Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 8

Uwar y'an mata complete - Chapter 8

Uwar y'an mata complete Chapter 8: Uwar y'an mata complete Chapter 8. "Watarana Nana Aisha(R.A) tana zaune a gidan Annabi (SAW) sai ga wata mata ta shigo…

4,337 words

"Watarana Nana Aisha(R.A) tana zaune a gidan Annabi (SAW) sai ga wata mata ta shigo gida,tare da ƴaƴan biyu tana neman taimako,nan Nana Aisha ta shiga ɗakinta,ta ɗauko dabino ƙwara uku ta ba baiwar Allah nan,matar tana amsa tayi godiya sannan ta baiwa ƴaƴanta kowa ɗaya-ɗaya,"sauran ɗayan ta ɓare tasa bakinta"ko da ta duba ƴaƴan ta mata har sun cinye wanda ta basu,wannan ragowar ɓarin sai ta ciro a bakinta ta baiwa yaran."Sai Abin ya baiwa Nana Aisha mamaki har matar tayi tafiyarta,Manzo (SAW) yana dawowa ta ce"Ya Rasulillahi yau naga abin mamaki nan ta bashi labarin matar nan mai ƴaƴa mata."Sai Annabin rahma ya ce"Haƙiƙa duk wanda Allah yaba ƴaƴa mata,to ya haɗa shi da amma kuma idan aka kula da rayuwar su tun ƙurciyarsu har auren su to za'a dace."

Saboda duk mai ƴa macce to haƙiƙa ya samu lasisin shiga Aljanna."Haka idan ƴa macce ta tashi ba tarbiyya ta hanyar sakacin iyaye to akwai matsala."

Don haka ina jan hankalin ku ƴaƴa na kunga ku mata ne,don Allah ku ci gaba da kare mana mutuncin ku,duk abinda ya kamata iyaye yiwa ƴaƴa daga ni har Abbu muna iya ƙoƙarin mu,ina so ku kasance masu biyayya da tarbiyya da riƙon addini da kamun kai,don watarana kuma fa iyaye ne."sannan ku sani duk abinda ɗa yay ma iyayen sa sai ya haifi wanda zai masa..."

In shaa Allah Ammi zaki same mu masu biyayya inji Nabeela tana kallon Ammin su,Aysha ta ce"Ammi har naji ina ƙwaɗayin nima na haifi ƴaƴa mata in shiga Aljanna...Murmushi tayi ta ce"Ai da ƴaƴa mata da maza duk ɗaya ne Aysha ki roƙi Allah idan zai baki ya baki masu albarka macce ko namiji."Karki sawa rayuwar ki zaɓen jinsi kedai ki roƙi mai Albarka."Girgiza kanta tayi da alamar ta gamsu ta ce"Ammi Allah ya bamu masu Albarka...Amin Yaseera ta ce tana tattara littafansu."Khadija ta ce "Ammi ina da tambaya

Meye tambayar ki?inji Ammi tana kallon Khadija

Ta ce"Ammi ɗazu a talabijin ina kallon wa'azi sai naji malam ya ce"Idan za'ayi Alwala za'a iya ɗiban ruwan a wanke hannu,a shaƙa ruwa,a wanke fuska a haɗe sau uku."Gyara zama tayi ta ce"Eh ya halalta a ɗibi ruwan ayi wannan sau uku sannan kuma zaki iya ɗiba ki wanke hannu sau uku,shaƙawa da fyacewa uku,sai kuma ki wanke fuska sau uku Allah masanin gaibu."Jazakhallahu Khairan sukace dukan su yayinda suka rungume Ammin su."

Sai da ta samu ta saita tunaninta sannan ta kira wayar,ba'a ɗauki lokaci ba ta ɗauka,Zillaziya fashewa tayi da kuka!ta dinga labartawa Hajiya Babba wai Hajiya Halima ta daketa ita da yaran sun mata taron dangi duk sun ji mata ciwo,haƙuri sosai Hajiya ta bata,ta ce "A'ah Hajiya bari kawai na tafi gida saboda zasu taru su kasheni wallahi nan ta koma rushewa da kuka!Da sauri Hajiya ta shirya ta nufi gidan,Zillaziya ko tana ajiye wayar ta nemi reza duk ta yaga kayanta gaba da baya,fartunan ta masu akaifa ta dinga yagar jikinta da su,nan take jikinta ya ɗauki zafi!inda Halima ta mareta ta duba yana nan kunbure shu'umin murmushi tayi sannan ta koma tsakiyar falo ta ƙwanta tana kuka kamar wacce aka kawowa hari."

Tun a mota ta kirashi a waya ranta a ɓace ta ce"duk inda yake su haɗu gidansa yanzu nan bata tsaya jiran amsar shi ba ta datse kiran a fusace!"Mamakin kiran na gaggawa da Hajiya Babba tayi masa yake daman yana masallacin gidan nasa,shiyasa ya tsaya jiran isowar Hajiya Babba sai tunani yake amma ya kasa gano bakin zaran."

Idan banga ruwan comment ba zanje hutu👌🏽

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 28/29

~ALHAMDULILLAH...ALHAMDULILLAH...ALHAMDULILLAH~ .

```Today 26 Sept 2021 is my Wedding Anniversary Day``` 🎂

*May this day of our anniversary, make our relation stronger and lovelier for ever and ever Ameen* .

INA MIƘA SAƘON GODIYA TA, GA MASOYANA ƳAN UWA DA ABOKAN ARZIKI A BISA FATAN ALHERIN KU GAREMU ALLAH YABAR ZUMUNCI AMIN.

************** Gaba ɗaya layin gidan Buzu mai shayi da ke unguwar fagge,sun shaida Zillaziya ta shigo dan kuwa cikin haɗaɗɗiyar motar Alhaji Bello,direban gidan ya kawo ta,ai kuwa abin nema ya samu dan ƴan sa ido sun sami abin karin safe,maganar dai ɗaya ake tattaunawa" Allah ya yi ruwa garin yay sanyi,don gashi gidan Buzu Allah ya yi dashe."Kuɗi naira dubu goma ta ba Garbati, wani matashi da ta ke shiri da shi tun kan tayi aure,ta ce "Ya tafi banki ya canzo mata sabbi naira hamshin,mutanen unguwa da yara sai shigowa kallonta ake."

Saboda ta canja tayi fari da jiki ga haɗaɗɗen material da ta sa,glass ne manne a fuskarta,jikarta da mayafi a jikinta,takalmanta masu tsini suna sanye a ƙafafunta...kan kujera ta ke a ƙofar ɗakin su sai wani ƙyanƙyami takeyi tana busar hanci."

Karima zaune ta ke gefenta tana zuba mata fira,yayin da Safara'u tayi jigum dan Zillaziya ko kallonsu batayi ita da Tasi,sai cingam take ci tana danna waya."Garbati ne ya dawo ya ce"Ranki ya daɗe gasu,amsa tayi ta ƙirga dubu ɗaya ta bashi,fita yay yana gofiya tare da mata kirari."Gyara zama tayi yaran maƙota kowa ya shigo ta bashi hamshin sabuwa fil,ko kan kace me"Har iyayensu sun fara shigowa kawo gaisuwa su kuma ɗari biyu ta dinga basu,Karima taji daɗi shiyasa ta shiga ɗaki ta canja tufafi sabbi ta zo ta zauna nan fa maƙota su ka fara mata fada,sai da kuɗin ya ƙare sannan mutane su ka ragu dan Tasi ya rufe gidan su sarara."

Wannan ne ya baiwa Karima damar tattaunawa da Gimbiyar suna cikin fira sai ga direban ya dawo daga aiken da tayi masa kasuwa,kayan abinci da na masarufi ne ya dinga jidowa daga mota yana shigowa da shi wanda Zillaziya ta bashi kuɗi,ya sawo daman shiyasa ta faɗawa Alhajinta tana buƙatar kuɗi ta sayi kayan ƙwalliya,Karima wata irin guɗa tayi har sau uku sannan ta ce "Allah na gode Zillaziya ƴar arziki mai ƙashin hamdala ko da na santalo ki tsiya na bacci har yanzu bata farka ba Allah yay miki Albarka giwa ta gidan Moloniya Alhaji Bello uwar magaji zinariya abin wasoso..."Rungumeta tayi ta ce "Momma ki shiru har Direban ya wuce,ban so ya raina ni...Dariyar Tasi ta katseta harara ta zabga mashi nan yay shiru yana kallon Safara'u wacce ta zamo kamar mutum mutumi."

Direba na gama jido kayan ya wuce da zummar da yamma zai zo ya maidata gida,ta ce "To"sannan ta dubesu ta ce"Ke Safara'u ku tashi kusa kayan nan ɗaki bana son gulma,yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba inji Zillaziya a gadarance."Karima tashi tayi ta fara ɗaukar galam manja da mangyaɗa ta ce"Hakane kedai, ba'a da gadonka, amma aƙwai na zancenka, bari ki gani ai ni yanzu zan ɗaukesu,A'ah Mommah ga yara kai Tasi ba da ku na ke magana ba!Karima ta dubesu ga ƴan jakkar uba!Hajiya na magana kuyi mata banza,Yayar ku ce fa in yau na mutu ota ce magajiyata ita zata zame maku uwa,amma kun rainata hegu baƙin ciki ku ke mata kome?na lura tun zuwanta da kuka gaisa ba wanda ya ce mata ko ci kanki munafukan banza...Haba mommah bana so kina ta da harshe ki barsu ai na gane ƴan hassada ne,jikarta ta zuge ta ƙirga dubu biyu ta watsa musu ta ce"kun ga wannan ba don halin ku ba,daga nan ta ƙwashe kayanta zuwa ɗakin da ƙyar ta iya zama saboda gudun kar ginin lakan ya ɓata mata tufafi."Karima ko ƙwashe kayan abincin tayi sarai har buhun semo da ƙwalayen idomi da taliya dasu magi duka ta ƙwashe buhun ɗangote bata iya ɗauka shiyasa ta tsawata masu su ka taso suka tayata aka ɗauke."Kuɗin da Zillaziya ta basu Safara'u ta ɗauka suka raba da Tasi ta ce "ai ko ruwan marowaci kasha ka ƙware shi."

Ƙofar gidan ya ajiyeta, ta shiga shi kuma ya gyara hancin motarsa, yadda da zarar ta fito ta shiga zasu iya wucewa.Cikin izza isa da gadara ta ke tafiya har ta isa tsakiyar gidan tana sallama,gabanta ya faɗi jin muryarta shiyasa ta zabura ta fito daga ɗakin tana gyara ɗaurin zaninta da ke neman ƙwancewa,idon ta ya gane mata abinda ta ke tsammani,shiyasa ta ɗan daburce ta ce"A'ah Hajjaju ce a ranar nan?Safara'u "Na'am ta amsa tare da fitowa,ɗauko min tabarma Hajiya ce,Tabarma Karima ta amsa tana shinfiɗawa gabanta sai faɗuwa yake,cikin sa'a Hajiya Babba ta zauna nan su ka fara gaisawa,Zillaziya bata san me ake ba da waƙar ta ke saurare da (earpiece) a kunnenta."

Hajiya Babba ta ce"Abinda yasa na taso na zo gareki Karima,abu biyu zuwa uku ne,abu na farko ba sai na maimaita miki ba kin sani sarai na haɗa auren Ɗan Inna da Zillaziya ba don komai sai don Asamu canjin iri"Ma'ana canjin jinsi a gidan sa."sannan na zaɓi ɗiyarki don in tufa muku asiri ku samu abin korewa bakinki ƙudaji."Sai abu na biyu da ke tafe dani ina son ki ƙara baiwa Zillaziya haƙuri da magana,ta ƙwantar da hankalinta don na fahimci ta tsorata da sha'anin shu'umar matar nan UWAR ƳAN MAATA"daman shiga inda aka riga ka sani sai da haƙuri amma ƙwace goruba a hannun kuturu abu mai sauƙi ne."Abu na ƙarshe na sanki na kuma san halinki,ke ma kuma kin san wacece Karima kisani duk iya biɗarki da shige-shigenki ba zaki taɓa kama ƙafata ba har abada,don haka idan dai ita Matar shi zaku baɗeta da magani kuyi abin ku amma Kuuuuul Karima banda Ɗan Inna!nan da kike ganinsa gamji ne sha sassaƙa ba dai yin mutum ba,sai ta Allah ko kunyi masa magani muddin bani nayi ba aikin banza ne,don ba zai kama shi ba,na jika na bashi,na dafa na bashi,nayi mai wanka na murza mai tun yana yaro."sannan ita ma matarshi tana da tsari ba boka ba mallam amma mai kowa da komi gareta ALLAH na sha aiki tana lalatawa da addu'ointa,naso na rabasu na tura masa tsanarta ƴaƴanta amma duk ta warware,to ni yanzu na gaji da ɓarnar kuɗi ta gefenta na tsayu ga ɗana,ita kuma ta hanyar tsana zata gaji ta ƙara gaba,don yau da gobe sai Allah."Idan ko ta jure to amma maganar gaskiya karku ƙara barnar kuɗinku wurin yi ma ɗana magani dan zakuyi a banza"Ke ko guba kuka sa masa ga abinci yaji zata koma ba zatayi masa komi ba Karima,ku kiyaye ke da ƴarki daga taimako sai a faɗa magani,saboda ƙwaɗayi da tsabar so abin duniya,ai idan kun ƙwantar da hankalinku zaku ci amma yaushe akayi Karima?sunkuyar da kanta tayi ƙasa wani wan wani kenan inji ƴan magana."Hajiya Babba ta tuntsure da dariya tare da tashi ta ce"Ni ba zan haifi ɗana ba uwar wata wai matarsa ta ce"ta mallake shi ba!ai ba abanza na same shi ba,don haka kubi sannu kuci rabonku,idan ba haka ba za'ayi faɗuwar guzuma ba uwa ba ɗa."jikkarta ta buɗe kuɗi ta ɗauko masu yawa ta dinga fifita dasu sannan ta miƙa ma Karima ta ce"Ga wannan a sayi sabulu,amsa tayi zufa shakaf a jikinta jiki ba ƙwari ta ce"Na gode Meri kiyi haƙuri in sha Allah wannan ne na farko na ƙarshe in dai akan Alhaji ne."

Ahto!idan kunne yaji dai sai jiki ya tsira!amma ba zan zuba ido a mallake ɓin ɗa ba,don ba wanda ya aifa min shi,sannan nidai idon gari ce,duk abinda gari da mutanen gari ke ciki ina sane musamman idan an taɓo gefena."Har ƙofa Karima ta rakata sannan sukayi sallama da ita ta wuce."

Ɗakin ta faɗa a lokacin duk ta suke kuɗin da Hajiya Babba ta bata a ƙugu,In da Zillaziya ta ke ƙwance ta nufa tare da cewa"ke tashi an yanka ta tashi...Da sauri ta cire abinda ke kunnenta ta ce "Lafiya Mommah?ina ko lafiya wannan tsohuwar banza ta lalata muna shiri duk abinda mukeyi tana sane ta ajiye malamin da ke karanta mata lissafin mu...Bangane ba Zillaziya ta tambaya"Nan Karima tayi mata bayanin komai,A fusace ta tashi ta ce"Kai ina!ai ba zai yuyu ba!dole aƙwai wanda yafi nata bala'i idan har ke barazanarta ta tsorata ki,to ni ta ƙara min ƙaimin in shiga in fita in nema in samu,har ta isa tayi mana shamaki da burin mu!Waigowa tayi tana zubda ƙwallah!ta ce "Mommah wato yanzu na gane Hajiya ta haɗa auren nan don in nasamu ɗa namiji buƙatar ta ta biya,sai ta dinga mulkar mu sai yadda tayi da mu saboda muna talakawa!To wallahi tayi kaɗan...Ni uwar magaji sai na zamo komai kuma kowa a gidan mijina ba wata ƴar duniyar tsohuwa da zan bari ta taka mun birki ni da ita hege kan fasa!wasa farin girki...."

Ajiyar zuciya Karima tayi tare da dafa Zillaziya ta ce"Ina so ki fahimce ni,na fiki sanin wacece Maryam ba zaki iya ja,da ita ba,shu'umar gaske ce da naso ki haƙura ko yanzu ai sai munci...Mommah ba iya ku ci burina ya tsaya ba!duk matsayinda Hajiya Babba ta taka a rayuwa to ni ina so ki wuceta...don haka ba zan haƙura har sai burina ya cika wallahi!kuma duk zamanta shu'uma na fita,saboda yanzu kaina ya waye sanadin waya na haɗu da manyan mata ƴan duniya wanda suka san kanta duniya to gurin zan nemi ƙarin haske kan matsalata da Maryam komai ta fanjama fanjam!

Me kike nufi Zillaziya ?Karima ta tambaya

Wani shu'umin murmushi tayi mai ɗauke da manufofi da yawa ta ce "Mommah ma'anar maganata ko rai ko mutuwa ni da Maryam!"Buɗe ido Karima tayi tare da riƙe baki ta ce"Tabbas aƙwai ƙura nan gaba kenan,Zillaziya ta ce "Ba ƙarama ba ki gyara bakin zaran Mommah wataran zaki ga ƙarshen sa..."

Caaaaaf aƙwai ƙuraaa....Fans me ku ka fahimta a cikin wannan wuta da zata kunno kai ya makomar Hajiya Babba?Zillaziya da kuma Hajiya Halima....ajuri zuwa rafi inji Ƴar mutan Dikkawa

Idan banga comnents ba zan mayar sa shi na kuɗi daga wannan page

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 32/33

*FIVE STAR'S INCENCE*

*Mun zo muku da turaruka na ban mamaki, ko da kuɗinku sai da rabonku, mu na da kayan ƙamshi masu ƙamsashe jiki da gida baki ɗaya sai an gwada an kan san na ƙwarai,masu buƙatar sari ko sayen ɗaya,ƙofar mu a buɗe ta ke muna tura koyanmu ko'ina.*

~PRICE PER LITER OF INCENCE;~

HAWEE-6000 \ SCENTED GODDLES 10,000

SENEGAL KAJIJI-6000 / BLACK KHUMRA-7500

HALUT-4500 / CREAMY WHITE 5500

ROSE INCENSE-4500 / SWEET DREAMS-6500

SENEGAL ROYALE-5500 / CLASSY QUEEN-20,000

SIGNATURE BAKOOR- 4500 / RED KHUMRA-6500

SIGNATURE SANDAL 4500 / MEN KHUMRA-8500

BLACK KAJIJI-4500 / BATH KHUMRA-5500

MAI AYA -4000 / ROOM MIST-6000

VIP MISK-5000 / KWALLACHAM-7000

SANDAL FLAKES-4500 / TURAREN MOPPING-4000

2 in1-4000

SANDAL ROSE-6500

AƘWAI;

QUEEN OF THE NIGHT VESELINE 600, 1200

ROOM MIST 600

BATH SCENT 600

MOPPING FRAGRANCE 600

ROOM FRESH 600

KHUMRA 1000

TURAREN GARWASHI 1000

SANNAN MUNA DA ƘAYATATTUN SPICES MASU ƊANƊANO DA SINARAN ƘAYATA GIRKI A RAHUSA

Ga masu son sayen ɗaya ko sari na kayan Ƙamshi da duniyar girki sai kun tuntuɓe ta wannan👇🏿👇🏿👇🏿

07068048901

COME ONE COME ALL

******************** Ƙofar gidan ta ce"Direban ya tsaya,ganin Alhaji Bello a tsaye,ƙofar gidan Hannayen sa sanye cikin aljihunsa."Inda su ka tsaya ya nufa,da sauri ya buɗe bayan motar yana faɗin"sannu da zuwa Hajiya."Fuskarta a ɗaure ta amsa sannan ta fito ta fice,bayan ta yabi gabansa na faɗuwa duba ga yanayin da yaga mahaifiyar sa."A babban falon gidan ta tsaya tana ƙarewa ko'ina kallo ba motsin komai sai ƙarar talabejin da ke tashi daga sashen Halima da hayaniyar yara,ƙwafa tayi ta ce "Biyoni muje,kamar raƙumi da akala hakan ya bi bayanta ta wuce fuuuuuu...sai sashen Zillaziya."

Tana jin motsin alamu shigowar su ta dinga murzar idonta da ta wanke da sabulu sunyi jajur,kuka ta dinga yi tana mulmula daga farkon falon har tsakiya,A wannan yanayin suka sameta da sauri Hahiya Babba ta taro Zillaziya daga ƙofar ta ce "Me zan gani yau a gidan nan?Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un!ya faɗi yana ƙoƙari dosar inda ta ke ya ce"Ke lafiya meke faruwa?A fusace Hajiya Babbba ta ce"Ina lafiya kuwa...Uwar ƴan mata da marar tarbiyan yaranta su ka farmata,saura kaɗan su kasheta me yay saura ka dubeta kamar ba ita ba!har kayan jikinta an yaga...Zillaziya tana kuka har shiɗewa tana juya idonta kamar makauniya...ta lalubo Hannu Hajiya"Ta ce don Allah Hajiyata ki mayar dani gurin mammanah zadu kashe sun zubar min da ruwan ido bana gani sosai,kinga jikina duk sun yageni,kunga fuskata da Anty Halima ta dinga tazga min maruka ina ganin kunnena ya taɓu har wani dumnnn nakeji."Rarrafawa tayi gurin shi idonta a rufe murya a disashe ta ce "Don Allah ka taimaka ka sauwaƙe min ba zan iya zama da kai matuƙar da muguwar matar nan a gidan nan,saboda ta faɗa min sai tayi ajali na,na gane karanbani ne da ƙaddara su ka kawo ni gidan nan amma babu muhalin wata macce a ciki matuƙar ba ita ba,kai da ita hanta da jini ne....Kukan ne ya ci ƙarfinta ta durƙushe tana rusa kuka mai tsuma zuciya.''

Hankalin Hajiya ya tashi hannu ta aza aka itama tana rusar kukaa ta ce"shi kenan ka tabbata shanyayye ɗan Inna,ni meri naga taskon rayuwa na haifawa wata banza ɗa,yanzu kai har haka ta faru a gidan ka saboda ka tabbata mijin ta ce sai ka zuba ido ba zakaje ka ɗauki mataki ba!"

Ba haka bane Hajiya tayaya zanyiwa magana hawan ƙaho na ɗauki mataki ba tare da na bincika ba...ita Zillaziya kafin ta kiraki a waya bazata kirani ba ina ma ƙofar gidan tun da magariba...Da zafin nama Hajiya ta wanke shi da mari ta nuna shi da yatsa ta ce "Wallahi baka isa ba,yanzu lalacewar da shanyewar ya kai kaji haushi don an kirani an faɗa min ga matsala!to yau dole ka zaɓa ko ni ko uwar ƴan mata ba zan zo a banza in koma a wofi ba!kaje kai mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata sannan ka zo muje akai ƴar mutane asibiti."wani shu'umin murmushi Zillaziya tayi ranta don ga alamu ta kusa cimma gaci."

Tana sashenta ba tasan wainar da ake toyawa ba,saboda hayaniyar yaran ita kuma tunda ta zauna magrif ta dinga lazimi bayan ta kammala Azkhar tana jiran sallar Isha."Ƙofar ɗakinta taga ya buɗe da ƙarfi tamkar an jeho shi,a jujuce "Hasbunallahu wa ni'imal wakil ta faɗi a zuciyarta."Kallon shi tayi tsaf sannan ta ce "sannu da zuwa."Me ya haɗaki da yarinyar can?Meyasa zaku taru ku daketa?

Haka ta faɗa maka kai kuma meyasa bazaka tambayi ba'asi ba?Dakata Halima kin sani sarai bana son fitina meyasa zaki ta dota a gidana...kinga yanzu har Hajiya Babba ta shigo cikin lamarin nan,ni kaina banji daɗin yadda ku ka tashi yin kisan kai a gidana ba,ai kishi ba hauka bane idan kina sara ki dinga duba bakin gatari...Har zatayi magana ya ce"bana son jin komai daga gareki ki zo muje ki ba Hajiya da Yarinyar nan haƙuri!"

Hawayen ɓacin rai taji suna mata zuba ta ce"Haba Abban Zeenat ka san irin haƙurin da nakeyi da Zillazayi amma a haka zaka laifina wallahi marinta kaɗai nasan nayi amma zaka ce naso kasheta,sannan ka cire yarana a zancen don ko da akayi basa gidan nan,dukan su suna makaranta ina limina da har zan tasa yarana gaba mu daketa tana matsayin matar uban su,kenan na koya masu yadda idan su ma sukayi aure zasu koyar da ƴaƴansu..."A'ah to ni kaina ya ɗaure daga ke har ita na rasa gane mai gaskiya muje falo a sasanta lamarin nan abinda mamaki ga shi duk an jimata ciwo hakan...Tsaki yay ya fita daga ɗakin,Allahu Akhbaar kabeeran ta furta a fili,to me shirin faruwa?Ɗaga hannayenta tayi sama tana hawaye ta ce"Ya Allah kaine masanin gaibu ka shiga tsakanina da waɗannan bayi naka,duk wuya duk runtsi Allah kasa nayi galaba akan su da sharrin su Allah da kai na dogara..."Daga nan ta shafa ta fita."

Ɗakin ya shiga a ladabce ya ce"Hajiya ga Halima can falo nayi mata faɗa sai dai ita ma tayi min bayani wanda yasha banbam da na ita Zillaziya sai ku fito ai musu sulhu a tsakanin su,don a gaskiya bana son tashin hankali duk ita kanta Halima nasan ba ma'abociya ta da husuma ba ce zuwan abu ne kawai..."Hajiya ɗaga Zillaziya tayi ta ce"To muje Alaramma mayafi ta azawa Zillaziya da ta ƙasa tsayuwa riƙeta tayi suka fito falon tana ɗingishi."

Sun sameta zaune da Hijab ɗinta tasbaha a hannunta, daga ganin ta kasan bata ciki walwala da daɗin rai,ganin Hajiya yasa tayi saurin gaidata,Hajiya Babba ajiye Zillaziya tayi saman kujera sannan ta waigo bata tsaya ko'ina ba sai gurin Halima ta wanketa da mari,da sauri ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin magana shi ma ta wanka mishi mari!lokaci suka dafe fuska,Halima sunkuyar da kanta tayi tana zubda ƙwallah...Muryar Hajiya ke tashi a falon "Ta ce ke ko bariki kin iya wai har da gaidani nace miki ina buƙatar gaisuwar ne makira,munafuka sum sum kamar ta ƙwarai,amma kina neman kisan kai to wallahi yau sai kin gwammacewa kiɗi da karatu...Zillaziya sau nawa matar nan ta mareki?Hajiya ta tambaya ranta a ɓace

Tana sheshsheƙar kuka ta ce"Sau uku ne...ai kan ta rufe baki Hajiya ta kife Halima da mari uku a jere,tun tana tsaye har ta faɗa kan kujera tana rusa kuka!Kasancewar yana karyayyar zuciya yasa shima ya dinga kuka!Hajiya ta ce" wato saboda kaine inuwar da ta raɓa ta ke shan iska shiyasa zaka tayata to sannunku masoya wallahi kukan nan da kayi yasa naji na ƙara tsanarta kuma yanzun ka sallameta tavɓbae gidan nan don ba da ƙwabon tsohonta da tsohuwa ka gana shi gumin ka ne meyasa ba zaka gane shinkafa mau tsakuwa batayi sai an raigaye"Dole ka raigaye baƙar tsakuwar da ke neman illata rayuwarka."Jin hayaniya yasa hankalin su ya tashi don ko ba'a faɗa ba sun san mai muryar,Zeenat ta fara fitowa falon yayinda ƙannanta taƙwas suka mara mata baya da sanɗa suka shigo falon,ganin Daddy da Mommy da kuma Anty Amarya na kuka ya sa jikinsu mazari."Hajiya janyo Hannun Zeenat da Saudat tayi ta ce duk ku zo nan munafukai har kun ƙasaita ku taya uwar ku faɗa duk kun ƙwanta ta ce tana fidda ido a tsawace, nan ta ke kowa yay ƙasa,jikin talabijin ta isa ta zaro kebul ta dinga zabga masu a ɗuwawu da jikinsu,kowa kuka yake yana don Allah Hajiya kiyi haƙuri."Wani irin kuka mai tsuma zuciya Hajiya Halima tayi wanda yay sanadin razanar Alhaji Bello bai san sadda ya isa inda Hajiya ya riƙe kebul ɗun ya ce"wallahi Hajiya basu daki Zillaziya ba...ke Zeenat ko kun daketa cikin kuka ta ce"Daddy bamu san meke faruwa ba!bamu taɓa dokan Anty ba...Saudat ta ce Daddy idan mun daketa ai Mommy zata yanka mu."Mamu tashi tayi tsaye tana sosa jikinta ta share majina ta ce"Allah ya isa Aunty kin mana sharri Hajiya kema Allah yay maki yadda kikai mana daga nan ta gudu ta rufo ƙofa."Sake kabul ɗin tayi tare da juyawa ta ce "Ga bayana ka dakeni ɗan Inna saboda na daki ƴaƴanka mata,gashi a gabanka Maryam tayi min Allah ya isa."Sake mata yay yana goge ƙwallah ya rasa ina zai sa kanshi wannan masifa har anyi sallar isha ana abu ɗaya."Kuka ƙananan yaran keyi wiwi wiwi su ka nufi inda momynsu rungume su tayi tana kuka."

Zillaziya wani daɗi ya mamayeta amma a fili nishi ta ke,tsaf Hajiya Halima ta gane sharrin da Zillaziya ta haɗa mata ganin yadda duk kamanunta su ka sauya,kuma da zarar sun haɗa ido ɗaaar ta dinga mata murmushi da gwalo."

Kaiwa da komowa takeyi ta rasa irin hukuncin da zata yanke idonta a rine ta dubeshi ta ce"Ɗan Inna idan har ni maryam ni na haifeka to ka saki Uwar ƴan mata bana sonta na tsaneta duniya da lahira har abadan abidina bana fatan zama inuwa ɗaya da ita,zama da ita asara ne bata haifa kuma tana baƙin cikin ashigo gidan nan a haifa maka ka samu magaji abokin zuwa masallaci da kasuwa."Ina son yanzu ta tattara ita da ƴaƴanta su bar gidan nan....Haba Hajiya ina zataje cikin daren nan,bayan kin san ba ƴar garin nan bace bata da kowa sai mu."kuma yara nawa ne ba dasu ta zo ba don haka ina son su ba inda zasuje."

Haɗe hannuwanta tayi a ƙirji tare da kaikaice kai da ido ta ce"To naji bata da kowa sai kai,idan ta fita ta haɗu da ajalinta a hanya,amma sai tabar gidan nan horar abinda ta aikata su kuma ga ɗakin su suje su zauna zaman uwar su."

Ganin abin na neman wuce gona da iri yasa ta tashi tare da kama hannun yaranta ta shiga sashenta haƙuri ta basu tare da sanya masu albarka tana kuka suma suna kukan,ta haɗa aƙwati ɗaya ta fito inda duk suka mara mata baya suna,Mommy don Allah karki tafi,dare ne garinku da nisa mommy kar asace ki mu ba zamu zauna ba sai ki tafi damu..."In da yake tsaye ta isa ta ce"Abban Zeenat ka bani takarda ta zan ƙara gaba ga yarana nan na bar maka su amana don yanzu basu da sauran masoyi bayan kai..."Duk abinda zaki faɗi ki faɗa kai tsaye don ciwo na ga fillo mallam ko sai tofi."Inji Hajiya

Goge ƙwallah tayi tare da waigowa don yanzu zafi da raɗaɗin da ta ke ji,yasa ta samu ƙarfin gwuiwar mayarwa Hajiya martani ta ce"Hajiya haƙiƙa na ɗaukeki uwa,kuma na baki girma fiye da ƙima sannan ina ƙoƙarin kaucewa duk wani fushin ki,sai dai kash duk wannan ki watsar da su,saboda wani ra'ayi naku na dabam wanda ba shi acikin Addini.A ganina ke uwa ce sannan ke macece kuma macce ta haifoki to banga dalilin da zaku tsaneni akan ƳAƳA mata ba,bani na baiwa kaina ba ubangiji ya bani to meyasa zakuyi ja in ja da hukuncinsa ba,kisani duk"Kunnen da baya ɗaukar ji,to cikinsa da ƙurji don haka aƙwai gyara ga wannan lamarin."Ina roƙon ki gafara da ki yafe min sannan duk da baki son yarana ki sani gudan jininki ba za'a taɓa canja jini ba,Allah ya riga ya haɗa na baki amanarsu ko da za'a taru a kashe su,su ɗin ƴaƴan MUHAMMAD BELLO BABALE ne."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull