayenta,taso tayi jarumta amma ta kasa,tashi tayi tana zagayen ɗakin duk da hasken sa amma ita duhunsa ta ke gani matuƙar ba Alhaji ta gani ba,jikin tagar ɗakinta taje tare da yane labulen, farfajiyar gidan ta ke kallo kamar wata k'asa ba waje Nigeria ba,domin ko'ina haske ne ɗaar,ga furanni da masu kyau,goge hawayen ta tayi tare da ajiyar zuciya,washe baki tayi ta dinga tikar rawa tana fad'in"ga gidana...ga gidana tana ƙyalƙyala dariya..."Hasken motar da ta hango daga wajen gidan yasa ta koma saman gado ta rufe fuskarta dan tasan angwayen ne tafe."

**********Hajiya Halima tana sashen ta ita da ƴaƴanta da ƴan uwanta,da su ka zo auren da k'anwar Hajiyarta.sai kuma matan yayyenta biyu."Sai baki su ke bata akan ta ci gaba da dakiya da haƙuri tare da kawar da kai akan duk abinda zataji ko ta gani a gidan,ta sake kowa ta kama Allah." Murmushi tayi ta ce"Ai ba komai idan da sabo na saba kuna gani fa yau ma tun daa rana danginsa su ke min arashi su na habaici tare da kirana uwar ƴan mata,ita ɗiyar ƙanwar Hajiya ce ke faɗin Allah dai ya kawo amarya lafiya ta zamo uwar magaji,kamar haihuwar ɗa namijin a hannunsu yake..."

Aunty ta ce"Karki damu da waɗannan zantuka nasu Halima,don na fahimta cutar jahilci ta toshe musu kai, ta buɗe baki tayi magana sai sukaji sallamar shi."

Amsawa sukayi fuskokin su asake, Alhaji Bello ya gaisa da cikin kulawa tare da musu ban gajiya,su Zeenat,Khaleesat,Saudat da Bilkisu ne basu bacci ba,su ma sannu da zuwa sukayi masa,Nan ya baiwa Hajiya Halima manyan ledoji uku yace"Ta sameshi falon sa,su Aunty da Daada ta miƙawa, sannan ta wuce ɗakin ta dan ta kimtsa ta ta tafi."

Daada ta bud'e leda ɗaya Naman kaza ne cike,ta biyun kuwa fresh milks ne masu sanyi,sai ta ukun chocolates ɗin yaran ne,Ta ce"Bawan Allah Bello."Hmnnnnn da alama zaiyi adalci wataƙila ko duk na dannar kirji na,ake Inji Anty Saratu.

Ai yana da kirkin sa Bello dan kawai Hajiyar sa tana shiga tsakanin sa da Halima ne,kuma ko ita canjawarta fa sanadin haihuwar yaran nan mata tara ne,shi ne ta tsaneta har sauran dangi su ka mara mata baya."

Uhumnnnn Allah ya kyauta Daada,amma ko yanzun sai Sadiya tayi haƙuri ki duba ko kawo amarya da ake gurin uwargida, Yan uwan Amaryar da dangin mijin basu kawota ba,kinga basu nemi hanyar zaman lafiya ba."

Bari kawai Anty Halisa ashe bani kad'ai abin ya baiwa mamaki ba,Ace akawo amarya har a 'yan kawota su koma mirsisi, ba tare da an kaita inda uwargidan ta sun gana,Inda ba gida ɗaya ba ne,ba laifi amma ana zaune guri ɗaya."

Daada ta katse su tare da fad'in kudai ku barsu kawai to meye aciki?shi wanda ya had'a su,ba gashi nan zai tarasu ya yi masu jawabi ba!su suka sani dahuwar mutum mai ƙosar da shi,kuma aniyar kowa ta bishi,Allah ya tsare mana Sadiya da tsaronsa,ya kuma kareta da kariyar Ameen....Ke Zinatu ɗauko mana faranti muci kaazaa..."

Dariya Zeenat ta yi Ta ce" su Daada masu bakin cin kaza,Saudat ma dariyar ta yi tare da ƙokarin daukar minti ta kai bakinta, nan su ka sauya firar tare da yiwa yaran nasiha sosai don yanzu zaman ya sauya,duk da kowa na nashi sashi amma dai suyi hattara da Amaryar."

Ko da Alhaji Bello ya shiga ɗakin amarya, zuciyar ta, ta kawo wuya wani haushinsa take ji don ita a zatonta dakinta zai fara shigowa,da zarar ya shigo amma sai ta ga saɓanin hakan."Da ƙyar ta iya amsa sallamar sa tana turo baki,shi kam bai ma kura ba, zaunawa ya yi,tare da fad'in Amarya sannu da zuwa."

Yawwa Angona,sai mamaki ta ke a zuciyarta,to ina abokan ango da zasu sayi bakin nata su ke?Maganar shi ta katse mata tunani yace"To sai ki fito muje falo ga yayarki can...in maku nasiha sai mu ƙwanta dan nasan kowa a gajiye yake bacci nakeji sosai."kuttt...ta haɗiye wani malolon ɓacin ranta, ɗagowa tayi tare da yaye mayafinta...Idonta ya yi arba da shi sanye da jallabiya kalar kasa,yake ba komai a hannun sa,kamar ba ango ba."

A hasale Ta ce" Haba Alhajina dubeka wai Ango ne da jallabiya,ba shiga mai kyau irin na angwaye,wato ban cancanci ai min ƙwalliya? gaskiya banji daɗi ba har par ledar kaza babu a hannunka."Duban ta ya yi sosai idonta a tsaye ko alamar kuka babu, girgiza kan sa ya yi tare da murmushin mamakin Zillaziya."

Ya ce"To malama ai haƙuri wato gajiye na dawo shiyasa ina shiga sashen Hajjaou wato yayarki sai na wuce nawa sashen na cire kayan angwancin na ɗan watsa ruwa, afwan Amarya kinji ban san laifi ba ne, sannan batun kaza da kikeyi ban manta ba tana sashena na ajiye maki kura sarkin kwaɗayi...

Murmushi tayi yanzu nice kura Alhajina?Dariya ya yi yace to kin aza faɗa dan baki ga ledar kaza ba,A'ah nifa ba dan komai nayi magana ba sai don ina ƙaunar ka,abin fa da haushi ango ba ƙwalliya ba Leda."

Wucewa ya yi gaba tana bayan sa har falon sai dai ba kowa,zaunawa sukayi nan ya danna waya ya kira,ɗauka ta yi ya ce" ranki ya daɗe muna jiranki, wata harara Zillaziya tayi masa a fakaice tamkar idon zasu zube ƙasa, tare da cizon yatsa ta gyara zamanta daf da shi ta na wani kaudi."

Jimnnnn kad'an ƙamshin turaren ta ya mamaye falon,wani iri Zillaziya taji a jikanta,bata ƙara tsinkewa ba sai da ta ji zazzakar muryar Hajiya Halima tana musu sallama."

Taso daurewa ta amsa amma ta nemi miyau bakinta ta rasa don duk sun ƙwafe,Alhaji Bello ne ya amsa mata,Gefen sa ta zauna tare da fad'in sannu da hutawa Yallaɓai."

"Yawwa, sannu dai Gimbiya Inji Alhaji yana murmushi."

Bayan ta zauna nan Alhaji ya fara jawabi tare da nasihohi akan sun zauna lafiya kowa ta ɗauki girmanta da matsayinta,sannan baya so a sako ƴaƴansa a cikin rayuwar zamantakewar auren su da dai sauran su,ya daɗe yana lurar da su,har ya kammala duk jawabansa,sannan ya dubi Halima yace"Ranki ya daɗe ko da abinda zakice?"

Murmushi tayi Ta ce,A ba abinda zance,duk abinda ya kamata na faɗa ka faɗa,In sha Allah ba damuwa yallaɓai zaka same mu masu biyayya,Allah ya bamu zaman lafiya,da zuriya ɗayyiba."

Tsaki Zillaziya tayi tare da tashi tsaye wani kallon sama da k'asa tayi masu kana ta tashi zata wuce a fusace!"

Alhaji ya ce"Kenan dai ke ba ki da abinda zakice?babu Alhaji dan Uwar Ƴan mata ta gama zance Allah ya ba mu Alheri." mamakin ta yake kamar ba salihar yarinyar ba, mai hankali,duk da ya san wataran tana da rawar kai amma ya lura,tana da zafin kishi."

Tashi tayi Ta ce"To sai da safe,batare da ta dubeshi ba ta huce zuciyar ta na bugawa!wani kishin sa ne ya mamaye duniyar kirjinta ,da kyar ta samu ta isa ɗakinta tana fara rusa kuka,wato Amaryar sa ma da hakan zata kirata shiyasa bata gaidata ba,domin tun waje an labarta mata wacece ita!A zuciyarta tace idan kuwa haka ne ba zan lamunce wulaƙancin dangin miji da na kishiya ba dole zanyiwa tufkar hanci."

A dakin Zillaziya sai yawo ta ke tana zubda ƙwallah domin ta fahimci Alhajinta yana son kawo mata wani salo,ya za ayi ta ga yana kulawa da uwargidan sa,bayan Hajiya tace kashi ya fita a gidan,tayaya zai nuna mata soyayya bayan nce baya sonta kuma duk su Hajiya Babba da sauran dangi basa son ta,tayaya hakan ta faru to?Bayan ita tazo a matsayin matar so ake neman mayar da ita bora."

Hmnnnnn akwai aiki jaa a gabanta kenan dan taga uwar ƴan mata ta fita haɗuwa da komai,babu ma abinda zata nuna mata tun kan zubi da tsari har cikar halitta da haiba."

A hakan ta sauya kayan ta zuwa na bacci har ta ƙwanta amma mamaki da takaici ya hanata shaƙat,ɗakin da ya nuna mata a matsayin na shi ta nufa, don duk zatonta ya shigo ya rarrasheta amma babu shi ba labarin sa,A ranta ta ce" wallahi sai naje na amso kaaza ta ai idan sun san wata basu san wata ba,har mu ake ma bariki...hmnnnnn basu san wacece ni ba.''

Jikin ƙofar ta isa murd'a k'ofar,shiga tayi cikin iya taku,da sallamar ta zaune ta sameshi ya dafe kan shi,a zuciyarsa nazarin ta ya keyi har ta isa tayi masu tsaki dan rashin kunya!jin an taɓashi ya sa ya dubeta da sauri...."

Janye hannun tayi cike da kunya,ta ce dan Allah Alhajina kai haƙuri nasan bai dace nayi mata tsaki ba don yayata ce,sai dai zafin kishin ka,da soyayyar ne suka rufe min ido har na aikata babban kuskure hakan,gurfanawa tayi tare da dafa kafafun sa,My Dear kayi haƙuri ko zan samu sukuni,kai ne farin cikina,farin ganina,hasken rayuwata in shaa Allah gobe zan nemi ta yafe min zan bita sau da ƙafa zan girmamata....Hawayen da takeyi ya goge mata, tare da fad'in kiyi shiru na yafe maki,daman na fahimci kurciya ke damunki,amma ki kiyaye aikata hakan bana son raini kuma ba zan lamunce hakan daga gareki ba."

To Alhajina zan kiyaye,nuna mata leda ya yi yace"Dauko ga kaazar ki can,da sauri ta tashi ta ɗauko tana lasar baki,buɗewa ta yi yawonta ya ƙara tsinkewa, sai zare ido take bud'e ƙafafu tayi domin tuni ta manta da amarya ce,Naman kaza ta dinga ci, ko kallon Ango batayi ba,sai da ta cinye rabi sannan ta bud'e lemon ƙwali ta sha,ta ci gaba da cin kaza tatas ta cinye kaza d'aya."Ya ga abin mamaki wannan wace irin mayyar yariya ya auro sai tazgar nama take,dariya ya yi ya na dubinta."

Sai da cikinta ya ɗauka komai ke dawo mata musamman da taga ita ya ke dubi,ga shi har ƙashi ta taune ta tsotse,cike da kunya ta sosa kai,wallahi naji yunwa rabona da abincin kirki yau ƙwana biyu,Alhaji lafiya dai?

Lafiya law kice inda nasani na sawo kaza biyu,murmushi tayi ta ce" har mun cinye wannan ne?

Dubanta ya yi yace ai kece kika cinye ta tatas,ki ƙwantar da hankalinki in dai kaji ne sai sun isheki agidan nan,don har gonar su ina da."

Washe baki tayi ta ce"Haba Alhajina ashe faɗuwa tazo dai-dai da zama,daman ina da matsalar iskokai,Momma ta manta bata faɗa maka ba!Da zarar naga kaza to yanzu suna hawan kaina har sai sun cinye ko nawa ne,ai inda kazar nan biyu ce ko uku zaka sha mamaki dan tatas zasu cinye ta.Kayi haƙuri ban san na cinye ba duka kazar ba."

Dariya ya yi ya dubeta,yace "Zillaziya lalle wannan Aljannun zasu ci kaji har su gaji dole su fita jikinki.Yanzu shiga bayi ki wanke bakin ki,ki ɗauro Alwala muyi sallah mu ƙwanta."

Bayi ta faɗa ta jima bata gane kan kayan da ke cikinsa ba,a karshe dai shi ta kira a kunya ce ta fad'a masa ta k'asa gane yadda zata bud'e famfon ne."Sai da ya koya mata sannan ya fita.ita kuma Alwala ta d'aura ta fito."

Bayan ta fito suka ta da sallah.Addu'oi ya yi tare da mata tambayoyi akan wanka da Sallah,ta amsa wasun,wasun kuma ta k'asa dan ta daɗe rabonta da islamiyya,Safara'u kaɗai ke zuwa."

*'YAR MUTAN DIKKAWA CE*

[11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

18/19

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

Ina manyan mata maganin ƙananan mata ku garzayo domin gyaran ciki da ban fata,Aƙwai mata,aƙwai muna mata,aƙwai mun rako mata,aƙwai cikon mata,To mata muke nema ƴan ƙwalisa ku zo inda *Mg's skincare* mai abin mamaki tana magana... Hi my people🙋‍♀️ Ina gaisuwa Toh albishirinku😬ku karkade kunnuwanku kuji inamai sanarmaku cewa set dinmu ayanzu yazama available maiso yarugo aguje karya tsaya Sanya ayi babushi☺️kundaisan kayan *mg's* dabanne ba karya indai tafannin gyaran jikine kunsan yanda sabulun mg's herbal whitening black soap kemaida fata tazama Babu kuraje, pimples, acne,eczema, stretch mark, knuckles,black head,spot,dama duk wani matsala daya danganci fata duk wnd yayi anfani dashi yasan yanda yake maida jiki yazama abun burgewa abun kwatance, fata tadinga haskawa tana walwali duk inda kikashiga sai anyaba😍 toh Inaga wannan zazzafan set Mai maida tsohuwa yarinya☺️Uwargida Takoma amarya😁 amarya Takoma tamkar yanmata❤️yanmata Kuma sudawo Yan Sha shida fata tadinga walwali tana daukan Ido 😉 wani abun ba'a magana shiru akeyi sai Wanda yajaraba shine zai karas😘bama cika Baki duk wnd yagwada shine zaifadi ynd product din mg's yake❤️Kuma munakara Fadi cewa kayanmu organic ne bana bleaching ba suna tsagwaran gyaranjiki ne fiye da tunaninku kuyi kokari kushigo Kuma adama daku Wanda bayada halin siyan set toh sabulun mg's kadai kukarike kankat ne insha Allah🤭 Set dinmu yakunshi Soap,body cream,face cream,body nd face scrub, cleanser, Price:13k Kaman ynd nafadi Wanda bazasu iyasiya set ba sabulun kadai zaibaku mamaki shikadai kukayi anfanidashi zaigoge duk wn prblm na skin living the skin fresh,smooth nd make the skin to glow set din kawai zaikara murje fatane buh ko soap mutum yake anfani dashi ba'a magana🤭 Soap price:3k

Mai bukatan Kaya should chat:08062991549 Call:08064532391 To plc ur order Munada komai available now so hurry nd grb urs before you hear sold out🤗

Karkubari abarku abaya ko abaku lbr domin kynm yanagyara ko fatan d Mai yabata komutum bashida komai zai iya using kayan zaisa jikin k yafidda wn kyau medaukan hnkl duk inda kikayi se ankalla,show ur skin some luv domin mata da gyara akasanmu😍just gv it a try nd ur skin will definitely/forever thank you❤️

Mn Kaya kowani gari buh delivery is not free🤗

Team glow🧖‍♀️ ******************** "Kasancewar an wayi gari da Amarya da gidan,duk da kowa da sashen sa,sai dai ba'a zuba ma Zillaziya kayan abincinta ba a nata sashen,saboda hakan ne yasa Hajiya Halima ta tasa ƙeyar yaran,don su haɗa abin kari."

Abinci mai rai da lafiya su ka haɗa,aka jerasu gurin da aka tanada domin cin abinci,komawa tayi ɗakinta ta shirya tsaf, tare da zuba kaya masu kyau ta fito,yaran ta samu duk sunyi wanka su ma sun shirya,tana fitowa ta samesu falon su na kallo."

Sareena ta ce"Mommy muje mu ci abinci,yunwa nikeji."Murmushi tayi tare da dubin wayarta,tunanin tayi ta kirashi sai kuma ta ga rashin dacewar hakan,kuma tana ganin kamar wani abu ne,idan Alhajin ya fito ya samu sun karya,bayan tare suke karin a gidan."

Tana cikin tunanin ta jiyo sahun tafiyarsa,da ƙamshin turaren sa,runtse idon ta domin jin wani abu,da ya taso ya tokare mata zuciya wani jiri taji yana ɗibanta" _Hasbunallahi wa ni'imal wakik_"kalmar da ta furta kenan,dai-dai shigowarsa falon da sallama,daga ita har yaran amsawa sukayi tare da gaida shi,da farin ciki ya amsa yana dubanta amma taƙi bashi damar su haɗa ido da shi."

Zama ya yi tare da jan yaran da fira,nan dai ta ce"Yallabai muje mu karya ina ƙanwar tawa?"Tana can tana bacci muje kawai dan ni zan fita shago idan ta tashi ta ci daga baya."A'ah ba'ayi haka ba duk da ba daɗi a tasheta amma bari na cire mata nata,zuwa anjuma na aika mata,yafi mu ci mu rage mata Amarya ce dole a karramata..."Katse ta ya yi ya ce"To mai ƙanwa duk yadda ki kayi ba damuwa."In da teburin suka nufa kowa ya zauna cif ba sauran kujera,nan suka karya bayan sun kammala ɗakinsa ya koma ya ɗauko mukullan motarsa da tarkacen da yake fita da su,ya fito rakiya tayi masa tare da adawo lafiya."

*************Sai wajajen sha ɗaya da rabi ta farka daga bacci,ɗakinta ta shiga ta watsa ruwa tasa gayu sannan ta fito tana hurar hanci,tana isa falon ta samesu zaune,gaida ita sukayi amma ta watsar da su tana hararen su ganin bata ga Hajiya Halima ba shiyasa ta ce"Kai marasa kunya ina Uwar Ƴan Maata?Banza su Zeenat sukayi mata...Ta ce kai ina Uwar ku nace...?Zeenat ta ce Uwar mu tana ɗaki!kije ki rika min ita Zillaziya ta ce tana ta da murya."Jin magana sama-sama yasa ta fito daga ɗakin ta ce"Zeenat menene?Bakomai Mommy bamu mata komai ba ta zo tana kiranki,da Uwar ƴan maata kamar yadda su Hajiya ke kiranki."Tana isowa tace"Amarya da kanta kin tashi lafiya?inji Halima."

Riƙe ƙugu tayi tare da turo ɗan ƙwalin ta gaba,ta ce "Da ban tashi lafiya zaki ganni?kice ƴaƴan naki mata basu da kirki, kin gansu nan daga tambaya shi ne suke min rashin mutunci...Kiyi haƙuri dan Allah sha'anin ƙurciya ne,Ta maida dubanta ga yaran ta ce ku kuma ku kiyaye ni kar na ƙara ji ko ganin hakan kunji ko!maza kuce tayi haƙuri...Dan Allah kiyi haƙuri sukace dukkan su."

Tsaki Zillaziya tayi kana ta wuce sashenta, a ranta tambaya ta ke ina Alhajin?Tsaye tayi tana mamakin yadda Amaryar ta shigo gidan,ajiyar zuciya tayi tana mamaki amma addu'ar zaman lafiya tayi sannan ta kira mamu ta kai ma Zillaziya abin cin ta,ɗauka tayi tana fushi ta isa ƙofar ɗakin tana bugawa.Daga can ta ce" Alhajina shigo ban rufe ba,ai a buɗe ta ke...Shiga tayi da kuloli biyu a hannunta, ta ce "Amarya ga abinci inji Momyn mu,Kallonta tayi ta ce "Ajiye nan marar kunya tana hararan mamu,nikam da kunyata Amarya haka kawai, kuma harara ba mari ba,sai dai ruwan ido suyi kanta,mamu ta ce tana murguɗawa Zillaziya baki ta wuce abinta tana karkaɗa kugu."

Riƙe baki tayi ta ce"To ikon Allah lallai aƙwai rashin daraja a gidan nan,wannan marar kunyar yarinya sai naga abinda ya turowa buzu naɗi ni da ku,abincin ta buɗe ta fara ci har da tanɗar hannu."Wayar shi ta kira ruri uku zuwa huɗu,ya ɗauka ta ce Alhajina na tashi bacci banganka ba,ya ce"Amarya ni na fita tun ɗazu idan kin tashi kije ki gaida yayarki ta tanada miki abin kari sai na dawo,daga ya kadhe wayar ya ci gaba da aikinsa."Wasu hawaye ta goge masu zafi!cikin takaici, ta goge tare da ajiyar zuciya tana cizon yatsa....Daga waje ta jiyo sallamar ƙawayenta,a waje suna kururuwa da dariya suka shigo ɗakin da murna ta tarbesu nan su ka zauna aka ci aka tanɗe,sai buɗa musu Zillaziya su ke,ƙawayen kuma sai ƙara zuzuta ta sukeyi."

Da misalin ƙarfe biyu da rabi na rana,ta fito falon da ƙawayenta su ka zauna sai faɗi banza,faɗi wofi suke,yayin da Hajiya Halima ke madafa da yaran suna ɗaura girkin rana,sai da suka gama tsaf suna jin su Zillaziya na habaici da arashi,shiyasa tayi sashenta da rana su ka zauna su na kallo.Tana ganin hakan ta faɗa madafa,ta ɗebo shinkafa da su kabeji,miya na saman gas bata ida nuna ba,ta ƙwaso da duk naman kajin ta ajiye masu falon,ruwan gora da lemuka ta ƙwaso sukayi zaune suna ci suna holewarsu."

Zeenat ta fito duba miya amma ta samu akasin yadda suka barta,ganin su na cin abinci yasa ta tafi inda Momy tana faɗa mata,A fusace ta fito daga falonsu ta faɗa madafa ta duba tsaf duk an lalata shirin da tayi an zubar da abinci miyar ma an ƙwashe rabi,haɗin kabejin ma duk an zabge,rainin hankali ta ce a fili ta samesu suna ci suna ba da ruwa "Kallonta sukayi sama da ƙasa su ka fashe da dariya,iya ƙuluwa ta ƙulu da wannan iskacin nasu,shiyasa ta ce"Haba Amarya ya zaki ɗibi abinci,ba tare da kin sanar dani ba!kina gani miyata bata ko nuna ba,amma duk kinbi kin lalata komai idan ma kinyi amfani da abu bazaki ƙoƙari ki mayar ki rufe yadda yake,kamar ƙaramar yarinya,bana si karki ƙara min hakan..."Dakata!Uwar ƴan mata me kike nufi?ni da abincin gidan mijina amma sai kin min gori,to bari kiji yadda kike da matsayi a gidan nan haka nima da bamu da banbamci da ke,haka kawai ki zo a gaban ƙawayena kina ƙoƙarin cin mutuncina,saboda abinci abinda ni da ke duka muke da ƴanci dashi...kin sani sari ni ba ƴar yunwa ba ce,sannan ba girman Alhajina bane ai koke abinci a gidan sa."

Ke Daraja Larai Baraka ku buɗe ƙafafun ku kuci ku sha ku ɓararraje gidan arziki kuke bana tsiya ku ƙwashe arziki Allah ya kawo ƴar arziki rabonku ya ko ka."A'ah Hajiya Zillaziya bari kawai mu tafi ƙawayenta sukace bayan sun lashe abinci tatas suna tauna ƙashin kazaa,Haba dan Allah kuyi zamanku idan ma kuna son ƙari ai sai na ƙaro muku,nan suka ɗauki mayafinsu da ruwa lemo suka ƙara gaba."

Zillaziya ta ce "To Uwar ƴan mata burinki ya cika kin korar min ƙawaye...Bin su tayi har get ta musu rakiya sannan ta dawo,Hajiya Halima yaran ta kira suka ɗauke kayan tare da gyara Babban falon tsaf,sannan tasa su gaba tayi tafiyarta."

Zillaziya na shiga sashenta ta kira Karima ta faɗa mata ƙarya da gaskiya,kissa da kisisina tare da jawabin makirci ta zayyana ma ta."Daga nan Hajiya Babba ta kira tana kuka ta faɗa mata abinda Halima tayi mata cike da ƙarya tana sharɓar kuka,Hankalin Hajiya ya tashi sai haƙuri ta ke bata tare da faɗin zata ɗauki mataki."

Hajiya ki ɗauki matakin akanta da ƴaƴanta dan wallahi ba zan iya ba,haka kawai su haɗe min kai,bani da ƴanci!korar kare tayiwa ƙawayena akan abinci ni gaskiya gida zan koma,ko kuma ki zo da kanki ki mana shamaki."Karki damu gobe zan shigo da yardar Allah zasu san da ni su ke zancen,ni fa akanki komai zanyi ina ga idan uwar ƴan mata batayi hattara ba zata bar gidan a ƴan ƙwanakin nan."

"To Hajiya ki ɗauki mataki amma dan Allah karki nuna ni ce na faɗa miki,nidai ina son ki ƙwato min ƴanci na,bana son Alhaji ya ga da shigowata gidan na fara kaita ƙara a gurin ki..."Karki damu sai na zo,kashe wayar tayi ra dinga tiƙar rawa ta ce "WASA FARIN GIRKI."

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE

MORE COMMENT MORE TYPING [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄 💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_©️HAK'K'IN MALLAKA_

' ```YAR MUTAN DIKKAWA```

BABI NA 22/23

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

*Ina mai ba ku hak'uri masoya na, Ina ganin sak'onnin ku da k'orafe-k'orafen ku, akan labarin nan,wani lokaci na kanyi dariya😂 Kuyi min uzuri dan Allah,bana canja salon rubutuna domin wani ko wata,tun kan na fara nasan farko,tsakiya da ƙarshen labari na,wanda muhimman saƙon da zan isar yana bayyana,so abubuwa ne su kai min yawa ban samu damar ba da amsa ba,mafi yawan lokuta na kan shiga busy akan sabgogin online,amma zan gyara In shaa Allah za ku dinga ganin UWAR 'YAN MAATA yadda ya dace,Amma zance akashe Hajiya Babbar kar Zillaziya ta haifi ɗa namiji duk bai taso ba komai na Allah,Hajiya Halima da Ammi sun gaishe ku😀 na gode da nuna k'aunar ku gareni,hak'ik'a ku 'Yan baiwa ne domin ina jin dad'in Addu'oin ku, ni 'Yar mutan Dikkawa ta ku ce masoyana masu bibiyar zafafan novels d'ina.❤️

_____________________________________

Yau gidan Abbu su na cikin tashin hankali domin sun wayi gari Ammi ba lafiya."daga Abbu har yaran sun k'asa nutsuwa, domin tuni suka ɗauko ta zuwa asibiti agigice, an shiga da ita d'akin da aka tanada don bayar da taimako na gaggawa, Umma a firgice ta k'araso asibitin na Hamdallah Medical Center wanda ke kan titin D'orayi da ke Kano."

Ganin Umma ya sa hankalin su duka ya dawo gareta, Nabila da Aysha na hawaye su ka k'araso gurin kakar tasu, yayin da Yaseera da Khadija ke zaune kan teburi sun hade kai da gwuiwa, Muryar Umma na rawa Ta ce"Nabeela kuyi shiru mana, Fatima k'aramar daga cikin su Ta ce"Umma jikin Ammi yayi tsanani bata ma san inda ta ke ba...Kukan ne ya ci ƙarfinta ta koma fashewa da kuka."

Abbu da ke dafe da gefen kansa da ke masa tsananin ciwo! Ya yin da zuciyar ta tsananta bugawa,da k'yar ya dubi mahaifiyar sa."Ya ce"Umma barka da yamma har kin iso?"

"Eh...Ai ni hankali na ya matuk'ar tashi, tunda kai min waya naji muryarka a disashe,nace to abun ya tsananta!Wai me ke faruwa? ina ita Juwairiyya? Ya jikin nata kuma?Me kuma sukace ke damunta? Umma ta tambaya a jere."

Manyan idanunsa ya zubawa Umma wanda suka rikid'e tamkar jan gauta ya ce"To jikin da sauk'i fitowar su ne muke zaman jira yanzu hakan don tun isowar mu aka shiga da ita!"

To Allah yasa muji alheri Inji Umma tana ƙoƙarin zama inda jikokinta su ke zaune,tayi jugum tare da yin tagumi itama idonta ya dinga kawo k'wallah domin tausayi d'anta da yaran ya ratsa zuciyarta." Anan Umma ta k'ara tabbatar da zancen nan na macce ta gari gink'in gida ce. ta koma yarda idan ba ita gida ya faɗi."

****************

Zaune ta ke a cikin wani Babban zaure, su na tattaunawa da wani matashi."Ya ce tabbas Inna babu tantama akan duk abinda na fad'a miki, kuma muddin ba'a karya sharud'd'an mu ba, to za a kai gaci,nidai na fad'a miki a kula, don bama son garaje domin muddin aka samu matsala, ba'a bi hanyoyin da nace ba maganin nan ba zaiyi aiki ba."Kuma shakka babu gurbi zai b'ata Sha,dan k'yaik'yayi zai koma kan mashek'iya.Ina fatan kin haddace..."

Washe bak'i tayi Ta ce"Tabbas ko gargada babu, Matashi na Matasa."Zan fad'a mata kuma za 'ayi kamar yadda ka faɗa ba matsala...Na gode Allah ya ƙ'ara sani a ci gaba da taimakon mu, Inji Karime ranta fal da murna."

Dariya ya yi tare da gyara zaman sa, ya ce"Ba komai ai an saba Inna Karima,kuma na yaba da ke ina godiya nima,ki duba duk lungun nan na fagge,babu maccen da nake huld'a da ita kamar ke,saboda kin yarda da ni, muna ji kuma mu na gani, su matsiyatan matan lungu nan wani guri suke zuwa yawon neman taimako,bayan gamu muna sana'ar baki da hanci,wai a cewarsu in sun zo gurina asirin zai iya tonuwa,mutane su gan su. Amma ke Inna baki damu ba, kin wanke ƙafa ki zo,ki biyo duhun dare ki biyo hasken Rana,ki biyo da fad'uwar rana ki zo nan,to me zai hanani in taimake ki bayan nima kina taimakona, da na cefane har da kaji....ya tuntsure da dariya."

Karima tashi tayi tana k'okarin k'ulle maganin a gefen zanenta, Ta ce"Mallam ka barsu kawai ai duk bakin da Allah ya tsaga,sai ya ci,ko ana mazuru ana shaho sai ya ci ya sha, sannan rabo baya wuce mai shi, nidai ina tare da kai,dan ko na yadda da aikinka ai ya wuce yankan wuk'a. Kai ne fa ka warware asirin da Buzu yay min ya aure ni,sannan kayi min maganinsa na mallake shi sai yadda nace kamar raƙumi da akala, kayi ma Zillaziya na farin jini ka bamu sa'ar Alhaji da Uwar shi har an kayi,yanzu zuwa gaba za'a ƙara zazafa su."Ko Safara'u nasan tsabar nauyin jininta ne yasa har yanzu shiru,amma tabbas na yadda aikin ya yi kuma lokacin na zuwa...Hakane Inna ai Safara'u na duba taurarin ta duk bak'ake ne sai ma kin ba da wasu kud'i an sabunta aikinta don tuni ya lalace ya dawo ƙasa,kuma Inna bak'in jininta kamar na gado ne sai an tashi tsaye."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull