Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 9

Uwar y'an mata complete - Chapter 9

Uwar y'an mata complete Chapter 9: Uwar y'an mata complete Chapter 9. Tana kaiwa nan ta koma kan shi ta ce"Ka sallameni don ba amfanin zamana da kai lafiya…

4,454 words

Tana kaiwa nan ta koma kan shi ta ce"Ka sallameni don ba amfanin zamana da kai lafiya matuƙar babu farinciki a zukatan ƴaƴana,muddin wutar ƙiyayya ta kunnuwa tsakani na da Hajiya da sauran danginka tofa ba wani sauran jin daɗi."Ke kuma Zillaziya kiji tsoron Allah ki gujewa son zuciya ki sani shiga da fice a tsakanin ma'aurata ba abu ne mai kyau ba."ki sani tuwo sunansa tuwo ko da kuwa ya ƙone."Ba zance komai akan tuggun da kika ƙulla ba,amma kisani watarana jifa zai dawo ƙasa komai nisan sa."Jikar ta riƙe tayi tsaye tana jiran shi...Hajiya ta ce"lallai wuyanki ya ƙosa ya isa yanka uwar ƴan mata ni zaki faɗawa magana har da ƙazafi a fakaice...kai maza ka saketa...Don girman Allah Hajiya ki taimaka min ki tausayawa yaran nan ina zan kai su wallahi Zillaziya ba zata iya ɗawainiya da su ba,ki bara a sasanta...wallahi idan baka saketa ba zan iya tsine ma Albarka ɗan Inna...Tun ya ce komai taja aƙwatinta tayi ficewanta daga gidan,yaran bin ta sukayi har harabar gidan suna kuka!tare da faɗin ta dawo ko waigowa batayi ba ta fice daga gidan."Don zuciyar ta turniƙe ba abinda ta ke sai bugawa wani jiri ke ɗibanta ambaton Allah ta ke ciki da wajen zuciyarta."

A tsakiyar gidan su ka durƙushe su na rusa,kuka wanda yay sanadin mai gadin ma ya fashe da kuka don yasan ba lafiya ba,A falo ma sai zanga masifa Hajiya Babba keyi tana faɗin wallahi ko direba ne sai an aika da takardar nan shegiya shiyasa ta wuce ba amsa ba, munafuka banza kawai maza ka rubuta sakin nan ka bani zansa direba yaje har garin su ya kaima iyayenta."Zaune yay dirshim a falon ya haɗe kai da gwuiwa ya kuka!tsaki tayi tare da cewa ke Zillaziya tashi muje asibiti na lura baki da lafiya."

A sanyaye ta ce "Hajiya yanzu zanyi wanda da ruwan ɗumi ina da rub zan shafa sai in sha shayi da magani nasan zuwa gobe zan wartsake."To shi kenan gobe zan zo Hajiya ta ce "sannan ta bar falon,a tsakiyar gidan ta samesu suna kuka!wuce su tayi ta wuce abinta,mai gadin ya lallaɓa su suka koma daga ciki,inda yake zaune yana kuka suka zauna suma suna kukan tare da roƙonsa akan ya dawo musu da momynsu...Rungume su yay yana basu haƙuri...wani haushi ya kama Zillaziya don ta lura ko ta jikinta bayayi ya kama yaran sa shiyasa ta tashi tabar falon da takaici."Sai dai tana shiga ɗakinta wani amai ya taso mata bayan tayi nan take jiri ya ɗebeta ta faɗa gado kankace me jikinta ya ɗauki zafi har da rawar sanyi."

Ko ina Halima ta nufa?

Ina labarin Ammi?

Me ke damun Zillaziya?

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 34/35

*HAƘIƘA BANYI MAMAKI BA,YADDA MUTANE DA DAMA SU KA SHA KUKA, A BABIN MU NA BAYA,NI KAINA ABIN YA TSUMANI.AMMA KU SANI KOWANNE ƊAN ADAM DA NASHI JARRABAWA, KOWA KUMA BA ZAI WUCE NASHI JARRABAWAR BA.*

_COMMENTS ƊIN KU AKAN UWAR ƳAN MAATA YANA SA NI FARIN CIKI_

Tafiya mai tsawo tayi,da ƙyar ta samu mai adaidaita sahu, shiga tayi tare da faɗa masa in da zai kaita.Sun ɗauki lokaci suna tafiya,ba abinda ke tashi sai sheshsheƙar kukan ta!Har su ka kawo ƙofar gidan ya ajiyeta,kuɗin shi ta bashi sannan ta fito da aƙwatin ta,wayarta ta fito da ita ta ƙira lambar Lubabatu.

Da sallama ta amsa wayan,ajiyar zuciya tayi sannan ta ce"Lubabatu gani ƙofar gidan ki,ina fatan kina nan?"A ɗayan ɓangaren ta ce"Eh Sadiya ina gari,ina fatan lafiya?"Shace majina tayi ta ce"Ba lafiya Lubabatu ki zo gani inji Halima."Da sauri Lubabatu ta sauko daga sama zuwa ƙasa da sassarfa ta buɗe gidan tare da kallon ƙawarta wacce tayi wani iri.Da mamaki ta dubeta tsaf ta ce "Sadiya me ke faruwa?Me ye bai faru ba Lubabatu...Hannunta ta kama tare da jan aƙwatin sannan ta rufe gidan,su ka wuce daga ciki.

Bayan sun zauna ruwa masu sanyi ta ɗauko,a firijin ta tsiyaya mata ta ce"Ungo ruwan sanyi kisha Sadiya don na lura sai ajiyar zuciya ki ke."Ruwan ta amsa ta sha,sai kuma ta dubeta ki ka ce suna da sanyi?Eh mana bakiji ba?Girgiza kai tayi ta ce"naji akan harshena sai dai a zuciyata zafi najiya."Daga inda ta ke ta ƙaraso inda ta ke tare da riƙa hannunta ta ce"Tabbas ba ki da lafiya,don Allah ki hanzarta faɗa min matsalarki Sadiya!Sanin kanki ne daga ke har ni muna da matsala,gashi Allah ya haɗamu ba mu da kowa dukan mu ba ƴan Kano ba ne,zaman aure ya kawo mu,yayin da muka ci karo da ƙaddarar rayuwar Aure."Idan kin faɗa wata matsala bayan wadda ki ke ciki,ta tsana da kishiyar huce haushi to na tabbata nima zuwa gaba kaɗan ba zan tsallake tawa ƙaddara ba."

Wani kuka mai tsuma zuciya ta fara rerawa wanda ke fitowa daga ƙasan zuciya, don ta da tuna da yaranta,ko wane hali su ke ciki?Babu mai bata amsa.Lababutu kuka ta rushe da shi,ta ce"Haƙiƙa aƙwai matsala!Babbbar matsala ma kuwa...Hajiya Halima ta amshe zancen ƙawarta ta ce"Lubabatu yau dai nabar yarana duk yadda na tsani nisanta kaina da su,labarin duk abubuwan da su ka faru tayi mata."Lubabatu ta jinjinawa lamarin,amma tayi hamdala tunda Alhaji Bello bai riga ya saki ƙawarta ba,haƙuri da ban baki tare da ƙwantarwa da Hajiya Halima hankali tayi,har ta samu ta ɗan ci abinci sannan su ka hau sama zuwa ɗakin bacci."Ƙwantawa sukayi kowa da abinda ke cin zuciyarsa,Hajiya Halima ba abinda ta ke zubarwa ƙwallah fa ce halinda su Zeenat zasu shiga musamman Sareena ƙaramar a cikin su,A ranta tana jin babban giɓe ne uwa ta fita tabar ƴaƴanta,musamman mata domin uwa kaɗai ce zata iya kula da rayuwar ƴa macce mai ɗauke da ɗinbim hatsari."Ita kuma a gefe tunanin mijinta ta ke wanda yau kusan satin sa ɗaya,rabonsa da gidan ta a cewarsa"wai ya yi tafiya,amma ta san idan ya ɗauki hutu gidan amaryar ya ke tarewa su na rayuwar su da ƴaƴan sa,a hankali ta ke tuna rayuwar gidan na ta da alaƙarta da Sadiya."

*********Lubabatu ƙawar Hajiya Halima ce,sun haɗu a group ɗin kasuwanci, na yanar gizo,daga nan su ka fara zumunci da kasuwancin su tare,faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama don rayuwar Halima da Lubabatu ku san duk iri ɗaya ne.Lubabatu kanuri ce,ƴar asalin jihar maiduguri daga ita har Sadiya ba ƴan kano bane. Zuwa yanzu shekararta goma sha biyar da aure amma Allah bai bata haihuwa ba,sanadin hakan yasa dangin mijinta su ka juya mata baya har su na kiranta da "juya, cin mutunci da cin fuska ba wanda basu mata."Mijinta Labaran yana ƙaunarta kuma bai rage ta da komai ba,idan da ciwon zuciyarta a rayuwar aurenta ba zai wuce dangin mijinta ba.saboda yanzu sun tasa Labaran gaba dole sai ya yi aure ya samo mai haihuwa,Ba don yaso ba dole tasa ya ƙara aure ko shekara ba ayi ba,amarya Zuhra ta samu ciki bayan wata tara ta haifo ƴarta macce wacce ta ci sunan Hajiyar su Labaran wato Hajara inda ake mata alkunya da (Hanan) daga lokacin aka ƙara juya mata baya don ta tabbata juya saboda zuwa yanzu Zuhra ta kusa haife hanjinta duk shekara sai ta haihu."A yanzu hakan Zuhra ce mowa yayin da Lubabatu ta dawo bora Labaran kawai ta ke jin sanyinsa duk ko shi yanzu hankalinsa yafi karkarta akan Zuhra da yaranta,kasancewar ba gida ɗaya su ke ba kowa da unguwarsa,shiyasa duk abinda Labaran ke ma Zuhra sanadin yaran bata sani duk wanin kuma ta sani amma tana kawar da kai."Addu'ar Lubabatu ɗaya ce Allah ya bata haihuwa mai Albarka ko ɗaya ne macce ko namiji ita dai ta samu rabonta."A kullum ta dubi ƴaƴan Sadiya ji ta ke ina ma Allah ya bata irin su koma fiye da hakan.Abin takaici Allah ya baiwa Sadiya haihuwa har tara amma ana muzguna mata akan su."Hawaye ta goge tare da gyara matashin kai tana ci gaba da kokawa nata ƙarshen."Daren dai ya zamo daren baƙinciki da taƙaici a zuciyar Hajiya Halima,Lubabatu su Zeenat da kuma Alhaji Bello.

******************* Washe gari tun da wuri ta tashi, ta fara ayyukan gidan,inda su Nabeela sy ka tayata bayan sun ƙarya makaranta su ka wuce,Abbu ko gurin aiki ya nufa,shi ya bata damar ƙarasa dukkan ayyukan gidan,bayan ta kammala,da misalin ƙarfe goma da rabina safe ta bar gidan,zuwa makarantar matan aure ta safe, da ta ke karantarwa yayin da su ke tashi ƙarfe sha biyu da rabi.Ta samu ɗalibanta ci ke da aji suna jiran isowanta da fara'ah su ka gaisa sannan ta fara musu karatu bayan ta gama ta shigo musu da nasiha akan haƙƙoƙin ma'aurata.

Gyara zama tayi tare da gyaran murya,gilashin idonta fari fes ta ƙara masa mazauni a fuskarta,wanda yay mata kyau sannan ta ce"Yau zamuyi tsokaci akan Haƙƙoƙin miji akan matarsa da kuma Haƙƙoƙin mazajen mu da ke kan mu."

Haɗa baki ɗaliban sukayi wurin faɗin"Ma sha Allah malama muna biye."Ta ce Haƙiƙa macce tana da Haƙƙoƙi goma akan mijinta sai ku saurara da kyau,duk wanda a cikin su ta ga mijinta ya tauye mata abu ɗaya tana da damar masa ƙorafi,idan mai ilimi tabbas zai gyara don yasan ba yinki ba ne faɗan Allah (SWT)da manzo rahma (SAW) ne Haƙƙi na farko shi ne"Ciyarwa,bi ma'ana namiji zai ciyarda ke abinci mai kyau wanda ba zai cutar da ke ba."

Na biyu shi ne"Shayarwa,bayan kinci ana son ki sha,shayarwa ta kama da duk abinda a halal wanda zaki iya sha."

Sai abu na uku shi ne"Sutura ana son namiji ya dinga yiwa matarsa sutura(Tufafi)

Abu na Huɗu"Kayan ƙwalliya,kadancewar macce ƴar ƙwalliya ce ana son miji ya dinga samawa macce kayan ƙwalliya don ko ana da kyau to ana so a ƙara da wanka."

Na Biyar kula da Lafiya, Na Shidda kula da ilimi, Na Baƙwai Haƙƙin aure, Na Taƙwas ya kula tsaftar ta Na tara muhalli mai kyau, Na goma Kyautata mata a zamantakewa."A gurguje waɗannan duk ana so namiji ya kula dasu domin Haƙƙoƙi ne da su ka rataya akan sa."

Sai mu mata a matsayinki na macce mai daraja wato matar aure,ya kamata kisan haƙƙin mijinki a kanki wanda idan kin tauye masa to zaki tunano ki tuba ki gyara."Haƙƙin namiji Biyar ne akan macce Na farko ki zamo mai "Biyayya."

Na Biyu ki zamo wacce idan ya ce yi to ki yi."

Na uku idan ya ce"Kiyi to kiyi idan ya ce" bari sai ki bari."

Na Huɗu "Ki kasance mai tsaron mutuncinki."

Na Biyar "ki zamo mai faranta masa.wasu malammai sunce a ƙarƙashin farantawa ne,Tsafta,kulawa,iya girki,iya magana,kula da danginsa,kula da iyalinsa da sauran dai abubuwan da ya kamata kiyi don ki faranta masa su ke."In sha Allah anan zamu dasa Aya sai kuma gobe idan mai kowa,mai komi ya kai mu abinda na ke so ku hankaltu ku gyara Allah yasa mu dace Amin.

Jazakhallahu khairan Malama,ɗaliban su ka daga nan tasa shugabar Ɗaliban tayi addu'a su ka shafa sannan kowa ya tashi.

************ Yadda Zillaziya ta ga dare haka ta ga rana,har yanzu Alhaji bai ko leƙota ba,bare ya san a halin matsanancin ciwon da ta ke ciki,Shi kuma tun ya ƙwanta kan shi ke masa zafi shiyasa yana dawowa masallaci inda yaran ya nufa,ya samu Su Zeenat su ta da sauran suna wanka don shirin zuwa makaranta,kuɗin abinci ya basu amma Zeenat ta ce"Ta ɗaura abinda zasuje da shi makaranta kamar dai yadda Mommyn su ke masu,wani daɗi yaji a ransa kuma ayau ya ƙara gane ƴa macce hutu ce,don inda basu iya ayyukan ba,da sai ya nemo mai dafa musu."Duk da hakan kuɗu ya basu don ya lura duk sun canja sunyi sukuku da su ba ƙarfin jiki da sukuni a tattare da su."Ƙara rarrashin su ya yi sannan ya wuce sashen sa,wayar Hajiya Halima ya gwada kira amma har yanzu bata zuwa wanda tun daren jiya yake nemanta baya samu,da tunanin ya ƙwanta har yanzun bai farka ba,su kuma yaran daman direba ke kai su makaranta sun wuce.Shiyasa har yanzu da rana tayi ba alamun motsin kowa a gidan."

***************Batayi mamakin yadda taji gidan tsit ba,don tana da tabbas akan yaran sunje makaranta,wataƙil uban baya nan ya fita shago shiyasa kanta tsaye ta nufi sashen Zillaziya. Falon ta shiga duk hargitse ba kowa,ɗakin ta nufa don duk a zatonta tana ɗakin mai gidan,sai da me?saman gado ta hangota a duƙunƙune cikin bargo,tana rawar sanyi in da ta ke ta dosa sai dai wani mugun warin tusar ciwo ya bugi hancinta da sauri tayi baya tana ajiyar zuciya.Toshe hancinta tayi ta ce"Zillaziya me ke faruwa? wannan tusa kamar ta aike?Da muryar ciwo ta ce"Hajiya ban san me ke min daɗi ba tunda ki ka barni jiya ban rutsa ba,bani da lafiya kuma rabona da Alhaji tun tafiyarki,amai da zazzaɓi ke damuna har ciwon ciki ga jiri!

Subhanallahi maza tashi muje asibiti aikam wagga tusa bata lafiya bace inji Hajiya Babbba tana ƙoƙarin fita daga ɗaki,jikin taga ta isa ta zuge gilas ta dinga zubda yawu.Wayar shi ta kira har ta tsinke ba'a ɗauka ba,koma kira tayi da sauri ya ɗauka yana gaidata,ta ce"Ɗan Inna kana ina?gani gida Hajiya.yanzu kana gida ciwo na neman kashe matar ka?wallahi ka kiyayi ɓacin raina...ka fito a kaita asibiti in ko ba na asibiti bane mu ziyarci mallam don daga ni baga banza ba,wataƙila ije muguwar matarka tayi mata don ta huce haushi.Daga nan ta kashe kiran.Bayi ya faɗa yay wanka ya wanke baki,jallabiya ya zubo ya fito nan ya sameshi suna jiransa Hajiya sai masifa ta ke masa akan yadda yake masifa da rayuwar Zillaziya.Shi kuma tun jiya haushinta yakw shiyasa bai nemeta ba, anan ya gane ya yi ƙusƙure dan haƙƙinsa ne ya ga ya iyalinsa ta tashi.Haƙuri ya dinga basu Hajiya Babba ɓacin uwa da uba da ƙazafi ba wanda batayiwa Haj Halima ba,har ya su ka isa asibiti tana faɗin daa hannunta a ciwon."

Likita su ka samo akai ma Zillaziya aune-aunen jini,da fitsari da me bayan wani lokaci aka gano tana da juna biyu,Bayan sun fito da ita akai ma Alhaji Bello da Hajiya Babba bayani tare da basu takardar magani,da irin abinda akeso taci ta sha da sauransu."Hajiya iya ƙarfinta ta rangaɗa guɗa har sau uku,sai da likita ya ce"Mama kin manta a asibiti ne!"Haba ɗannan asibiti maƙabarta ne,kabarni naji daɗina Allah ya kawo rabo,Janyo Zillaziya tayi ta ce"Sannu kinji Allah ya saukeki lafiya uwar magaji."Ta dubeshi ta ce Ɗan Inna halan bakaji me Likita ya ce ba?Najiya Hajiya Allah ya bata rayayye wato banjin daɗi ne shiyasa,Tsaki tayi ta ce"Likita ka duba ka ga me zata haifa?"Dariya yay ya ce"A'ah Mama ba yanzu ba,kuma ba lallai ko lokaci ya yi,mun faɗi a haifo abinda muke hasashe ba,Allah ne masani,daga nan yay sallama da Alhaji ya juya.

Ya fara tafiya kenan sai ga Alhaji ya zube saman kujerar da ke gurin da sauri Likita ya dawo,ya tallafo shi wanda tuni ya daina numfashi,Hajiya Hannu ta aza aka tana salati ta ce"Shi kenan ta koma ta kan shi,ta bada shi!tsakani na da ke Halima Allah ya isa.Zillaziya ciwonta ya isheta amma hankalinta ya tashi kar dai Alhajinta mutuwa ya yi?Shiyasa ita ma ta fashe da kuka!don bata shirya ya mutu tun yanzu ba,Hajiya ma kuka!ta ke tana kururuwa tare da tsinewa Halima."Gadon da aka kawo ne yasa su ka ƙara firgita har likitocin su ka aza shi zuwa ɗakin bayar da taimakon gaggawa."

Tirƙashi! Ƴan magana kance ana bikin duniya... Ku ci gaba da bibiyan littafin more comments more post

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 36/37

Su na gama ƙarin safe tayi wanka ta shirya tsaf,sai dai ta rasa ina zata dosa?Nasihar Maman su ta dawo mata sabuwa a rai" _Halima gashi dai Allah ya yi yau kinyi aure ina fatan ke da Bello mutu ka raba,nasiha ta gareki ita ce"ina son ko dani ko bani a duniya,ko da wasa karki kuskura ki gwada yaji,ki sani yin yaji ga macce rashin daraja ne,ki zama jajirtacciya jarumar a gidan ki,kowanne aure yana da ƙalubale duk macce da kika gani a gidan miji to tana zaune tana haɗiyar abubuwa da dama a ranta,don haka komai ɗaci da wuya da zafi kiyi tsaye gidanki a cikin iyalanki,ba zan hanaki zama tare dani ba amma idan zaki zo nafi so ki zo min da wata shaida mai ƙarfi,amma ba dai yaji ba don nasan kowa ba zai tsallake jarabawarsa ba..."_ajiyar zuciya ta sauke tare da goge ƙwallah!ya zatayi yanzu?Ba zata doshi garin su ba takarda ba,kodai ta koma ta karɓo sakinta kafin ta wuce?Kenan ta tabbata Bello baya sonta don tun safe ta buɗe wayarta ba kiransa wanda tayi tsammanin haka.Shigowar Lubabatu ɗakin ne ya dawo da ita hankalinta,wani ƙamshin sinadaran turaruka ya doki hancinta,kallonta tayi ta ce" Uwargidan Labaran ba dai wanka ba,gaskiya kinyi kyau kamar wacce zataje gasar nuna kyau."Inji Halima tana murmushi.

Lubabatu zama tayi kusa da ita taba faɗin "Tsiyar taki ta tashi ko Sadiya? don Allah muji da damuwar mu,gaskiya kinyi kyau don karki wai ba don kina ƙawata ba ne, ba kuma ina kushe Zuhra ba ne,amma ƙwatan kyaunki da dirinki Amaryarki bata kama ƙafa ba,Dariya Lubabatu tayi ta ce "Ai gwara Zuhra na da ƙiba da taki wannan Zillaziya feƙaƙƙa mai zubin ƴan karkara ko ajin ƴar aikin gidan ki bazata ɗauka ba.yanzu dai ya za'ayi ni da zakibi shawarata Sadiya ki zauna ko na mako ɗaya ne,idan har Abban su Zeenat ba nemeki sai ki wuce,ina tsoron Mama kin san halinta kaifi ɗaya ce,idan har ta fahimci abubuwan da ki ke ɓoye mata da irin cin ƙashin da ki ke a gidan ko na zinari ne zata hanaki dawowa,kuma na lura kina son mijinki.Ni kaina ba zan goyi bayan ki tafi ki bar ƴaƴan ki ba, don haka mu ƙara masa lokaci don Allah."

Ajiyar zuciya tayi,ta dubi Lubabatu ta ce"Tabbas zancenki dutsi amma ki sani yaji taƙi jinin ace ko matan yayyena sunyo yaji bare ni,shiyasa ma nake tunanin tunkarar gida son Bello da yarana ya hanani tsayawa na amshi takarda ta,da na amsa da yanzu ina da hujja,amma yanzu ba zamu shirya da Mama ba sai an sha fama kafin ta saurareni kinga ni duk abinda ake min bana faɗa mata bata san wace rayuwa nake fuskan ta ba."Sai dai zamana anan kamar da takura idan labaran ya dawo...karki damu duk ɗakunan gidan nan?ko wata ɗaya zaki gidan nan idan na so ba zai sani ba,saboda baya zama tunda ya auri Zuhra,ranar girkina da ya shigo ya ƙwana wayewar gari ya fita ko yanzu kinga ya ce"Baya gari."Nidai Allah na kaiwa kayana don haka ki zauna na wani lokaci.

To shi kenan, na gode ƙawata, Halima ta ce, tana kallon Lubabatu, kowa da abinda yake ji a ransa.

**************** Karima da Safara'u ne su ka shigo asibitin, kamar an jeho su.Inda Hajiya da Zillaziya su ke suka dosa guri tinjim da mutane ƙannan Hajiya Babba maza da mata kasancewar ita ce Babba a gidan su,ga abokan Alhaji Bello mutum biyu da sauran dangi.

Bayan sun gaisa Karima ta ke tambayar ya mai jiki?,)Hajiya ta ce"Ai da sauƙi nan tayi mata bayanin har da Zillaziya bata da lafiya, sun kawo ta asibitin ne, shi kuma sai ya faɗi. Amma Likitoci sun auna shi ance"Jinin sa ne yahau,anyi masa allura, da sauran abubuwan da su ka dace''Sosai Karima ta jajanta musu, don Zillaziya bata tsaya mata bayani ba, tana kuka ta kira ta ce"Alhaji ba lafiya su na asibitin mallam Aminu kano."Shiyasa bata san wainar da ake toyawa ba."Sun jima sosai a asibitin don har yanzu Alhaji bai farka ba,shiyasa su ka tashi,Zillaziya da ya ke taji dama kuma ta ɗan ci abincin da ƙanwar Hajiya,gwaggo larai ta kawo ta sha magani.Shiyasa taji ɗan dama rakiya tayiwa su Karima har harabar asibiti,nan ta zayyanewa Karima komai daga farko har ƙarshe,Dariya Karima tayi ta ce"Allah abin godiya wannan labari yay min daɗi,yanzu dai Halima bata gidan kuma kina ciki ko?"Murmushi tayi ta ce"Faɗa ki ƙara faɗa Mommah ai kakarmu ta yanke saƙa,nidai Allah yasa kar ya mutu tun yanzu don ina cikin fargaba...Ki ƙwantar da hankalinki ai zai tashi,baƙuncikin rabuwa da baƙar matarshi ne ke tuyar zuciyarsa,na ɗan lokaci ne,yanzu ma wurin mallam matashi zanje a cire masa cutar nan cikin ranshi ya manta da ita."Tafawa sukayi Zillaziya ta ce"Na dai godewa Allah da yabani ke,amatsayin uwa maba ɗa mammah,baki da burin da ya wuce ki sani farin ciki ina alfahari da ke uwata."Sha kuruminki uwar ɗan Baba da sannu zaki zama tauraruwa mai wutsiya a gidan Bello,waɗancan gayyar na ayyah duk zan miki maganin su,daga Babbar har ƙananun...Wai Hajiya Babbba ai ni na gama da shafinta na rufe Mammah da naji dama zaki ji labarinta ya sauya kala."Safara'u wani Haushi ya cikata yadda yayarta da mammanta su ka ɗauki duniya wurin zama shi ke ƙara tunzura shiyasa daga inda ta ke tsaye ɗan nesa dasu ta ce"Mamma na gaji da tsayuwa mu tafi!Harara Zillaziya ta watsa mata ta ce"Munafuka bayan kin kashe kunne kina sauraron sirrin uwa da ƴa kin cika cikinki zaki wani cw kuje...tsaki tayi ta ce"Mommah zamuyi waya don na kula ƙwailar ƴarki mu ta ke sauraro kinsan mutum abin tsoro."Karima ta dubeta amma ke san dai Safara'u ba zata faɗawa kowa ba,ba zata cutar da ke ba,ba kuma zata iya fallasa mu ba.Daga nan ta ce Safara'u mu tafi,wucewa tayi Zillaziya har bangazarta,Murmushi tayi mata ta ce"Allah ya baki lafiya Zillaziya,ya baiwa Alhaji ya kare Anty Halima da ƴaƴanta daga baƙar aniyar ku."Karima bata ji ba, don har ta wuce,Zillaziya juyowa tayi tana dariya ta ce "Komai baƙin cikin tanda sai ɓun ci waina."Idan har wata gareki kije ki faɗa musu abin da kikaji shashasha marar kishin kai,daga nan tayi tafiyanta,Safara'u fatan shiriya tayi musu sannan ta cimma Mamma suka tafi."Tana komawa inda su Hajiya Babba ta samu har Alhaji ya farka,ya ce"A sallame shi nan dai aka duba shi,komai da sauƙi aka sallamo su suka tattaro su ka dawo gida.Hajiya Babba ta ce"Zata ci gaba da zama gidan duba da Zillaziya ba lafiya,gashi ba masu aiki shiyasa tasa ƴar aikinta ta dawo gidan har Alhaji da Zillaziya suji sauƙi."

***********RANAR LARABA rana ce ta nasiha...

Ya kamata kiji tsoron Allah Malama Basira,ki sani sa'in sa da mijinki ba abu ne mai kyau ba,saboda zaki iya faɗan abinda bai kamata ba,ko kuma shi ya aikata abinda daga ke har shi zaku zo daga baya kuna dana sani.Da fatan kin fahimta ?Inji malama juwariyya(Ammi) a lokacin da ta ke amsa tambayoyin ɗalibanta.

Basira ta ce"Na'am malama na fahimta kuma in sha Allah zsn kiyaye.Daga can gefe wata mata ta ce"Wato malama wataran ko kaso ka danne sai su faɗa maka abinda baka iya haƙuri,Ajin ya haɗe da hayaniya kowa na faɗin Albarkacin bakinsa akan Halayen maza Ayau.Murmushi tayi ta ce"To ya isa wato dai Basira ta taɓo muku inda ke muku ƙyaiƙayi,ai baku san wani abu ba,muddin namiji ya ran macce ya ɓaci to a lokacin zai ƙara tunzura ta,saboda mazan da su na da bambanci dana yanzu,Ada idan iyayen mu maza sun ga ran iyayen mu mata ya ɓaci,sun kanyi ƙoƙari su rarrashe su har su huce,amma na yanzu sai dai haƙuri ya kamata ku gane yanzu fa lalacewar mutanen zamani yasa komai ya taɓarɓare sai addu'a,don haka zancen faɗa da cacar baki ba naki bane,ki riƙe addu'a ki kama sana'a sannan ki ci gaba da haƙuri shi ne mafita a rayuwar aure."Idan kuma kin biye ta namiji to ƙarshenki ciwon zuciya da hawan jini,masana ilimin sanin zamantakewar aure sun ce"Yayin da ma'aurata ke mayarwa junansu martani, ma'ana idan suna faɗa,to macce ke ƙwaruwan namiji don macce zata iya fidda kalma dubu goma sha taƙwas yayin da namiji iyakaci ya fidda kalma dubu goma sha huɗu,kun ga anan mata ne zasu ɗaukarwa kansu zunubi matane zasu iya fidda abubuwan ashsha,don haka a kiyaye.

A ganina duk maccen kamila ta girki a duniya bata da burin da ya wuce abu uku,na ɗaya ta samu Uba nagari,na biyu ta samu miji na gari,na uku ta samu ɗa na gari,don duk ta rasa ɗaya zata tozarta,Idan uba ya aurar da ke ga miji wataran zaki dawo hannun ƴaƴanki."Anan idan kin rasa ɗaya kin samu matsala amma kuma idan kinyiwa ɗa tarbiya zai iya maye maki gurbin uba da miji,idan har ɗanki ko ƴarki sun wayi gari a gabansu kina faɗi in faɗi da ubansu to ya kenan?

Tsit sukayi tamkar ruwa ya cisu ,ta ce"Baku bani amsa ba?Daga gefe wata Babbar mata ta ce"Malama daga wannan lokacin ai komai ya lalace."

To kun gani kun ba kanku amsa da kan ku,don haka ai ta haƙuri mata,a daure neman lahira sai da jajircewa Allah ya bamu zaman lafiya wanda su ke cikin matsaya ya yaye masu, mata masu matsala da mazajensu ko dangin miji da sauran ya daidaita su.

Ameen ƴan ajin su ka ce dukan su.wanda tuni jikin su yay sanyi musamman Basira da tayi tambayar akan yadda idan suna faɗa mijinta da zarar ya faɗi sai ta bashi amsa,wai tana da laifi ko bata laifi?

Wannan tattaunawa ba Ammi da ɗalibanta kaɗai zasu amsa ba har ku fans wannan matsala ana samunta da dama shin kuna ganin dai-dai ne?Macce na mayarwa mijinta martani me ku ke ganin zai faru?wane hasashe ku keyi akai?

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE😍 [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 38/39

*WANNAN BABI KYAUTA NE GA; KEBBI STATE ONLINE WRITERS(KESOW) ALLAH YA ƘARA HAƊA KAN MU,YA KAWO CI GABA MAI ƊAUREWA A JIHAR MU,YA ƘARA BASIRA,HAZAƘA DA FIKRA,AMEEN.*

Wayar ta ke dannawa kira ba adadi, amma har yanzu ba'a ɗaga ba,dab da kiran ya tsinke aka ɗauka.Sai dai daga gefen ta shiru tayi don ba kasafai ta ke amsa kiran sabon layi ba,ko yanzun ganin an dameta da kira ya ta ɗauka. Assalamu Alaikum,Mommy... Zeenat ce.

Da sauri ta ce"Wa alaiki salam Zeenatu na ya ku ke? Ya su Saudat,Khaleesat,Sareena,Mamu,Mima,da Mami dasu Bilkeesu duk kuna lafiya?"Mommy duk muna nan amma rashin ki yasa mun dawo kamar marasa lafiya,don Allah ki dawo garemu...Kukan da ya ƙwace Zeenat ne yasa tayi shiru tana rusa kuka!

Wata jarumta ta aro, duk da zuciyarta ta karaya, jin yadda gudun jininta ke kuka, kuma irin na damuwan nan,Shiyasa ta ce"Zeenat kuyi haƙuri ni kaina ba don son raina zan barku ba,amma ya zanyi?a gaban ku Kakar ku ta ce"Sai na fita,ina so ku cigaba da addu'a kuma ku ƙwantar da hankalin ku zan dawo gareku kinji ƴar Albarka."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull