Kenza eBookz

Uwar y'an mata complete - Chapter 10

Uwar y'an mata complete - Chapter 10

Uwar y'an mata complete Chapter 10: Uwar y'an mata complete Chapter 10. Momy kinga yanzu hakan tun jiya Hajiya Babba ta dawo gidan nan,duk da mai aikinta…

4,374 words

Momy kinga yanzu hakan tun jiya Hajiya Babba ta dawo gidan nan,duk da mai aikinta ta dafa abinci amma kaɗan ta ce"A bamu, sai da na shiga madafa, na ƙara dafa mana wani sannan ya ishemu.Momy muna cikin wani hali gamu nan a takure don Hajiya ku fita mukayi daga duka sai zagi don Allah idan ba zaki dawo ba,ki taimaka ki zo ki tafi damu...Zeenat, Hajiya ta dawo gidan da zama ne?A 'ah Momy naji tana faɗin zata zauna na wani lokaci ne,saboda Daddy ba lafiya jiya har asibiti aka ƙwantar da shi,Anty Zillaziya ma bata jin daɗi." inji Zeenat tana shace majina muryarta na rawa.

Allah ya basu lafiya,inji Hajiya Halima a lokacin zuciyarta na suya, don ita kaɗai ta san irin raɗaɗin da ta ke ji,Yanzu ina ki ka samu waya?"Mommy ta mai gadi ce,na sayi kati ma kira ki,gobe idan mun dawo makaranta zan kiraki in ba Sareena saboda kullum sai tayi mana Kuka tana kiranki."Wasu Hawaye masu ɗumi ta goge ta ce"To shi kenan Zeenat ki duba ɗakina a cikin dorowar gado aƙwai kuɗi,ki ɗiba ku dinga sayen abinda kuke so amma banda almubazzaranci sannan aƙwai komai a madafa da ke da Bilkisu,Khaleesat,Hajaru,duk zaku iya abinci idan yau wannan yay gobe da jibi wani ya yi kinji?To Mommy" Ai na raba masu aiki,daga sashen mu na ki kullum sai an share da bayi an wanke a goge kamar kina nan inji Zeenat...Ta buɗe baki tayi magana sai taji dif Zeenat ta kashe wayar,Ajiyar zuciya ta sauke tana dubi gilashin wayar don ta fahimci aƙwai dalilin da yasa Zeenat ta datse kiran,shiyasa batayi gigin kiran layin ba,kanta ta kife a gwuiwa ta dinga kuka,a ƙarshe bayi ta faɗa ta ɗauro Alwala gabas ta fuskanta ta dinga jera nafilfili sannan ta duƙufa da karatun maganin komai wato"Alƙur'ani mai girma"wani sanyi tayi ranta salati,istigafari,hailala tayi tare da addu'oin samun mafita a gurin wanda ake kaiwa koke kuma ya share hawayen bayin sa "Allah (SWT)."

Zeenat jin kiran da Hajiya Babba ke mata ne, yasa tayi sauri kashe wayar, ta baiwa mai gadi tana godiya, sannan ta shiga falon da sauri. Tana shiga Hajiya ta wanketa da mari ta ce"Da gidan uban wa ki ka fito tun ɗazu baki falon nan?"A rikice ta ce Hajiya ina harabar gidan wurin dabi zaune."Tsaki Hajiya tayi ta ce"Ki wuce sashen Zillaziya ki mata shara da goge-goge,To Zeenat ta ce"Ƙwallah na mata sintiri a fuska."Hajiya gyara zamanta tayi su ka ci gaba da kallo ita da mai aikinta,Zeenat ɗakin su ta shiga tana rusa kuka,Mamu ta ce "Yaya lafiya?Labarin kiran da tayiwa Mommy da saƙon da ta bata garesu,ta faɗa musu, har kawowa marin da Hajiya tayi mata,Mamu cizon yatsa tayi ta ce"Kiyi haƙuri na san abinda zanyi."Me zakiyi Mamu meyasa kin cika rigima?Kin san Halin nan naki ne Mommy bata so Inji Saudat."

Zeenat ta ce"Addu'a ita ce matakin da zamu ɗauka,don haka kowa ya dinga yiwa Mommy da Daddy Addu'ah,daga nan ta fita zuwa Sashen Anty Zillaziya."

Alhaji Bello yana sashen sa yana fama da jiki,bai san abubuwan da ake gidan ba,saboda yana sama suna ƙasa don yaran sun fi hawa sama sashen Mommyn su idan tana can,yanzu ko bata nan baiji motsin kowa ba, Cikin sa'a wayar da ya ke kira, ta shiga da sallama aka ɗauka.

Amsawa ya yi sannan su ka gaisa,sai kuma kowa yay shiru,Ya ce"Halima nayi ta kiran wayarki a kashe,shi ne ko ki nemeni? yanzu hakan gani ƙwance ba lafiya,don Allah karki ɗauki abin da zafi!kinga ba laifi na bane,kuma naji daɗin yadda ki ka wuce ba tare da kin tsaya amsar baƙar takarda ba haƙiƙa kina ɗinbim hikima,Halima ki ƙara haƙuri,kuma ki ba Mama haƙuri, da yardar Allah zan shawo kan matsalar da naji sauƙi,naso na kirata amma ban san ya zata ɗauki lamarin ba,da naso ki tafi gidan Abokina Alhaji Hashim idan komai ya lafa ki dawo...Kukan da ta ke haɗiyewa ne ya suɓuce mata jin yadda yake magana a wahalce daga ji yana cikin damuwa,ani tausayin sa dana ƴaƴanta su ka lullube marfin zuciyarta yayin da wani ƙaton abu kamar dutsi ya danne ƙasan zuciyarta...Don Allah ki daina kuka!Nima sai kisani nayi kukan sanin kanki ne bana iya dake ɓacin raina,nan ta ke zanji zuciyata ta karye kiyi shiru ki saurareni,kukan da ta ke rerawa ne yasa shi fashewa da kukan,sun ɗauki tsawon lokaci suna darzar kuka,da waya a maƙale a kunnen su,sai can ta ce"Kar ka kira Mama,don ban tafi can ba,ina gidan ƙawata Lubabatu..."Ajiyar zuciya yay ya ce"Zan zo gobe don yanzu nan Likita zai zo ya dubani kuma na san zan sha maganin bacci,ba don haka ba da yanzun nan zan zo Sadiya,Da dasasshiyar murya ta ce "To...shi kenan Allah ya baka lafiya."Ameen ya ce"Dai dai shigowar Hajiya Babba da sauri ya kashe wayar ya lunƙume cikin bargo,Ɗan Inna...Ɗan Inna ya jikin?ta ce tana ƙoƙarin taɓa shi,jin shiru yasa ta ce"Yau kam kasha bacci,sauƙi ya samu kenan,to Allah ya baka lafiya,Allah ya tashi kafaɗunka "Uban magaji."Daga nan ta fice daga ɗakin ta rufo masa ƙofa."Jin ta fita yasa ya sauke numfashi saƙo ya tura ma Halima da an juma da dare zai kira,sannan ya koma ya ƙwanta yana tunanin mafita."

Tunda ta ga saƙon shi,ta fahimci Hajiya Babba ce,kusa da shi shiyasa tayi lamo saman gadon tana tunanin wannan ƙaddarar ta su,tana son mijinta yana sonta, ga ƴaƴan su barkallah kyawawa son kowa ƙin wanda ya rasa,amma Hajiya na neman masu katangar ƙarfe."Ta jima ɗakin sannan ta fita falo inda ta samu Lubabatu na kallo,Ta ce Sadiya har kin tashi daga bacci?Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo ta ce "Eh"Lubabatu ta ce "Ga abinci can a dining na gama tun ɗazu har naci,sai kije ki ci ko?"Allah sarki Lubabatu sannu da aiki ai ban san kin ɗaura sanwa ba,da na fito na tayaki,tun ɗazu ma na tashi daga bacci,Bakomai Sadiya ina ke ina gurki kiji dai damuwarki kawai Allah yay mana jagora yay mana mafita mafi Alheri,Ameen ya rabbi,Na gode Lubabatu kin wuce Aminiya agareni ke ƴar uwa ce,ba don ke ba da ban san a ina zan saka raina da kaina ba a daren jiya."

Bayan ta gama shara da goge ciki da wajen sashen na Zillaziya,wanda duk ya lalace da datti,ko ba'a faɗa ba ganin wurin zai tabbatar da ƙazantar mai sashen,Zeenat ce ta fito a gajiye kugunta har ya riƙe, saboda duƙin da tayi da darzar bayi.Har zata wuce Zillaziya wacce ta cika bakinta taf da yawu,tayi ma Zeenat alamar ta zo,zuwa tayi ta ce"Gani"Da yawun a baki ta ce"Danna min ƙafafuna ciwo su ke min,wasu hawaye ya zubo ma ta,don ƙugunta wani irin ciwo ya ke mata,amma ta san da zarar tayi gaddama Anty Zillaziya baki buɗe zata faɗawa Hajiya Babba.Shiyasa ra durƙusa ta dinga mata tausa sai da Zillaziya taji don kanta ta gaji sannan ta sallami Zeenat.

Falon Zillaziya ta fita ta zauna inda su Hajiya Babba sai zuba iya yi take ta ci wannan taci wancan sai wash!kash!wayyo take a duk dogon motsin da zatayi, Hajiya da Mai aiki sai faman sannu su ke mata,ana tarairayarta uwar magaji menene? me ki ke so sannu ko?da sauran su. Mamu fitowa tayi ta gaida su,bukiti da tsintsiya riƙe a hannunta,Hajiya ta ce"Ke taƙwara ina zaki rasa kunya ɓeran masallaci?Murmushi Mamu tayi ta ce"Hajiya ɗakin da ki ka sauƙa zanje in share miki inyi turare in kuma goge,naga Yaya Zeenat tayiwa Anty Amarya."Kallon sama da ƙasa Hajiya tayi mata ta ce"Su Maryamu yau da abin kirki,nifa shiyasa ke kaɗai nake jin wannan araina ko ke don albarkacin sunana ne,jinin mu ya haɗu,shegiyar gora amma kin rashin mutuncinki ya tashi ki ta baza min shi,ungo wayata kisa min caji daga can...Amsa Mamu tayi tana kallo Zillaya wadda ke zabga mata harara ta ke.Shu'umin murmushi Mamu tayi sannan ta wuce."

Kasancewar aƙwai ɗakuna a gidan da komai acikin su,shiyasa Hajiya ta tare ɗaya daga cikin masu gadaje mai kyau,mai aikinta kuma ɗaya ɗakin baƙi. Shiga mamu tayi ta gyare ɗakin tsaf har da turare da komai sannan ta fita ta rufo ƙofa,dawowa tayi falon ƙasa ta zauna gefen Hajiya su na kallo."Likita ne ya shigo bayan sun gaisa ya tambaya ya masu jiki?Hajiya ta ce"Da sauƙi nan ya ƙara yiwa Zillaziya sannu,sannan ya shiga sashen Alhaji ya sameshi a farke ba kamar yadda Hajiya ta ce" Bacci yakeyi"ya dubashi sosai jiki ya yi sauƙi sai da jinin yaƙi sauƙa,nan Likita ya tambayi Alhaji akan damuwar sa,don ita ke sa shi tunani,yanayin da dogon nazarin ke haifar masa da hauhawar jinin,Alhaji Bello baiyi ƙasa a gwuiwa ba,ya faɗawa Likita damuwar sa,jim na wani lokaci Likita ya yi,sannan ya ce "Alhaji ya ƙwanta yay kamar ya sheme,nan ya fita ya kirawo Hajiya Babba da sassarfa ta shigo ɗakin tana faɗin Likita in jin dai ba jikin ba ne,Alhaji ko kamar ɗan wasa ya dinga jan numfashi yana kakari,Likita ya dubeta da damuwa ya ce"Mama aƙwai matsala!jininAlhaji ya ƙara hawa,kiyi haƙuri idan har baku taimaka ba ina ga ya kusa rasa ranshi,na tambaye shi meye damuwar da yasa aransa wacce ke barazanar haifar masa da bugun zuciya na ƙarshe!amma yaƙi ya faɗa min watakil ke zai faɗa miki kin tambayi shi muji ko za'a iya shawo kan matsalar don rayuwar na ɗauke da barazana a halin yanzu."Shure-shure Alhaji ya fara ya juye ido da fidda harshe...Da Likita da Hajiya su na rige-rigen isa gareshi,wani irin Kuka!Hajiya Babba ta ƙwamtsa ta ce"Mutuwa don Allah ki tsaya shi kaɗai gareni Ɗan Inna tashi na san matsalar akan Halima yau ba sai gobe ba,garin su zani in dawo ma da ita karka mutu,Likita ya ce"Alhamdulillah ita wannan Halima ita ce damuwar Mama?Likita ita ce"Baƙar giwa nidai ta zame min ciwon ido,amma babu komi na yadda ta dawo in dai zai rayu."Riƙe hannun shi tayi ta ce"Ɗan Inna tashi na yadda uwar ƴan maata ta dawo ɗakin ta ai vaka saketa ba,to na janye duk abubuwan da nace wallahi..."Wani ajiyar zuciya ya sauke tare da yi ma Likita inkiya da ido ɗaya,a lokacin Hajiya ta kife ga gado tana kuka,Likita ya ce"Mama kinga na duba jinin ya fara sauka ma,har ya samu bacci mu fita,kar ya tashi kiyi haƙuri ki daina kuka."A Hanyar fita daga ɗakin ta ce"Dole in kuka Likita Ɗan Inna kaɗai gareni a duniya,ga muguwar matarsa ta zame mashi ƙarfe ƙafa."Da haka su ka isa falon Likita ya wuce tana masa godiya tana share ƙwallah,bata ga Mamu ba don ta koma inda ƴan uwanta,shiyasa ta dinga zagin Hajiya Halima tana basu labarin duk yadda akayi yanzu,kamar saukar baƙar duma haka Zillaziya taji a ranta,mai aikin ko daɗi taji a zuciyarta don tana tausayin yaran,kuma tana ganin darajar Hajiya Halima.

Haushin da ta ke yadda Uwar ƴan mata zata dawo da wuri hakan,tashi tayi fuuuu ta wuce,kallon ta Hajiya Babba tayi da mamaki ta ce"Eyye samun wuri tusar asuba...kinga wai kishi ta ke kamar ba ta zo ta sameta ba a gidan,Idan banda rashin godiyar Allah irin na ɗan yau abinda ita ce nike so,ni Halima dowawarta ai abin azo ai min jaje ne,a tayani alhini maƙiyata zata dawo guribinta inda naso na rabata har abada,mai aiki ta ce"sai haƙuri Hajjajo kin san mai ciki zuciyarta a baki ta ke."Haka ne kuma, ni na shiga ciki, inji Hajiya,A fito lafiya mai aikin tayi mata.

Mamu ta kasa kunne tana jiran taji labarin ya sauya,shiyasa tayi wanka ta canja kaya,ta feshe jikinta da turare,cingam ta kaɗa a bakinta tana kallo,Zeenat ko ƙwana wahala takeyi tunda ta dawo tayi wanka,sauran ko wasu kallo wasu karatun da ayyukan da aka basu daga makaranta sukeyi."Buɗe ɗakin tayi wani ƙamshi da sanyin Ac ya bugi hancinta,ta ce" Jaaa'iraaaa...bata ƙarasa ba tayi wani suluuu,santsin layals da ruwan omo ya jata,wata hajijiya ta ɗauke sai ji kai tiiiiiffff...sai ga Hajiya a ƙasa ta dafshe baki ya fashe sai jini,duk da jirin da ke ɗibanta ɗakin na mata yawo bai hanata ƙwallara ƙara ba ta ce"Wayyo!Ni meri na ga bone,da gudu mai aikin ta shigo tana Hajiya lafiyaaa...kafin ta ƙarasa sulɓin ya jata tayi suuuluuu ta farma Hajiya a ƙafa,wani cizon wulaƙanci Hajiya ta girtsa ma mai aiki a kafaɗa,Wayyo!Hajiya kiyi haƙuri ta ce"Tare da hankaɗe Hajiya gefe wacce ƙugu da kafarta su ka riƙe,Kuka Hajiya ta ke tana faɗin" shi kenan na ƙarye ɗiyar muguwa wacce tayi gadon mugunta mai gyaran ƙaddara ta halani."da ƙyar mai aikin ta samu ta tashi tana ɗingishi ta janye Hajiya Babba ta goge wurin sannan ta fito falo tana kiran yaran ta faɗa musu haka ta sanarda Zillaziya."

Mamu dariya tayi har da kifewa ta ce"Ai na faɗa muku zan ɗauki mataki,shiga ɗakin sukayi suna ma Hajiya sannu, kuka take tana zagin su tare da ɗebewa shara da mofin ɗin Mamu Albarka.Haƙuri suke bata Mamu ta ce"Kiyi haƙuri Hajiya ban san basu gogu ba,inda naga da ruwan omon ai da zan goge...Shigowar Zillaziya yasa tayi shiru a zuciyarta tana kitsa saura ita,wani daɗi ya lulluɓe Zillaziya ganin ƙafar Hajiya da Baki sunyi suntum,har da murmushinta a zuciya tana fatan Allah yasa Hajiya tayi kariyar da ba zata iya ko da tafiya ba.Amma a fili ɓata rai tayi tana nuna damuwarta har da yiwa Mamu faɗa,sai sannu take jera ma Hajiya wacce zuwa yanzu ita kaɗai ta san irin azabar da ta ke ji,Ƙannanta ta kira a waya ta faɗa musu,nan ta ke sukace suna zuwa yanzun tare da duba targaɗe."Daga nan korar yaran tayi daga ɗakin tana musu zagin uwa da uwar uwa."

Zeenat faɗa tayi ma Mamu sosai akan abinda ta aikata,wanda bai dace don ko ba komai Hajiya kakarsu ce kuma uwa ga uban su,dole suyi mata biyayya tunda ko uban yana mata,Mamu tuɓure baki tayi tana falin to naji Yaya ba zan sake ba,amma cikin ranta Zillaziya ce."

More typing more comments

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 40/41

Tanko da Isuhu ne su ka zo da mai gyaran targyaɗe,Sun sami Hajiya Babba na ƙwallah,saboda ƙafarta ke ma ta zillah,ga bakinta yay suntum ya sundule gwanin dariya da tausayi, mai gyaran ya duƙufa da manmatsa ƙafar Hajiya sai faɗin ta ke"Wayyo!Tanko kuce masa yay a hankali."Dariya Isuhu ya yi ya ce"Hajiya kinga bakin ki da ki ka faɗi Wayyo!kamar kutikuti...Haba "Meyasa baka da lissafi?"Inji Tanko a fusace ko da ya dubi Hajiya kallon baki yay da sauri shi ma ya ƙumshe dariyar sa."Hajiya takaici da zafi ya dameta shiyasa tayi musu banza."Sosai mai gyaran ya duba tsagewar ƙashi ne,da yake ya ƙwarai sosai gurin aikinsa,nan ta ke ya gyare tsagewar ƙashin yay ma Hajiya ɗauri. Bayan ya kammala maganin shafawa,ya bata tare da mata samun lafiya ya ce"Bayan ƙwana biyu zai dawo ya duba,Sallamar shi Hajiya tayi ya wuce daga nan ta fara zagin su Isuhu da Tanko.Haƙuri su ka bata sannan suka wuce,inda mai aikin ke zaune a gefenta tana lura da ita.

Zillaziya na komawa sashen ta, Kirama ta kira a waya ta shaida mata duk abubuwan da ke faruwa,Haushi taji a ranta domin ga ƙoshi ga ƙwanan yunwa,Amma ƙwantarwa Zillaziya da hankali tayi inda ta shaida mata zata shigo duba Hajiya,daga nan aƙwai ƙullin da Malam Matashi ya bata.Ta ƙara da cewa"Ki barsu duk zasu yabawa Aya zaƙinta,ita kuma Hajiya yanzu ta fara gani,Allah yasa ƙafar ta ruɓe."Ajiyar zuciya Zillaziya tayi tare da lumshe ido,wani sanyi ya ratsa zuciyarta,Ta ce "Mommah na gode,sai kin zo."Karki damu Uwar ɗan Baba."Inji Karima

Tana gama wayan da Mommah,ɗakin Hajiya Babba ta shiga ta sameta ƙwance duk a dabaibaye ƙafa da karan ɗauri.Daɗi taji aranta ta zauna da damuwa ta ce"Ayyah!Hajiyata Allah ya baki lafiya,yanzu faɗuwar nan har ta kai ga kariya...Mai aikin ta ce"A'ah Amarya tsagewar ƙashi ne,ba kariya ba."Murna ta koma ciki sai ta dubi gefen su ta watsar ta ce"Allah ya ba da lafiya."Hajiya goge ƙwallah kawai ta ke, don bakinta yay mata nauyi ko magana bata iyawa."

Alhaji Bello wanka yay ya shirya a cikin shiga ta alfarma,don ya shiryawa zuwa ɗaukar uwar gidansa,fitowa ya yi inda Zillaziya ya nufa ya samu bata nan,falon ma ba kowa,ɗakin da Hajiya Babba ta ke ya nufa,a lokacin da yay ido huɗu da ita, hankalinsa ya tashi da sauri ya ƙarasa yana tambaya meke faruwa?Zillaziya da karaɗi ta labarta mata abinda ke faruwa,tana danganta shi da Mamu ce sanadi."Sannu ya dinga jerawa Hajiya da kai ta dinga amsawa,a gefe Zillaziya kutsa kanta tayi a cinyoyinta ta dariyar bakin wanda ya koma kamar an buga baranda.

Ya ce"Haba!Zillaziya ina cikin gidan nan HAJIYATA ta faɗi ba zakije ki tasoni ba?Ai wannan sakaci ne,har akai ga mata ɗauri ban da labari...Tsaki yay ya zauna gefenta yana duba ƙafar,Hajiya riƙe masa hannu tayi,janye hannun ya yi,tare da mata sannu yana ci gaba da faɗa akan rashin sanar da shi da ba'ayi ba.

Murguɗa baki tayi ta ce"Haba Alhajina meyasa zaka sani gaba kana min masifa?Hajiya fa ta ce"Kar a tasheka don Likita ya ce"Kana buƙatar hutu.Shiyasa ba'a faɗa ma,yanzu kuma gani ya kori ji ai da ka zo ka gani ya wadatar...Tashi tsaye yay ya ce"Hajiya ni zan fita sai na dawo."

Daga nan bai zame ko'ina ba,sai gidan Lubabatu, a ƙofar gidan ya tsaya tare da danna mata kira,ɗauka tayi nan ya shaida mata yana ƙofar gidan,da yake tayiwa Lubabatu bayanin komai dangane da maganar su da Alhaji Bello,kuma taji daɗi sosai tare da masu fatan alheri. Bayani tayi ma Lubabatu Alhajin ya zo,daman ta shirya tsaf shiyasa sukayi banƙwana da ƙawarta ta fito ta sameshi,ganinta ya haifar masa da wani nutsuwa a ransa,ido ya zuba mata ƴar caras da ita,kamar ba matar aure ba don ko makaho ya laluba ya san Hajiya Halima ta isa ta kowanne fanni. Inda motar ta dosa,buɗe mata marfin motar ya yi ta shiga tare da jefa aƙwatinta baya,gaida shi tayi a ladabce tana murmushi,amsawa yay tare da jifanta da wani kallo kana ya tada injin mota,suna tafiya suna fira jefi ita kam a ranta ta ƙosa,taje taga ƴaƴanta.

Lokacin da mai gadi ya buɗe gidan idonsa ya yi masa tozali,da Hajiya Halima a gaban mota,Tsalle ya yi tare da dubin gabas ya godewa Allah don ya san daren yau sai ya ci abinci,yana rufe ƙofar,da gudu ya isa gurinsu,a lokacin har sun fito,har ƙasa ya kai yana ƙwasar gaisuwa ya ce"Hajiya haske ginshiƴin gida an dawo lafiya,yau kam sai naci na ƙoshi inuwa mai ba da sanyi ta dawo,ai "Hajiya har ciwon ulcer ya kamani,yanzu hakan sai inji hanjina na ƙuna..."To ɗan dirama ungo aƙwati shiga dashi inji Alhaji Bello yana dariya."Hajiya Halima ma murmushi tayi tana faɗin "Allah ya kyauta."Yana shiga falon ya dinga kiran Zeenatu,Mamu uwar masu gida,Sareena autar uwargidan rangida duk kufito haske maganin duhu ta dawo,ku zo ga Mommyn ku uwa ɗaya tamkar dubu."Zeenat da ke madafa tana dafa musu taliya da sauri ta fito falon,ganin aƙwatin Mommymn su yasa ta gasgata mai gadi...kafin ta ce"Komai sa ga su da gudunsu suna faɗin Yaya Zeenat"Ina momyn?Me ku ke ci na baka na zuba...ganin sun shigo falon yasa yay shiru yana ƙoƙarin fita,da gudu sukayi kanta dukan su suka rungumeta tare da mata oyoyo,wani daɗi taji a ranta tare da sauke ajiyar zuciya,tabbas ƴaƴa rahama ne ta faɗi a ranta.A fili kuma sai murmushi ta ke wanda a ƙarshensa ya dawo hawaye,duk sun riƙeta ko tafiya sun hanata,Alhaji ƙwallah ya goge na tausayin yaran,Ya ce" to ku shiga daga ciki mana."Ta ce"Ayshine sun wani riƙeni kamar ɓat zanyi,Sareena ta ce"Mommy gani nake kamar komawa zakiyi ki barmu Hajiya na dukan mu tana zagin mu da Anty Zillaziya...Ya isa haka autana ba gani ba,ai duk wanda aka daka laifi ya yi,na san ku da rashin ji."Shiru Alhaji Bello ya yi don shi bai san azabar da Hajiya da Zillaziya suke ma yaran ba,duban su ya yi ya ce"Wallahi Halima ban san abinda ya ke faruwa ba,kar kiga ban riƙe maki amanar da ki ka bani ba!Mamu juya ido tayi ta ce"Daddy da kasan irin aikin da mukeyi ko mai aiki batayi musamman su Yaya don ni wallahi ba wanda ya isa ya ci amanta in ƙyaleshi,nan ta labarta masa komai da ke faruwa."Duk da Hajiya Halima na harararta baisa tayi shiru ba sai da ta kai aya.Da damuwa ya ce "Ke Zeenat meyasa baku sanarda ni ba?Sai aita wahaldda ku baku faɗi min ba?Ko ance muku matsayin ku ɗaya da masu aikatau?Kayi haƙuri Daddy na ga ko kai Hajiya ta baiwa umurni zakayi bare mu ƴaƴanka shiyasa mukeyi don umurnin daga Hajiya ya ke fitowa ba gurin Anty Zillaziya ba.Inji Zeenat tana zubda hawaye.

Yaji daɗin maganarta, kuma ya yaba, da kaifin hankalinta da basirarta,ya ce"To na gode kuyi haƙuri kunji?su kace to"Daddy ai mu tunda farincikin ɓu ta dawo ba mu da damuwa."Wasu hawaye masu ɗumi su ka zubo ta a lokacin da ta dubi Alhajin da yaran duk sun zagbe sun rame a cikin ƙwana biyu,duk da kasancewar ita ta ɗan rame amma tafi su dama,aƙwatin su ka ɗauka su ka nufi sashen Mommy nan su ka hau gyare-gyare har su turaren yayin da ita da Alhaji su ka shiga ɗakin Hajiya Babba don tun a mota ya faɗa mata,abinda ya faru da ita.wani faɗuwar gaba ya risketa a lokacin da su ka shiga ɗakin,yana gaba tana bin shi a baya,ganin su yasa mai aiki rusunawa ta gaida su sannan ta fita,Zillaziya a kiɗime ta tashi daga gefen Hajiya tana kallon su,da sanyin murya Hajiya Halima ta gaida Hajiya Babbba tare da mata ya jiki?Kawar da kanta tayi gefen tana sharar ƙwallah don bata ƙaunar ta sake yin ko ido biyu da Halima.Alhaji ya ce"Hajiya ga Halima nan na dawo ita,don Allah ai haƙuri da komai,tana miki ya jiki,ido sharaf da hawaye ta harare shi tare da masa alamar Halima ta fita,Zillaziya ta ce"Uwar ƴan mata da ke Hajiya ke magana ta ce"ki fita bata son ganin ki...wani yunƙurin amai tayi tare da toshe hanci,ta ce"don Allah ki fita wannan warin turaren ne bana so yana tasae min da zuciya,ko kina baƙin ciki da cikin na Magaji?Da sauri ta nufi bayi tana ƙaƙulo amai,Allah ya baku lafiya Hajiya Halima ta ce"sannan ta fita."Alhaji faɗa ya ringa yiwa Zillaziya daga bayi ta dinga bashi amsa a fusace ya fice daga ɗakin,Hajiya Halima ya samu ya bata haƙuri akan abinda sukayi mata.Buɗar bakinta ta ce"Kar ka damu mijina nifa kasan banda riƙo don har na manta,idan ma sun ɓata min, to na yafe masu,Allah ya ƙara mana haƙuri da juriya,nidai idan zan samu Aljannata ta ƙarƙashinka,to zan rungumi ƴaƴana in mayarda haƙuri abokin tafiyata."Ma sha Allah "Haƙiƙa naji dalin kalaman ki ƴar Aljanna,dariya tayi ta wuce madafa domin sama masu abinda zasu ci don yaran na can na cancara mata gyaran sashenta duk a gyare yake haka kawai su ka ƙirƙiri sabon gyara.

BAYAN SALLAR MAGRIB

Zaune suke dukan su suna fuskantar Ammi wacce ke masu bayani akan muhimmancin TSALKI ta ce"Shi tsalki wajibi ne kuma hanya ce ta tsaftace jiki,mata da yawa na fama da matsalar tsalki,wata maccen batan san menene tsalki ba,bata ya ake yinsa ba,shiyasa nake son kusan shi duk da tun kuna yara na koya muku,kuma ina yawan kula da yadda kukeyi amma darasin mu na yau akan tsalki ne, shin kun san

*MENENE TSARKI?*

Bismillahir Rahmanir Raheem; "إن الله يحب التّوّابين ويحب المتطهّرين" Tsarki na nufin tsafta, Amma a shari'ance tsarki na nufin tsaftace jiki daga hadasi babba da karami, da kuma dukkannin kazanta daga jikin dan adam da tufafinsa da wuraren yin ibadarsa.

Idan aka ce hadasi babba ana nufin: Dukkan abin da zai wajabtawa mutum yin wanka na tsarki saboda faruwarsa. Kamar fitar maniyyi saboda jima'i ko saboda sha'awa, ko haila, ko nifasi.

Idan kuma aka ce hadasi ƙarami ana nufin: abinda zai wajabta mutum wankewa ko goge wani sashi na daga jikin dan adam. Kamar fitsari, kashi, ko jin rauni ƙwata da dai sauransu. ku lura cewa ibada bata inganta sai da tsarki. ya kamata ku san

*RABE-RABEN TSARKI* Tsarki ya rabu rabo biyu, tsarkin kari, da tsarkin dauɗa. Tsarkin kari kamar wanka daga Janaba, tsarkin dauda kuma shi ne tsarki daga bawali ko (kashi). Abubuwan da ake tsarki dasu su ne ruwa tsarkakakke ko ƙasa tsarkakakkiya don yin taimama, ko hoge da sauran su ina fatan kun gane?

Nabeela ta ce "In sha Allah,Ammi mun gode Allah ya saka maki da alheri inji Aysha,Yaseera ta ce"Ammi haƙiƙa muna alfahari da samunki a rayuwa haƙiƙa duk ƴaƴan da su ka samu uwa ta gari kamar mu,to abin azo ai masu barkah ne."

Murmushi tayi tace "Allah yay muku Albarka,daman haka ake so uwa ta kasance mai koyawa yaranta halaye da ɗabi'un kirki,ba wai a makarantar islamiyya kaɗai ake koyarwa,uwa ma makaranta ce mai zaman kanta..."

To fa gareku iyaye shin a matsayinki na uwa sau nawa ki ke zaunar da yaranki kina karantar da su?

Sau nawa ki ke koya masu halaye da ɗabi'u nagari tare da tarbiya mai kyau?

ƳAR MUTAN DIKKAWA CE [11/9, 8:35 PM] Nabila Dikko: 💄💄 *UWAR ƳAN MAATA*💄💄

💄💄💄💄💄

*NA*

*NABEELA DIKKO*

*EXQUISITE WRITERS FORUM (EWF)*

_Home of Brilliant Writers forum_

_LABARI_

_TSARAWA_

_RUBUTAWA_

_HAƘƘIN MALLAKA_

_ƳAR MUTAN DIKKAWA_

BABI NA 42/43

*BARKA DA JUMMA'A ƳAN UWA MUSULMI,ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRAN DA KE CIKIN WANNAN RANA,ALLAH YA KAWO ZAMAN LAFIYA DA CI GABA MAI ƊAUREWA A CIKIN ƘASATA NIJERIYA AMEEN.*

~MASOYAN UWAR ƳAN MAATA INA JINJINA DA FATAN ALHERI~

*Maata Maata Maataa iyayen nagarta💃🏻💃🏻*

Shin kin iya girki? Idan kin iya wane iri kikafi ƙwarewa akai?

To ba haushe ya ce dai ko kona da kyau ka ƙara da wanka🛀🏾.

Ina muku albishir da cewa Season 7 sun shirya tsaf dan koyar daku yanda zaku haɗa cake na celebration kala kala, da kuma donuts ga kuma bonus recipe na yanda zaki haɗa lemo💃🏻💃🏻💃🏻.

Duk wannan garaɓasar za'a haɗata ne da Videos kamar agabanki a keyi💃🏻💃🏻💃🏻. Baya ga haka kuma zamu baki damar mallakar pdf da zaki ajiye abunki a waya dan gaba.

Idan bakya sauyawa yara abincin makaranta kullum sai indomie wannan damar ki ce.

Duk wannan abin zaki iya shine da garaɓasar Naira dubu ɗaya kacal 1k💃🏻💃🏻💃🏻. Maza biya kuɗinki a nan lambar akawunt ɗin. 0026971316 Gtbnk Balkisu Musa Galadanchi.

Saiki tura shaidar biyanki ta nan. 07084161619.

Ku tuntuɓi wannan lambar domin ƙarin bayani. 08039424298.

Sai an gwada akan san na ƙwarai.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull