Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 7

Uwar y'an mata complete - Chapter 7

Uwar y'an mata complete Chapter 7: Uwar y'an mata complete Chapter 7. Amma karime ta ce ba zai yuyuba ta fito tun yanzun,Ita kuma Ta ce"Bata yarda a baiwa…

4,395 words

Amma karime ta ce ba zai yuyuba ta fito tun yanzun,Ita kuma Ta ce"Bata yarda a baiwa ƙannanta su kawo ba,kar suyi kuskuren mata bayani ko akasin hakan,A ƙarshe Karima cewa" Tayi "Goben zata shigo da kanta gidan,ta kawowa Zillaziya sak'on, da zarar tayi mata waya ta shaida mata surukin nata ya fita."

Da hakan su kayi sallama cike da jin , daɗi. Safara'u ta sha fad'a sosai,agurin Mommah duk akan abubuwan da take yiwa yayarta Zillaziya bata kyautawa, don ta sa ni yanzu ta canja zane ba irin da bane, yanzu sai da rarrashi domin Zillaziya ta zama babbar macce sai da dabaru kafin su samu suma su ci nasu ƙason arziki."

A cikin ran Safara'u taji haushin zantukan Mommah,amma daurewa tayi ta bata hak'uri,Ta ce ba zata ƙara ba.Ta tashi ta barta gurin sai mita take an taɓa ƴar gwal.ƙwallan bacin rai ya k'waranyo mata tana dubin yadda Mommansu ta k'ara a manna da duniya,son abin duniya da k'wad'ayi ya rufe mata ido bata ganin kowa sai Zillaziya,ajiyar zuciya ta sauke tare da musu fatan shiriya sannan ta ci gaba da aikin ninke tufafinta da ta wanke."

Da misalin k'arfe takwas da minti arba'in na dare, Abbu ya dawo asibitin d'auke da ledoji.Inda su Umma su ke zaune ya samesu tare da gaidasu,Hajiya Arziki da Umma amsawa sukayi a lokaci d'aya."

Bayan ya zauna na wani lokaci,Umma ta shaida masa likita na nemansa, tambaya yay har yanzu Juwairiyya bata farka ba? Umma Ta ce "Har yanzu dai muna jiran tsammani daga mu har likitoci muna yawan lek'awa amma shiru tana bacci."

Hajiya Arziki Tace" Ai in shaa Allahu zata tashi domin har ta k'ara awa ɗaya Allah dai ya tasheta Lafiya.

Ameen,Umma Ta ce tana jan carbin hannunta.

Yace"Hajiya ga su Ayaba nan an yanka kuma an wankesu ku sha,bari naje inda likita.

To sai ka fito inji Umma tana kokarin bud'e ledojin,Hajiya Arziki Ta ce "Bawan Allah rana ɗaya har ya zabge hakan...Daga ganin hakan ai kasan macce ta gari, ta dabam ce a rayuwar iyalanta."

Hakane domin gashi mun koma wasu iri yuni ɗaya Inji Umma.

Ofishin ya k'wank'wasa sau biyu daga can akace ya shigo,da sallama ya shiga tare da gaisawa da likitan.

Amsawa likita ya yi tare da bashi hannu sukayi musabuha,daga nan yayiwa Abbu bayanin matsalar Ammi wacce ciwon (Asma) ya yi mata mugun kamu na bazata,duk abubuwan da ya dace ta kiyaye likita yay masa bayani har ya gamsu,aƙarshe magungunna da sauran allurori ya rubuta ya ce"A nemo."

Godiya Abbu ya yi sannan ya fita inda ake sayarda magani ya sawo,ko da ya dawo ya samu su Umma na shan kankana zama ya yi tare masu bayanin da Likitan yay masa, ya ƙara da ƙwantar musu da hankali."

Umma Ta ce "Ba komai Allah ya yaye mata"Amin. ya ce"Yana dafe kai.Abinci ta zuba masa Ta ce"ungo kaci da zafin sa, murmushi ya yi yace"Umma ban iya cin abinci a asibiti idan na koma gida zanci su Nabeela na can suna girkin,amma zan sha Wad'annan ya d'auki tufa ya na ci.Nurse ta k'araso gurin su Ta ce"sannun ku Mama dan Allah waye Abbu...A zubure yace"ni ne tare da sake tufan saboda fad'uwar gaban da ya riskeshi,Ta ce muje da sauri! nan tayi gaba yana bin ta baya, Domin daga ɗakin da Ammi ta ke ta fito."

Umma da Hajiya Arziki cike da fargaba su ka dafa masu baya zuwa ɗakin da marar lafiyan ta ke.sai dai Abbu na shiga nurse ta rufe ƙofa!tare da basu haƙuri...."

Sanadin bugawar da zuciyata keyi yasa Kai na ya ɗaure komai ya tsaya min caaak!

Shin me ke faruwa?

'YAR MUTAN DIKKAWA CE😍

More comments more typing... [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR 'YAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

©️ *NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

~Home of Brilliant Writers forum~

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_®️HAK'K'IN MALLAKA_

_'YAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 26/27

_SANARWA...SANARWA... SANARWA...ASSALAMU ALAIKUM,YA KU ABOKAN KASUWANCI...MASU BUƘATAR TALLAH ƘOFA A BUƊE TA KE._

*INA MANYAN MAATA MAGANIN K'ANANAN MAATA?INA UWAR GIDA,AMARYA DA 'YAN MAATA?INA MATASA DA ƘANANA ƳAN ƘWALISA? KU SANI MACCE BATAYI SAI DA ƘWALLIYA DA ƘWALISA,MASU SON ADO DA ƘWALLIYA TARE DA ƘAYATA SUTURUNSU KU HANZARTA KU GARZAYO INDA;*

*HAJIA RALIYA KANGIWA*_(C.E.O OF RALIA KGW BEAT WORK)_

*DOMIN KAWO AYYUKAN KU,TANA BEAT WORK,NA LACES,ATAMFA,SHADDA, VOILE, MATERIALS DA SAURANSU, DUK AKAN FARASHI MAI SAUƘI.*

_MASU BUKATAR AIKIN BEAT WORK KO TRAINING ZAKU NEMETA TA WANNAN ADIRESHI_

*@KEBBI STATE*

OPPOSITE TO; ƊAKI TAƘWAS, GWAZANGE AREA ARGUNGU

070-32-99-02-39📲

_MASU BUK'ATAR KOYO, DA WANDA ZA'AYI MA AIKI MUNA MARABA._ ___________________________________ Alhaji na dawowa daga shago, sashen Uwargida ya fara nufa,tsarabar su ya bata wacce yake shigowa da ita kusan kullum,zama yay tare da faɗin "Ya Allah"Gaisawa sukayi tare da masa ya kasuwa ya ce "Alhamdulilkah"kana su kai masa fatan alheri kamar yadda su ka saba,fira suka taɓa sosai shi da ita har da yaran cikin fatinc ciki. Ya ce"Hajjaju abin ci...yanayin yadda ya yi maganar ya bata dariya sai da tayi mai isarta,sannan ta ce" Haba Alhaji! ka manta ba gurina ka ke ba?Ni fa ba zan lamunci ba ka abinci ta ɓarauniyar hanya ba,ga kayan daɗi da kaji can Amarsu mai kayan ƙamshi ta soya ma,ta shirya ma gangariyar girki ka zo nan wai sai na sammaka...Tsaki yay tare da dubin Zeenat ya ce"Ke jeki zubo min abin da ta dafa,tashi tayi bata jima ba, ta kawo mashi da ruwa har lemon tsamiya da sukayi,Mommy sai mita ta ke masa da tsiya,amma baice komai ba sai da ya ci ya ƙoshi, sannan ya tashi yana musu sai da safe."Yana fita Mamu ta tuntsure da dariya ta ce"Wallahi wannan Amaryar ta ga bone,bata iya abinci ba fa Yah Zeenat,hmnnnn Yah Khaleesat kin san me ko ɓeran daji ba zai ci ba,kun ga fa shiyasa Daddy baya son cin abincin ta..."

Maza rufe min bakinki!wa ya tambaye ki? kedai kullum sai kin kawo mana gulma Auntyn na ku,shiyasa ki ke lallaɓawa kina shiga inda ta ke ɗaukar rahoto kina zuba mata na mujiya ko...inji Hajiya Halima a ɗan zafafe."Mamu turo baki tayi ta ce"Ni fa Momy na ci naji wallahi kamar an dafa kashi...Ba zaki shiru ba kenan?To ki ci gaba,bana mugun ɗabi'un nan naki Mamu idan maganata bata tasiri akan ki nasan watarana jikinki zai faɗa maki...ta shi ki bamu guri bama son gulma,Allah baki haƙuri Mommy,Inji Mamu ta fita daga falon tana fushi."

Bayan ya kammala shirin sa na ƙwanciya,sai gata shigo ta sameshi cikin wasu watsattsun kaya,kallo ɗaya yay mata ya kawar da kai"Alhaji ga abincin ka can,ko yau ma ka ƙoshi a shagon?"Gaskiya ita kam bata kyautawa rayuwarta ba,da ta saba maka da cin abincin dare a waje!"Kallonta yay ya ce"wa kenan?kanta tsaye ta ce"Aƙwai wata ne bayan uwar ƴan mata...tsaki yay ya ce "In tambayeki?Kai ta rausaya tana kallonsa "Ina jin ka."Wai meyasa sallama ta ke maki wuya?Sannan ke ba'a koya miki yadda zaki gaida mijinki,ki masa sannu da zuwa idan ya dawo?Kawai da na dawo baki da aiki sai zuba kamar famfo.Ɓata fuska tayi ta ce"To kayi haƙuri Alhajina zan gyara amma wallahi ko a cikin horo an min wannan huɗuba."Allah yasa ki gyaran ya ce tare da gyara ƙwanciyarsa."Alhaji abin cin fa?"Ba zanci ba dan na ƙoshi."Zama tayi gefen gadon tana faɗin uhumnnn wasu mata da kam anga ɓuss sai asabawa miji da cin abinci waje!"Kinga Zillaziya bana son rashin kunya Ni da Halima duk ba sa'ar ki bane dole kisan girman mu...dariya tayi har da tafawa ta ce "Alhajina kenan daga faɗan gaskiya?to kai inji kunyar ka akan me?bare wata bare,ai da kai da kaya duk mallakar wuya ne,jemage fa daren mutuwar sa kaɗai ne bai gani ba,ai an zama ɗaya ni da kai, sannan idan har girma ku ke so ga ƴaƴanku nan zasu baku amna banda ni Alhaji haka kawai."dafe kansa yay aransa yana danasanin auren ƙaramar yarinya musamman marar tarbiyya da ilimi.rufe idon sa yay kamar yana bacci ita kuma sai zuba ta ke." ************* Yadda ya sameta zaune kan gadon,yasa faɗuwar gabansa ya ragu! Alhamdulillah ya furta a fili tare da ajiyar zuciya,inda ta ke ya nufa ya ce"Ammi sannu ko?kinji sauƙi...Murmushi tayi a yanayin ciwo ta ce"Na gode Allah Abbu,Likita da Nurse murmushi sukayi don gaskiya sun burgesu,Yanzu dai ba abinda kikeji?Eh babu komai Likita ta bashi amsa,Nurse ta ce"Daman tana farkawa da sunan Abbu a bakinta shiyasa nayi hanzari na kira ka,Allah ya ƙara bata lafiya."Ameen Abbu ya ce cike da murna,Nurse dan Allah ko su Umma zasu iya shigowa? na san hankalinsu na can atashe. Ta ce "A'ah ka ƙara haƙuri ka bamu ɗan lokaci, nan su ka ƙara mata aune-aune sai da su ka tabbar babu wata sauran matsala,sannan suka fita tare da ba su Umma umurnin shigo ɗakin."

Sunyi murna sosai ganin yadda jikin Ammi yay kyau,ita ma taji daɗin yadda su ke nuna mata kulawa,gashi har iyayenta basu faɗawa ba,a hakan aka sallameta suka tattara zuwa gida,sai dai Likita ya ce"Bayan sati biyu zata dawo a ƙara dubata."Har wasa ya dinga jan Umma ya na faɗin" Mama mai jikoki ƴan mata kyawawa sai na zo abani ɗaya..."Da raha su ka bar asibitin zuwa gida." ************

*WASHE GARI* Ta ƙosa lokacin fitan shi kasuwa yay, don tun da safe ta ke shan kira wurin Mommah Karima,shayi da biredi ta haɗa sai soyen ƙwai,a daddafe ya karya sashenta don ƙwan ba inda ya soyu,sai magi da yaji ga mai latsam yana tsiyaya ba yabo ba fallasa aci maganin yunwa shi yasa ma karin yau,yana gamawa ya ɗauki jikarsa,inda Halima ya shiga su ka gaisa ita ma ya sallameta sannan ya wuce."

Yana fita ko awa ɗaya ba'ayi ba, ɗan Acaɓa ya ajiye Karima,da yake sun jima laɓe awani kusurwa suna jiran fitowarsa daga gidan. Sabod ta ƙosa ta kuma ƙasa haƙurin jiran kiran Zillaziya.Don tun da safe ta fito daga gida."Katafaren gidan ta nufa tana zuwa ta hau buga ganbun,buɗewa yay tare da kallonta sama da ƙasa,kutsa kanta tayi da niyyar shiga, amma da zafin nama Habu mai gadi ya turota baya! ya ce"Haba baiwar Allah talauci hauka ne?zaki kutso kai cikin gida kamar mayya ai wannan salon mugunta ne,idan bara ki ka zo, ko maula sai ki jira har na baki izini,ke kin ganni nan...da ƙaton jahili daƙiƙi ne amma yanzu da naira ta shani mari nayi hankali har na fara karatun yaƙi da jahilci ta wayar nan tawa Vivo,kuma ni ma fa ɗan ƙauye ne kamar ke na goge na waye, amma kin zo kina abu kamar dabba!Idan ma Alhaji ki ke nema kin zo neman taomako baya nan ya fita,sannan yau matsiyaciyar Amaryar nan ke girki agidan nan nima ina neman karin safe balle na baki ragi sadaka, dan haka ki kama gabanki."Salati tayi tare da riƙe baki ta ce"Wato ƴar tawa ce matsiyaciya,kasan ko ni wacece da zaka min rashin arziki?"Ina ruwana da ko ke waye! a hakan koɗaɗɗiyar tsohuwa da ke zakice min wai ke wata ce,tsaki ya yi ya ci gaba da aikinsa."Kiran Zillaziya ne ya shigo wayar Karima don ta shaida mata ta zo Alhaji ya fita,sai dai jin muryar Karima tayi rai a ɓace ta shaida mata tana ƙofar gidan,mai gadi ya hanata rawar gaban hantsi wai ba zata shigo ba,a fusace ta kashe wayar ta nufi wajen gidan tana kiran shi...Da sauri ya isa yana gaishe ta, ta ce" kaje ka shigo da matar nan!"Da sauri yaje ya buɗe ma Karima ƙofa,shigowa tayi gidan tana zunduma masa zagin.Ya ce" Hajiya kiyiwa ƴar maulan nan magana fa kinji tana neman wuce gona iri,don ba dan ke ba yau in ta shigo gidan nan hege ni ke!Karima ta ce "Da ko ka tabbata marar uba!baƙauyen banza...kinji ko Zillaziya da kunnenki ina so ki nuna masa matsayi na agidan nan,ɓata fuska tayi ta ce"Kai Habu wannan Mahaifiyata ce karka ƙara mata hakan akanta zaka rasa aikin ka,ka bata haƙuri...Hannu Habu ya aza aka,da gudu ya faɗi gaban Zillaziya yana basu haƙuri daga nan su ka wuce,shi kuma yana tashi ya ce"Lallai ɗan talaka bai iya samu ba,ashe haka uwar taki ta ke kamar sandar kiwo, amma ki zo kina mana iko da kalkon banza." ya ƙosa sauran ma'aikatan gidan su zo ya labarta musu,har hoton Karima sai ya ɗauka musu idan ta fito don gani ya kori ji."

Hayaniyar da suka jiyo a waje yasa suka fito har Mommy a babban falon ta ce" Saudat ta duba me ke faruwa Habu da waye yake faɗa?don ta san halin sa sarai saboda su sanda Zillaziya ta fita basu cikin falon,Saudat na buɗe ƙofar su kuma suna kawowa tsaye tayi tana kallo mabaraciya yau a falon,Ke kauce marar kunya!janyewa tayi daga jikin ƙofar sannan ta rufe ta mara musu baya,har su ka kawo falon,ido su ka zuba mata wasu ku atsorace kar dai mayya ce, dan duk da Karima tayi shirin ƙwarai da zata zo amma bai hana ramarta bayyana ba,Sallama tayi da fara'ah Halima ta amsa don kuwa ta ganeta ƙawar Hajiya ce da suke zuwa jefi-jefi tare da ita,ganin Mommy ta amsa yasa suka gaidata don sun ƙasa ganeta duk ta ƙare kamar kuɗin gado,Hararen su Zillaziya tayi suka wuce zuwa sashenta,Zeenat ta ce" Mommy wacece?Saudat ta ce" yau kuma ƴan maula ta samu,Bilkisu ta ce"sai addu'a nake idonta manya gasu jajaye gashi ta cika baƙin ƙwalli sannan batada nama kamar Aljana..."Momy ta ce "Ya isa bana son yawan maganar nan naku fa,Maman Zillaziya idan taji kunga ba daɗi ku daina ba kyau bana so."Da mamaki su ka dubeta su na haɗa baki gurin faɗin "Mommy wannan yanzu ita ce Maman Anty Amarya lallai ma...Mamu ta ƙwashe da dariya ta ce" abu kamar kalangu wallahi duk ranar da ƙara kiran Mommy da Uwar ƴan mata sai nace tafi mai kama da naman suna..."Raƙwashi tayi mata aka ta ce Oh!ni Halima bakin ki ko Mamu zaki gane,sosawa tayi da tsiwa ta ce"Mommy ƴanci muke son ƙwato miki fa!Ni daga ita har uwarta ina iya zaune su tana faɗin hakan ta gudu daga falon,Allah ya shirya Momy ta ce tare da ci gaba da kallonta."

Tana shiga falon ta dinga dube-dube cikin jin daɗi ta ce"Dare ɗaya Allah kanyi Bature, yanzu ke ce a wannan daula Zillaziya? Allah na gode ma,murmushi tayi tana kallonta ta koma mata ƴar ƙauye,Ta ce "Ki zauna mana daga nan ta nufi firijin,lemon fanta da ruwan gora da kayan lambu ta jibgo a ture ta ajiye gaban Karima, sannan ta nufi madafa kajin da ta soye jiya ta shaƙo filet da su,ta ce bari in dafa miki indomi,A'ah barni da waɗanga sun isa ranki ya daɗe,tana janyo kayan gabanta,Hijab ta cire tare da banye ɗaurin zaninta ta lanƙwashe saman turan naman kaji,da fanta,Zillaziya sai labari ta ke bata, yayin da uwar hanzanyarta ya fara karɓan saƙo,sosai ta ci kamar bazata ƙoshi ba, sannan ta ce" bari ki gani,kasusuwa da sauran naman ta juye cikin ledar da ta ɗauko cikin jikarta,tatas ta ƙwashe komi ta tura cikin jikar. bayan ta fito da magani,bayanin komai tayiwa Zillaziya,sannan ta bararraje tana kallo tana dariya har da lalewa sai wajajen la'asar ta bar gidan ba don taso ba saboda ko sanyin gidan kaɗai wata duniya ce."

Abubuwa da dama Zillaziya ta haɗa mata su naman kaji dana rago danye,lemon ƙwalba ,ruwan gora madara, sabulai,har kuɗi da sauran su." Karima taso Zillaziya ta zabgo musu shinkafar ɗangote sai dai Zillaziya ta hanata a cewarta za'a gane ta ɗiba,idan har abinci yay sauri ƙarewa bata son Alhaji ya fara fahimtar hakan,amma sai zuwa gaba buhu zata dinga saya musu,da hakan su ka fito Karima ɗauke da Ƙumshe-ƙumshe cikin Hijab,bakinta duk mai sai gyatsa ta ke."Sun so su fita daga gidan ba tare da ta Halima gansu ba,amma har sun kai ƙofa sai gata ta fito da ƙatuwar leda taba Karima da kuɗi,a kunyace ta amsa tana godiya tare da fatan alheri,Zillaziya ma godiya tayi ma Hajiya Halima duk da bata kai har ciki ba,har get ta rakata a lokacin me gadi yana bayi hakan bai mai daɗi ba,don yaso ya bata pics."

******** Wani sabon babin rashin mutunci Zillaziya ta bud'e a gidan,duk yadda zatayi ta bak'antawa Hajiya Halima da Yaranta Rai shi takeyi,Amma biris yaran sukayi da ita,bare Mommyn su da banza yafi fiye mata dad'in kallon a madadin Zillaziya. Wanda hakan baiyi mata Dad'i ba,Shiyasa ta k'ira Mommanta a waya ta labarta mata komai sai su ka canja sabon salon tafiyar ta su.

A gefen Hajiya Halima ko tafi nono fari,tuni ta k'ara jawa yaranta kunne,akan suyi taka tsam-tsan da Auntynsu domin sun fahimci inda ta dosa, Bata buri irin ta ga ta muzguna musu, Dan kawai tana takama da Hajiya Babba a matsayin garkuwarta.

Alhaji Bello a yanzu bayada matsala kamar zillaziya da halayenta amma babban ciwon kansa Hajiya Babba Dan bata tab'a bari a takawa zillaziya burki a gidan,Shiyasa ta ke yadda take so karanta takeci ba babbaka Dan Hajiya ta tsaya mata, har shi kansa tana neman ta raina shi.

Ta kowanne b'angare zaman hak'uri ake da zillaziya Domin ta zamo ciwon ido a gurin Hajiya Halima,k'arfen k'afan Alhaji Bello, k'adangaren bakin tulu wa yaran gidan, Haka dai rayuwa ta Cigaba da tafiya a gidan kowa yana sabgar gabansa.

Ammi jiki ya yi kyau Ma Sha Allah, ayyukan gidan sun dawo hannunta,kamar yadda ta saba kula da gidan da me gidan da kuma yaran gidan,Abbu ma Hankalin ya K'ara kwantawa, su Nabila sun koma makaranta, Domin ci gaba da karatunsu, Kasancewar hutu ya k'are.

Umma ma Hankalin ta ya kwanta, domin tana tabbacin Juwairiyya ta samu lafiya, kuma zata kula da shan magani akan lokaci sannan zata kiyaye duk wasu sharud'd'an da likita ya gindiya mata, domin ance lafiya uwar jiki.

Ta kasance ranar Assabar,Rana ce ta hutun mako,ga yara da kuma ma'aikata amma banda 'Yan kasuwa irin su Alhaji Bello.

Ya shirya tsaf a cikin farin boyel me manyan zane,dinkin manyan kayana ne da babbar Riga,hula yasa ita ma fara tas da agogo ruwan azurfa,ya yi kyau matuk'a yana gaba Hajiya Halima na binsa abaya rataye da jikkarsa ta fita shago,ita ma ba laifi sanye take da bubu ta wani leshi ruwan kwai,Mai laushi Yana da zanen manyan fulawa bak'i da ratsin kore,leshin irin marar nauyine me kwantawa a jiki,tayi kyau matuk'a sai k'amshi turaren "kill us'' ke tashi.

Har Babban falon ta rakashi dap da ya fita, ya dawo tare da duba agogon da ke d'aure a tsintsiyar hannunsa,ya duba lokaci k'arfe goma da rabi na safe,dafe gefen Kan sa yay,yace"Oh!na manta bari naga zillaziya."

Murmushi tayi tare da rausaya kanta tace"okay"bara na zauna na jiraka ta zauna Kan kujera tare da rungume jikarsa tana Danna wayarta.

Sashen ta ya nufa Yana sauri tura kofar yay a rufe alamun Bata tashi ba,Shiyasa ya buga kusan har sau uku sannan aka bud'e,Hamma tayi tare da murza ido,tana turo bakinta alamun bataji dafin tashin ta da akayi ba.

Kallonta yay yace"Ni zan fita da fatan kinyi sallah?"

Mik'a tayi Tace"Wallahi Bacci ya kwasheni Alhajina"Ina kwana?

Kenan bakiyi sallah ba?ya jefeta da tambaya tare da kafeta da ido.

Kasancewar bata tsoron ta kwana,Shiyasa tace"Eh banyi ba,Amma yanzun zanyi."

Wani warin bakinta da hamamin warin hamutta ya doki hancinsa, da sauri ya kauce tare da ja baya yana d'an toshe hanci, yace"Dan Allah kije kiyi wanka ki wanke Baki kiyi sallah.

B'ata Rai tayi!Tace "me kake nufi Alhajina yanzu Kuma sharrin da aka turo min kenan warina kakeji to Allah ya raba mugu da nagari.nidai anjuma zan tafi gidan mommah kamar yadda na tambayeka jiya, sannan ina buk'atar kud'i,Dan zan sayi kaya in kai mata kasan bazani hannu a sake ba,sai kayan shafawana sun kare kuma Ina so....

Dakata ya isa hakan yace,tare da d'aubo kud'i a aljihun sa ya bata,Ki gaishe su.

Amsa tayi Tace to zasuji sai ka dawo ta wuce bayi.shi kuma inda uwar gida ya koma ya amshi jika ya wuce bayan Addu'oin fatan alheri da tayi masa.

A mota sai mamakin zillaziya yake dudu auren da bai wuce wata daya ba ace har kusan akwati biyu na mayukan shafawanta sun kare?gashi in me ya bata hannu kawai zata sa ta amshe ba gode bare nagode. sabanin Halima da komai kankantar kyauta zata dinga k'waranyo masa Godiya. ga shi da wuya ta rokeshi wani abu amma ita wannan Amaryar kullum a bata kamar marokiya.

Hajiya Babba ta shirya tsaf cikin shigar Abaya ja me ratsin ruwan zinare, takalmi da jikka tasa wanda ya dace da shigarta,madubinta fari tas ta manna sannan ta fito me aikinta na take mata baya,har suka kawo jikin mota inda direba ke zaman jiran fitowarta.

Bud'e mata baya direba yay, ta shiga sai tak'ama take, tana hurar hanci. Mai aikinta adawo lafiya tayi mata,Amsawa tayi Cikin isa da gadara sannan Tace"ki kula da gida duk Wanda ya zo ya jirani yanzun zan dawo,To Hajjaju mai aikin tace ta wuce,Ita kuma sai faman danna iPhone dinta ta ke wanda ba abinda ta sani daga (games) sai kuma in an kirata ta d'auka.

Direba ta da injin motar yay (Range rubber) su ka fita daga gidan a lokacin da Mai gadi ya wangale musu k'ofa,Sai da suka kama hanya sannan Hajiya Babba Tace Unguwar fage zamuje .

To Hajiya Babba. Yace dokin ko bata fad'a yasan inda suka nufa.

_MUJE ZUWA FANS_

POST

SHARE &

COMMENTS [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 30/31

*MASU BUƘATAR ƘAYATATTUN DOCUMENT ƊIN PAID BOOKS ƊINA ZAFAFA MASU ƊINBIM AL'AJABI ZASU IYA FARA PAYMENT* 👇🏿 SANIN GAIBU...200

DUK ABINDA KA SHUKA...200

BASU SAN WAYE NI BA 200

Masu buƙata zasu iya biyan 500 domin samun littafan duka zaku iya tuntuɓar wannan lamba don samun bayani kan yadda zakuyi payment 07068048901

***************** Tun ranar da Zillaziya ta baro gidansu ta dawo burika a ranta,shiyasa ta ɗauki ɗamarar maganin Hajiya Babba da Hajiya Halima a cewarta"Wanda ke kan dutsi baya tsoro ko fargabar wasan jifa."Don haka ba gudu ba ja da baya har sai ta abinda ya turewa buzu naɗi."Ita ɗin ba kanwar lasa bace gada tayi ba shige ba."

Iko da rashin mutunci tuli-tuli ta ke a gidan amma ba mai tanka mata,duk Hajiya Halima ta sha Alwashin duk ranar da Zillaziya tayi kiringin shiga gonarta to zata koyar da ita yadda ake wasan kafce."

Su Zeenat Hutu ya ƙare sun koma makaranta don suna shekarar ƙarshe ta kammala sakandare,Zeenat da Khaleesat da kuma Bilkisu da yake basu da wata tsera shiyasa Daddy yasa aka ajiye su dukan su ajin ƙarshe duba da yanayin girman jikinsu."Tun sanda su ka koma makaranta karatu suke fuskanta ba ji ba gani,sauran kuwa kowa ya mayar da hankali da karatun sa."Idan da matsala a gidan ba zai rasa nasaba da Zillaziya ba."

Duk da kowa yana sashensa amma saboda tsabar jan magana sai ta dawo Babban falon gidan ta zauna,haka ta ke shiga madafan Halima ta ɗebo abinda ranta ke so ta ci."Yau ma hakan ta faru Hajiya Halima na ɗakinta tana karatun Alƙur'ani mai girma,ba ta san wainar da ake toyawa ba,yayin da duk yaran sun tafi makaranta,da yake can suke islamiyya da tahfiz shiyasa basa dawowa,sai ƙarfe shiddan yamma,shiyasa ta shiga madafa ta ɗaubo tuwo da miyar taushe tare da soyayyan naman kaji da taga an soye."Dawowa tayi falon ta ɓararraje ta dinga ci tana kallo sai dariya ta ke ƙwasa tamkar zautatta,naman tasa gaba da lemon roba ta ci tana ba da ruwa."Bayan ta kammala addu'oin ta fitowa tayi don ta zubo abinci sai dai me zaune ta sameta tana taunar ƙashin cinya..."Tsaye tayi tana kallonta da mamaki ta ce"Lallai ma yarinyar nan kin raina ni!duk kawar da kai da nake kan ƙurciyarki bazaki karatun ta nutsu ba!To bari kiji ana barin halal don kunya ne,ina raga miki saboda cuta uku da ke damunki"Na ɗaya jahilci, na biyu rashin tarbiya, na uku ƙauyanci"Amma daga yau nayi miki kashedi da duk abinda ya kasance mallakina don ba zan kandir ba in haskaki ina ƙone jikina..."Don haka ki kiyayeni ki fita idona ina raga miki ne kan waɗancan cutaka da ke damunki,sannan ba girmana ba ne biyewa ƙurciyarki kisani ba don tsawo akan ga wata ba,daga yanzu kika ƙara gigin shiga sabgata sai na saɓa miki...Duk maganar da Hajiya Halima keyi tsaf a kunnenta amma tanɗar hannunta take kamar bata ji komai ba,sai da ta gama ta sha ruwa tayi gyatsa sannan ta ce"Haba Uwar ƴan mata meyasa ko yaushe akan abinci za'a ji ki?ni fa nan da kike gani na"murucin kan dutsi ce,da shirina na shigo gidan nan koni ko ke ko kuma tsohuwar ƴar duniyar can kakar ƴan mata."Wallahi ku fita idona na rufe ko jiki magayi..."Tsaki Hajiya Halima tayi ta ce"Allah sarki to aini idan bana haihuwa bana raina masu haihuwa ki jira ƴaƴanki maza kafin ki dinga kirana uwar ƴan mata ita kuma Hajiya da kakar ƴan mata don ba'a gane mabaraci in ba ƙoƙo muje zuwa uwar ƴan maza!"Daga nan ta juya da niyyar tafiyarta sau kawai Zillaziya ta riƙe Hijab ɗinta daga baya,da mamaki ta waigo me ki ke nufi?ke yarinya sakeni!ni sa'anki ce..."

Dariya tayi ta ce"Ke kika haifeni karshen son girma ina wani girma gareki bayan mun haɗa miji?uwar ƴan mataaaa...wani mari Hajiya Halima ta wankawa Zillaziya sai da ta ga wuta,yayin da sararin falon na mata yawo!nuna ta tayi da hannu ki sani "Ban iya sakayya da abin ƙi ba!sannan masanin ƙima shi ke girmama na ƙasa da shi,amma duk da haka sawun ƙarfe ce ni ina taka wanda ya takani!daga nan ta shige sashenta rai a ɓace."

Zillaziya dafe fuska tayi gabaki ɗaya komai ya ɗauke mata,yayinda lissafin ta ya dawo sabo,kuka zatayi ko ramawa zatayi ta ƙasa gane bakin zaren,hawaye masu zafi!ke ƙwaranyowa a fuskarta!zuciyarta na tafasa da ƙyar ta ja ƙafafunta da sukayi nauyi ta nufi sashen ta tana saƙa da warwara."

Da misalin ƙarfe shidda da minti ashirin, yaran su ka dawo daga makaranta,Bayan sun ci abinci sunyi wanka inda Mommynsu su ka shiga sai dai sun sami Momynsu a ɗakinta tana rusa kuka!jin motsin su yasa ta daina,amma zageyeta sukayi suna tambayarta lafiya?tayi ƙoƙarin ɓoye masu damuwarta,duk da manyan a ciki sun fahimceta amma a haka suka dinga rarrashinta har ta sake."

Kasancewar jikinta yay kyau ta wartsake yasa ta ci gaba da koyar da yaranta kamar yadda aka saba,kamar yanzun su na gama sallah magrib su ka fara karatun

Ammi ta ce" Yau zan baku labarin wata kissa ta wata mata mai ƴaƴa mata"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull