Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 6

Uwar y'an mata complete - Chapter 6

Uwar y'an mata complete Chapter 6: Uwar y'an mata complete Chapter 6. Ware Ido Karima tayi tare da rufe Baki ta sassauta murya Ta ce"Mallam wallahi nawa ne…

4,449 words

Ware Ido Karima tayi tare da rufe Baki ta sassauta murya Ta ce"Mallam wallahi nawa ne ta gado nima da ina budurwa haka iyaye na su kai ta fama har na san ciwon kaina na shiga na fita nima amma kaga ƙarshe na wai Buzu Mai shayi,ta ƙarashe zancen tana b'ata fuska."Amma masu kuɗi da yawa sun fito fa,da asirin ya yi sai dai ka ga tsabar rashin rabo duk ba'ayi da su ba,ko da yake shima magani yay min dan naci kuɗin shi,biredi,shayi,ƙwai sai nayi kyau..."

Tuntsurewa ya yi da dariya ya ce"Ashe abin duk jaaar kanwar ce Inna, ƙwarai matashi, yanzu dai sai na dawo za'a san yadda za'ayi. Ya yi Inna na gode,ya ce tare da mata rakiya har bakin zaure ita kuma tuni ta wuce tana surutai ita kaɗai a hanya akan lamarin Safara'u."

************* Hajiya Halima ce kwance a kan makeken gadon ta, tana nazarin akan wad'annan sabbin dokoki da Hajiya Babba ta gindiya masu akan Amarya Zillaziya.Caaf lallai akwai caƙwakiya Ta ce "A ranta tare da mamakin lamarin,duk da tun ɗazun ta tara yaranta ta ja masu kunne a kan harkar Auntyn su Zillaziya,kuma ta nuna masu ita ɗin mamansu ne domin matar uban su ce, kuma tana da tabbacin jan kunnen da tayi masu ya shigesu sosai."

A na ta b'angare kam ba sassauci komai zai faru sai dai ya faru dan ba zata tab'a ɗaukarwa kanta wulakanci ba. Dan muddin Zillaziya ta shigo gonarta to zatayi mata wankin Babban bargo."Su Aunty ta kira a waya tare da masu godiya da ban gajiya,haƙuri da kowa ke bata shawarwarin yadda zata zauna lafiya da abokiyar zamanta, Daga nan Hajiyarta ta kira su ka sha fira sosai ita ma dai lurar da ita tayi akan muhimmancin haƙuri da kawar da kai ta ce" Ta dage da yin Addu'oin neman tsari ita da yaran sannan kar ta kuskura tayi sakaci da Addu'oin Azkhar."

Godiya Hajiya Halima tayiwa mamanta tare da cewa in Sha Allah zasu k'ara kiyayewa, sannan sukayi sallama."

************* Zillaziya taji Dad'i kwarai da gaske da duk abubuwan da Hajiya Babba ta Alk'awarta mata kafin ta wuce gida,don gashi ta fara gani ba me shiga shirginta,rashin mutunci ba shafin da bata buɗe ba,har ta fara tunani akan yadda zamanta zai ɗaure a gidan da irin mulki da daular da zatayi musamman idan Allah ya bata haihuwar D'a namiji wato magajin Alhaji Bello.Tunano maganar Hajiya Babba tayi da Ta ce"To fa Zillaziya zata zamo sarauniyar majalisar dinkin duniyar gidan Hamshakin Alhaji Bello muddin ta haifo mana Magaji."

Da zumuɗi ta shirya acikin wasu kananun kaya,don yau Alhaji gurinta yake shiyasa ta dafa abinci,gado ta fad'a tana Jin daɗi ga sanyin AC na ratsa dukkan sassan jikinta, wayarta ta ɗauko tare da danna sunan mommah ta kira,ba jimawa Safara'u ta dauka."

Sallama tayi Zillaziya ɓata fuska tayi bata amsa ba, Ta ce"Ke yarinya Ina me wayar ne?

Tak'aici Safara'u taji a ranta ta ce ban sani ba jaka kawai tunda baki iya amsa sallama ba,tsaki tayi ta kashe wayar."

Kallon wayarta tayi Ta ce eyye lallai yarinyar nan ta raina ni, kamar ni matar Alhaji, uwar magaji, Hajiya Zilly,wata kucakar baƙauyar yarinya ƴar yunwa zata raina?lallai ma zata san ta kirani da jaka! zanje gidan agaban Buzu da mommah inyi mata rashin mutunci ba kuma wanda zai tanka domin yanzu ni ce mai juya gidan nasu....k'wafa tayi tare da cizon yatsan ta, sannan ta tashi, a Babban falon gidan taje ta zauna ba kowa, d'aura kafa ɗaya kan ɗaya tayi tana kallo, tana cin cingam, Zeenat... Zeenat... Zeenat!!!ta dinga k'walawa kira daga ɗakinsu Zeenat ta fito Ta ce "Anty Ina yuni gani...Tsaki tayi Ta ce" lafiya, bakiji tun ɗazu nake kiranki ba?

Ina bayi shiyasa ban amsa inji Zeenat

To su 'yan uwanki mata ba zasuce kina bayi ba?Ni dallah je madafa ki dauko min naman kaji idan uwar ku ta dafa,yau ban dafa ba!sannan cinya huɗu da ƙwallin lemon abarba da kufi tangaras da ruwan gora zaki kawo."

To Zeenat Ta ce"Sannan ta wuce haka akai dan duk ta ɗauko abinda Antynta ta umurceta a ranta tana mamakin wannan Amaryar kullum cikin cin nama ta ke bata gajiya. Ajiyewa tayi har zata wuce Ta ce" Ke dawo...ki zuba min lemun a kofi,To Zeenat Ta ce tare da zubawa ta bata, Kina iya tafiya,saura inji anyi gulmata yaro ya ɗanɗani kuɗarsa."

Wucewa Zeenat tayi tana mamakin Anty to wai ma me ta ke nufi da su ne...?lalle ma akwai babban aiki dan ba zasu zama 'yan aiki a gidan uban su ba."Kawai don suna bin umurnin ɓomynsu ne da tabasu akan duk abin Antyn ta sa su kar suce a'ah."

Bayan Zeenat ta wuce dariya Zillaziya tayi Ta ce" Aiki yanzu ku ka soma da kanku zaku bar gidan nan ta hanyar baku wuya,daga ku da uwar ku,ai idan masara taji wuta da kanta take kuka."

Naman kajin ta dinga ci tana shan lemu ɗad'i fal a ranta,k'atuwar cinyar kazan ta duba ta fashe dariya Ta ce"Wallahi kaza Ina da takaicinki kuma zaki gane bakin talaka yayi miki kad'an gurin ci, daga yanzun zan darjeki kamar an aikoni, ko da kuwa ina ci ina amayeki ne... koma gaftar cinya tayi tana murmushi har da lumshe ido,wayarta ta d'auki ruri yayin da Momma ya bayyana a gilashin wayarta har ta so tak'i ɗauka,sai kuma tayi tsaki cike da yanga da fusge fuska ta d'auka tana hurar hanci.....

Laifin Dad'i....

Ku biyoni domin jin yadda zata kaya

Shin Zillaziya zatayi nasara kuwa?

Me ke damun Juwairiyya?

Ya makomar UWAR 'YAN MAATA ta ke da yaranta?

Shin ko burin Hajiya Babba da Karima zai cika?

Duk Wand'an nan amsoshin, zaku samesu matuk'ar kuna turon da Zafafan comments dinku

More comments

More typing

Share nd post

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_ _TSARAWA_ _RUBUTAWA_ _HAK'K'IN MALLAKA_

```'Yar mutan Dikkawa```

BABI NA 20/21

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

______________________________________

```SANARWA... INA MANYAN MATA DA 'YAN MATA 'YAN K'WALISA NESA TA ZO KU SA, KO DA KUD'IN KU SAI DA RABON KU, DA ABIN KU KUYI DARIYA HAR DA SHEWA. INA MASU SON HAD'A KAYAN

LEFE

SUNA

DA KAYAN SALLAH

@5 STAR'S FASHION TRENDS SUN ZO MUKU DA KAYA NA BAN MAMAKI, SABODA SU NA HAD'A KAYA GANGARIYA NA ƘASASHEN WAJE HAR MA DA NIGERIA.

AKWAI DISCOUNT MAI KYAU GA MASU SAYEN ƊAYA KO SARI, KO KUMA WAƊANDA ZA'A HAƊAWA KAYA NA ALFARMA.

AKWAI;

LACES

MATERIALS

ATAMFA

SHADDA

ABAYAS

JALLABIYA NA MAZA

TAKALMA,JIKKA DA GYALE, SARƘA,ƳAN KUNNE,AGOGO NA ƘASASHE DABAM_DABAM

BUGU DA KARI AKWAI

BEDSHEETS

FRAMES KAMAR ;ARABIC, ENGLISH,FLOWER, AWARD, HOTELS FRAMES

TURARUKAN GARWASHI HUMRA, KALACCA, ARABIAN PERFUMES ƳAN MAIDUGURI

MUNA DA KAYAN ƘASASHE KAMAR NA ;

UK

INDIA

CHINA

MALESIA

DUBAI

TURKEY

MUNA TURA KAYAN MU KO'INA DAGA SASSAN K'ASAR NAN TA NIGERIA HAR MA DA ƘASASHEN ƘETARE.

KAYAN MU MASU KYAU NEH

ORIGINAL NEH

MASU LASTING NEH

SANNAN QUALITATIVE NEH

FARASHIN MU DABAM YA KE DA NA SAURAN MUNYI RAHUSA DOMIN MURMUSHIN COSTUMERS NA MU

SAYEN DAYA KO SARI

MUNA MARABA

https://chat.whatsapp.com/IEUdOSV8nGTECNWaJnB2dy

```

*************** Hancin motar Hajiya Babba ne, ya kunno kai gidan,direba na tsayawa ya fito da sauri ya buɗe mata,fuska ba walwala ta fita daga motan zuwa cikin gidan.

Zillaziya sai cika ta ke tana batsewa, domin ta ga alamun UWAR 'YAN MAATA na shirin yi mata sakkiyar da ba ruwa,amma idan ta san wata ai bata san wata ba don ta hanyar bata wuya zata bar gidan ko tana so ko bata so." Ta tagar falon Mima ta hango Hajiya Babba da yake sun ɗauke labulen,kallonta take cike da mamakin ƴar duniyar tsohuwa, sanye ta ke da rantsattsar Abaya ruwan madara,mai aiki jinin kare,da duwatsu farare,ta yafa mayafinta da farin gilashi manne a fuskarta, iPhone 11 da jikka ne rike a hannunta tana tafiya kamar sarauniya, jikin tagar falon ta baro da gudu, yay saura da ga Sareena sai Saudat da Mamu su na kallo."

K'wank'wasa k'ofar falon Hajiya Babba ke yi, sai faman hura hanci ta ke. daman yaran sun san ita ce dan mima ta fad'a musu, shiyasa su ka k'i bud'ewa sai da Hajiya ta matsa da buga k'ofar da zafin nama, sannan Mamu ta isa gurin ƙofar tana tub'ure baki domin sun tsani masifar tsohuwar."

Bud'ewa tayi sannan ta juya zata wuce abinta ba tare da ta dubi Hajiya ba,ita kuma Hajiya Babba daman ta fusata!Da tak'aici ta janyo Mamu tare da had'e mata hannuwa ta murtsuke su kamar tana k'wantan su,Wash...!Mamu ta ce" tare da ya ɓata fuska, tana hararan Hajiya cike da tsiwa."

Hajiya Ta ce"Yau na ga 'yar karen munafukar Allah, mai kama da naman suna...yanzu ke takwara ni zan shigo ki wuce baki gaida ni ba?ko uban ki D'an Inna da uwar ki Sadiya su ka ganni sai sun gaida ni bare ke,kaaai tir...da halinki baki d'auko halina ba,ni da na san haka ki ke da tsaurin ido da rashin kunya da ban yarda an mini takwara da ke ba yarinya sai tsiwa da rashin kunya,dangwarar Mamu, Hajiya tayi Ta ce 'yar buhun kankana da goron tula maza, je ki kira min ubanki duk inda yake a cikin gidan nan."

Mamu murza hannunta tayi da Hajiya ta sake wanda ya yi jajur, saboda zafi!idonta yay ja!Amma taurin ranta ya hanata kuka!tafiyan ta tayi ta koma saman kujera ta ƙwanta tana gunguni,cike da isa Hajiya ta iso tsakiyar falon ta zauna, su saudat a ladabce su ka dinga gaisheta ƙin amsawa tayi sai ma kallon banza da ta ke musu cike da tsana!Ta ce" Amma yaran nan kunji ciwo yanzu duk kuna nan zaune nayi ta buga k'ofa saboda tsabar baƙin ciki kun ka ki buɗe min?ni da gidan ɗa na kuna so ku min katanga wato ku mamaye komai shawarakayye!masu ido kamar na mujiya."

Ta dubi Mamu Ta ce" takwara bazaki ba ko?Mamu Ta ce"Hajiya to me nayi miki da za ki k'wanceni?mu fa muna jin dadin mu kika zo ga shi kina mana masifa! haka kawai,me nayi miki? kuma Daddy ban san inda yake ba kije ki nemo shi,haka kawai baki son mu, ba ki son mommyn mu to Wallahi mu bama sonki eheeeee!daga nan Mamu ta shige sashen su tana murgud'a baki har da karkad'a duwawu....Hajiya sake baki tayi Ta ce"lallai nan da shekara goma akwai hatsari gidan nan, duk wanda ya ga budurcinki Maryam sai ya ga rashin kunya, tun kina hakan kin iya rashin mutunci da tsiwa bare kin zama budurwa taf ɗi jaaam.

Saudat da Sareena kallon Hajiya sukeyi su na k'unshe dariya, harara ta watsa musu Ta ce"Shegunan goraa...dani ku ke zance bari na fara duba Zillaziya yarinyar kirki ba irin muguwar uwar ku ba."

************* Umma da Hajiya Arziki ne zaune a k'ayataccen falon ta, su na hirar duniya dan yanzu Hajiya Arziki ta rage saka tunani a ranta,don ta ƙara miƙawa Allah kukan ta akan ya karkato mata,diyanta maza gareta. Shiyasa hawan jininta ya sauka kuma tana samun kulawa da ban baki a gurin Umma."

Su na cikin firar ne sai ga Hajiya Hassana da Husaina, nan fa falon ya ƙara kacamewa da hirar bayan rabuwa, kasancewar ƙawayen su ne tun ƙurciya."Hajiya Hassana da Husaina tagwaye ne, sai dai halin su dabam domin tun asali Hassana ce da rawar kai da ƙwad'ayi Husaina kuwa ba ruwanta."

To ko yanzun hakane domin Husaina tana da yara maza uku duk sunyi aure, Hassana ko tana da mata biyu su ma suna auren maza masu kuɗi ƙwarai, da taimakonta har 'ya'yanta su ka mallake mazan nasu, garin Abuja da kwatakwat ta ke zuwa inda suke wurin musu hutu.A taƙaice dai Hajja Hassana da yaranta su na cin duniyar su da tsinke, sai abinda ta ce, sai kuma idan bata buk'atar abu, komai ya wadace ta, shiyasa ta ke alfahari da Kasancewar ta UWAR 'YAN MAATA."

A kullum tana tursasawa Husaina wannan aƙida irin ta ta akan itama ta tare gidan 'ya'yanta maza amma fafur ƴar uwarta tak'i ta amincewa a cewarta 'ya'yanta maza basu rageta da komai ba, hakan matansu na mutunta ta, bazata shiga sabgar su ba."

Dalilin hakan ya sa tagwayen basa wani jituwa sosai. Domin kowa da rayuwar sa haka kowa da halinsa Hassana son abin duniya ita kuma Husaina haƙuri da kawar da kai, yanzun ma daga gidan sunan 'yar uwarsu su ka fito a cikin unguwar shiyasa su ka biyo ta gidan Hajiya Zainab."

Fira sukeyi sosai har su ka gangaro gefen 'ya'ya nan aka sosawa Hassana inda takeso, ai ko ta hau basu labarin sakaci irin na Husaina wai matan diyanta duk sun mallake mata yara gashi tana son zuwa ta k'watowa Hussai 'yancin agidan yaranta, amma ta hanata dan ta ga ita yaranta maza ne, Ai ita bata hana ta nuna iko akan diyanta mata ba Momy da Ummita."

Ta ce" Duk da hakan kuma Alhamdulillah,domin ita kam mazan diyanta, ita ce ke mulkarsu yadda dace sai abin da tace kuma komai ta ke so ta samu.''Husaina girgiza kanta tayi cikin rashin jin daɗin zantukan ƴar uwarta,Ta ce" Ba haka bane Hassana ya kamata ki fahimce ni."

Umma Ta ce" Hussaina ki bar ja'ira kin san me hali baya bari,Allah ya shiryaki Hassana."

Amin ai ku kuma baku san kai ya waye ba,a kullum kuna cikin duhun rashin wayewar zamani Ta ce" tana dariya ."

Umma ma dariya tayi,to munji wayayyiya Hassana...kinga nima dai sai hamdalla ta gefena don matar Habibu bata da matsala nan ta basu labarin Juwairiyya suruka ɗaya tamkar goma,amma Hassana cewa tayi gaskiya Haj.zainab da ni ce ke da tuni na tare gidan, sannan in sa ai mata kishiya amma ina dad'i a gida ba magaji? Kisa ya ƙara aure ki samu jika ɗan saurayi don na gane surukar ta ki UWAR 'YAN MAATA ce."

Jimmmm Umma tayi tana nazari kana tayi murmushi Ta ce" A gaskiya surukata tana da kirki,ina matuƙar ƙaunarta,kuma bata da makosa sannan da ki ke batun magaji ai Allah ne mai basuwa ban damu da wannan ba don mutunci yafi komai."

Tab'e Baki tayi ta dubi Hajiya Arziki ta ce"Ke kuma meye damuwar ki?ana firar duniya,kin nutse duniyar tunani?

Hussaina Ta ce"ko dai jikin ne har yanzu Arziki?

Umma Ta ce" Kai jiki Alhamdulillah ai taji sauƙi sosai,abubuwan rayuwa ne kowa da kalar nashi jarrabawa."

Hassana Ta ce"Hmnnnn wallahi matsalar Arziki ita ce ta so, ni fa har cewa nayi ta zo in kaita inda mai kankat ta mallake diyanta su dawo gareta amma taƙi aiko ga hawan jini nan yay maki dirar maƙiya,da tun yaushe an shafe babin waɗancan ƴan iskan surukan nata ɓarayi."ita haihuwa ɗiyar wani da wata da more arzikin ƴaƴan...

Hajiya Arziki ta sauke numfashi ta ce"Ai ba komai Hassana watarana sai labari, nidai na riga da na barwa Allah komai, na san watarana su idirisu zasu dawo gareni domin Rana dubu ta b'arawo ce,Rana ɗaya Kuma ta mai kaya tunda aƙwai Allah babu wahala."

Tabbas Hajjaju Inji Hussaina da sigar tausayi daga nan abinci su ka ci su ka sha kana suka bar gidan.Duk da Hassana ba hakan ta so ba,taso ta zuga ƙawayen nata, don su bi hanyar da tabi wacce ta ke ganin mai ɓullewa ce."

*************Cikin d'akin ta sameta ta had'e kai da gwuiwa tana narkar tak'aici cikin ranta,kosallamar Hajiya bata amsa ba,da gudu ta rungumeta tana hawaye. Hajiya Babba ta janye jikinta daga na Zillaziya tare da dubanta ranta ba dad'i!ta ce lafiya?To meye abin b'acin rai anan?Ai tunda kin sanarda ni magana ta ƙare,yanzu tun jiya baki huta ba,ƴar nan kina nan kina mulkar ɓacin rai ke kaɗai kamar mayya."

ƙ'ara narke murya Zillaziya tayi cike da makarci kamar yadda Karima ta koya mata, ta dinga zazzagawa Hajiya ƙarya har da ƙarairayi tana kuka, akan abinda Halima da Alhajinta su kai Mata agidan daga tarewarta gidan kawowa yau."

Haushi ya ƙara cika Hajiya Babba ta ce''Lallai ma Halima ta zamewa D'an Inna k'arfen k'afa ni kuma tana neman zame min ciwon ido ke kuma tana shirin zame maki ƙadangaren bakin tulu... tabbas zan d'auki mataki a kanta,duk da na daɗe da ɗauka yana ƙwancewa,duk inda na kai sunan da na shi dan asaka masu tsanar juna,ƙwana biyu kamar aiki ya yi sai ta lalata shi da addu'a,tana da tsarin da asiri baya taɓa tasiri akanta nayi har na gaji,wallahi na tsaneta kamar yadda na tsani mutuwata,bani da burin da ya in ga ta wulaƙanta, abin haushi ba halin in ce ya saketa ina zan kai waɗannan tawagar 'Yan Mata...ko ke zaki iya zama da su?

A ah Hajiya nikam ɗiyar kowa ba zan riƙa ba,sai dai ke ki riƙe kayanku meye haɗin kifi da kaska,waɗanga 'ya'ya na ta kamar larabawa azo a ɗauka ni ce 'yar aikinsu,a kasa bambance matar gida ni da su,abarta da abinta nidai ki d'auki mataki ta gane nice matar so mowa a gidan nan,nafi so ta gasu har ta fara kuka da kanta,a ƙuntata mata taji gwara lahira da gidan nan, kuma fa karki nuna ni na fad'a miki."

Ki ƙwantar da hankalinki Zillaziya, duk kin ruɗe kinsan damuwa a ranki,ki cire wannan tsoron nata ki kwantar da hankalin ki...Muje

Nan su ka fito falo sun sami Hajiya Halima zaune da yaran suna kallo da fara'a Ta ce"a Hajiya barka da zuwa cikin girmamawa,harara Hajiya ta watsa mata tare da zama saman kujera Ta ce" Zillaziya kira min shi,a ɗan tsorace ta dubi Halima kana ta maida kallonta ga Hajiya,Aunty Halima Alhaji yana nan kuwa?wani kallo tayi mata da mamaki ta ce"kije ki duba bansani ba,Hajiya ta ce"Eyye zuwa kiran nasa sai an baki dama?To maza ki kira shi,Ta ce to Mommyna tana karyar kugu tare da hararan Hajiya Halima ta gefen Ido,ta wuce zuwa sashen Alhaji Bello."

Fitowa sukayi a tare sai wani yanga Zillaziya keyi, Hajiya Halima dariya abin yaso ya bata dan tayi wani iri, da ta jero da shi, kamar kuyanga(Anya ba kishi bane Halima?)

Zama yay tare da gaida Hajiya wani kallo tayi masa sannan Ta ce"Lafiya law,Anya ɗan inna kana tsoron Allah?Amanar yarinyar nan dana damƙa maka an bari ka riƙeta?To buɗe kunnenka ka saurare ni daman abinda ya kawoni gidan nan shi ne, Domin in taraku da kai da UWAR 'YAN MAATA har marasa ta ido gasu nan 'yan hancin kad'an uwa!in ja muku kunne akan ƴah tah Zillaziya."

Bari in fara ta kan ka D'an Inna ka ga yarinyar nan Amana ce mahaifiyar ta tabani ni kuma na damƙa ma,wallahi ko da wasa kaci amanarta ko ka tauye mata haƙƙi, ko ka d'auki aci zarafinta a gidan nan to ban yafe maka ba."

Da sauri ya dubeta...cike da mamaki!zaiyi magana Ta ce dakata!

Sai ke mai abin haihuwar mata...Wallahi ko da wasa ke ko diyanki kun ka kuskura kuka ci zarafin diyata Zillaziya to ki rubuta ki ajiye ƙarshen zamanki gidan nan yazo da ke har su."

Ku kuma 'yan tattasai da attarugun tsiwa daga yau ba raini sai girmamawa a tsakanin ku da ita gata nan da Mommy zaku kirata dan matar uban ku ce....

"A ah Hajiya kodai Anty sukace ba laifi karsu tsufar dani Inji zɗZillaziya tana murmushi."

Hajiya Babba Ta ce" To Auntu takeso daga yau da hakan zaku dinga kiranta,Ba raini ba tsiwa da rashin kunya,musamman ke Zeenatu da Balkisu da Khalewsat kun ga ku ne manya ko?to kar Inji kar kuma in gani."

Kema Zillaziya ke d'auki girmanki karki saurarawa kowa a gidan nan,duk wanda yay maki ba dai-dai ba,ki rama ke har mataki na baki izinin ɗauka."

Sannan daga yau kowa ya dafa abincin shi dabam saboda bazaki iya dafa abincin da zai ƙosar da waɗanga tumaki ba"

Wani iri Hajiya Halima taji a ranta amma ta daure,su Zeenat kam a fusace su kabar falon su na zubda hawaye irin yadda kakarsu ke musu basa jin daɗi,sun ƙosa hutu ya ƙare su kuma makaranta ko zasu huta."

Alhaji Bello rai ba dad'i ya tashi shi ma yace"zai wuce mita Hajiya Babba ta dinga yi masa har ya wuce abinsa,daga nan su ka dinga arashi da zagin Hajiya Halima a fakaice shiyasa ita ma ta bar musu falon fira suke har da tafawa Hajiya da Zillaziya (Hmnnnn muje zuwa dai...)

Yunin Ranar a gidan Hajiya Babba tayi shi, amma Zillaziya indomie ta dafa mata da ƙwai sukaci duk da Hajiya Babba bataji ɗaɗin indomin ba ko kaɗan,shiyasa ta ƙasa ƙarashe cin ta, Salma ce ta shigo da kula cike da ƙayataccen girki mai dad'i ta basu inji momynsu."

Amsa Hajiya tayi nan su ka hau ci har da santi ita da Zillaziya ba kunya bare tsoron Allah."

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍

Comments ɗin ku zai bani damar ƙarashe littafin nan.

Post

Comments

Masu buƙatar tallah munayi.... [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

©️ *NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_®️HAK'K'IN MALLAKA_

_'YAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 24/25

```Wannan Shafin kacokam na mallakawa Anty Billy Galadanci , Uwar tafiya mai gayya, Allah ya barmu tare acikin Aminci Amin. ``` _BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

___________________________________

Da ƙyar likitoci su ka shawo kan matsalar Ammi,sai da akai allurori da sauran abubuwa, sannan aka mayar da ita d'akin jinya na musamman mai zaman kansa."

Abbu ya samu k'wanciyar hankali sosai ganin anyi nasara, Umma da yaran ma hankalin su ya ƙwanta, domin likita ya basu tabbacin babu wata damuwa, da zarar alluran su saketa zata iya farkawa nan da awa biyu zuwa uku."Godiya Abbu yayi ma likita, sannan ya koma a inda su ke zaune, su na zaman jiran farkawar uwargida rangida."

Umma ta dubeshi da tausayi tace"Ya kamata ka d'auki yaran nan hakan,kuje gida ku huta ni zan zauna tare da ita,sai ku ci abinci nima na kira mai aiki yanzu zata kawo mana ruwan shayi da abincin da nace ta dafawa Juwairiyya, kayan cikin rago ya yi ruwa kaga zata iya ci bayan ta sha shayin,ni ko in ci tuwo."

Numfashi ya sauke tare da dubin Umma,ya kuma kalli yaran duk sun canja,kamar basu ba. Ya ce to ku tashi muje daga nan sai na watsa ruwa nayi sallah, amma Umma zan dawo zuwa bayan Isha."

Ta ce" To ai ba damuwa ke Nabila sai kuje ku samu abinda zaku girka kuci, kuyi sallah daga nan kuyiwa maman ku Addu'a,duk ku ƙwantar da hankalin ku da yardar Allah zata samu lafiya."

Ajiyar zuciya Nabila tayi,tare da dubin Aysha da Yaseera gwanin tausayi idonta,ya kawo ƙwallah!ta goge tare da cewa to Umma.

Abbu yay gaba su na biye da shi jikinsu a sanyaye domin da son samu ne ba zasu tafi gida ba,amma tunda Umma da Abbu sunyi magana zance ya kare."

Suna fita likita na isowa gurin umma yace"Mama barka da hutawa,Tace barka dai likita."Ya ce Alhaji nake tambaya?

Umma Ta ce"ka ga yanzun nan ya je ya mayarda yaran nan gida,wani abu ne ?

Murmushi yay tare da sosa kai yace A'ah Mama,ba damuwa idan ya dawo ina son ganinsa.

Umma Tace to shi kenan likita zan faɗa masa,mun gode.

Injin dai surukata ba wata matsala gagaruma ta samu ba...Inji Umma ta goge ƙwallah da hijib dinta.

Da mamaki ya dubeta yana ware ido,ya ce" Mama daman ba kece kika haifeta ba?

Ni tamkar mahaifiyar ta ce likita, domin surukata ce,matar d'ana d'aya tilo,kuma uwar jikokina 'yan matan nan da kagani kyawawa guda biyar,ina sonta ina ƙaunarta bana son inji kace ga abinda ya sameta..."

Yanzu kam dariya Umma ta ba likita jin har tana yabe jikokinta,ya ce" gaskiya Mama samun irin ki sai an tona dan yadda mu ka ga hankalin Alhaji da ke ya tashi,mun ɗauka kece Mamanta.Allah ya saka maki da alheri, ku ƙwantar da hankalin ku daman ta samu sarƙewar numfashi ne,har tayi dogon suma kuma yanzu mun gano bakin zaren zata warke a hankali, matuk'ar bata sab'awa ka'idar da zamu ɗaurata akai ba. Daga nan ya wuce Umma na masa godiya. A daidai lokacin kuma sai ga Hajiya Arziki da mai aikin Umma tafe nan su ka zauna, Umma na masu bayani amma ta tabbayar masu jikin da sauki."

**************** Hello... Zillaziya Tace muryarta a dak'ile,a d'ayan b'angaren muryar Karima ta karad'e mata dodon kunne tana cewa Alo kina jina?

Eh momma ina jin ki,An wuni lafiya?

Lafiya law, ya kike ya zaman bakunci? ko da yake an zama masu gida.

Lafiya law momma, na kiraki yanzun nan shi ne marar mutuncin yarinyar nan k'waila ta d'auka dan tsabar raini harda datse kirana!Wallahi Momma ki shiga tsakanina da 'yarki idan ba haka ba, zanyi maganinta da rashin mutuncinta har ta isa ta kirani da jaka...cinyar kaza ta tazga bakinta cike da naman ta ci gaba da magana,yanzu kamar ni ace ƙannaina basu daraja ni?

Kiyi hak'uri zan mata fad'a Allah ya huci zuciyarki.inji Karima da sigar rarrashi.

Zillaziya ta koma zabgar nama,Ta ce "Uhumnnnn Ameen Momma, sannan ta kurbi lemo.

Karima Ta ce" Ɗiyar nan me kike ta ci hakan?naji bakinki tunbatse,ko biredi ne mutumenki?

Wata dariya Zillaziya tayi har sai da Karima ta janye wayar a kunnenta,Ta ce" Haba Momma kamar ni matar Alhaji, zan zauna ina cin biredi? Hmnnnn ai sanin da ne da kika min a gidan Buzu mai shayi,Wallahi kin ganni nan Momma cinyoyin kaji ne nake yiwa dirar makiya ba dare ba rana,a yuni sai inci kaza biyu ko uku ni kaɗai..."

Ke....Zillaya kodai duka gidan?Karima ta ce da karfi!

Momma kenan sai kingansu kuma dak'wa-dak'wa irin na turawan nan masu mai...ni ko ga cin su to yana da gonar kaji nomawa kawai ake agyare asa mana a firjin,su fa matsiyata bata damesu ba,wataran in ci ta sashena in dawo nasu idan na gani in ƙwashe,gani nan har nayi ƙiba na fara tada komaɗa yunwa tayi hannun riga dani,bari kawai wani shagali sai duniyar auren mai hannu da shuni, kamar tana gaban Zillaziya tayi zuru tana saurare sai lashe bakinta tayi,tare da had'iye miyauta k'uuut...

Wata dariya Zillaziya tayi Ta ce"Allah sarki Momma me kikeci na baka na zuba?ki daina had'iye yawo kema zakici kaji wallahi tunda Allah yay miki gyad'ar dogo na auri mai hannu da shuni. Momma zakici kaji ki kuskure baki da lemon fanta mutuniyarki....

Dariya tayi tare da sake had'iye yawu a karo na biyu,Ta ce" Dan Allah karki mance damu Zillaziya idan ta kama na aiko Tasi ne sai na turo shi ya amsa mana."

Karki damu ba zan manta da fad'i tashin da kikeyi har na shigo gidan nan ba, zaki fanshe wahalarki, daga nan ta labarta mata duk abubuwan da suka faru har yadda sukayi da Hajiya Babba."

Karima taji dad'in maganar ƙwarai, ita ma ta fad'awa Zillaziya ta amso magani a gurin mallam, tare da sanar mata komai daki-daki da duk sharud'd'an da ya gindaya da komai.Taji daɗi matuƙa,shiyasa ta ce" zata shigo da kanta ta amsa gobe da safe."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull